Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana jijjiga kafaɗunta ne, yasa Neelarh da Samiupter suka farka daga ɗan baccin da ya fara ɗaukar su a firgice suna zazzare ido cike da tashin hankali.



Wani irin ban ko ƙofar akayi Sannan wannan ƙaton Gardin wato Gaddafi ya shigo ɗakin cikin ƙatuwar muryarsa kuma cike da bala'i yake faɗin.





"Wani mara rabon ne, yake mana ihu anan wurin, da alama ya gaji da rayuwar sa ne..."




Ya yi maganar ne yana ƙari sawa wurin da Aasief yake a durƙushe bai dena jijjiga Zaynerb yana faɗin ta faɗa masa gaskiya ba.




Cike da tsantsan mugunta ƙaton Gardin yakai hannu ya finciko Aasief ya miƙar da shi tsaye sannan ya saita bakin bindigan hannunsa a ta bayan Aasief ɗin yana ƙoƙarin juyo da shi.


Cikin Wata kalar da fusata da zafin nama Aasief ya juya gaba ɗayansa sannan ya dunƙule hannayen sa yakai ma masa wani wawan naushi a ido.


Zubewa Gaddafi ya yi ƙasa cike da azaba idanun sa na fitar da jini.


Bin sa ƙasan Aasief ya yi Dan bala'i, yana kai masa naushi a fuska ta wurin da ya tabbatar yana masa rauni, cikin wata kalar murya kakkausa yake faɗin.





"Dan uban ka ina tambayarta abin da ya faru shekaru biyar baya, shi ne zaka shigo tsakani da wannan jahilar Muryar taka, wato dama bakasan haushin ka nake ji ba, kaine ka harbeni ko zakaci uban ka yau."



Maganar Aasief yake yana kuma kai masa naushi a ta ko'ina na fuskar sa, Aasief bai dena dukan Gaddafi ba har sai da yaga ya daina motsi alamar ya suma...






Sannan ya dakata sannan cikin fitar da huci na mugun ɓacin rai ya juya kamar wani kububuwa yana kallon Zaynerb wacce ganin abin da yake yi, yasa idan banda rawa babu abin da gaba ɗaya ilahirin jikinta yake yi, tun kafin yace da ita komai ta fara masa bayani.





Cikin lokaci ƙanƙani Zaynerb ta koroma Aasief gaba ɗaya bayanin abin da ya faru lokacin da taje Room nasa, ta faɗa masa irin tashin hankalin da ta shiga da kuma irin maganar da Erisha ta faɗa ma ta.





*Aasief*

Wani wawan naushi ya kai ma bangon ɗakin wanda har sai da gaba ɗaya ɗakin ya amsa.

Idan banda huci babu abin da Aasief yake yi tunda yake a Duniya ransa bai taɓa ɓaci ba irin na yau.


Wai ashe duk waɗannan shekarun da aka kwashe idan Zaynerb zata tuna sa, tuna sa take yi a matsayin Mazinaci mayaudari....


Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un


Zubewa ya yi a ƙasan idanun sa na fitar da ruwa.


Miƙe wa ya yi a fusace ya fara zagaye ɗakin faɗi kawai yake.






"Saina kashe Leo, Tabbas da hannuna zan kashe Leo da wancan kafirar Erisha ko tabbas sai nayi musu KISAN GILLA."






Tabbas indai lissafin sa ya tafi dai dai yadda tunanin sa ya basa ke nan dai Leo da Erisha su ne suka shirya komai na abin da ya faru tsakanin sa da Zaynerb...





"A wancan Ranar ba Ni ne na turo Miki da wannan saƙon ba, domin kuwa sace wayata akayi a Ranar, nasha wahala sosai wurin neman ta amma ban gani ba, haka na haƙura na nufi hanyar komawa gida cikin motata a hanyar ne na haɗu da Accident, ban farka ba sai washe gari na ganni a Room na ga Leo a gefe na, yana faɗa min wai a Hanyar sa na komawa gida ne, ya ganni nayi Accident shi ne kawoni gida..."






Shiru Zaynerb tayi tana sauraren abin da yake faɗa ma ta kuma yana ma ta maganar bada kakkaurar murya ba, cikin murya ma dai dai ciya yake ma ta bayanin.


"Dama Leo yasan Estate naka ne?."


Zaynerb ta tambaya har lokacin jikinta bai bar rawa ba, ga kuma siraran hawaye da suke bin fuskarta.



"No bai sani ba, kuma a lokacin ban tambaye sa ta ya akai ya sani ba."



Da bata amsar, miƙe wa ya yi tsaye yana gogen jinin dake fita a ƙafarsa.




"Ku taho muje..."



"Ina ke nan?."


Zaynerb ta tambaya tana kallon sa cikin faɗuwar gaba.


"Barin nan zamuyi, ada banyi niyyar guduwa ba, amma wannan labarin da kika bani yasa na yanke shawarar mu gudu saboda banaso Leo yakai Yammacin yau bai mutu ba."

Zaro ido Zaynerb tayi cikin tashin hankali bakin ta na rawa take faɗin



"Mu-mummtuwa fa kake faɗa....."






*ABUJA*
*Haleesat*



Baya tayi ta jingina kanta da kujerar motar ta, idanunta akan Babban Ofishin bincike reshen manyan laifuka dake Abuja. C.I.D.

Sosai ta shiga matsanancin tashin hankali da kuma damuwa na sace Zaynerb da kuma rashin lafiyar Afeefah.
Wanda sanadin haka ne koda University bata samu taje, cikin haka ne wata ƙawarta ta bata shawarar zuwa ofishin c.i.d. domin basu report duk da cewa shima Daddy yana iyakar bakin ƙoƙarin sa haka ma Maleek.


Ranar ta fito daga bathroom ta duba wayarta nan ne taga message da Maryam ta turo ma ta, cikin hanzari ta buɗe ta fara karantawa.


"Sunan sa Suhais Sulaiman Interval, just 'Interval' aka fi sanin sa da shi.
Rank Officer.
Batch Number T3,783 :: D8... Specialization.
Shekarun sa Twenty something.....
D.O.B......
Iya kar abin da na sani akan sa na faɗa miki, kije wurin sa Insha Allah zai taimaka da nasa binciken domin shi ɗin qwararren Jami'i ne wanda yasan makamar aikin sa, sannan bayada wata matsala."


Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke a lokacin bayan gama karanta saƙon.

Nan ba tare da ɓata lokaci ba tana gama shiryawa ta ɗauki mota ta tuƙa har zuwa Babban Ofishin.



Koda isarta ofishin ta nema a haɗa ta da shi.
Da farko Jami'in ƙi ya yi, amma tana faɗa masa Wanene mahaifinta a ƙasar, cikin rawar jiki ba tare ɓata lokaci ba, shi da kansa Jami'in ya kaita har gaban Yallaɓan Officer Interval, sai dai kuma menene zai faru bayan ganin sa da Haleesat tayi?.....


*What Next*


_______💓💓💓
The Nainarh Kd
💓💓💓_________



Sam Haleesat ta kasa nutsuwa tayi masa bayani yadda ya kamata a lokacin, sakamakon ganin wannan jami'in ba kowa bane fa ce, Mutumin da ta haɗu da shi a Mashaya, kuma tayi Drawing face nasa As masoyinta sannan kuma take ƙaunar sa har tayi masa laƙani da Souvenir....




Doguwar ajiyar zuciya taja bayan ta kawo nan da tunanin nata sannan ta saka hannu ta buɗe motar ta fito.


Kai tsaye office nasa ta nufa domin kuwa shi da kansa yace ta dawo yau akan binciken nasu.


Sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin haɗaɗɗen ofishin.


Amsa wa ya yi ƙasa ƙasa idanun sa akan Laptop dake gaban sa, ba tare da ya kalle ta ba.


Zama tayi ƙoƙarin yi a kujerar dake fuskantar sa, sai dai jin muryar sa da tayi ne yana magana, yasa ta miƙewa tsaye da sauri tana sakin Murmushi domin kuwa ayyana wa kawai take yi anga Zaynerb an wuce wurin.


"Mun sama labari akan wani wuri da ake zargin kidnapper's sun ɓoye Kansu ciki, yanzu haka can wurin zamuje, idan ya kasance anan cikin Abuja ko kafin Abuja aka sace ta, Confirm zai iya yiwuwa waɗanda muke zargi ne, idan kuma tun acan Kano ɗin ne..."


Katse sa tayi da faɗin.

"Bana tunanin anan Abuja aka yi Kidnapping nata, sai dai kuma ban sani ba, yanzu ne zamu tafi can ɗin?."


Kallon ya yi a nazarce kuma a gajarce jin abin da ta faɗa.


"What do you mean, do you think dake zamu tafi, ko kuma mene?."


Dariya tayi na rainin wayo tana basa amsa da faɗin.


"Of Course Ƴar uwata ce fa aka sace, idan ba'a tafi binciken nemo ta dani ba, ina kake tunanin za'aje dani?."


Haleesat tayi maganar da gaske kuma fararen idanunta tar akan sa.


Shigowar da wani jami'in ya yi yana faɗin, "Sun gama shiryawa shi ake jira ne."

Yasa ya dakata daga kallon ta sannan ya miƙe tsaye ya ɗauki bindigarsa yana gyara alburusan ciki.


"Yauwa idan ka gama gyarawa nima ka miƙomin tawa bindigar Yallaɓai Officer."


Haleesat tayi maganar a dake kuma tana masa nuni da gaske take binsu zatayi.


So yake yaga iya gudun ruwanta da iyakar taurin zuciyar ta da jarunta.

Saboda haka ba tare da yace da ita komai ba, ya miƙa ma ta ƴar ƙaramar bindigar da ya fito da ita daga cikin locker a ofishin.



Sai dai ga mamakin sa karɓa tayi tana gyara zaman alburusan ciki.


Cike kuma da tsantsan qwarewa, tamkar dama can ta saba da amfani da bindigar.






Toh haka ma koda aka zo tafiya, dagewa Haleesat tayi akan dole dole da ita zasu tafi, idan kuma sun ƙi zata kira Daddyn ta faɗa masa.


Zuwa lokacin ran Interval ya fara ɓaci sai dai ya shanye.


Bisa umarnin na sama da shi a aikin wato Chief Murtala Dawood da yake shugaba a duka Ofishin badan Interval yaso ba.

Haka suka kama hanyar zuwa can wurin samamen da zasu kai tare da ita, bayan an bata rigar tare alburushi ta saka kamar dai sauran Jami'an.


Duka su takwas zasu tafi sumamen duk da Haleesat ce suka zama tara, sai kuma wata mace ita ma Jami'a ce amma ta kasance Likita ce tana taimakawa waɗanda suka sama rauni a filin da ga.




*Aasief*


Da dabara da taimakon Allah suka samu suka fito daga cikin wannan Gabjejan gidan, yana saɓe ne da Neelarh wacce a lokacin da suka zo fitowa daga gidan, wani daga cikin kidnapper's ɗin kuma mai kula da gidan ya gansu.

Ya saita bindigar sa zai harba Aasief ita kuma ta tare, harsashin ya wuce ta saitin kunnen ta da wani ƙara fiiiooo, wanda dalilin hakan ji da ganinta na ɗan lokaci ya dakata, tayi ƙasa zata faɗi, Aasief ya tarota bayan yakai ma mutumin mahangurɓa ɗaya ya zube sumame.


Zaynerb kuwa hannunta yana cikin na Samiupter ne, yayin da ɗayan hannun ke riƙe ƙam cikin na Aasief.


Gudu kawai suke falfalawa na tashin hankali, gudun suke amma tamkar basa yi, tun kafin Rana ta sauka suke gudu basu dakata ba, har sai da duhu ya yi gaba ɗaya dajin ya gauraye da duhun dare.


Cike da tsananin gajiya suka zube bakin wata doguwar hanyar da ta rabu gida biyu ɗaya yabi left ɗayan Kuma right.





"Wayyo Allah na shiga ukuna ni Zaynerb wannan wata kalar mummunar ƙaddara ce, inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, Allah ka kawo mana ɗauki..."




Maganar take yi a galaɓaice cikin fitar hayyaci idanunta suna buɗewa da rufewa da sauri sauri kuma lokaci ɗaya.




Dukkansu sun sha wahala sosai, wahala kalar wacce ko wannensu bai taɓa tunanin zai shiga makamancin ta ba a rayuwa.


Especially ma Samiupter D'Souza ita da take Bama ƙasar take ba, amma da yake haka zanen ƙaddara yake gata yau ta wayi gari cikin wani hali.





"Neelarh kiyi haƙuri Kinji, duk ni ne na janyo kika shiga halin da kike ciki a yanzu, da'ace nayi haƙurin mintuna talatin kacal mu sama jirgi da duk ba hakan ba."




Zaynerb uban tagumi ta zabga hannu bibbiyu tana kallon sa, yayin da wasu hawaye waɗanda ba za ta ce na Menene ba suka cicciko ma ta a idanu.



Allah Sarki ita, ga ita Neelarh tana ma da wanda zai kalleta ya bata haƙuri ya lalleshe ta As a partner.



Ita kuma fa, one zero ke nan, ko kafin ta an kara wasu hawayen sun ƙara wanke ma ta fuska.




"Allah Sarki Afeefah ta, wayyo rayuwa da ƙaddara Daddyna kuyi haƙuri nasan kun shiga damuwa sosai, amma ni nasan kaso Tamanin bisa ɗari na abin da yake tsakiya da faru dani, ni ce ma jawa kaina tabbas..."



Ƙarishe maganar zucin tayi cikin ƙunar rai da kuma tarin da tasani mara amfani, mugun fusatar zuciya ta kaita ta baro.


Kallon Samiupter dake kwance tayi ɗai ɗai a tsakiyar kwalta Zaynerb tayi tausayin kanta dana Yarinya yana ƙara cika ta.


*SHIN ZAKU IYA YARDA IDAN NACE A WANNAN WURIN SUKA KWANA GABA ƊAYA?.....*



Tabbas haka ne da gaske anan wurin suka kwana cikin duhu da cizon sauro ga sanyi, gashi cikin daji, gaba ɗaya Ƴan matan saman jikin Aasief ko wacce ta sama wurin maƙalewa, sakamakon wani irin tsoro da suke ciiki da ji, domin kuwa can cikin dare suka dinga ji kamar muryoyin mutane cikin kuka, ko kuma da ƙarar raki marasa daɗin sauraro, hardama ifa ce ifa ce na mutane dana dabbobi harma dana Alhan.👹





Shima Aasief dan ya cika cikakken Namiji ne, haka suka kasance sun kwanta a wurin maƙale da shi kowacce tana sakin numfashin wahala cikin bacci, yayin da shi kuwa Aasief haka ya kwana idanun sa a buɗe, domin kuwa bai ga sukunin da har zai samu ya yi Bacci ba.






Koda gari ya waye haske ta ko'ina tan garas, haka gaba ɗaya su ukun suka yi tai mama suka fara jero sallolin da babu adadi, sannan kuma ta inda zuciyarsu ta raya musu nan ne Alƙibla.

Yayin da Samiupter tayi tsuru tsuru tana kallon su.



Basu motsa daga wurin ba, koda suka idar da Sallahr a wurin suka dakata ko zasu sama wani na kirki da zai biyo hanyar.
Toh kodama sunce zasuyi gaba basu san wacce daga cikin hanyoyin da suka rabu biyu zasu bi ba sam.



*RAYUWA KE NAN*😓



Wai yau an wayi gari ga Zaynerb Mai Kyau tsakiyar titi tana neman taimako, wanda zai rage musu hanya.


Faɗi take.....
"Taimako a taimake mu Dan Allah ku tsaya ku taimake mu mutane mu wayyo mu tsaya...."



Haka kawai take faɗa cikin yarfe hannu a tsakiyar titi, Aasief yana daga gefan ta shi ma yana iyakar nasa ƙoƙarin wurin ganin sun sama na kirki da zai taimaka musu.



Cikin yardar Allah kuwa wata babbar mota irin na kiwon shanu ta taho zata wuce ta hanyar.


Ihun neman taimako da Zaynerb keyi Neelarh na tayata ne yasa Driver motar ya dakata sannan ya fito daga motar shi da karen motar (mai kula da fasinjoji) da farko a tsorace suka fito, ganin mutane tsakiyar titi mata uku da Namiji suna neman taimako, ga Zaynerb wacce fuskarta tayi buɗu buɗu da ƙura, idanunta sun yi zuru zuru dasu. Ta zama kamar wata Dodo da ita.😟



Amma daga ƙarshe da suka fahimta bayan ƙari sawa wurin da suka yi, Zaynerb ke faɗa musu su taimake su kidnapper's ne suka yi garkuwa da su yanzu sun samu sun kubta ne da yardar Allah. Kuma Abuja suke so a ƙari sa dasu.


Jin abin da Zaynerb da ta fi zaƙewa ta faɗa ne yasa karen motar yaji tsoro yana shirin arcewa ana kare.😆



Amma sai Drivern ya dakatar da shi, sannan cikin tausayawa Dattijon Driver da bazai haura shekaru hamsin da ɗauriya ba.



Ya kalla Zaynerb yana miƙa ma ta gorar ruwa da ya ɗauko, sannan yana faɗin.



"Karku damu Yarana Insha Allah kun tsira tunda har kun haɗu damu. Dama kuma Abuja muka nufa kai tsaye."






"Masha Allah, Mun gode sosai Baba da wannan taimakon."


Cewar Aasief yana shafa kansa, sannan yana miƙowa Neelarh gorar ruwa da Zaynerb ta basa bayan ta sha, ba tare da ya sha ba.



Kwankwaɗar Ruwan Neelarh tayi sosai, sannan tabawa Samiupter ita ma tasha cikin wahala, dama magwogwaronta a mugun bushe yake ga yunwa.






Nan batare da ɓata lokaci ba gaba ɗaya suka shishshiga motar a baya, don gaba ya yi musu yawa a bayan wurin da shanu da tumaki suke zama nan suka zauna, wai danma babu dabbobin a motar ne, sunje kudu sun siyar sun dawo, shi ne fa a hanyar suka haɗu dasu Zaynerb ɗin.






*RAYUWA KE NAN WAI YAU GA ZAYNERB MAI KYAU KWANCE CIKIN MOTAR KWASAR TUMAKI.*😭😭😭


*TABBAS KIDNAPPING SU ZAYNERB DA AKA YI, SHIRYAWA AKA YI,😣 SAI DAI WANENE YA SHIRYA HAKAN?.*🥺


🔥*WHO IS THE MASTER PLANNER??*🔥





















Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment