Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin gate ɗin nan muka shiga kallon kallo tsakani na da shi tsawon mintuna, sannan ya katshe shirun ta hanyar buɗe baki da niyyar ya yi min magana, cikin tsananin sauri da tafarfasan zuciya na dakatar da shi idanuna a rufe nake faɗin



"Menene kazo kayimin?, ko kuwa kazo ka ƙara tayar min da ciwon da na samu ya fara warkewa ne.
Mayaudari maci Amana Aasief ka yaudareni bazan yafe maka da Abin da kayimin ba wallahi."


Maganganu kawai nake sakar masa babu adadi kuma ba tare dana tauna su ba.


Daga ƙarshe da ya tunzura iya tunzura nan shi ma ya fara aman zafafan kalamai a gare ni, waɗanda sai da suka saka na zubar da hawaye maganganu kawai yake sakarmin tamkar ba shi ne ya yimin laifi ba.


Cikin maganar sa ta ƙarshe da ya yi ne wacce ta daki zuciyata iya duka. Cewa wai ya yi.


"A haukar ki bansan abin da yake tsakanin ki da Leo bane ko mene, ko kuwa an faɗa miki banga pictures da kukayi tare da shi a mashaya bane?...."


Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un

Ta nan kuma ya ɓullo?......


Na tambaya zuciyata, yayin da jikina ya ɗauki rawa na ɓacin rai.


Buɗe idanuna da suka yi jajur fi ye da baya nayi, domin nima na gasa masa maganar da tafi wacca ya yi min.


Sai dai kash.....!!!!


Cikin rashin sa'a naga wai har ya bar wurin ya shiga Taxi.


Gaza jurewa nayi domin kuwa a lokacin yadda zuciyata take tafasa idan bawai na faɗa masa magana mai zafi fi ye da yadda ya faɗa min ba, ina ganin tarwatsewa zuciyata zatayi tsaban baƙin ciki da ƙiyayyar sa da nake ji lokacin yana taso min.



Haka ƙafafuwana ko takalma babu sannan a yadda jiki na yake sanye da Doguwar riga ta bacci kaina da hula.


A hakan nima cikin zafin rai na tare mai taxi nima na shiga, akan ya kaini can Estate ɗin ayi ta ta ƙare a yau ba gobe ba.......



*Abin Takaici*

Ashe ba Gidan ya tafi ba kai tsaye, domin ko da na ƙari sa ban ganshi ba, domin kuwa a kulle naga ƙofar tasa.



Kai koma yana nan, toh rufe ƙofar ya yi ta ciki.

Ba haka naso ba, sai dai bani da yadda zanyi, haka na juya nabar ƙofar Room nasa, sannan na shiga Elevator.


Saukowa ƙasa nayi ina shirin fitowa, dai dai lokacin wata kyakkyawar matashiyar budurwa ita kuma ta shigo cikin Elevator ɗin. Hannun rungume da jaririya.


Ƙoƙarin fita nayi ina sha re bisassun hawayen fuskata.


"Ah nace ba, please Madam a hawa na nawa Room na Aasief Mai Waje yake?."



Tambayar da Budurwar tayimin ke nan, wacce tasa na kasa koda motsi.


Cikin shiga tashin hankali sama da baya na juya ina kallon ta, sannan kuma ina ma ta tambayar da take cin zuciyata.


"Aasief Mai Waje kika ce, wata kalar alaƙa ce tsakanin ki da shi?."


Murmushin da ya bani mamaki tayi sannan ta bani amsa da faɗin.


"Ae Miji na ne shi, gama Jaririyar mu, Surprising nasa nakeso nayi, Shiyasa dana shigo ƙasar ban tuntuɓe sa ta waya ba."


Tayi maganar tana dariya kuma tana min nuni da jaririyar dake hannunta.



Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un


"Wai shin Wanene wannan Aasief ɗin, da mai yake taƙama ne haka?."

Na tambaya zuciya yayin da nayi saƙale ina kallon ta.


Cikin dauriya na kalleta cikin dan ne zuciyata na faɗa ma ta lambar Room nasa.

Inaji tana yimin godiya, sai dai ina..! Nayi nisa bata ita nake ba, tafiya kawai nake bansan inda zan je ba.



***
Allah Sarki ni Zaynerb Mai Kyau, na tsinci kaina cikin wani hali mara daɗi, Soyayya ta wahalar dani sama da tunanin mai tunani.


Na ƙara ramewa na fita hayyacina har takai ta kawo ko makarantar bana iya zuwa.

Halin da na shiga silar Soyayya bana fata wata Ƴa mace ta shiga kalarsa.😓


Tun daga wancan Ranar Rayuwata ni Zaynerb Mai Kyau ta tashi daga layin farin ciki, na koma bani da aiki sai tunane tunane, wanda hakan ya haifar min da babbar illa.


Tsawon Wata da watanni ina cikin wani mummunar hali sanadiyyar Soyayya, ta kai ta kawo ba bacci bana samun damar yi.


Daga ƙarshe dana haɗu da ƙawa wacce bata kirki ba, ta jefa ni cikin halin shaya shaye.


Takai ta kawo idan ban sha kwalbar barasa ba, bana iya taɓuka komai.


A shekarar farko da shiga University, shekarar farko na karatuna na tashi Carry Over.


Hankalina ya ƙara tashi sosai, naji na tsana ƙasar Amsterdam ɗin ma gaba ɗaya.


Daga ƙarshe ma tattara ya nawa ya nawa nayi na dawo nan Nijeriya na ci gaba da Rayuwata da Ahalina kuma na fara karatuna amma na canza course madadin ilimin halittar furanni, na koma karantar Shari'a.


Tun daga wancan Ranar ban sake haɗu wa Aasief Mai Waje ba, ko ma Erisha dasu Leo gaba ɗaya cikin su babu wanda na sake haɗu wa da shi.


Kuma hakan ya yimin daidai domin ko idan na haɗu dasu ban san menene abin da zai biya baya ba.🔥


Na dawo Nijeriya amma halayyar Shaye Shaye taƙi rabuwa dani, haka ma soyayyar Aasief Mai Waje, ban san dalili ba kuma.


*This Is My Badly Sadness Love Story*
*Zaynerb Mai Kyau*
*End Zaynerb & Aasief Babu ƙara Soyayya Har Abada*👎👎👎

_____




"Me yasa kika tsaya ne, ki ci gaba mana, Dan Allah Anty Lailah ci gaba da karantawa, so kawai nake naji ya ya Anty Zaynerb suka ƙare wa da shi."


Deejarh ce take wannan maganar cikin kuka hawaye shaɓe shaɓe.



Cike da tsantsan tausayin Zaynerb Lailah ta a je Jotter ɗin a gefe, ita ma cikin sha re kwalla take bawa Deejarh amsa da faɗin

"Menene zan ci gaba Deejarh?. Ai iyakar labarin ke nan, Allah Sarki Anty Zaynerb yanzu duk ta iya jure duk wannan, wayyo rayuwa."




"Kuka ba shi ne abin yi ba yanzu, hasa lima banga amfanin yin sa ba."



Cikin sauri Lailah ta katse Afeefah da tayi wannan maganar da faɗin


"Yanzu idan bamu yi kukan tausayawa Anty Zaynerb ba, menene kike so muyi, na'am ki faɗa min?."


Ko kafin Afeefah ta bawa Lailah amsa, Haleesat ta rigata da faɗin


"Abin yi yanzu shi ne musan yadda za'ayi soyayyar su ta dawo..."


"Ban gane abin da kike nufi ba, Humm wai so kike kice mana, kina da yadda za'ayi Anty Zaynerb su ci gaba da Soyayya da wannan mayaudarin?."


Lailah ce tayiwa Haleesat ɗin wannan tambayar cikin sauri. Ko kafin Haleesat ta nema amsar da zata bata, suka jiyo Muryar da basu yi tsammani ba, ta bayan yana faɗin


"Qwarai kuwa, tabbas abin da ya kamata ayi ke nan yanzu, musan yadda za'ayi soyayyar Zaynerb da shi Aasief yake ko wane?, ta ci gaba da gudana, saboda kwata kwata banma yadda wai shi ɗin zai iya Yaudarar ta ba, duba da yadda ya nace ma ta da farko, da'ace cin Amana ko yaudara ne a zuciyar sa tabbas ba za suyi daɗewan da suka yi a tare ba."



Maleek ne duk yake wannan maganar yayin da yake saukowa daga saman Staircase's na part nasa, sannan ya ƙari sa palon ya zauna daga gefan Afeefah saman 3sieter.


Ashe tun farkon fara karanta labarin soyayyar na Zaynerb da Lailah tayi yake tsaye daga saman Bene, tabbas yaji komai, kuma sannan har zuciyar sa bai yarda cewa Aasief yaci amanar Zaynerb ba.



"Tabbas nima ban yarda ba wallahi, duba da yadda ta rubuta labarin, cewa tayi fa wannan Leo yace yana son ta, sannan ita ma Erisha ce ko, ta ce tana son Aasief, idan kukayi duba da irin Abin da Zaynerb tayiwa Leo ɗin a tsakiyar makarantar, gaban dubban ɗalibai, da kuma irin rashin mutuncin da ta ce tayiwa ita Erisha ɗin, Tabbas a tunanina zai iya kasancewa Leo da Erisha sun haɗa kai ne..."



"You are right sister Haleesat ni ma haka nake tunani."


Cewar Deejarh tana yunƙurin kuma cewa wani abu suka haɗa idanu da Maleek, da sauri tayi ƙasa da kanta tana rufe bakinta, ita fa wallahi waɗannan rikitattun idanun nasa tsoro suke ba.😁



"Duka kunce wani abu amma yanzu Menene abin yi?."


Fadeelah ce tayi maganar yanzu, duk da cewa ba wani shiri ne tsakanin ta da Zaynerb ɗin na azo a gani ba, amma wallahi sosai ta tausayawa Zaynerb jin wannan labarin nata a soyayya.💓



"Abin yi ɗaya ne yanzu, shi ne mu fara sanin Wanene shi Aasief, musan ƙasar da yake, musan su waye familyn sa, da komai nasa, sannan koma menene sai ya biyo baya."



Maleek ne ya faɗa hakan, don a tunanin sa hakan ne yafi kamata ayi cikin wannan taƙin da suke ciki.



Sannu a hankali Momy Rafi'at da ita ma taji kuma ta saurari komai na abin da ya faru da Zaynerb a soyayya, ta fara ja da baya, Allah Allah take ta koma sama, don bata fata wani daga cikin su ya fahimci taji komai.



Cikin zuciyar ta kuwa faɗi take.


"Ohoo Very very amazing, wai dama haka labarin soyayyar Zaynerb ɗin ya kasance, lallai kuwa idan haka ne, sara ne yazo ma ta daidai da bakin gatarin ta..."


Da isar ta Bedroom bata tsaya jiran komai ba, ta lalubo lambar sa cikin sauri sauri ta danna masa kira, domin ya faɗa ma ta abin da ya kamata tayi, don kuwa kanta ya ɗaure, ba za ta iya komai ba, sai da shawaran mutane ukun nan da ta yarda dasu sama da komai a duniyar ta.


A palo kuwa ci gaba suka yi da tattaunawa akan yadda zasu ɓullo wa al'amarin, sai dai sun yanke iya su zasuyi, Daddy ko Momy Rafi'at koma ita kanta Zaynerb ɗin, babu wanda a cikin su zai san da wannan nufi nasu.


Sosai suka tattauna da Yayan nasu Maleek akan al'amarin soyayyar na Zaynerb. Da yadda zasuyi komai ya koma daidai.






*KANO*
*STATE*


*Jiddarh Komai Naga*💃
💋*Sarauniyar kyau ta Kanawa*💋


Daga zaunen da take saman Dressing Mirror tana fesa daddaɗan turaren ta mai tsadar gaske, ta jiyo Muryar Auntie (Mrs Komai Naka) tana kwala ma ta kira ita da Humaira.


Cikin sauri ta mayar da kwalbar turaren ma'ajiyar sa, sannan ta fito daga Bedroom nata da sauri, saukowa Down tayi, kana ta ƙari sa wurin Auntie tana faɗin.


"Gani Auntie wannan kira haka, Allah ya sa dai lafiya?..."


Kallon Jiddarh Hajiya Jamila (Mrs Komai Naka) wato Auntie takeyi daga sama har ƙasa, dan da nan wani takaici ya ziyarci zuciyar ta, ƙiyayyar da take yiwa mahaifiyar Jiddarh ɗin ya dawo sabo fil cikin zuciyar ta. Ita fa ta tsani wannan Yarinya Jiddarh sama da komai a Duniyar ta, ace Yarinya sai shegen kyau kamar wata huru'in.


Dan ne abin da take ji, tayi kamar yadda ta saba a kullum.


Sai da ta saita nutsuwar ta, sannan ta fara magana cikin sakin fuska da dariya, nuna musu Magazine na Daily Just dake hannunta ta yi tana faɗin.


"Yarana Jiddarh da Humaira ku duba wannan abin farin ciki da ya samemu haka, wai fa Abban ku ne (Alhaji Jafar Komai Naka) shi ne Mai Arziƙi na Bakwai a Nijeriya, shi ne ya fito cikin jerin mutanen da sukafi kowa kuɗi a ƙasar nan fa..."


Cike da mamaki game da farin ciki Jiddarh ta washe baki kamar gonar auduga faɗi take.


"Lah lah Auntie wai da gaske kike Abba ne ya fito cikin jerin mutanen da suka fi kowa kuɗi a ƙasar nan, lallai dole yau musha shagali a gidan nan."

Tayi maganar tana karɓar magazine ɗin daga hannun Auntie ɗin don sake tabbatarwa.


Ita kuwa Humaira tsaban farin ciki kasa magana tayi, sai mamaki, huh Allah mai iko, mamaki take yaushe Abbansu ya yi dukiya haka?.







*Zaynerb Mai Kyau*🥰
💓*Queen Of Love*💓




Da sauri taja wani wannan burki sakamakon buguwar da motar su tayi da motar dake gaban su, kuma ita ce da laifi, dan kuwa juyawar da tayi tana yima su Mah'eesha da Haseeya da suke back seat zazzaune magana ne, yasa ta bugi motar gaban su ba tare da ta sani ba.


Ƙasa tayi da kanta gaban ta mugun bugu, Addu'a take Allah ya sa bata kaɓe kowa ba.


Sannu a hankali ta ɗago da kanta tana kallon titin.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe murfin motar ta fito.


"Kuyi haƙuri Dan Allah ina mai baku haƙuri, akasi aka samu, na kusa buge motarrr...."

Kasa ƙari sa maganar tayi zuciyar ta na mugun bugu da sauri sauri sakamakon ganin mutumin da ya fito daga motar da tayiwa ɓanar tare da wasu Ƴan Mata biyu.

A yadda ya fito daga motar ransa a mugun ɓace, niyyar sa ya yi wa koma uban waye ya bugi motar sa, dukkan mutuwa.

Sai dai mai?....

Cak ya dakata daga ƙoƙarin ƙari sawa wurin da ya yi niyya.

Kamar ta tsaya cak tana bin sa da Kallon mamaki.

Toh shima Aasief a nasa ɓangaren haka abin yake.


Da farko kwata kwata bai gane wacece ba, har sai da ya kusa ƙari sawa dab da ita.

Sannan ne ya fahimci wacece, kuma ya gane ta.

Duk da cewa ta ƙara girma, tsayi, haske,da kyau, sai dai tana nan a yadda ya santa babu ƙiba.🙃



*After One Hour*


"Zaynerb! Zaynerb!! Wai bada ke nake magana ba, menene haka kike ƙoƙarin yi ne, Kawai tashi guda kice zaki koma Abuja da yamma nan, wai menene abin da ya faru, kuma Wanene wannan Mutumin ki faɗa min?."


Dakata wa Zaynerb tayi daga ƙoƙarin ta na cusa kayan ta cikin Akwati, sannan ta juyo tana kallon Mah'eesha da take ma ta tambayoyi, tana mai bata amsa da faɗin


"Eh tabbas Abuja zan koma, saboda bazan iya kwana da gari ɗaya da wancan mayaudarin ba wallahi."


"Me kike nufi da mayaudari, kina nufin kice shi ne wanda kuka taɓa Soyayya da shi a ƙasar Amsterdam?."


"Yes, of course, shi fa."


Zaynab ta bata amsa, tana ci gaba da cusa kayan cikin Akwatin ta.


"Okay, Toh Menene da hakan dan ya kasance kun taɓa samun matsala da shi?."

Haseeya ce tayi maganar a yanzu.



"Oh ni Zaynerba wai bakuji menene abin da yake faɗa min ba, cewa fa yake ni ce da laifi bawai shi ba.... Kai!! wai mutumin da na ga mace a Room nasa, shi yake faɗa min baya da laifi. kuma kuna goyon bayan sa kukeyi ke nan?, lallai ma."



Maganar take cikin huci da ɓacin rai, sannan ta ci gaba da cewa


"Kuna dai gani ɗazun a gaban ku komai ya faru, har wani Challenging yake bani kuji fa.
Wai sai dai dama can Burin Yaudarar sa nake, wai wata ƙila ni ce na shirya komai, kuji fa Mah'eesha... Na rantse yau babu mai hanani konawa Abuja da daren nan."


Ta ƙari sa maganar tana jan ƙaramin Akwatin ta sannan ta fito daga Bedroom ɗin, kai tsaye parking lot ta nufa, da yake Momy Suwaiba ba ta nan, shi ma Uncle Sagir bashi.


Biyo bayan ta Mah'eesha da Haseeya ɗin sukayi, Haseeya tana faɗin


"Tun da kin matsa zaki koma, kiyi haƙuri mana kibi jirgi, kinsan tafiyar mota ba zai yiwu ba, saboda hanyar bata da kyau, baya da hakan Yamma ya yi sosai, yanzu fa 5:55pm kiyi haƙuri Zaynerb ki dawo."


Haseeya ta ƙarishe maganar cikin lallashi da son Zaynerb ɗin ta fahimce ta.



Duk yadda Haseeya da Mah'eesha harma da Mah'fuz da ya dawo gidan, ya tarar da abin da yake faruwa, duk yadda suka so Zaynerb tayi haƙuri ta bari, zuwa washe gari ta koma Abuja, ƙi tayi.


Zaynerb tana da mugun taurin kai sosai, ba'a sakata, ba'a hanata, duk lallashin da aka ma ta akan ta haƙura ƙi tayi.


Daga ƙarshe haka suna ji suna gani Zaynerb ta shiga Mota Driver yaja suka nufa hanyar Abuja da wannan Yammacin.




*Aasief Pov*



"Neelarh! Neelarh. Kina ina ne, ma za ki shirya yanzu yanzu zamu koma Abuja bazamu ƙara kwana a garin nan ba."


Cike da tsantsan Mamaki take kallon ƙanin nata, jin abin da yake faɗa, gani take kamar baya hayyacinsa, idan ba haka ba, mutumin da yazo da niyyar ya yi ma ta one week, ko two days basu yi ba, shi ne zai ce zasu koma.



"Aasief wai menene abin da kake nufi ne, da kake maganar Neelarh ta fito ku tafi, kodai ka manta one week zakuyi min?. Sannan nayi maka tambaya akan Budurwar ɗazu baka bani amsa ba, menene abin da kake nufi?."


Tayi masa tambayar tana shimfiɗe Jaririyar ta mai watanni huɗu a duniya, saman sofa, zama tayi tana jiran amsar da zai bata.


"Sister Raadwa na roƙe ki, da kibar yimin tambaya akan abin da ya shafe ta, sannan yau kuma yanzu nake da buƙatar mu koma Abuja da Mata ta, dan bazan ƙara kwana a nan State ɗin ba...."



Katse sa tayi ta Hanyar faɗin.


"Aasief ke nan a tunanin ka ban fahimci komai ba ne, ae fahimtar komai ne yasa nace ba zaka koma Abuja da Matar ka Neelarh a yau ba, har saika faɗa min Wacece waccan Budurwar da kukayi cacan baki da ita ɗazu, gaskiya ka bani kunya, ace kamar ka, kake biyewa mace a tsakiyar titi...."



"Ya isa Raadwa ki dakata haka, tun da so kike kisan Wacece ita, toh ita ce ZAYNERB..."

Ya bata amsar yana kawar da kansa gefe domin zuciyar sa ba za ta iya jurewa ba sam.


Wani irin bugu zuciyar Neelarh da ƙari sowarta wurin ke nan taji abin da Aasief ya faɗa na ƙarshe tayi na hankali.


"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."

Kawai take iya furta wa daga farko har ƙarshe.
Shikenan ɗan farin ciki da take tunanin zata samu tare da shi ba zai yiwu ba, shikenan Zaynerb ta dawo Rayuwarsa, zata tarwatsa musu farin ciki.


Da kyar take iya tafiya haka ta ƙari sa palon, ta tsaya daga gefe tsumu da ita tana jiran abin da zai biyo baya.




*Zaynerb*

Tsaban buguwar da kanta ya yi, sakamakon burki da Driver yaja a tsakiyar Dajin, yasa ta kasa buɗe idanunta da suka ma ta nauyi yadda ya kamata.


Ƙarar harba harben bindigun da suka ji ta ko'ina na dajin ya ɗauka ne, yasa tayi saurin toshe kunnen ta tana rumtse idanu cikin tsananin tashin hankali.






Ƙari sowa wurin motar nasu wani ƙaton jibgegen Gardin Basamuden Mutumin ya yi.



Hannu ya kai ya fasa gilashin motar, sannan ya buɗe motar ya finciko Zaynerb da idanunta suke lumshewa a hankali tana gani dishi dishi. Da hannu ɗaya ya fito da ita daga cikin motar.






Watsar da ita ya yi daga gefan wurin da suka tara Ƴan Mata daban kamar wata kayan wanki haka ya watsar da Zaynerb.





Tsaban azaba yasa ko motsi kasayi Zaynerb tayi. Yayin da shi kuwa Driver gefan maza aka watsar da shi. Shi ma bayan anyo waje da shi daga motar.



Can gefen da suka tara motocin mutanen da suka yi Kidnapping cikin Dajin, wannan Gabjejan mutumin da ya ɗauki Zaynerb, yaje ya aje motar su Zaynerb.
Sannan ya dawo kusa da ƴan uwansa kidnapper's ɗin maza da mata wurin su Ashirin cike da dajin hannayen ko wannen su ɗauke da gaggan makamai masu haɗarin gaske.



*Zaynerb*


Tamkar a mafarki haka take Ganin al'amarin da yake kan faruwa dasu a halin yanzu, wai fa da gaske kidnapper's ne suka yi Kidnapping na ta.

"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."


Ta furta laɓɓanta na rawa, tana bin ƙaton dajin da kallo, da kuma waɗannan gaggan Kidnapper's. Akan tulin mutanen da suka yi Kidnapping idanunta suka sauka.


Mutane ne kala kala maza da mata yara da manya. Masu kuɗi da talakawa, ɗalibai da ma'aikata.




Wurin da suka saka ƴan mata daban wurin maza daban haka ma wurin ƙana nan yara daban.





"Na shiga ukuna ni Zaynerb, wannan wacce kalar ƙaddara ce ta kawoni hannun waɗannan mutanen?....."






Zaynerb tayima kanta tambayar hannu a ka cikin tsananin tashin hankali, gani take kamar mafarki take yi bawai da gaske Kidnapping nata akayi ba.




Baya Baya motar da ta shigo dajin tayi kamar zata koma inda ta fito.


Cikin sauri da an karewa gaba ɗaya kidnapper's ɗin suka sassaita manyan bindigun su ga motar da shirin su harbe koma uban waye a ciki, muddun ya nema yi musu taurin kai.


Ƙari sawa wurin motar, wannan Gabjejan mutumin baƙin ƙirin da shi ya yi, sannan ya saka baƙin hannun sa ya buɗe motar.


Da alama halinsa ne finciko mutum daga cikin mota.

Dan kuwa duka ƙarfin sa ya saka wajen finciko mutumin dake cikin motar.

Sai dai da alama wanda yake motar shima mugun ɗan taurin kai ne.


Duba da yadda Baƙin mutumin ya dage wajen ƙoƙarin finciko shi, yayin da shi kuma na cikin motar yaƙi basa damar hakan.



"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un. Aasief ne wallahi shi ne, na shiga ukuna ni Zaynerb inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."



Zaynerb tayi wannan maganar cikin tsananin tashin hankali na ganin mutumin da wannan ƙaton Arnen ya sama damar fitowa waje da shi ba kowa bane fa ce Aasief.






"An kara! An kara!! kwalawa sun sama labari, kai GADDAFI ya kamata muyi gaggawar barin wurin nan kafin su ƙari so, su tarar damu fa."




Ɗaya daga cikin kidnapper's ɗin ne ya yi wannan maganar ga Ƴan uwan nasa kidnapper's a lokacin da ya mayar da wayar da aka sanar da shi abin da ke faruwa ta cikin ta cikin aljihun rigar jikin sa da take ta tare alburushi.




"Wannan munafukin ne ya faɗa musu shakka babu, domin kuwa ga waya nan a aljihun sa."


Baƙin mutumin da aka kira da GADDAFI ya faɗa hakan a daidai lokacin da yake sakarwa Aasief ɗin Alburushi a tsakiyar ƙafafuwan sa.



Wani irin ihun neman taimako Neelarh da take tare da Aasief ɗin ta saki tana mai kiran sunan sa cikin tsananin tashin hankali.






Zaynerb kuwa kusan susu cewa za'a iya cewa tayi na ganin yadda jini yake tsata ta daga ƙafafuwan Aasief da ya zube ƙasa cikin tsananin Azaba.....






Mgnr Payment duk wacce tasan bata biya 300 na littafinan ba, kuma ta karanta gaskiya ina ga ban yafe ba, fisabilillah 300 ne fa kacal. 👌👊



*Idan kina shirye da biyan ɗari uku (300) kisha karatu cikin kwanciyar hankali, to ki biya ta wannan details ɗin.* 👇👇



*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*


_____

*🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥*
_-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_



ɯ&ʂ_-_📖🖋️📲
💓 The Nainarh Kd 💓



_-_ҽρ.11_15



*💝ƚԋҽ ҽxƚɾασԃιɳαɾყ ʅσʋҽ αɳԃ ɾσɱαɳƈҽ ιɳ Ⴆιƚɯҽҽɳ ȥαყɳҽɾႦ $ ααʂιҽϝ💝*





*Lailah Mai Kyau*


A hankali take bubbuga yatsarta akan cup of coffee dake tsakiya saman teburin da suke zaune.

Kyawawan idanunta suna saman kyakkyawar fuskar sa mai cike da haiba, tana ƙare masa kallo zuciyar ta na bugawa kaɗan kaɗan.



Tun bayan kammala yadda ya kamata su ɓullo wa al'amarin Zaynerb da Aasief da suka yi, ita da Afeefah suka shirya kai tsaye suka wuce Hospital domin ganin matar da Afeefah ta taimakawa ta haihu a Restaurant.
Koda suka je anan ne suka haɗu da Sabbir, ashe wai matar da Afeefah ta taimakawa ɗin, matar Yayar shi Sabbir ɗin ne.

A lokacin sosai Sabbir da Lailah suka sha fira abin su, dama kuma suna ɗan yin waya jefi jefi da shi.


Washe gari yau ke nan, sune rakiyar Afeefah izuwa wurin tantancewa na Miss Nigeria da za'ayi anan Abuja, kiran Sabbir ya shigo wayar ta, koda ta ɗauka cike da zumuɗi sai yace ma ta, su haɗu a Restaurant ya bata Address sannan ya ƙara da faɗin haɗuwar tasu tana da muhimmanci domin akwai wata magana da yakeso ya yi ma ta.

Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin gaggawa da zumuɗi ta shirya, sannan ta taho Address na Restaurant da ya yi ma ta kwatance.


Tsawon mintuna da zaman su a wurin, amma bai ce da ita komai ba. Ita ma haka ba tace da shi ƙala ba.



Ƙarar da wayar ta tayi ne, yasa suka dawo hayyacinsu daga Duniyar tunani da kowannen su ya lula.

Murmushi tayi bayan tayi picking call ɗin, ganin Afeefah ce ta kira ta.

"Hello Miss Nigeria To be, toh ya ake ciki ne, ya ya tantancewar ta kasance ne, Allah yasa dai munyi Nasara?."


Lailah tayi maganar cikin son jin yadda tantancewar ta kasance.



*The Queen Afeefah*💓

Murmushi tayi mai kyau, tana zama cikin haɗaɗɗiyar motar ta sannan ta bawa Lailah amsa da faɗin



"Tantancewa ta tafi yadda ya kamata, domin na shiga cikin jerin Ƴan Mata goma sha Takwas da zasu shiga Gasar Miss Nigeria da za'a Gudanar a Lagos nan da ƴan kwanaki."





"Kai Masha Allah, gaskiya naji daɗi sosai sosai, ki ce daga Miss Nigeria sai Miss World idan Mai duka ya nufa."





Lailah tayi maganar cike da jindaɗi tana Dariya.


Dariyar ita ma Afeefah ta yi a ɓangaren ta, sha re maganar Lailah ta yi tana faɗin.


"Yanzu haka ma wata ƴar ƙwarya kwaryar Party da wannan Jiddarh take ko, wannan dai Queen Of Beauty ta Kano tohm ita ce ta shirya mana Party yanzu haka ma wurin na nufa kai tsaye."


"Iyye kaga manya harda wata ƴar ƙwarya kwaryar Party za'ayi, tohm Allah ya tsare hanya yasa ku kammala lafiya ki dawo gida Muma muyi namu acan, dan nasan zuwa yanzu ya isa ace Jirgin su Aunty Zaynerb ya sauka anan Abuja tunda da wuri ta ce miki zata taho jiya da kukayi waya ko?."




"Eh haka ne, ta ce da wuri zata taho."


Afeefah ta bawa Lailah amsa cikin Murmushi.


"Okay Tohm Allah ya sauke su lafiya, ke kuma Miss Nigeria To

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment