Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tadda ita****"yauwa gashi lemun kwakwane da sanyinsa ɗaxun nan nahaɗama abbanku dake yana gari yau"
Amsa tayi tana faɗin yawwa mommah Naaaaa shiyasa nake ƙaunarki bani amsa tayi ta ajje a gefe, Nan suka shiga fira, kafin tace mata ita salla zatayi.
Dadduma ta shimfiɗa mata ita kuma tayi bayin dake cikin parlourn dan ɗauro alwula, fitowa tayi tahau kan daddumar tare da tada fara sallar, tana idarwa maleek na shigowa parlourn, cikin murmushin Nan nata kamar koda yaushe ta shiga faɗin "id0n ka kenan my S0N yanxun ganinka sai an ciki form"
Murmushi kawai yayi tare da shafa sumar kansa yana faɗin "wallahi Mommah abubuwan ne sai ahankali**
"Ga ayyukan da suka tiso miki Ni agaba!"

"Ayya sannu my S0N komai zai wuce wata rana sai labari"

"Mai labarin ma wata Rana babu shi" cewar jaddah take zaune saman dadduma duka su biyun da kallo suka bita kowa da abinda yake saƙawa aransa daban,
"Oya tashi muje zamu tahi gida" ayya sorry yaya bara na amshi lemuna awurin Mommah" da kallon baki da hankali ya bita dashi, itama kallon da hankali na tsabb ajikina tayi masa tana amsan jug ɗin sanyin da Mommah tayi saurin ɗauko mata.
Lemunta ta juye domin acikin cup ɗin, dan harga Allah ranta ya biya lemun***
Afusace yaja hannun ta suka bar parlourn, suna barin harabar ɓangaren nata yasaki hannunta yace " ke baki da hankali ga dukkan alamu, to wallahi jikina yasama matsala saikin biyamin abuna;" ya faɗi hakan yana huci "mene yayi zafi saina zo ka kuma yimin wani meye aciki" ke nine nake faɗa miki Magana kike maida min"
Hannuntan mai lemun ya kama ya murɗe hakan yasa kofin subcewa ya faɗi lemun ya zube, ganin lemunta malale bisa tyless ɗin tsakar gidan ne yasata fashewa da kuka, ganin shiru babu ita da mai qiranne kuma yasa ammeyn biyo bayansu,turus taja ta tsaya ganin jaddah da maleek tsaye ga kuma jaddahn tana kuka, hakan yasa ta qarasa sowa gaban su cikin qiɗima ta shiga faɗin "meya faru? Menene? Meye yasameki AYSHA"
"Babu abinda ya sameta sai tsabar bakin ciki, wai matar Nan ce ta bata lemun kwakwa shine ta amshe zata sha!" To meye aciki dan tasha ɗin BABANAAA banason fitina faaaa"
"Ke kuma muje dama nima haɗa miki wani dake nasan yanxun kina s0nshi, shima dana shi na gyaɗar dana masa"
Kai kawai ta iya ɗagawa ammeyn tana bin bayanta, ko inda maleek yake bata kalla ba haka tabi ammeyn sukayi gaba suka barshi, yana kallon ikon Allah suna zuwa ko zama ammey bata barta tayiba tace mata "ga naki shima yazo ya ɗauki nashi bazan iya muku da wannan shegiyar rigima takuba"
Yana xuwa dama yana daga bakin qofar parlourn hakan yasa ya suri nashi fuuuuuuu ya fice, itama fuuuuuuu tabi bayan nashi "kwadaiji dashi" ammeyn ta faɗa tana shigewarta bedroom nata.
Acen harabar gidan ta tsinceshi hakan yasa tayi sauri ta cimmasa hannunsa ta kamo cikin nata, fusge hannunsa yayi yana ɓalla mata wata uwar harara hakan ne ita kuma yasata saurin ɗauke wa qasa tana riqe cikinta yafara murɗaɗɗawa,cikin hamzari ya duqo xuwa gare ta yana faɗin****
"NOORIE mene yasami cikin mu wuce asbitin, ganin yacce duk ya bi ya tada hankalinsa ne yasata fashewa da wata iriyar dariya, ganin hakanne shima yasa shi sakin murmushi sai kuma kawai ya sureta sai cikin motarsunnn.

Kuyi haƙuri dajina shiru pls Ina mai qara baku haƙuri.
Ayyukane sukamin yawa inawa kowa fatan alkhairi🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Na GODE da qaunarku gareni♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
*🔥♥️ KAREN BANA♥️🔥*
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
*AMMEY LAYLERH SHALELEN DAZZLING STAR'S*

Page 36&37

08104493215

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
===≠===≠======≠=====≠====≠==

_____________________
Ganin hakanne shima yasa shi sakin murmushi sai kuma kawai ya sureta sai cikin motarsunnn.
Shima zagayawa yayi shima ya shiga yawa motar key, kafin ya cilla motarsa kan shimfiɗeɗen titi, haka jaddah taci gaba dawa maleek dariya har bacci yazo yayi awon gaba da ita.
ganin tayi barcine kuma yasa shi sakin wani shegen murmushi irin na gefen bakin Nan, har suka qarasa gida bata farka ba ganin hakan ne kuma yasa maleek ɗaukar ta, akafaɗarsa tare da nufar parlourn su kai tsaye da ita, bedroom nashi ya wuce da ita ya kwantar da ita akan bed, kayan jikinta ya samu ya rage mata.
Shi kuma ya faɗa toilet ruwa masu ɗumi da ƙamshi ya haɗama kansa, acikin ƙaton bathtube wani irin lumshe idanunsa yayi tare da budewa yana shaƙar daddaɗan ƙamshim turaren wankan kuma ɗumin ruwan loqacin daya shige cikin bathtube ɗin.
Akalla ya kusan mintina goma akwance acikin ruwan, kafin ya samu yayi wankan nashi***
Ɗaure da towel ya fito akan west ɗin sa ɗaya hannuwansa kuma wani mini towel ɗin ne, yana tsane gashin kansa da inban daddaɗan ƙamshim na gyaran data Kesha babu abinda take fiddawa,dan kuwa ba qananun kuɗi maleek yake kashema sumar tashi ba:
Haka ya qarasa gaban tanqamemen mirrorn ɗakin lotions masu daɗin qamshi ya shiga shafe jikinsa dasu, kai tsaye kuma cikin clothes na kayansa ya shige tare da shiryo kansa cikin wasu haɗaɗɗan kayan barci riga armles da dogon wando masu santsi kana ya fito sai zabga uban qamshi yake.
Sai kuma yanufi kan bed tare da kwanciya, bayan ya gama tofesu da adda'oina barci****
Kwanciya yayi agefen jaddah tare da rumgumota jikinsa tare da jan duvet yaja ya rufesu.

*********
Suna fita Hajiya LUBNA ta saki wani irin shegen munafikin murmushi tare da komawa cikin sofa ta kule, wayan ta ta ɗauka tare da ci gaba da abinda take yi, "MALEEK! MALEEK!! Zans0 ganin ranan dazan ga zubar ruwan hawaye daga cikin idanunka MALEEKkkk"
Sai kuma taci gaba da latsa wayarta. Inda kaikayi da karan bani na suka sa na lekoma masu karatu wani abu daya kusan tashin kaina baki ɗaya!.

*6 Bosses*
*The leaders of the country and you know*
Naga tana chart dasui!
"Yanxun haka sune suka shigo kuma suka fita, tabbas matarsa tana ɗauke da cikinsa!"

Hhhhhhhh

Shine abinda Kashim baba ya turo tare da emoji na dariya against,
*K baba*
"idan kuwa har haka ne to tabbas zamu ajje duk wani shiri da harin da muke shirin farmakar MALEEK dasu, mun samo hanya ɗaya mafi sauƙi mafi muni kuma ta hanyar tarwatsa RAYUWAR MALEEK ɗin!."yanxun duk wani hari namu yana kan abinda MALEEK zai haifa dole ɗin dole!!"

*Tanbuwal*
Akwai babban shagali kenan dole mu shirya ma wannan babban shagali tsaraba ta musamman!

*Atiku*
Har naji kamar mu janwo nesa kusa, dole yayi kukan jini wannan karon, kafin yayi mutuwar na mutu ban mutu ba, mutuwar wulaƙanci tare da tsinuwar al'umma, dan kuwa inajin kabb DUNIYAR Nan nafi kowa tsanar MALEEK, domin shine maqasuɗin abinda ya rabani da kujerata, ya sani tseren tsiran da ban shirya waba! Shege la'antacce"

*Isa hasarara*
Hhhhhhhhhh lalle tafiya da gwani akwai daɗi hausawa sunyi gaskiya, basuy qarya ba dole wannan karon ya amshi SAKAMAKO mafi munin gani, MAZA bisa kanka ba MATA ba yaro!

*Ibrahim NERA*
*The worst*
*more dangerous*
*The president*
Hahahaha hahahahaha
Hahhahahaha MALEEK harka bani tausayi yaro!
"K baba bayan sheƙesu na baka kwangilar auren matarsa!
Idan har Ni na aureta me duniya zata ji za kuma ta gani, dan haka qungiyar mu ta baka AUREN AYSHA MATAR MALEEK,
Zan ga zan ga zan ga wannan ranan Ni na saniiiii, ZANYIIIII party zanyi rawa zanyi yadda nakesooooo0 kuma da ƙasa ta"
"Dama wancen munafikin chief of army ɗin ne yasa ban tsige banza daga kan matsayin saba, yanxu kuma hhhhhhhhhhhhhh"
***************
Naji tsoro na kuma firgita da ganin wannan abu, innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un, innalillahi wa'innah ilaihir'raji'un, shugabannin mu maka sanmu!.
To miye hakan yake nufi*****
_______________
ADAMAWA
_________________________
Gaba ɗaya Al'amura sun sako Hajiya LAURA gaba ta kasa gane kan al'amarin, gashi gaba ɗaya mai martaba sarki abdulphata Omar yasa andakatarta da xuwa sashen sa gaba ɗaya, amma dake makirar macece sai take nuna hakan tamkar bai damemeta ba****
Nan kuwa idan da abinda yafi ɗaga mata hankali to wannan abu ne da mai martaba yasa aka mata, MARYAM ABDULJALAAL tayi tayi tayi magiyar taba da haƙurin wajen ganin mai martaba ya janye wannan babban al'amarin atsakankanin uwar gidansa, amma ya nuna mata ɓacin ransa qarara akan Wagga batu.
Hakan yasa take kaima Allah kukanta haɗi da naimawa abokiyar zamanta yafiyarsa da kuma ta mijinta, tsawon watanni huɗun Nan a haka take fama amma kullum maganar ɗaya ce ta janye tun kafin ya hmmmm, ba'a dai magana kawai.
Su Malam Abdullahi kuwa suna Nan cikin garin Adamawa, inda mai martaba ya bashi wani qaton gidansa, tare da aiki yin dake dama malam Abdullahi yayi karatu, sammm baisamu mastala da hakan ba, haka suke zaune kusan kullum sukan ziyarci wadannan bayin Allah, domin dangin su ma ba'a barsu haka ba kowa da irin tarin alkhairukan da aka masa.
Hakan yasanya wasunsu kuka, da LADAMAR Rayuwa.
Lallai Malam ba haushe yayi gaskiya dayace da yace****
Lokutta da dama akan yiwa wasu kall0n wulaƙantattu daga baya suzam abin misali a rayuwa* tabbas haka yake, dan sun ɗauki kyakkywan darasin rayuwa akan kansu ma ba sai anje ko ina ba.
Rayuwa tama su ummey da malam Abdullahi daɗi dan kuwa harta ɗalibansa almajiransa ya dawo dasu Nan Adamawa, inda babu wani ɗalibin dayake Bara kamar da sun tashi daga matsayin Disciples sun koma free people kamar kowa.
Adda'oi kuwa wannan bayin Allah suna shanta, tuni Malam Abdullahi Rano da almajiransa suka bazu sunansu yayi popular, Inda aka maida malam Abdullahi limamin babban masallacin Adamawa, dama limamin ya rasu babu jimawa.

***********
Haka rayuwar su MALEEK taci gaba da waka na cikin aminci da kuma kwanciyar hankali,inda suke baiwa junansu wata iriyar kulawa da SOYAYYAR da take wahalar samu a yanxun, sai wurin ɗaidaiku, S0 da ƙauna suke nunawa junansu zalla, inda ɓangare guda suka cigaba da bama cikinsu kulawa ta musamman, yanxun haka jaddah tayi nauyi ɗan cikin ta yana wata na tara haihuwa Yau ko gobe***
Hakan yasa Ammey ta dawo da ita gabanta tunda haihuwar farice, aykuwa maleek na yace baisan zance ba haka shima ya dawo gidansun da zama, suka tarema ammey agida,badan ma albarkacin aiki ba dasu ammey sun ga boni, abu kaɗan yace kodai haihuwar ne mutafi asbiti, sannu kuwa bata yanke wa motsi kaɗan sannu da sannu tana yawa to data fara akan jaddah****

JUMA'AT
Babbar rana tunda jaddah ta tashi takejin maranta na mata wani irin ciwo, amma ta daure gudun kada ta tadawa su ammeyn hankali kuma taje ba haihuwar bane, tunda ta jima tana jin irin hakan a tattare da ita shi yasa take daurewa.
*******
Misalin ƙarfe huɗu da rabi na yammacin ranan tana zaune, tana tsincewa ammey Ayar da zata mata kunun Ayar da tacema Ammeyn shi kawai takes0****
Duba da yana yin nata bayan ta gama tsince Ayar tass ta miƙa zata kaima ammey ayarne kuma, taji zuuuuuuu wani abu mai kama da ruwa nabin ƙafarta, hakan yasa tayi saurin komawa birnin ta zaune, tare da kwalla ƙiran ammeyn.
Kasancewar tasan halin yanayin ta yau ɗin ta tashi, acine yasa ta rugowa a guje, ashe duk ɓoye ɓoyen da take ammeyn tana sane da ita, ganin bata nuna mata bane yasa itama ta tafi ahakan, tasan dai dole idan me gaba ɗayar tazo tofa dole ta nemeta.
Tana zuwa gurinta tace "AYUSHA ko haihuwar ce" cikin qarfin hali da girgiza mata kai haɗi da faɗin "a ahhhhh ammey kawai dai marana ce naji tana sukana, ina miƙewa kuma naji wani abu nabin ƙafafuna".
"Haihuwar ce mu tafi asibiti kawaiiiiii" mu bari ajima koda zuwa dare ne Ammey"
Ganin kuma ba wani abu bane yasa ammeyn dakatawa kaɗan, ganin kuma ta ware harma tayi sallar magrib lafiya ne yasa ammeyn sakin ranta, wajajen isha'i tace ma da ammeyn tana s0n balangu amma na siyasar wa, haka ammey ta bada aka siyo mata balangun aka kawo mata shi a baƙar leda.
Soma cin balangun nata kenan, wani irin azababben ciwon mara ya turnineƙa a furgice ta soma ambaton sunayen Allah, nan danan kuwa ammey ta ida rikicewa. Ana haka sai ga maleek ya dawo a wurin aiki, tamkar kuma wacce dama shigowar nasa ake jira Nan take ta soma wani irin murɗaɗawa tare da kukan azaba,tun tana ambaton sunayen Allah harta koma sai kuka kawai take.
A 36 maleek ya saɓeta a kafaɗarsa yayi cikin mota da ita, ammey ce tayi saurin biyo bayansu itama ta shige cikin motar.
Cikin ƙanƙanin loƙaci maleek ya isa asibiti mafi kusa privete me kyau da tsada inda dama Anan ne jaddan take xuwa awon ta.
Nurse INDO ADO Mai UNGUWA ce ta amshi haihuwarta emagerncy room tayi da ita, ganin wanda ke tare da ita sananne ne a kasar ma baki ɗaya, hakan yasa ita da sauran nurse suka amsheta jiki har mazari yaje, cikin gaggawa suka sóma bata dukkan wani taimakon da suka san zasu iya mata.
Haka aka dinga fama su MALEEK sun kasa tsaye sun kasa zaune, gashi ance musu haihuwar da saura.
Hakan yasa maleek yake ganin kamar ko basu iya aikinsu da ƙyau bane, daƙar ammey ta lallashehi ya barta cikin asibitin, haka jaddah taci gaba da kanta wani irin tukuƙin bala'i ne idan ya faro daga tafin qafarta saiyazo daidai mararta zai cakeee Anan, aikuwa idan ta soma wani irin murɗaɗɗawa da surutan da itama kanta batasan mene take faɗa ba, idan kuma ya lafa mata CENN xuwa jimawa wannan turnuƙun zai kuma dawo mata, gashi ana ta fama amma har wajajen sha biyun dare shiru babu haihuwa babu dalilin ta, hakan yasa jaddah sarewa******
Har take ga kamar itace ba zata iya haihuwar da kanta ba, hakan yasa cikin kuka ta shiga roƙar nurse INDO ADO ɗin dake tsaye akan, akan kawai su taimaka su mata tiyata, nan suka shiga bata baki suma suna qara kwantar mata da hankali, suna faɗin ta kusa saura qiris...
wajajen qarfe ɗaya da rabi loqacin duka nurse basa wurinta sai iya INDO ADO ceeee itama barci ɓarawo ya soma kwasarta hakan yasa jaddah kuwa tayi wuff ta diro a gadon nan, ta saɗaɗo ga azabar ciwon mara da ciki amma haka ya fito wurin da ammey ke zaune, tana zuwa ta zube tana kuka tana faɗin "ammey nasan baxan iya haihuwar nan da kaina ba pls acenzan asibiti muje Amin CS kawai na huta, ana haka nurse INDO ADO ta ƙaraso wajen, bayan ta farka bata ganta bane, hakan yasata fitowa wajensu a guje, ta kuma meda jaddah.
shi kuwa maleek bama ya wurin yana a cikin motarsa ya ɗauka tasbaha yana faman yima Annabi salati, kan Allah ya saukaƙama wannan baiwar Allah tashi.
Wajen ƙarfe uku da mintuna arba'in, naƙuda gadan gadan ta kuma tasar ma jaddah, haka suka shiga fafatawa a filin yaƙin mata, cen tace ma nurse INDO ADO ɗin zatayi kashi, inda dama akwai wani qaton foo na musamman domin irin haka nan akace ta sauƙo tazo tahau, haka ta ƙaraci nishinta amma ko ƙyamass ta gaza yin kashin Nan.
Tana komawa gadon kuwa nurse INDO ADO mai unguwa zira hannu, sai kawai ta ji kai ya taho, hakan yasa tace ta ware ƙafafunta ga kai nan tahowa, Nan tasa ta fara nishi, tun tanayi da qarfinta har qarfin nata ya kusan qarewa, qiran sallar farko tare da dirowar santaleken baby boy ɗin nan ya faɗo duniya, Nan kuwa baby ya zankata ma su ammey qiran salla na biyu, nan ta yanke cibiya tare da gyara babyn da uwar babyn, badai raki ba Dan wurin yasar jini ma ansha daru, inda wata nurse INDO ADO ta fara mata, tayi sau uku tace ya isa.
Nan kuwa wata gabjejiyar nurse ɗin tace ta bari ta qara mata koda so biyu ne, ai kuwa jaddah tana kyalla id0 ta hango hannuwan wannan nurse yayi biyun na nurse INDO ADO...
nan kuwa tace bal bata san zance ba,. Haka nurse INDO ADO da ƙyar ta qarisa mata yasar jinin.
Tsabar farin ciki kuwa ammey harda hawayenta, shi kuwa oga maleek sujjada yawa subhanahu wata'ala, wanda ya bashi wannan farin cikin da yasan duk duniya in za'a hadesu babu mai iya bashi, aikuwa ana kammala kimtsa masu jego yayi wuff, ya shige ɗakin yana xuwa baibi takan mutanen cikin ɗakin ba ya haɗe babyn da maman babyn ya rungume su tsammm acikin ƙirjinsa, ya kuma ƙi cikasu ganin rashin kunyar na neman yawane yasa ammey korar shi daga cikin ɗakin.
Nan yashiga ɗaukar babynsa zafafan pics a wayarsa qirar samfurin samsum galaxxy 8 4100.
Kafin kace me har wannan haihuwa ta gama zagaye dangi da ma social media, Inda har mutanen Adamawa Kano sun gama bayyanuwa suma acikin asibitin.
Kasan cewar a jirgine suka zooo su duka inda harda su Malam Abdullahi da ummey.
Nan jaddah aka sami abinda akeso ta maƙalƙale ummey ta hanata koda ganin ɗan be wanda ubansa harya riga ya masa huɗu ba, saidai babu wanda yasan sunan wayene ya masa huɗu bar dashi.

Gaba ɗaya faɗin irin farin cikin da wannan ahali suke ciki faɗa loƙacine, inda kowa ƙoƙarin ganin ya faran tama jaddah rai yake, nan aka basu sallama suka ɗun guma gidan Maleek kai tsaye suka nufa, inda suka yanke shawaran ummey ne zata zauna da ita zaman wanka har arba'in.
Ai kuwa ummey taji daɗin wannan abu da suka mata, domin sun nuna mata har yanxun matsayin ta yana Nan a wurin jaddah na uwa, malam Abdullahi ma yayi murna da hakan.
*********
Mutane MADINAH ma sun qira video call, inda suka ga santalelen babyn nasu mai kama da maleek sakk babu abinda ya bari nashi, saima kusan kereshi da yayi wajen hasken fata da kuma ƙyau, duba da cewar uwarsa ba cikakkar Hausa bace half cast ce ruwa biyuce, hakan yasa babyn ya zarta mahaifinsa a komai da komai.....

Kwana biyu a tsakani mutanen MADINAH suka dira tare da uban kayan barka saukace hauka, aikuwa zokaga yadda ake ruwan kayan barka, ga uban shimilin kayan akwatunan da maleek ya musu ita da babyn, banda wanɗanda suka dinga saya suna ajjewa.
Kai wannan baby yazo duniya a sa'a.
A kuma babbar rana sarki ABDULPHATA OMAR, sarki MALEEK IBN SUFFYAN ma haka suka kawo nasu kayan barkar, inda abinda sarki ABDULPHATA OMAR ya kawo gurgiza zukata da yawa domin jirgin sama guda yaba jikan nasa yace shine jika na farko kuma mafi soyuwa daga ɓangaren matarsa Hajiya maryam abduljalaal yeko,shi sarki maleek ibn suffyan shima ƙyautar da yawa babyn ta girgiza zukata, inda maleek ne da kansa ya garga ɗeni da kada na gayawa FAN'S abinda ya bashi.
Mai girma maleek kuwa ya bawa NURSE INDO ADO MAI UNGUWA kujerar maka tare da wasu maƙudan kuɗaɗen dani kaina AMMEY LAYLERH bansa nawa bane.
___________

Mom sani ita ce mace ta farko acikin FAN'S na KAREN BANA ta tazo wa jaddah barka, tana zama saiga bloody AYSHANTY tazo kamar anjefota, tana muzurai wai danme mom SANI ta gudo ta barta.
Shi kuwa maleek yana daga gefe sai faman murmushi yake musu domin yasan akan meyene suke hakan.
Cen kuma ƙofa ta fara buɗe wa inda OUM SHAHEED, tare da maman Inaya suka diro suma cen saiga masoyiya ✨ Asmitar hydar tare da Aunty Reema suma sun zo barka, a ahhh saiga su teemah shalelen Abba sun bayyana suma.
Ai kuwa nan FAN'S of KAREN BANA suma ƙofa ta buɗe musu💃
Gaba ɗaya KAREN BANA FAN'S groups ne suka zo atare, inda SAPWAN AHMED ya raɓe a bakin ƙofa yana jiran umarni daga MALEEK akan ya masa is0, aikuwa saiga maleek ya taho tare da rungume SAPWAN AHMED, dan shifa maleek baya da tsayayyen abokin daya wuce JAWAD., Gashi JAWAD baya ma qasar hakan yasa yakes0n su raba farin cikin tare da SAPWAN AHMED🥰.
Aikuwa zokaga murna wajen SAPWAN ganin loƙaci ɗaya ya samu shiga a wurin maleek ɗinnnnn...

Hajiya LUBNA

Idan tace zata yi kuka to kuwa tayi qarya domin ta gwada yin kukan, yafi cikin carbi amma ya gaza zuwar mata, hakan yasa cennnnn ƙasan zuciyarta ya kuma kaikasgewa da bushewa.
Inda ta kuma ɗana uban Target ɗin dayafi nada tsanani,

HAJIYA LAURA
Loƙacin dataji cewar jaddah ta haihu, ji tayi kamar ta mutu dan baƙin ciki, Ashe bataji komai bama lokacin dataji cewar Sarki ABDULPHATA OMAR jirgin sama guda ya mallakawa ɗan gidan kishiyarta shi kuma ƴarsa ɗan kuma jikansa, jika na farko a wurin sa ai saida takaita ga faduwa ƙasa warwass...

Ahalin malam Abdullahi Rano ma sunyi masa kara wajen zuwa barkar samun qaruwar da sukayi.
*🔥♥️KAREN BANA ♥️🔥*

Na Maryam Naseer mirrah
*Ammey laylerh*

Page 38&39

08104493215

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
==================================

________________________
FRIEND kuwa faɗin irin uban kayan data saima babyn ɓata baki ne.
Zo kuga yacce jadderh take samun kaya ita da babyn nata, oga maleek kuwa hamm ba'a magana, gaba ɗaya yabi ya kanainaye babyn da maman babyn! Wanda saidai ammey tayi da gaske kana ya shiga taitayinsa, dan da kammm ma hana ɗaukar babyn nashi yayi.
Abbie ma campanynsa na sarrafa auduga sukutum ya mallaka wa babyn.
Bayan kwana biyu
Wanda ya kama saura kwana uku suna kenan, duk ƴan uwa na kusa dana nesa kowa yazo ganin wannan babyn mai farin jini, kuma ɗan gatan dangi.
Ai kuwa gida ya cika ba'a magana su aunty sumayya da aunty yusrah ma duk sunzo Kasan cewar suna manya kuma ba'a nan suke da aure ba!
Ita sumayya tana aure a Lagos yayinda yusrah take da aure a London ƴaƴan Hajiya lubna kenan.
Tare da aunty hauwa'u itace babba a ɗakinsu na Hajiya talatu nera tana aure a Kaduna.
Amma fa tun kamin suzo tuni sunga hotunan babyn da maleek ya tuttura musu, wasu kuma suka gani a status nashi da sauran yaran gidan.
Barin ma auta Zahra da taci wayanta da hotunan baby, kowa ya gani dole ya yaba.

Pan's ma hotuna duk sunzo muku na sani😄🤣🫰🏻

Ammey kamm tayi ƙememe a ɗakin ta hana maleek sakewa, dan tunda jadderh ta haihu bata taɓa bari sun ƙeɓe da juna ba,
Masha Allah baby dai kam yayi goshi , kayan Barka ba'a magana aunty sumayya da nata aunty yusrah da nata, aunty hauwa'u da nata!*****

A babban masallacin dake ƙofar gidan Alhaji taufiq aka raɗa suna, inda aka sanya ma babyn sunan malam Abdullahi.
Aikuwa zo kaga murna wurin wannan bawan Allah, kowa yayi murna da wannan kara da maleek yawa malam Abdullahin! Faɗin tarin farin cikin da suke a ciki ɓata loƙacine.
Saniya guda aka yanke ranar sunan Abbie kuma ya ɗakko ƙaton rago daga gidan gonarsa irin wanda ake masa kiwo a ƙauye, shima aka yanke, kai gata dai iya gata wannan yaro ya samu inda yanke Za'a na qiran babyn da AYMAN wajen karantawa malam Abdullahin.
Daga nan aka fara shagalin suna inda suka shirya ƙwarya²walima iya cikin gidan nasu!
Ai kuwa Ranar suna saiga babbar ƙawa kuma ƴar ɗaya tilo Basma Ibrahim ɗin jadderh, ai kuwa kamar suyi hauka bare an daɗi ba'a haɗuba.

{Nasan masu karatu masu manta Basma Ibrahim ba! Ƙawa ɗaya taki da jadderh take da}

5:0pm na yamma su mom Sani dasu bloody Ashanty su Reema, Oum shaheed, Sis bilkisu AUTARMU, maman inaya, Asmeetar hydar cutie sumy suka shirya tasu gagarumar walimar suma!.
nima nida ƴan KAREN BANA Pan's muka shirya tamu ƙwarya²walimar muma, muka ce ba za'a barmu a baya ba eheeeeeee, ai kuwa Pan's sunsha casu.
Irinsu Fatima Aliyu , qanwan taeba maman taeba, fatima lawan60
Maryam Yahaya, samira Eli, Indo Ado, M Y M, maman hannat, Iclass hhhh tsabar rawa saida maleek ya fito ya kashe musu djn, dan yaga basa da alaman dakatawa🥰😄.

Alhamdulillah suna yayi suna su MALEEK da AYUSH sunsha ƙyau photographer kammmm sunsha ɗaukar pics nasu ba iyaka, inda photographer ɗin ta kasance UMMI MUHD {maman humairatu}

Aikuwa kowa jikinsa ya faɗa masa, sabo da gajiya, ita kanta me jegon a gajiyan take.

***********

Bayan kwana biyu kuma kowa ya kama gabansa, sai iya ummie, kai kace gidan bai

Please Login or Register in order to submit comment