Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na xaune hankalinta baya jikinta sosai,


Sanda xasuje da fauxie suka je gida bayan sunyi godiya, gida suka nufa sunyi parking sun fito dai dai da fitowar baba danashi escort a bayansa, daga Iman har Deedah ba Wanda ya kallesa, fauxie Kuwa tunda suka haďa ido dashi take harararsa tana Jan tsaki da qaramin bakinta,

Ya tsaya yana kallon yarinyar cikin tsananin mamaki har suka fice,

Ke tsakin me kike, wakike harara haka? Cewar Deedah

Yaya babane, I hate him,
Yayi shiru kawai.....

*

Tana tsaye tana xare safar hannunta jikinta har wani rawa yake idanunta sunyi jawur,

Safiyar yau sau uku tana karban haihuwa jaririn yana mutuwa, abinda bata taba samu ba,

Lafia Lau suke haihuwa komai normal but kafin ta gama yankan cibi jaririn xai mutu,

Nurses ďin da take aiki tare dasu taga damuwa a tare da fuskokinsu da kyar ta iya jan qafafunta ta nufi office ďinta da file guda uku a hannunta na dead case,


She is not happy today duk da san basuda tsawon Numfashi a duniya ne, taja numfashi a hankali tana kallon time,

'wow fauxie is back from school, so batason barinta ita kaďai a gida saboda baba karka ya cutar da Ita, ta tashi ta soma haďa kayanta, ta fito daga asibitin,

Ta buďe motar ta xuba shirgin dake hannunta, wata nurse ya qaraso da gudu tana haki,

"Dr fatyma ","Dr fatyma",
ta juya tana kallonta harta qaraso,

'kixo ki taimaka please wata patient aka kawo yanxu, baxata iya haihuwa da kantaba and she is also bleeding, ta yatsina fuskarta,

'I have alot to do at home, ki Kira Dr Fulani ko Umayma,

'duk sun shiga meeting basu fito ba har ynxu,

Kasancewarta Mai sanyin xuciya Kuma xuciyarta Mai laushi da haquri batada Wulaqanci ko kaďan ya Sanya likitoci da nurses suke qaunarta har patient ma domin ta iya tafiyar da marar lafiya cikin sauqi,

Ta rufe motarta suka koma cikin asibitin,

Tana tsaye akan matar sosai ta galabaita da kyar Iman ta samu ta ciro yaron, kuka yaron keyi kafin wani lokaci Kuma sai sukaji shiru, dubawar da xatayi baya Numfashi, wannan Karon har xufa ke xubowa daga goshinta, baxaka iya gane wane irin yanayi take kai ba,

Cikin qarfin hali ta miqawa nurses jaririn, ba Wanda ke xarginta da komai sai dai yau sun rasa gane meyasa jariri baya tsayawa a yau, ta wanke hannunta kana ta fice nurses su gyarata.

4:00pm


Deedah ya dawo gidan tayi mamakin ganinsa ta tambayesa, ya gayamata ynxu 4 yake tashi daga gurin aiki har Sa'eed ma,


A yanda ya lura tana cikin damuwar sosai sai ya tambayeta, ta kasa boye masa damuwarta ta xaiyana masa komai, ya dawo ya xauna kusa da ita,

Ba abin damuwa bane Iman, duk Wanda kikaga ya mutu lokacin sa ne yayi, inace agaban nurses kike karban haihuwar, ta gyada kai tana kallonsa,

'so kinga ba Wanda xai xargeki kawai su ba rayayyi bane, ki riqa addua a kowane lokaci idan zaki shiga haihuwa,

'shikenan nagode,
'haďa min ruwan wanka, ta tashi tana faďin,
'anjima xn fita super market,
Sai da gabansa na faďi daya tuna anjima xasu shiga wurin,

'ki canxa super market,
'meyasa ta tambeyasa tana kallonsa da mamaki,
'ba komai amma kada kije can,
'customers ďina duk acan suke Kuma abinda xn siye xn sameshi a can batare dana wahala ba,
'you can make customer in any where, banason kije Kuma kada kije, tayi shiru batare da ta tankaba tayi shigewarta toilet,

To 6pm ta shirya ta nufi super market lokacin Deedah ma ya fita, bataga dalilin dayasa xata canxa guri ba bayan ga inda ta saba siyayyarta, tabar Fauxie gida tana shan golden morn,

tana cikin super market din ta juyo Kukan bindiga, mutanen dake ciki suka soma fita da gudu wasu Kuwa na neman mafaka,

Ta rikice ta rasa ta Ina xatabi, oh shiyasa deedah ya hanamata xuwa amma ta dage taxo,

Tana tsaye ta hangosu suna shigowa wasu sun tsaya daga waje ko wane fuskarsa a rufe idanunsu ne kawai a waje,


Sosai sunyi barna a ciki Kuma sun kwashi kuďi da yawa, Deedah Kuwa baiyi niyar shiga ciki ba amma tunda yaga motar Iman a waje hankalinsa na tashi ransa inyayi dubu ya baci wato sai da taxo, da bindiga a hannunsa ya shiga yana nemanta tsoronsa kada a harbeta,

Iman Kuwa jikinta rawa yake sosai kayan dake hannunta duk ta xubar burinta taga ta fita daga ciki, tana lababe kada su ganta dan taqi kwanciya a qasa kamar yanda sauran mutane sukayi,

Kicibis sukayi karo da juna, a raxane ta juyo cikin tsoro har hawaye sun soma xubo mata, yayi Saurin toshe mata baki da tafin hannunsa ganin xatayi masa ihu, qamshin turarensa ya daki hancinta gabanta yayi matuqar faduwa bai bari sun haďa ido ba yayi waje da Ita, ita kuwa idanunta akan fuskarsa tana son gane wani abu,

Yana fitowa ya cillata a waje,tayi tangal tangal xata fadi,wani ya saita bindiga xai harbeta yayi Saurin katsesa,


'Nooo don't shoot.....
tayi saurin tsaida hankalinta jin muryar da ta fito daga bakin mutumin daya fito da Ita waje kafin ta juyo tuni mutumin yabar gurin bata gansa ba ta soma waiwaye,

'ke kibar gurinnan kada na ďauki numfashinki a ynxu....

da sauri ta juya jikinta har bari yake saboda tsoro da raxana.



My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina....*


©fertymerh Xarah 💞

28


Tana shiga motar ta tabar gurin, bata jima da ficewa ba suka fito dai dai da qarasowar police,


Duk ynda sukayi basu ci nasarar kama ko ďaya ba kuma sunqi su bisu saboda suna tsoron makaman dake hannunsu,

Deedah kuwa har sukaje suka kai Kuďin baya cikin walwala, iman ta taka dokar da yabata, da wani abu ya same ta fa, sai ya nufi gida bayan sallar isha'i,

Niyarshi yau sai Allah kaďai xai saukar dashi daga fushinshi,
'duk daďin bakin nan nata da tattausan labbanta masu mantar da wani ďa namiji 'duk wani jinkai taqama da muqaminsa,
'duk kissa da kisisinarta,
'duk lailaya da rarrashinta,
'duk taushin hannunta,
'duk kukanta da shagwabarta sunyi kaďan su sauke fushinsa akanta,

Amma Kuma sai me suna haďa ido da ita duk sai yaji jikinsa yayi sanyi, wani sonta na ratsa xuciyarsa, sai ya ďauke kansa daga gareta ya nufi ďakinsa, fauxie na yaya sannu da xuwa bai tankata ba, iman Kuwa kallo tabisa dashi kallone na tuhuma,

ta dawo da kallonta ga fauxie,

'sai me ya rage kuma?
'anty saura tracing,
'ke baxaki iya tracing cow bane, kiyi da kanki a exam baxaki ganni ba ballantana kiyi tsammani xn maki,

tayi shiru tana kallon littafin, pencil a bakinta ta dubi Iman,
'anty yaushe xaki kaini inda Amira,
'ba ynxu ba sai kunyi hutu,
ta cigaba da tracing Iman na gyara mata harta kammala, ta maida littafin a Jakarta, fauxie ta kwanta a jikinta tana waqe waqenta na makaranta har tayi barci, iman ta dubeta har wani daďi taji datayi barci da wuri, Fauxiya akwai rigima masu aikin gidan ma bata bari ba, ga surutu kamar hauka, ta dubi qaramin bakinta ta tsukeshi sosai, tayi murmushi ta cigaba da kallon da takeyi,

Ta jima sosai kana ta ďauki fauxie tayi ďakinta da Ita, addua tayi mata dai dai kunnenta kana ta fice,

Deedah na xaune da laptop ďinsa ta shigo, fuskarsa ba walwala batasan meke damunsa ba, taje ta sauya kayanta xuwa na barci kafin ta dubesa,

'kagayamin dalilinka na hanani xuwa super market yau, kamar baxaiyi mgn ba sai Kuma ya bata amsa batare daya kalletaba,

'meyasa tun farko baki nemi sanin dalilin ba sai ynxu bayan kinje kin dawo,

'na tambayeka ne baka gayamin ba shiyasa naje cos baka taba hanamin xuwa ba,

'ban taba hanaki ba kuma dana hanaki sai kikaje saboda bn isa da ke, da wani abu ya sameki fa?

'taya akayi kasan naje can? ya ďan dubeta,
'labari naji kuma an gayamin har fito dake akayi waje,

'Waye ya gayama, ai Kaine Deedah, kagayamin ko Kai Waye xn jure komai a rayuwa amma banda xama da barawo, ya mata wani irin duba

'ni ne barawo Iman, ni kika jifa da wannan mummunan kalma,

'Naji muryanka Deedah, Naji qamshin turarenka duk da banga fuskarka da idanuwanka ba, idan xargin da nake Gaskiyane ka cutar da rayuwata Deedah,

'wannan ba hujja bace Iman, am a good man with a good personality, kowa ya sani kema shaidace, turare bani kaďai ke dashi ba kuma na maxa ne, murya Kuma amonta kikaji amma bani bane banje super market ba sai dai kuma an gayamin an ganki wani ya fito dake, Waye shi? Miye haďinki dashi daxai taimakeki har ya riqa hannunki,

Hankalinta inyayi dubu ya tashi, qafafunta na neman gagarar ďaukarta, muryarta har rawa takeyi musamman yanda taga fuskarsa a ďaure kada wannan dalilin ne yasanya yake ta fushi tun ďaxu,

'ni bakomai tsakani na dashi, ban sanshi ba bansan dalilinsa na taimakona ba, nayarda ya riqa hannuna saboda turarenka danaji a jikinsa Ina xaton kaine,

'saboda kin daukeni barawo, ban yarda dake ba idan ba kin sanshi ba baxai taimake kiba,

Hankalinta ya tashi ta soma rantse rantse tana hawaye, yana kallonta yaji daďi cos ya sami dabarar wanke kansa,

'Ni yau kake xargi, shekara nawa muna tare dake,

'kema xargina kike yi bakiduba tsawon lokacin da muke tare dake ba kai tsaye xaki kirani barawo,

'ban tabbatar ba Ina so nagane ne amma kayi haquri baxan qara tsallake umarninka ba, kuma ba xarginka nake ba kawai hasashe ne,

'nima hasashe ne, xo ki kwanta, ta saki ajiyar xuciya fuskarta da murmushi ta kwanta haďe da lumshe idanuwanta, kallonta yake kafin ya maida kansa kan abinda yake, shi kaďai yasan planning da yake haďawa su oga nas dan baxai iya cigaba da xama dasu ba, duk da ynxu yadaina fashi ya daina harbi sai dai yayi rakiya kawai ya qudira a ransa ko police suka biyosu baxaiyi harbi ba sai dai ya nemi hanyar tsira amma baxai taimaki kowa ba, lokaci yake jira.....


2 days~

Tana xaune da fauxie a falo, kanta take gyaramata, tana mamakin irin tsawo da cikar kai na fauxie, gashi da tsantsi shiyasa ba'a fiye yimata kitso ba warwarewa yakeyi sai dai kalaba,

'anty kinga baba ya ganni wai inxo yabani chocolate,

'karkije kome ya baki kada kici,

'ai anty ban karba ba, harararsa nayi nace banaso,

'good girl gwanda da baki karba ba amma kada ki qara harararsa,

'Kuma anty naganshi ya siyo sabuwar tedy xnje yabani,

_(ba tedy bace jikinta ne kamar tedy acikinta duk kayan tsafinsu ne da sima ta qara rabamasu duk ynda xasu tafiyar da alamuransu xasu yi da ita, duk Wanda tashi ta sami matsala ya sami matsala cewar Sima)_

'idan na sami lbrn kije ko gidannan sai nayi maki duka a gidannan Kuma muyi faďa dake, kibari yaya yaxo ya qara siyomaki wata,

Ta soma dariya taji daďi amma tasanya a ranta sai taje ta ďauko wannan,

*

A hospital yau ma kamar kullum ta karbi haihuwa jaririn baixo da rai ba, tana tsaye nurses xasu karbi haihuwa Kuma yaran su rayu sai ta shiga tsoron kanta, har aka tashi aiki bata qara leqa labour room ba sosai ta shiga damuwa,


Da dare bayan sun gama shirinsu na kwanciya ta sanardashi abinda ke faruwa, yayi shiru yana naxari bai taba kawo baba bane a tunaninsa sai ya qara rarrashinta tare da kwantar mata da hankali, inda yayi ta bata misalai da yawa da suka qunshi haka, yace su dage da addua Allah xai shige masu gaba, sai ta saki ranta murmushi a fuskarta taja dogon hancinsa,

Deedah ya canxa I agreed, yana xaunawa yaji matsalata ya Kuma sharemin hawaye na,

Murmushi yayi Wanda ya qara fito da kyawun fuskarsa,

'Ina son Iman da farin cikinta dole na cnxa,

'Ina son mijina, xn jure xama dashi a kowane hali... ta sumbacesa a gefen kumatunsa ta kwanta tana murmushi tana jin sonsa ta ko ina a jikinta,


Yayi mata wani irin murmushi da har abada baxai gushe daga xuciyarta ba,
Yabi bayanta ya kwanta hot kisses yake blowing ta kowacce kusurwar jikinta, ita kanta batasan Ahmed ya iyasu ba sai a yau ya mantar da Ita damuwarta, ya ďauke ta ya jefata a duniyar soyayya harta manta damuwarta da halin da take ciki har batasan lokacin da tasa hannu ta rungume abinta sosai a qirjinta ba.

Asuba ta gari Iman & Deedah,


Getting better, tnx for your du'a, still nid ur prayers.

My wattpad Phertymerh1

*BABANA DA MIJINA....*


*©Fertymerh Xarah 💞*


29



Dr. Deen ya fito daga office ďinsa hankalinsa a tashe, yanayinsa xai nuna ma baya cikin kwanciyar hankali,


Kicibis sukayi karo da juna, files ďin dake hannunta suka xube a qasa,

'oh gosh, am sorry Dr. Fatyma...... sai ya fice da sauri, tabi bayansa da kallo bayan ta girgixa kanta kana ta sunkuya ta kwashe files ďin ta fice,


Kallo ďaya yayi mata ya gane she is in bad condition, jikinsa har rawa yake Idanunsa sun kawo kwalla ya sunkuya ya sumbaci goshinta haďe da sarqe hannunsa cikin nata,


'I don't want you to die, pls karkije kibarni, my life will be useful without you,

Ta rumtse idanuwanta cikin azabar ciwo, hawaye ke fitowa a idanuwanta,

'yaushe xn haihu Deen? ya dubi cikin nata kafin ya maida kallonsa gun ta,

'da sauran lokaci but bari na duba Merah yaxo ya duba ki, ya fice da sauri.......

*

'Am tired salima, nagaji da wannan hali naki, aure xn qara.....


Hankalinta inyayi dubu ya tashi da jin kalaman Sa'eed, ta juyo tana kallonsa bayan ta jefar da wayar dake hannunta,

'aure fa, meyasa Sa'eed?
'you know the reason and you are asking me why? ni xn xauna na koya maki yanda xaki tafiyar da rayuwar auren kine, can you imagine wai Mai aiki yau ke wanke min undis, oh god wannan wace irin rayuwace da tonon silili, Ni banida sirrin kaina komai nawa sai mai aiki tasani instead of you,


'ynxu saboda wannan xaka qara aure Sa'eed, to kayi haquri baxata qara wankewa ba, xn riqa haďawa mai wanki duka yana wankewa hope is ok?


Yayi shiru Kamar ya rufeta da duka yakeji, ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu kallonta yake cikin tsana da takaici yana tuna soyayyarsu kafin aure yanda take kula dashi kamar xata haďiye shi dan so, ynxu sunyi auren ba kulawa, idan mai aiki bata mishi ba shi xaima kansa, ruwan wanka ma shike haďawa kansa, barin ma ta kansa yaransu da basa Samin kulawa, dole xai qara aure, amma wa yake so waxai aura?


Xuciyarsa nayi matuqar bugawa, matar amininsa yakeso, fatyma yakeso, he will be happy with her, she is loyal to her husband inama shine, ynda yaga tana kula da Deedah bai damu ba, ya rumtse idanuwansa, yana matuqar sonta, yana son bata kulawar da ta rasa gun miji itama ta bashi kulawar da bai samu gun matarsa ba, ganin yayi shiru salima ta matso,

'kayi haquri xn gyara, ya dubeta Idanunsa jawur,
'kiramin Indo,
'me xatayi ma, gayamin xnyi ma,
'ki kiramin Indo nace..... ganin yanayinsa ya sa ta fice da sauri bata jima ba sai gata sun dawo tare, Indo ta tsugunna gabansa, kallonta yayi,

'xaki aureni Indo..... Tambayar ta xo mata a baxata ta ďago tana kallonsa wani ihu da salima ta sanya sai da suka tsorata gabaki ďayansu, tayi Kan Indo xata daketa ya tareta,

'wallahi ka aureta sai na kasheta na kasheka, Baka isa ba Sa'eed, ka cuceni ta soma kuka sosai, yayiwa Indo alama ta fice, ta fita da sauri ya juyo gareta fuskarsa ba alamar Wasa,

'believe me salima and I mean it, idan har baxaki gyara halinki ba, aure xnyi, I can't continue like this..... ya juya xai fice sai Kuma ya juyo,

'karki yarda ki taba Indo ko ki korata gidannan, idan tabarshi kema kin barshi dan bakida amfani acikinsa......

Salima ta xauna gefen gado ya shiga duniyar tunani dole xata cnxa halinta ta kawar da Indo daga mijinta,


*

Dr Merah da Dr. Deen ke tafiya suna tattauna Mgnr ciwon matarsa har suka isa ďakin haihuwa,

Har ynxu da sauran lokaci Deen, in lokacin yayi bata haihu ba dole xa'a mata tiyata,

Deen ya sauke numfashi da kyar yana kallonta itama idonta akansa tsoro ya cika xuciyarta gani take kamar baxata tashi ba,


Merah ya cigaba da faďin, I don't want to miss my flight so xn damqawa Dr fatyma case ďin, ko tiyata ne xata iya mata,

'Shikenan Dr. Merah, a tare suka fito suka nufi office ďinta,
Tana xaune tana duba wasu takardu suka shigo, ganinsu ya sanyata cire farin glass ďinta kana ta tashi cikin girmamawa tana gaidasu,

'Uhm likita case ďin matar Dr Deen, xn damqa miki, idan bata haihu ba ayi mata tiyata ga files ďin ta, jikinta ya ďauki rawa ta dubesa,


'why me Dr Merah, kabawa wani case ďin, am busy patients sun min yawa,

'I trust you fatyma, help me, Phoenix xnje by 10 o'clock, I nid to see sultan tun last week baida lfy so I don't want to miss the flight....


'but likita, amma.... uhm.. Muryarta na soma rawa hankalinta ya tashi,

'why are you behaving like this fatyma, wannan bashine Karo na farko da kika soma tiyata ba, ya ajiye file ďin ya juya da sauri ya bar office ďin, ta maida kallonta ga Deen tuni idanunta sun kawo kwallah,

'what's wrong likita? ta girgixa kanta bayan ta ďauke guntuwar kwalla da ďan yatsanta, ta ďauki file ďin tana dubawa,

'Hajara Deen, shine rubuce akai, ta rufe file ďin kamar xatayi kuka tsoronta ďaya ta karbi haihuwar jaririn yaxo ba rai tafi kowa sanin Waye Dr Deen mutum ne mai matuqar son yara ya jima yana kwadayin haihuwa sai wannan karon matarsa ta samu, yana aiki a paediatric, amma saboda son da yakewa matarsa baxai misaltu ba, bashida buri ko mgn a asibiti kamar ita musamman da xata haifa masa yaron, idan yaron ya mutu a hannunta fa.....

'please fatyma let's go.... ya Katse mata tunani, tayi firgigit tana kallonsa kafin tabi bayansa,

'naquda taxo gadan gadan sai dai baxata iya haihuwa da kantaba dole yasa hannu ayi mata tiyata, ta Kira nurse's suka turata theater room harda Dr. Deen aka shiga,

Komai akan idonsa yanda fatyma ke tafiyar da aikinta, yana kallon lokacin da ta fasa cikin matarsa nurses na taimaka mata, tana ganin jinjirin ta kasa cirosa saboda tsoro Kuma yana raye, sai tayiwa wata nurse da nuni akan ta ciro jaririn da kanta,

Bayan ta ciro suka nufi gurin gyarashi Deen yabi bayansu farin ciki fal a xuciyarsa,

Iman murmushi tayi cikin samun nasara kana ta soma ďinke uwar,

Baba dake ďakin a labe kusa da Iman yana jiran ta karbi haihuwa ya xuqe jinin jaririn ya bata rai sai dai tsawar da sima tayi masa ta tsoratashi, ba Wanda yaji sai Shikadai kamar yanda bamai ganinsa,

_'ka ďauki jinin matar tunda ta hana jinjirin, ka kashe uwar._


Bayan sun kammala gyara maman suka nufi amenity da Ita, batasan meyasa take jin mutuwar jiki ba, har wani Xaxxabi takeji ga xufa dake karyo mata ta ko ina,


Ta fito ta sami Dr Deen rungume da jinjirin sai faman murmushi yake, farin ciki fal a xuciyarsa, ta leqa yaron kyakkyawan gaske ne tana son karbarsa tana tsoro, murmushi kawai tayi a xuciyarta tana Allah ya raya yaron,


Wata nurse ta fito da sauri tana faďin,

'she is bleeding through her nose and mouth,

'who? Fatyma ta tambaya hankalinta a tashe, shima Deen ya juya yana kallon nurse ďin jin ko Waye,

'Mrs Deen....

Fatyma da Deen suka nufi ďakin, bakinta da hancinta sai jini ke xuba, Dr ya miqa jaririn ga wata nurse ya nufi hajara ya rungumeta xuwa jikinsa, tana son masa mgn ta kasa, akwai abinda takeson gayamasa bakinta ya qi buďuwa haqoranta sun kafe,

Fatyma Kuwa kusan mutuwar tsaye tayi kamar mutum mutumi ta xama sai kallo da take binsu dashi idanunta na fitar da kwalla, kafin wani lokaci rai yayi halinsa batasan da haka ba sai da taji Dr Deen yana faďin,

_'Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un_ kusan sau uku, kafin ya ďora kansa jikin matar yana kuka, itama batasan sanda Kukan ya xo mata ba.



My wattpad Phertymerh1

[20/03, 5:12 p.m.] Pherty 🎤👯:


*Babana da mijina......*


©Fertymerh Xarah 💞


30



Da kyar ta iya janyo qafafuwanta ta fito daga ďakin, idanunta sunyi luhu luhu sun kumbura, ga xuciyarta dake tashi kamar mai jin amai,

Tana tsaye a corridor tare da Dr Umayma taga an fito da gawar, ta ďauke kanta gefe hawaye sharrrrr kamar da bakin fanfo,

'ya salam Dr fatyma, kinbi kin damar da kanki tunda bake kika kashe ta ba miye na kuka haka, kwanakinta suka qare, ba itace gawar farin a hannunki ba meyasa kika damu,

Ta girgixa kanta tana share kwalla,
'ba komai, ina tausayin Dr Deen ne, da jaririn da aka bari,

'hakane amma kidaina damar da kanki,

Iman ta matsa gefe da sauri tana kwararo amai, Dr Umayma sai sannu take mata, ta bata pure water dake hannunta ta kuskure bakinta,

'xo muje na duba ki, banyarda dake ba likita, iman murmushi kawai tayi tabi bayanta,

'oh God, jininki ya hau sosai 180, narasa gane kanki fatyma, meke damunki,

Iman ta sunkuyar da kanta qasa tana faďin,
'bnda damuwa bayan stress, bana samun barci I don't know why, ga aikin asibiti hutun da kuke samu bana samu, komai Dr fatyma komai sai ni fa......

'Gaskiyane Kuma fa likita, amma ai Kuna da farin jinine, mgnr gsky ma cikin mu kin fimu haquri shiyasa kowane likita ya tashi kece,

Iman ta sauke ajiyar xuciya tana yatsina fuskarta,
'Ina ji inada ciki ne, na jima bnsha tablets ďina ba,

'nima nayi xaton haka, Allah ya tsayar da wannan?

'Amin ta faďa xuciyarta a raunane,



Tun da ta dawo gida take kwance, sallah kawai tayi abincima ta kasa ci, fauxie na gefenta sai surutai take mata,

'kiyi shiru haka fauxie, ke bakya gajiya ne,

'anty kema kina rubuta noise makers ne? Iman ta dubeta,

'eh idan bakiyi shiru ba gobe xnsa anty tayi maki bulala, I fauxie ta matsa baya kaďan da Ita tana kallonta a shagwabe,

'anty ai ba class bane keba monitor bace,
'tor kije falo kiyi surutunki ko kije indasu adama, kina damuna anan Inaso nayi barci, fauxie ta dawo jikinta ta kwanta tana faďin,

'anty jiya nayi mafarki,
'mafarkin me,
'baba ya mutu..... sai da gaban Iman na faďi ta dubi yarinyar,
'Kuma anty, malam yace duk wanda ya mutu baya dawowa, wai xa'a sanyashi a rami a rufe da qasa, baxai qara cin abinci ba kuma baida friends shi kaďai xai xauna wai hakane anty? Iman ta gyada Kai tana kallonta,

'Kuma anty wai malam yace idan ka riqe sallah itace xata tayaka kwanciyar kabari,

'idan ka riqe karatun qur'ani watarana xai yi ceto a gareka, anty wai hakane? ta gyada Kai tana kallonta har lokacin jikinta a sanyaye yake da Kalaman yarinya,

'tor anty idan baba ya mutu shi qur'ani baxai cecesa bane?

'inji waye ai shi musulmi ne,

'tor anty ai baya karanta qur'ani, kuma baba baya sallah, na gayawa malam babana baya sallah a class jiya,

Iman ta xaro ido tana kallonta,
'kin gayawa malam baba baya sallah ke uban Waye ya gaya maki baya sallah, (ta kai mata duka ta goce tana tunxure baki),

'a'a kajimin yarinya, kewai ba aljannu akan kine Anya ke kaďai kike rayuwa kuwa? dole sai a gabanki xaiyi sallah ne,

'anty nace malam yaxo yayiwa babana mgn ya dinga sallah shi kaďai nace kuma anty a.....

'shut up silly girl, why can't you control your mouth fauxie, angayamaki agaban kowa ake faďin kowacce magana ne, shikenan is your life friends ďinki basu sanni ba ke kaďai suka sani xasu riqa cewa babanki baya sallah tunda baki iya bakinki ba kuma kowa xai sani kiji kunya,

'anty bana jin kunya cos he is not my father, ai yace shi ba babana bane indai na ce masa baba, wai yaya ne babana, hakane anty?

'ke xo ki fice min daga ďaki inba haka ba bakinki xaiyi jini, ta diro daga Saman gadon ta ďauki tedy ďin ta tana kallonta,

'Anty Kice adama

Please Login or Register in order to submit comment