SHALELEN ALHAZAWA Complete Hausa Novel Document by SHALELEN ALHAZAWA


SHALELEN ALHAZAWA

Cover Design Copyright and attribute to Gnovels

Uploaded by @Admin

Total Words: 46447



SHALELEN ALHAZAWA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 16, Jun 2025

Author: Unknown

Ebook Compiler : GNOVELS

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08082589590

Book License : Free

Category: Romance Books

File Size: 235.89 kb

File Type: txt

Views: 67+

Download: 59+

Last download: 1 day ago

Description/Story:

Turo baki Najmeer ta yi har da matso Æ™wallan Æ™arya, "Wai ke Mamu meye matsalarki da karuwancin da nake yi, duk wannan fa dan ke nake yin sa, idan ban fita na samo mana ba Uban wa zai ciyar da mu?" 

 

"Ubanki zai ciyar da mu, marar kunyar yarinya wato fitsarar taki za ki fara ko? tom bari idan Kawunki ya zo sai na faÉ—a masa cewar Karuwancin da ki ke zuwa saboda ni ki ke yi".

 

Kawu Jamilu Ƙani ne ga Mahaifin Najmeer Uwa ɗaya Uba ɗaya su uku ne dama, shine Autansu, Namjeer na masifar tsoronsa, shi kaɗai ne wanda take shayi a halin yanzu, a duk lokacin da ta haɗu da shi to fa yanzu zata rasa natsuwarta, dan tsananin tsoronsa.

 

 

A É—an tsorace Namjeer ta ce "Kinga Mamu duk abin be kai haka ba, ke wace irin tsohuwa ce iyeeee? ni zan shiga daga ciki bacci nake ji" 

 

Ba tare da ta saurari abin da Mamu zata faɗa ba ta shige ɗakinta tana turo ƙofa.

 

Ko mintuna biyu masu kyau bata yi da shiga ɗaki ba suka ji sallamar Kawu hannunsa ɗauke da leda, bayan sun gaisa da Mamu ne ya ce "Ina yarinyar nan ne? Allah ya sa bata fita yawon iskancin nata ba" Duk da cewar Mamu ta ji zafin abin da ya ce amma sai ta yi murmushin yaƙe, "Najmeer na daga ciki ai yau babu inda ta tafi" Duk abin da suke faɗi tana jinsu sai ma ƙara lafewar da ta yi dan kar ya ce a kira ta.

Ledar Goron ya miÆ™awa Mamu yana faÉ—in "Nikam ya batun Jabir É—an gidan Malan Bukar da na ce zan haÉ—a shi aure da Najmeer ko ita ce ta hana shi zuwa zance?" 

"Imban da abinka Jamilu ni menene nawa a ciki? tana ɗaka ai ka sameta sai ku yi magana" Ɗakin Kawu ya nufa yana mai ɓata fuska shi ala dole Mamu ta gasa masa magana.



Read / Download SHALELEN ALHAZAWA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album