Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

be, asha shagali lafiya, tunda babu gayya ta."


Dariya kawai Afeefah tayi bata ce komai ba, sannan suka yi sallama.




"Uhum Mister Sabbir Mai Naira, ka wani zubamin idanu ina waya, sai kace baka taɓa ganina ba."


Lailah tayi ma Sabbir Maganar tana mayar da wayar nata cikin haɗaɗɗiyar jakar ta.



"Uhum Miss Lailah Mai Kyau ba dole na zuba Miki idanu ba, wannan kyau haka kamar wata SARAUNIYAR KYAU gaskiya kin haɗu sosai."


Sabbir ya bata amsa cikin zabga Murmushi idanun sa akan ta.



"Okay Nagode sosai, sai dai inaga muyi maganar da ta haɗa mu anan, kace Kanada maganar da zaka faɗa min mai muhimmanci, saboda haka Go ahead ina sauraren ka."




Lailah tayi maganar tana gyara zamanta idanunta akan sa, kamar yadda nasa suke akan ta.




Shiru Sabbir ya yi da alama yana tauna maganar da zai faɗa ma ta ne, bayan ƴan sakanni yaja ajiyar zuciya still idanun sa akan ta sannan yace.



"Ina son ki, Lailah da gaske ina ƙaunar ki, please zaki Aure ni?."




Tamkar saukar aradu haka Lailah taji maganar da Sabbir yake faɗa ma ta cikin tsakiyar kanta.



Ware idanunta tayi tarr, tana masa wani irin kallo mara fassara.




"Sabbir I You Mad?. So fa kace, wai kuma da gaske Ni ce kake so?, Lallai baka da aiki."




Lailah tayi maganar ranta a mugun ɓace tana miƙe wa tsaye zata bar Restaurant ɗin.



"Yes Lailah I'm Mad akan ki, tabbas na zare akan ki."



"Sabbir wallahi bani da lokacin ka fa."



Lailah ta basa amsa tana ƙoƙarin barin wurin zuciyar ta na bugawa da sauri sauri.


"Ki dakata Lailah da gaske nake Auren ki nakeson yi, wai duk menene hakan, bakya so na ko mene?."





Dakata wa tayi da tafiyar da take yi sannan ta juyo tana kallon sa da idanunta da suka yi jajur take basa amsa da faɗin




"Yes Sabbir bana sonka, kuma ban taɓa son ka ba, kawai dai a matsayin aboki na ɗauke ka, bawai saurayi ba, please ka rabu dani, bani da niyyar sonka balle kuma Auren ka, wallahi tallahi kaji ma na rantse maka?."




Da gama faɗin hakan ta saka kai ta fice daga Restaurant ɗin, bata damu da irin kallon kinyi rashin mijin Aure da ƴan matan Restaurant ke bin ta dashi ba.





Tamkar wani sakarai ko nace zararre haka Sabbir ya koma ya zauna daɓas saman kujerar ya yi zaman ƴan bori.



This is the first time da wata ƴa mace ta kalla tsaban idanun sa ta furta bata son sa balle kuma tunanin Auren sa.


Saboda haka sosai maganar da Lailah ta buga masa ta bugi zuciyar sa.


Ya kasa koda kwakwkwaran motsi a wurin.


"Bata sona kuma bata da da niyyar sona."

Haka Kawai Sabbir yake faɗa tana maimaita wa a fili zuciyar sa na tuƙuƙi.


Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un


Shi kuwa yake furta wa cikin tashin hankali, ya ya zayyi da Dakon sonta da ya ɗauko babu gammo.😣





*The Queen Afeefah*💓

Sosai suka sha Shagalin da Jiddarh Komai Naga, ta shirya musu isu isu Ƴan Mata da aka tantance domin shiga Gasar Miss Nigeria.




Sun ƙayatu iya ƙayatuwa da shagali, sun yi lafiya sun watse lafiya ko wacce ta koma state nata harda Jiddarh, dama Afeefah ita ce kaɗai ƴar Abuja, sai dai sauran suma akwai Waɗanda suke zaune a Abujan.









Karon da taji tayi da mutum ne, yasa ta ɗago kyawawan idanun ta domin ganin ko wanene?.





A dai dai lokacin shima kuma ya ɗago nasa Blue eye ɗin ya zuba ma ta.





"Lah ashe ma kaine, na ganeka fa, ba kaine mutumin da na haɗu da kai a Shopping Mall ba, har muka yi magana akan inaso ka bani perfect perfume, kaƙi ka bani, kuma kaine wanda na gani lokacin da muke video call da Haleesat a gidan Sunainah, ko duk ba kai bane faɗa min?."




Afeefah tayi maganar ne tamkar wacce ta yi tatul da barasa, zama tayi saman kujera dake wurin idanunta da suke lumshewa akan sa.





Da hannu ya yi ma Bodyguard na sa alama da karya ƙari so wurin, dan ya lura niyyar ƙari sowa wurin yake da shi.




Haka kawai yaji yana marmarin magana da ita, ba tare da dalili ba, don kuwa ji ya yi tamkar ya taɓa jin kalar muryarta a wani wuri bayan haɗuwar da suka taɓa yi a shopping Mall.






"I You in drink?."



Ya yi ma ta tambayar da take bakinsa bayan ya zauna a kujerar dake fuskantar wacca take kai.





Zare fararen idanunta tayi cikin sauri tana ware su akan sa jin abin da yace da ita.

Kamar wata ƙaramar Yarinya haka Afeefah ta koma cikin taɓe baki da shagwaɓa kamar mai shirin kuka take faɗin.





"Wayyo Daddyna, ga wani yana kiran Shalelen ka da ƴar basara, kazo ka taimake ni..."😆


Tayi maganar kamar dai bata hayyacinta tana zaro wayarta daga Aljihun tsadadiyar jakar ta sannan ta lalubo lambar Daddyn wai da gaske kiran sa zatayi ta faɗa masa abin da aka ma ta.🤓


Sai dai rashin sa'a domin wayar a kashe take.


Dariyar gefan fuska wacca bayyi shirin fitowarta bane ta kufce masa.


"Kaga kayimin laifi huɗu ke nan ko?. Na farko ka hanani perfect perfume. Na biyu idanunka sun kusa sakawa nayi Accident. Na uku ka kira ni Ƴar barasa. Na huɗu kana yimin dariya saboda na kira Daddy wayar sa a kashe. Saboda haka saina kira maka Saurayina yanzu yazo ya ramamin...."



(_-_Mun bani🥺 Anya kuwa Afeefah qalau take kuwa 🤔_-_)





Idanunta suna lumshewa kamar mai jin bacci, a hakan Dan bala'i take lalubo lambobi cikin tsadadiyar wayar hannun ta, gajiya tayi batasan wata lamba zata kira ba, yasa ba tare da tunanin komai ba, ta danna kira da lambar da hannun ta ya kai kai.




"Kasan menene kuwa, Saurayina yana sona sosai kuma fa sunan sa 'Rishi' sannan..."


Gajiya da surutun ta da ya yi ne yasa shi tambayarta ta hanyar faɗin


"Do you know who really i am?."



Kallon sa tayi tana lumshe ido, ita ma ta mayar masa da kalar tambayar da ya yi ma ta da cewa


"Kasan ni Wacece kuwa?."


Shiru tayi sakamakon ƙari sowa wurin da wani daga cikin securities nasa ya yi.


Miƙa masa waya Baturen security ya yi cike da girmamawa sannan ya juya ya bar wurin.


"Okay pick up."

Ya faɗa a gajarce idanun sa akan Afeefah.
Murmushi ta saki ganin an yi picking call da take yi, kara wayar tayi a kunne tana faɗin


"Hello Rishi Dear kana inaaaa..."


Tsitt Afeefah tayi tana zazzare fararen idanunta sakamakon jin muryarta da tayi raɗau tana fitowa daga cikin wannan tsadadiyar waya ta gaske dake hannun sa.


"Lah wai kaine mutttt..."

Shiru tayi tana kuma zare ido dan batasan abin faɗa ba.


"Wai kina nufin kice kece Yarinyar da take takuramin da kira muddun na shigo ƙasar nan, Ke nan kece 'RISHITA'?."


*TASHIN HANKALI*😳


Rasa abin yi ne yasa Afeefah ta miƙe tsaye sannan ta ciro Takalma masu tsini dake ƙafafunta, ta gyara jakar hannunta, sannan ta kallesa tamkar wata ƙaramar Yarinya tayi masa Grin (Gwalo) kana ta ruga a guje ta ƙari sa wurin motar ta da sauri sauri gaban ta buga wa take faɗi ga Mosses Driver.





"Mosses yi sauri ka ja motar nan mu bar wurin nan tun kafin wancan mutumin mai shuɗayen idanu ya kamani."



Tayi maganar tana jefa jakar ta cikin motar sannan ita ma ta shiga ciki, shi kuma Driver Mosses ya ja motar da gudu duk ya tsorata, ya bar Park ɗin da ita.🤣😂😘




*Three Hours To Go*



Wuntsilowar da tayi daga saman Royal Bed nata ne tare da azabar da ya ziyarci dukkan ilahirin sassan jikin ta, yasa ta saki wani marayan ihu tana gungure a tsakiyar Room ɗin jikin ta nan naɗe da Blanket gaba ɗaya gashin kanta ya barbaje ya rufe ma ta fuska.





A hankali take buɗe fararen idanunta da alama Bacci bai ishe ta ba.



Miƙa tayi tana jan wata doguwar hamma, kama sumar kanta da ya rufe ma ta fuska tayi sannan ta ɗaure a tsakiyar kanta.


Hannu takai tana laluben ta wurin da zata jiyo wayar ta, jin babu alamar wayar ne yasa ta miƙe tsaye magagin baccin da tayi bai gana sakin ta ba.




Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta fito kai tsaye Palo ta fita dan tanada tabbacin Deejarh ce ta ɗauka ma ta wayarta ba kowa ba.



"Deejarh! Deejarh!! Wai kina ina ne zo nan ki bani wayata kafin na nemo ki."



Afeefah tayi maganar daidai lokacin da ta ƙari sa ƙofar Bedroom na Deejarh sannan ta shiga.


Can saman Bed ta hangota ta juya baya da alama Game take bugawa.



Hawa saman ɗin tayi sannan ta karɓe wayar daga hannun Deejarh ɗin tana faɗin

"Ke Deejarh yaushe kika san password ɗin da na sakama wayata?."


Tayi ma ta tambayar tana nufar hanyar fita daga Bedroom ɗin ya yin da ta dan nawa Jiddarh kira ta wayar, ba damuwa da amsar da Deejarh zata bata tayi ba.




Palo ta fita sam bata lura da Lailah dake kwance tayi nisa a Duniyar tunane tunane ba, ta ƙari sa saman 1sieter ta zauna, Deejarh da ta biyo ta a baya tana faɗin


"Lallai ma Balarabiyar India ai ba password mai wahala kika saka ba, just 'Perfect' fa kawai kika saka abu mai sauƙin."





Deejarh tayi maganar tana zama ganin Afeefah ta fara waya ne, yasa ta mayar da kallon ta kan Lailah cike da mamaki dan ita ma bata lura akwai mutum zaune a palon ba. Sai yanzu.





"Hello! da Queen Of Beauty na Kano wato Jiddarh nake magana, ko kuwa ba ita bace, dan kuwa idan ita ce Bala'i zata sha na ƙin ƙara wa..."





Dariyar ƙeta Jiddarh tayi daga ɓangaren ta tana faɗin


"Tabbas Jiddarh ke a kan layi, wacece ke magana?, idan Queen Of Beauty ta Abuja ce wato Afeefah toh ta riƙe layi akwai labarin da nakeso na bata."



Katseta Afeefah tayi da faɗin


"Tabbas wannan muryar ta Jiddarh ce mara kirki kawai, wai ma da farko menene kika sakamin da lemon da kika bani ne?."





Dariya Jiddarh ta tuntsire da ita, tuna tsiyar da ta shuka, sai da tayi mai isarta sannan ta dakata dan kanta tana bawa Afeefah amsa da faɗin.





"Allah kuwa da gangar nayi duk abin da nayi, domin kuwa gani nayi kamar kina damuwa bakyama kowa Magana a wurin anata shagali banda ke. Shiyasa ni kuma na saka miki kwayar da zai sa ki dinga zuba taɗi ko ba'a tambaye ki ba, a lemo sannan na baki ke kuma ƴar qwalama kika kwankwaɗe lemon."🤣


Jiddarh ta ƙari sa maganar cike da shaƙiyanci tana dariya cike da nishaɗi



"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, Aikuwa Queen Of Beauty kin cuceni kin saka na saki baki a wurin da bai kamata ba nayi abin da bai dace ba."😑







Zaro ido Jiddarh tayi cikin Dariya tana tambayar Afeefah abin da ya faru


Cike da takaici Afeefah ta kwashe duka abin da ya faru tsakanin ta da Official ta faɗa wa Jiddarh ta ƙara da cewa


"Kuma fa yanzu nasan kallon wata Fan's ɗin sa ko kuma wata muguwar masoyiyar sa yake yimin fa."


Afeefah ta ƙari sa maganar tana kyaɓe fuska cike da takaici Jiddarh ta cuceta



Jiddarh tsaban dariya batasan lokacin da ta faɗo ƙasa daga saman kujerar da take ba, faɗi take


"Aikuwa Queen Of Beauty Wannan Drama naki ya kusa kala guda da nawa, sai dai nawa akwai takaici ciki bisa naki fa."


"Okay, ke Menene ya faru dake ɗin Afeefah ta tambaya cike da qwulewa na dariyar da Jiddarh take ma ta, ga kuma Deejarh kamar wata mahaukaciya ita ma daga ɓangaren ta tana dariya na jin labarin da Afeefah ta bawa Jiddarh, ita ma Lailah duk da bata cikin yanayi na nishaɗi sai da abin da Afeefah tayi ya bata dariya.



Sai da Jiddarh ta saita nutsuwarta sannan ta koma ta zauna sannan ta fara cewa


"Queen Of Beauty Ina baki Story mun iso nan Kano lafiya mun sauka a Jirgi ni da Humaira da tayimin Rakiya, anan Airport naga wani haɗaɗɗen Guy ina baki labari kyakkyawa da shi, ƙarshe a kyau Guy nan yake.
Kin sanni bana gani na gyale, ganin yadda gaba ɗaya Ƴan matan Airport suke binsa da wani mayen kallo ne, yasa ba tare da shawara ko tunanin komai ba, na cire facemask dake rufe da fuskata sannan na cire After Dress dake saman kayana, nan fa na bayyana cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU na, nan hankalin mutanen Airport ya dawo kaina waɗanda suka gane ni suka ƙari so wurin da muke nida Humaira cikin tafiya na gayu, gaba ɗaya suka rufe ni daga masu roƙo akan na tsaya muyi pictures, sai masu bani Biro da takarda wai nayi musu sa hannun ƙauna.

Abin takaici wanda nayi hakan danna na burgesa ya bar wurin, amma waɗannan mutanen basu gyaleni ba sai da kyar fa nake gaya miki.."





Dariya Afeefah tayi tana tambayarta da faɗin

"Ke nan dai idan na fahimta kinyi abin da kika yi ne, saboda ki burge wannan Guy sai kuma aka yi rashin Nasara mutane suka shiga tsakani ko?."


"Yes of course haka fa nake nufi."


Jiddarh ta bata amsa. Nan dai suka ci gaba da shan fira ko wacce tana bada labarin abin dariya tamkar waɗanda suka yi one Year ko fiye da haka da haɗu wa, bacin sau biyu kawai suka taɓa haɗu wa.



Sai da Afeefah ta kammala waya da Jiddarh sannan ta kuma dan nawa Daddyn ta Mister Mai Kyau dake Jamus kira dan tayi kewar sa sosai.



"Assalamu Alaikum Daddy wato shi ne koka kirani ko?. Ae nayi fushi ma."😩



Afeefah tayi maganar cike da tsantsan shagwaɓa ga Daddyn nata.


Ƙayataccen Murmushi Mister Mai Kyau ya yi daga yadda yake zaune a hamshaƙe saman kujerar sa ta alfarma cikin haɗaɗɗen ofishin sa dake hawa na ƙarshe cikin katafaren company nasa dake can Germany (Jamus).


"Wa'alaiki Salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu. Kaina bisa wuya Shalele uzurori ne suka yiwa Daddyn ki yawa sosai, shiyasa ban samu na kiraki ba, sannan ae nayi tunanin Zaynerb ta dawo ne, kodai ba yau ne zata dawo daga Kano State ba?."

Wani irin bugu na tashin hankali kuma mara dalili zuciyar Afeefah tayi jin Daddy ya ambaci Zaynerb, ita fa wallahi shaf ta manta yau Zaynerb zata dawo Abuja, cikin sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta duba Time 4:50pm hankali a tashe ta mayar da wayar kunnen ta tana faɗin.


"Subhanallah, Daddy Anty Zaynerb fa bata dawo ba, nifa gaba ɗaya na manta yau zata dawo, kuma tun jiya da muka yi waya da ita ta ce Yau zata dawo bamu ƙara waya ba fa, wayyo Daddy tsoro nakeji kar wani abu ya sama Anty Zaynerb na..."



Jin yadda Afeefah take maganar hankalin ta a mugun tashe ne.

Yasa Daddy saurin tarar ta da faɗin.


"Ki kwantar da hankalin ki wata ƙilama Zaynerb ɗin ta fasa dawowa Abuja yau ɗin ne fa, amma dai gudun zargi riƙe waya, barina tuntuɓi Uncle Sagir naku muji."





Da "Toh." Kawai Afeefah ta amsa masa amma bata tunanin zata iya kwantar da hankalin ta, bacin batasan halin da Zaynerb Yayarta take ciki ba.


Tsuru tsuru Lailah da Deejarh harma da Haleesat wacca tashin ta daga Bacci ke nan ta fito palon a gaɓar da Afeefah take faɗin Zaynerb bata dawo ba.








"Assalamu Alaikum Babban Yaya. Yau Harkokin Kasuwanci sun bari an tuna damu ke nan, tun da naga kira da Yamma nan."




Uncle Sagir ne duk yake waɗannan maganganun cike da farin ciki na ganin kiran da Ɗan uwan na sa ya yi masa.


"Sagir ba wawan ne a gabana yanzu ba, wai nace Zaynerb ta fasa dawowa Abuja ne, sai ta ƙara kwanaki ko kuwa, Afeefah ta kirani tana faɗin Zaynerb bata ƙari so ba har yanzu."




Cikin sauri Uncle Sagir ya katse Daddy da faɗin.


"Zaynerb kuma wata Zaynerb ke nan, wai dama ba tun jiya Zaynerb kuka ce ta koma Abuja ba?."


Ya yi tambayar yana kallon Mah'fuz dake zaune gefansa yana jin abin da ke faruwa.




"Zaynerb kuma Abhu anya kuwa, ae Zaynerb tun jiya tabar nan, ta ce zata koma Abuja, babu yadda bamu yi da ita ba, akan ta tsaya gari ya waye saboda a jiyan babu Flight, amma Zaynerb taƙi ji saboda taurin kai da Yammacin ta ɗauki Driver da mota suka nufa Abuja, gashi kuma har yanzu Drivern bai dawo ba..."


Duk wannan maganar Mah'eesha ce take zubosu a lokacin da ta ƙari sa shiga cikin palon mahaifin nasu sannan ta a je masa kayan maƙulashe da ta kawo masa saman center table.






"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, na shiga ukuna Daddy kanaji fa wai cewa suke Anty Zaynerb ɗita tun jiya ta kamo hanyar zuwa nan, gashi kuma har yanzu batazo ba, Daddy tsoro nakeji kar'a cutar min da Yayata Daddy please kayi wani abu kaji Daddy i'm begging you please Dad say something to me pleased......"



Ƙari sa maganar Afeefah tayi cikin tsananin kuka muryarta na fita da kyar kuma cikin wahalar fitar numfashi.



"Subhanallah Afeefah menene nakeji kike faɗa ne, wai kina nufin Zaynerb bata dawo ba, inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un menene ke nan yake faruwa i'm so confusing fa."

Uncle Sagir ne yanzu ya yi maganar jin muryar Afeefah da kuma irin abin da take faɗa.






"Afeefah! Afeefah!! Kina jina kuwa, please kiyi magana mana?...."


"Na'am Daddy ina jinka domin ban mutu ba, tukunna amma muddun ba'a nemo min Ƴar uwata Zaynerb ba. Tabbas Daddy zan iya mutuwa a kowane irin lokaci...."




"Subhanallah Afeefah kina da hankali kuwa kin san menene kike faɗa, nace ki kwantar da hankalin ki Zaynerb ba ɓata tayi ba Insha Allah za'a ganta kinji Shalele ta!?...."



Tanaso tayi magana sai dai abin da ya tokare ta a maƙushi shi ne ya hanata yi magana.


Ji take a maqwoqwaronta tamkar ana jajjagen yaji a ciki duk yadda taso tayi magana abin cutura ya yi.



Zubewa tayi a ƙasa sumammiya yayin da bakinta yake fitar da wani irin kumfa tamkar wacca tasha poison.


Da gudun tsiya gaba ɗayan su tun daga Haleesat da Lailah har da Deejarh suka ƙari sa kanta suna kiran sunan ta cikin tsananin tashin hankali.


Sai dai ina Afeefah ba jinsu takeyi ba domin kuwa tashin hankalin da ta shiga ne yasa ciwon ta yake ƙoƙarin tashi.



*TASHIN HANKALI*
*WANDA BA'A SAKA MASA RANA*


Tofa fi ye da haka gaba ɗaya Ahalin Mai Kyau suka shiga domin kuwa Afeefah ciwo ya tashi kuma yazo da mugun gardama.

Yayin da ita kuma Zaynerb an tabbatar da saceta akayi. Sai dai a yadda labarin yaje musu bawai ita kaɗai kidnapper's ɗin suka sace ba harda wasu mutanen.








A Ranar da abin ya faru M.MK ya dawo ya biyo ta private jet. Nasa ya dawo ƙasa Nigeria cikin tsananin tashin hankali domin kuwa abin haɗe masa biyu ya yi ga ciwon Afeefah wanda baya jin magani ga kuma ɓatar da Zaynerb tayi. gaba ɗaya yabi ya fita hayyacin sa, danma wani abun Maleek ne yake yi da kansa musamman akan binciken nemo inda Zaynerb take.





Gaba ɗaya Ahalin sam basa cikin kwanciyar hankali na abin da yake faruwa, tsawon kwanaki uku ke nan da sace Zaynerb kuma babu ita babu labarin ta, sannan kidnapper's basu kira sun faɗa adadin kuɗaɗen da suke so a basu ba.

Wanda hakan yasa aka fara zargin da wuya idan saboda kuɗi suka yi Kidnapping nata.


Babu shiri gaba ɗaya Ahalin Uncle Yusuf suka tattaro suka dawo Abuja Gidan Mister Mai Kyau da zama har zuwa Ranar da kidnapper's ɗin zasu kira su faɗin Abin da suke so.



A 6angaren Momy Rafi'at kuwa za'a iya cewa tafi kowa shiga tsananin damuwa na sace Zaynerb da aka yi da kuma ciwon Afeefah.


Sai dai na ciki na ciki, Dan ita kaɗai tasan Gadar Zaren da take shiryawa


*WANNAN KE NAN*
*KAƊAN DAGA CIKIN IRIN HALIN DA AHALIN MAI KYAU SUKA SHIGA SAKAMAKON KIDNAPPING ZAYNERB DA AKAYI*




*ZAYNERB*😣


"Na kammala fa."

Tayi maganar tana kawar da idanunta da kallon sa, sai dai cikin rashin sa'a suka shiga cikin na Yarinyar da yake tare da ita kuma ta ambaci kanta da matar sa.

Rumtse idanun nata tayi ƙam tana nuna kalar baƙar wahalar da suka sha hannun waɗannan kidnapper's.


A lokacin da ɗaya daga cikin su ya sanar police sun sama labarin wurin suke, cikin gaggawa gaba ɗaya kidnapper's ɗin, suka tattara mutanen da suka yi Kidnapping, cikin wasu motoci tamkar awaki haka suke zuba mutane a motocin. Sannan suka bar wurin dasu, tsawon kwanaki biyu suna tafiya dasu suna shiga dasu cikin tantagaryar daji, sannan bayan shafe kwanaki biyu da sa'o'i suka ƙari so da su wani ƙurman gida ƙaton gaske cikin dajin.




Sosai mutum zai yi mamakin ganin irin wannan gida a daji.
Cikin gidan suka shishshiga dasu Zaynerb kamar wasu awakai, sannan ne aka fara neman wanda zai cire wa Aasief harsashin dake ƙafarsa, da muka wata Budurwa ita ma da alama tayi musu taurin kai ne, suka harbeta a kafaɗa.




A lokacin cike da Qwarin gwiwa Zaynerb ta ce dasu ita likita ce saboda haka zata iya kula da masu raunuka.


Ba tare da ɓata lokaci ba suka ware ma ta wani ɗaki a cikin gidan sannan suka kai ma ta kayan aikin da zata buƙata.


Nan ne fa da shigarsu ta fara ƙoƙarin cire masa harsashin.

Ta sha wahala sosai sannan da kyar ta samu ta cire tana haɗa uban haɗa gumi sannan take cewa da shi ta kammala.


A hankali ya janye ƙafar tasa yana rumshe idanu saboda azaba.


"Karka damu na haɗa maka da Allurar kashe zafi, zuwa anjima zaka nema zafin ka rasa."

Zaynerb tayi maganar ba tare da ta kallesa ba, bayan ta buɗe idanunta sannan ta ƙari sa wurin ɗayar Budurwar da aka harba a kafaɗa.


Cikin taimakon Allah Zaynerb ta samu tayi ma ta treatment da ya kamata, sannan ta kalleta tana ƙare wa irin shigar dake jikin Budurwar kallo, ta tambaye ta


"What is your name?."


Tayi ma ta maganar da turanci ne dan ta fahimci da wuya idan tanajin Hausa


"Samiupter D'Souza..."


Budurwar ta bata amsa.


"Daga wata ƙasa kike, kuma menene ya kawoki nan ƙasar, sannan garin ya ya waɗannan mutanen suka yi Kidnapping naki?."


Zaynerb ta jero ma ta tambayar kamar wata ƴar jarida idanunta akan Budurwar da ta kira kanta da ' Samiupter '.



"Ƙasar Indiya nake yanki kudanci, nazo Birthday Party na ƙawata ce, a hanyar mu na zuwa Abuja daga Kano waɗannan mutanen suka yi garkuwa damu, kuma sun kashe Ansha, dama tare da ita nake. Ta ce zata rakani Abuja saboda ban san kowa anan ƙasar ba."😭



Cikin kuka Samiupter ta ƙari sa bawa Zaynerb labarin muryarta har dashewa tayi saboda tsananin tashin hankali da wani irin hali da take ciki.


Rungumo ta Zaynerb tayi tana lallashi cike da tausayin ta.

Yayin da shi kuwa Aasief ido ya zubawa Zaynerb ɗin yana kallon ta.


Neelarh kuwa tuni baccin wahala ya yi gaba da ita tana daga gefen sa ta jingina da kafaɗarsa.



"Zaynerb kin canza sosai kamar bake ba, kuma ban san dalili ba, kece kika yimin laifi, amma ni kika ɗaura wa laifin..."


A hankali Zaynerb ta juya ta kallesa jin irin maganar rainin wayo da yake son kawo ma ta, ranta a ɓace ta basa amsa da faɗin.


"Aasief kaine ka canja ba kamar yadda na sanka ba, ka canja daga Aasief mutumin kirki dana sanka, gaba ɗaya halayyar ka basu yi ba, ban taɓa tunanin ka da irin halin da na tsinceka ciki ba a wancan lokacin, ka rasa wacce zakayi Alaƙa da ita sai wannan Arniyar Erisha haba wallahi ka bani mamaki ba kaɗan ba."



Zuwa lokacin kansa ya fara ɗaurewa da kalaman Zaynerb, sam bai fahimci abin da take nufi ba kwata kwata.


"Kiyimin bayani yadda zan fahimta, nifa cikin ruɗani kawai maganganun ki suke jefa ni, dan ban san inda suka dosa ba sam."


Wannan karon kallon sa tayi da kyau idanunta na cika tab da kwalla take faɗin.


"Haba mana Aasief ya kakeso ka mayar dani shashasha ce, ko an gaya maka wancan Ranar da kace na sameka Gidan ka banga komai bane?."





"Me kike nufi ne Zaynerb, wacce Ranar kuma?."



"Kaji ko ƙara raina min wayyo kakeyi fa, wancan Ranar mana da dare da saƙon ka ya shiga wayata kana faɗin nazo Estate naku gidan ka, ko kuwa dai ka manta Ranar?...."


Dafe kansa dake mugun sara masa Aasief ya yi wani tunani tana ɗar suwa a Ransa, cikin sauri ya kalleta don ya ƙara tabbatar da tunanin sa, yake tambayarta da faɗin.




"Ina jinki a Ranar menene ya faru da ki ka zo Estate bayan kin ƙari so Room nawa, menene ya faru, please Zaynerb Tell me anything everything, please ki faɗa min duka abin ya faru da kuma wanda kika gani?."





Cikin tsorata da irin yanayin da ya fara shiga, idanun sa sun yi jajur na ɓacin rai Yayin gaba ɗaya jijiyoyin kansa suka tatashi, kai kana ganin sa kasan ransa ya yi matuƙar ɓaci.




Bai damu da kalar raɗaɗi da kuma jinin da ƙafarsa da aka harba take fitarwa ba, ya miƙe tsaye ya ƙari sa wurin ta.




Jijjiga ta yake yana roƙon ta akan ta faɗa masa abin da ya faru a lokacin, ihu da kuma maganar da yake ma ta da ƙarfi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment