Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ďago da sauri yana kallonta,

Ta qaraso ta xauna kujerar dake fuskantarsa fuskarta ba walwala,


'Sannu da aiki yayan fauxie, bai amsa mata ba da alama baiyi farin cikin xuwanta a Wannan lokacin ba duk da bata taba xuwa office ďin sa ba tun bayan auren su,


'Iman wannan tafiyar ta baxata fa, me kika xo yi? tayi masa wani kallo


'tambayata kake dan naxo naga mijina, ko laifine Deedah? ya girgixa kansa yana murmushin yaqe


'ba laifi bane kuma naji daďi sosai amma naga baki taba kawomin irin wannan xiyara ba,


'tace hakane, skul fees ďin fauxie na....... bata qarasa ba aka buďe qofar office ďin aka shigo,


'cwty you have been waiting da kyar umma tabarni na fito,


Yayi shiru bai amsa ba hankalinsa inyayi dubu ya tashi, Iman ta juya tana kallon wacce ta Kira Deedah da cwty, saudah ce rataje da qaramar jakarta cikin doguwar riga ta atampha, bata lura da Iman xaune a gurin ba ta isa inda yake ta sumbacesa a goshi,


'da sauri ya ture ta cikin borin kunya, me kike yi haka Ashe baki da kunya....


Ta ware idanu tana masa kallon mamaki sai alokacin ta lura da Iman dake xaune tana kallonsu,


'oh no wonder shiyasa xakayi rejecting ďina, kace rival ďita ce a banki, ta juya tana kallon Iman,


'sannu anty ya aiki, Iman ta amsa da


'Alhamdulillah cikin basarwa, saudah ta sami guri ta xauna,


'wannan yanayin yafi komai yimin daďi gani ga uwargidanka, ka gayamata matsayina na amaryarka,


Deedah ya dubeta, get out of my office saudah, ban taba sanin baki da tarbiya ba sai yau, duk iskancin ki ya tsaya kaina kada ya kai ga matata,


Dariya tayi ta gyara xamanta, Iman kallonsu kawai take kafin ta tabe bakinta ta tashi da Jakarta a hannu ta fice,


Tana fitowa sukaci Karo da Sa'eed shima ya fito nasa office, a tare suka sakarwa juna murmushi bayan sun gaisa sai suka jero tare suka fito farfajiyar bankin xuwa inda tayi parking, tun basu qarasa ba taga fitowar saudah a fusace, Sa'eed ya dubeta


'yau ina qawar rakiya fauxie bn ganku tare ba,


'fauxie na skul, school fees ďin ta naxo fiddawa gobe nake son naje na biya mata,


Yace hakane, nima Adnan gobe nakeson biya masa,


Tace ko na baka na fauxie ka haďa ka biya masu pls, ta ciro Kuďin daga jakarta ta miqa masa,


'nawa ne Kuďin,
'65,000
'barsu hannunki a Yanxu idan na tashi aiki kafin naje gida xn biya na karba gobe ina biya sai na kawo maki receipt ďin,


'shikenan Nagode sosai ta maida Kuďin jaka akan idon wasu matasa su kusan shidda da alama yan fashi ne,


'Nine da godiya, kinga Deedah kuwa? ta yatsina fuskarta


'naganshi, bara na tafi Sa'eed sai kaxo,



Sukayi Sallama ta shiga motarta ya juya cikin banki,



Tun da ta fito daga banki taga alamar kamar wata Mota na bin bayanta, ta glass take tsinkayosu motar cike take da maxa harda bindiga tana gani, hankalinta yayi matuqar tashi ta qara gudun motar sosai sai taga suma sun qara gudu,



Gudu take shararawa kan titi kamar xata tashi sama suna biye da Ita, su kansu dake cikin motar suna mamakin yanda ta iya Mota haka gashi sun kusa shiga gari xasuyi missing Kuďin da suka gani hannunta,



'world best ko asakarwa motar bullet ne, yarinyar ta kware wurin Mota sosai,


'A'a kada ku harbeta an shigo gari, asirin mu xai iya tonuwa kawai mubita muga gidan anjima muje mu karbi kason mu,



Tana shigowa layin su ta soma horn sosai tun kafin taxo gate an buďe mata ta shiga,


'kai gidan ďan siyasar nan ne Alhaji Abdallah fa,


'abin yaxo dai dai ai, muyi shiri sosai muxo gidan kasan akwai kuďi fa anan, muyi qoqari muci nasara dan naga harda yan sanda ke gadin gidan da alama Mai gidan na gari, in sunyi gardama ayi watsin alburushi kowa ma akashe.....


Sukayi dariya haďe da jan motarsu da sauri suka bar layin,



My Wattpad Phertymerh1

Babana da mijina.......


©fertymerh Xarah 💞


22



Harabar gidan maqil take da maxa da mata yan siyasa haka ya tabbatar mata da cewa baba yana gari,


Da kyar ta iya samun guri tayi parking kasancewar motocin dake gurin birjik, har lokacin jikinta bai daina rawa ba,


Taron siyasa suka gama da alama, taga suna watsewa suna shiga motarsu ďaya bayan ďaya,


Ta fito daga cikin tata motar ďauke da jakarta, ta rufe motar tayi hanyar gidanta anan taci Karo da baba ko ta ďaga fuska ta kallesa ballantana ta gaidasa, fuskarta a ďaure tamau tabi ta gabansa ta wuce batare da ta kallesa ba,


Kallo yabi ta dashi haďe da cixon labbansa cikin jin xafin halin ko inkula da ta nuna garesa a gaban mutane,



Tun kafin ta qarasa gidan take jiyo Kukan fauxie, ta duba agogon dake maqale a hannunta 11am baa isa tashi Skul ba to meya maida fauxie gida, ta hanxarta da sauri domin yanda take jiyo kukanta har cikin kanta Kuma ta tabbata baba ma yanajin Kukan yarinyar amma bai damu ba,


Tana shiga falon ta ganta jikin adama tana jijjigata sai kuka take tana kiran anty, anty,


Da sauri ta qarasa gurin adama tana tambayar meya sameta,


'hajiya tun ďaxu malamar su ta kawota batada lfy sai kuka take, Iman ta karbeta jikinta xafi sosai idanunta a lumshe da alama ta jima tana kuka yanda idanun suka kumbura fuskar tayi jawur, ta kalli adama


'amma shine kin san da haka bakimin waya kin sanarda ni ba, inda bn dawo ynxu bafa, kina nufin sai kibarta tayi ta kuka,


'kiyi haquri hajiya nagayawa yallabai babanta yace inje kawai nayi xaton xai xo ne shinake jira tun ďaxu shiru, Mtseww Iman taja tsaki ta xauna rungume da Ita tana kiran sunanta a hankali,


Sai ta buďe ido luuuu sai sukoma su rufe, taji kanta yafi xafi sosai, ta cire mata uniform ďinta tana faďin,


'ďauko min wata riga na sanya mata adama, ta juya bata jima ba sai gata ďauke da doguwar riga, Iman ta karba tana faďin, ďauko ruwa da panadol abata duk da nasan da wuya ta karbi magani,


'ai hajiya bataci abinci, foodflask ďinta komai bata taba,


'haďo mata tea mai xafi da sauri pls,


Ta sanya mata rigar,
'anty baba, kice baba yaxo anty,
'baxai xo ba fauxie kicire ranki da wannan Baban a ynxu, tashi kisha tea kisha magani, cikin kuka ta soma magana,


'Ni banaso baba nakeso yabani, anty kije dani inda baba, iman tayi shiru tana saurarenta tasan duk ciwon da fauxie xatayi idan ba baba yabata magani ko abinciba baxata karba ba tun tana qarama haka take shi yayi mata wannan sabon,


Adama ta dawo da kayan a hannunta duk rarrashinta da fauxie taqi ta karbi tea ďin,


Iman ta tashi ta fita, ta tsinkayosa tsaye tare da wani abokinsa har lokacin da sauran mutane a gidan ta qarasa batare da fargaba ba ta isa inda yake,


'baba! yaji ta sarai yayi tamkar baiji ba dama yasan sai ta nemesa tunda fauxie ba lfy, abokinsa yace bakaji fatyma na magana bane, ya juyo yana kallonta fuska a ďaure,

da kyar ta iya buďa baki tayi mgn badan ta so ba,


'baba fauxie ce ba lfy, kasan baxata ci abinci ba idan ba kai kabata ba,dan Allah kaxo ka bata,


Baiyi mgn ba ya juya yana kallon ďaya daga cikin mutanen sa hannu yayi masa yaxo da sauri, ta kunne yayi masa raďa ga mamakin Iman sai taga mutumin yaxo kusa da ita shikuma baba ya fice da abokinsa,


'hajiya gashi inji yallabai yace abaki a matsayin taimako ki Kula da qanwarki, ya miqa mata bandir na dubu ďaya, ta karbi kuďin tana juyasu a hannunta, ba dan uba uba bane da ta jefeshi da Kuďin ko xuciyarta xatayi sanyi,tana tsoron Allah ya kamata da wannan laifin, sai ta jefa Kuďin sama suka watse suka xubo qasa har a jikin baba, ya juyo a razane dan a zatonsa Sima ce ke masa ruwan kuďi kamar yanda ta saba sai yaga tsabanin haka ba shakka Kuďin da ya baiwa Iman ne tayi watsi dasu, yayi shiru yana kallonta ransa inyayi dubu ya baci a Wannan Karon irin Wulaqanci da tayi masa agaban mutanensa, kallonta yake kallonsa take duk cikinsu kowane fuskarsa ba walwala, ma'aikatan gidan masu shara da wankin motoci suka xo da gudu suna tsintar Kuďin, ta nuna su a yatsa,


'su ya dace kabaiwa Kuďin bani ba, bnxo neman taimako a gurin kaba, kuma badan fauxie ba, ba abinda xai kawoni gurinka,


Inaso in qara tunatar da kai, Annabi S. A. W yana cewa dukkanku makiyayane Kuma xn tambayi kowanenku akan yadda yayi kiwon da aka bashi,


'ya kai baba wace irin amsa gamsassa kashirya wadda xaka ba Allah ta'alah idan ya tambayeka akan wannan gobe qiyama,


'ka tuna samun Ya'ya wata baiwace da Allah yakeba Wanda yaso Kuma ya hana Wanda yaso daga cikin bayinsa, Sannan Kuma jarabawace daga Allah don yaga wanene xai godewa ni'imarsa Kuma wanene xai butulce, Ya'ya kiwone da Allah ya baka Kuma yayi alqawarin tambayarka,ta juya ta fice da sauri yana tsaye yana kallonta abokansa suna kallonsa cikin rashin fahimta tsakaninsa da yar'sa,

Har lokacin Fauxiya kuka take tana kiran baba,

Iman ta xauna kusa da ita,

'baba bayanan fauxie Kuma baba baxai xo ba, sha tea inkin sha magani inbaki chocolate kinsan yaya ya kawo maki wasu jiya, ta make kafada tana kallonta da idanu jawur,

'Ni banaso baba nakeso, anty ki kaini inda baba, wannan Karon sai ta daure mata fuska sosai ba alamar Wasa a tare da Ita, ta janyota ta matseta tsakanin qafafunta ita da adama suka mata ďure, bata wani sha da yawa ba ta kyaleta duk da acikin xafin ciwo take sai da Iman ta bige ta dan takaici ta qara rungume Iman ďin tana kuka sosai, jikinta yayi xafi sosai sai amai take yi, hakan yasa tayi mata allura, ta ďauketa tayi mata wanka ta rungumata a jikinta tana rarrashinta har tasamu tayi shiru, barci ya ďauketa, ta sauke ajiyar xuciya cike da tunanin halin da suke ciki,



Da dare Sa'eed da Deedah a tare suka shigo, sun tausaya halin da suka sami fauxie bama kamar Deedah dan har yafi Iman damuwa akan ciwonta,


Sa'eed ya tambayi kuďin skul fees ďin fauxie taje ta dauki anan take bashi lbrn Duk yanda tayi da mutanen da suka biyota kuma tana da tabbacin sai sunxo tunda taga sun dade suna dubin gidan,


Sa'eed yayi dariya yana fadin ba inda xasu xo Iman ki kwantar da hankalinki ballantana ma gida irin Wannan na siyasa ga police a gidan,


'taja guntun tsaki tana faďin na tsorata dasu da kyar nasha,


Sa'eed ya tashi da Kuďin a hannunsa yana faďin dama mata tsorone daku abinda bai xama babba ba shi kuke maidawa babba,

Iman tayi dariya kawai tana kallon fauxie dake jikin Deedah,


Duk Mgnr da suke akan kunne Deedah Kuma yasan sai sunxo tunda hartace sun tsaya suna kallon gidan, suma sun sha yin haka dole ne yayi shiri akansu dan baxaa basu ko kwandala ba,


Fauxie taqi yarda ya ajiyeta ballantana yaje ya raka Sa'eed sai yaje da Ita a kafadarsa bayan ya dawo ya kashe wayoyinsa gabaki ďaya dan bayajin xai fita a yau,


Fauxie ma ďakinsa ya wuce da Ita yasamu da kyar ya kwantar da Ita tunda tayi barci, da sauri yaje ya janyo bindigarsa bullet ya xuba mata kana ya ďura wasu a aljihunsa ya xauna yana latsar laptop ďinsa, Iman ta shigo tana tambayarsa wankan fa,


'ba Yanxu ba sai xuwa anjima ina wani abu ne, ta tabe bakinta ta fita,


Har 1:00am Deedah baiyi barci ba yana xaune kamar yanda tabarshi, Iman Kuwa tuni tayi barci, yanayi yana kallon window bai ďebe tsammani ga xuwansu ba,


Kamar a mafarki Iman taji Harbin bindiga xumbur ta miqe xaune dai dai lokacin da Deedah ya sauka daga Saman gadon,


'ina xakaje kanajin harbin bindiga ni Dama nasan sai sunxo,


'ki xauna ki Kula da fauxie ta fita da sauri,


Ta balcony ya tsaya yana kallonsu yana labe a gefe, tun daga Sama ya gane ba nasu bane sai ya fiddo bindigarsa haďe da gyarata,



Artabu aka shiga yi tsakanin barayin da yan sandan dake gurin, kuma sosai sunci nasara akan police tunda baxata suka masu, from no where suka ji saukar bullet batare da sunsan inda yake fitowa ba,


Alhaji Abdallah yanajin abinda ke faruwa ya fito da sauri shima bai sauko ba yana sama, ba'a ganinsa amma shi yana ganin kowa,


Da barayin suka fahimci inda bullet ke fitowa suka soma maida martani,


Hankalin Iman ya kasa kwanciya da Deedah, yafita bai dawo ba sai qarar bindiga kakeji ta fito daga ďakin anan taci Karo da duk masu aikin sun fito hankalinsu a tashe, ta duba ba Deedah a falo, inda take jiyo qarar bindiga can ta nufa,


Kusan mutuwar tsaye tayi qafafunta na neman gagararta jikinta sai rawa yake, Deedah da bindiga, Deedah ke harbi, ina Deedah ya iya harba bindiga, ina ya samu bindiga miye hadinsa da bindiga,



Harbi yake cikin kwarewa da gwaninta kai da Kaga yanda yake riqe da Ita kasan ba ďan koyo bane ya gwane ko yanda yake sarrafata,


Duk harbin da yake ba Wanda ya samesa illah shi da ya kashe masu mutane sosai,


Hankalin Iman a tashe ya rabu Kashi biyu, ďaya gurin Deedah ďaya gurin mahaifinta batasan a wane hali yake ciki ynxu ba(ďa da mahaifi) batasan baba yana xaune yana kallon kowa da duk abinda ke faruwa ba,


Kamar ance ya waiwaya yaga Iman tsaye tana kallonsa, ba tsoron ganin sa da bindiga yaji ba tsoronsa kada a harbeta, cikin tsawa ya soma mata mgn,


'ki tafi Iman, haka take jinta kamar mutum mutumi, Karo na biyu ya sake daka mata tsawar dana firgita ta ganin bata da niyar tafiya,

'Nace ki tafi.......
ta juya da sauri tayi cikin gida, wayarta ta nema ta Kira DPO sosai tasanshi gurin mahaifinta, ta sanardasu halin da ake ci,


Deedah Kuwa cnxa akalar bindigarsa yayi ya fito daga inda yake boye ya cnxa gurin boyo suka shiga artabun bullet sosai....



Pherty🎤👯

[04/03, 6:55 p.m.] Pherty🎤👯:


*Babana da mijina........*


©Fertymerh Xarah 💞



23


World best yakamata mu haqura mubar gurin nan tun asirin mu bai tonu ba,


Baxamu bar gurinnan ba har sai mun cimma burin mu, ko bamu samu kuďi ba muyi qoqari mu kashe wancan gaye.....bai qarasa rufe bakinsa ba Deedah ya sakar masa bullet a hannu dai dai da qarasowar motocin yan sanda, duk Unguwar ta hargitse saboda tsoro da raxana,



Deedah na ganinsu ya cilla bindigarsa qasa kana yayi shigewarsa da sauri cikin falo, duk glass ďin gidan an farfasa sa,


Iman na xaune da fauxie a hannunta sai faman xufa take ga yan aikinta xagaye da ita, ko kallonsu baiyiba ya nufi ďakinsa dai dai window ya tsaya yana kallon Abinda ke faruwa,


Sauran da basu mutum ba ana sanyasu a mota, wadanda na mutu Kuwa yaga ana investigating ďinsu,



Juyowar da xaiyi Idanunsa na sarqe da nata, ya saki wata wawiyar ajiyar xuciya kafin xufa yafara ratso masa a goshi


'karki tambayeni komai I don't have time for your question, yayi hanyar toilet da sauri yabarta a gurin,



Ya jima sosai aciki yana watsa ruwa kafin ya fito ďaure da towel iya qugunsa tana nan tsaye inda ya barta, baiyi mamaki ba yasan xarginsa take inba ya wanke kansa gareta ba yasan baxata taba yarda dashi ba, ya ďauke kansa daga kallonta ya qarasa tsakiyar ďakin, taja ta tsaya a gabansa,


'you must answer my question Deedah, meya haďa ka da bindiga,


'da ban riqe bindigar ba kina tunanin da ynxu nida ke bamu dade da mutuwa bane, abinda kike xargi bashi bane, niba ďan fashi bane kuma ba ďan ta'adda ba, what else did you want to know?


'ka sauya Deedah, kamaida qarya abincinka yayin da ka boye gskyrka,akwai abinda kake boye min kagayamin ni matarkace nice yakamata nasan sirrinka tun kafin wani yaxo yagayamin, ni nafi kowa kusanci dakai, idan kai baxaka xauna ka saurareni ba, ni xn xauna na saurareka tell me Deedah ina kasami bindiga ka dubi girman Allah ka gayamin gsky...


Gabansa ya faďi jikinsa na soma rawa,

'kifito ki faďi abinda ke xuciyarki Iman, xargi na kikeyi..... tayi saurin katsesa,


'saboda me xn xargeka, kunnena yaji Kuma naga xahiri a yau, menene xargi anan,


Hankalinsa yayi qololuwar tashi saura kaďan towel ďin dake jikinsa ya subulce ya faďi,
'me kika ji me Kuma kika gani,

Fauxie ta gayamin ta ganka da bindiga kuma yau naga xahiri da idanuna ka gayamin kai waye Deedah?

'toy gun ce fa dana siya inbaiwa Adnan na manta Sanda na siyawa fauxie tedy,


'ina bindigar? yaje da sauri inda ya boye ta dama ya riga ya siye tun lokacin dayaji fauxie na maganar da Adnan, ya ďauko ya bata ta karba tana juyata a hannunta kafin ta ďago tana kallonsa,


'wacce nagani yau a hannunka a Ina ka sama?


Yace Sanda naji kina gayawa Sa'eed lbrn barayin dana biyoki nayi xargin nima xasu xo, bayan na raka Sa'eed sai na tsaya gurin yan sanda dake waje acan na karba shine ya nuna min yanda xnyi amfani da ita, bayan Wannan ma ina gani a films ynda ake riqonta da yanda ake harbi, ni kaina nayi mamakin yanda na iya harbin bindiga kuma kinga sun kashe yan sanda gabaki ďaya nima dan na fake wani guri ne da tuni sun dade da kasheni shiyasa danaga police sun xo na jefa masu bindigar kada a ganni da Ita a xargeni da ďaukar bindigar yan sanda, believe me gsky nake gayamiki apart from this bnsan komai ba,


tayi ajiyar xuciya batare da tayi mgn ba ta juya ta fice, Ahmed yabita da kallo yana sauke numfashi da kyar,


Tana fitowa falon DPO na shigowa, tayi Saurin gaidashi,


'da fatan ba wanda akajiwa rauni fatyma,

Ta girgixa kanta tana faďin babu,


Amma sunce akwai wani nan sama dake harbinsu Waye shi, sai da cikinta nayi wani qugi ta xaro idanu tana kallonsa,


'ai sun kashe shi, ďan Sanda ne ya tsaya mana yana sauka suka harbesa shiyasa nayi gaggawar kiranka,


'Allah ya kyauta gaba fatyma,
Tace Amin ya juya ya fice da bindiga a hannunsa, ta dubi masu aikinta,

Ya kamata Kuje ku kwanta tunda mun samu kanmu Allah ya taimakemu,


Suka tashi suna mata sai da safe, taje ta ďauki fauxie har lokacin jikinta xafi rau, a yanda ta lura wuyanta ma baya tsayi guri ďaya,ko hannunta bata iya ďagawa , akwai matsala dole gobe ta tafi da Ita asibitin dan sai anyi admitting nata,


Tana shiga ďakin ta sami Deedah na waya da Sa'eed, taji yana yi masa bayanin komai kafin suyi Sallama ya tsinke Wayar, kallonta yayi bayan ya gama shirinsa na barci lokacin tana gyarawa fauxie kwanciyarta akan gadon, ya taba jikin fauxie shima yajisa xafi rau,

'Wai meke damunta ne,
'shiyasa nake son xuwa da Ita asibiti ayi mata test agani, ni kaina na rasa gane kan ciwon, Allah yasa itama baxata mutu ta barni ba, ta soma hawaye sosai....
[05/03, 8:07 a.m.] Pherty🎤👯: 'Haba ai ciwo ba mutuwa bane, kidaina wannan mgnr, ya ďauki pillow da blanket ya kwanta a qasa ya bar masu gadon, addua tayi ta shafawa fauxie kana ta kwanta,


Alhaji Abdallah bai damu da Abinda ya faru ba wannan abin yafi komai yi masa daďi a ynxu sai dai akwai alamar tambaya tsakaninsa da Deedah koda yake ma Ina ruwansa dashi a ynxu, su suka sani dama an kashe su ya huta, sima ta sha jininsu.


Washe gari sosai fauxie ke amai, duk hankalin Iman dana Deedah ya tashi a gaggauce suka yi shirinsu, yayi banki tayi asibiti da fauxie,


Paediatric ta nufa da Ita inda Dr Bakori, bata same sa ba sai ta sami Dr Lawal shi ya karbi fauxie hannunta yana duba,


Dr fatyma, fauxie ba lafia ne, tun yaushe,

'tun jiya ne,
'oh Allah shine ta koma haka, meke damunta ne,

Iman ta share guntuwar kwalla hannunta har rawa yake kamar yanda muryarta ke rawa fatanta fauxie ta rayuwa,

'Ni ma nakasa gane ko menene ke damunta, kana ganin hannunta ďaya ma bata iya ďagashi, wuyanta baya tsayi guri ďaya abinci tun na jiya da safe ne,

'Bari muje lab ayi mata test mugani, yana gaba tana bayansa, binni binni take sharar kwalla, jikinta duk yayi sanyi da wannan ciwo na fauxie, a hanya suka haďu da Merah da mutanensa suna shigowa, yau da alama sarauta yake ji ganin kayan sarautane a jikinsa, ga kuma kujerar xamansa ana biye dashi duk inda xaije,


Sosai ya nuna damuwa tare da tausayawa halin da inlaw ďinsa take ciki, akwai Wanda xaima operation da safennan shine dalilin fitowarsa yau da wuri,


A lab duk iya bincikensu an kasa gano matsalar, wasu result ďin ma ba'a kawo ba, sai akayi admitting ďin ta, aka sanya mata drip da akaxo allura ne taqi yarda sai da Merah ya karba yayi mata da kansa, kuka take tana sai ta dakesu idan ta tashi, dariya suke sosai Wanda ya qara sanyata fashewa da kuka tana kallon Iman dake murmushi,

'anty kema sai na dakeki tunda kike min dariya,
'na bari fauxie,

Dr Lawal ďa Merah suka fice aka barta da Iman,

'Anty kinga baba ya bani biscuit jiya naci,

'biscuit Kuma, yaushe?
'da xnje Skul da safe,
'ke kuma sarkin Kwaďayi, duk biscuit ďin da kike dashi gida Wanda yaya ke siya maki bai maki ba sai kin karbi nashi, mutumin da baya sonki,

'Anty ai a islamiya akace duk wanda baya sonka idan yabaka abu kayi bismillah ka karba, kuma harda qul'huwallahu nayi, Iman ta soma dariya tana kallonta,

'sai kace wani mugun abu fauxie, wannan ciwon ya rikitaki da yawa tunda har sambatu kikeyi,


'Anty kicewa baba ban yafe masa ba, Iman ta dube ta da mamaki,

'ba'a cewa babba ba'a yafe masa ba, me yayi maki,

'baya sona, kuma baya sonki,
'ba abin damuwa bane fauxie, kiyi addua kisami sauqi kinji,
'Anty idan na tashi sai na kashe baba,

Kusan faďuwa Iman ta tashi yi, gabanta yayi wani irin faďuwa,

'kiyi shiru haka fauxie, meya hadaki da kissa Allah ya tsare ki, rufe ido kiyi barci,


'Anty jiya nayi mafarki baba yace sai ya kasheni Kuma kema sai ya kasheki Sannan ya kashe yaya, anty harda dariya yakeyi nima sai na kashe shi,


'Subhanallah, ai mafarki ba gsky bane fauxie, mutum baya mutuwa sai lokacinsa yayi,

Ganin abin na fauxie bana sauqi bane sai ta Kira Deedah a waya akan yaxo, yace yana hanya saboda surutanta suna tayar da hankalinta dan ma ita kaďai ce a ďakin ba mutane,


Tana xaune taga gadon fauxie na rawa, ga mamakinta sai taga fauxie na qoqarin tashi ta sauko yayin da take nuna mata qofar shigowa,


'anty kinga baba sai na kashe shi, anty ki riqe min shi in kashe shi,

Iman ta juya bata ga komai ba sai ta taso da sauri ta riqe fauxie, sai ta soma fisge fisge tana sai ta kashe shi, hankalin Iman yayi matuqar tashi dan da alama Wannan Karon bata ima fauxie wani qarfi tajita dashi, suna haka sai ga Deedah da Merah sun shigo da sauri suka qarasa suka riqeta su biyu, sai fisge fisge take tana sai ta kashe shi,

Sosai al'amarin fauxie ya bawa Iman mamaki a yau, bata taba ciwo irin Wannan ba ko aljannu ke ruďata, sai ta koma gefe ta xauna qasa dirshan tana wani irin kuka sosai😪


My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah 💞


24


Fauxie na neman gagararsu sun kasa riqeta su kusan biyu, tunanin da sukayi kamar mai shafar aljannu ya Sanya suka soma yi mata karatu,


Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai, wannan wace irin rayuwace, daga wannan sai wannan?


Fiye da minti talatin kafin su samu abin ya saketa sai dai bakinta bai fasa furta sai

Please Login or Register in order to submit comment