Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kashe shi,


'Waye xaki kashe? Merah ya tambayeta,


'baba xn kashe, ina tashi sai na kashe baba, yaya ka ďauko baba in kashe shi, baba yana min dariya dan banida lfy, baba yace sai ya kashe anty da yaya nima sai na kasheshi,


Duk sun ruďe da kalamanta wataqila xafin ciwone ke sanyata sambatu haka acewar Merah, Deedah kamar yaso ya fahimci wani abu agame da maganarta sai ya sunkuya haďe da riqo hannunta,

'yaushe baba yace xai kashe mu fauxie? Ina kika ganshi yana miki dariya?


'ai nayi mafarki jiya yace sai ya kashemu,kuma Yanxu yaxo yana min dariya,


'ina kika ganshi yana dariya, suka tambaya lokaci ďaya,

Ta nuna masu qofar ďakin inda taganshi tsaye a ďaxu yana tsoratata da kamanni iri iri, tana faďin

Ai anty ta ganshi na nuna mata shi, iman ta tashi a firgice tana kallonta,

'banga komai ba fauxie,

Deedah ya gyara tsayuwarsa wannan ba ciwon asibiti bane, Merah ma ya tashi yana faďin nima Abinda na fahimta kenan dan haka xnje da fauxie gidana, wazirina xai dubata harta sami sauqi yasan irin waďanna matsalolin,


Deedah yace shikenan nima xn qoqarta anan gida mugani,


Iman batace komai ba illah hawayen da takeyi har Merah ya ďauke ta suka fita,

Yana fitowa fadawansa suka taso xasu karbeta ta qanqameshi, yace su barta,


Iman da Deedah na tsaye ya sanyata a mota suka bar asibitin, wani irin kuka Iman take gwani tausayi, ina fauxie ta haďu da aljannu yarinyar da kullum take tofe ta da addua, Deedah ya riqo ta,

Is not time to cry Iman, pray for her,

A yanda takeji ko ta tsaya asibitin baxata iya aikata komai ba hankalinta xai karkata gun fauxie sai ta nufi gida Deedah Kuwa ya nufi gurin aikinsa tare da qudurin idan ya dawo xai sami babansu yasanshi yasan kowa shi, idan har ya kashe fauxie xai iya tona sa idon duniya Idan Kuma bai bar fauxie ya daina wahalar da itaba xaiyi masa baraxanar tona masa asiri.



Sima tsaye tana kururuwa da alama Wannan Karon ranta a matuqar bace yake da al'amarin Alhaji Abdallah,


Shi kansa dake gabanta jikinsa rawa yake bai taba xaton kashe fauxie xai masa wuya haka ba, yarinyar akwai tsari sosai a jikinta shiyasa ma ta wahala haka da tuni ya kasheta,


Wannan yarinyar taka akwai baki, akwai wayo, batada tsoro Kuma tana da tsari a jiki, bamason sheďanin yaro abamu jinin fatyma, sima fatyma take so a ynxu jinin fatyma take da buqata fauxie tafi qarfin mu,


Baba yayi shiru kansa a sunkuye yafi kowa sanin fatyma, yasan duk asuba idan tayi sallah bata komawa barci takan xauna tana addu'oin tsari, tana karanta Ayatul kursiyyu, Amanarrasulu, suratul ikhlas, falaqi da nasi, Sannan a koda yaushe xakajita tana faďin,

_Allahumma inni as'alukal afiyata fi dini wa dunyaya wa ahli wa mali, Allahummastur auraati wa amin rau'aati, Allahumma fazni min baini yadayya wa min khalfi, wa'an yamini wa an shimali, wa min fauki wa a'uzu bika an ughtaala min tahti (manzon Allah s.a.w baya barin yin wannan addua safe da yamma)_.

Akwai matsala ya shugabata fatyma tafi fauxie tsari amma me xai hana mu hana mata kwanciyar hankali Kamar yanda mukayi da mijinta muke hadasu faďa akai akai, meyiwuwa rashin jituwarsu a Yanxu xaisa tunani yayi mata yawa har ta shagala da yin addua sai mucimma burinmu akanta, idan an kasheta xamu iya kashe Fauxiya da mijinta,


Sima tayi wata irin dariya mai firgitarwa kamanninta ma abin tsoro ne, tana sanye da wata doguwar riga baqa mai kyalkyali har qasa rigar ke ja, a gefe Kuma an tsagata har xuwa cinyoyinta, ga wani irin Gashi ba kyan gani daya xubo a fuskarta da bayanta, tana da wasu irin haqora masu mugun tsawo har sun fito ta bakinta sai idanunta da baxaka tantance kalar suba kamar red kamar maroon, akaifun hannuwanta dasu take tsafi suma tsawo ne dasu kamar me,


Ban yarda da wannan shawarar ba Abdallah, mijinta yana sonta duk yanda sukayi faďa sai sun shirya, sima na tsananin fushi da fatyma Kuma fushin sima bala'i ne, dan me fatyma xatayi tsarin iyali bayan tasan cikinta shine abincinmu dashi xaka cimma burinka..... Baba ya dubeta a raxane,


Tsarin iyali, bnsan tayi ba ya shugabata ynxu mecece mafita,


Mafita ďaya ce duk sanda fatyma xataje karban haihuwa kabita a boye ka karbo mana rayuwar jaririn Inka sami dama harda uwar jaririn abamu jininta, idan tana tunanin ta hana mana cikinta mukuma xamu janyo mata baqin jini Wanda mutanen asibiti xasu tsani ta karbi haihuwa har hakan ya janyo mata matsala ta shiga tunanin duniya ta manta ko ita wacece tadaina addua har burinmu ya sauka akanta...


Hakan yayi ya shugabata,

Abokinsa dake gefe ya kallesa lallai wannan uban bashi da imani dama an dauki rayuwarsu ne su huta da quncin duniya,


Abu na biyu kuma xaka maido fauxie a jikinka ka shagaltar da Ita kamaidata kamar da idan lokaci yayi xn gayama abinda ya kamata kayi,


Ya gyada kansa, godiya nake ya shugabata,

Sima ta juya ga wani da bai dade da shiga harkarba ta nunasa cikin tsawa da fushi,


Mun umurceka kabamu mahaifiyarka kaqi, idan kabari fushin sima ya sauka akanka duniya xata juyama baya kuma kowa xai qika ya gujeka.....


Kiyi haquri ya shugabata Ina matuqar son mahaifiyata, itace gatana a duniyarnan ta wahala dani kibarni da Ita.....


Ta ďauki wata mugunyar dariya sai da ilahirin gurin na amsa kafin ta tsaida,


'baka isa ba, kai baka isa ba, dole sai ka bada, kowa da kake gani gurinnan, ya rasa Abinda yafiso a duniya, wani uwa, wani uba, wani mata, wani Ya'ya dan haka kaima sai kabada, dolene ka bada, kai kuma kasami abinda kakeso wato *kuďi* ta juya gana kusa dashi,


Sima na godiya da jinin abokinka, ta wadatu anjima xakaga kuďi, da haka tabisu ďaya bayan ďaya har suka gama meeting ďin su.


*

A daren ranar ya fito daga wanka yana tsane kanshi da ďan qaramin towel,

Tana kwance rigingine a gefen gado cikin doguwar rigar barci mai tsantsi marar hannu, ruwan madara,


Kyawawan qafafuwanta da cinyoyinta a miqe sambal tayi xurfi acikin tunanin kowane hali fauxie take ciki a ynxu,

Son matarshi da qaunarta yana qara girgixa xuciyarsa yana hargitsa gangar jikinsa,

Bayan ya gama shirinsa na kayan barci ya kwanta a gefenta sai yaji jikinta xafi rau,

Ya juyo da Ita sosai yana fuskantarta, ta buďe idanuwanta a hankali Waďanda suka qanqance sukayi jawur tana kallon sa, shima ita yake kallo,

'Naji jikinki da xafi meyake damunki,
'nima ban sani ba,

'you are silly and nonsense doctor Iman, bakisan meke damunki ba, ya tashi a fusace yana faďin tashi muje asibiti a dubaki,

Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma xuciya, jikinta har rawa yake, batasan meke shirin faruwa da Ita ba nan gaba dan tana da tabbacin xuciyarta gab take da bugawa, ya dawo Saman gadon yana kallonta,

'meke damunki, tell me,
'ďaxu koda na duba jinina ya hau sosai, bansan inada hawan jini ba sai a yau, ya xnyi da rayuwata, sosai ya gigice ya riqota xuwa jikinsa,

'hawan jini Iman, menene damuwarki saboda me xaki kamu da wannan cutar, me kika nema kika rasa a rayuwarki? ta fisge jikinta daga nasa,


'inada wata damuwa ne bayan ta *babana da mijina*,Kune damuwata Kune kuka sanyani a Wannan halin, ni har sai yaushe xnji daďin rayuwata na xama mace kamar kowacce macen aure, tun bayan mutuwar mahaifiyata ban qara jin daďin duniya ba.... ta soma kuka sosai, hankalinsa yayi matuqar tashi da jin shine sanadi, how comes matarsa xata kamu da wannan cutar ta hypertension, in Kuwa haka ne gwanda ya rasa komai dan farin cikinta gwanda ya rasa aikinsa da komai dan ya xauna da Ita yabata irin kulawar da takeso, yasani rayuwar fatyma abar tausayawa ce sosai duk da batasan sirrin babanta da mijinta ba, ya yarda xai bar komai dan farin cikinta,

'he is ready to do everything for her to make her happy and feel she is the only one in his life, sai ya matso sosai xuwa jikinta ya juyo da Ita suna fuskantar juna,


'tell me Iman am ready to change and I mean it, menene bakyaso daga gareni, ko aikina kikeso na ajiye to make you happy?

'fitar dare nake so kadaina, ka xauna damu kaji matsalarmu, ka ďebe mana kewa ka Kuma bamu farin cikin da Muka rasa, xaka daina yawon dare?

Yayi shiru yana kallonta cikin ido xuciyarsa na bugawa, soyayyarta ta rinjayi xuciyarsa sai ya maidata qirjinsa ya rungumeta yana shafar kanta,


'nadaina, nadaina Iman kema ki cire damuwa da tunani a ranki, saboda jininki ya sauka banason Wannan cutar.... Magana yake kamar xaiyi kuka,


Karka damu, ynxu da ya hau sosai yanada nasaba da halin da fauxie take ciki....

'fauxie xata sami sauqi ki kwantar da hankalinki.


Pherty novels.....

[08/03, 8:14 p.m.] Pherty🎤👯: *Babana da mijina*


©Fertymerh Xarah 💞


25


Da tunani iri iri Deedah ya kwanta a ranar, barci ya kasa daukarsa har lokacin da Iman tayi barci sai ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta kana ya sauko daga Saman gadon ya fito,


Da sanďa ya fice daga nasu gidan ya nufi gidan baba, ba kowa ko Motsin mutum babu sai na kukan tsuntsaye,


Batare da tunanin komai ba kai tsaye ya shiga falonsa dai dai lokacin da baba ya fito daga ďakin bautarsa da kayansa jajjaye na tsafi hannunsa ďauke da kwarya jinine aciki,


Ganin Deedah na qaramin tsoratashi yayi saura qiris kwaryar dake hannunsa ta faďi a qasa, Karo na biyu Deedah ya kamasa dumu dumu sai ya take fuskarsa bayan ya ajiye kwaryar a gefe ya juyo yana kallonsa,

'Waye ya Baka ixinin shigo min gida a Wannan lokacin har cikin falo na,

'ba neman kai nake da kaya ba ballantana na nemi ixinin shigowa wannan falon, baba ya buďe ido sosai yana kallon Deedah da mamaki, me yaron ke nufi kada dai ya rena sa ne yana son ya manta shi surukinsa ne,


Deedah yacigaba da faďin,
'naxo kan mgnr qanwata fauxiya, nasan ciwon ta baxai rasa nasaba dasa hannunka aciki ba, idan baka kyaleta ba wani abu ya sameta kasani tamkar a idon duniya ne,

'abin kunya, abin takaici da haushi yarinyar cikinka kake neman salwantar wa saboda neman duniya, har akwai abinda xaka nema a duniya najin daďi kamar kasancewarka da Iyalanka, ko kamanta haqqinsu dake kanka, idan yau ka faďi ka mutu gobe kacewa Allah me? Kana tunanin haqqinsu ma xai barka, meyasa kake son kashe su, kaji daďi har Allah yayi ma kyauta da yaran, ni shekarata uku da aure matata na samun ciki yana xubewa, ina son yara Kuma still nake xaune da Ita cikin qauna da aminci,


Baba ya nuna sa da yatsa,
'kashiga taitayinka Ahmed, kafita daga idona ba ruwanka da iyalina,

'inada ruwa dasu kasancewar nike riqonsu suna min kallon miji, yaya kuma uba, wallahi idan baka cire muguntarka akan su ba, *Ni Ahmed Deedah xan xama ajalinka*, I will not care da kai ko waye, you are nothing to me, idan har fauxie da fatyma ba ya'yan ka bane don't ever call me your inlaw ko kuma kariqa min kallon suruki,am not...... ya faďa cikin tsawa yana nunasa da yatsa daga yanayinsa xaka karanci bacin rai sosai a fuskarsa,


'kafin ka xama ajalina ni xn xama ajalinka Deedah, kana raye kana gani xn kashe matarka da qanwarka kafin na kasheka Kuma kafin nan sai na wulaqantaku a duniya na toxartaku yanda kowa xai tsaneku, na rasa matata da Ya'ya na maxa ballantana waďanna mata, *Ni na kashe su da hannuna*,ya faďa cikin tsawa cikin subutal baki,


'kai ka kashe su Alhaji Abdallah, har kake ikirari da wannan, Subhanallah....jikinsa na soma rawa,

'na rasa matata na haqura ballantana su, tunda kayi gigin shigo rayuwata sai na kashe ka na kashe fauxie na kashe fatyma......... kai yaji muryar Deedah tare da Kukan harbin bindiga,

Deedah ne riqe da bindiga ya harba kwaryar dake ajiye a gefe kana ya nuna sa da Ita Idanunsa jawur,


Kukan Harbin bindigar ya tayar da Iman daga barcin da take, ta duba gefe ba Deedah gabanta yayi matuqar faďuwa ta sauko da sauri tana kiran sunansa a hankali,


'shoot me Deedah idan kana tunanin bullet xai iya shiga jikina, ko kana xaton a banxa nake xaune, you can't kill me sai dai ni na kashe ka, get out of my house,


'I promise you ni Deedah na ďauki alqawarin baxaka iya cutar da kowane daga cikin mu, kana nan xaka ga qarshenka haqqin Waďanda ka kashe ma baxai barka ba nima baxan Barka ba, for now danasan kowaye nasan mugun abun da ka aikata sai kayi danasanin sanina a rayuwarka, ta cikin ruwan sanyi slow poison xn xamema Kuma batare da fatyma ta sani ba,

'ka iya bakinka Deedah akaina, a ynxu xn iya nakasaka kaxama abin kwatance a gurin su....


Hankalin fatyma tayi matuqar tashi, tana sanye da hijab ta fito daga gidan, taji Kukan bindiga a Ina ne, ina Deedah ya shiga a Wannan daren bayan yayi mata alqawari baxai qara fitar dare ba,


Tana tsaye gurin taganshi ya fito gidan baba, a yanda ta lura kuka yakeyi taga yana share hawayen fuskarsa har kamar baya kallon gabansa, ta maida kallonta gidan baban tana ganin inuwarsa a tsaye ta window tor meya hadasa da Deedah, yaushe ma Deedah yaje can kuma Kukan miye Deedah keyi, ta juya tana kallon inda Deedah yake wayam babusa babu alamarsa ya fice daga gidan, ina ya nufa?


Da sauri taje bakin gate tana dubawa ko inuwarsa babu hankalinta yayi matuqar tashi, kada dai baba ya kori Deedah ne daga gidan, har xataje inda baban sai ta fasa ta fito nan bakin gate ta xauna tana jiran Deedah acikin wannan daren babu tsoro a xuciyarta burinta taga mijinta taji dalilin kukansa.
[08/03, 10:01 p.m.] Pherty🎤👯: *

Deedah Kuwa tafiya yake yana tunanin maganganun baba, kuka yake sosai bai damu da inda xaije a wannan daren da nisan tfyr da xaiyiba,

Sai ynxu yake regretting rayuwarsa kasancewarsa ďan fashi, he loves fatyma, yana qaunarta komai xai iya akanta,yana son kareta da qanwarta ga hannun axxalumin mahaifinsu, yana son basu kulawa da farin cikin da suka rasa gun uwa da uba, yana son xame masu uwa ba uba ba......


Tafiya yayi sosai acikin wannan daren kafin ya iso gidan oga nas, qofar ya soma bugawa ahankali, duk yaran dake gidan suka tashi da sauri kowane da bindiga a hannunsa haka shima oga nas xaune da qatuwar bindiga a hannunsa yana kallon qofar da Deedah ke bugawa a tunaninsu hari aka kawo masu,


Mutum ďaya ya buďe qofar tare da nuna Deedah, suna ganinsa suka ajiye bindigoginsu suka koma suka xauna,

Kai tsaye inda oga nas ya nufa suka sami guri suka kebe dan yayi mamakin xuwan Deedah haka,


'kayi haquri idan na batama a tsawon xaman da mukayi da kai, daga yau nadaina fashi...... Dariya sosai oga nas keyi har yaransa na jiyosa yana kallon Deedah,


'ta yaro mai take bata qarko, ai baka isaba, idan kaga kabar wannan sana'a to ka mutu acikintane, inaaaa waye kai,


Deedah ya murtuqe fuska,
'na kasance da kai tsawon shekara uku ina yima aiki, bn taba nuna gaxawata akan kaba, ina shiga haqqin matata, idan bata yafemin ba Allah baxai barni da haqqinta ba, nagane wannan sana'a bamai kyau bace agareni da kai Ina roqonka kaima ka shiryu kamar yanda Allah ya shiryani kadawo hanya kadaina fashi,


'saboda matarka xaka bar wannan aikin, to ai kamar baraxanace ga rayuwarta, nasan ta nasan asibitin da take aiki acan ma xn iya samunta na ďauke ranta da alburushi Kaga idan ta mutu ai ba batun haqqinta dake kanka,


Sosai Deedah ya tsorata da Kalaman oga nas, yasan wayeshi yasan abinda xai iya da Wanda baxai iyaba, wannan qaramin aikinsane dole ta ruwan sanyi xai biyo masa idan yana son suyi rabuwar arxiki sai yayi shiru yana kallonsa,

'idan kanason kasancewa da matarka lfy ka xauna dani, shekarun baya musu bai taba hadani dakaiba karka Bari mu somayi dakai Deedah,


Deedah ya tashi ya fice ransa a bace batare da yayi mgn ba, oga ya bisa da kallo Deedah nason Wasa dani idan yayi sake sai in kashe sa dashi har matar tasa....


Koda Deedah ya dawo yasami Iman xaune bakin gate tana jiransa, tambayar duniya tayi masa yaqi ya gayamata komai sai kuka da yake har wannan lokacin, ynxu shida iyalinsa suna tsaka mai wuya,

Kukansa ya daďa tayar da Nata hankalin itama sai ta tsinci kanta cikin tayasa Kukan, a Wannan ranar daga shi har ita bawanda ya rumtsa sai juye juye da suke faman yi,


Washe gari har sukayi shirinsu bamai walwala a fuska breakfast ma basuyi ba suka fice kowa ya nufi gurin aikinsa,

Tana office ďinta xaune tana tunanin idan ta tashi xataje ta duba fauxie sai ga Deedah ya shigo jikinsa a sanyaye,

Ta dubi agogo to ten ynxu, ta maida dubanta garesa bayan ya xauna farar takarda ya miqa mata idanunsa jawur kamar xaiyi kuka,


Jikinta na rawa ta karba kada Deedah ya saketa ne, da kyar ta warware tana dubawa, ta barin aiki ce.. ...ta ďago da sauri tana kallonsa,

Wane aiki Deedah?

'farin cikin ki shine nawa Iman, I promise to change, inason kasancewa dake kamar yanda kike so nabaki farin ciki irin wace mata ke buqata a gurin mijinta shiyasa na bar aikina na banki a yau, are you happy Iman?


'happy with what Deedah? Ta faďa da tsananin mamaki tana kallonsa ido a buďe,

'why xaka bar aikinka saboda ni, ni nace kabar aikinka, tell me Deedah idan Baka aiki what did you want to do? Gida xaka xauna ni nafito aiki or what, akwai abinda ke faruwa tun jiya kaqi ka sanardani, pls tell me miye damuwarka Deedah?

Ya xare baqin glass ďin idonsa, sai a lokacin ta lura da yanda idanunsa sukayi jawur da alama yasha kuka, nan da nan hankalinta na tashi idanunta suka kawo kwallah,

'ba haka nake nufi ba Deedah, bnce kabar aikin ka saboda ni ba, training dakace na dare kanayi nace Kabari, fitar dare nace kadaina Deedah ba aikinka ba.....


Pherty novels

*Babana da mijina.....*


©Fertymerh Xarah 💞


26


Yayi shiru kawai yana kallonta, baisan yanda xai gayamata fitar dare baxata yiwu ya daina ba saboda abinda oga nas ya faďa masa a daren jiya,


'Naga you have not sign it, so baxaka bar aikin ba, ta yage paper into pieces kana ta xuba a dustbin, ta dubesa,


'kaje gurin aikinka tunda bnda muhimmanci da xaka gayamin damuwar ka, jiya naganka ka fito gidan baba kana kuka, meyasa? Meya haďa ka dashi? Me ya kaika gidanshi bayan na gayama abinda ke faruwa ynxu, kai tsaye ya bata amsa,

'saboda lfyr fauxie naje, tayi masa wani irin kallo,

'ban fahimceka ba, miye hadinsa da lfyrta mutumin da bai damu da Ita ba,

'yana da sa hannun a ciwonta, bakiga ynda ta rikice tana kiran sunansa ba tana sai ta kashe shi, bakiyi noticing komai akai ba,


Tayi shiru tana tunani, mgnr Deedah gsky ce idan tayi laakari da Mgnr fauxie da ta gayamata biscuits yabata taci, meke nan baba sihiri yakeyi ko malamai yake bibiya dan yaga bayanmu, ya salam ta furta a hankali bayan ta dafe kanta da hannuwanta duka biyu xuciyarta har wani xafi takeyi,


Deedah yace muyita addua Iman, kada ki tambayeni dalili, amma mu dage da addua Kuma fauxie xata sami sauqi,

Tayi shiru tana kallon sa da tagumi idanunta sunyi jawur, dole tasa ido sosai akan mahaifinta tana son sanin me yakeyi, nan da nan kwakwalwarta na soma tunano mata wasu abubuwa,

'lah anty dubi irin kayan baba....
'anty shi baba baxai shiga aljanna ba,
'baba baya shan sobo a cup ko battle sai dai a kwarya,
'baba yace sai ya kasheni, ya kashe ki kuma ya kashe yaya,
'anty ga baba can, kibarni in kashe shi,

Ta bigi teburin dake gabanta,
'Nooooooo ta faďa da qarfi, impossible.... Sai da Deedah ya tsorata da yanayinta,

'me kike tunani?tayi shiru,

'baba baxaiyi haka ba, baba baxai aikata haka ba, Akan wane dalili bayan yana da kuďi, mexai nema a duniya ynxu? Astagafirullah tayi gaggawar tuba kan xarginsa da tayi haďe da kawar da tunanin daga kanta, ta dubi Deedah,

'muje muga jikin fauxie....

*

Tana ďauke da wata qatuwar tedy a hannunta sai gudu take tana xagaye falon tana dariya, Amira na bayanta yarinyar Merah kusan sa'anin juna ne,


Affiya dake xaune a tsakiyar falon ta dubesu,
'baxaku daina gudun ba sai kun faďi kunji ciwo?
'Mummy kice ta bani tedy ďita tunda ba daddynta ya siyamin ba,

'fauxie tace nima baba ya siyamin nawa, anty ta siyamin kuma ranar yaya ya qara siyamin wata qatuwa,

Affiya tace ki aramata Amira, she is your new friend bakiga batada lfy ba,

Amira ta make kafadarta tana buga qafafunta a qasa,
'Ni baxan aramata ba sai ta bani, ta fashe da kuka dai dai da saukowar Merah, yanajin duk abinda ke faruwa,


Amira baxaki arama qawarki tedy ba, ta gyada kai tana kuka, Merah ya karbi tedy hannun fauxie ya miqa mata,

'ga kayanki, ba ruwana dake munyi faďa, juyowar da xaiyi sai yaga fauxie na kuka sai share hawayen ta take da rigarta, ya dubi Affiya,

'Ina tedys dake gidannan,
'suna ďakin Ameera,

Ya riqa hannun fauxie daina kuka muje inbaki wata kibarta da abinta, Ameera tayi Saurin miqo mata tana faďin,

'daddy gashi na aramata,
Fauxie taqi karba,
'daddy wai bataso kace ta karba..... Sallamar su Iman ta Katse su, da sauri fauxie ta juya jin muryarta suna haďa ido ta saki hannun Merah taje da gudu ta rungumeta, sosai Iman ta qanqameta a jikinta cikin tsantsar farin ciki ganin ta sami lfy,


Slaves ďin dake falon suka soma fita da sauri yayinda wasu suka fara hidima da tarbon baqi, Deedah ya bashi hannun suka gaisa kana suna xaxxauna, iman ta gaisa da affiya da Merah,


'Dr kinga fauxie ta sami lfy tun kafin ayi mata komai abin kamar sihiri, tayi murmushin yaqe xuciyarta na bugawa,

'Ina godiya sosai Dr Merah, farin ciki na a yau ynda na sami fauxie Allah ya qara kiyayewa duk suka amsa da Amin,

'Ameera taxo ta kawo mata tedy ďin ta aramata,

'Banso ai anty nima inada tawa tedy ko? ta gyada Kai tana kallonta,

'Kuma ai anty tafi tata kyau ko, iman ta girgixa kanta, fauxie ta bata fuska xatayi kuka,

'tafi tata kyau,
Ameera Tace ai nima inada su da yawa daddy ya siyamin, ke kuma babanki bai siyamaki ba😝

Yaya ai baba ya siyamin ko? Kuma babana yafi daddy ki kuďi ai,

'qarya kike daddy yafi babanki kuďi,

Kuyi shiru hakanan, faďa ya qare cewar Iman,

Merah yace qurciya ke damunsu kibarsu, yau Ina off shiyasa bn shiga asibiti ba,

'naga alama ai,

(Faďan dai bai qare ba tsakaninsu)

'daddy ya siyamin keke da Mota, kuma yace xai kaini Phoenix inda yaya sultan inyi karatu,

'ai nima baba yace xaije dani India inyi karatu irin na anty, kuma ya siyamin Mota, harda soja aciki da bindiga, kuma ya siyamin gida qatoto harda jirgi, Amira ta dubi Merah,

'daddy nima xaka siyamin gida da jirgi? Ya gyada kansa yaran ma mamaki suke ba kowa a falon, ta dubi fauxie tana dariya,

'nima daddy xai siyamin,
'fauxie tace ai baida kuďi irin babana,
'daddy yana da kuďi masu yawa acikin drawer,
'baba yana da kuďi da yawa da yawa acikin ďakinsa, sun xubo da yawa qasa a Sama ma suke faďowa ko anty? Ta juya tana kallon Iman cikin shigar tambaya.....

*BABANA DA MIJINA......*


©Fertymerh Xarah 💞

27

Babana yana da kuďi da yawa da yawa acikin ďakinsa, sun xubo da yawa qasa a Sama ma suke faďowa ko anty? Ta juya tana kallon Iman cikin shigar tambaya......


Deedah yayi xuruf yace waďanda aka ďora akan drawer ne ke xubowa, kuma ai bamasu yawa bane, ta juya tana kallon Amira,


'tor kingani, tayi mata gwalo tana dariya, Amira ta faďa jikin Merah tana kuka, ya cirata yana faďin,

'is ok, daddy ma akwai kuďi har akan drawer, itama ta juyo tana yiwa fauxie gwalo,

Sosai yaran sun baiwa affiya dariya, iman Kuwa

Please Login or Register in order to submit comment