Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM* *Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad s a w, yau ma kamar kullum na ƙara kawo muku shahararren book ɗina me taken Shalelen Alhazawa, ina fatar za ku bibiyeni domin jin yanda zata kasance, ban yi wannan littafin dan na ci zarafin wani/wata ba duk wanda ya yi daidai da rayuwarsa to akasi ne, ban yarda a juya min book ta kowacce suffa ba, idan kunne ya ji jiki ya tsira, kar wanda ya yi gangancin ɗora min book a Website ko You tube ba tare da izini na ba, idan aka yi hakan za ka iya ganin sammaci daga kotu dan haka a kiyaye, ni ce ta ku har kullum Asmeetar Hydar marubuciyar littafin Gidan Mulki Mayaudari. Littafin Shalelen Alhazawa akwai faɗakarwa ilmantarwa gami da nishaɗantarwa uwa uba al'ajabi, ku dai ku bibiyeni domin jin yanda zata kasance* *08082589590* P. 1 Tun da ta fara ratsa unguwarsu take rufe hanci saboda warin da ke tashi, kayan jikinta kawai idan ka gani zaka ce ɗiyar wani hamshaƙin me kuɗi ce, kaya ne na alfarma zai kai kimanin dubu ɗari biyu, handbang da takalman ƙafarta kuwa sun kai dubu ɗari, wayar hannunta ƙirar iphone 13promax ce, tafiya take cikin iya taku da karairaya har ta fito daga unguwar tasu, sai da ta yi tafiya me nisa kafin ta shiga wata unguwar, daga nesa wata bugaggar mota ce da alama ita ake jira. A gadarance ta ƙaraso tana sakin murmushi, ba tare da wata fargaba ba ta shige motar tana mai rufe ƙofa. Alhajin da ke ciki kuwa zai kai kimanin shekaru arba'in, haƙoran makka biyu ne a bakinsa, washe baki ya yi kafin ya ce "Barka da zuwa Zinariyar mata" Ɗan gyara zaman mayafin jikinta ta yi wanda sai cikakkun ƴaƴan masu kuɗi zasu iya saka shi ta ce "Thanks love am very tied tun safe muke abu ɗaya, waɗannan talakawan kullum cikin yi musu kyauta ake, yau Dad ɗina be samu damar zuwa ba shine fa ya ce na wakilce shi" Ta faɗa tana fari da ido. "Eyyeh gaskiya akwai gajiya amma be kamata Dad ya turo kyakykyawar mace kamar ki irin wannan unguwar ba, but ina Driver ne?" Da sauri ta katse shi da faɗin "No ai bana buƙatar Driver because ba kowa nake son ya san ko ni wacece ba" "Okay zamu iya tafiya ko?" "Yes we can go dan ina son mu yi sauri mu dawo kafin Dad ya dawo gida, ya tafi Meeting a ƙasar Dubai yau zai su shigo". Gyaɗa kai Alhajin ya yi alamar gamsuwa tare da kunna mota yana mai barin unguwar. Wani haɗaɗɗen Hotel suka nufa wanda sai manyan masu kuɗi ne zasu iya shigar sa, ɗagewa Gate ɗin ya yi sama, Alhajin kuwa ya danna hancin motarsa a ciki, Najmeer kam tun lokacin da aka shigo ta ƙara haɗe fuska tamkar ɗiyar shugaban ƙasa, a mota ta tsaya shi kuwa ya shige daga ciki domin biyan kuɗin room ɗin da zasu sheƙe ayarsu, mintuna uku ya ɗauka kafin ya fito yana sakin murmushi. A tare suka nufi ɗakin tana rungume a jikinsa, wani ƙayataccen room ne wanda ya gaji da haɗuwa, mayafin da ke jikinta ta ɗora kan makeken bed ɗin da ke baje a ɗakin tana mai fara yaye kayan da ke jikinta, Alhajin kuwa ya zuba mata ido kamar zai haɗiye ta ganin yanda shape ɗinta ya fito sosai, daga saman ƙugunta zuwa ƙasa ya buɗe, can bayan mazaunanta ya ɗago sosai gwanin sha'awa, cikinta ya shafe har ya hana cibiyarta fitowa, a hankali ta juya tana mai girgiza jigidar da ke ɗaure a ƙugunta, wani mugun numfashi Alhajin ya ja wanda ya yi sanadiyar faɗawarsa kan bed be san lokaci ba, tun da Allah ya halicce sa be taɓa ganin mace me kyan diri irin na Najmeer ba, rigar jikinta ta fara cirewa tana faɗin "Ka haɗa mun ruwan wanka ina son na shiga" Kamar wani Dolo haka Alhajin ya shige toilet ɗin yana mai juyowa dan ko kaɗan baya son ɗauke idanunsa daga barin kallonta. Sai da ta gama sauke duk kayan da ke jikinta kafin ta zauna kan bed tana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gashin kanta da ke yawo har ƙarshen bayanta ne ta ɗaure dan yana takura mata, baƙi ne sosai me laushi ga wani ƙamshin da ke tashi tamkar an yi ɓarin turaren gashi a kai, na shanunta kuwa sun ɗago sama ƙyam gwanin sha'awa, su ba girma ba kuma ba ƙaranci ba masu masifar kyau da jan hankali, Najmeer fara ce sol wanda haskenta me ɗaukar ido ne, macece me kyau wadda duk unguwarsu ake kwatance da ita, a iya binciken da aka yi babu wata macen da ta kai ta kyau a duk faɗin unguwarsu, kyawunta na ƙara mata farin jini gurin maza musamman manyan Alhazawa, bata harka da yara ko talakawa, idan ka ganta tare da namiji tabbata hamshaƙin me kuɗi ne, ƙwarjinta ma baya bari wasu mazan tunkararta, idanuwanta manya ne masu kyau da ɗaukar hankali, ƙwayar idon nata kuwa blue ne siɗik shiyasa wasu ke cewa ba mutum ba ce, wasu ma suna faɗin Aljana ce shiyasa kyawunta ya yi yawa, bakinta ɗan ƙarami ne me ɗauke da pink lips haƙoranta kuwa sirara masu haske, a tsakiya sun raba kaɗan sai haƙoran suka ƙara kyau tamkar ita ta jerewa kanta, hancinta dogo ne daga sama har ƙasan shi, gashin girarta baƙi siɗik ga yawa har ya kwanta ƙasan idanuwanta, Namjeer macece wadda ta haɗa duk wani abun da cikakken namiji me ji da kansa ke buƙata, kayan da take bugawa sun wuce ɗiyar sarkin garin Jos ta saka su, Najmeer yarinya ce ƴar shekaru goma sha bakwai wadda kana ganinta ka san yarinya ce amma yanayin jikinta zaka iya cewa ta fi hakan, domin duk wasu halittu na jikinta sun fito tamkar ita ta tsarawa kanta, cikakkiyar shuwa'arab ce me ji da tsagwaron kyau da kwarjini gaban manyan mutane, iyayenta sun rasu tun tana da shekaru uku a duniya, tana zaune tare da Kakarta ta gefen Mahaifiyarta wadda suke kira da Mamu, iyayen Najmeer kuwa ita ce kaɗai ƴarsu a duniya daga ita basu sake samun haihuwa ba, bayan shekara uku da samun Najmeer Mahaifiyarta me suna Maryam ta rasu sakamakon ciyon cikin da ya kama ta, ko wata ɗaya bata yi da rasuwa ba gobara ta kama gidansu Mahaifinta Malan Bala da sauran jama'ar gidansu Allah ya yi musu rasuwa, itama Najmeer ɗin da ƙyar aka samu damar ceton rayuwarta, ta yi saukar Alqur'an tana da shekaru takwas a duniya, ta yi haddarta lokacin da ta cika shekaru goma sha biyar, batun makarantar boko kuwa babu shi dan Primary kawai ta yi ta daina zuwa, babu yanda Mamu bata yi ba dan ta koma makaranta amma abin ya gagara, rana ɗaya ta daina zuwa islamiyar ma gaba ɗaya, a kullum za ta fita tun safe sai dare take dawowa, tun Mamu Kakarta na kuka da damuwa har ta daina, Mamu ce kawai ke haƙuri da ita dan babu yanda ta iya, duk ƴan Uwan Mahaifinta sun ce kar ta sake zuwa gidansu tun da ta zama karuwa, kasancewar Najmeer akwai zuciya ne ya sa ta janye ƙafarta daga gidan, amma duk da haka suna zuwa dan cin arziƙinta, tun tasowar Najmeer bata da ƙawa ko ɗaya a cewarta bata son munafurci, duk mutanen da ke unguwar sun san wacece ita, inhar za'a yi kwatance idan ba ka ce Shalelen Alhazawa ba babu wanda zai gane, duk ƴan unguwar da sunan da suke kiranta kenan, rashin jin maganarta kuwa sai ƙaruwa yake dan wasu lokutun ma a waje take kwana. Miƙewa ta yi daga inda take zaune tare buɗe Handbang ta ciro wata farar leda tana sakin murmushi, Frigd ɗin da ke gefe ta buɗe tana mai ɗauko Drink ta zuba a Cup, da sauri ta maida kallonta kan Alhajin da ya fito daga toilet fuskarsa na kallonta, cikin basira da ƙwarewa ta zuba maganin kamar guda uku tana sakar masa murmushin da ya tashi ɗimauta shi, gaba ɗaya hankalinsa na kanta be san wainar da take toyawa ba, a hankali ta ɗaga Cup ɗin tana mai nufar inda yake, wani irin juyi ta yi wanda ya ƙara firgita shi, "Ga wannan ka ɗan taɓa kafin na fito wanka My sweet Guy". Najmeer ta faɗa cikin zazzaƙar muryarta, karɓar Cup ɗin ya yi yana mai kaiwa baki, sai da ya sha sosai kafin ya ce "Thank you Baby Girl am waiting for you, and this your kayan marmari" Ya ƙarasa maganar yana shafa bayanta, sai da ya ja mugun numfashi jin wani mahaukacin laushi ya shige sa. Ba tare da Najmeer ta ce komi ba ta shige toilet bakinta ɗauke da addu'ar shiga. Sai da ta kai kusan mintuna talatin a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul, kwance ta sami Alhajin yana sharar bacci harda sakin nunshari kamar gandamemen ƙato, a fili ta ce "Gud job" Mintuna biyar ya ɗauketa gurin shiryawa, sai da ta duba gaba ɗaya ɗakin da kyau dan ta san wasu Hotels ana saka Camera a ɗakunan mutane, sosai ta duba tare da tabbatar da ba bu Camera ko ɗaya, a gaggauce ta fara bincika aljihun kayansa, ai kuwa sai ga kuɗaɗe masu yawa, tattara kuɗin ta yi ta zube cikin Handbag ɗinta, wayarsa da ke gefe ta ɗauka tana mai danna wasu pin, cikin ƙanƙanin lokaci ta cire security sannan ta yiwa kanta tranfer na 10million, kayansa kuwa a leda ta zuba takalmansa ma haka, babu abin da ta bar masa face wayarsa, shima dan kar a yi bincike akai ne, hatta gajeran wandonsa sai da ta ɗauka, cikin hanzari ta goge alert tana mai barin Hotel ɗin. Sai da ta yi nisa da tafiya kafin ta tari adaidaita, kwatance ta masa har unguwarsu, a bakin layi ta ce ya ajeta, sannan ta biya sa kuɗi tana mai nufar hanyar gidansu, har me adaidaita zai juya ta yi saurin dakatar da shi tana faɗin "Bawan Allah tsaya, ga wannan kayan idan zasu yi maka" Kayan Alhajin ta miƙa masa, cikin murna me adaidaita ya karɓa yana ta zuba mata godiya, ita kuwa ta wuce ba tare da ta amsa masa ba. Bakinta ɗauke da sallama ta shigo gidan, a tsakar gida ta sami Mamu na jan carbi, kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kai, Najmeer na murmushi ta ƙaraso tana mai zama kusa da ita "Allah ya sa dai ba laifi na yi ba, Mamu wannan hararar ta mecece?" Ƙara haɗe fuska Mamu ta yi "Najmeer.....Najmeer.....Najmeer......., sau nawa na kiraki?" "Sau uku" Namjeer ta amsa tana kallonta. "Na gaji da halinki, na gaji da maganganun mutane, ke ce kullum yawo cikin gari, meyesa baza ki tausaya min ba, ko zagin da mutane ke min idan na fita bakya gani ki daina wannan yawon iskancin" Turo baki Najmeer ta yi har da matso ƙwallan ƙarya, "Wai ke Mamu meye matsalarki da karuwancin da nake yi, duk wannan fa dan ke nake yin sa, idan ban fita na samo mana ba Uban wa zai ciyar da mu?" "Ubanki zai ciyar da mu, marar kunyar yarinya wato fitsarar taki za ki fara ko? tom bari idan Kawunki ya zo sai na faɗa masa cewar Karuwancin da ki ke zuwa saboda ni ki ke yi". Kawu Jamilu Ƙani ne ga Mahaifin Najmeer Uwa ɗaya Uba ɗaya su uku ne dama, shine Autansu, Namjeer na masifar tsoronsa, shi kaɗai ne wanda take shayi a halin yanzu, a duk lokacin da ta haɗu da shi to fa yanzu zata rasa natsuwarta, dan tsananin tsoronsa. A ɗan tsorace Namjeer ta ce "Kinga Mamu duk abin be kai haka ba, ke wace irin tsohuwa ce iyeeee? ni zan shiga daga ciki bacci nake ji" Ba tare da ta saurari abin da Mamu zata faɗa ba ta shige ɗakinta tana turo ƙofa. Ko mintuna biyu masu kyau bata yi da shiga ɗaki ba suka ji sallamar Kawu hannunsa ɗauke da leda, bayan sun gaisa da Mamu ne ya ce "Ina yarinyar nan ne? Allah ya sa bata fita yawon iskancin nata ba" Duk da cewar Mamu ta ji zafin abin da ya ce amma sai ta yi murmushin yaƙe, "Najmeer na daga ciki ai yau babu inda ta tafi" Duk abin da suke faɗi tana jinsu sai ma ƙara lafewar da ta yi dan kar ya ce a kira ta. Ledar Goron ya miƙawa Mamu yana faɗin "Nikam ya batun Jabir ɗan gidan Malan Bukar da na ce zan haɗa shi aure da Najmeer ko ita ce ta hana shi zuwa zance?" "Imban da abinka Jamilu ni menene nawa a ciki? tana ɗaka ai ka sameta sai ku yi magana" Ɗakin Kawu ya nufa yana mai ɓata fuska shi ala dole Mamu ta gasa masa magana. Ya jima a ɗakin wanda har Mamu ta kasa haƙuri ta kira sa, duk da hakan sai da ya ƙara sama da mintuna biyar kafin ya fito fuskarsa a ɗaure, ko sallamar arziƙi be yiwa Mamu ba ya fice daga gidan, sheshsheƙar kukan Najmeer ne ya sa Mamu nufar ɗakin a kiɗime dan babu abin da ta tsana kamar ganin kukan Jikanyar tata. Najmeer na ganin Mamu ta shigo, ta yi saurin tasowa daga kwancen da take ta faɗa jikinta tare da sakin kuka me cin rai, cikin kukan take faɗin "Mamu dan Allah kar ki bari Kawu ya aura min Jabir, wallahi bana son shi, yanzu kamar ni zan auri namiji irin Jabir wanda ko Boko be yi ba, kuma ba wayayye ba haba dan Allah" Jin yanda ta ƙarasa maganar ne ya ba Mamu dariya, tureta daga jikinta ta yi "Yooo yau naga ja'irar yarinya, ke Bokon ki ka yi ne? ai da wannan taɓarar da ki ke gwara a aura miki shi ku je can ku ƙarata" Ƙara rushewa da kuka Najmeer ta yi "Ai kuwa ba zan aure shi ba, ke Mamu kinga na yi miki kalar macen da zata auri talaka, kalleni da kyau cikakkar mace amma a rasa wanda za'a haɗani da shi sai Jabir" "Ke ni rabani da zancen banza, in kinso ki auri ɗan Sarki ba me kuɗi ba, mtsssss" Mamu ta faɗa tana barin ɗakin, ita ko Najmeer ta shiga mitar maganar har aka kira sallar magrib, alwala ta haɗo tare da yin sallah, ta jima a zaune tana karatun Alqur'an har aka kira isha, dama sun yi da wani Alhaji kan cewa zasu haɗu bayan sallar isha, sai da ta gama sallah kafin ta shirya cikin wando iyakarsa cinya, sai Top me gajeren hannu milk Colour kasancewar wandon Blue ne, wasu uban takalma sawu ciki masu masifar kyau ta saka Milk kalar rigar jikinta, sai gashin kanta da ta ɗaure daga baya ya zuba har ƙugunta yana rito, hula ta ɗora a kai tana mai juyi cike da salo, sai da ta tabbatar cewa komi ya yi need kafin ta yi wankan turarukka masu mahaukacin ƙamshi, a tsakar gidan ta sami Mamu na ƙoƙarin shiga ɗakinta, da sauri ta koma da baya har Mamu ta shige ɗaki, Najmeer na ganin haka ta fice daga gidan, a tsarinta bata bayar da Numbern wayarta balle a kira ta, idan ka haɗu da ita a hanya zata faɗa maka inda zaku haɗu kuma da lokacin da zaku haɗu, asalima bata yawan anfani da wayarta. Kamar yanda suka aje da Alhajin kuwa haka aka yi, wata hamshaƙiyar unguwar da ke can bayan layi Namjeer ta ce masa idan ya zo ya tsaya, dan haka ta nufi can cikin tafiyarta me masifar jan hankali, ba sabon abu ba ne ganin Najmeer cikin irin wannan shigar, dan duk ƴan unguwarsu sun san ita ce macen da ke fita tamkar ba musulma ba, tun ana gulmace-gulmace har ta kai idan suka ganta sai dai ka ji ana faɗin, Shalelen Alhazawa-Shalelen Alhazawa, ita kuwa Najmeer idan tana cikin nishaɗi zaka ga ta fitar da kuɗaɗe tana watsa musu tamkar wadda bata san zafinsu ba. Tun da ta fara ratsa titin layinsu mutane ke kallonta har ta fice gaba ɗaya, wani farin hankacif ɗan ƙarami da ke hannunta ne ta saka bayan aljihun wandonta. Motoci uku ne bugaggu masu masifar kyau, daga waje masu tsaronsa ne kusan su biyar majiya ƙarfi, wani irin yawu Najmeer ta haɗa jin yanda gabanta ke faɗuwa, cikin ƙarfin hali ta ƙaraso gurin, tun kafin su tare ta Alhajin ya fito daga motar yana mai sakin murmushi tare da ware hannayensa alamun ta zo gare shi, cike da iya barikanci Najmeer ta nufesa tana mai shigewa jikinsa, masu tsaronsa kuwa baya suka basu cikin girmamawa, "Baby kin haɗu sosai, wallahi ko a matan larabawa sai an bincika" "My Alhaj banda matan larabawa, a barni a Jos ma kawai is okay" Najmeer ta faɗa tana shafo tsakiyar bayansa, wani irin shiɗewa Alhajin ya kuma yi, "Baby faɗa min account numberki" Dama abin da Najmeer ke son ji kenan, a makirce ta zayyano masa, sai da ya gama tura mata kafin ya ce "Mu shiga daga ciki ko? na tura miki 50million ba yawa, amma tun da muna tare za ki ci arziƙi Baby" Ɗan taɓe baki Najmeer ta yi "Okay but ina zamu nufa yanzu?" "Gidana zamu tafi, akwai wani gida a can Area 1, wanda nake zuwa dan hutawa" Ba tare da jin tsoron komi ba Najmeer ta shige motar, masu tsaron kuwa suka rufe ƙofa suna mai shiga sauran motocin, cikin ƙanƙanin lokaci suka bar unguwar. A gafen Mamu kuwa ganin har tara na neman bugawa amma Najmeer bata fito ta ci abinci ba ne yasa ta nufi ɗakinta amma wayam ba kowa, gaba ɗaya gidan ta duba ba bu Najmeer ba bu alamunta, ƙamshin turaren da ta ji ne ya tabbatar mata cewar Najmeer ta yi abin da ta saba. Jikin Mamu a sanyeye ta koma ɗaki, duk idauwanta sun ciko da ƙwalla a fili ta ce "Haƙiƙa Najmeer kin ɗauko hanyar da baza ta ɓulle miki ba, tun da ki ka san ciyon kanki har zuwa yanzu kullum sai kin sakani kuka, yanzu me zan faɗawa iyayenki idan muka tashi a gaban Ubangiji? na tabbata cewa a halin yanzu mutane suna ɗaukar cewa na sakar miki jiki kin lalace saboda ke marainiya ce, Allah ya kare ki a duk inda ki ke kuma Allah ya shiryeki". Mamu ta ƙarasa maganar tana mai share ƙwallan da ke zubo mata kamar an buɗe pampo. Su Namjeer kam a wani tangamemen gida suka shiga wanda ya gaji da haɗuwa, kasancewar Namjeer ta saba shiga manya-manyan gidajen Alhazawa ne ya sa take ganin wannan gidan ma ba komi ba ne, ɗakinsa suka nufa Najmeer na gefensa ya rungumota ta baya, har rawa jikinsa ke yi tsabagen jaraba, dan ba ƙaramin tafiya da iamaninsa ta yi ba. Tamkar aljannar duniya haka ɗakin ya tsaru, komi na ɗakin da Gold aka yi shi, hatta bed ɗin na Gold ne barin ma ƙofofin gidan, hasken ɗakin da ya gauraye ne yasa Alhajin ƙara zubawa Najmeer ido, a ransa ya ce tabbas Allah ya zuba halitta a anan, wannan ƙwayar idon nata tamkar zinari, ajiyar zuciyar da Najmeer ta sauke ne ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga, cikin ƙasaita ta nufi Frigd ɗin da ke ɗakin ta ɗauko drinks da Cup, kamar wani soko haka Alhajin ya miƙe tare da karɓar kayan da ke hannunta "Baby ai wannan aikin ba irin na mata kamar ki ba ne, let me help you with it, amma ba bu abin da ki ke son ci kuwa?" Zama kan bed Najmeer ta yi, ta ɗauki mintuna biyu kafin ta ce "Akwai Shawarma?" "Yes akwai Shawarma" Alhajin ya faɗa yana latsa wata ƙararrawa, ɗaya daga cikin masu aikin ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, kallon Namjeer ta yi tana mai mamakin ganin ƙaramar yarinya kamar wannan tare da Dattijo irin me gidanta, tsawar da Najmeer ta daka mata ne yasa matashiyar matar da zata kai shekaru talatin razana cikin tsananin tsoro, a fusace Najmeer ta miƙe tana mai ɗauketa da mahaukacin mari, "Ke dabba jaka me ki ke kallo? kinga na yi kama da wadda za ki zubawa ido kamar wata tsohuwar mayya, tom bari na ba ki amsar abin da ki ke son sani, kallon da ki ke mun ya nuna cewar kina son sanin meya kawoni gidannan ko?" A hankali ta koma tana mai zama kan cinyar Alhajin cikin iya barikanci ta shafo gefen fuskarsa tana faɗin "Ni Karuwa ce, cikakkiyar ƴar tasha me zaman kanta, idan kuma da abin da ki ke son sani za ki iya faɗa mun" Jikin matashiyar na ƙyarma ta ce "Allah ya ba ki haƙuri insha Allah hakan baza ta ƙara faruwa ba, Sir me ka ke da buƙata?" Ta ƙarasa maganar tana kallon me gidanta. "Shawarma za ki kawo mata na ba ki minti ɗaya" Cikin biyayya ƴar aikin ta fice tana mai rufo ƙofar, ko cikakken minti ɗayan bata yi ba ta dawo hannunta ɗauke da plate, a gaban Najmeer ta aje sannan ta fice daga ɗakin, har yanzu Najmeer na kan cinyarsa sai yamusta fuska take, cike da makirci ta ce "Ka haɗa mun ruwan wanka kafin na gama" Tun kafin ta gama magana Alhajin ya miƙe dan cika umarni, ita kuwa ta fara cin Shawarmar tana lumshe ido saboda daɗin da ke ratsa ta. A haka Alhajin ya fito ya sameta, ko kallon inda yake bata yi ba ta cigaba da abin da take, "Ranki ya daɗe na haɗa miki idan kin gama sai ki shiga daga ciki" Najmeer ta kai kusan mintuna uku kafin ta ce "Okay" Tana mai miƙewa dan rage kayan jikinta, kasa haƙuri Alhajin ya yi domin ta gama firgita shi, a ruɗe ya rungumota yana mai kissing ɗin gefen wuyanta jin wani ƙamshin da ke tashi a jikinta, Najmeer kuwa bata hana shi ba sai ma murmushin muguntar da take a zuciya har suka zube ƙasa, a wannan lokacin ne ta samu damar ɗaukar hankacif ɗin da ke aljihun wandonta ta shaƙa masa a hanci, lokaci ɗaya ya ja numfashi tare da zubewa a sume. Wata irin dariyar mugunta Najmeer ta saki tana faɗin "Yanzu aka fara Alhaji" Wanka ta shige abinta, ta jima a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul, kamar yanda ta barshi hakan ta same shi, sai da ta gama duk shirin baccinta hankali kwance, ɗakin ta fara bincikawa cikin ƙwarewa da iya sata, duk wasu Gold da kuɗaɗensa sai da ta kwashe, sannan ta yiwa kanta tranfer na kuɗaɗe tana mai cigaba da dariya. A hankali ta nufi ƙofar fita ta danna mata key, dan ta san idan ta ce zata bar gidan a yanzu asirinta zai iya tonuwa, dan haka ta koma ken bed ta yi kwanciyarta tare da addu'ar bacci, cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita. Asubar fari ta farka har tana zamewa, a gaggauce ta shiga bayi, har ila yanzu Alhaji na kwance yanda ta barshi, bayan ta fito ne ta duba hijab a wadrop da mamaki ta samu sabon hijab har ƙasa, sai da ta gama sallah kafin ta kama hannayensa ta ja shi zuwa ƙarƙashin bed sannan ta rufe shi da zanin gado, toilet ta koma tana mai kunna shawa sannan ta fito. A daidai lokacin da aka fara buga ƙofar room ɗin, sai da Najmeer ta daidaita natsuwarta sannan ta ɗauki jakkar da ta zuba kayan da ta sata tana faɗin "Am coming" Ƙofar ta buɗe da mamaki take kallonsa "Waye kai?" Cewar Najmeer a taƙaice "Ni ne me kula da Sir a kullum safiyar Allah" "Okay ya shiga wanka already mun yi sallama da shi ni zan tafi" Kamar matashin be yarda ba sai kuma ya gyaɗa kai saboda jin ƙarar ruwa daga toilet ɗin. "Okay Shalele za ki iya tafiya, idan ba damuwa mu tafi na kaiki gida" A tsorace Najmeer ta ce "Ya aka yi ka san sunan da ake kirana" Murmushi Matashin ya yi "Ai yanda naga Sir ya laƙe miki daga jiya zuwa yau ne ya sa na ba ki wannan sunan" Cikin samun natsuwa Najmeer ta ce "Bana buƙatar rakiyarka" Ba tare da jiran abin da zai ce ba ta bar gurin. Tun da ta yi nisa da gidan hankalinta ya fara kwanciya a lokacin haske ya fara, adaidaita ta samu tare da yi masa kwantancen inda zai sauke ta, a can bayan layinsu ya aje ta. Allah ya sa Mamu tana ɗaki cikin sanɗa ta shige nata ɗakin tana rufo ƙofa, kamar daga sama ta tsinkayo muryar Mamu na faɗin "Idan kin gama laɓe-laɓen sai ki fito ki faɗa mun gidan Uban da ki ka kwana" "Dan Allah Mamu ki shafa mun lafiya, gidan Ubana na kwana mana, shikenan ba zan leƙa waje ba sai ki rinƙa zargin ina kwana a waje, to baza a fito ba idan kuma akwai wanda ya isa ya fito da ni" "La'ilaha illallahu mahammadan rasulillah, Najmeer ni ki ke faɗawa magana haka? laaaaa biri ya yi kama da mutum, ashe bancin Karuwanci har shaye-shaye ki ka fara" Banza Najmeer ta yi tana mai kwanciya domin bacci take ji. Mamu ta jima tana zuba masifa amma ko uffan Najmeer bata kuma cewa ba har ta gaji ta koma nata ɗakin. Yau kwana biyu kenan Najmeer bata fita koda nan da waje ba, ba ƙaramin daɗi Mamu ta ji ba hakan ya ƙara mata natsuwa duk a tunaninta Najmeer ta shiryu, sallamar da yaro ya yi ne yasa Mamu amsawa tana faɗin "Wa ka ke nema?" "Wai Jabir yana sallama da Najmeer" Najmeer da fitowarta daga bayi kenan cikin shigar doguwar riga irin ta larabawa me adon duwatsu rigar ta masifar yi mata kyau, pink colour wadda zata kai kimanin dubu ɗari, gashin kanta ta laulaya shi sannan da ɗora mayafi ƙarami a kai, ƙafarta sanye cikin silifas me taushi "Tafi ka ce masa ko Ubansa Bukar be isa ya kira ni na tafi ba balle shi ɗan Akuya" Cewar Najmeer tana jifar Yaron da aka aiko da butar da ke hannunta, da gudu yaron ya fita yana ihu, salati Mamu ta rafka "Yoooo ni Mamu naga ta kaina, ke Najmeer surukin naki ki ka ambata haka?" Tun kafin Najmeer ta amsa wani yaron ya sake shigowa "Wai dan Allah ta yi haƙuri ta fito" Da mugun gudu Najmeer ta nufi randar ruwan da ke tsakar gidan har takalmanta na cirewa, sai da ta cika wata roba da ruwa ta nufi hanyar waje, Mamu na ganin haka ta miƙe tana kiran sunanta amma ina har Najmeer ta fice, wani matashi ne da zai kai kimanin shekaru ashirin da bakwai sanye cikin fararen kayansa, ɗan mashin ɗinsa na gefe ya sha wanki, fuskarsa ɗauke da murmushi, ba zato ba tsammani ya ji an kwara masa ruwa, ai be ankara ba ya ji an zuba masa ƙasa a jikinsa, sai da Najmeer ta shafe mashin ɗinsa da duk jikinsa da ƙasa tana mai banka masa harara, Mamu da ƙarasowarta kenan ta damƙo hannun Najmeer tare da sharara mata mari, ai tun kafin Mamu ta sauke hannu Najmeer ta watsawa Jabir mari cikin mugun rashin kunya ta ce "Ƙarya ne wallahi, baza a mareni saboda kai ba, munafukin banza yau sai na illataka jira ni kaga" A fusace ta shiga gida tana surutai kamar zararra, gaba ɗaya mutane sun taru a ƙofar gidan, Jabir kam kasa magana ya yi Mamu sai haƙuri take bashi, duk mutanen da ke wajen suna yi ta cewa ya gudu tun kafin ta fito, ihun Najmeer suka jiyo daga bayansu ta nufo shi da Wuƙa a hannu fuskarta banu alamun wasa, ai kuwa ƙafa me naci ban baki ba, Jabir ya runtuma da gudu ko ta kan Mashin ɗinsa be bi ba, mutanen da ke gurin suma duk sun watse dan sun san cewa ba shakka Najmeer na iya dawowa kansu. Mamu kam zaman dirshan ta yi tare da dafe kanta tana mai karanta duk addu'ar da ta zo bakinta. Labari ko har ya kai kunnen Kawun Najmeer, a fusace ya nufi gidansu Jabir, tun daga bakin ƙofa ya fara jiyo Mahaifin Jabir na zuba ashar, da sallama Kawu Jamilu ya shiga gidan "Kar ka tako ƙafarka cikin gidana idan ba haka ba wallahi sai ran kowa ya ɓace, har ni wata Karuwa za ta wulaƙantawa yaro? yoooooo me ake da wata ƴar tasha wadda bata gaji mutunci ba, daga yau na saka wuƙa na datse alaƙar Jabir da shashashar yarinyarku" Haƙuri Kawu Jamilu ya shiga bashi yana mai neman afwa, "Haba Bukar me ya yi zafi haka? wallahi idan a yau ku ke son aurennan za'a iya ɗaurawa" Zumbur Jabir ya ce "Eh a ɗaura a yau kowa ya huta, Baba dan Allah ka yarda na aureta ina msifar son Najmeer" Ba ƙaramin so Bukar ke yiwa Yaron nasa ba kasancewar shi ɗaya Allah ya mallaka masa, ba wata dukiya ce da su ba amma duk Unguwar sun fi kowa rufin asiri shiyasa ma Kawu Jamilu ya liƙe musu domin ya lashi arziƙi. "Shikenan a ɗaura a yau ɗin, amma idan har ta ƙara wulaƙanta min Yaro babu wanda ya isa ya haɗa aurennan" Godiya Jabir da Kawu Jamilu suka shiga yi, miƙewa Jabir ya yi yana mai faɗin "Bari na shiga na shirya, Baba a samu a ba Kawu kuɗin sayen goron ɗaurin aure" Jikin Kawu na rawa ya ce "Yawwa yaron kirki ashe ka gane" Dubu goma aka miƙa masa, carafffff ya karɓe yana washe baki. Ƙarfe huɗu suka isa gidansu Najmeer, wannan karon har da limamin Unguwar da wasu dattijai uku ƴan uwan Mahaifin Jabir. A lokacin Najmeer na zaune tsakar gida tana cin shinkafa da miya sai naman kajin da ke saman abincin, gefe ɗaya kuwa drinks ne masu sanyi, sai sautin waƙar M-Sharif ke tashi wadda ta kunna a wayarta, Mamu na zaune tana linke kayanta wanda ta karɓo daga gun wanki. Sallamar su Kawu ne ya sa Mamu ɗagowa tana amsawa fuskarta ɗauke da murmushi, amma tana ganin su Bukar da Yaronsa har ma da Liman ta ji gabanta ya faɗi, maraba ta yi musu tare da nuna musu shimfiɗa, duk bidirin da ake Najmeer bata saniba saboda ƙarar waƙar da ke tashi, bayan sun gaisa ne Kawu ya kalli gefen da Najmeer ke zaune tare da daka mata tsawa ganin abin nata yana son wuce gona da iri "Ke dan Ubanki ba kiga mutane ba ne? ki ke wannan haukar" A tsorace Najmeer ta miƙe jikinta na ɓari, sanye take cikin wando da kaɗan ya wuce mazaunanta sai ƴar rigarta marar hannu wadda ko cibiyarta bata rufe ba, gashin ganta ya sauko yana rito fuskarta ɗauke da simple makeup, ba Jabir ba har Liman da sauran mutanen sai da suka gigice, ji ka ke kawai Liman da Mahaifin Jabir sun buga salati, Liman ya ce "Subhanallahi, Allah ya shirya" Sai a lokacin Najmeer ta tuna da kayan da ke jikinta, da sauri ta nufi ɗaki ƙirjinta na dukan uku-uku kar dai a ce ƙararta Jabir ya kai gurin Kawunta, to idan ƙarar ta ya kai meyesa Liman ya zo gidansu abin da bata taɓa ganiba. Gaba ɗaya ta kasa ba kanta amsar waɗannan tambayoyin, Mamu ce ta ce "Sannunku da zuwa, Allah dai ya sa lafiya naga har da su Liman" Murmushi Liman ya yi "Lafiya ƙalau alkhairi ne ke tafe da mu, da farko dai ga goron ɗaurin aure, yanzu haka na saka a tara jama'a a ƙofar gida domin su shaida auren Jikanyarki Najmeer da ɗan wajen Malan Bukar Jabiru" Wata irin muguwar ashar Najmeer da ke laɓe bakin ƙofa ta ja, "Allah ya tsinewa mutanen da ka tara a ƙofar gidanmu daidai gwargwado, kai Liman har ka isa ka ɗaura mun aure, wallahi duk sai na shuka muku rashin mutunci" Jikin Jibir ne ya fara rawa dan yanzu kam tsoronta yake, Kawu Jamilu ne ya miƙe rai ɓace ya nufi ɗakin, Najmeer na ganin haka ta kwasa da gudu, ai kuwa ya rufa mata baya, daga waje kana jiyo ihunta taja faɗin wallahi ta yarda da auren, kuka take kamar ranta zai fita, ita kanta Mamu bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, ba ƙaramin tausayin Najmeer take ba, ta san cewa dukanta Kawu Jamilu ya yi, a duniya ba abin da take son gani fiye da farincikin Jikanyar tata. Fuska a murtuƙe Kawu ya dawo tare da zama kusa da Jabir "Kwantar da hankalinka Najmeer ta zama matarka, ke kuma Mamu ga naki goron ki rabawa mutanenki, mu zamu tafi daga waje mutane na jira" Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, Malan Bukar da su Liman ma suka rufa masa baya, suna fita Mamu ta nufi ɗakin Najmeer dan har yanzu tana jin sautin kukanta. LONDON ................. Wani irin numfashi ya sauke wanda ya sa matashiyar da ke kwance sauke ajiyar zuciya, sun jima a haka kafin ya ƙara ƙanƙameta a jikinsa na tsawon mintuna biyar, a hankali ya koma gefe yana sauke numfashi. Cikin salo da iyayi matashiyar ta ƙara haurawa saman jikinsa ta shafo haɗaɗɗen sajensa, "Love you are so sweet, but why do u want to go back to Nigeria?" Ta tambayesa tana shafa ƙasan mararsa, kyakykyawan matashin da zai kai kimanin shekaru ashirin da takwas ne ya ce "Colm down Babe you know my Dad said i should go back, and yau satina ɗaya da ƙare School amma kin hana mun komawa" "Amma Love........" "Shhhhhhhhhh......." Ya ɗora yatsarsa a lips ɗinta "Not another word Babe, anjima jirginmu zai ɗaga zan shiga wanka" Ya faɗa yana miƙewa daga kan bed ɗin, sanin halinsa ne ya sa ta kasa magana, zubawa halittarsa ido ta yi tamkar yau ta fara ganinsa, dogo ne daidai gwargwado me faffaɗan ƙirji, gashin kansa kamar na larabawa, shi ya ƙara bawa fatar jikinsa da ke fari tassss damar fito da kyawunta, yana da manyan idanu farare masu jan hankali ɗauke da gashi zara-zara, idan ya motsa bakinsa kuwa zaka iya ɗauke muntuna biyar ba ka daina kallon bakin nasa ba, ɗauke yake da red lips me laushi tare da fararen haƙora masu jan hankalin me kallonsa, dogon hancinsa kuwa har ya ɗan kwanta a sama kuwa ya yi tsayi gwanin sha'awa, gashin girarsa baƙi ne wulikk ga cika ga kyau, yatsun ƙafarsa zara-zara ne masu ɗaukar hankali, kamar yanda gashin ƙirjinsa ya kwanta luff-lufff kana gani ka san cikakken namiji ne me tsafta da kwarjini, cigaba da ƙura masa ido matashiyar ta yi har ya shige ƙayataccen toilet ɗin da ke ɗakin, duk da cewar itama ba ƙaramin kyau ne da ita ba, haskenta ma har ya haɗa da sirkin ja, saboda gashin kanta ba wani baƙi ba ne, kana ganinta ka san Baturiya ce cikakkiya, kamar wadda aka tsikara ta miƙe tare da shigewa toilet ɗin, sun ɗauki kusan mintuna talatin a ciki, sannan suka fito a tare daidai lokacin da wayarsa ta fara ƙara, cikin taƙama ya ƙarasa yana mai kallon screen ɗin, ganin sunan Dad ne ya sa shi saurin ɗagawa amma be ce komi ba. Daga can ɓangaren Dattijon ya ce "Sultan baza ka yi magana ba ne? har yanzu kana London kamar wanda aka jona jininsa a ƙasar, to na ba ka nan da anjima ka shigo Nigeria if not sai na ɓata maka rai" Ba tare da jiran abin da Sultan ɗin zai ce ba ya Dad kashe waya, da ƙarfin tsiya Sultan ya buga wayar tasa a ƙasa ƙirar iphone 15promax nan take ta yi kaca-kaca, wani irin mugun huci ya furzar yana dafe saitin zuciyarsa, a kiɗime Matashiyar ta ja baya ganin halin da ya shiga, ba tare da ya kalleta ba ya fara shiryawa cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya masu masifar kyau da ɗaukar ido, wani ƙayataccen agogo ya saka na Gold yana mai fesa turarukka masu daɗin ƙamshin, a lokacin zuciyarsa ta fara sanyi amma idanuwansa sun rine sun yi jajir, "Malika what are you waiting for?" Ya faɗa a tsawace. Jikin wadda aka kira da Malika na rawa ta ce "Am......am......am waiting for you". "What.......? idan na buɗe idona na ganki a nan sai na kakkarya ƙasussan jikinki" Tun kafin ya gama rufe baki ta kwashi kayanta a hannu tare da barin ɗakin cikin mugun gudu, dan ta san cewa yau ransa ya ɓace. Cikin ƙanƙanin lokaci ya nufi airport, ba ɓata lokaci jirginsu ya tashi, gaba ɗaya mutanen da ke cikin jirgin kallonsa suke musamman mata, ganin tsananin kyawun halittarsa me matuƙar jan hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya sauka a babban airpor na garin Jos, wata Matashiya da ke bayansa ne ta ƙura masa ido har suka sauko daga kan matattakalar, daga nesa Drivernsa me suna Umar ya hangesa cikin hanzari ya ƙaraso yana mai karɓar Trolyn da ke hannunsa, "Ƙaramin Alhaji barka da zuwa?" Drivern ya faɗa yana murmushi ko kallonsa Sultan be yi ba ya bar gurin, bayansa Umar ya bi cikin rashin damuwa dan sun saba da halinsa a gidan, balle yanzu da ya tafi ƙasar turai ai dole zai ƙara hartsinewa. Motoci uku ne masu masifar tsada suka zo tarbarsa, daga cikin motocin akwai ƙirar Loxes me jan hankali, glass ɗinta black ne ba ka ganin wanda ke ciki, amma da alama akwai mutun a cikinsa, cike da miskilanci Sultan ya kalli Drivern da ya saka troly a boot "Waye a cikin motar nan?" "Ƙaramin Alhaji ai Oga Junaid ne tare da shi muka zo" Da sauri Sultan ya nufi motar cikin mamaki dan be yi tsammanin Brother ɗin nasa zai zo tarbarsa ba, Drivern da ke jan motar Junaid ne ya yi saurin buɗewa Sultan ƙofar motar, ai kuwa ya shige cike da ƙasaita. A zaune ya same shi waya kare a kunnensa, ƙamshin turarensa ya gama hautsine gaba ɗaya motar, a cinyarsa kuwa Laptop ne da alama aiki yake yi, Matashi ne fari sol me matuƙar kyau wanda kana ganinsa ka san hutu da kuɗi sun gama baje hajarsu a jikinsa saurayi me taƙama da aji ɗan shekaru talatin daidai a duniya, kamanninsu ɗaya da Sultan har ma zaka kasa gane wanda ya fi wani kyau a cikinsu, sai dai shi Junaid lips ɗinsa pink ne saɓanin Sultan da nasa red ne, sanye yake cikin manyan kaya yadi me masifar tsada da ɗaukar ido wanda kana gani ka san kuɗi sun yi kuka, wayarsa ƙirar 15promax ce ya sauke a hankali yana mai kallon ɗan uwan nasa, cikin muryarsa me ɗan karen daɗi ya ce "Ba ka iya gaisuwa ba ne Sultan" Ɗan cije lips Sultan ya yi dan baya son abin da Brother ɗin nasa yake masa, amma babu yanda ya iya dole ya sosa gashin kansa fuska a haɗe ya ce "Barka da war haka" Sai da Junaid ya ɗauki mintuna uku yana latsa Laptop ɗinsa wanda har jikin Sultan ya fara rawa tsabagen takaici babu abin da ya tsana irin wulaƙanci, kamar daga sama ya ji ya ce "Lafiya ya hanya" "Hanya Alhamdulillah" Sultan ya amsa a taƙaice. Ba tare da Junaid ya kuma cewa komi ba ya ce "Driver we can go because i have alot to do" Cikin girmamawa Driver ya ja motar, nan take sauran motocin suka mara musu baya, tun da suka fara tafiya babu wanda ya sake magana daga Junaid har Sultan kowa na ji da kansa. Wata arniyar Unguwa suka nufa wadda suke kira da G R A, babbar area ce a cikin garin Jos wanda duk wani me kuɗi da ke ji da kansa zaka same shi a unguwar, a bakin wani tangamemen gate motocin suka tsaya nan take gate ɗin gudu uku suka ɗage sama, gida ne wanda tun daga wajensa zaka tabbatar da cewa ba ƙaramin hamshin me kuɗi ne ya gina shi ba, gaba ɗaya ginar gidan Golding Colour ne, gate ɗin kuwa na Gold ne wanda kafin ya ɗage sama sai ya yi searching idan har ba ka ɗauke da wani mugun abu, a pearking place suka tsaya wanda duk iya gulmarka baza ka ga ƙarshen motocin da ke baje a gurin ba, and you can't even count it. Every where security's ne kowannensu riƙe da bindiga suna tsaron lungu da saƙo na gidan. Gida ne me hawa-hawa har huɗu lafiyayyu na faɗa a ji, kowanne hawa da kalar pentinsa kuma kowanne hawa da kalar tsarinsa, a iya binciken da aka yi gaba ɗaya garin Jos babu gidan da ya kai gidan Chif Muhammad kyau, gaba ɗaya gidan Flowers ne masu ɗaukar hankali Golding colour waɗan da idanu basu taɓa gani ba, grass carpet ne a baje me matuƙar ɗaukar hankali, guraren shaƙatawa kuwa ya fi biyar a gidan, kama daga swimming pool har gadin. Da sauri wani matashi ya ƙaraso tare da buɗe musu motar. Cikin gadara Sultan ya sauko da ɗayar ƙafarsa yana ƙarewa gidan kallo zuciyarsa na kaɗawa, sai da ya ɗauki tsawon mintuna uku a haka kafin ya fito a lokacin Junaid ya jima da isa haɗaɗɗen parlourn gidan wanda ko gidan shugaban ƙasa be kai shi haɗuwa ba, ta ko'ina kayan more rayuwa ne kamar basu san zafin dukiya ba, manya-manyan TV ne guda uku masu rai da lafiya manne a bangon parlourn, ɗaya daga cikin haɗaɗun royal ɗin da ke gurin Junaid ya zauna bakinsa ɗauke da bisimillah. Daga sama ya ji ana faɗin "Where's he?" A hankali Junaid ya sauke rikitattun idanunsa kan Dad ɗin nasu "He's coming Dad just wait a minute" Daga haka Junaid be sake cewa komi ba. Dattijon mutumin kuwa da ke cikin kayan alfarma ne ya fara saukowa daga matattakalar fuskarsa a haɗe, kana ganinsa ka san shine Mahaifinsu dan kamanninsu ya nuna hakan, sai dai shi ya fi su tsufa ne kawai. Kayan jikinsa sun isa tabbatar maka cewar babu wani abun da suke nema a duniya face gamawa da ita lafiya. Saman kujera me zaman mutum ɗaya ya zauna yana mai duba agogon gold ɗin da ke hannunsa daidai lokacin da Sultan ya yi sallama cike da taƙama, dirrect gurin Dad ɗin nasa ya nufa yana mai ware hannayensa "Hi Dad am back......" "You are very stupid Sultan, is that how za ka gaida mahaifinka? ashe ka watsar da tarbiyyar da na yi shekara da shekaru ina ba ku". Idanun Sultan ne suka ƙanƙance tsabagen fusata har jikinsa ya fara rawa jijiyoyin kansa sun tashi ruɗu-ruɗu, a fusace ya nufi matattakalar ba tare da ya ƙara magana ba, cikin tsawa Dad ya ce "Sultan don't add another step if not wallahi sai dai ka canja wani Uban amma ba ni ba......" Cakkkk ya tsaya yana mai damƙe hannunsa da ƙarfin tsiya, Junaid da ke jin duk abin da ke faruwa ne ya ɗago kyawawan idanunsa yana mai saukewa kan Sultan, lokaci ɗaya kuma ya miƙe tare da nufar Frigde ɗin da ke parlourn, robar ruwa ya ɓalle sannan ya zuba a Cup. Cike da takunsa me jan hankali ya ƙaraso gaban Sultan da har yanzu tsaye yake kamar wanda aka dasa, "Take this ka sha ko zuciyarka zata yi sanyi, but remember one thing please he's our Dad not our mate". Hannunsa ya kama ya ɗora masa Cup ɗin sannan ya haura sama yana mai sakin murmushi. A fusace Sultan ya ɗaga Cup ɗin ya kai bakinsa, kurɓa uku kawai ya shanye ruwan yana mai jingina bayansa kan ƙarfen da ke steps ɗin, duk abin da yake Dad na kallonsa yana mamakin zuciya irin ta ɗan nasa, sai da ya ƙara mintuna uku ahakan kafin ya fara saukowa kan steps ɗin a hankali, kujerar da ke fuskantar Mahaifin nasa ya zauna cikin sanyin murya kamar wanda ke ciyon magana ya ce "Ina wuni Dad ya gida" Sai da Dad ya ƙare masa kallo kafin ya ce "Lafiya lau ya karatun? ina fatar ka gama tattaro komi naka da yake can, saboda kai da ƙasar London har ƙarshen rayuwarka, waɗannan shekarun da ka yi ka gama sauya rayuwarka gaba ɗaya dama ko a can baya sai a hankali". "Yes Dad amma na bar abu me muhimmanci da gaba ɗaya Family sai sun koma saboda shi" "What are you saying Sultan, wanne abu ne haka da har zai sa Family su tafi wata ƙasar?" "Dad wadda zan aura" Sultan ya faɗa cike da gajiya da magana dan ba ƙaramin wahala magana take yi masa ba. Rai ɓace Dad ya ce "Ashe ka isa da kanka tun da har zaka tafi wata ƙasar ka kwaso mana wata macen acan, to bari ka ji na faɗa maka idan har na isa da kai kuma ni ne Ubanka babu kai babu wannam yarinyar" Ba tare da Dad ya jira abin da Sultan zai ce ba ya miƙe yana mai barin parlourn a lokacin da wata Dattijuwa ke saukowa daga saman bene fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Sultan, haɗaɗɗiyar atamfa ne jikinta me tsadar gaske duk jikin nata Gold ne, ba ƙaramin kyau ta yi ba, domin har hutu da jin daɗi na ƙoƙarin ɓoye tsufanta, Sultan na ganinta ya miƙe da sauri ya nufeta tare da hugging ɗinta kamar ƙaramin yaro ya ce "Hi Mom am back" Ƙara faɗaɗa murmushinta ta yi "Hi Son welcome ya London ɗin?" Ta faɗa tana mai kama hannunsa suka koma kan kujera me zaman mutum uku. Sultan na yamutsa fuska ya ce "So amazing but Mom kina jin Dad wai ba zai barni na yi aure a ƙasar waje ba" Gefen fuskarsa ta shafa cikin so da ƙauna ta ce "Don't mind him babu wanda ya isa ya hana ka auren wadda ka ke so. "Thank you so much Mom that's why i love you" "Love you too Sweetheart ka je ka watsa ruwa kafin ka gama zan sa a haɗa mana abinci yau a babban parlour za'a ci abinci tun da ka dawo" Fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙe yana faɗin "Okay Mom" Cikin so da ƙaunar ɗan nata take kallonsa har ya haura sama cike da gadara. A hawa na biyu ya isa wanda anan ne part ɗinsa, wani irin mashahurin room ne wanda komi nasa blue colour ne hatta penting ɗakin, ƙayataccen bed ne irin na manyan ƴaƴan masu kuɗi, komi na ɗakin set biyu ne hatta Mirrow, girman ɗakin kuwa ya wuce misali dan zaka iya tafiyar mintuna uku kafin ka kai ƙarshen ɗakin, dukiya ce a zube tamkar basu san zafinta ba, a bangon ɗakin kuwa wani tangamemen hotonsa ne sanye cikin manyan kaya ya masifar kyau amma fuskarnan a haɗe, a lokaci ɗaya kuma tunanin burdurwarsa ta London ta faɗo masa, wani irin juyi mararsa ta yi kamar zata bar jikinsa nan take jikinsa ya fara rawa, da ƙyar ya isa gun troly ɗinsa ya buɗe hannunsa dafe da mararsa idanuwansa sun yi jajir, Laptop ɗinsa ya ɗauka yana mai zama kan sofa, da sauri ya shiga wani chat yana mai typying kamar haka (Hi Guy am back and i really need a hort Girl urgent) ko minti ɗaya massage ɗin be yi ba aka yi reply da (Okay akwai wata Babe me zafi da take zuwa Clup a duk ranar yau na san you will like her saboda gaba ɗaya Jos babu me kyawunta balle kyawun surarta her name is Shalele suna kiranta Shalelen Alhazawa) jin sunan da aka kira yarinyar da shi ne ya sa Sultan jin muguwar faɗuwar gaba sai da ya ɗauki mintuna uku ba tare da ya yi reply ba daga ƙarshe ya tura masa (Okay am waiting for you Guy ka sameni a gida around 10:00pm wallahi a matse nake) Yana tura hakan ya kashe Laptop ɗin yana mai cije lips ɗinsa da ƙarfi dan wani zugin da mararsa ke masa, ya san cewa ba ƙaramin haƙuri ya yi ba tun da har ya kai wannan lokacin without havin sex, a daddafe ya miƙe tare da shigewa toilet yana mai rufo ƙofar. *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P. 2 He took almost 40 to 50 minutes kafin ya fito ɗaure da tawul me laushi da ƙamshi, ɗayan kuma yana tsane haɗaɗɗen gashin kansa. Ba wani lokaci ya ɗauka gurin shiri ba ya fito cikin jallabiya fara sol me kyau da tsada, rikitattun turarukkansa ya fesa waɗan da ya saya a ƙasar London masu sihirtaccen ƙamshi yana mai saukowa ƙasa cike da taƙama. Ƴan aikin part ɗinsa mutane uku ne mata, a tsaye ya samu ɗaya daga cikinsu me suna Sumayya, cike da girmamawa ta gaida shi tana mai zuba masa ido, wani mugun kallon wulaƙanci ya yi mata ganin yanda take kallonsa, "Zo nan ke dan Ubanki" Ya faɗa a tsawace, jikinta na rawa ta ƙaraso tana mai sunkuyar da kai ƙasa, cike da jaraba ya janyota ta faɗo jikinsa, a ruɗe ya fara romance ɗinta kamar zai zaunce, ƴar aikin me suna Sumayya kuwa dama abin da take so kenan dan ta jima tana kwaɗayin jikin Sultan saboda ba ƙaramin so take masa ba, sosai yake yamutsa ta har suka zube ƙasa, sai ƙara shige masa take tana ƙoƙarin haɗe bakinsu, wata irin razananniyar tsawar da aka daka musu ne ya sa dukkaninsu dawowa cikin hayyacinsu a ruɗe. A mugun rikice Sumayya ke kallon Junaid da hankalinsa ya gama tashi ganin abin da be taɓa zato daga gurin ƙanin nasa ba, tsawar da ya ƙara daka mata ne ya sa ta miƙe jiki na rawa "Idan na sake buɗe ido naga wannan ƙazamin jikin naki anan a bakin aikinki ballagaza mahaukaciya". Junaid ya faɗa yana mai dafe kansa da ke sarawa, babu abin da ya tsana irin yaga mutum na aikata zina ko kuma saɓon Allah. Da gudu ta bar part ɗin har tana zamewa, Sultan kuwa haɗe fuska ya yi ganin abin da Junaid ya masa, a ƙufule ya raɓa ta gefensa yana ƙoƙarin wucewa, ba zato ya ji Junaid na faɗin "Sultan why......?" Cakkkk Sultan ya tsaya ba tare da ya ce uffan ba kuma ba tare da ya juya daga inda yake ba, "Sultan ƙanwar wani ce fa, kuma matar wani ce wadda idan har kana da ƙanwa aka yi mata hakan baza ka ji daɗi ba, kana son Allah ya yi fushi da kai ne?" Junaid ya ƙarasa maganar hawaye na zuba kan kuncensa, a hankali Sultan ya maida kallonsa kan yayan nasa, ba ƙaramin mamaki ya yi ba ganin hawaye na zuba kan fuskar Junaid abin da tun da Allah ya haliccesa be taɓa gani ba, har Sultan ya kai hannu da niyar dafa kafaɗarsa Junaid ya ɗaga masa hannu rai ɓace "Don't......, ka je ka wanke janasar da ke jikinka" Ya ƙarasa maganar yana barin gurin cike da takaicin halin da ya sami ƙanin nasa, Sultan kuwa kafaɗa ya ɗage alamun ko a jikinsa. A babban parlourn ya sami mutanen gidan amma banda Junaid, "Hi guys whtp?" Ya faɗa yana dunƙule hannu ya miƙawa Mom ɗinsa itama ta dunƙule hannu tare da miƙa masa suka haɗe suna murmushi, ko kallon inda suke Dad be yi ba ya cigaba da cin abincinsa yana mai nemawa ɗan nasa shiriya a zuciya. Da sauri me seving abinci ta ƙaraso ta zuba masa haɗaɗɗar shinkafa julof wadda ta sha naman rago, sai dambun naman da ya ji kayan haɗi, ɗan ƙaramin Cup ɗin zinarin da ke gurin ta zuba masa juice na apple wanda ke tashin ƙamshi, ba zancen bismillah Sultan ya fara cin abincin yana lumshe ido, "Ina Junaid ne?" Mom ta tambaya tana kallon Sultan, sai da ya ɗauki mintuna biyu kafin ya ɗago yana yamutsa fuska "Maybe ya fita" Daga haka be sake cewa komi ba, ba wani abincin ya ci ba dan Sultan be damu da abinci ba, miƙewa ya yi yana mai faɗin "Dad Mom ni zan fita" "Babu inda zaka tafi" Dad ya faɗa kansa a ƙasa. "What......why? Dad wayana ne ya samu matsala nake son a karɓo mun wata" "Ka sami Junaid a ɗaki ba zai rasa waya ba, ɓace mun da gani please" Sultan na ɓata fuska ya nufi ɗakin Junaid. Mom da ke kallon Dad ne ta ɗan rai tana faɗin "Wai meyesa ka ke takurawa wannan yaron ne? tun kafin ya dawo ka ke nuna fushinka a kansa" "Kina ganin hanyar da nake ɗora shi ba daidai ba ne?" "Ba haka nake nufi ba Chif, amma a ganina tsananin ya yi yawa" "Ai sai ki nuna mun cewa ke ce Uwarsa ni kuma ba Ubansa ba ne" Dad ya ƙarasa maganar yana miƙewa daga zaunen da yake. Har Mom ta buɗe baki da niyar magana ya ɗaga mata hannu "Bana son jin komi" Shuru ka ke ji ta kama bakinta dan ta san halin Dad baya son yana magana ana amsa masa. Sultan kuwa a kwance ya sami Junaid yana latsa wayarsa, a gefensa Coffee ne me zafi da ƙamshi wanda yake sha a duk rana ta Allah. Ciki-ciki Sultan ya yi sallama sanin halin Junaid baya son a shigo masa ɗaki ba sallama, ɗaki ne wanda ya amsa sunansa, ɗakin ya masifar yin kyau, komi na ɗakin Golding ne hatta penting da aka masa, kamar yanda komi set biyu ne a room ɗin Sultan haka ma room ɗin Junaid sai dai room ɗin Junaid ɗin ya fi kyau nesa ba kusa ba, saboda yana yawan canja kayan ɗakin nasa lokaci zuwa lokaci, saɓanin Sultan da rabonsa da gida shekara ɗaya kenan. Cike da ƙasaita Sultan ya ce "Bro wayana ne ya fashe ina hanyar dawowa can i get another phone with you" "Ya hakan ta faru?" Cewar Junaid. Ɗan sosa kai Sultan ya yi cikin gajiya da zancen ya ce "Na zauna a kai ne a rashin sani" "Ka duba a loka akwai 15promax da nake son na yi giveaway gobe insha Allah sai ka ɗauki ɗaya daga ciki" Daga haka be sake cewa komi ba, shima Sultan ɗin gurin lokar ya tafi ba tare da ya amsa yayan nasa ba, wayar ya ɗauka cikin kwalinta sabuwa galllll yana mai ficewa daga ɗakin. Room ɗinsa ya koma dan haƙurinsa ya fara ƙarewa, duk zaman da ya yi da su Mom daurewa kawai yake amma mararsa dammm take da feelings. Layinsa na Nigeria ya ɗauko tare da sakawa a sabuwar wayarsa yana mai danna wata number me suna Majeed, bugu biyu aka ɗaga, cike da miskilanci Sultan ya ce "Guy how far yarinyar zata samu zuwa kuwa?" Daga can ɓangaren ne aka ce "Ai babu Friday ɗin da bata zuwa Clup kawai ka zauna a shiri" "Wait Guy ina fatar ba ƙazama ba ce ba" "Haba My Sultan wannan yarinyar ko tsafta ta fika......" Wani mugun ashar Sultan ya narkawa Majeed yana faɗin "Har akwai wata tsinanniyar karuwar da ta fini tsafta a faɗin garinnan" "Sultan calm down be kai haka ba, yanzu magrib ya kusa mu haɗu ƙarfe goma kamar yanda ka ce, amma Dad fa? how will you come out?" Sai da Sultan ya ɗauki mintuna biyu ba tare da ya ce komi ba, sai can kuma ya ce "Don't worry i'll call you, mu haɗe a bakin gate by 10:00pm". Ya faɗa yana kashe wayar. ..................... A ɓangaren Najmeer kuwa sosai Mamu ta rarrasheta har ta shirya cikin tsadaddun kaya masu masifar kyau, duk jikinta ya mutu mafita kawai take nema. A lokacin gaba ɗaya wajen gidan ya cika da mutane, Kawu kam sai raba goro yake yana mai washe baki. Bayan an gama sanarwa ne Kawu Jamilu ya nemi izinin shigowa gida dan ya faɗawa Mamu za'a ɗaura auren, ihun da ya ji ne ya sa shi ƙarasawa cikin gidan da gudu dan ganin abin da ke faruwa. A ƙasa ya samu Mamu na rusa kuka kamar ranta zai fita, nan da nan gidan ya cika da maza domin kukan Mamu ya tsananta, Kawu Jamilu kuwa ba kukan ne damuwarsa ba sai wulla ido yake inda zai hangi Najmeer amma babu ita babu alamunta, a mugun fusace ya damƙi wuyan Mamu kamar zai kasheta yana faɗin "Ina shegiyar yarinyar nan ne? kar ki ce mun ta gudu dan wallahi baza ta saɓu ba". Mutanen da ke gurin ne suka rirriƙe Kawu ganin da gaske kashe Mamu zai yi, ai kuwa ya rarumi icce ya rinƙa dukan mutane yana kiran sunan Najmeer, duk waɗan da ke gurin sun watse dan kar ya illata su, ɗakin Najmeer ɗin ya nufa dan tabbatar da gaskiya, ai kuwa ko tsinke a cikin kayanta bata bari ba, duk wata sutura da kayan kwalliyarta ta kwashe, kayan ɗakin ne kawai bata taɓa komi ba, wani irin ihu Kawu ya daka wanda yasa su Jabir da iyayensa shigowa ɗakin da gudu, nan suka tarar da abin da ya rafu, ai kuwa Jabir ya rarumi Kawu Jamilu ya damɓara shi a ƙasa, ji ka ke timmmmm, Bukar Mahaifin Jabir da ƴan uwansa suka rufa masa baya, sai da suka yiwa Kawu mugun dukan tsiya, da mahaukacin gudu Kawu Jamilu ya bar gidan yana mai neman ceto, bayansa Jabir suka bi suna mai zage-zage kamar zautattu musmaman Jabir wanda ji yake duk burin rayuwarsa ya lalace. Mamu kuwa na ɗaki ta gaza zaune balle tsaye sai hawayen da ke rito kan kuncinta, kamar an ce ta kalli gefen pilo sai ga baƙar leda, da sauri ta ƙarasa tana buɗewa. Kuɗaɗe ta gani masu yawan gaske, zaro ido ta yi dan ta san aikin Najmeer ne, ai bata gama mamaki ba ta ji sallamar yaro a tsakar gida, cikin hanzari ta ɓoye kuɗin tare da fitowa, ɗan ƙaramin yaro ne wanda zai kai shekaru sha uku zuwa sha huɗu, bayan ya gaishe da Mamu ya ce "Wai ga saƙo in ji Shalele" Bakin Mamu na rawa ta ce "Tana ina ne?" Wata takadda yaron ya ciro a aljihun wandonsa ya warware sannan ya fara karantawa kamar haka "Ina mai ba ki haƙuri da kuma neman yafiyarki ga watsa muku ƙasa da na yi tare da tozarta ku gaban mutane, amma ina mai tabbatar miki cewa zan dawo gare ki idan lokaci ya yi, bayan haka zan rinƙa turo miki da duk abubuwan buƙata......." Kukan da Mamu ta fashe da shi ne ya sa yaron tsagaitawa, bayan ta rage sautin kukan ne ya cigaba da faɗin "Kar ku yi wahalar nema na, domin baza ku taɓa samu na ba, ina cikin garin Jos na kama gida har zuwa lokacin da Kawu zai canja ƙudirinsa a kaina, sannan kuma ya sa Jabir ya sake ni, na san cewa yanzu am ɗaura aurena da Jabir amma ba zan taɓa yi masa biyayya ba, kuma ba zan taɓa zama a ƙarƙashinsa ba, daga ƙarshe ina miki fatan alkhairi da kuma roƙonki da ki taya ni da addu'a". Yaron ya ƙarasa yana miƙa mata takaddar sannan ya fice daga gidan, in banda karkarwa babu abin da jikin Mamu ke yi, tsoro fargaba da kuma tashin hankali ne kwance kan fuskarta, a haka ta ja jiki zuwa ɗakinta. ................ Najmeer kuwa tun da ta bar Unguwarsu ta nufi wata unguwa me suna Dutse uku wadda tana da nisa sosai da unguwarsu dan sai ka shiga mota, wani ƙaramin gida ta kama haya me ɗakuna biyu da toilet ɗaya sai kichen, babu abin da zaka rasa a gidan kama daga bed kujeru da kayan kitchen, cikin ƙanƙanin lokaci ta jere kayanta a wadrop sannan ta ƙara gyara ko'ina ta yi mopping, wajen ƙarfe bakwai na dare ta kammala. Wanka ta shige dan jikinta duk ciyo yake mata, sai da ta haɗa da alwala kafin ta fito sanye da ɗan ƙaramin tawul daidai santala-santalan cinyoyinta masu kyau da jan hankali. Haɗaɗɗen man shafawarta ta ɗauka cikin ƙanƙanin lokaci ta gama shafawa tare da saka ƙaton hijab ta kabatarta sallah. Sallamewarta ke da wuya ta fara jiyo ihu da kuka tare da maganganu iri-iri, dama part biyu ne a gidan daga part ɗinta sai na wasu a can gafe, kuma daga nan take jiyo kukan, babu alamun tsoro ta tattara hijab ɗinta ta nufi part ɗin dan ganin abin da ke faruwa. Abin da ta gani ne ya mugun firgitata, wani matashi ta gani wanda zai kai kimanin shekaru talatin daga ganinsa kaga mashayi, duk jikinsa kaca-kaca abun ƙazanta, a ƙasa kuwa wata budurwa ce wadda baza ta haura shekarun Najmeer ba, iya ƙarfinsa yake zuba mata iccen da ke hannunsa, a ɗayan hanun kuwa kwalbar giya ce ya yi mankass, cikin mugun ɓacin rai Najmeer ta ɗauki wani tiren da ke gefe a ƙasa ta buga masa, ai kuwa ya saki ƙara tare da zubewa ƙasa a sume, budurwar na ganin haka ta tashi da sauri ta nufi Najmeer tana mai rungumeta, duk da cewar Najmeer na iya jiyo warin jikin yarinyar ama hakan be hanata rungumeta ba, duk tausayinta ya kama ta, a hankali Najmeer ta janye jikinta tana faɗin "Zo mu shiga ɓangarena kafin ya tashi" Bayanta matashiyar ta bi har parlour, sai da Najmeer ta haɗa mata ruwan wanka wanda ta zuba turarrukan ƙamshi sosai, sannan ta ce ta shiga ta watsa ruwa, cike da murna matashiyar ta shige toilet dan rabonta da wanka yau sati ɗaya kenan. Ta jima a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul ɗin da Najmeer ta miƙa mata, cike da mamaki Najmeer ke kallonta a ranta take faɗin, wai dama fara ce kuma haka take da kyau, matashiyar ce ta katse mata zancen zucin da faɗin "Thank you so much and i can't forget the way u help me from that wicked Man" Ƙura mata ido Najmeer ta yi dan bata san abin da ta ce ba, lura da hakan ne ya sa matashiyar zama a hankali tare da dafa Najmeer ta ce "Can you speak english?" Kasancewar Najmeer ta san wannan kalmar ne ya sa ta girgiza kai alamun bata jin turanci, murmushi matashiyar ta yi a karo na farko kafin ta ce "Da farko sunana Meera, ni ƴar garin Maiduguri ce, iyayena sun rasu dalilin wasu ƴan ta'adda da suka shigo garin, duk a cikin Family na babu wanda suka bari sun kashe mun kowa, ni ɗaya ce na rayu sannan na baro garinmu na dawo nan garin da zama, a lokacin da na shigo dubu ɗaya ce kawai ta rage mun kuma gashi dare ya yi, ina cikin tafiya na haɗu da wannan bawan Allah me suna Maleek, daga nan ya ce zai taimaka mun idan har ina so, a lokacin ba wani wayo ne da ni ba yasa na amince masa, ya kawo ni wannan gidan wanda a ranar ya keta mun haddina, na yi kuka marar iyaka tare da nadamar rayuwa, tun daga ranar Maleek ya mayar da ni kamar matarsa, kuma haka zai je ya sha giyarsa ya dawo ya mun dukan tsiya, wasu lokutan a hospital nake tsintar kaina, yanzu maganar da nake miki na zama cikakkiyar Karuwa me zaman kanta, shekaruna sha bakwai ina cikin sha takwas, zan iya sanin ko ke wacece?" Meera ta faɗa tana kallon Najmeer da idanunta sun ciko da ƙwalla, sai da ta kai kusan mintuna uku kafin ta ɗago tana kallon Meera "An kira sallar isha, mu fara yin sallah kafin lokaci ya tafi" "No bana sallah wahala take mun, ke ki yi kawai" A mugun tsorace Najmeer ta ce "Sallar ce ke miki wahala?" Itama Meera a tsoracen ta kalli Najmeer jin yanda ta ɗaga murya, "Yes ita ce ke mun wahala, sai ranar da na ji ina ra'ayi nake yi" "Ya subhanallah" Cewar Najmeer tana zama kusa da Meera tare da kama hannunta "Meera kin san hukuncin wanda ke wasa da sallah kuwa?" Girgiza kai Meera ta yi alamun bata saniba. Cike da basira Najmeer ta cigaba da faɗin "Meera a matsayinki na mace kuma wadda ki ke fatar Allah ya shiryi rayuwarki domin ki gina sabuwar rayuwa be dace ki kasance marar bautawa Allah ba, gara ma a ce bakya sallar gaba ɗaya da a ce kina wasa da ita, saboda wutar me wasa da sallah ta fi azaba fiye da wanda baya yi gaba ɗaya, kamar masu haɗa sallar asuba da ƙarfe biyu har ma sallar ƙarfe huɗu, Meera ina son ki sani cewa sallar da za ki rinƙa yi kina faɗawa Allah damuwarki zai iya silar shiriyarki, dan Allah ki yi mun alƙwarin baza ki ƙara wasa da sallah ba, saboda bana son ki tashi ranar lahira cikin mutanen da za'a saka su a wutar da ta fi kowacce azaba". Jikin Meera ne ya yi sanyi jin kalaman Najmeer, sai a lokacin take fara nadamar rashin yin ibadah, kuma take ganin wasu matsalolinta sun haɗa da rashin bautawa Allah, saboda Ubangiji yana rabuwa da duk wanda ya daina saka shi a lamuransa. "Na gode sosai kuma na yi miki alƙwarin daga yau zan cigaba da ibada, amma ba ki faɗa mun sunanki ba" "Sunana Najmeer, ki tashi ki yi alwala bari na fito miki da hijab" Miƙewa ta yi tana mai buɗe Wadrop ta ciro ƙaton hijab, ita kuwa Meera ta shiga toilet dan ta yi alwala. Bayan ta fito ne Najmeer ta shiga ta sake canja alwala itama. A tare suka kabbarta sallah, abin tashin hankalin shine gaba ɗaya Meera bata iya sallah ba, bayan sun gama Najmeer ta yi mata gyara sosai kafin suka cigaba da fira, duk iya wayon Meera dan ta san labarin Najmeer amma ta kasa samun dama, domin daga ta kawo zancen Najmeer ke saurin canja wani topic, a haka har tara na dare ya buga, Najmeer ce ta ce "Meera akwai shagon da ake sayar da kayan abinci a kusa haka?" "Yes akwai da yawa ma, akwai abin da ki ke so ne?" Miƙewa tsaye Najmeer ta yi tana faɗin "Eh mu tafi ki raka ni" Itama miƙewa Meera ta yi tana nufar ƙofa, wani kallo Najmeer ta yi mata me kama da ina zuwa haka, sai kuma ta cire hijab ɗin da ke jikinta dama daga ita sai wata riga ta roba daidai gwuiwoyinta, riga ce me masifar kyau da ɗaukar ido red colour, gashin kanta ta sake shi ta baya tana mai gyara zaman rigar, duk abin da take Meera ta zuba mata ido daga bakin ƙofa tana kallon ikon Allah, ita kuwa Najmeer ta nufi ɗan ƙaramin trolynta ta ciro wando da riga masu kyau da tsada ta jefawa Meera, "Ki saka wannan dan baza ki fita da ni a cikin wannan ƙaton hijab ba. Baki sake Meera ke kallon Najmeer, a haka har ta gama saka kayan, wando ne da kaɗan ya wuce gwuiwar Meera, sai rigar me gajeren hannu, kayan sun bala'in amsarta kasancewarta fara. Ai Meera bata sake tsinkewa da lamarin Najmeer ba sai da taga sun fito a haka, a tsakar gida suka sami Maleek zaune yana dafe kansa, bishi-bishi yake kallonsu har suka fice daga gidan. Tun da suka fara tafiya mutanen unguwar ke kallonsu, musamman Najmeer kamar zasu haɗiyeta da kallo. A wani haɗaɗɗen shago suka shiga me girma, ba ɓata lokaci suka zazzaɓi kayan abinci masu yawa da tsada, duk abubuwan buƙata sai da suka ɗauka, a wajen shagon suka kira almajirai dan su kwashe musu kayan, lokacin da suka shigo goma daidai ta buga na dare, kuma lokaci ɗaya alarm ɗin wayarta ya fara ƙara. Cikin gaggawa ta sallami almajiran sannan ta faɗa bayi, wani sabon wanka ta kuma yi sosai ta haɗe cikin wando da riga masu rikitattun kyau, duk da cewar Meera mace ce amma sai da ta kasa ɗauke idanunta daga kallon Najmeer, wandon kuwa da kaɗan ya wuce mazaunanta, a ƙasansa akwai rabaja sai rigar marar hannu me tsage ta baya, Najmeer na murmushi ta miƙowa Meera wasu kayan, itama cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya tana faɗin "Ina zamu je ne? gaskiya lamarinki abun tsoro da mamaki ne" "Hmmm Meera kenan, a sannu za ki san ko wacece ni, inda zamu je kuwa be wuce Clup ba, na kwana biyu ban tafi ba kuma na san Guys ɗina sun yi missing ɗina sosai" Ihu Meera ta saki dan murna tana faɗin "Ki ce kema ƴar harka ce, gaskiya na ji daɗin haɗuwa da ke, nima ina zuwa Clup amma wanne ki ke zuwa?" Meera ta faɗa tana fari da ido. "Secret Clup idan muka tafi za ki gani" Daga haka Najmeer bata kuma cewa komi ba har suka gama shirinsu, sosai ta yi ɓarin turare a jikinta, ita kanta ta san bata taɓa yin kyau idan zata je Clup kamar yau ba. Wasu arnayen takalma suka saka masu tsayi da kyau, Meera ce ta fara fita kafin Najmeer, sai da ta tabbatar ta rufe ko'ina na part ɗinta kafin ta saka keys ɗin a handbag tana mai nufar inda take jiyo surutun Maleek da Meera, da sauri ta ƙaraso ta shiga tsakaninsu "Lafiya dai Malan? wallahi kar hannunka ya yi izgilin taɓa jikinta idan ba haka ba sai na wulaƙantaka a garinnan" Najmeer ta faɗa a tsawace. Gaba ɗaya Maleek be san abin da take faɗa ba, dan shi kyawunta da kyawun dirinta ne ya tafi da imaninsa har ta gama masifa ta ja hannun Meera suka fice daga gidan, da gudu ya bi bayansu yana kiran sunan Meera. Shan gabansu ya yi a fusace ya damƙo gashin kan Meera tare da matsewa "Ke dan ubanki ina zuwa? har ni wannan Aljanar ƙawar taki zata gayawa munanan kalamai" Cike da jin zafi Meera ta ƙwalla ƙara tana bashi haƙuri, wani gigitaccen marin da Najmeer ta watsa masa ne yasa shi sakin gashin a ruɗe tare da duba wanda ya mare shi, sai da ya kai mintuna biyu a haka kafin kunnensa ya dawo daidai, "Uban waye ya mareni? na ce wani ɗan hegiyar ne ya gallaramin mari" Yanda yake ɗaga murya da zage-zage ne ya sa mutane taruwa gurin ana kallonsu, cike da gadara Najmeer ta kama hannun Meera tana nuna shi da yatsa "Wannan ya zama na ƙarshe da zaka kai hannunka jikin Ƙawata, idan kuwa ka ƙara jahilin gangancinnan sai dai Uwarka ta haifi wani amma ba kai ba" Ta ƙarasa maganar tana jan hannun Meera suka bar gurin, ihu da shewar mutane ne ta cika gurin, dan Samari da dama sun kamu da son Najmeer musamman yanda ta fara takawa Maleek burki a Uguwar kasancewar ya hana kowa shan iska, "Ku kuma Uwar waye ku kewa shewa anan?" Ya faɗa yana rarumar abun da zai dake su, da gudu kowa ya watse dan tsoron kar ya illata su. A Restaurant suka fara zuwa dan gaba ɗayansu yunwa suke ji, a lokacin da suka shiga babu kowa sai masu sayar da abincin, dan haka suka yi Oder Julof na indomie wadda ta sha ƙwai, sai naman kaza da kuma drinks, rabon da Meera ta ci naman Kaza har ta mance, ai kuwa ta zage damtse ta ci har ta ture, Najmeer dai sai kallonta take tana murmushi. Ƙarfe sha ɗaya ta yi musu ne a bakin Clup ɗin, tun daga waje ka ke jin ƙarar sauti na tashi, tabbas gurin ya tsaru wanda ƙarya ne kaga ɗiyan talakawa a nan, ido Meera ta waro da mugun firgici bakinta na rawa take nuna sunan Clup ɗin "Soultan Clup......." "Yes Soultan Clup, wani abun ne ya faru?". Najmeer ta tambaya. Meera da duka ta daburce ta ce "Kin san waye Sultan kuwa, kin san waye Ubansa, kin san waye shi kuwa?" Meera ta jero mata duk wannan tambayoyin a lokaci ɗaya tana ƙoƙarin komawa da baya, a fusace Najmeer ta damƙo hannunta a lokacin idanunta sun koma dark blue, gaba ɗaya farin idonta ya ɓace, cikin yarda da kai ce "Meera wannan ba shine lokaci na farko da na taɓa zuwa ba, asalima abokin me Clup ɗin muna shiri da shi sosai, me Clup ɗin ne kawai ban taɓa gani ba kuma ban san shi ba" Ajiyar zuciya Meera ta sauke tana mai kawai da kai gefe ganin yanda idon Najmeer ya canja, ba tare da fargabar komi ba suka shige, cike da ƙasaita Najmeer ke taka steps kamar yanda ta saba. Ba ƙaramin tsaruwa Clup ɗin ya yi ba, daga ƙofar shiga wasu manya manyan majiya ƙarfi ne suka nufo su, amma suna ganin Najmeer suka basu hanya cikin girmamawa har ma ɗayan na faɗin "Allah ya ja da ran Shalelen Alhazawa, ke ba sa'arsu ba ce ta manya ce, ke ɗin tauraruwa ce me haskaka duk wanda ya yi arba da ke" Jin yanda ake zuba mata kirari ne ya ƙara ba Meera mamaki, Najmeer kuwa ta ciro kuɗaɗe ƴan dubu-dubu ta fara zuba musu, nan fa kirari ya ƙara yawa har mutanen da ke ciki suna jin yanda ake koɗata, hakan ya ƙara tabbatar musu cewa Shalele ta shigo, cikin sauri Majeed ya fito wanjen dan ganema idanunsa, ai kuwa ya yi arba da ita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙaraso suka rungume juna tare da kashe hannu, "Hi Shalele, gaskiya mun yi kewa sosai, ni na tabbata za ki shigo yau shiyasa ma na yiwa Oga na arbishir da samunki" Wani irin fari da ido ta yi tana mai faɗin "Waye kuma wannan da ba zai iya zuwa da kansa ba har sai ya turo ka?" "Friend ɗina ne kuma shine me wannan Clup ɗin". "Friend ɗinka fa ka ce? kaga na yi kama da wadda zata yi harka da low class masu irin shekarunka......" Saurin rufe mata baki Majeed ya yi "Hold on Shalele dan Allah kar ki jaza mana, kin san waye Sultan kuwa? wallahi ko ba ki amince da shi ba zai iya sa ki dole kuma babu abin da za'a iya a garinnan" Ran Najmeer ne ya mugun ɓaci jin abin da Majeed ke faɗa "Toh wallahi banga wanda ya isa ya sa na tarbi abokin naka ba, idan kuwa akwai shi sai ka kawo na gani" Ta ƙarasa maganar tana shigewa daga ciki. Jikin Meera na rawa ta kalli Majeed "Dan Allah ina Sultan ɗin ne? nikam zan koma gida dan baza ta jaza mun ba" Ƴar dariya Majeed ya yi ganin tsananin tsoron Sultan kan fuskar Meera. "Ai be ƙaraso ba, a tare muka fito amma ya tsaya wani gurin, na tabbata duk inda yake yana kan hanya a yanzu......" Majeed be gama rufe baki ba gate Man ya wangame gate. Wata farar Mota ce a gaba bugagga wadda sai ƴaƴan manya za su iya shigarta, a bayanta motoci tara ne masu jahilin kyau, jiniya kawai ke tashi har suka gama shigowa daga ciki, duk mutanen da ke cikin Clup ɗin fitowa suka yi dan sun san cewa tabbas Sultan ne, kuma idan har ya zo gurin kowa fita yake sai ya fara shiga kafin mutane su shigo daga baya. Sai da aka gama fitowa amma banda Najmeer wadda ke zaune kan wata arniyar kujera me kafurin kyau da tsada wadda aka aje domin zuwan Sultan. A hankali Meera ta taɓa Majeed tana faɗin "Wai ina Najmeer ɗin ne? nifa banga fitowarta ba" Zaro ido Majeed ya yi ganin da gaske Najmeer bata fito ba, daidai lokacin da Driver ya buɗewa Sultan ƙofar mota, daga nesa kana hangen walƙiyar da sarƙar Gold da ke wuyansa ke yi, kunnensa kuwa ƴan kunne ne da ake mannawa shima na Gold, gashin kansa a gyare tamkar baza a mutu ba, wasu rikitattun kaya ne jikinsa masu kafurin kyau, wando ne da kaɗan ya wuce gwuiwarsa ya zazzalo da wandon ta ƙasan mazaunansa, daga ciki kuwa guntun wando ne me kyau da tsada, rigarsa maroon ce me ɗauke da zanen fuskarsa, a gaban rigar an rubura Soultan Chif, lokaci ɗaya turarukkan jikinsa ya fara baje harabar Clup ɗin. Takalman ƙafarsa kuwa sawu ciki Black na gaban kwatance, sai da ya ɗauki mintuna uku yana ƙarewa mutanen da ke gurin kallo kafin ya fara tafiya, ai kuwa kowa ya ɗauki sowa da tafi ana masa kirari, ɗaga musu hannu ya yi alamun ya isa, nan take kowa ya yi tsitttt, daga ɗan nesa ya hangi Majeed da Meera sai da ya ƙarewa Meera kallo kafin ya ja dogon tsaki a ransa yake faɗin, ashe wannan jahilar zai kawo mun na zata wata zazzafa ce, kai tsaye ya nufi gurin da suke tsaye shima Majeed ya nufo sa yana miƙa masa hannu suka tafa, kallon wulaƙanci ya yiwa Meera wanda hakan ya sa ta ji fistari na neman suɓuce mata, tun da take bata taɓa ganinsa ido da ita ba sai yau, gaba ɗaya kyawunsa da kwarjinsa sun gigitata, cikin ƙasaita kamar me ciyon magana ya ce "Wannan ce Karuwar.......?" Muryar Majeed cike da rashin gaskiya ya ce "No...no....no...haba ba ita ba ce" "To ina wadda ka ce mun?" Sultan ya faɗa yana ɓata fuska gami da shan ƙamshi. "Ai tana daga ciki" Cewar Majeed a kiɗime. Wata irin tsawa Sultan ya daka wadda ta sa kowa tsorata a gurin, idanunsa sun gama rinewa jijiyon kansa kuwa sun yi ruɗu-ruɗu, bakinsa na rawa ya ce "Uban waye ya ce mata ana shiga daga ciki ba tare da na fara shiga ba?" Haƙuri Majeed ya fara bashi wanda hakan ya sa Meera cewa "Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mata......." Ido Sultan ya waro jin yana magana Meera ta saka masa baki, ai kuwa ya ɗaga hannu da niyar sharara mata mari, kamar daga sama ya ji an damƙe hannun daga bayansa, wanda hakan ne ya hana shi samun damar marin Meera, kamar wani me ciyon jiki haka ya fara juyawa dan ganin wani me tsautsayin ne ya dakatar da shi daga abin da yake son aikata. *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATON* P. 3 A tsaye take cikin gadara da nuna isa. Lokacin da ya sauke rikitattun idanuwansa kan kyakykyawar fuskarta ne ya tsaya chakkkkk na tsawon mintuna uku, wanda hakan ya bawa gurin damar yin tsittttt kamar an ɗauke ruwan sama, wani mugun kallo Najmeer ta watsa masa tana mai jefar da hannunsa gefe, cikin muryarta me daɗin sauraro ta maida kallonta kan Meera tana faɗin "Me ki ka yiwa wannan yaron yake son ya ɗaga ƙazamin hannunsa kan fuskarki..." Wani irin gummmm.....kunnuwan Sultan suka yi dan ji yake kamar a mafarki ake yarfa masa kalamannan. Ba Meera ba hatta mutanen da ke gurin jikinsu rawa yake dan babu wanda ya san abin da zai biyo baya, idanunsa ne suka rine jajir gashin jikinsa sun mimmiƙe, hatta ƙafarsa rawa take, ƙirjinsa kuwa ya ƙara tashi wanda har kana hangowa daga wajen rigarsa. A tsawace Najmeer ta kuma cewa "Magana nake miki, wanne laifin ki ka masa?" Bakin Meera na rawa ta ce "Dama.....dama....dama..haƙuri na basa saboda kin masa laifi" "Wacece ta masa laifin"? Najmeer ta kuma tambaya. Majeed ne ya yi saurin katse zancen da faɗin "Shalele please ki ba Sultan haƙuri wallahi akwai matsala..." Ɗaga masa hannu Sultan ya yi kafin ya ɗago idanuwansa da ko garwashin wuta ba zai nuna masa ja ba, "Wacece wannan.....?" Ya faɗa yana jan mugun numfashi, Majeed ne ya kuma cewa "Ita ce wadda na faɗa maka" Tun kafin Majeed ya gama rufe baki Sultan ya damƙo gashin kanta da tsananin ƙarfi, tun da Najmeer take babu wani mahaluƙin namijin da ya taɓa damƙe gashin kanta da niyar muzgunawa, daidai saitin fusarsa ya ɗago tata fuskar har suna jin saukar numfashin juna, duk da cewar raɗaɗi da azaba na shigar Najmeer amma hakan be sa ta nuna alamun tsorata ba, a hankali Sultal ke kallon kwayar idanunta ganin gaba ɗaya blue ne babu ɗigon fari ko kaɗan, ya tsorata matuƙa amma hakan be hana shi faɗin "Ke ƴar gidan Uban waye? da har za ki dakatar da ni daga yanke hukunci" Shuru Najmeer ta masa dan ganin take ya yi yaro sosai ta tsaya magana me tsayi da shi kamar haka. A fusace ya kuma cewa "Na ce ke ƴar gidan Uban waye" Kamar wadda aka cilla haka Najmeer ta mugun daka tsalle sama tana mai ture shi daga jikinta, lokacin har mutane sun fara guduwa saboda abin ya fi ƙarfin ganinsu, cikin mugun zuciya ta ɗauki wata kwalbar giya da aka aje gurin ta damɓara masa a kai, ji ka ke tassss, ai kuwa tuni mutane sun watse da gudu ganin an bugawa Sultan kwalba. Jiri na ɗibarsa jini na zuba ya dafe kansa, masu tsaronsa ne suka rugo da gudu sai Majeed da ya kama shi ta baya dan kar ya faɗi, Najmeer na ganin haka ta kama hannun Meera suka fice daga gurin da matsanancin gudu. Dirrect hospital aka nufa da shi, da farko likitocin basu so karɓarsa ba, dan sun ce sai an kira police, sai da Majeed ya faɗa musu ko waye Mahaifin Sultan kafin aka shiga da shi cikin gaggawa. Ba wani ɓata lokaci aka tsayar da jinin tare da saka masa bandeji da kuma allura. Duk abin da ake Sultan na kallo amma bakinsa ya kasa furta kalma ɗaya, tun da Allah ya haliccesa be taɓa jin tsanar wani mahaluƙi kamar yanda yake jin tsanar Najmeer ba, daga zaran ya tuno da tozarcin da ta masa gaban mutane sai ya ji duk kunya ta kama shi, wai mace ce ta yi masa wannan haukar macen ma ƙaramar yarinya wadda ko kama ƙafar shekarunsa bata yi ba. Wani irin mugun naushi ya kai wa glass Cup ɗin da ke saman ɗan ƙaramin table nan take ya tarwatse hannunsa ya fara fitar da jini, Majeed da shigowarsa kenan ya yi aurin ƙarasawa yana kama hannunsa "Sultan meye haka? jini ne ke zuba fa" A mugun tsawace Sultan ya dakawa Majeed tsawa "An so what? don't try to calm me down idan har ina cikin fushi" Ya faɗa yana ficewa daga room ɗin. A harabar hospital ya samu motocinsa cikin ɓacin rai ya shige yana mai bada umarnin su koma gida, ba ɓata lokaci motocin suka nufi hanyar G R A cikin matsanancin gudu. Kasancewar gate uku ne ya sa suka shige gate ɗin bayan gidan wanda zaka iya shiga ba tare da kowa ya sani ba, a lokacin sha biyun dare har ta wuce ana neman ƙarfe ɗaya, A miskilance ya shigo parlourn ya mance cewar babu wanda ya san da fitar sa, steps ɗin ya fara takawa cikin iya tafiya me ɗaukar hankali "Sultan where are you coming from?" Ya tsinkayo muryar Dad, ba tare da Sultan ya ce uffan ba ya juyo yana kallon Dad ɗin nasa da ke zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ke parlourn da alama yaron nasa yake jira. "Don't let me repeat myself, and me ya sameka har aka saka maka wannan bandejin?" Dad ya kuma magana yana miƙewa tsaye, Junaid da ke saukowa daga steps ne ya ce "Dad a tare muke na riga shi dawowa ne kawai" Murmushi Dad ya yi kafin ya ce "Ina ku ka tafi cikin wannan daren?" Shi dai Sultan ɗan kallo ya zama jin yayan nasa na ƙoƙarin kare shi, har da yiwa Dad ƙarya abin da be saba yi ba. "Ohh dama Sultan ne ya faɗi a steps shine muka tafi Hospital" Junaid ya faɗa yana watsawa Sultan mugun kallo. "Alright Allah ya ƙara tsare gaba, ai shi wanda nake tambaya ma ya mayar da ni banza kamar ba da shi nake ba, na rasa sanin yaushe Sultan zai daina wannan shegen miskilancin nasa, wani lokacin kamar ya fika wani lokacin kamar ka fi shi, Allah dai ya shirya mun ku gaba ɗaya" Junaid ne ya amsa da ameen, Dad kuwa ya nufi room ɗinsa. Ba tare da Sultan ya kuma kallon inda Junaid ke tsaye ba ya nufi nasa ɗakin yana mai buga ƙofar da ƙarfin tsiya. Toilet ya nufa tare da sakarwa jikinsa ruwa, bandejin da ke kansa kuwa ya fizge shi da ƙarfi ya cilla shi gefe, ya jima a hakan kafin ya fito jiki a sanyaye, jin wayarsa ta ɗauki ƙara ne ya sa shi matsawa yana duba me kiran nasa. Majeed ya gani a rubuce kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya yi pearking a kasalance ya ce "Yes Majeed what do you want?" "Nothing Guy ya jikin naka?" "Mtsss is that why you call me?" Sultan ya faɗa cikin ɗaga murya. "No calm down Guy Allah ya ba ka haƙuri good night" "Hold on Majeed i want to ask you something" "Ina jinka" Cewar Majeed zuciyarsa na bugawa dan ya san maganar me zai masa. Sai da Sultan ya ɗauki mintuna biyu yana nazari kafin ya ce "Ina buƙatar sanin ko wacece ita, kuma waye ubanta a garinnan, a bincika min sana'ar da uban nata yake yi nan da zuwa gobe" Majeed ne ya ce "Wallahi yana da wahala a san gidansu, ni kaina ban taɓa jin wanda ya ce mun ya san hanyar gidansu ba ma balle gidan nasu, but i'll try my best" "Good....." Sultan ya faɗa yana kashe wayar. Sallamar Junaid ne ya sa shi maida kallonsa kan ƙofar, da alama ya ji wayar da ƙanin nasa ke yi. Sanye yake cikin haɗaɗɗun kayan bacci milk masu shegen kyau, ƙamshin turarensa ne ya mamaye ɗakin har ya zauna gefen bed ɗin yana mai ƙurawa ƙanin nasa ido, kamar yanda Junaid ɗin be ce uffan ba haka Sultan ɗin kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kai. Gyaran murya Junaid ya yi kafin ya dafa kafaɗar Sultan cikin kulawa ya ce "Wacece ita Sultan?" A ɗan tsorace Sultan ya kalli yayan nasa, sai kuma ya basar "Wa ka ke nufi Bro" "Wadda ta fasa maka kai nake nufi" Junaid ya kuma faɗa yana haɗe fuska alamun babu wasa tattare da shi. Shima Sultan ɗin haɗe fuskar ya yi dan yanzu ne ma yake jin mugun baƙin cikin abin da Najmeer ta masa, da ƙarfin tsiya ya miƙe ya fara dukan ginar ɗakin da hannayensa yana faɗin "She have to die, wallahi sai na kashe ta kuma babu abin da zai faru a garinnan" Cikin sauri Junaid ya riƙe shi tare da rungume sa a jikinsa yana bubbuga bayansa a hankali, hannun shi ya kama suka isa gun Frigde ɗin da ke ɗakin, fuskar Junaid ɗauke da murmushinsa me matuƙar ƙara masa kyau ya zubawa Sultan ruwa me sanyi tare da miƙa masa, cikin hanzari ya karɓa ya kafa a baki, sai da ya shanye tasss sannan ya jefar da glass Cup ɗin nan take ya tarwatse. Hannunsa Junaid ya kuma kamawa ya zaunar da shi kan bed, ɗan ƙaramin Box ɗin da ke kan table ya ɗauko ya fara gyara masa inda jini ke zuba a hannunsa da kuma gefen goshinsa, bandeji ya ɗaura masa yana shafa gashin kansa cikin so da ƙauna ya ce "Relax Sultan ka samu ka kwanta ko jikin naka zai yi sauƙi" Ba musu Sultan ya kwanta yana rufa blanket a jikinsa, ƙara gyara masa blanket ɗin Junaid ya yi kafin ya ce "Kar ka mance da addu'a, sannan ka cire zancen kisan kan da ka yi magana dan idan har ka kashe rai babu wanda zai barka, dan ko Dad zai yi duk yanda zai yi domin a ƙwatar mata haƙƙinta" Junaid ya ƙarasa maganar yana mai ficewa daga ɗakin. Gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idanun Sultan, daga zaran ya buɗe ido sai ya rinƙa ganin fuskar Najmeer, abin da ya ƙara harzuƙa shi kenan. Kamar yanda ya ga rana haka yaga dare, sai tara na safiya ya tashi bacci duk jikinsa na zafi kansa kuwa kamar zai rabe gida biyu, a haka ya faɗa toilet ya watso ruwa gamida da alwala ya fito, sallar ma a zaune ya yi a cewarsa ba zai iya duƙawa da miƙewa ba. Yana gamawa ya haɗa ruwan tea ya sha sannan ya sha maganin ciyon kai. Da sallama Mom ta shigo sanye cikin less me tsadar gaske fuskarta ɗauke da damuwa ta ƙaraso daga ciki, Sultan na ganinta ya miƙe daga kan sofa tare da hugging nata "Hi Mom how far" "Not fine Love ɗazu Dad ɗinka ke faɗa min abin da ya faru, ya jikin naka" "Da sauƙi Mom ba wani ciyon ba ne" "Alright ka same mu a dianing kai mike jira" Komawa ya yi ya zauna yana faɗin "No need yanzu na gama shan tea hakan ma is okay" Murmushi Mom ta yi "Okay ka samu Dad ɗinka akwai maganar da yake son ya yi muku" "Okay" Sultan ya faɗa yana mai latsa wayarsa. Sai da ya gama shan ƙamshinsa kafin ya nufi part ɗin Dad dan ya san a can suke karin kumallo, sosai part ɗin ya masifar haɗuwa dan shine ɓangaren da ya fi kowanne ɓangare kyau a faɗin gidan, hatta ƙofar shiga da Gold aka yi shi, kuɗin kujerun da ke part ɗin ya isheka gina ƙaton gida me rai da lafiya, a dianing ya same su har Junaid ɗin, yana sanye cikin ƙananan kaya wando black sai rigar white me taushi, fuskarsa ta ƙara kyau da kwarjini gashin kansa kuwa ya haɗe sosai, da sallama Sultan ya ƙaraso tare da zama yana gaishe da Dad, "Lafiya ƙalau Sultan ya ƙarfin jikin?" "Alhamdulillah na ji dama" Masha Allah suka amsa gaba ɗaya kafin kowanne ya fuskanci abincin da ke gabansa banda Sultan da ya nuna baya ra'ayi, Junaid kuwa mamakin rashin gaisuwar da Sultan be masa ba yake, amma sai ya share. Bayan sun gama ne suka ɗan taɓa fira irinta Family kafin Dad ya ce "Ina son ku bani hankalinku sosai a nan" Kallonsa suka yi tare da mayar da duk wata natsuwarsu dan jin abin da zai ce, gyaran murya Dad ya yi yana faɗin "Junaid kasancewar ku biyu Allah ya mallaka mun kuma kai ne babban ɗana wanda nake tsammanin kafi Sultan sanin ya kamata da kuma shekaru, hakan ya sa na zuba maka ido dan jiran matar da zaka kawo a matsayin wadda zaka aura amma har yanzu babu labari, ka duba yanzu duk wani abun da ka ke buƙata a rayuwa ka samu bayan haka kana aikin ka, ya kamata ka fito da wacce zaka aura tun kafin ni na zaɓa maka" Numfashi Dad ya sauke kafin ya maida kallonsa kan Sultan "Kai kuma a ranar da ka dawo ka ke faɗa mun zancen ka samu matar aure a London, wanda na nuna maka ban amince ba, to na zauna na yi nazari sosai idan har ka yarda da tarbiyyarta sai ka fito da ita a ɗaura muku aure, amma fa duk abin da ya biyo baya ka kuka da kanka" Dad ya ƙarasa maganar yana mai kallon Mom da itama shi ɗin take kallo, sunkuyar da kai Junaid ya yi kafin ya ce "Dad ayi mun afwa dan wallahi bana da kowa a halin yanzu a ɗan bani lokaci" "Lokaci kamar ya? zaka ce mun duk matan da ke sonka babu wacce ka ke ra'ayi, shekaran jiya fa har gida wata ta biyo ka amma ka ke faɗa mun zancen ba ka da zaɓi" "Am sorry Dad tarbiyyarsu ce bata mun ba, ina son na kawo macen da ta san darajar kanta, wallahi Dad dukkaninsu basa da kunya kuma babu me saka hijab wani lokacin ma a haka suke fita ba mayafi, kowanne namiji na son ya auri macen da ke suturta jikinta, duk wannan nuna tsiraicin da suke baya burgeni asalima ɗaukar mahaukata nake yi musu" Junaid ya ƙarasa maganar cikin gajiya da dogon bayanin da ya yi, daga Dad sai Mom ne kawai ke samun damar yin doguwar magana da Junaid amma ko a Hospital baya tsayawa bayani sai dai ya saka ayi. Sultan da ke sauraronsu ne ya ce "Thank you so much Dad, insha Allah zan kira Maleeka anjima na sanar mata wannan babban albishir" Ɗan taɓe baki Dad ya yi "Bayan haka zaka fara aiki ranar Monday a kanfanina, dama karatu ne kuma ka kammala". "Yes Dad nima na yi tunanin hakan" Sultan ya faɗa cike da farinciki, dan shi zancen aurensa da Maleeka ne ya saka shi murna, tun da yake be taɓa haɗuwa da macen da yake jin daɗin harka da ita ba kamar Maleeka, kuma shine namiji na farko da ya fara kwanciya da ita shiyasa yake ƙara daraja ta. Mom da ke murmushi ne ta ce "Yawwa ai yanzu sai kowa ya fito da matar da yake son aura, kai Junaid ka tabbata ka nemo mata nan da wata ɗaya idan ba haka ba zan haɗaka da Humaira ƴar gidan ƙawata dan naga alamun tana masifar sonka kuma ita ba kalar matan banza ba ce" Ɗan sosa kai Nunaid ya yi "A dai ƙara haƙuri Mom zan nemo da yardar Allah amma wata ɗaya kamar ya yi sauri" Dad ne ya ce "Ai sati ɗaya ma nake so ka nemo mata" Dariya suka yi gaba ɗayansu jin yanda Dad ya yi maganar. ............................. Najmeer kuwa tun da suka shiga gida ba wanda ya leƙo waje har garin Allah ya waye, bayan sun gama karyawa ne suka baje a tsakiyar parlour suna firar abin da ya faru daren jiya, Meera ta kalli Najmeer da ke game a wayarta ta ce "Kai amma ke hatsabibiya ce, yanzu Sultan ki ka wulaƙanta haka? ai ni jiya na rasa bakin magana shiyasa ki ka ga muna dawowa na kwanta dan a tsorace nake" Murmushi Najmeer ta saki wanda ya ƙarawa fuskarta kyau "Ke Meera im banda abinki waye zai taɓa mun ke ya zauna lafiya, daga jiya zuwa yau na yi saba da ke sosai, ina jinki kamar ƴar uwata ta jini" "Hmmm nima haka na ɗaukeki, Allah ya bamu ikon riƙewa juna amana" "Ameen ya Allah wai ina Maleek ne? rabon da na saka shi a ido tun jiya" Cewar Najmeer tana ƙunshe dariyarta. Dogon tsaki Meera ta ja har tana rufe ido "Allah ya tsare ai ni yanzu ganin kaina nake babbar celebrity na wuce sanin Maleek, anjima zan kwaso kayana dan ba zan iya kwanciya a part ɗinsa ba" Dariyar da Najmeer ke riƙewa ce ta ƙwace mata "Wai da gaske ki ke? Maleek ɗin naki" "Mtsss zan zageki fa Najmeer wallahi ki fita idona, salon na koma ya cigaba da dukana" Cike da jin haushi Najmeer ta miƙe zaune tana dafa kafaɗar Meera ta jijjigata da ƙarfin tsiya "Ashe ba ki san abin da ki ke ba, kar ki mance ke macece wadda zata iya shiga ko'ina, kar ki taɓa barin wani kafurin namiji ya rinƙa dukanki a banza a wofi, ke ɗin macece wadda take da ikon kanta, idan har kina son zama da ni sai kin koyi yanda ake dakawa maza gumba a hannu, sai kin zama jajirtacciya marar tsoro, ni da ki ke gani nan......." Numfashi Najmeer ta ja kafin ta cigaba da faɗin "Bana shakkun kowanne ɗan iskan, ni kaina tsoron kaina nake, shiyasa na nunawa wancan yaron cewar iskanci ma guri ya samu" Ta ƙarasa maganar tana mai komawa ta kwanta. Sosai maganganunta suka shigi Meera, ai kuwa ta miƙe zumburrrrrr ta fice waje, a harabar gida suka ci karo da Maleek wannan karon be sha komi ba, kallonta ya yi sama da ƙasa kafin ya ce "Ke gidan Uwar wa ki ka kwana? a jiya ma na yi mafarkin kin samu wata ƴar tujara wadda ta zabgan mari, sai da na farka nake ganin ashe ba gaskiya ba ne dan na san babu wata ƴar tashar da zata iya taɓa jikina" Cikin fusata Meera ta ɗaga hannu tare da saukewa Maleek maruka guda biyu tana nuna shi da yatsa ta ce "Kar ka sake kiran Ƙawata da waɗannnan mugayen kalaman, yanzu na daina tsoronka kuma zan kwashe kayana na bar maka gidan..." Maleek da ke riƙe da kuncensa ne ya duba gabas da yamma kudu da arewa dan ganin wanda ya mare sa amma bega kowa ba, cikin mamaki ya maida kallonsa kan Meera da ke tsaye a gabansa ta riƙe ƙugu "Hehehehe Meera...., shin kinga wanda ya mareni kuwa?" Cewar Maleek yana ƙara duba gefe da gefe, harara Meera ta galla masa kafin ta ce "Uwar wa zata mareka imba ni ba, ni ce nan na wanke ka da maru, kuma wannan kaɗan kenan idan ba ka fita daga rayuwata ba......." Ai tun kafin ta gama rufe baki Maleek ya ɗagata sama ya damɓarata da ƙasa ji ka ke timmmmmm, wata irin muguwar ƙara Meera ta saki tana cije lips ɗinta a lokacin jini ya ɓalle daga ƙasanta, Maleek kuwa ya shiga dukanta hannu da ƙafa, ihunta ya sa Najmeer fitowa da gudu, abin da ta gani ne ya mugun fusata ta, ai kuwa ta koma cikin ɗaki da sauri ta rarumo Wuƙa me kaifi ta fito kamar wata ƴar daba, tana isa ta daka tsalle tare da ɗanewa bayan Maleek da ƙarfin tsiya da yanka masa Wuƙar a fuska, nan ta shiga yayyaka masa Wuƙar tana cije baki, Maleek da ya gama ficewa a hayyacinsa ne ya fara runtuma ihu da neman taimako, sai da Najmeer ta yi masa mugun rauni kafin ta yi jifa da Wuƙar gefe, cike da jarumta ta ɗaga Maleek sama da hannu biyu ta buga a ƙasa, ruwan cikinsa ta hau ta rinƙa gwara masa maru, "Yau sai na illataka Maleek ka kawo ƙarshen dukan mace, dan kawai ana zuba maka ido kana iskancin da ka ga dama, ai mu tun iskanci be san kansa ba mike yinsa" Marinsa ta cigaba da yi har sai da ya sume a gurin, Meera kam ta gama tsorata da lamarin Najmeer dan ta fara zargin anya Najmeer ba Namiji ba ce kuwa, dan bata taɓa ganin mace me ƙarfi kamarta ba" Ƙarasowa Najmeer ta yi da sauri ta sunkuci Meera zuwa hanyar waje, Allah ya sa suna fita suka samu adaidaita, a baya suka shiga Najmeer ta ce ya kaisu hospital ɗin da ke kusa. Suna isa aka shige da Meera dan sosai jini ke zuba, a kujerar da ke wajen Hospital ɗin ta zauna duk ta daburce, a ranta take faɗin anya ba kashe Meera Maleek ya yi ba. An ɗauki awa ɗaya ana duba Meera kafin wata Nurse ta fito duk ta yi zufa, dirrect gurin Najmeer ta nufa "Ke ce wadda ta kawo wannan matashiyar ko?" Da sauri Najmeer ta ce "Yes i'm the one, ya jikin nata ne?" "Ki biyo ni a office" Nurse ɗin ta faɗa tana yin gaba, bayanta Najmeer ta nufa a zuci take roƙon Allah ya sa ba mutuwa Meera ta yi ba. Bayan Nurse ɗin ta gama rubuce-rubcenta ne ta miƙawa Najmeer wata takaddar, "Am sorry to say ƴar uwarki ta yi ɓari, cikinta da ke wata ɗaya da kwana biyu ya zube saɓanin mugun faɗuwar da ta yi" Waro ido Najmeer ta yi "Ciki.......?" "Yes ciki ko bata da aure ne?" Da sauri Najmeer ta sauya yanayin fuskarta "No matar aure ce, thank you zamu iya tafiya gida ko akwai abin da ya rage" "No sai zuwa anjima saboda an saka mata ruwa yanzu, kuma tana buƙatar hutu sosai ina ganin ki koma gida anjima ki dawo" Godiya Najmeer ta yi kafin ta fito daga Hospital ɗin, sai yanzu take tuna cewar ai bata ba me adaidaita kuɗinsa ba, dube-dube ta fara amma babu kowa, dan haka ta nufi bakin titi ko zata samu abun hawa, tun da ta fara tafiya take jin kamar ana bin bayanta, daga zaran da juyo sai taga ba kowa har ta kawo bakin titi. Horn ɗin motar da aka yi ne ya sa ta ɗan janye gefe, da mamaki ta ga me motar ya tsaya a gabanta tare da sauke glass ɗin, wani Alhaji ne sanye cikin manya kaya masu tsadar gaske, Najmeer kam yanayin motar ne ya tafi da imaninta dan ba ƙaramin tsada zata yi ba. Kasancewar tana da jan aji ne ya sa ta matsa gaba, shima ya ƙara matsowa idan ta matsa sai ya matso, a tsawace ta ce "Haba Malan wai meye haka ne?" Kashe mata ido Alhajin ya yi kafin ya ciro wata ƙaramar bag da ke cikin motar ya fara watsa mata dollers "Ki kira ni da Alhaji me dala ba Malan ba, shigo daga ciki na shayar da ke ruwan dukiya da jin daɗin rayuwa". Ya ƙarasa maganar yana dariya, Najmeer kam wani mugun daɗi ne ya kamata dan so ɗaya ta taɓa riƙe dollers, ai kuwa ta haɗe fuska tana mai faɗin "Ka fito ka kwashe kuɗinka, ko ka ga na yi maka kama da me neman kuɗi, ka kalleni sama da ƙasa kaffff matanka babu me kyawuna ko kyawun diri na" Ƙara bushewa da dariya Alhajin ya yi kafin ya ce "Hakane maganarki ki shigo daga ciki zan kwashe kuɗin da kaina" Fitowa daga motar ya yi Najmeer kuwa ta zagaya ta shige bakinta ɗauke da addu'a. Sai da Alhajin ya kwashe kuɗin kafin ya shigo motar yana mai kallon Najmeer da ta haɗe fuska kamar wadda aka yiwa saƙon mutuwa "Amma kinga yanda fushi ke miki kyau kuwa? a gaskiya ke ta musamman ce" Murmushi Najmeer ta saki me ƙara mata kyau, a hankali ta ɗora hannunta saman ƙirjinsa tare da shafowa ta ce "Faɗa mun abin da ke tafe da kai" Bakin Alhajin na rawa ya ce "Ke nake muradi" "Ka samu Alhaji na Shalele, menene tukyuicina" "Faɗamun duk abin da ki ke so duniyar nan ko menene a yau ɗinnan za ki samu" Fari Najmeer ta yi da ido kafin ta maida kallonta gaban motar "Benz nake so wadda ake ya yi" Dariya Alhajin ya yi kafin ya ce "Wannan shine kawai abin da ki ke so? to zan haɗa miki da ƙaton gida me hawa biyu, ina son ki zamo mallakina Shalele" "Na riga da na zama taka ɗan Shalele" Cewar Najmeer tana murmushi. "Kinga muna yita magana ban sanar da ke wanene ni ba....." Saurin katse shi Najmeer ta yi da faɗin "Bana buƙatar sanin ko waye kai, abin da na sani shine kai nawa ne" Wani mugun daɗi ne ya kama Alhajin wanda sai washe baki yake. "Amma na ganki tsaye anan ina zuwa ne?" "Ohhh ina jiran Driver na ne, ya tafi karɓo mun wasu kuɗi a bayan layinnan" "So kina nufin a gidan iyayenki ki ke?" "Yes a gidan iyayena nake amma zan iya kwana a waje ba tare da Dad ɗina ya hana ni ba" "Wow i like your stile yanzu ina muka nufa" "Inda zaka tafi" Najmeer ta faɗa cike da gajiya da magana, lura da hakan ne ya sa Alhajin zube mata dollers ɗin a hannunta sannan ya tada motar tare da barin gurin. Sai da suka wuce unguwa uku kafin ya tsaya bakin wani danƙareren gida me masifar kyau da tsada, ba ƙaramin girgiza Najmeer kyawun gidan ya yi ba ta tabbata cewa gidan zai zuba kuɗi sosai. Ba tare da Alhajin ya fito ba ya ɗauki wayarsa yana mai danna wata number, bugu biyu aka ɗaga, shuru ya yi da alama ana gaida shi ne daga ɗayan ɓangaren kafin ya ce "Lafiya ƙalau ka fito mun da takaddun gidannan ina bakin gate" Ba tare da ya jira abin da za'a ce ba ya katse wayar, Najmeer dai ta zuba ido tana kallon ikon Allah. Ba jimawa wani Dattijo ya fito daga gidan ɗauke da takaddu a hannunsa, sai da suka ƙara gaisawa kafin ya miƙa masa saƙon, karɓa Alhajin ya yi sannan ya ce "Zaka iya tafiya gida yau already na yi kyauta da wannan gidan, amma zan kira ka next week sai na ga yanda za'ayi" Godiya Dattijon ya yi kafin ya bar gurin, Alhajin kuwa kallonsa ya maida kan Najmeer tare da miƙa mata Keys da takaddun gidan. Cike da ƙasaita ta karɓa tana mai sakin murmushi "Thank you my Alhaj" "Don't worry idan kina tare da ni za ki samu fiye da wannan, mu shiga daga ciki na nuna miki motarki da kuma yanayin gidan" A tare suka shiga cikin gidan, gida ne wanda ya amsa sunansa, gaba ɗaya tsarin ya tashi hankali, duk wani abin da ake buƙata na more rayuwa akwai shi, pearking space suka nufa inda wasu bagaggun mota ke baje kusan guda biyar, kallonta Alhajin ya kuma yi tare da kama hannunta "Ki zaɓi ra'ayinki cikin wannan" Najmeer duk ta gigice dan murna, da sauri ta ƙarasa gurin wata arniyar Benz me halakakken kyau maroon colour. Ai kuwa ya miƙa mata key ɗin motar, da gudu ta ƙaraso tana mai faɗawa jikinsa dan murna, "Thank you Alhaj and nice to meet you, yanzu lokacina ne da zan faranta maka fiye da yanda ka faranta mun" Najmeer ta faɗa tana janye jikinta cike da makirci. Sai da ta shiga motar ta zauna tsawon mintuna biyu kafin ta fito, "Ni zan koma gida saboda akwai aikin da ke gabana and na san yanzu haka ƴan Maula sun cika ƙofar gidanmu zan je na raba musu abin da ya dace" "Okay mu tafi na sauke ki ko" "No need my Alhaj, kawai ka faɗa mun numberka zan kira idan na isa" "Number Alhajin ya bata kafin suka fito daga gidan, a bakin titi ya sauke ta sai da ta tabbatar ya yi nisa kafin ta tari adaidaita ta nufi gidansu. Koda ta shiga gidan babu kowa har Maleek ɗin da ta barshi a kwance bata same sa ba, a gaggauce ta ɗora shinkafa da miya wadda ta ji kayan haɗi, lemun kankana da apple ta haɗa tare da jerewa a basket, ta san cewa yanzu haka Meera ta isa farkawa, wanka ta shige da sauri a lokacin an fara kiraye-kirayen sallar ƙarfe biyu, bayan ta fito ne ta yi sallarta sannan ta shirya cikin doguwar riga daidai gwuiwarta black me kyau an yi mata adon duwatsuna na gold, haɗaɗɗen gashin kanta ta ɗaure tana mai yafa ɗan ƙaramin mayafi, sannan ta fesa turarukka masu daɗin ƙamshi, ba ƙaramin kyau ta yi ba musamman yanda hips ɗinta da mazaunanta suka bayyana, sai da ta tabbatar ta haɗu ta ko'ina kafin ta ɗauki handbag ɗinta da basket na abinci ta fito tare da rufe part ɗinta. Har wannan lokacin ma bata ga alamun Maleek ba kuma bata damu da halin da yake ciki ba, dirrect titin unguwar ta nufa ta samu adaidaita. Sai da ta fara biyansa sannan ta shige daga ciki, mintuna kaɗan suka iso bakin hospital ɗin, da sauri Najmeer ta fito tare da nufar cikin asibitin. A bakin ƙofa suka haɗe da Nurse ɗin da ta duba Meera, Najmeer ce ta fara gaisheta kafin ta ce "Ya me jikin? ina fatar ta farka ko" "Jiki Alhamdulillah har ma ta ci abincin da Yayanku ya kawo mata" Nurse ɗin ta faɗa tana barin gurin, mamaki ne ya kama Najmeer jin abin da aka ce, waye kuma Yayanmu, ta tambayi kanta a zuci, ganin ba me bata amsar ne ya sa ta nufi ɗakin da Meera ke ciki. A zaune ta same ta tana shan kankana, fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Najmeer kin dawo? sannu da zuwa" Shuru Najmeer ta yi tana mai zama kan kujerar da ke gurin, cikin alamun zargi ta ce "Maleek ya biyo ki ne?" A tsorace Meera ta ce "What are you saying? me kuma zai kawo Maleek a nan?" "Kamar ya me zai kawo shi? bayan an ce mun akwai wanda ya kawo miki abinci" Ɗan murmushi Meera ta yi kafin ta ce "Waye zai kawo min bayan ke? nima lokacin da na tashi a haka na samu waɗannan kulolin cike da girke-girke kala-kala, na zata ke ki ka kawo mun" Jin abin da ta ce ne ya sa Najmeer zaro ido a mamakince "Tashi tashi mu bar hospital ɗinnan" Ta ƙarasa maganar tana kama hannun Meera, ko ta kan abincin da ta kawo basu kuma bi ba suka fice daga hospital ɗin. ...................... A ɓangaren Sultal kuwa wayarsa ce kan kunnensa da alama da Girlfriend ɗinsa ƴar London yake waya, anan yake shaida mata cewar Dad ɗinsa ya amince da aurensu. Sosai Maleeka ta yi murna jin wannan haɗaɗɗen labarin, sun jima suna fira wanda duk yawan firar babu daɗin ji saboda abin ya ƙazanta, a haka har Sultal ya samu natsuwa. Ƙarfe uku na rana ya sauko parlourn ƙasa sanye cikin gajeren wando da singlet fara sai ƙamshi ke tashi a jikinsa, saurin dakatawa ya yi jin an yi hugging ɗinsa ta baya tare da shafo ƙirjinsa, da ƙarfi Sultan ya gimtse ido jin wani yanayin da ya shige sa, Sumayya da ke manne a bayansa ne ta juyo a hankali tana mai shafa fuskarsa, sannu-sannu Sultan ya buɗe rikitattun idanunsa ya sauke kan fuskarta, cikin mugun ɓacin rai ya ture ta daga jikinsa yana mai zabga mata wawan marin da ya sa da buga kanta a ginar da ke gurin, wata irin ƙara Sumayya ta saki jin zafin da ya shigeta, "Are you okay? do i look like your type? idan ki ka sake gangancin kallona ba ma taɓa jikina ba sai na kawar da ke a doron ƙasa, dabba kawai ɓace mun da gani tun kafin na tattake ki". Da gudu Sumayya ta haura sama tana rusa ihu, kasancewar Dad sun fita da Junaid ne ya sa gidan ya yi shuru sai masu aiki, Mom kuwa tana part ɗinta. Har ya juya zai koma sama ya ji wayarsa ta ɗauki ƙara, sunan Majeed ya gani kan screen ɗin hakan ya sa ya ɗaga ba tare da yace uffan ba, Majeed ne ya ce "Sultan an samu gidan da Shalele suke zama, yanzu haka ina tare da addrees ɗin...." Tun kafin Majeed ya rufe baki Sultal ya ce "Kana ina yanzu haka?" "Ina bakin gate ɗinku". Ɗiffff Sultan ya kashe wayar, da saurin tsiya ya fito harabar tare da dakawa masu tsaron gidan tsawa "Ina buƙatar motoci ashirin yanzunnan" Ai kuwa duk sun daburce nan take aka jere motoci ashirin a harabar gidan, be damu da kayan da ke jikinsa ba ya shige motar da ta fi kowacce ɗaukar ido sannan ya bada umarnin su tafi. Kasancewar Majeed ya zo da motarsa ne ya sa ya shige gaba, motocin Sultan kuwa na bayansa, da mahaukacin gudu suka bar unguwar tare da nufar gidansu Najmeer. *Mu haɗe a next page, ina ganin ƙorafin rashin typing kullum da kuma ƙorafi kan cewa na ƙara yawan typing wannan baya isarku, maganar gaskiya ita ce ba zan iya ƙara yawan typing ba, sai ma ragewa da zan yi, saboda ina ƙoƙarin yin typing sosai, kuma ina da ayyuka da dama a gabana ciki kuwa harda haddar alqur'an, ba rubuta littafi nr kawai nake ba, ba zan zauna yin typing kullum ba ku yi haƙuri da duk randa ku ka samu posting, zai iya yuwa ma na dakata da rubuta book ɗin, thank you all* *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P. 4 Tun da suka fara ratsa kowacce unguwar mutane ke kallonsu har suka shigo arean su Najmeer, kasancewar motoci basa iya shiga ne ya sa suka dakata, cikin tsawa Sultan ya ce "What the heck, me kuma ya faru?" "Alhaji ƙarami hanyar ce motoci basa shiga" Da mamaki Sultan ya ce "What do you mean? wai anan ne arean da zamu tsaya?" Drivern ne ya kuma cewa "Eh anan ne" Cike da ƙasaita ya fito motar ba tare da jiran a buɗe masa ba, daidai lokacin da ya hangi adaidaita sahu na tsala gudu har ya iso ta gefensu, kamar an ce ya juya ai kuwa ya hangi su Najmeer suna faɗin me adaidaita ya ƙara gudu, suna haɗa ido Najmeer ta sakar masa murmushin da ke kama da na mugunta, tabbas ba zan mance da wannan fuskar ba ko da kuwa zan mutu na dawo ne, ya faɗa a ransa yana ƙare musu kallo, ganin cewa suna neman tserawa ne ya sa Sultan bada umarnin a bi bayan me adaidaitan, cikin sauri ya shige motar yana dakawa Drivensa tsawa, da kafurin gudu suka rufawa su Najmeer baya a lokacin har sun yi nisa sosai. Gudu suke kan titi wanda ya tashi hankalin mutane, kasanacewar akwai tazara me yawa tsakanin motocin Sultan da adaidaitan da su Najmeer ke ciki ne ya sa basu riske su ba. Maleek da duk fuskarsa ke manne da bandeji ne ya biyo kan mashin ya fito daga asibiti, ai idanuwansa na kaiwa kan su Meera da Najmeer da ke cikin adaidaita suna ba me adaidaita umarnin ya ƙara gudu ne ya sa Maleek faɗin "Dan Ubanka me mashin shiga bayan waɗan can Karuwan tun kafin su ɓullewa ganinmu" Ai kuwa me mashin da duk tsoron Maleek ya rufe sa ne ya sa shi karya kan mashin ɗin nasa ya shiga bayan su Najmeer da mugun gudu. Meera da duk hankalinta ya tashi ne ta ƙara leƙa bayansu tana faɗin "Yau mun shiga uku wallahi ga Maleek nan a bayanmu, anya ba shine ya sanarwa su Sultan inda mike ba?" "Kinga Meera duk wannan zancen zamu yi shi daga baya, yanzu neman tsira mike yi, amma ki sani ba wai tsoron Sultan ne ya sa nake gudu ba, ina son na yi masa tanadi na musamman wallahi sai na koya masa hankali" Shuru Meera ta yi dan ita ganin take duk magana ɗaya Sultan na iya jin abin da suke faɗa. Ta bayan layinsu Najmeer me adaidaita ya shigo, inda ta bashi umarnin ya rinƙa shiga kwanar da motoci basa iya shigowa, ganin hakan ya sa Sultan cewa a tsayar da motoci, da sauri ya fito tare da bin hanyar da matsanancin gudun da be taɓa sanin yanada irinsa ba har ya tsere su Maleek da ke kan mashin, cakkkkk ya tsaya yana kallon adaidaitar da ke tsaye kan hanya, tabbas ita ce wadda ke ɗauke da su Najmeer, abin mamakin shine ba bu kowa a ciki, Maleek da ke ƙarasowa ne ya ce me mashin ya tsaya ɗan nesa da inda Sultan ke tsaye, cikin ƙasa da murya kamar me raɗa Maleek ya cewa me mashin "Wai wancan ba Sultan Chief ba ne?" Me mashin na jin haka ya saki mashin ɗinsa tare da runtumawa da gudu gurin Sultan yana masa kirari, ai kuwa mutane suka cika gurin ana faɗin ga Sultan Chief ga Sultan Chief, kafin ka ce me gaba ɗaya unguwar ta cika da mutane, su Majeed da masu tsaronsa ne suka ƙaraso ana tattare mutanen da ke ƙoƙarin isa gurinsa, Sultan kuwa duk baƙin ciki ya cika shi ganin babu kowa a cikin adaidaita har me tuƙin nata, a tsawace ya kalli mutanen da ke gurin yana faɗin "Dallah Malamai kun ishemu da surutun banza da wofi, wannan ai hauka ne sai hayaniya ku ke min a kunne" Ya ƙarasa maganar yana barin gurin cikin tsananin fusata, mutane sai jayewa ake ana bashi hanya ganin yanda ransa ya ɓaci. Sultan na isa gurin motocinsu ya daki glass ɗin mota ɗaya da hannunsa da ƙarfi, nan take glass ɗin ya tarwatse hannunsa kuwa ya ɓalle da jini, Majeed ne ya yi saurin kama sa "Sultan what is this please? za ka halaka kanka saboda wata macen" Idanun Sultan sun ciko da ƙwalla but taurin rai be bari sun zubo ba, ya ɗago kafuran idanuwan nasa da suka yi jajir ya sauke kan fuskar Majeed, ai kuwa Majeed ya sake masa hannu yana mai ja da baya a mugun tsorace, tun da Allah ya halicce sa be taɓa ganin ɓacin ran Sultan irin haka ba, wata irin razananniyar ƙara Sultan ya saki wadda ta haddasa watsewar duk mutanen da suka taru a gun, waɗan da ke cikin gida kuwa suka rinƙa kulle ƙofofinsu dan sun yi tsammanin ɓarayi ne suka shigo unguwar tasu. Kan gwuiwoyinsa ya durƙusa yana dafe kansa jikinsa kuwa ya hau ɓari tamkar me jin sanyi, duk wata jijiya ta jikinsa sai da ta fito, jin an dafa kafaɗarsa ne ya sa ya naɗa naushi me zafin gaske ya doki wanda ke bayansa, amma sai ya ji an riƙe naushin nasa, da mugun fusace ya ɗago dan ganin wani me ƙarar kwana ne ya riƙe masa hannu, Junaid ya gani a tsaye cikin suit baƙaƙe, kayan sun masifar yi masa kyau musamman da ya ɗora glass ɗan ƙarami me kyau da ɗaukar ido, gashin kansa ya haɗe ya ƙara kyau, da mamaki Sultan ke kallonsa dan be san yanda aka yi yayan nasa ya san sun zo nan ba. Hugging ɗinsa ya yi yana mai sauke ajiyar zuciya me zafi, cikin muryar da shi kansa be san yana da ba ya ce "Bro wallahi idan har ban kashe yarinyar nan ba zan iya kashe kaina, dan Allah ka nemo min inda take, yanzu ma na sake rasa ta" Bubbuga bayansa Junaid ya shiga dan ya san duk abin da Sultan zai faɗa a yanzu baya cikin hayyacinsa, Junaid ne ya shigar da shi mota sannan ya bada umarnin su koma gida. Tun da suka fara tafiya Sultan ke kwance kan cinyar Yayan nasa, duk hankalinsa baya jikinsa daga zaran ya rufe ido sai ya rinƙa ganin lokacin da Najmeer ke sakar masa murmushin mugunta, duk ya rasa abin da ke masa daɗi a rayuwa, sun ɗauki ɗan lokaci l kafin suka ƙarasa gida kasancewar akwai jayewa. Suna shiga Junaid ya kama Sultan suka nufi room ɗinsa, Allah ya sa babu kowa a parlourn. Majeed na bayansu jikinsa duk a sanyaye, kan bed Junaid ya kwantar da Sultan sannan ya shiga aikin gyara masa gannunsa da ke fitar da jini, bayan ya gama ne ya maida kallonsa kan Majeed da duk ya tsure guri ɗaya, cikin muryarsa me ɗan karen daɗi gami da uban miskilanci kamar me ciyon magana ya ce "Majeed wai wacece wannan yarinyar da duk Sultan ya tada hankalinsa saboda ita?" Ɗan sosa kai Majeed ya yi alamun rashin gaskiya "Bro Karuwa ce fa, me zaman kanta" A razane Junaid ya waro rikitattun idanuwansa me ƙara masa kyau cikin mamaki "Karuwa kuma? meye haɗinku da Karuwa?" Sanin halin Junaid ɗin ne ya sa Majeed kwashe duk abin da ya faru ya sanar masa daga farkon haɗuwar Sultan ɗin da Najmeer har yau. Jinjina kai Junaid ya yi "Tun ina kan hanya na hangi motocinku na gudu kamar za ku tashi sama, shine na bi bayanku dan ganin inda za ku tafi, ashe Karuwa ku ke bi ya subhanallah" Sultan da ke kwance ne ya ɗan kalli yayan nasa, sai kuma ya mayar da kansa wani gefen dan ya rasa abin da ke masa daɗi a halin yanzu, zuciyarsa kuwa sai ƙara fusata take. Junaid ne ya kuma cewa "Majeed a ina yarinyar take kuma me ka sani game da ita?" "Shalelen Alhazawa kenan wadda bata harka da yara sai manyan masu kuɗin da ke ji da kansu, cikakkiyar ƴar bariki ce me zaman kanta, wani lokacin har Clup take kwana idan har bata ra'ayin kwana da wani namijin......" Saurin ɗaga masa hannu Junaid ya yi zuciyarsa na mugun duka da ƙarfi, a rayuwarsa ya tsani mace marar kamun kai, wani irin mugun zafi zuciyarsa ke masa tamkar zata faso ƙirjinsa, "Allah ya shirya su" Ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da barin ɗakin. Sun kai mintuna biyar a haka ba wanda ya ce uffan, shima Majeed ɗin be yi yunƙurin magana ba dan ya san Sultan ba zai amsa masa ba, Sallamar Mom ce ta sa Majeed miƙewa yana gaisheta tare da ficewa daga ɗakin. Da sauri ta ƙaraso tana mai zama gefen bed ɗin "Sweetheart me ya sameka ne? na shiga ukuna wai me yake faruwa ne kwanakinnan" Mom ta faɗa cikin damuwa da ɗan nata, Sultan da ke kwance ya ɗago kansa a hankali ya ɗora kan cinyar Mom yana mai fashewa da kukan da ya daɗe a zuciyarsa, cikin tsananin tashin hankali Mom ta shiga rarrashinsa dan ta san yau kam ran maza ya ɓaci, abin da zai saka Sultan kuka ba ƙarami ba ne, sai da ya yi me isarsa kafin ya ɗago rinannun idanuwansa masu masifar ban tsoro "Mom please ku nemo mun ita duk inda take, idan ba haka ba za ku rasa ni, na tsaneta Mom wallahi na tsaneta...." Ya ƙarasa maganar muryarsa na sarƙewa, bubbuga bayansa ta shiga yi cikin tausayawa tana faɗin "Wacece ita? faɗa mun ko ƴar gidan uban waye sai an kawota har nan gidan ka zartar mata da hukunci" Saurin ɗagowa ya yi "Da gaske Mom?" Hawayen da ya zubo mata ta share cikin gazgatawa ta ce "Na yi maka alƙawari duk inda take a faɗin garinnan sai an nemo ta, ka saka wannan a ranka idan har ba'a kawo maka ita ba ka canza mun suna, amma meye sunan yarinyar?" Ɓata fuska Sultan ya yi "Wai Shalele na ji ana kiranta, amma ki tambayi Majeed zai sanar da ke" "Alright ka kwantar da hankalinka ni ce nan na shaida maka cewar ka gama ganinta?" Mom ta ƙarasa maganar tana murmushi. Wani mugun farinciki ne ya lulluɓe Sultan dan ya san babu abin da Mom zata masa alƙwari bata cika ba, kwanciyarsa ya yi kan cinyarta suka cigaba da fira kamar ba abin da ya faru. ........................ A ɓangaren su Najmeer kuwa, me adaidaita na sauke su suka shige ƙwanar da zata sada su da hanyar gidansu Mamu, ai kuwa da sauri suka shige, me adaidaita ko ya ɓoye dan ceton ransa. Lokacin da suka shiga ba kowa dan haka Najmeer ta ja hannun Meera zuwa ɗakin Mamu, kwance suka sameta tana rawar sanyi cikin sauri Najmeer ta ƙarasa tana mai tallafota "Mamu lafiya? me yake damunki?" A ruɗe Najmeer ta jero mata tambayoyin, duk da cewar Mamu na jin jiki amma hakan be hanata gane wadda ke gabanta ba, "Najmeer......?" Ta faɗa cikin muryarta da bata fita sosai. "Na'am Mamu sannu, bari na ɗaga ki ko za ki samu ƙarfin jikinki" Kamata ta yi tare da ɗorata kan gado, Meera ce ta ɗora mata pilo a bayanta, Najmeer kuwa ta fito tsakar gidan ko zata samu abin da zata dafa mata, dan alamun yunwa sun bayyana a jikinta. Cikin ƙanƙanin lokaci Najmeer ta yi tuwo da miyar ganye, duk abin da take buƙata akwai shi a kitchen ɗin, sai da ta tabbata ta gama tasss kafin ta kwaso abincin zuwa ɗaki. A nan ta samu Meera da Mamu na fira, duk da cewar Mamu sama-sama take magana amma Meera na jin daɗin firar sai washe baki take, har Najmeer ta aje girkin. Da ƙyar ta samu Mamu ta ci tuwon, Meera kam sai da ta lashe kwano. Bayan sun gama ne Najmeer ta kwashe kayan ta wanke. Duk abin da take Mamu na kallonta, dan bata taɓa zaton Najmeer zata dawo ba, cikin sallama Najmeer ta shigo tana mai zama kusa da Mamu "Sannu Mamu ya ki ke jin jikin naki yanzu?" "Mtsssss wai da waye take magana?" Cewar Mamu tana kallon Meera, bushewa da dariya Meera ta yi "Da ke take, tana tambayar ya jikin naki" Najmeer ce ta ce "Haba Mamu yanzu kuma me na yi? idan bakya son dawowar nawa sai na koma" A ruɗe Mamu ta ɗago tana kallonta sai kuma ta fashe da kuka tare da rungumeta, itama Najmeer ɗin rumgeta ta yi tana rarrashinta, duk tausayinsu ya kama Meera bata san lokacin da ƙwalla ta zuba mata ba. Cikin kuka Mamu ta ce "Najmeer me na yi miki ki ka nemi kashe ni tun lokacin mutuwata be yi ba?" Jin abin da ta ce ne ya sa Najmeer da Meera fashewa da dariya, cikin fushi Mamu ta janye jikinta tana ɓata rai "Yoooo na ga iyashege dariyar me ku ke min?" Tun kafin waninsu ya kuma cewa komi suka ji an banko ƙofar gida da ƙarfi, Najmeer na jin haka ta koma bayan ƙofa ta ɓoye, Meera dai sai zare ido take dan ta kasa matsawa ko'ina, Kawu ne ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi cikin masifa ya ce "Ina shegiyar yarinyar ne? an ce mun ta zo gidannan" "Wa ya faɗa maka hakan Jamilu? ni kaina ina neman Jinkanyata ido rufe amma kun korar mun ita, Allah sai ya saka mun" Mamu ta ƙarasa maganar tana sharɓe hawaye kamar gaske. Sai a lokacin Kawu ya lura da Meera da ke zaune tana kallon yanda Mamu ke kuka, "Ke kuma daga ina?" Ya faɗa yana lashe baki kamar tsohon maye. Haɗe fuska Meera ta yi dan ganin yanda yake kallonta, "Am....am....ni sunana Meera kuma na zo ganin Mamu ne" "To to to ya yi kyau har wanne lokacin za ki kai anan gidan?" "No ba daɗewa zan yi ba ziyara ce kawai na kawo mata". Kawu na washe baki ya ce "Hakan nada kyau, ko za ki je gidana ku gaisa da matana" Saurin karɓe zancen Mamu ta yi da faɗin "Kai Jamilu kai Jamilu ka shiga hankalinka, kuma ka nemo mun Jikanyata duk inda ku ka kai mun ita idan ba haka ba, hukuma ce zata raba ni da kai" Jin Mamu ta ambaci hukuma ya sa Kawu ficewa da sauri yana zage-zage, sai da Najmeer ta tabbatar ya yi nisa kafin ta fito tana murmushi. "Meera ashe mun kusa shan biki" Harara Meera ta gallawa Najmeer "Bikin waye kuma?" "Naki mana na ji yanda Kawu ke rawar ƙafa kamar da wata a ƙasa" "Hmmm kin ga Najmeer bana son haka fa, Mamu kina jinta ko?" Murmushin ƙarfin hali Mamu ta yi dan jikinta ya fara zafi, zazzaɓi take ji sannu a hankali yana shiga jikinta, amma sai ta daure saboda bata son hankalin Najmeer ya tashi "Nikam ku ake ji, ku koma can ɗakin nata ku ƙarasa ni zan samu na kwanta" Fita Meera suka yi suna dariya jin yanda Mamu ke magana. Da kallo Mamu ta bisu tana mamakin inda Najmeer ta samo budurwa kamar haka, tana son tambayarsu amma sai sun samu natsuwa. Ɗakin Najmeer suka koma cikin mintuna talatin suka gyara shi tassss, duk jikin Meera ya saki kasancewar ɓarin da ta yi, kan bed suka baje suna maida numfashi "Wai nikam Najmeer me Docotor ya ce game da jinin da ya zuba a jikina" Cikin alamun tsoro Najmeer ta ce "Dama...dama...." "Dama me? faɗa mun mana ai babu abin da zai sa mu ɓoyewa juna sirrinmu a yanzu" Duk da jikin Meera ya yi sanyi amma cikin dauriya ta ƙurawa Najmeer ido dan jin amsar tambayarta, "Cikin jikinki ne ya zube Meera" A mugun tsorace Meera ta zazzaro ido "Cikin jikina kuma? ban fahimce ki ba Najmeer" Meera ta ƙarasa maganar tana jijjiga Najmeer da ƙarfi. "Yes Meera kina da ciki amma ya zube sanadiyar zubar jinin da ki ka yi" Kuka Meera ta fashe da shi tare da rungume Najmeer cikin tausayin kanta, "Shikenan duk farincikin rayuwata ya ƙare, waye zai aureni a haka? bayan Karuwa ma har ciki na yi" Sosai Meera ke kukan tana dukan jikinta, da sauri Najmeer ta riƙeta ta shiga rarrashinta tare da yi mata nasiha me ratsa jiki "Meera ki sani cewar kowanne bawa da tasa ƙaddarar, kuma duk iskancin mace baza ta rasa me aurenta ba idan har Allah ya zaɓa mata, ina son ki kasance me ɗaukar ƙaddara a kowanne lokaci...." Jin kiran sallar ƙarfe huɗu ne ya sa suka miƙe dan yin ibadah. Wanka suka fara sannan suka yi sallah, sosai Najmeer ta yi musu addu'a. Bayan sun gama ne ta kunna wayarta tana mai danna wata number, bugu uku aka ɗaga. "Hi My Alhaj....." Najmeer ta faɗa cikin wata arniyar murya me ɗaukar hankali, wanda aka kira da Alhaj ne ya saki murmushi me sauti yana faɗin "Shalelen Alhazawa, ai wannan muryar taki baza ta ɓace mun ba, gaskiya na shiga wani halin na rashinki a kusa da ni, please ki bani dama na zo na ganki" Cike da makirci Najmeer ta ce "No ba yau ba sai zuwa gobe yanzu haka ina cikin Airport zamu tafi Dubai karɓo wasu kaya" "Wow that's why i love you, ki tura mun account numberki yanzu" "Okay yanzu kuwa, anjima zan kira ka byeee" Kashe wayar ta yi tana dariyar mugunta, Meera kam sai kallon Najmeer ta ke jin ƙaryar da ta zuba, account number Najmeer ta tura masa, ko minti ɗaya bata yi da turawa ba ta ji saukar alart na 10million. Ihu Meera ta yi cikin mugun mamaki, "Kai Najmeer amma wannan waye haka? wanda be san zafin kuɗi ba" Har Najmeer ta buɗe baki da niyar magana suka ji faɗuwar abu a tsakar gida, a tare suka fito dan ganin meye, da gudu Najmeer da Meera suka ƙarasa gun da Mamu ke kwance a sume, cikin sauri suka kamata jikinta ya ɗauki zafi sosai alamun zazzaɓi ya shigeta. A ruɗe Najmeer ta ce "Kama mun ita mu tafi Asibiti jikinta ne ya tashi" Ba ɓata lokaci suka nufi babban Hospital ɗin da ke cikin gari, suna isa aka shiga da Mamu dan bata taimakon gaggawa, Najmeer da Meera sai zarya suke har aka kira sallar magrib, a nan suka yi sallah har Nurse ɗin ta fito tana mai ƙarasowa inda suke "Ku biyo ni office ɗina" Jiki a sanyaye suka bita har zuwa office, sai da ta gama rubuce-rubucenta kafin ta maida kallonta kan Najmeer "Ga wannan takaddar sune magungunan da za ku saya, amma wannan baza ku samu a nan ba" Ta faɗa tana miƙa mata wata ƙaramar takkadar. Karɓa Najmeer ta yi "Mun gode sosai, but ana buƙatar maganin a yanzu ne?" "No ba yanzu ba sai zuwa gobe idan ta tashi daga bacci, mun yi mata allurar bacci ne" Godiya suka ƙara yi kafin suka fito. Har kusan goman dare ba wanda ya samu bacci a cikinsu, Najmeer ma kasa cin komi ta yi, Meera ce ta samu awara me zafi a bakin titi ta sayo. A hospital ɗin suka kwana, sai wajen tara na safe Najmeer ta fito domin sayo maganin da ake buƙata, Meera da ke ƙoƙarin shiga ɗakin da Mamu ke ciki ne ta ce "Ina zuwa haka?" "Zan siyo maganin da suka ce ne, ko za ki mun rakiya?" "Aa sai kin dawo, ba bu kyau barin marar lafiya shi ɗaya, ki sayo mun abu me daɗi please" Tsaki Najmeer ta ja tana mai barin gurin. A harabar Hospital ɗin ta tsaya neman adaidaita saboda har ciki suna shigowa, amma da mamaki yau ba kowa, hakan ya sa ta fara tafiya har kan titi, duk wanda ta tare sai ta ga da mutane a ciki, babban titin ta iso tana mai duban inda zata samu abin hawa, kamar daga sama ta ji ƙarar motoci sun mugun rikita mata kunne, gaba ɗaya ƙura ta baje gurin tamkar wasar motoci ake, motoci hamsin ne masu kafuran kyau da tsada, a rikice Najmeer ta dafe kunnenta tana mai neman hanyar da zata wuce, cikin ƙanƙanin lokaci motocin suka zagayeta wasu majiya ƙarfin maza kusan su goma ne suka fito daga wata arniyar mota black, ba tare da ɓata lokaci ba gardawan suka kama Najmeer da ƙarfin tsiya zuwa mota, ihu take tana neman ceto amma ba bu me saurarenta wasu ma guduwa suke dan tsira da rayuwarsu, da sauri motocin suka bar gurin da ita cikin matsanancin gudu. Duk Najmeer ta firgice dan bata san su waye ba, gashi sun rufe fuskarta da baƙin ƙyalle, sai da suka yi tafiya me ɗan nisa kafin suka tsaya bakin gate ɗin, cikin ƙasaita motocin suka fara shigewa har suka shige gaba ɗaya, Najmeer dai tun tana ihu har ta daina dan numfashinta ya fara ɗaukewa. *Mu je zuwa yanzu aka fara, sorry yau ba yawa, pleae share and ku min uzuri na faɗa muku cewa ina hadda, shiyasa bana samun typing akai-akai* *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P.5 Da ƙarfin tsiya wani ƙaton ya fincikota daga motar yana mai jifa da ita gefe. Duk da cewar numfashin Najmeer na sama da ƙasa amma hakan be sa ta kasa jin zafin faɗuwar ba. Wani gigitaccen marin da aka ɗauke ta da shi ne ya sa ta saki ƙara me rikitarwa, lokaci ɗaya aka janye ƙyallen da ke rufe a fuskarta, Sultan ne a tsaye cikin baƙaƙen kaya idanuwansa manne da glass baƙi wulikk, fuskarnan kuwa ba bu alamun rahama ko kaɗan. Gashin kanta ya damƙo da ƙarfi yana kallon Mom da ke murmushi "Thank you so much Mom, yau kin cika mun burina" Ya ƙarasa maganar yana yiwa mutanen da ke gurin alamun su wuce. Ƙayataccen parlorsu ya nufa Najmeer kam ta fice a hayyacinta dan bata ganin fuskar kowa sai dishi-dishi, a hawa na ƙarshe ya nufa da ita tare da jefata cikin wani ɗakin da babu haske sai duhun da ke bayyane, cikin tsoro da fargaba Najmeer ta ƙwalla ƙara tana faɗin "Waye kai........? idan ka isa ka fiddani ɗakinnan wallahi sai na koya maka hankali" Jin abin da take faɗi ne ya sa Sultal juyawa cikin ɓacin rai da niyar shiga ɗakin, Mom da ke bayansa ne ta yi saurin riƙe hannunsa "No Son kar ka shiga a yanzu, ka jira har Dad ɗinka ya bar ƙasar ya ce mun za su tafi meeting a Mali" Cije lips Sultan ya yi yana mai barin gurin, Mom kuwa ta rufe ɗakin tare da saukowa ƙasa, anan suka ci karo da Dad yana ƙoƙarin sauka ƙasa "Wai ina Junaid ne ya? ina son zai mun rakiya Aiport?" "Sai dai Sultan shine kawai a gida" "Kina nufin be tafi aiki yau ba? wai me Sultan yake son zama ne, kira mun shi yanzunnan" Cewar Dad yana barin gurin. A harabar gidan ya sami Dad na jiransa fuska babu walwala "Dad barka da war haka" Ko kallonsa Dad be yi ba dan ya tsani shiririta "Sultan aikin ne ba ka tafi ba lafiya dai ko?" Haɗaɗɗen gashin kansa ya sosa yana lumshe ido "Yes Dad bana jin daɗi ne, amma zan shiga gobe da yardar Allah" "Masha Allah, Allah ya yarda" Ɗago kai Dad ya yi kafin ya kuma ce "Zan yi tafiya sai nan da one week mun yi sallama da Mom ɗinka, Junaid ne ban samu ganinsa ba idan ya dawo ka sanar masa" "Okay Dad a dawo lafiya" Da ameen Dad ya amsa yana shigewa motar da aka buɗe masa, da sauri motocin suka fice daga gidan, Sultan na ganin haka ya nufi cikin gidan da sauri dan ya matsu ya fara gallaza mata. A parlour ya sami Mom na shan lemu me sanyi, kana ganinta ka san tana jin daɗin zaman, ba tare da ya kalli inda take ba ya nufi sama, "Sultan ina zuwa haka da sauri?" Ya tsinkayo muryar Mom "Ohhhhh Mom please kin san cewa wannan yarinyar na gidannan ina son na hukuntata ne daidai da laifinta, ni ina ganin kasheta zan yi kowa ya huta" "Kisan kai......? no Sultan ban amince maka ba, idan har da wani hukuncin za ka iya yi mata amma banda kisan kai" "But Mom why?" Ya faɗa yana mai dawowa inda take. "Look Son ka san bana son na rasa ka, idan har ka kasheta wallahi Abbanka zai iya shige mata gaba har a hukuntaka". "Okay fine" Sultan ya faɗa tare da nufar room ɗin da Najmeer ke ciki. Daga bakin ƙofa yake jin yanda ake tattaka tiles ɗin ɗakin kamar tafiyar doki, sai kuma kukan Mage me ban tsoro da firgitarwa, a ɗan tsorace Sultan ya tsaya yana sauraren yanda kukan Magen ke ƙara sauti, can kuma ya ji ihun Najmeer da surutai kamar zararra, cikin fushi ya daki ƙofar ai kuwa ta ƙara sautin ihun nata, kukan Magen da yake ji kuwa ya ɗauke chakkkk kamar ba abin da ya faru. "Keeee Uwar wa ki ke wa ihu kamar kin samu gidan Ubanki?" Sultan ya faɗa yana danna hasken ɗakin, da sauri Najmeer ta rufe rikittatun idanuwanta da tafukan hannunta, ƙarasowa Sultan ya yi yana mai chakumo wuyanta da ƙarfi "Magana nake miki ƙaramar Karuwa" Sai yanzu Najmeer ke buƙatar ganin ko fuskar waye, ta tabbata cewa Sultan ne kawai zai iya yi mata hakan, amma sai ta ƙara runtse idanuwanta ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba. Cikin muryar da ta tashi rikita shi ta ce "Har yanzu ba ka nuna mun kai namiji ba ne, tun da ka kasa bari mu haɗa jiki da kai, idan kana son tabbatar min kai cikakken ɗan iska ne ba sai ka saceni ba" A fusace Sultan ya ɗaga hannu gami da sharara mata mari ji ka ke tasssss, "Keeee idan har kwanan baya kin faɗa mun son ranki, a yanzu ba zan lamunce miki ba, ke ba kowa ba ce face Karuwa" "Kai kuma mazinaci ko?" Kamassss ya buge mata baki yana mai sakin wuyan nata "Waye mazinacin? ina ganin wannan bakin naki ba zai daina surutu ba sai na koya masa hankali, wallahi na tsaneki Karuwar banza da wofi" Caraffffff Najmeer ta karɓe zancen da faɗin "Ka mance da suna ɗaya" Zuba mata ido Sultan ya yi jiran abin da zata ce, har ila yanzu idanuwanta a rufe su ke, "Bayan Karuwa ni ɓarauniya ce, and soon zan nuna maka asalin ko wacece ni, sai na lalata maka rayuwa sai na mayar da kai abin tausayin da kai kanka sai ka zubarwa kanka da hawaye" A mugun fusace Sultan ya cire belt ɗinsa ya shiga dukanta ta ko'ina kamar Allah ya aiko shi, sai da ya yi mata shegen dukan da ta kasa tashi, tun Najmeer na ihu har ta kasa magana. Sultan na layi kamar mashayi ya iso bakin ƙofa gami da kashe hasken ɗakin ya fice waje. Kasancewar ɗakin ɓoyayye ne ya sa duk yanda za ka yi ihu ba bu me jinka, wannan dalilin ne ya sa ba wanda ya ji ƙarar da Najmeer ke yi. Wani irin sarawa kansa ke masa a haka ya sauko ƙasa, inda ya sami Mom yanda ya barta amma wannan karon da wata matashiyar yarinya me kyau zaune cikin shigar ƙananan kaya, ita ba fara ba kuma ba baƙa ba, a kanta gashin doki ne ya sha gyara sai wayar da ke hannunta iphone 15promax tana latsawa. Jin saukowar mutum ne ya sa ta ɗago da sauri, ai kuwa ta tashi da gudu ta nufi Sultan gami da hugging ɗinsa "Hi love am so happy to see you, jiya nake dawowa daga ƙasar nan ake ce mun ka shigo, welcome back sweetheart". Ta ƙarasa maganar tana ƙara shigewa jikinsa, cike da ɓacin rai Sultan ya tureta daga jikin nasa har sai da ta kusa faɗuwa, dama ba wani jikin take da ba, idan aka yi iska me ƙarfi zai iya ɗagewa da ita sama. "Are you mad? Surayya sai yaushe za ki yi hankali ne?" "What? haba love yanzu me nayi maka? Mom kina ganinsa ko, bansan meyesa Sultan ya tsane ni ba" Cewar Matashiyar da ya kira da Surayya tana mai zama kusa da Mom cikin shagwaɓa. "Ke kuma ban da abinki ai kin san Sultan baya son hauka, amma kin kasa hankali ai yanzu kin shiga taitaiyinki, ina ganin baya cikin good mood ki barshi kawai" Turo baki Surayya ta yi kamar zata yi kuka "Sultan please ka mun magana ko so ɗaya ne" Wani mugun kallo Sultan ya jefa mata yana barin parlourn. Sumayya da ke can sama tana kallon duk abin da ke faruwa ne ta taɓe baki tana faɗi a hankali "Shegiyar banza ai kin kawo ƙarshen iskanci, ai kuwa yanzu mun shiga uku tun da kin dawo Nigeria" Ta ƙarasa maganar tana jan tsaki yanda ba bu me jinta. Surayya kam tana ganin Sultan ya shareta ne ta miƙe cike da fushi ta bar parlourn ko sallama bata yiwa Mom ba, Mom kam ko kallon inda take bata yi ba dan ta san dama gurin Sultan ta zo. Kamar wadda ake turawa haka ta ƙarasa gurin bugaggar motarta tana dakawa gate Man tsawa cikin ɓacin rai. Sanin halin Surayya ne ya sa gate Man danna remote da sauri, da mahaukacin gudu ta bar gidan kamar zata tashi sama. Junaid da ke office kuwa gaba ɗaya yau gabansa faɗuwa yake ya rasa dalili, hakan ya sa ƙarfe biyar ya bar Hospital tare da nufo hanyar gida, Allah ne kawai ya kawo shi lafiya amma duk jikinsa ya gama mutuwa, koda ya shiga ba kowa a parlourn dan haka ya nufi nasa ɗakin, yana shiga ga faɗa toilet dan sakarwa kansa ruwa. Ya kai kusan mintuna talatin kafin ya fito ɗaure da pink tawul me kyau da laushi, a hankali ya zauna kan Mirrow yana karanto alqur'an suratul Mulk, zazzaƙar muryarsa ta gama karaɗe ɗakin, har ya shirya cikin jallabiya ruwan toka me masifar kyau an yi mata ɗinkin wuta, jallabiyar irinta larabawannan ba ƙaramin fito da shi ta yi ba, kasancewar Junaid akwai sihirtaccen kyau. Sai da ya gama gyara haɗɗen gashin kansa sannan ya fesa turarensa me ƙamshin daɗi. Wayarsa da ke gefe ya ɗauka tare da nufar dianing dan yunwa yake ji. Ƴar aikinsu me kula da ɓangaren abinci ce ta jere masa lafiyayyen girki cikin natsuwa dan ta san halin Junaid baya son garaje. Hankali kwance ya yi bismillah ya fara cin abincin, be wani jima ba ya kamalla, bayan ta kwashe kayan ne ya ɗago kyawawan idanunsa masu kyau yana faɗin "Ina Mom ne?" "Oga Junaid ina ganin tana part ɗin Alhaji ƙarami" Ba tare da ya ce uffan ba ya ɗaga mata hannu alamun ta tafi. Part ɗin Sultan ɗin ya nufa amma ba kowa hakan ya sa ya tafi ɓangaren Mom nan ma be sami kowa ba, da mamaki ya danna number Sultan ɗin but har ta tsinke be ɗaga ba, and yana jiyo ƙarar wayar daga bayansa. Cikin tafiyarsa me jan hankali ya fara bin hanyar da yake jin ƙarar wayar. Daidai koridon da zai sada shi da hawa na huɗu ne suka ci karo da Sultan da Mom na ƙoƙarin saukowa, Junaid ne ya ce "Lafiya kuwa? na ga kamar bakwa cikin natsuwa and Sultan kana ganin kirana shine baza ka ɗaga ba" Sultan da ke cikin haɗaɗɗun manyan kaya masu kyau yadi wanda ya sha ɗinki ne ya sosa kai a hankali cikin alamun rashin gaskiya "Amm.....dama ina son na sameka da kaina ne" "Dama ka san na dawo ne?" Junaid ya jefa masa tambaya. Mom ce ta yi saurin katse zancen da faɗin "Kun ga mu koma ƙasa sai ku yi duk wannan surutun" Ta ƙarasa maganar tana jan Sultan tare da barin gurin. Da kallo Junaid ya bisu yana mamakin abin da su ka je yi a hawa na huɗu, tabbas akwai abin da suke ɓoye mun amma da sannu zan gane ko meye. Cewar Junaid a zuci yana mai bin bayansu. .................... A gafensu Meera kuwa hankalinta ya mugun tashi ganin har yamma babu alamun Najmeer, kuma babu wani kuɗin da ke hannunta da zata karɓowa Mamu magani, wayar Najmeer da ke hannunta ne ta kalla da kyau gashi bata san pin ɗin ba balle ta yi tranfer a POS ta sayo magani. Mamu da ke kallon Meera ne ta ce "Ƴarnan lafiya dai ko? har yanzu Najmeer ɗin bata dawo ba ne?" Jikin Meera a sanyaye ta ce "Wallahi har yanzu, nikam ina ganin ba lafiya ba, dan Najmeer baza ta tafi yawo bayan ta san bakya da lafiya ba" "Nima na san da hakan, Allah ya sa lafiya gaskiya na fara tsorata, amma ki tambayi likitoci ko za mu koma gida na gaji da kwanciyar nan" Meera ce ta ce "Eh sun ce zamu iya tafiya tun ɗazu, dama rashin dawowar Najmeer ɗin ne ya tsaya mun a rai" Sosai Mamu ta ji tausayin Meera ganin ko abinci ta kasa ci, rarrashinta ta shiga yi kafin suka haɗa tarkacensu zuwa gida. Kuɗin adaidata ma rasawa suka yi sai da wani bawan Allah ya taimaka musu. Har ƙofar gida aka sauke su, inda suka sami Jabir tsaye yana faman washe baki, "Affff har zan tafi sai gashi kun dawo" Ya faɗa yana ƙarasowa gurin su Mamu, Meera kam rashin sanin ko waye ya sa ta ja hannun Mamu suka shige gida, bayansu Jabir ya bi yana faɗin "Ina Najmeer ɗin ne? sai magana nake kun yi banza da ni" Daga Mamu har Meera ba wanda ya amsa masa, ganin hakan ne ya sa Jabir fusata, "Wai meye haka ne? ina matata zan shuka muku rashin mutunci fa sai magana nake ana shareni ita kuma wannan ƙanzon fa?" Ya ƙarasa maganar yana nuna Meera, cikin gajiya da hayaniya Meera ta ce "Bawan Allah me ka ke buƙata ne? dan Allah ka shafa mana lafiya idan Najmeer ce bata tare da mu, ka tafi nemanta wannan surutun banzan naka ya yi yawa" Jin abin da Meera ta ce ne ya sa Jabir laulayo ashar ya maka mata "Kutumar ubancan ke har kin isa ki gasa mun magana?" Mamu ce ta yi saurin faɗin "Jabir kana da hankali kuwa? ko rashin auren Najmeer ɗin ne ya haukata ka? ka fice mun daga gida tun kafin na tara maka jama'a, bayan kun raba ni da Jikanyata shine za ka biyo bayan fage kana surutan banza, to duk inda ku ka kai mun ita sai kun nemota yawwa" "Rufe mun baki munafukar tsohuwa ai duk munafurcin da ku ke haɗawa ya dawo kunnena, na ji labarin Najmeer ta dawo gidannan kuma an faɗa mun cewar an ga lokacin da ku ka fita tare, dan haka ki aje duk wani makirci ki fito mun da matata" "Kai Jabir ne sunanka ko waye? zan ci Ubanka anan gun na fika akuyanci, Mamu ka ke faɗawa wannan maganar?" Cewar Meera tana ɗaukar wani icce da ke gurin cikin masifa, ganin da gaske zata iya dukansa ne ya sa ya matsa da baya yana faɗin "Ku jirani zan dawo wallahi sai na ɗauki mataki a kanku, musamman ƴar tashar yarinyar nan marar kunya sai nayi maganinki" Ficewa daga gidan ya yi yana surutai kamar zararre. Meera kam ɗaki ta nufa da Mamu ba tare da ta koma bi ta kansa ba, har Meera ta yunƙura zata fita Mamu ta kama hannunta tana mai share ƙwallan da ya zubo mata "Ina zuwa ƴarnan Allah ya sa kema ba tafiya za ki yi ki barni ba" Mamu ta faɗa tana mai fashewa da kukan da take riƙewa. Da sauri Meera ta zauna tana faɗin "Aa ba tafiya zan yi ba Mamu, idan na tafi waye zai kula mana da ke? kuma ni bana da kowa a yanzu daga ke sai Najmeer iyayena sun rasu, zan iya cewa ku ne dangina, dan Allah ki daina kuka kar ki saka ni nima" Cikin sauke ajiyar zuciya Mamu ta ce "Allah ya jiƙan waɗan da suka riga mu gidan gaskiya, kuma Allah ya bayyana mana Najmeer a duk inda take cikin ƙoshin lafiya" Da ameen Meera ta amsa kafin suka cigaba da fira sama-sama kasancewar kowa da abin da yake tunani a ransa. Sai da aka kira sallar magrib kafin suka yi sallah Meera ta ɗora musu girgi, ba laifi jikin Mamu ya yi dama dan tana iya miƙewa amma babu ƙarfin jiki, wayar Najmeer kuwa sai kira ake amma ba bu me ɗagawa daga ƙarshe Meera ta kashe wayar. Wajen tara na dare ne suna zaune da Mamu a tsakar gidan sun yi jugum-jugum jiran ganin Najmeer amma shuru ka ke ji. Mamu ce ta ce "Nikam na fara tsorata sosai kan lamarinnan? anya kuwa ba Jamilu ne ya sace Yarinyar nan ba" Jin abin da Mamu ta ce ne ya sa Meera ɗagowa a firgice ta ce "Na san wanda ya sace ta" Itama Mamu a kiɗime ta ce "Waye ya sace mun Jikanya dan Allah faɗa mun" "Sultan Chief ne yaron hamshaƙin me kuɗinnan da ke GRA" "Chief..., wanda na sani me taimakon talakawannan?" "Ƙwarai kuwa shine, saboda shi muka baro gidan da mike har can ya zo da niyar kama Najmeer, na tabbata cewa shine ya sace ta" "Subhanallahi, me Najmeer ɗin ta yi masa yake son illata min ita?" Cewar Mamu a tsorace. Duk abin da ya faru Meera ta kwashe ta sanarwa Mamu har zuwansu nan gidan, sosai hankalin Mamu ya ƙara tashi dan ta san Chief me kuɗin gaske ne, duk abin da aka yiwa Najmeer baza ta iya ɗaukaka ƙara ba. Har Mamu ta buɗe baki da niyar magana suka ji ana buga ƙofar gidan da ƙarfi, cikin sauri ba tare da zargin komi ba suka miƙe tare da nufar ƙofar har suna rige-rigen isa. Meera ce ta buɗe ƙofa ai kuwa ta ji an doka mata abu a kai, nan take ta zube a sume,Mamu kuwa ture ta ƙasa aka yi kafin ta miƙe an rarumi Meera da ke kwance tare da shigewa adaidaita cikin sauri me adaidaitan ya bar unguwar. Ihu da kuka Mamu ta shiga yi amma ba wanda ya kawo mata ɗauki, sosai ta rinƙa kiran sunan Meera da Najmeer cikin mugun tashin hankali. Sai da aka yi tafiya me nisa da Meera kafin suka tsaya wani gida me ɗauke da ɗaki ɗaya, Jabir da ke bayan adaidaitar riƙe da Meera ne ya tallafota yana dariyar mugunta "Ni za ki nunawa barikanci? yau zan koya miki hankali kuwa". A ɗakin ya shige da ita sannan ya cewa me adaidaita ya tafiyarsa. Sai da ya duba ko'ina ba bu me ganinsa kafin ya faɗa ɗakin tare da rufo ƙofar. A lakacin Meera ta farka sai dafe kai take dan zafin da yake mata. Kallonta ta mayar kan Jabir da ke tsaye yana lashe baki, a firgice ta miƙe tsaye 'Kai Jabir me na yi maka ka kawo ni nan gurin?" "Auuuuu tambaya ki ke? yanzu kuwa zan ba ki amsa ƴammata" Ya faɗa yana fara cire kayan jikinsa, Meera na ganin haka ta fara ja baya tana faɗin "Kar ka ƙaraso ni wallahi zan tara maka jama'a" "Ai ko duniyar nan za ki tara mun sai na aikata abin da nake so da ke sannan na kora ki waje tsirara" Cewar Jabir yana faɗawa kan Meera cikin rashin imani. ........................ A ɓangaren su Sultan kuwa ba ƙaramar azaba ya ke gallawa Najmeer ba, rana ɗaya ta canja kamanni ta fita a hayyacinta, duk bayan awa ɗaya sai ya shiga ya yi mata dukan tsiya. Yawan shige da ficen da yake ne ya sa Junaid ya zuba masa ido dan ya kasa gane abin da ke faruwa da ƙanin nasa. Yanzu haka zaune suke kowa na tunanin da ke ransa, Mom na gefe tana kallon program ɗinta, sai Sultan da ya sha'afa da kallon wayarsa da alama ba alkhairi yake kallo ba dan sai matse ƙafa yake har Junaid ya lura da shi, ganin yanda Junaid ya ƙura masa ido ne ya sa shi miƙewa tare da nufar ɗakinsa a lokacin ƙarfe tara na dare ta kusa bugawa, room ɗinsa ya nufa yana mai danna key, ya jima a ciki kafin ya fito sanye cikin wasu kafuran kayan bacci masu ɗaukar ido, a steps ya ci karo da Junaid na ƙoƙarin zuwa nasa ɗakin, ko kallonsa Sultan be yi ba ya sauko abinsa. Sai da Junaid ya ƙare masa kallo kafin ya ce a ransa, tabbas gurin Sumayya zai tafi kuma ba zan bari hakan ta faru ba. A parlour Sultan ya sami Mom na shirin shigewa, cikin shagwaɓa ya ƙaraso yana mai faɗin "Mom har kin gama kallon ne?" Itama murmushin ta yi tana mai shafa fuskarsa "Yes bacci nake ji kaima ya kamata ka kwanta ko za ka samu zuwa aiki gobe" "Yes Mom but......" "But....what Son?" "Zan kwana a ɗakin waccan yarinyar" Ɗan zaro ido Mom ta yi "Meyesa za ka kwana a ɗakinta? kana son asirinmu ya tonu ne?" Junaid da ke laɓe ne ya dafe saitin zuciyarsa, wai me ke faruwa a gidannan ne. Ya tambayi kansa, ganin ba bu me amsa masa tambayar ne ya sa shi cigaba da saurarensu. Sultan kuwa kama hannun Mom ɗin nasa ya yi "Ba bu wanda zai gane Mom, kawai na rana ɗaya ne ina son na keta mata haddi dan wallahi ba zan raga mata ba, na sha wahala kafin na sameta dan haka sai ta ɗanɗani azabar da na tanada mata" Ya ƙarasa maganar yana mai nufar upstears. Mom kam bata yi yunƙurin hana sa ba, dan bata ƙaunar ɓacin ransa ko kaɗan. Junaid na ganin Sultan ya nufo sama ne ya yi saurin lafewa inda ba zai gansa ba, cikin sanɗa ya rinƙa bin bayansa har hawa na huɗu, da mamaki Junaid ya ƙara zaro ido har Sultan ya shige ɗakin, da ƙarfin tsiya Junaid ya faɗa ciki dan ganin abin da ake ɓoyewa. Cikin firgici Sultan ya kunna hasken ɗakin tare da sauke idanunsa kan yayan nasa, Junaid kuwa yarinyar da ke kwance cikin mawuyacin hali yake kallo, duk gashin kanta a baje ya rufe mata fuska shiyasa be bashi damar ganin fuskar tata ba. Wani irin girgiza ɗakin ya yi wanda ya sa Sultan da Junaid zubewa ƙasa kamar waɗan da aka jefar, sosai ɗakin ke girgiza komi na ɗakin ya tashi saman iska tare da fitar da wata ƙara me rikitarwa, cikin mugun firgici Sultan ke kallon Najmeer da ke saman iska tana mai fitar da wata irin dariya me tada hankali, shi kansa Junaid ya tsorata matuƙa. Cikin mintunan da basu wuce biyu ba Najmeer ta rikiɗe zuwa wata irin jibgegiyar Mage fara tasssss, duk jikinta tabon duka ne, idanuwanta blue masu ban tsoro. Faratanta kuwa zara-zara kamar reza, bakinta na fitar da wani irin kuka me mugun rikita me saurare. Cikin mugun gudu Magen ta daka tsalle sama tana mai dira gaban Sultan. *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P. 6 Kafin ta yi wani yunƙuri Sultan ya rikiɗe zuwa wata jibgegiyar Kada me ban tsoro, girman Kadar da tsayinta kuwa ya gauraye gurin. Junaid da ke gefe tuni ya sume ganin ƙanin nasa ya sauya halitta zuwa mummunar Kada me jajayen idanu, cikin fusata Magen da Kada su ka nufi juna tare da fara kaiwa junansu yanka da faratan hannayensu, sosai su ke faɗan tamkar baza su daina ba, tsalle ɗaya Magen ta yi tana mai hawa bayan Kadan cikin zafin nama ta yanki Kadan a wuya da mugun ƙarfi, zafin yankan ne ya sa Kadan ɗaga jelarsa ya doki Magen a kafaɗa, ji ka ke timmmm Magen ta faɗo ƙasa cikin mawuyacin hali, kafin Kadan ya ɗago tuni Magen ta ɓace ba bu ita ba bu alamunta. Kadan kuwa ya rikiɗe ya koma Sultan da wuyansa ke fitar da jini jiri na ɗibarsa. Da ƙyar ya ƙarasa gurin da yayan nasa ke kwance, da hannu ɗaya ya saɓa shi kan kafaɗarsa suna mai barin ɗakin. Be diresa a ko'ina ba sai room ɗinsa, kan bed ya kwantar da shi yana mai gyara masa kwanciya, jinin da ke fita a kafaɗarsa ne ya sa shi zamewa ƙasa a sume, kasancewar ba ƙaramin yanka Magen ta masa ba, a gafen gurin kana iya ganin dafin Magen blue. Junaid be farka ba sai gurin ƙarfe ɗaya na dare, a firgice ya tashi bakinsa ɗauke da addu'ar da duk ta zo masa, a ransa yana godiya ga Allah da ya sa mafarki ne ba gaskiya ba, kansa da ke juya masa ya dafe yana mai kallon inda Sultan ke kwance cikin jini, cike da dauriya gami da taurin rai ya ƙaraso tare da tallafosa kan cinyarsa, daidai lokacin da Sultan ya saki nannauyar ajiyar zuciya, "Bro......" Ya faɗa yana lumshe ido, bakin Junaid na rawa ya ce "Sultan....? dama abin da na gani ba mafarki ba ne?" "Bro wani abun ya faru ne?" Cewar Sultan yana tashi zaune. "Kana nufin wannan jinin da ke fita a gefen wuyanka ruwa ne ba jini ba?" Junaid ya faɗa a suface. Saurin shafa gurin Sultan ya yi, sai ga jini kan hannunsa har ya fara daskarewa. Miƙewa ya yi tare da ƙarasawa gurin mirrow, daga gefen wuyansa har ta bayan duk yanka ne ga niji na ɗiga kaɗan-kaɗan. Matsawa ya kuma yi gun Junaid yana mai jijjiga shi da ƙarfi "Waye ya mun wannan yankan? me ya sameni kuma ya aka yi na shigo ɗakinka?" Duk a lokaci ɗaya Sultan ya jefowa Junaid waɗannan tambayoyin, a harzuƙe Junaid ya shige toilet ba tare da ya amsa masa ba, ganin haka ya sa Sultan barin ɗakin ransa a mugun ɓace, gaba ɗaya ya kasa tuna abin da ya faru da shi. Junaid kuwa ruwa ya sakarwa kansa yana mai tunano lokacin da Sultan ke rikiɗewa zuwa Kada, sosai hankalinsa ya ƙara tashi idaunwansa sun ƙanƙance, shin me yake shirin faruwa ne, ya tambayi kansa a zuciya. Ya jima a haka kafin ya yi wanka tare da ɗauro alwala. ..................... A ɓangarensu Meera kuwa tana ganin da gaske Jabir zai iya aikata abin da ya faɗa ne ya sa maganganun da Najmeer ta faɗa mata a ranar ya faɗo mata rai, cikin ƙarfin hali ta chakumo Jabir gami da buga kansa kan ginar ɗakin, azabar da Jabir ya ji ne ya sa shi sakin mugun ƙara yana mai dafe kansa. "Wayyyyo Allah ta kasheni". Meera na ganin ya faɗi ta buɗe ƙofar da gudu ta fice. Gudu take sosai ta rasa inda zata tafi, yanzu haka baza ta gane wacce unguwar ce ta su Najmeer ba, dan haka ta nufi kan titi cikin layi da neman mafita. Sai da ta yi tafiya me nisa kafin ta hau kan titin unguwar, me adaidaita ɗaya ta samu a hanya dan haka ta shige tare da faɗa masa unguwar da zai kai ta, Meera ta san cewa bata da wata mafita a halin yanzu face komawa gurin Maleek, a ƙofar gidan me adaidaita ya sauketa, har ta juya da niyar shigewa gidan ta ji ya ce "Malama kuɗin fa?" Zare ido Meera ta fara alamun rashin gaskiya "Amm....am.... am so sorry wallahi bana da ko sisi" "Kutumar uba, ai kuwa baza ta saɓu ba, har kin isa na kawo ki a kyauta dan Uwarki" Fitowa ya yi tare da kama rigarta yana zuba ashar kamar ba musulmi ba, Meera kuwa sai haƙuri take basa amma tamkar ƙara zuga shi take, kamar daga sama ya ji an ce "Ga kuɗinka ka sake mata riga......" Wata irin murya suka ji me ban tsoro da firgita me saurare, ba shiri me adaidaita ya saki rigar Meera yana kalle-kalle, sai kuma ya kalli hannunsa da kuɗi ke ciki ba tare da ganin wanda ya ɗora masa kuɗin ba, da mugun gudu ya shige adaidaitar yana barin arean. Meera da bata san abin da ke faruwa ba ne ta ji ana jan hannunta zuwa cikin gida sai dai bata ga kowa ba, ihu ta fara tana janye hannunta gami da sakin numfashi da ƙarfi dan ta tsorata matuƙa, har cikin gidan aka shige da ita wanda ihun da take ne ya farkar da Maleek, ba shiri ya fito yana mitsike ido alamun bacci kwance kan fuskarsa. Ganin yanda Meera ke ihu da maganganu ne ya sa shi ja baya a tsorace, daga nesa ya ce "Ke Meera uban me ki kewa ihu haka?" Meera da duk hankalinta baya kanta ne ta kalli Maleek cikin firgici "Na shiga uku Maleek ka taimaka mun, za su cire mun hannu wallahi ba ni ke tafiya ba, bansan waye ke ja mun hannu ba". Jin abin da Meera ta ce ne ya sa Maleek runtumawa ɗaki da gudu yana banko ƙofa. Part ɗin da Najmeer ta kama aka nufa da Meera, a lokacin har ta fara ɗauke numfashi. Cikin mintin da be fi ɗaya ba Najmeer ta bayyana riƙe da hannun Meera da ke ƙoƙarin sumewa, Meera na arba da Najmeer ta ƙara sakin ƙara me rikitarwa wadda ta sa Maleek ƙara shigewa ƙasan gado domin ceton kansa. Najmeer kuwa ta zube ƙasa tana sakin numfashin wahala, jikin Meera na rawa take nuna Najmeer da hannu "Najmeer.........., Aljana.....?" Meera ta faɗa bakinta na karkarwa. Sai da Najmeer ta kai kusan mintuna biyar a hakan kafin ta ɗago da ƙyar tana kallon Meera, sai kuma ta sakar mata murmushi tana faɗin "Lafiya ki ke kallona haka?" Meera da duk hankalinta baya kanta ne ta ce "Lafiya ƙalau....." "Amma ya naga jikinki sai rawa yake? ko ba ki da lafiya ne" "No lafiyata ƙalau, ke ce dai marar lafiya" Meera ta faɗa a tsorace. "Ni kuma? sai dai Mamu ko, itama ai jikinta ya yi sauƙi tun da har ta samu bacci" Najmeer ta faɗa tana nuna bed ɗin da ke ɗakin, cikin sauri Meera ta maida kallonta kan gadon ai kuwa ta yi arba da Mamu kwance tana sharar bacci, har Meera zata saki ihu sai ta ji bakinta ya kasa motsawa tamkar an ɗinke shi. Murmushi Najmeer ta sakar mata a karo na biyu tana mai miƙewa tsaye "Shhhhhhhh, lokacin bacci ya yi ni zan shiga wanka, gobe zamu bar gidannan". Ba tare da jiran abin da Meera zata kuma cewa ba Najmeer ta nufi toilet dan watsa ruwa. Firgici, tashin hankali, ruɗani, duk sun mamaye Meera tare da tarin tambayoyin da ta kasa bawa kanta amsa, sai yanzu take tuna kalmar nan da Najmeer ta taɓa faɗa mata ranar da suka fara haɗuwa, kar ki damu a sannu za ki san ko wacece ni. Tana zaune har Najmeer ta fito ɗaure da haɗaɗɗen tawul, daga kafaɗarta kuwa shayun duka ne sai wasu wurare a jikinta da duk tabon belt ne, hannu ta ɗaga sama cikin wata irin murya me rikitarwa ta fara faɗin wasu kalamai, Meera kam wannan karon motsin kirki ma kasawa ta yi, sai da Najmeer ta jima a haka kafin ta shafa hannunta gurin da duk wani tabon ciyo ke kwance, lokaci ɗaya ciyon ya ɓace tamkar ba abin da ya sameta, hatta dukan da Sultan ya rinƙa yi mata sai da tabon ya ɓace. A natse ta shirya cikin kayan bacci milk masu kyau da sheƙi, sai da ta feshe jikinta da turarukka masu ƙamshin daɗi kafin ta saka ƙaton hijab ɗinta sannan ta rama sallar da ake binta, duk abin da take Meera na zaune tana kallon ikon Allah har ta kammala, addu'a ta yi sosai kafin ta koma kan ɗayan bed ɗin ta kwanta. Sai a lokacin Meera ta iya miƙewa kamar wadda ƙwai ya fashewa, bakin ƙofa ta nufa da niyar fita ta tsinkayo muryar Najmeer na faɗin "Ina zuwa Meera?" Bakin Meera na rawa ta ce "Gurin Maleek?" Bushewa da dariya Najmeer ta yi har da riƙe ciki "Maleek kuma? Malama ki zo ki kwanta idan kina son zaman lafiya" Jin abin da ta ce ya sa Meera komawa ta kwanta nesa da inda Najmeer ke kwance, tana mai karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. Washe garin ranar tun asuba har ƙarfe tara ake tashin hankali tsakanin Mamu da Najmeer, sosai Mamu ke faɗa da tambayar waye ya kawota gidannan, Najmeer kam sai dai ta yi dariya dan rasa amsar da zata bawa Mamu ta yi. Ganin Najmeer ta shareta ne ya sa dole Mamu yin shuru ba dan tana so ba. Sai da suka gama tattara komi na gidan wanda mallakinsu ne kafin Najmeer ta nemo masu kwashe kaya. A harabar gidan suka ci karo da Maleek na ƙoƙarin fita, wani mugun kallo ya watsawa Najmeer "Ke kam daga ganinki ke mayya ce, tun da ki ka shigo rayuwarmu na daina jin daɗin duniyar" Har Meera ta buɗe baki da niyar magana Mamu ta yi saurin katseta da faɗin "Barshi kar ki ce masa komi, kai kuma ka bi duniya a sannu, ko ba bu komi a tare da ita muke be dace ka jefeta da munanan kalamai irin haka ba" "Mtsssss ke kuma fa? kun ga wata munafukar tsohuwa, ko kema karuwa ce?" Cewar Maleek yana dariya. A fusace Najmeer ta ɗago rikitattun idanuwanta da suka koma blue, da sauri Mamu ta riƙe mata hannu tare da janta zuwa wajen gidan. Maleek kuwa ya shiga zage-zage kamar ɗan tujara "Ai sai ki barta na ga abin da zata mun, shegu haihuwar wayyo Allah, yooo ni akwai wanda nake tsoro ne a yanzu? idan ta isa ta zo mu gwada ƙarfi, wallahi da rabon na kakkarya banza" Najmeer na jin duk abin da yake faɗa, amma Mamu ta ƙi sake mata hannu har suka shige motar kwasar kayan. Tun da suka fara tafiya Najmeer ke musu kwatancen unguwar da za su tafi har suka isa. Daga Mamu har Meera mamaki ne ya kama su ganin haɗaɗɗen gida me masifar kyau da ɗaukar ido, fitowa motar ta yi sannan ta buɗe gate ɗin gami da bada umarnin a shigo da kayan, haka kuwa aka yi cikin ƙanƙanin lokaci komi ya yi need, kuɗi ta biya masu motar suka kama gabansu. Cikin gidan Najmeer ta ja su tana mai nuna musu ko'ina da kuma yanda tsarin yake, kasancewar Meera wayayya ce ya sa kayan aikin gidan be bata wahala ba, kan kujerun ɗakin masu masifar kyau suka baje, kallon Najmeer Mamu ta yi ciki alamun tambaya "Najmeer gidan waye wannan? ko sayar da mu ki ka zo yi?" Dariyar da ke ƙara mata kyau ta yi, "Haba Mamu wannan fa gidana ne, halak malak aka mallakamun shi, idan ba ki yarda ba sai na nuna miki takaddun gidan" "Gidanki....?" Meera da Mamu suka haɗa baki. "Yes gidana, kuma har abada zai zauna a matsayinsa na gidana" Mamu ce ta ce "Yanzu da kuɗin haram ki ka saye wannan danƙareren gidan Najmeer? subhanallahi na shiga uku ni Mamu" Saurin katseta Najmeer ta yi da faɗin "Kin ga please kar ki fara dan Allah, wannan gidan ba da kuɗin haram na saya ba, asalima kyautarsa aka bani, ina buƙatar kowannenku ya je nasa ɗakin ya huta zuwa anjima zan yi baƙo, but bana buƙatar ki fito waje Mamu, duk abin da ki ke buƙata zan kawo miki kafin na samo mana ƴar aiki" Najmeer ta ƙarasa maganar tana hawa sama. Da kallo suka bita har ta shallewa ganinsu. Jiki a sanyaye Meera ta matsa gun Mamu tana faɗin "Wai nikam Najmeer mutum ce kuwa?" A rikice Mamu ta rufewa Meera baki tana mai girgiza mata kai alamun ta yi shuru, hakan ya sa Meera barin zancen ba dan tana so ba. Sai wajen ƙarfe biyar na yamma ta fito cikin wata arniyar riga daidai cinyarta, kayan sun masifar yi mata kyau musamman yanda shape ɗinta ya bayyana, gashinta ta ɗaure shi yana rito a baya, kunnenta ɗauke da waya da alama magana take, Meera na bayanta ɗauke da basket na kayan motsa baki. A babban parlour suka shirya kayan cikin tsari da ɗaukar ido, ba jimawa Alhajin ya iso harabar gidan, cike da makirci Najmeer ta fito tana ɗaga masa hannu, ko kunyar Meera da ke wajen be yi ba ya rungumota yana mai manna mata kiss a kumatu "Shalelena wallahi na yi kewarki sosai, yanzu ne na ƙara tabbatar da cewar ke ta musamman ce" Fari da ido Najmeer ta yi sannan ta shafo gefen fuskarsa "Godiya nake my Alhaj, nima kewar ce ta sa na baro Dubai dan kawai na haɗu da kai" Sosai kalamanta ya yi masa daɗi, sai a lokacin ya lura da Meera da ke kallon ikon Allah, cike da mamaki suka gaisa kafin Najmeer ta masa iso zuwa parlourn. Meera na gefe tana kallon yanda Najmeer ke zuba makirci da kalaman soyayya kamar daga gareta aka fara sarrafosu. Sun jima a hakan suna fira, kayan marmarin da drinks ɗin ma kaɗan ya sha. Wata ƴar bag da ya shigo da ita ya miƙawa Najmeer yana murmushi "Shalelena ga wannan ko? i know you will like it" Itama murmushin ta sakar masa tana buɗe bag ɗin, waya ce ƙirar iphone 15promax sai ɗayar 13promax, ɗayar ledar kuwa agogo ne na gold me masifar tsada irin na ƴaƴan manya. Cikin farinciki Najmeer ta ƙara ƙanƙame shi, "Thank you so much, kamar ka san ina buƙatar agogo, but wannan be mun ba anjima zamu tafi na zaɓi wanda nake ra'ayi, and ga friend ɗina itama ya kamata a saya mata" "Ba ki da matsala as you wish, ai ke ɗin kin wuce hakan" Jin saukowar mutum ne ya sa dukkaninsu kallon gurin, Mamu ce sanye cikin kayan da Najmeer ta bata, atamfa ce me kyau da tsada sai mayafi kalar atamfar, sosai kayan suka yi mata kyau, zaro ido Meera da Najmeer suka yi, dan sai da Najmeer ta hana mata fitowa dan kar ta basu kunya. Ƙarasowa Mamu ta yi tana washe baki ganin kayan marmari zube kan tire, da sauri Alhajin ya rusuna yana gaisheta, ba tare da Mamu ta amsa masa ba ta ɗauki lemu ɗaya tana zama kusa da Najmeer "Lafiya ƙalau ɗannan ya gidan?" Alhajin na sunkuyar da kai ya amsa da "Alhamdllh" Ganin yanda Mamu ke wulla ido gashi tana neman yarfasu ne ya sa Najmeer miƙewa a fusace ta damƙo hannun Mamu tana faɗin "Keeeee rashin kunyar taki ta ƴan aiki har ta kai haka? waye ya ba ki izinin shigowa har parlourna gaban baƙona, kuma ki ka saka mana ƙazamin hannunki cikin abincinsa" Meera ce ta karɓe zancen da faɗin "Hmmm gaskiya wannan tsohuwar akwai rigima, shiyasa na ce miki ki kawo matashiya wadda zata iya aiki cikin natsuwa amma kin kwaso mana me taɓin hankali" Daga Alhajin har Mamu kallon su Najmeer suke, musamman Mamu da duk tsoron Allah ya kamata, har ta buɗe baki da niyar magana sai ta ji tamkar an saka mata makulli, duk iya ƙoƙarinta na ganin ta yi magana amma ina, Meera ce ta kama hannunta ta nufi sama da ita, "Am sorry Alhaj ka san halin talakawa da rashin wayewa" Cewar Najmeer tana zama gefensa. "Auuu kar ki damu, ai haka wasu suke basa sanin inda ke musu ciyo daga zaran sun fara tsufa" Ba ƙaramin zafi maganar ta yiwa Najmeer ba, amma sai ta dake tare da faɗin "Sosai kuwa, dole zan canja ƴar aiki, yau ina ganin anan gidan zamu kwana, anjima da ƙarfe goma na dare ka shigo sai mu tafi na zaɓi kayan da nake so ko?" "Yes ma, kuma ina son ayi mun wanka na ɗaukar hankali, amma ina son na faɗa miki wata magana idan baza ki damu ba" "Ina sauraronka" Najmeer ta faɗa tana mai danna wayarta, "Aurenki nake so" Wani irin tari ne ya ƙwace mata, sai da ta gama kafin ta ɗago blue eyes ɗinta masu firgitarwa ta ce "Aurenaaaaa?" "Eh aurenki nake so, wallahi na kamu da matuƙar ƙaunarki, ki amince mun na tura gidanku a yi magana" Gaban Najmeer ne ya shiga dukan uku-uku, tabbas asirinta ya kusa tonuwa, da farko ta masa ƙaryar family, sannan ta ɓoye masa cewar ita matar aure ce. "Tunanin me ki ke haka? duk abin da ki ke so zan miki ko menene, matana biyu ina son ki zamo ta uku, idan ma kina son a watsa su waje ne sai ayi yanda ki ke so" Waro ido Najmeer ta yi "Waneni, su ma ai iyaye ne, bana buƙatar a kori ɗaya daga cikinsu amma ina buƙatar ka bani lokaci na yi tunani" "Baza ki iya auren me shekaruna ba ne?" "Ba haka ba ne ka san komi sai da shawara, ina ganin kamar Dad ɗina zai kawo mana matsala" "Kar ki samu matsala da shi, idan har kuɗi na aiki ba abin da zai hana ya bani ke" "Amma ka san cewa Dad ɗina ya fi ka dukiya da matsayi, baza ka iya sayensa da kuɗi ba, dukiyarka tamkar ƙwarar zarra ce ga dukiyar mahaifina" Jin abin da ta ce ya sa jikin Alhajin yin sanyi, dan ya san idan har Dad ɗinta ya fishi kuɗi da wahala ya aura masa ita. "Zan iya ganin Dad ɗin naki a gobe" "Why not, Allah ya kai mu goben" Cewar Najmeer tana miƙewa, "Ni zan shiga daga ciki idan ka gama zaka iya tafiya" Bata jira abin da zai ce ba ta haura sama cikin tafiyarta da ke ƙara mata kyau. Alhajin kuwa wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana danna wata number, sai da wayar ta yanke ba'a ɗaga ba, ƙara dannawa ya yi amma sai da ta kusa yankewa kafin aka ɗaga, cikin girmamawa Alhajin ya ce "Allah ya ƙara maka nisan kwana ta shigo hannu, amma mahaifinta ne kawai zai bamu matsala" Daga can ɓangaren ba ka jin abin da ake faɗa, amma Alhajin ya yi shuru da alama magana ake, sai da ya kai kusan mintuna biyu suna waya kafin ya yi masa sallama tare da ficewa daga gidan. .......................... A masifance Sultan ke saukowa daga uptairs yana kiran duk ƴan aikin da ke gidan, gaba ɗaya hankalin kowa ya tashi jin yanda yake ɗaga murya. Mom da ke part ɗinta ne ta fito dan ganin abin da ke faruwa, a babban parlour ta sami Sultan zaune kan kujera me zaman mutum ɗaya, duk masu aikin na zageye da shi sun rusuna jikinsu sai rawa yake. Sanye yake cikin suit blue me kyau sai glass ɗin da ya ɗora gaban aljihun rigar tasa, gashin kansa ya sha gyara sosai, ba bu wani alamu da ya nuna akwai abin da ya faru da shi a daren jiya, kana ganinsa ka san dawowarsa daga aiki kenan, cikin ɓacin rai ya ce "Waye ya shiga room ɗin da na hana kowa shiga?" Cikin alamun tsoro kowa ya ce bashi ba ne, "Sultan wanne room ka ke magana?" Mom ta faɗa tana dafa kafaɗarsa, cikin ɗaga murya kamar ba mahaifiyarsa ba ya ce "What are you saying Mom? kamar ba ki san ɗakin da nake magana ba, gaba ɗaya na duba amma banga waccan yarinyar ba" Rarrashinsa Mom ta shiga tana mai faɗin "Kai a cikinku waye ya taimaka mata har ta fita, idan ba ku faɗa mun ba wallahi zan ɗauki mataki me tsauri game da ku" Sumayya ce ta yi saurin cewa "Wallahi Hajiya ba bu wanda ya san yarinyar da ku ke magana, asalima tun jiya ba wanda ya haura hawa na huɗu" Maganganun Sumayya ba abin da suka ƙarawa Sultan face baƙin ciki da ɓacin rai, a mugun hasale ya miƙe tare da ɗauketa da mahaukatan maru "Ke dabba shashasha ke ce me bakin magana ko? dallah ku ɓace mun da gani kafin na koya muku hankali" Tun kafin ya gama rufe baki kowa ya arce. Dafe kansa ya yi yana mai zama gefen Mom "Sorry Sultan insha Allah zan sa a dawo maka da ita a duk inda take" "How Mom? ta ri ga ta gudu bansan yanda aka yi ta fice gidannan ba tare da wani ya ganta ba" Har Mom ta buɗe baki da niyar magana Sultan ya ɗaga mata hannu "No Mom bana son jin komi a yanzu, ina buƙatar hutu" Be jira abin da zata ce ba ya haura sama cike da ƙasaita. Junaid da ke tsaye bakin ƙofa ne ya sauke ajiyar zuciya, ƙarasowa daga ciki ya yi tare da zama kusa da Mom yana mai riƙe hannunta "Kin ga abin da Dad ke magana ko, wannan shine dalilin da ya sa Dad yake yiwa Sultan faɗa, yanzu ki kalli yanda yake miki magana kamar ba mahaifiyarsa ba, gaba ɗaya ba bu tarbiyya a ciki" "Look Junaid waya faɗa maka Sultan baya da tarbiyya? ransa ne kawai ya ɓaci amma zuwa anjima zai sauko" "Amma...." "Shhhhhhhh....., yanzu ka dawo daga gun aiki ka je ka hutu" Ba musu Junaid ya nufi ɗakinsa dan ba zai iya jayayya da Mom ɗin nasu ba. Har zai nufi part ɗinsa sai kuma ya karya hanya zuwa part ɗin Sultan, daga bakin ƙofa ya fara jin maganganu ƙasa-ƙasa kamar ana meeting, be ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya rinƙa jin gurnani kamar na Zakuna da kuma kuka irin na jarirai, hannun Junaid na rawa ya murɗa ƙofar ɗakin, kamar daga sama ya ji an doko shi ji ka ke timmmm ya zube ƙasa, cikin azaba Junaid ya ce "Ya Allah......." Yana dafe bayansa da ke masa mugun zugi, ɗagowar da zai yi suka haɗa ido da Sultan tsaye yana sakar masa murmushi "Bro lafiya dai na ganka a ƙasa" Hannu ya kai da niyar taimaka masa Junaid ya galla masa harara yana miƙewa cike da jarumta, ba tare da ya kuma kallon inda yake ba ya bar gurin cikin mugun al'ajabi. Sultan kuwa ya shige ɗakinsa tare da rufo ƙofa. Tun da Junaid ya shiga ɗakinsa ya kasa samun natsuwa, gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake. Ya rasa abin da ke shirin faruwa a gidan, kuma ba wanda ya faɗawa zacen ƙanin nasa, sai da ya watsa ruwa kafin ya shirya cikin ƙananan kaya masu kyau, yau ko turaren da yake sakawa ma be tsaya sakawa ba ya sauko ƙasa dan sanarwa Mom abin da idanuwansa su ka gani duk abin da zai faru ya faru. A dianing ya same su, Sultal kuwa na video call da alama da ƴar London yake waya dan har Mom sai da suka yi magana da ita, fuskar Junaid ɗauke da damuwa ya zauna tare da ƙara gaida Mom, cikin kulawa ta ce "Junaid lafiya na ga kamar ba ka cikin natsuwa?" Murmushin yaƙe Junaid ya saki "No Mom lafiya ƙalau kawai gajiya ce ke damuna" Gyaɗa kai Mom ta yi alamun gamsuwa. Maleeka da ke video call da Sultan ta ce "Love waye nake jin muryarsa, voice ɗinku ya so ya yi iri ɗaya" "Brother Junaid kenan wanda nake ba ki labari" "Wow can i talk to him?" "Yeah sure love gashi ku gaisa" Sultan ya faɗa yana miƙawa Junaid waya, ba musu Junaid ya karɓa, ganin shigar jikin Maleeka ne ya sa ya ɗan kalli Sultan yana mai girgiza kai, Maleeka kuwa ta gama ruɗewa da ganin mahaukacin kyan da Junaid ke da, sai take ganin kamar ya fi Sultan ɗin nata kyau, bakinta har rawa yake gurin faɗin "Hi dear how are you?" Sai da Junaid ya daidaita natsuwarsa kafin ya haɗe fuska alamar ba rahama kafin ya ce "Fine how's London?" "London is amazing when you guys will come?" Cike da gajiya da zancen Junaid ya cije pink lips ɗinsa yana faɗin "Very soon, kema kin kusa zuwa saboda ƙanina zai dawo mana da ke gaba ɗaya" Ɗan taɓe baki Maleeka ta yi tana mai kashe masa ido "Hakane ni kaina na matsu na dawo Nigeria" Duk maganar da suke idanun Junaid na ƙasa dan baya iya kallon shigar da ke jikinta, Maleeka kam ta ƙura masa ido ko ƙyaftawa bata yi, sai da ta gaji surutunta Junaid be amsa mata ba, daga ƙarshe ya miƙawa Sultan wayar. Ba wani abinci Junaid ya ci ba dan yanzu ba abin da ke masa daɗi a baki, bayan sun gama ne ya maida kallonsa kan Mom yana gyara zama "Mom ina son mu yi magana idan ba damuwa" "Okay ina jinka" Cewar Mom tana kallonsa. Sallamar da suka ji ne ya hana Junaid faɗin abin da ke ransa, Surayya ce da Mommynta sai yayanta da ke bayansu fuskarsa ɗauke da murmushi, Junaid na ganinsa ya miƙe cikin farinciki suka rungume juna, bayan sun gaisa ne kowanne ya koma kan dianing, Junaid da Yayan Surayya me suna Imran kuwa suka nufi part ɗinsa. Sultan da tun da ya gaida Mommyn Surayya kansa ke ƙasa ne ya miƙe cike da gadara ya nufi sama, kamar wadda aka tsikara ta tashi tana faɗin "Hi Babe wannan shan ƙamshin fa?" Cewar Surayya tana matsawa kusa da Sultan. Ko kallon inda take be yi ba ya nufi room ɗinsa, ai kuwa ta rufa masa baya tana surutu. Mommynta me suna Hajiya Habiba ce ta ce "Hmmm Surayya ikon Allah, anya yarannan ba auren dangi za'ayi musu ba" Mom na jin abin da Hajiya Habiba ta ce ta haɗe fuska kamar wadda bata taɓa dariya ba "Uhmmm ai Sultan ya fitar da wadda zai aura, im banda abinki Habiba kin san cewa ban son auren dangi ko kaɗan ɓata zumunci yake yi" Cikin mamaki Hajiya Habiba ta ce "Salma kenan, ke yayata ce uwa ɗaya uba ɗaya amma ki ke gudun haɗa zuri'a da ni, ina laifin ki ce Sultan ya fitar da matar da zai aura ai ba sai kin nuna min ba ki son haɗin aurensu ba, imma ba Surayya da shegen nacin tsiya ba a kullum sai an wulaƙantata amma kamar marar zuciya" "Nima shi na gani sai nacewa yaro take, ta je ta nemi wani mana ko za'a dace" Ba ƙaramin zafi maganar ta yiwa Hajiya Habiba ba, amma sai ta saki murmushin da ya fi kuka ciyo "Allah ya sa mu dace, wai ina Daddyn Junaid ɗin ne ko an fita ne?" "Ya tafi neman na halak" Mom ta faɗa taƙaice. Sanin halin Ƴar uwar tata ne ya sa Hajiya Habiba canza wata firar duk da cewar ranta ya ɓaci sosai. Junaid da Imran kuwa a room suka baje suna firar yaushe gamo, sosai Imran ya gane ɗan uwan nasa na cikin damuwa, Imran fari ne amma ba can ba, ba laifi akwai kyau da ɗaukar wanka ga ibadah sosai shiyasa suke shiri da Junaid, kallonsa ya maida kan Junaid yana faɗin "Junaid faɗa mun damuwarka ko zan iya taimakonka da shawara" Ajiyar zuciya me ƙarfi Junaid ya sauke yana dafa kafaɗar Imran, cike da miskilanci ya ce "Imran ina cikin damuwa gaskiya, kuma wannan ba maganar ɓoyewa ba ne" Cikin natsuwa Junaid ya kwashe duk abin da ya faru a daren jiya ya shaidawa Imran, a mugun firgice Imran ke saurasonsa har ya dasa aya. Sun kai kusan mintuna uku ba wanda ya kuma cewa uffan kafin Imran ya ce "Zan iya taimaka maka Mom ta ga asalin wanene Sultan, amma bayan haka banada wani taimakon" Murna fal a ran Junaid ya ce "Yaya kenan hakan zata faru?" "Akwai addu'ar da zan ba ka wadda zaka karanta cikin gidannan anjima da dare, ina shaida maka cewar ba Sultan ba hatta wannan Magen sai ta zo gidannan, ina ganin akwai wani sirri da ke tsakanin Magen da Kadan" Jinjina kai Junaid ya yi kafin ya ce "Na gode sosai Imran, insha Allah zan aikata kuwa saboda Mom ta san abin da ake ciki" Addu'ar Imran ya rubuta masa a takadda har ƙarshe, sannan suka cigaba da fira. A ɓangaren Sultan kuwa yana shiga ɗakinsa Surayya ta rufa masa baya tare da rungomosa tana mai sauke ajiyar zuciya, wani irin yanayi ne ya fara shigar Sultan wanda hakan ya hana shi dakatar da Surayya ga abin da take ƙoƙarin yi. Ita kuwa tana ganin Sultan be dakatar da ita ba ya sa ta ƙara shigewa jikinsa tana mai shafo ƙirjinsa a hankali ta ce "Ina sonka Sultan......." Yanda ta furta sunan ne ya sa Sultan janyota zuwa gabansa, da ƙarfin tsiya ya matseta a ƙirjinsa har sai da ta saki ƙara. Mazaunanta ya shafo yana ɓata fuska "Mtsss wai ina kayan da maza ke buƙata anan? wallahi Surayya ba ki da duk wani abin da zan soki saboda shi, asalima aurena ya kusa, daga Dad ya dawo ƙasar waje zamu tafi ayi bikina" Ya ƙarasa maganar yana haɗe bakinsu, hakan ya sa Surayya danne kukan da ke ƙoƙarin zo mata, sosai yake kissing ɗinta har suka zube kan bed, sai da ya gama yagalgalata kafin ya yi jifa da ita gefe yana mai sauke numfashi, cike da jaraba Surayya ta koma jikinsa tana mai fashewa da kuka "Haba Sultan yanzu kana nufin baza ka aureni ba?" "Eh ba zan aureki ba, kuma bana da ra'ayin auren mata biyu" "Haba Sultan......" "Get out please" Ganin zata sake magana ne ya sa shi daka matsa tsawa "Na ce ki fita before na canja miki kamanni" Da gudu Surayya ta fice tana kuka. Dafe mararsa ya yi da ƙarfi jin yanda take juya masa, rabonsa da mace tun da ya dawo Nigeria, sosai zufa ke karyo masa miƙewa ya yi ya ɗauko maganinsa, cikin dauriya ya isa gun fridge ya zuba ruwa tare da watsa maganin a bakinsa. Ahankali kuma ya zame ƙasa yana sauke numfashi. Sai bayan isha su Imran suka fito domin tafiya, har harabar gida inda motarsu ke ajiye su Junaid suka yi musu rakiya sai da suka fice daga gidan kafin su Mom suka koma ciki, a lokacin Sultan na saukowa daga room ɗinsa cikin shirin ƙananan kaya ya ci uban ado da alama fita zai yi, fuskar nan tasa ɗauke da murmushi kamar wanda aka yiwa albishir da gida Aljannah. Junaid ne ya ce "Sultan ina zuwa haka?" Ɗan sosa kai ya yi kafin ya ce "Clup ko akwai abin da ka ke so ne?" Ya faɗa yana nufar hanyar fita, da sauri Junaid ya ciro addu'ar da ke aljihunsa ya fara karantawa yana mai tofawa da ƙarfi, ba Sultan ba hatta Mom sai da ta tsorata da yanda gidan ke juyawa, Junaid ko be daina karanta addu'ar ba sai ma ƙara ɗaga murya da yake yi. Nan take Sultan ya fara rikiɗewa zuwa ƙatuwar Kada me girman gaske, Mom da ke tsaye kuwa ta zube ƙasa cikin mugun tashin hankali. A gaban idonsu Sultan ya koma jibgegiyar Kada me ban tsoro, idanuwansa jajir kamar garwashin wuta, ba zato kuma suka fara jin kukan Mage na tashi, gurnanin magen ne ya ƙara yawa kamar na Zaki, tafiyar Magen kuwa tamkar Doki, a ruɗe Mom ta maida kallonta inda kukan ke tashi dan ganin meye. *Ku yi sharing saboda Allah, mu je zuwa yanzu aka fara, ku dai ku kasance da alƙalamin Asmeey ta haidar domin jin yanda zata kasance* *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* P. 8 Ido huɗu suka yi da Sultan da ke watsa mata mugun kallo cike da tsana, "Ka mareni da wanne dalilin?" Najmeer ta faɗa tana kallon Junaid da Meera. Junaid ne ya ce "Keeeee.... wai dama ke ce me driving ɗin? ba shakka shiyasa ki ke tuƙin hauka" "Kai ne dai mahaukaci" Cewar Najmeer tana murguɗa masa baki. Hannu ya ɗaga da niyar shafa mata mari cikin sauri ta damƙe hannun tana girgiza masa kai, duk da cewar hannunta na ƙonewa sosai kamar ta saka shi cikin wuta amma hakan be hanata daurewa ta fara faɗin "Ban da wannan lokacin, kar ka sake izgilancin ɗaga ƙazamin hannunka na ƴaƴan talakawa a jikina, idan a lokacin baya ka dakeni na barka wannan lokacin ba zan ɗaga maka ƙafa ba, zan yi maka uzuri yanzu saboda na lura har yanzu kai ƙaramin yaro ne wanda be isa na tsaya sa'insa da shi ba" Ta ƙarasa maganar tana mai sauke hannunsa a hankali, a lokacin har hannayenta sun yi jajir kamar wadda ta saka hannun a wuta. Kallonta ta maida kan Sultan tana mai sakin murmushin da ita kawai ta san manufarsa "Kai kuma marin da ka yi mun bashi ka ɗauka, ka san cewa haɗuwarmu baza ta yi kyau ba, but next time sai na koya maka yanda ake girmama manya" Junaid ne ya katseta da faɗin "Wai ke lafiyarki kuwa? kin ga sa'anki anan ne da ki ke kiran kanki da babba, na lura cewar Sultan kaine ka janyo wannan yarinyar ta rainani amma zan ɗaukar miki mataki" Ya faɗa yana barin furin a fusace, Najmeer kuwa ta kama hannun Meera suka shige mota, da kallo Sultan ya bisu har suka bar gurin cikin matsanancin gudu. Tun da Junaid suka fara tafiya Sultan ke jan tsaki kamar wanda aka ce hanyar samun abincinsa kenan, gajiya da tsakin ne ya sa Junaid faɗin "Malan ka isheni fa, duk kaine silar wannan abin wallahi" Cikin haɗe fuska da takaici Sultan ya cije lips ɗinsa yana mai faɗin "How's that my fault? yarinyar nan fa na kasa gane inda ta dosa, ga shegen rainin tsiya" "Ai kuwa akwai raini sosai dan cikin jininta yake, ina ganin baza ta fi shekaru sha uku ba amma take faɗa mun baƙaƙen maganganu haka" Junaid ya faɗa yana dafe kansa dan ya gaji da magana. "Sha uku fa Bro? yarinyar zata fi shekaru sha uku ko kallon tsoro ka ke yi mata ne" "Ina ruwana da ita? da har zan ƙare mata kallo mtsssss" Junaid ya ja tsaki. Taɓe baki Sultan ya yi ba tare da ya kuma cewa uffan ba har suka iso gida, a parlour suka taradda Mom zaune tana kallon program ɗinta, bakin Junaid ɗauke da sallama ya shigo barin Sultan da be da niyar yin sallamar, Mom na ganin Sultan ta fara sunne kai tana ƙoƙarin barin parourn ganin haka ya sa Sultan nufota da sauri yana faɗin "Wai Mom lafiya kuwa? ko wani laifin na yi miki please ki daina gudu na haka" Tun kafin ya rufe baki Mom ta kai ƙarshen steps da gudu. Junaid ne ya bushe da dariya har da riƙe ciki abin da ya jima a rayuwarsa be yi ba kenan, sosai yake dariyar wadda ta ƙara masa kyau matuƙa, shi ko Sultan in ransa ya yi dubu ya ɓaci hakan ya sa ya haura room ɗinsa yana mai ƙara haɗe fuska. Da ƙarfi ya daki ƙofar tare da faɗawa ɗakin. A zaune ya sameta ta naɗe jelarta da ke kwance a ƙasa har tana jan ƙasa, a hankali Zakanyar ta wangame baki tana ɗaga kai sama alamar barka da zuwa, ɗan ɓata fuska Sultan ya yi tare da zama kan bed ɗin ba tare da ya ce uffan ba, miƙewa Zakanyar ta yi tana mai taku cikin izza har ta ƙaraso gabansa, Sultan ne ya ƙara haɗe fuska alamar ba rahama "Please ki tafi yau bana son dogon surutu, duk ke ce silar abin da ke faruwa a yanzu sai da na ce miki mu kashe wannan yarinyar amma kin ce mu bari har sai lokaci ya yi, yaushe kenan lokacin zai yi?" Kallonsa Zakanyar ta yi sai kuma ta girgiza kai alamun aa tana mai juya masa baya, "Idan har muka kasheta a yanzu burinka da nawa ba zai cika ba, bayan haka aurenku ya zama dole kamar yanda ka sani ya kamata ka koyawa kanka rayuwa da ita tun yanzu" "Okay fine zan yi ƙoƙarin yin hakan, but yarinyar akwai rainin hankali" "A haka za ka canja ta har mu samu biyan buƙata" Zakanyar ta faɗa tana mai ɓacewa. Dafe kai Sultan ya yi da ƙarfi yana mai jin mugun tsanar Najmeer daga ƙasan ƙafarsa har ƙwaƙwalwarsa. Cikin dauriya ya shige toilet dan sakarwa kansa ruwa. .................... A ɓangaren Prince kuwa yau tun safe ya fito dan neman unguwar da su Najmeer ke zama, sosai aka baza tsaro ana nemansu ai kuwa cikin ikon Allah Dogaransa suka samo addrees na gidan, zaune yake cikin mota sanye cikin kayan Sarauta kamar kullum ba ƙaramin kyau ya yi ba musamman yau da ya ɗora alkyabba a saman kayan nasa, ya sha rawani har kusa da kyawawan idanunsa masu kyau da ɗaukar ido, ba ka ganin fuskarsa sai dai da alama ya gaji da zaman da yake yi. Cikin biyayya ɗaya daga cikin masu tsaronsa ya ƙaraso yana faɗin "Allah ya ba ka nasara mun samu gidan da take" Kamar wanda aka tsikara ya ɗago yana ƙara lumshe ido "Ina buƙatar ku kaini yanzunnan" Cike da biyayya Dogarin ya amsa da an gama yana mai shigewa motar, motoci ashirin ne suke take masa baya har haɗaɗɗar unguwar da su Najmeer ke zama, bakin gate ɗin suka tsaya kamar yanda Prince ya bada umarni, sosai yake kallon gidan kafin ya fito tare da nufar gate ɗin, Dogaran ne suka fiffito suna bin bayansa amma ya ɗaga musu hannu alamun baya buƙata, ya jima yana buga bell ɗin gate har ya fara fusata dan babu wanda ya buɗe, juyawa ya yi da niyar tafiya ya ji an buɗe gate ɗin ana faɗin "Waye ne......?" Cakkkk ya tsaya ba tare da ya juya ba, ita kuwa Najmeer da ke bakin ƙofa da mamaki take kallonsa tana son tunano inda ta san me wannan kamannin, kawar da tunanin ta yi kafin ta ɗan juya ciki tana kallon gate Man da fitowarsa bayi kenan "Baba ina ka shiga ana buga ƙofa tun ɗazu" Cikin biyayya gate Man ya ce "Hajiya ayi haƙuri na zaga ne" "Haƙuri fa ka ce, ai hauka ne da rashin hankali wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe" Ta faɗa a tsawace, haƙuri ya kuma bata yana mai sunkuyar da kai, duk abin da suke Prince na jinsu sosai ya ji zafin yanda take wulaƙanta masu aikinta, cikin ƙasaita ya juyo yana mai watsa mata mugun kallo, ai kasa magana ya yi ganin kayan da ke jikinta kamar ba musulma ba, wata ƴar ƙaramar riga ce da kaɗan ta wuce mazaunanta, rigar me hannun vest ce daga baya a buɗe, gashin kanta ya baje amma ya sha gyara sosai, bakinsa na rawa ya ce "Ke.... wannan wanne irin iskanci ne" Najmeer kam tsoro ne ya shigeta ganin wanda ke gabanta tabbas shine wanda suka haɗu a gurin shaƙatawa, a tsorace ta runtuma da gudu cikin gida tana kiran sunan Mamu, yanda take gudun ne ya sa duk wata halittar jikinta motsawa, da sauri ya kawar da kansa ƙasa har ta shige sannan ya bi bayanta. Najmeer na shiga parlour ta sami Mamu da Meera suna kallo, da gudu ta faɗa bayan Mamu tana faɗin "Na shiga uku ga Miyar yauƙi har a gidanmu" Meera na jin haka ta fashe da dariya dan ta san wa Najmeer ke nufi, sallamar Prince ne ya sa ta ƙara daburcewa tana mai noke kai cikin jikin Mamu, Mamu kuwa sai zuba masifa take amma Najmeer taƙi fitowa, cikin biyayya Prince ya gaishe da Mamu yana mai kallon Najmeer ƙasa-ƙasa, Meera ce ta gaida shi ya amsa ciki-ciki yana mai zama nesa kaɗan da inda suke zaune, Mamu ce ta ce "Ɗannan sannu da zuwa" Lumshe ido Prince ya yi a karo na farko yana faɗin "Sannu Hajiya ya gidan?" "Lafiya ƙalau ka zo tafiya da ita ne ko? to dan Allah kar ka kwana da ita idan kun gama duk abin da za ku yi ku dawo a yau ɗinnan" Waro ido Prince ya yi yana mai dafe saitin zuciyarsa, Najmeer kam ƙara hargitsewa ta yi jin Mamu ta lalata mata shiri, dariya ce ta hana Meera miƙewa sai ƙara sunne kai da ta yi, cikin biyayya Prince ya ce "Hajiya ba tafiya da ita na zo na yi ba magana nake son mu yi da ita" "Wallahi ƙarya yake azzalumi jiya har fyaɗe ya tashi min a cikin bainar jama'a, hmmm ai Mamu idan na nuna miki yanda ya mayar da jikina sai kin sha mamaki, shine fa ya biyo ni har gida" "Keeee waye ya tashi yi miki fyaɗen?" Prince ya faɗa cikin mugun mamaki. Ɗago kai Najmeer ta yi tana mai yi masa gwalo sai kuma ta fashe da kuka har da birgima a ƙasa tamkar ƙaramar yarinya, hawaye kuwa daki-daki a idanuwanta, rarrashinta Mamu ta shiga yi tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un yanzu bawan Allah jikanyar tawa ka tashi lalatawa? yarinya kamila me tsoron Allah shine za ka yi mata fyaɗe, Allah ya fika da izininsa" Cewar Mamu itama tana fashewa da kukan, majina Najmeer ta sharce kafin ta ce "Ina faɗa miki Mamu sai riƙe sa ake mutane na bashi haƙuri amma haka ya rinƙa ture kowa da ke gabansa cikin tasha ya nufo kaina da niyar ɓata min rayuwa" Wannan karon kasa haƙuri Meera ta yi ta bushe da dariya har da riƙe ciki, Prince kam kasa magana ya yi idanuwansa sun rine jajir ransa ya mugun ɓaci jin sharrin da Najmeer ta laƙa masa, kuma daga zaran ya ɗago ido sai ta kawar da kai dan babu abin da take tsoro sama da kallon idanuwansa. "Kin gani ko Mamu wai na zo" Najmeer ta faɗa tana lailaya ido. Tsammm Prince ya miƙe yana mai ficewa waje ransa a mugun ɓace. Najmeer na ganin haka ta bi bayansa da gudu a lokacin har ya kusa gate, "Hi Mr Prince Miyar yauƙi" Ta faɗa tana kama ƙugu. Ran Prince a matuƙar ɓace ya juyo "Waye Miyar yauƙin?" Ya faɗa yana mai tsalle ɗaya ya damƙo gashin kanta, ihu Najmeer ta kurma kamar wadda ake cirewa rai "Sunan da ki ka samun kenan? ai kuwa zan koya miki hankali" Ya faɗa yana mai ƙara matse gashin kanta, sosai zafin ke shiga har tsakiyar ƙwaƙwalwarta, "Washhhh Allah please ka sake min gashina" Ba tare da ya saurareta ba ya cigaba da jijjiga kanta tsabagen mugunta, ai kuwa Najmeer ta rinƙa rafka ihu har su Mamu suka fito, Mamu ce a gaban Meera har tana ƙoƙarin zamewa ita ala dole an taɓa mata kamilar jikanya, Prince na ganin Hajiya Mamu na yanka gudu ta nufo inda suke ne ya sa ya sake Najmeer tare da ficewa da sauri. Sosai kan Najmeer ke sarawa tana ganin Mamu ta ƙaraso ai kuwa ta zube ƙasa tare da runtuma ihu "Wayyooo Allah kaina, wayyo Allah jama'a ya kasheni ku duba min ƙwaƙwalwar kaina ina ganin ya tafi da shi" Kamata Mamu ta yi tana duba gashin kan nata, "Mtssss ke rabani da shirmen banza ba abin da ya samu kan naki" "Dama Mamu na san kin daina ƙaunata imba haka ba ga kwanya na zuba ƙasa amma za ki ce ba abin da ya sameni" Najmeer ta faɗa tana dalalo yawu wai shine kwanya, Meera ce ta ce "Kai Najmeer ai wannan yawu ne ba kwanya ba, kuma dama idan an kama gashin kan mutum da ƙarfi sosai har zubar yawu zai rinƙa yi tsawon sati ɗaya" Najmeer na jin haka ta ƙara tattaro yawu ta cigaba da dalalowa tana ɗaga kai sama "Kin ji ko Mamu, shikenan Miyar yauƙi ya gama da ni haka kawai ya tasa ni gaba" Ɗagata Mamu ta yi tana zuba masifa ta inda take shiga ba tanan take fita ba, zagi kuwa babu wanda Prince be sha ba gurin Mamu har suka koma daga ciki. Suna shiga Najmeer ta yi baje-baje kan kujera tana ɗaga harshe sama, Mamu kuwa sai sannu take yi mata har da ɗauko tsumma ana goge yawun da ke zuba, sarai Meera ta san Najmeer ƙarya take ita da kanta take zubar da yawun, kamar me ciyon farfaɗiya Najmeer ta ce "Mamu na san cewa mutuwa zan yi tun da har ki ka ga ban daina zubda yawu ba, yanzu haka idona sun fara rufewa da buɗewa ina ganinki ne uku-uku dan Allah ki yafe min duk abin da na yi miki" Mamu na jin haka ta matso ƙwalla gami da sarce majina "Baza ki mutu ba Najmeer sai na ga ƴaƴanki da yardar Allah, ai shi ciyo ba mutuwa ba ne" "A a mutuwa zan yi Mamu, ina ji a jikina dan har wani sanyi-sanyi ke tashi daga tsakiyar kaina da alama mu ne gaba a gidan Aljannah" Najmeer ta faɗa tana wuwwula ido. "Ƙwarai kuwa ku ne a gaba ƴarnan, ai ina ji a jikina, amma dan Allah kar ki mutu har sai kin kaini umrar da ki ka ce" Daga Najmeer har Meera bushewa da dariya suka yi, cikin dariya Najmeer ta ce "Wai dama duk wannan tarairayar da ki ke min dan kawai zuwa umra ne? na zata duk cikin soyayya ce" "Mtsssss rabani dan Allah da shirmen banza da wofi, yooooo ni meye abin tarairaya gurinki idan ba wani abin nake so ba" "Ƙara narke fuska Najmeer ta yi tana mai karkace baki ta cigaba da magana kamar ɗazu "Wayyyooo Allah kwanyar kaina na zuba Mamu ki taimaka min ya raunatani" Ko kallonta Mamu bata yi ba ta haura sama. Wayar Najmeer da ke gefe ne ta ɗauki ƙara cikin hanzari ta duba tana mai jan dogon tsaki, sai da ta kusa yankewa kafin ta ɗaga. Daga can ɓangaren Alhaji ya ce "Shalelena sai kira nake ba'a ɗagawa" Ɗan taɓe baki Najmeer ta yi cike da salo ta ce "Yes mun tafi Abuja ne da Mom ɗina amma anjima zamu dawo" "Okay dama zamu zo da iyayena gobe da safe neman aurenki kamar yanda mu ka yi magana a baya, kasancewar wasu abubuwan ne suka tsayar da ni" Wani irin juyawa cikin Najmeer ya yi amma sai ta dake "Okay ƙarfe nawa za ku shigo goben?" "Misalin sha ɗaya na safe" "Allah ya kaimu" Najmeer ta faɗa tana kashe waya. Duk gumi ya wanke mata jiki, "Lafiya dai Najmeer?" Cewar Meera. Sai da Najmeer ta ƙara sharce gumi kafin ta ce "Wai Alhaji ne zai shigo neman aurena gobe" "Mun shiga uku, kina nufin zai gane ƙarya ki ke masa duk tsawon wannan lokacin" "Ba ma hakan ba Meera ina da auren Jabir a kaina fa" "What.........?" Meera ta faɗa da ƙarfi. "Yes Meera ranar da na koma gidan da ku ke zama a ranar aka ɗaura aurena da Jabir, shine dalilin da ya sa na bar gidanmu" "Amma Mamu ta ce min ba'a ri ga da an ɗaura auren ba" Ɗago kai Najmeer ta yi tana mai kallon Meera "Kin tabbata hakan ta ce miki" "Sosai kuwa na tabbata dan mun yi firar sosai, ta sanar da ni cewar an fasa ɗaurin auren saboda kin bar gida" Hamdala Najmeer ta yi tare da godewa Allah, dama wannan dalilin ne ya sa a kullum take jin ɓacin rai, gyara zama ta yi kafin ta kuma cewa "Ya ki ke ganin za'a yi, ni da iyayena sun rasu duk ƙarya ce nake shirya masa yanzu idan ya zo ya samu ba hakan ba ne fa" "Wai kina nufin aurensa za ki yi?" Meera ta tambaya. Murmushi Najmeer ta saki me ƙarawa fuskarta kyau "Sosai ma kuwa aurensa zan yi, meye a ciki? daga zaran na yi sati ɗaya zan kwashe duk wata dukiyarsa sannan ya sakeni" Bushewa da dariya Meera ta yi "Kina nufin be da hankali ne zai sakeki" "Kin ga Meera duk wannan zancen mu aje shi a gefe, hankalina a tashe yake kar fa asiri ya tonu" "Zamu yi tunani zuwa anjima yunwa nake ji yanzu, bari na kira Maryam ta ɗora mana girki" Meera ta faɗa tana miƙewa. .................. Yau ta kama Monday kuma a yau su Dad suka shirya zuwa London neman auren ɗansu Sultan, daga Junaid har Mom tare za'a tafi da su. Dukkaninsu sun haɗe cikin kayan alfarma kana ganinsu ka san cewa ba ƙaramar dukiya ce tare da su ba, yau Junaid wankan ƙananan kaya ya yi wanda hakan ya masifar karɓar jikinsa, Sultan kuwa an sha manyan kaya sai washe baki ake. Motoci hamsin ne suka nufi airport cikin tafiyar ɗaukar hankalin me kallonsu, jirgi ɗaya aka kama wanda zai ɗauke su, a can suka sami Surayya da Imran sai Alhaji Hafiz ƙanin Dad kasancewar da su za'a yi tafiyar. Kana ganin Surayya zaka san hankalinta baya kanta, duk ta rame ta tsigale sai kallon Sultan take har lokacin tafiyarsu ya yi, wanda Sultan ɗin be sakar mata fiska ba, Imran da Junaid kuwa suna tare da juna sai magana suke ƙasa-ƙasa da alama akwai abin da suke tattaunawa. Ba ɓata lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar London. Basu jima suna tafiya ba Sultan ya miƙe dan shiga toilet, hakan ya sa Surayya ta faki idanu ta bi bayansa jiki na rawa, kamar an ce ya juya kawai ya ga mutun tsaye a gabansa. "Surayya lafiya?" Ya faɗa yana haɗe fuska. "Ba lafiya ba Sultan, tabbas ka san matsalata kuma kaine maganinsa" "Kin ga kar ki soma please, yanzu fa ni mijin wata ne, ki yi haƙuri da ni ko kuma ki koma gun Junaid tun da shi baya da wadda zai aura" Waro ido Surayya ta yi a tsorace "Rufa min asiri, ai Juanid ɗin na fara so kafin kai amma sanin halinsa ne ya sa ban yarda ya san ina son sa ba, amma kai na bayyana maka soyayyata ka kasa amincewa, dan Allah Sultan ka aureni ko zuciyata zata samu sauƙi" "Ke wai ya zan auri ballagaza kamar ki, kalleki dan Allah duk wani abin da nake buƙata a gurin mace bakya da shi, a hakan zan aureki" Fashewa da kuka Surayya ta yi tana mai roƙon Sultan amma be saurareta ba ya shige bayi abinsa, jiki a mace ta koma tare da zama inda ta tashi, duk yanayinta ya canja Imran yayanta ne kawai ya san halin da take ciki dan bata ɓoye masa komi, sosai tausayin ƙanwar tasa ya kama shi ganin yanda lokacin ɗaya ta canja. Misalin ƙarfe sha biyu suka isa ƙasar, inda suka tarar da hamshaƙan masu kuɗi an zo tarbarsu, motoci fiye da ɗari ne ke gurin masu masifar kyau da tsada, da farko iyayen Malika sun haɗe fuska suna jiran ganin waɗan da suka zo neman auren ƴarsu, amma suna ganin kayan jikinsu Dad sai kowannensu ya fara washe baki, dan gaba ɗaya taronsu babu wanda ya saka kaya me tsada da ɗaukar ido kamar su Dad, Malika da ke can gefe ne cikin shigar ƙananan kaya waɗan da suka ɗame mata jiki duk wata halittar jikinta ta bayyana, da gudu ta ƙaraso tare da hugging ɗin Sultan, kiss ta sakar masa a goshi "I love you Babe" Daga Dad har su Junaid kasa magana suka yi, ganin rashin kunya a fili. Surayya kuwa hawaye ta share a gefe tana mai jin mugun tsanar Malika a ranta musamman da ta ga kyawun da Allah ya yi mata, ɗan janyeta a jikinsa Sultan ya yi "Love you too Baby, ki gaida su Dad mana" Sai da ta ɗan taɓe baki kafin ta ɗaga musu hannu tana faɗin "Hi guys welcome to London" Idanunta ne ya tsaya kan Juanid, ai kuwa ta nufesa da sauri har tana haɗawa da gudu-gudu, hannu ta ware da niyar rungumesa ya ɗaga mata yatsa tare da girgiza kai "Hi Malika ya ki ke?" Ya faɗa yana sakin murmushin yaƙe. Hakan ya sa ta sha jinin jikinta, nan fa aka fara gaisuwa da yi musu barka da zuwa, duk da cewar Dad ya ga rashin tarbiyya a tattare da Family ɗin amma hakan be sa ya nuna ko a fuska ba, Surayya na gefen Mom a tare suka shiga mota, ba ɓata lokaci motocin suka bar gurin. Kai daga ganin gidansu Malika ka san cewa ba ƙananan masu kuɗi ba ne, gida ne wanda ya amsa sunansa gida duk inda ka duba zubin dukiya ne tari-tari. Wani ƙayataccen parlour aka sauke su tare da zube musu kayan more rayuwa, Malika idanuwanta na kan Junaid ko ƙyaftawa bata son yi har Junaid da Imra suka lura da hakan, Imran ne ya ɗan mitsini Junaid a hankali ya ce "Wai kana lura da wannan yarinyar kuwa? sai kallonka take nifa lamarinta ya fara bani mamaki" Cikin cool voice Junaid ya ce "Ni kaina kallon ya isheni ka san bana son yawan kallo ai" Daga haka suka bar zancen ganin mutane sun fara taruwa ana ƙara yi musu sannu da zuwa, baƙin ciki ne ya hana Surayya ɗaga ko cokali balle ta ci wani abun, ba laifi sun ci abinci amma ba sosai ba, nan aka kai kowannensu nasa ɗakin, sai dai Mom da Surayya ɗaki ɗaya suke Dad kuwa da ƙaninsa Junaid yana ɗaki ɗaya da Imran, gogan ne Sultan aka warewa ɗakinsa daban wanda ya mugun haɗuwa. Ƙarfe huɗu za'ayi taro a harabar gida, wanda hakan al'adarsu ce idan har za'a zo neman aure sai an yi shagali tare da nunawa jama'a mijin da ya zo neman ƴarsu. Kasancewar a gajiya Sultan yake ne ya sa yana shiga ya kwanta dan baccin da ke idonsa. Dad kuwa tun da ya shiga ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunaninsa ɗaya wannan wanne irin Family ne Sultan zai haɗa zuri'a da su. Kamar yanda Dad ke cikin wannan tunanin haka ma Junaid da Imran waɗan da ke mamakin rashin kamun kai irin na Malika. Ƙarfe huɗu da rabi na yamma an gama shirya gurin taron tamkar baza'a mutu ba, komi na gurin white and pink ne, haka ma kowa ya saka kaya white and pink hatta su Mom, wanda anko ne da aka kawo musu na taron. Malika ta yi shiga cikin doguwar riga har tana jan ƙasa, a kanta babu ɗan ƙwali balle mayafi duk rabin dukiyar fulaninta a waje, wannan shigar ba ƙaramin ɓatawa su Dad rai ya yi ba, cikin fushi ya ja hannun Sultan gefe ransa a mugun ɓace ya ce "Sultan wannan wanne irin hauka ne haka? ka rasa wadda zaka kawo a matsayin matar aure sai wadda bata san darajar kanta ba" "Dad please wallahi ina sonta sosai and zan mayar da ita yanda ka ke so bayan aurenmu" "Haukar banza kenan, bayan sunana da zaka ɓata a gari har sunan ƴaƴan da zaka haifa ma dan babu wanda zai so haɗa alaƙa da irin wannan gidan, dukiyarsu ta banza ce tun da babu tsoron Allah a ciki" Dad ya ƙarasa maganar yana barin gurin, daidai lokacin da aka ce ana buƙatar Malika ta kama hannun mijinta ta kawo shi gaban taro. Cikin karairaya Malika ta miƙe tana mai tafiya a gadarance, kowa ya zuba mata ido sautin waƙa na tashi a hankali me daɗin dauraro, Sultan kuwa har da gyara tsayuwa yana mai sakin killer smile, da mamaki aka ga ta nufi Junaid fuskarta ɗauke da murmushi, nan fa kallo ya ƙara yawa dan mutane da dama sun san cewa ba Junaid ne angon ba. Malika na isa ta kama hannunsa tare da jansa zuwa gaban taron, kamar wani wawa haka Junaid ke bin bayanta cike da mamaki kamar a mafarki, sai da suka isa kafin Malika ta ɗauki speaker tana mai ƙara gaida mutanen da ke gurin cikin harshen turanci, sannan ta cigaba da faɗin "Kamar yanda kowa ya sani a yau ne aka zo neman aurena daga Nigeria, kuma kowa ya buƙaci ganin wanda zan aura hakan ya sa na yanke hukuncin nuna muku wanda zuciyata ke ƙauna sannan nake fatar na aura" Sai da ta kalli Sultan da duk idanunsa sun canja kala kafin ta cigaba da faɗin "Junaid nake so kuma nake burin na aura, dan haka a ɗaura min aure da shi ko na kashe kaina" Tsittttttttt kiɗa ya tsaya mutanen da ke gurin duk suka ƙara yin shuru ana sauraren abin da Malika ke faɗi tamkar a mafarki. *Jiya na ce zan yi posting bansamu na yi ba saboda matsalar rashin wuta da mike fama da shi a yanzu, wutar mu ta samu matsala bama samu kamar kowanne lokaci, dan haka a ƙara haƙuri ba kullum mike samun wuta ba* *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P. 9 A fusace Sultan ya ƙarasa gurin yana mai ɗauketa da wani rikitaccen marin da yasa kowa miƙewa tsaye, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta jikinsa sai rawa yake tsabagen ɓacin rai, da yatsa ya nunata bakinsa na karkarwa ya ce "My Brother........, shine wanda za ki aura? wow Malika wow, ai bansan cewa ke ɗin marar tunani ba ce sai yau, and babban kuskurena shine yarda da ke da na yi, wallahi na yi nadamar saninki a rayuwata". Sultan ya ƙarasa maganar yana mai barin gurin. Dad da su Junaid suka rufa masa baya, aka bar Malika na rusa ihu kamar mahaukaciya, iyayenta kuwa sai zagin Sultan da Family ɗinsa suke, ko minti biyu masu kyau basu ƙara a gidan ba suka fito cikin shirin tafiya Nigeria, gaba ɗaya gidan ya ɗauka da surutun mutane sai kukan Malika da ya ƙara cika gidan ita ala dole Junaid take so idan ba haka ba zata rasa rayuwarta. Jikin Junaid ya yi sanyi sosai ganin son da Sultan ke yiwa Malika, Surayya sai murna take a zuciya tare da zubawa Malika albarka dan ta gama biya mata komi. Airport suka nufa ran kowa a ɓace musamman Dad da har suka isa Nigeria be ce ƙala ba, ransa ya masifar ɓaci dan ko Sultan ba zai nuna masa ɓacin rai a yau ba. Tun a airport ɗin kowa ya kama gabansa, su Imran da sister ɗinsa suka nufi gida sai ƙanin Dad wanda shima be ji daɗin abin da ya faru ba, Mom kam sai rarrashin Dad take ganin yanda ransa ya ɓaci, a babban parlour suka sauka kowannensu da abin da yake tunani musamman Sultan, minti ɗaya be ƙara a zaune ba ya miƙe tare da nufar ɗakinsa. Kamar yanda ya saba haka ya sameta a zaune tana mai kaɗa jelarta sautin dariya na tashi daga bakinta wanda ke ɗauke da mugayen haƙora masu kaifin gaske, cikin fushi Sultan ya damƙo wuyan Zakanyar da hannu ɗaya ya shaƙe har sai da ta fara zare ido "Bari na fara kashe ki kafin burin rayuwata ya gama rugujewa tun da ke ce silar duk halin da nake shiga, na tabbata cewa ke ki ka hana wannan auren ba kowa ba" Sultan ya faɗa yana mai jifa da ita gefe. Ɗagowa Zakanyar ta yi a hasale ta doki cikinsa da ƙafa, ai kuwa Sultan ya yi tsalle sama tare da faɗawa kan bed, itama Zakanyar tsallen ta yi tana mai dira kan bed ɗin ta kai masa cizo daidai wuyansa amma sai ta tsaya cakkkk ba tare da ta cije shi ba, a hankali kuma idanuwanta suka fara fitar da ƙwalla wanda hakan ya sa Sultan hugging ɗinta gami da fashewa da kuka shima, sosai suke kukan a tare wanda duk yanda ka kai ga rashin imani idan ka gansu sai ka tausaya musu, tabbas ba ƙaramin abu ke tsakaninsu ba musamman yanda fuskar Zakanyar ta sauya lokaci ɗaya. Cikin sanyin jiki Sultan ya janyeta yana mai shafa gefen fuskarta "I'm sorry Habibaty na kasa daurewa ne" Ɗaga kai Zakanyar ta yi tana mai juya fuska "Na sani Sahibina ina son ka ƙara haƙuri har lokacin da burinka da nawa zai cika". Ta ƙarasa maganar tana mai ɓacewa. Naushi Sultan ya kaiwa bed ɗinsa a lokacin Junaid ya yi sallama tare da zama fuskarsa a haɗe, ko kallon inda yake Sultan be yi ba ya juya masa baya, Junaid ne ya ce "Me hakan ke nufi? ko kana tsammanin ni na hana Malika aurenka?" Ɗan sosa kai Sultan ya yi yana mai janyo blanket ya fara rufe jikinsa ganin ya fara sauya halitta zuwa Kada, kasacewar Junaid be lura da hakan ba ne ya sa ya cigaba da faɗin "Ya kamata ka yi magana da ita a yau domin tabbatar da abin da ke faruwa, but please kar ka ɗauki wannan a matsayin laifi" Miƙewa tsaye ya yi gami da taku ɗaya inda Sultan ke kwance "Amma kamar abin farinciki ne ka rabu da ƴar marassa tabiyya" Kafin ya ƙarasa maganar Sultan ya ɗaga jelarsa tare da kai masa duka a baya ji ka ke timmmmmm, "Ya subhanallah" Junaid ya faɗa yana mai dafe gurin da Kadan ya dakesa, da sauri kuma ya maida kallonsa kan Sultan da ya rikiɗe zuwa mummunar Kada me ban tsoro, yau lamarin ya fi muni dan har wani baƙin hayaƙi ke fita daga bakinsa, ganin hakan ya sa Junaid ficewa daga ɗakin da yana mai dafe bayansa da ke mugun zafi. .................. A ɓangaren su Najmeer kuwa sun gama tsara komi har da iyayen ƙarya waɗan da ta saya musu kayan da za su saka masu mafisar tsada, unguwar Rimi suka samu hayar wani haɗaɗɗen gida me hawa uku, sosai gidan ya tsaru tamkar baza a mutu ba, misalin sha ɗaya su Najmeer suka shirya cikin wasu masifaffun kaya masu shegen kyau less ne me tsada milk, anko su ka yi da Meera sai dai kayan sun fi zama daram daƙam a jikin Nameer, mayafinsu black ne kalar handbag da takalmar ƙafarsu wanda ya gaji da haɗuwa. Meera ce me driving Najmeer ne gefe Mamu kuwa tana bayan mota sai surutu take zubawa ba tare da sanin inda aka nufa da ita ba, suna isa ta yi horn Gate Man ya danna remote nan take ya ɗage masa Meera ta kunna kai ciki, bakin Mamu har yana dalalo yawu tsabagen kallo, kai daga gate ɗin zuwa harabar gidan ya isa tabbatar maka cewar an kashe dukiya me yawa. "Aljannar duniya" Cewar Mamu tana fitowa. Meera ta ce "Ai sai mun shiga daga ciki za ki tabbatar da gidan ƙarshe ne" "Kina nufin wannan duk wasan yara ne? kin ga motoci kamar a gurin saidawa" "Sosai kuwa Mamu ke dai mu ƙarasa daga ciki" Meera ta faɗa tare da jan hannunta. Najmeer na bayansu tana waya da Alhajinta har suka shigo ƙayataccen parlourn me ɗauke da duk wani abun da ake buƙata. "Wai wai rangammm" Mamu ta kuma faɗa tana mai kama baki, parlour ne me ɗan karen kyau yana ɗauke da kujeru kala uku masu tsadaddun kyau. Frigde kuwa uku ne ta kowanne ɓangere, sai Tv manya-manya guda biyu. Bakin Najmeer ɗauke da sallama ta shigo tana mai katse wayar, "Yawwa Mamu kin ga wannan gidan zamu zauna na tsawon sati ɗaya saboda hidimar bikina, ina son ki kasance makauniya kuma kurma, ina nufin duk abin da ki ga gani ki kawar da kai kuma duk abin da ki ka ji ki yi kamar ba ki ji ba" Mamu ce ta katseta da faɗin "Na boni na lalace ni Mamu tsohuwa ga Najmeer, ke dan ubanki auren ke za ki yiwa kanki da har za ki mayar da ni makauniya da kurma? yoooo ina uwayen da za su ɗaura miki auren bayan Kawunki Jamilu?" "Mu ne uwayenta kuma jigo a gareta" Cewar wasu Dattijai da ke saukowa daga upstairs cikin shigar alfarma, Namijin zai kai shekaru hamsin da ƴan kai, sai macen zata kai shekaru arba'in, fuskarsu ɗauke da murmushi. Cike da tafiyar ƙasaita suka iso tare da zama kan kujera me zaman mutum uku, Mamu na ganin haka ta sauko har ƙasa ta rusuna sai da ta dunƙule hannu kamar me gaida Sarki ta ce "Barka da zuwa ranku ya daɗe, shugaba me daraja sannunku da saukowa" Dariya ce ta kusa ƙwacewa Dattijan ganin yanda Mamu ke zuba gaisuwa amma sai suka ƙara haɗe fuska kamar yanda Najmeer ta tsara musu, Dattijon ne ya ce "Yawwa Hajiya ya hanya da mutanen gida?" "Alhamdulillah ai mutane kune mutane ga kuɗi ga mulki, ku kam Allah ya sallemeku" Mamu ta faɗa tana washe baki. "To muna godiya tashi ki zauna a sama" Dattijuwar ta faɗa tana mai murmushi, girgiza kai Mamu ta yi alamun aa, sai da aka yi da gaske kafin ta koma saman kujera, jin ƙarar motoci ne ya sa Meera kama hannun Mamu aka haura da ita sama, Najmeer kuwa ta ƙara tsara musu yanda za su yi sannan ta bi bayan su Meera. Motoci hamsin ne aka shigo da su gidan wanda daga gani ka san ba ƙananan mutane ba ne, duk inda ka duba manyan Alhazawa ne ke fitowa cikin shigar kamala. Daga gefe ɗaya Alhajin Najmeer ne sanye da farar shadda ya sha kyau sai murmushi yake, har babban parlour aka yi musu jagora inda suka tarar da Mahaifin Najmeer da Mahaifitarta na ƙarya da ta samo zaune suna mai yi musu maraba, cike da girmamawa aka gaisa kamar dama can iyayen gaskiya ne, ba ƙaramin mamaki Alhajin ya yi ba ganin iyayen Najmeer ko kaɗan basa kama da ita, amma hakan be sa ya kawo wani abun a ransa ba, wayarsa ce ta yi ƙara a ladabce ya nemi izinin fita sannn ya fice tare da ɗaga wayar. Daga can ɓangaren ba ka jin abin da ake faɗa amma Alhajin ya yi shuru da alama ana magana ne, kusan mintuna uku yana saurara kafin ya ce "Idan muka nemi ɗaura auren a yau akwai matsala dan za su iya zargin wani abun, amma a saka ranar auren hakan zai fi" Ƙara dakatawa ya yi alamun ana masa magana, sai can ya amsa da "Kar ka samu damuwa Najmeer ta zama mallakinka da yardar Allah ta shigo hannu" Sallama ya yi tare da kashe wayar, yana juyowa suka yi ido huɗu da Meera da ke tsaye tana mai sauraronsa, bakinta na rawa ta ce "Dama ba kai za ka auri Najmeer ba wani ka ke nemawa aurenta?" Da sauri ta juya zata koma ya yi hanzarin kama hannunta "No Meera please ki tsaya ki fahimceni zan faɗa miki koma menene amma sai idan baza ki hana aurennan ba" Mugun kallo Meera ta watsa masa tana mai ƙwace hannunta "Kana tsammanin za'a haɗa kai da ni a yaudari babbar aminiyata" "Ba haka nake nufi ba ki fahimceni Meera Oga na ne ke son ƙawarki, kuma baya ƙasar nan kawai ina masa aiki ne har zuwa lokacin da zai bayyana kansa" "Waye Ogan naka?" Cewar Meera a fusace. Sai da Alhajin ya duba gabas da yamma kudu da arewa kafin ya matsa kusa da Meera yana mai rage murya "Zan faɗa miki wannan alƙwari ne amma please kar ki sanar da Najmeer, ga number na sai ki kirani zuwa ajima bayan mun koma duk abin da ke faruwa zan sanar miki" Ba dan Meera ta so ba ta karɓi numbersa tana mai barin gurin cike da fargaban abin da zai je ya dawo. Komawa ciki Alhajin ya yi inda ya samu an tsayar da rana sati ɗaya Friday me zuwa za'a ɗaura aure, sosai ya ji daɗin lamarinnan ganin iyayen basu kawo matsala ba, kayan abinci da na sha kuwa sai da suka ture dan ba wani ci suka yi ba, duk abin da suke buƙata akwai shi a gurin, nama ko kala-kala ne kama daga naman shanu naman rago da sauransu. Million ɗaya suka aje tare da ficewa, sai da suka fito kafin aka kira Najmeer da Meera dan su gaishe da mutane, Najmeer na sanye cikin mayafinta me girma kamar gaske sai sunne kai take, sosai mutanen suka yaba kyawunta da kuma natsuwarta. Ba wata magana suka yi da Alhajin ba ta koma ciki, sosai ta ji daɗin yanda komi ya tafi yanda ta tsara, a parlour ta sami Mamu zaune ta haɗe ƙafa, ba tare da Najmeer ta kalleta ba ta maida dubanta kan Dattijan da ta hayo ta ce "Yawwa aikin yau ya kammala za ku iya tafiya har sai ranar ɗaurin aure nake buƙatar ganinku, na aje muku abubuwan buƙata da kuɗi a ɗakinku bana da wata alaƙa da ku sai wani satin a ranar da za'a ɗaura aurena" Godiya sosai suka yi mata tare da barin gurin. Mamu ce ta ce "Au dama ba gidansu ba ne? ikon rabbissamawati, Najmeer hayar iyaye ki ka yi? innalillahi wa inna ilaihir raji'un ni Mamu tsohuwa ga Najmeer" "Haba Mamu dan Allah ki shafa min lafiya, kema ai farincikin ki ne na yi aurennan ko za ki huta" "Amma ba irin wannan auren ba ja'irar yarinya me nema mana abin kunya, hauka ake da za'a ɗaura miki aure da gandamemen ƙato kamar wannan" Cikin fushi Najmeer ta ce "Ai ba a kanki zai zauna ba" "Ko ba'a kaina zai zauna ba ina ke ina wannan garjejen? ko Ubanki ba zai girmesa ba marar kunya kai" "Yanzu dai aikin gama ya ri ga ya gama aurena wani sati idan kin isa ki hana" Najmeer ta faɗa tana haurawa sama. Surutu Mamu ta shiga yi inda take shiga ba tanan take fita ba har Najmeer ta ɓullewa ganinta. A room ta sami Meera ta yi tagumi jikinta a sanyaye, dafa kafaɗarta Najmeer ta yi hakan ya sa Meera tsorata tana mai dafe ƙirji "Washhhh har kin tsoratani fa" "Tunanin me ki ke haka? ko Malik ki ke son gani" Dogon tsaki Meera ta ja tana mai taɓe baki "Kawai na rasa abin da ke min daɗi ne amma ba wani abun ba ne" Zama Najmeer ta yi tare da fuskantar Meera sosai "Kema kina tsoron kar na auri Dattijo kamar Alhaji ne?" "Ina tsoron kar ki auri wanda ba ki saniba dai" Meera ta faɗa bata san lokaci ba. Da mamaki Najmeer ta ce "Me ki ke nufi da hakan, Alhajin ne bansaniba ko me" Kame-kame Meera ta fara alamun rashin gaskiya "No ina nufin ba ki san halinsa ba" "Halinsa be shafeni ba idan har yana da kuɗi, ke nifa bana tsoronsa ko shan jini yake sai na aure shi na kwashe masa dukiya dan ubansa" "Allah ya ba ki sa'a amma fasa wannan auren zai fiye miki wallahi" "Meera wai meye matsalarki ne? ki barni duniya ta faɗa min amma ba ke ba" Najmeer ta faɗa tana miƙewa tsaye, sai da ta isa bakin ƙofa kafin ta juyo "Ki shirya zamu tafi wani gida anjima da dare, ina tsammanin kuɗin da ke account ɗina baza su isheni sayen kayan ɗakin da nake ra'ayi ba, shine na yanke hukuncin mu haura ginar wasu" Najmeer ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin, mamaki ne ya cika Meera har ta kasa koda motsin kirki, a ranta ta ce sata Najmeer ke son mu tafi ko me, gaba ɗaya tunani ya cika mata kai hakan ya sa ta miƙe tare da shigewa toilet. Misalin ƙarfe ɗayan dare ne Najmeer da Meera suka fito cikin shigar baƙaƙen kaya kana ganinsu ka ga ɓarayin dare, fuskarsu a rufe har suka fito harabar gidan, Najmeer ce mazaunin dirver Meera na gefe cike da fargaba, duk wannan abin da ake Mamu na ciki tana bacci bata san wainar da ake toyawa ba, cikin sauri Najmeer ta yi horn gate man ya wangeme ƙofa. Tun da suka fara tafiya Meera ta kasa samun natsuwa, dole ya sa ta tambayi Najmeer inda za su tafi, murmushi Najmeer ta saki wanda ya bayyana kyawunta "Gurin Malik za mu tafi" Zaro ido Meera ta yi a tsorace "Malik kuma, me zamu yi a gurinsa?" "Fashi zamu je a gidansu Sultal" "Innalillahi ki rasa inda zamu tafi fashi sai gidansu Sultan, dan Allah ki rufa mana asiri dan wallahi wannan karon haɗuwarku baza ta yi daɗi ba" "Kin ga Meera idan baza ki iya ba tun yanzu ki sanar da ni na aje ji kan hanya, abin da ya sa nake son mu tafi da Malik na tabbata ba zai rasa bindiga a gurinsa ba" "Hmmm na shiga uku ni Meera yanzu kina nufin Sultan ba zai ganemu ba" Dariya me sauti Najmeer ta yi a karo na farko "Kalli yanda muka yi shigar jikinmu na tabbata ko Malik ba zai gane mu ba balle wani banza Sultan" A haka suka cigaba da surutun har unguwarsu Malik, a bakin gate Najmeer ta tsaya tana mai faɗin "Ki shiga ki duba idan yana ciki lokaci na tafiya yanzu ƙarfe ɗaya da rabi ta kusa bugawa" A ɗan tsorace Meera ta ce "Sai dai ke ki shiga ko mu shiga a tare" Ba yanda Najmeer ta iya dole suka nufi cikin gidan, daga harabar kana jiyo sautin waƙa na tashi da kuma hayaniyar mutane, hakan ya sa Najmeer ɗaga ma Meera hannu alamar ta tsaya, a hankali Najmeer ta kunna kai cikin ɗakin tana mai yaye labulen, maza da mata ne cike ana shaye-shaye wasu na gefe sai zuba iskanci ake, daga gefe kuwa Malik ne zaune yana zuƙar shisha, ɗago kai da zai yi suka yi ido huɗu da Najmeer, cikin layi ya miƙe tare da ɗaga hannu alamar kowa ya dakata, nan fa gurin ya ɗauki shuru. Malik ne ya ce "Ke kuma wacece haka kamar ƴar daba?" Meera da ke bayanta ne ta ce "Malik Meera ce" Jin abin da aka ce ne ya sa duk mutanen ɗakin sakin shewa da ihu, Najmeer ce ta ce "Ya isa haka please, Malik muna son ganinka akwai wani babban aiki da za ka yi mana zan biyaka Dubu ɗari biyar" Cikin sauri Malik ya ƙaraso gurin Najmeer har jikinsa na rawa "Dubu ɗari biyar? mu tafi yanzunnan zan aikata duk abin da ki ka yi umarni" "Good hakan nake son ji, amma ina buƙatar maza biyar daga cikinku waɗan da ke da makami a hannunsu" Kafin ta rufe baki wasu manyan ƴan iska suka fito bakinsu ɗauke da sigari, kana ganinsu ka ga Tantiran gari, ɗaya daga cikinsu ne ya ce "Shugabata ni a ganina me zai hana mu bari zuwa gobe saboda mu yi shirin da babu wanda zai gane mu, na tabbata babban aiki ne tun da har ki ka ambaci makamai" Najmeer ce ta ce "Ƙwarai kuwa babban aiki ne ina buƙar bindigogi masu rai da lafiya" "Gaskiya ƙwara ɗaya muke da a gurinmu shima dan kare lafiyarmu ne idan wasu kafuran sun durfafo mu, sai dai waɗan da babu bulet a ciki" Malik ya faɗa yana huhhura hanci. Meera ce ta ce "Muna buƙata a hakan tun da ba kisan kai zamu yi ba, yanzu wanne lokaci zamu fito goben?" "Daidai wannan lokacin" Malik ya bata amsa. Godiya Najmeer ta yi musu kafin suka fice daga gidan. Washe garin ranar tun da safe Mamu ke zuba masifa wanda ya hana kowa bacci, dole ta sa Najmeer fitowa room ɗinta sanye cikin kayan bacci da alama surutun Mamu ne ya tashe ta, a ƙufule Najmeer ta ce "Wai Mamu lafiya ki ka tasa mu gaba kamar waɗan da suka kashe miki wani naki" Mamu da ke zaune kamar an dasa ta ne ta ɗago sai kuma ta ja dogon tsaki har tana rusunawa kamar me roƙon gafara "Ina fa lafiya yanzu nake jin labari a redio wai yaron hamshaƙin me kuɗinnan Chief da ke G R A ya tafi neman aure a ƙasar London amma matar ta ce yayansa take so ba shi ba, gaskiya lamarin akwai ban tausayi" Mamu ta ƙarasa maganar tana share hawaye kamar wadda ɗan uwanta ya mutu. Najmeer ce ta ɗan taɓe baki tana faɗin "Meye sunan yaron da aka ce? na san baza su rasa faɗin sunansa ba" Ɗan shuru Mamu ta yi alamun tana tunanowa, Meera da ke saurarensu tun lokacin da suka fara ne ta ce "Sultan Chief ko Mamu" Carafffff Mamu ta karɓe zancen "Ƙwarai kuwa Sultan Chief yaron kirki me addini da sanin ya kamata ga ibadah, gaskiya shegiyar baturiyarnann ta yi asara" "Wai ke Mamu kin san shi ne da ki ke yabonsa haka? har da wani faɗin me addini imma shine limamin unguwarsu wannan matsalarsu ce ni be shafeni ba" "Dama ai ban ce taki matsalar ba ce shashashar banza, abun baƙin ciki ya sami ɗan Lajeriya ai dole na yi kuka" Bushewa da dariya Meera ta yi kafin ta ce "Nigeria ake cewa ba Lajeriya ba" "Sannu iyawa matar iyayi ina ruwanki da yanda na faɗi sunan ƙasata? na fahimci baƙin ciki ku ke yi dan be auri ƴar ƙasarku ba ya tafi neman aure wata ƙasar" Haushin maganarta ne ya sa Najmeer barin gurin cike da tsanar Sultan ɗin a ranta, a duk lokacin da ta tuna shi ko ta ji an kira sunansa wani mugun haushinsa ke taso mata musamman yayansa Junaid. Kamar yanda suka tsara a jiya haka kuwa aka yi ƙarfe ɗaya da rabi ta yi musu ne a bakin gate ɗin su Malik, duk wanda ya ga shigar da ke jikinsu ya san ba alkhairi za su shuka ba, musamman Najmeer da ko yaya ka san fuskarta ko kuma yanayinta baza ka taɓa ganeta ba, Malik ma sun rurrufe fuskarsu kamar yanda su Najmeer ɗin suka yi, mota ɗaya ce ta kwashe su zuwa gidansu Sultan Najmeer ce me driving cike da gadara har suka iso babban gate ɗin gidan, nan fa kowa ya fara shiri Meera da Najmeer na riƙe da bindigogi, bindigar da ke hannun Najmeer ce kawai me bulet amma sauran fanko ne. Cikin biyayya Malik ya ce "Shugaba kina nufin gidansu Sultan Chief zamu yi fashi?" Sai da Najmeer ta yi dariya irinta riƙaƙƙun ƴar tasha kafin ta ce "Sosai ma kuwa duk yawan masu tsaron gidannan ba zai hana mu shiga ba, ku dai kawai ku jira ni a mota kar wanda ya yi motsi har sai na ce ku shigo" Ba tare da tsoron komi ba Najmeer ta fito motar, gaba ɗaya ƙofar gidan akwai haske kamar ba dare ba, duk fitilun gidan sun haske ko'ina, ta bayan gida Najmeer ta koma yanda su Meera baza su ganta ba, cikin secons uku ta rikiɗe zuwa Mage tare da haurawa kan ginar gidan ta faɗa ciki, a hankali take tafiya har ta kawo bakin gate ɗin, sai da ta tabbata masu tsoron gidan sun jima da bacci kafin ta danna wani madanni da ke bada haske, gaba ɗaya wajen gidan da harabar gidan ya yi duhu fitulun suka ɗauke. Lokaci ɗaya ta rikiɗe zuwa mutum, me gadin ne ya fito ganin haske ya ɗauke, a tsaye ya ga mutum na ƙoƙarin buɗe gate, har ya buɗe baki da niyar magana Najmeer ta nuna shi da yatsa ai kuwa bakinsa ya kasa motsi kamar an manne shi, kuma ya kasa matsawa daga inda yake tsaye. Ganin haka ya sa Najmeer buɗe gate tare da ba su Malik umarnin shigowa daga ciki, ba ɓata lokaci suka kunno kai cikin gidan kowannensu riƙe da mugun makami, dirrect parourn gidan suka nufa wanda Najmeer ke da tabbacin daga nan za su fara. *Na gama typing tun ƙarfe biyar na yamma wuta ne ya hanani post, Mu je zuwa yanzu aka fara* *SHALELEN ALHAZAWA* *Writing and story* *By* *Asmeetar Hydar* (Asma'u Ayuba) *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* P. 10 Littafi ya ɗauki zafi ya fara gangara wannan dalilin ne ya sa na ga ya dace na tsayar da free pages haka, kar ku bari wannan labarin ya wuce ku domin za ku nishaɗantu da ilmantuwa tattare da shi, akwai suger sosai tare da wannan book sai kun karanta za ku tabbatar da hakan, ga masu buƙatar cigaba da karanta book ɗin Shalelen Alhazawa sai su biya 500 ta wannan Account 3137937874 tani Bako first bank domin tabbatar da shaidar biyan kuɗi sai ku tuntuɓi wannan number ta WhatssAp 08082589590 ko kuma ku kira wannan number 08164403726 idan har ba waɗannan numbers ku ka tuntuɓa ba a gaskiya ba ni ba ce dan kar a yaudareku da sunan za'a ba ku book ɗina Najmeer ce a gaba sai wani huhhura hanci take ita ala dole ƴar fashi har abin ma ya so ya ba Meera dariya amma sai ta matse tare da rufa mata baya, suna shiga parlourn Sultan suka tarar zaune ya haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana mai zuba musu ido. A tsorace su ka ja baya gami da rirriƙe juna, lokaci ɗaya Meera ta saki fitsari ita da Malik wanda duk ya daburce saboda tsoro. Jin saukar ruwa ne ya sa Sultal miƙewa tsaye. "What ƙarar me nake ji haka?" Meera ce ta yi saurin cewa "Malik ne ya saki fitsari wallahi" "Ƙarya take ita ce ta yi fitsari idan ba ka yarda ba a duba jikinta, har za ki wani laƙa min tun da kin raina ni" Sauran samarin ne suka juya da niyar tserawa Sultan ya daka musu tsawa "Gidan uban wa za ku tafi? ai sai kun aikata abin da ku ka zo aikatawa ko kuma duk na ɗaureku" Samarin na jin haka suka fashe da kuka kamar ba gardawa ba har da majina. Najmeer ce ta ce "Mtssss wai lafiya ku ke kuka kamar waɗan da aka yiwa mutuwa?" Kallonta ta mayar kan Sultan tana mai haɗe fuska "Kai ina iyayenka da mutanen gida?" Shuru Sultan ya yi yana tunano inda ya san wannan muryar amma ya kasa tunawa, be gama nazarin ba suka fara jin saukowar mutum daga sama. Mom da surutu ya tashe ta daga bacci ne ta ƙarasa saukowa, ai tana ganin ƴan fashi ga bindigogi a hannu ta ja baya a tsorace "Ƙalu innalillahi wa inna ilaihir raji'un, me zan gani haka" Har ta juya da niyar komawa Najmeer ta daka tsalle ɗaya tare da dira a gabanta, bindiga ta auna saitin kanta "Idan ki ka yi motsi sai na fasa miki kai" Sosai Mom ta tsorata dan shi kansa Sultan ya ɗan razana ganin an ɗora bindiga a kan Mahaifiyarsa "Kin ga ki sauke wannan bindigar duk abin da ki ke so zamu ba ki amma kar ki taɓa lafiyarta" Sultan ya faɗa cikin sanyin murya. Dariya Najmeer ta bushe da shi sannan ta ƙara haɗe fuska "Na zata ba ka iya magana me daɗi ba, je ka kira min mutanen gidannan kafin na fasa kan wannan matar" Cije lips Sultan ya yi ransa na zafi ya nufi sama, dakatar da shi Najmeer ta yi kafin ta ce "Ɗaya daga cikinku ya bi bayansa dan kar ya yi izgilancin kiran jami'an tsaro" Duk da cewar Malik na tsoro haka ya rufa masa baya suka nufi sama, ba jimawa suka sauko tare da su Dad har da Junaid da ke tambayar dalilin da ya sa Sultan tashinsu cikin wannan daren. Tsayawa suka yi ganin abin da ke faruwa, ga Mom hannun Najmeer an ɗora mata bindiga, cikin zafin nama Junaid ya nufeta da niyar karɓe bindigar, Najmeer kuwa ta ƙara saita Mom tana faɗin "Kana ƙara taku ɗaya zan ɗauke ƙwaƙwalwarta" Dole ta sa Junaid ja baya yana mai naushin iska. "Kai marar kunya ko? sarkin zuciya" Jin abin da ta kuma cewa ne ya ƙara fusata Junaid da Sultan, Dad ne ya ce "Ƴarnan me ku ke buƙata da mu?" "Kuɗi mike so da gwalagwalai" Najmeer ta amsa masa. Malik ne ya ce "Gaba ɗayanku ku rage tsayinku tun kafin na fasa kanku" Be gama rufe baki ba Mom da Dad suka rusuna ƙasa gami da ɗaga hannu, Junaid da Sultan kuwa sai da suka ja lokaci kafin Sultan ya fara rage tsayinsa sai kuma Junaid, dogon tsaki Najmeer ta ja rai ɓace "Na ga alamar da sauran raini a idanunku zan koya muku yanda ake ladabi" Ɗaga ma Meera hannu ta yi alamun ta zo, cike da ɗari Meera ta iso Najmeer ta ce "Ki saita kan wannan matar daga zaran ɗaya daga cikinsu ya yi wani yunƙuri ki ɗauke kanta da bindiga" "An gama Shugaba" Meera ta amsa. Najmeer da Dad ne suka nufi ɗakinsa tana bayansa sai waige-waige take. Har room ɗinsa suka shiga ya tattaro kuɗaɗe masu yawa tare da zubewa kan bed jikinsa na rawa, "Nawa ne wannan?" Cewar Najmeer tana ƙara auna masa bindiga. Dad ya ce "Million goma ne" "Baza su isheni hidimar bikina ba ka tura min ta account" "Bikinki baiwar Allah?" "Yes bikina aure zan yi kuma kuɗin da nake da baza su isheni haɗa kayan ɗaki ba shiyasa na yanke hukuncin na nemi kuɗi da ƙarfin iko na" Najmeer ta faɗa tana yarfa ido kamar ƴar daba. Jikin Dad a sanyaye ya ce "Amma idan baza ki damu ba akwai wasu tambayoyi da zan yi miki" "Faɗi yambayarka da sauri dan banada lokaci" "Tambayar shine dama ke ƴar fashi ce ko kuma wannan dalilin ne ya sa ki ka fara zuwa fashi?" Ɗan tsayawa Najmeer ta yi tana mai gyaɗa kai sai kuma hawaye ya zubo mata da sauri ta share dan kar Dad ya gani amma abin da bata saniba shine Dad ya ga lokacin da take share hawayen, kan bed ya zauna a hankali ya ce "Ina iyayenki suke?" Wannan tambayar ce ta girgiza Najmeer hakan ya sa ta fashe da kuka gami da sakin bindigar da ke hannunta, sosai tausayinta ya kama Dad tare da jin wani abin a ransa game da yarinyar amma ya kasa gane menene wannan, sai da Najmeer ta ci kukanta Dad kuwa be hanata ba dan ya san akwai abin da ke damunta a zuciya, ƙyallen da ke fuskarta ta cire nan take kyakykyawar fuskarta ta bayyana lokaci ɗaya gaban Dad ya faɗi har ya miƙe tsaye be san lokaci ba, jikinsa na rawa ya ce "Yarinya wacece ke?" Jin tambayar da ya sake yi mata ne ya sa Najmeer faɗin "Ba kowa ba ce ni face marainiya wadda ta rasa uwa da uba tun bata san komi ba, na kasance talaka me ƙaramin ƙarfi wadda ta ɗauki rayuwa irinta manyan yara, a halin yanzu na saba da daula ba zan iya rayuwa cikin talauci ba" "Amma meyesa ki ka zaɓawa kanki mummunar rayuwa irin wannan?" "Saboda haka suke son ganina cikin rayuwar shiyasa na nuna musu cewar zan aikata fiye da yanda suke so?" Mamaki ne ya kama Dad dan be san su waye take magana ba, kawar da zancen ya yi da faɗin "Akwai inda ki ke zama ne? ina nufin tare da wa ki ke zaune a yanzu?" "Gurin Mahaifiyar Mamana ita ce me kula da ni" Jinjina kai Dad ya yi kafin ya ce "Na ɗauki nauyin komi na bikinki har da gidan da za ku zauna ke da mijinki, kuma na ɗauki nauyin komi naki ke da Kakarki za ku dawo gidana da zama duk abin da ku ke buƙata ki min magana, na lura sosai akwai babban al'amari tattare da ke" Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Kina makaranta ne?" "Primary kawai na yi daga nan ban ƙarasa ba, a gefen islamiyya na yi haddar alqur'an da sauran littafai" Ba ƙaramin burge Dad ta yi ba jin ta yi karatun islamiyya sosai. "Ya sunanki?" Ya sake tambayarta. "Sunana Najmeer" "Masha Allah Najmeer daga yau kin zamo ƴata kuma na yi alƙwarin riƙe ki hannu bibbiyu, yanzu ku koma gida amma kafinnan ki bani address ɗin gidanku zamu shigo zuwa gobe" Godiya sosai Najmeer ta yi masa tare da bashi address ɗinsu, haka kawai take jin Dattijon har cikin ranta, a zuciya take faɗin amma Sultan ya yi sa'ar Mahaifi ba kamar shi me mugun hali ba. Sai da ta rufe fuska kafin suka fito daga ɗakin. Ba su Meera ba hatta su Junaid sun sha mamakin ganin Dad da Najmeer na saukowa cikin fara'a da annashuwa kuma ba komi a hannunta alamun bata karɓi kuɗin da ta ce ba. Ai basu ƙara tsinkewa ba sai da suka ga Dad ya ce "To sai da safe a gaida mutan gida" Najmeer na murmushi ta ce "Mutan gida za su ji Alhaji" Ɗan ɓata fuska Dad ya yi alamun ya yi fushi "Kar ki sake kirana Alhaji ki kirani da Dad kamar yanda sauran Ƴan uwanki ke kira na" "Afwan Dad ba zan ƙara ba" "Yaww Allah ya yi miki albaka" "Ameen Dad" Najmeer ta amsa tana mai kallon su Meera ta ce "Mu tafi ko" Ficewa daga gidan ta yi su Malik na bayanta kamar raƙumi da akala cike da al'ajabi. Sultan ne ya ce "Dad me nake shirin gani, kana nufin wannan ƴar fashi ka ke kira da ƴarka?" Kusa da Mom Dad ya zauna yana faɗin "Ƙwarai kuwa labarinta abin tausayi ne, shiyasa na yanke hukuncin dawo da su gidana tare da ɗaukar nauyin aurenta saboda shine dalilin da ya sa ta shiga wannan halin" "Wallahi ba zai taɓa yuwa ba, babu wanda zai kawo mana ƴar fashi cikin gida" Mom ta faɗa a zafafe. Junaid de ya kasa furta komi sai kallonsu da yake, tashi Dad ya yi yana mai gyara zaman rigarsa "Magana ta rage gareku hukunci na yanke ba wanda ya isa ya karya dokar da na shimfiɗa, dole su dawo gidana da zama" Ba tare da ya kuma cewa komi ba ya nufi room ɗinsa. Mom na masa magana amma ko gefen da take be kalla ba, bayansa ta bi tana kiransa tare da faɗin ba wanda zai kawo musu ƴar fashi cikin gida amma Dad ko a jikinsa sai ma shigewa ɗakinsa da ya yi. Tsananin takaici ne ya hana Junaid ɗagawa daga inda yake Sultan ko sai huci yake kamar kumurcin maciji. Su Najmeer kuwa tun da suka fara tafiya ba wanda ya ce ƙala har suka iso ƙofar gidansu Malik, anan Najmeer ta tura masa kuɗin da ta yi masa alƙwari har ma da ƙari, sosai ya rinƙa yi mata godiya tare da sauran samarin. Barin gurin suka yi ganin ukun dare ya yi, gudu Najmeer ke yi kan titi har suka iso gida, Meera dai ta aje tambayoyinta dan ta san baza ta samu amsa a yanzu ba. A gajiye ta shige toilet dan watsa ruwa ga ciyon kai da ke damunta, nan kuma ta ji tunanin Prince ya faɗo mata a rai lokaci ɗaya ta saki murmushi tana mai lumshe ido, a hankali ta furta "Miyar yauƙi....." Yanda ta ja sunan ne ya bata dariya ai kuwa ta shiga dariya ita ɗaya a bayi, ta ɗauki mintuna goma kafin ta fito tana mai tsane gashin kanta. Kan kujerar da ke gaban mirrow ta zauna sannan ta fara shafa mai, a hankali Meera ta ɗago tana faɗin "A gaskiya lamarinki na rikitani Najmeer" "Meyesa ki ka ce hakan?" "Kin san abin da nake nufi ai, shi kuma Dad ɗinsu Sultan a ina ki ka san shi? ko yana cikin Alhazawanki ne" Bushewa da dariya Najmeer ta yi "Wai dama duk wannan ya sa ki ke faɗin haka? mtsss ni fa ko saninsa ban yi ba kawai taimaka mana zai yi" Duk abin da ya faru Najmeer ta kawashe ta sanarwa Meera, cikin kiɗima Meera ta ce "Mun shiga uku kina nufin gidansu Sultan zamu koma da zama? ai kuwa akwai babban tashin hankali marar ƙarshe" "Ke dallah Malama babu wani tashin hankali sai dai ayi ta gwarama duk rana ta Allah, dan ba zan raga musu ba har uwarsu me ɗaure musu suna yanda suke so, ke har Junaid sai na koya masa hankali a gidannan dan bawa zan maida shi" Dariya Meera ta fara har da riƙe ciki "Junaid ɗin ne za ki mayar bawa? lallai akwai yaƙi a gabanki" "Au kina ɗauka ba zan iya ba kenan? ai zamu gani sai ki zuba ido tun da tare da ke zamu zauna a gidan sai kin ce na faɗa miki" Jinjina kai Meera ta yi "Hmmm nikam zan ga chakwakiya Sultan Junaid Meera a gida ɗaya ai kuwa sai gidannan ya kama da wuta" "Hhhhhhh kin ga Meera barni haka dan Allah bacci nake ji gobe zamu ƙarasa wannan zancen" Najmeer ta faɗa tana mai hayewa kan bed. .......................... A gefen su Sultan kuwa yau tun da garin Allah ya waye Mom ta hana masu aiki girka komi a gidan, Sultan da Junaid ma a office suka karya, Dad kam be ƙara bi ta kanta ba dan ya san duk wannan abin da take saboda su Najmeer da zai kawo gidan ne. Har yamma ta yi Mom ta kasa samun natsuwa, wayarta ta ɗauka tare da latsa numbern ƙawarta Hajiya Halima bugu ɗaya ta ɗaga tana mai faɗin "Da girman kujerarki manya-manya maganin ƙanana" Cikin damuwa Mom ta ce "Hajiya Halima ina da damuwa wallahi na rasa yanda zan ɓullowa wannan lamarin?" "Subhanallahi me yake faruwa ne? fatar dai ba aure Alhaji zai ƙara ba?" Mom ne ta ce "A a ko ɗaya amma kamar auren ne, dan duk wanda zai kwaso maka talakawa ƴan fashi da makami ya kawo cikin gida ai kamar kishiya ce ya ƙaro maka" "Banganeba Hajiya Salma ki yi min yanda zan fahimta" Sai da Mom ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kwashe duk abin da ya faru ta zayyanawa Hajiya Halima. "Kutumar ubancan, yanzu Alhajin ya rasa waɗan da zai kawo gidansa sai yarinyar da ta tashi kasheki da ƴaƴanki? wai tsaya ki ka ce ya maidata ƴarsa, bakya tsoron ya tattara dukiyarsa ya mallaka mata" A rikice Mom ta ce "Ƙarya ne wallahi ai baza ta saɓu ba, idan har suka shigo gidannan da ƙafarsu za su koma dan sai na hana su zaman lafiya" "Yawwa ƙawata ki hana su shan iska dan lamarinnan ya fi a zuba ido dole ki tashi tsaye tun kafin a rabaki da kowa naki" Cewar Hajiya Halima tana mai ɗaga murya, sosai maganganunta suka shigi Mom har ta ƙara jin ƙarfin gwuiwa. Sallama suka yi a kan cewa za su yi waya anjima. Junaid ne ya shigo Sultan na rufa masa baya da alama daga aiki suka fito bakinsu ɗauke da sallama, yau an yi sa'a Sultan har da gaisuwa. A gajiye Junaid ya ce "Mom ina wuni?" "Lafiya ina Dad ɗin naku? ko da yake Sultan kai zan tambaya tun da a guri ɗaya ku ke" Kallon Junaid Sultan ya yi alamun ya faɗa ko ya yi shuru, Mom ce ta kuma cewa "Sultan magana nake ina Dad ɗinku?" "Ya tafi ɗauko ƴar fashi da ahalinta" Sultan ya faɗa yana mai barin gurin, salati Mom ta rafka har da tafa hannu "Shikenan za su raba ni da mijina, saura kuma ƴaƴana da alama wannan shegiyar yarinyar masifa ce a rayuwarmu tun da har an fara ta kan uban ƴaƴana" Junaid ne ya ce "Mom please ki kwantar da hankalinki Dad ya ce yarinyar nan ba halinta ba ne kuma ya ce aure ma zata yi" "Kai amma shashasha ne marar tunani, kana ganin za'a raba ku da dukiyar mahaifinku amma ko a jikinka" "Ki gafarceni Mom amma a ganina kamar taimako ne wannan" "Taimakon ubanka na ce taimakon ubanka zai yi? ba dan Allah ya sa ina da rabon shan ruwa ba da yanzu na daɗe da mutuwa, a gaban idonka shegiyar yarinyar ta ɗoran bindiga a kai amma ka ke faɗin taimako tashi ka bani guri tun kafin ranka ya ɓaci, na lura kaine ka biyo halin uban naka gurin taimakonku wata rana sai kun haɗu da Aljana" Mom ta ƙarasa maganar rai ɓace, haƙuri Junaid ya bata kafin ya nufi room ɗinsa, sanin cewa duk abin da zai faɗawa Mom a yanzu baza ta saurare shi ba balle ta yarda. Dad kuwa har bakin gate ɗin suka isa tare da horn gate Man ya buɗe musu dan Najmeer ta faɗa masa cewar tana da baƙo, motoci hamsin ne masu uban kyau da ɗaukar ido, har pearking space suka isa sosai mamaki ya kama Dad ganin gidan da su Najmeer ke ciki. A parlour Maryam ta masa rakiya tare da zube masa kayan abinci kala-kala, dan Najmeer ta dawo da Maryam nan gidan kafin su koma nasu gidan. Ruwa kawai Dad ya sha dan baya jin yunwa, ba jimawa Meera da Najmeer suka shigo sai Mamu da ke bayansu, Najmeer ce kawai ta yi shigar banza dan wando ne daidai santala santalan cinyoyinta da ƴar ƙaramar riga me gajeren hannu, ba ƙaramin kyau shigar jikinta ta yi mata ba, kallo ɗaya Dad ya yi mata ya sauke kai ƙasa, Mamu kuwa har ƙasa ta tsuguna tana gaishe shi da sauri Dad ya miƙe yana mai faɗin "Haba Hajiya dan Allah ki miƙe ai ni ne ya dace na gaisheki, fatar mun sameku lafiya?" Bakin Mamu na rawa ta amsa da "Lafiya ƙalau Cheif ya jama'a da hidima" Sai da Dad ya yi murmushi kafin ya ce "Alhamdulillah, amma Hajiya ya aka yi ki ka sanni har haka" Caraffff Mamu ta karɓe da cewa "Ai Najmeer ce ta ce za ka zo gidanmu a yau, na zata ƙaryar da ta saba ce ta sharara min ashe lamarin azimun ne, Allah ya yi da rabon zamu gana" "Masha Allah abin da jikanyarki ta faɗa miki gaskiya ne tashi ki zauna kan Kujera" Dad ya faɗa yana nuna mata guri, Najmeer da Meera ko suka gaishe shi cikin girmamawa, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Najmeer je ki saka hijab ki dawo" Har zata yarfa masa magana sai kuma ta kasa saboda gwarjinin da ya yi mata, dole ta sa ta nufi room dan ɗauko hijab ba dan tana so ba. Sanye cikin ƙaton hijab ɗinta ta fito tana tura baki, anan ta samu Mamu sai zuba zance take babu abin da bata sanarwa Dad ba har da auren da Najmeer zata yi da kuma iyayen ƙarya da ta hayo, sosai Dad ya girgiza jin cewar Najmeer ƴar bariki ce, a ransa ya ce shiyasa bata kunyar irin wannan shigar, kusa da Meera ta zauna tana mai haɗe fuska. Sai da Dad ya ƙare mata kallo kafin ya ce "Najmeer gaskiya kin aikata babban kuskure, kuma kina cikin aikatawa, ina ki ka taɓa ganin mace ta sakawa kanta rayuwar ƙarya irin haka? bakya tsoron mijin da za ki aura ya gane ke wacece?" Sunkuyar da kai Najmeer ta yi alamun kunya, sai kuma ta ɗago tana mai kallon Dad idanunta sun ciko da ƙwalla "Wallahi ban taɓa aikata zina ba, kuma bansan daɗin zina a rayuwata ba, ko wannan abin da nake ba yin kaina ba ne, addu'ar ku kawai nake nema amma ba zan iya daina yawo da rayuwar ƙarya ba ko da kuwa aure na yi" "Hehehe haukar banza waye ki ke cewa ba ki taɓa aikata zinar ba? je ki faɗawa shashashu amma ba mu ba, wasu lokutan ko gida bakya kwana kina can gurin yawonki na banza da wofi shine za ki ce ba ki taɓa kwana da namiji ba, ashe haihuwar jiya-jiya ce mu da ki ke faɗa mana shirme" Mamu ta faɗa tana mai jan dogon tsaki, Meera ce ta ce "Ni shaidata ce Najmeer bata taɓa aikata zina ba, saboda yanda take riƙo da addini ba zai barta ta aikata wannan babban laifin ba saboda ita sallah ma tana ƙarawa bawa imani a ransa musamman idan yana yinta cikin lokaci" Harara Mamu ta gallawa Meera "Yooo ai duk halinku ɗaya kawai ƙarya ce Najmeer ta fiki iyawa da kuma wayewa, amma yanzu zata iya buga waya ta ce gasu nan hanyar zuwa wata ƙasar ita da ƴan gidansu alhalin ko hanyar da jirgi ke bi bata saniba" Dariya su Dad suka kwashe da shi har da Najmeer jin abin da Mamu ke faɗa, kuma sai ta haɗe fuska sosai tana ɓaro zance. Dad ne ya ce "Okay yanzu dai shikenan, ni kaina duk da cewar daga jiya zuwa yau na san wannan jikanyar taki amma zan iya yarda da abin da ta faɗa, kuma na yanke shawarar za ku koma gidana da zama amma da sharaɗi" "Faɗi sharaɗinka Alhaji da yardar Allah zamu kiyaye" Cewar Mamu cikin zumuɗi. Gyara zama Dad ya yi kafin ya maida kallonsa kan Najmeer ya fara da faɗin "Da farko za'a tsayar da maganar aurenki har lokacin da ki ka fara makaranta ina son ku shiga School ke da wannan ƙawar taki na ji kakarki ta ce sunanta Meera, sharaɗi na biyu za ki daina kwana waje har abada, sharaɗi na uku za ki daina ƙarya" Waro ido Najmeer ta yi sai kuma ta girgiza kai alamun baza ta iya ba, "Nikam ba zan daina kwana waje ba, kuma bana son makarantar da za ka saka ni zancen ƙarya kuma sai dai idan ba'a kirani ba" Meera da ke gefe ne ta danne dariyarta ganin Najmeer ta dage baza ta daina halayyarta ba, ajiyar zuciya Dad ya sauke kafin ya kuma cewa "Dan Allah ki min wannan alfarmar ko dan matsayin ƴata da na ɗaukeki" Kallonsa Najmeer ta yi sai kuma ya bata tausayi, cikin shagwaɓa ta ce "Zan daina insha Allah amma sai kun bini a hankali saboda shi me hali a sannu yake dainawa" "Shikenan na gode, zancen auren fa?" Dad ya faɗa yana murmushi. "Shima na fasa har sai na fara school, amma ni zan zaɓawa kaina makarantar da nake so" "Okay fine duk makarantar da ki ke so zan saka ki da yardar Allah, ku shiya komi naku zuwa gobe zan turo a je da ku gida" Cikin farinciki Najmeer ta rinƙa masa godiya, barin Mamu wadda har da kukanta, itama Meera ta masa godiya sosai da kuma addu'a. Har gurin motocinsa suka yi masa rakiya kafin suka dawo ciki. Tun a parloun Mamu ke sakawa Najmeer albaka, "Ƴar nan kin gama biya min Allah ya jiƙan magaba, wai yau ni ce zan shiga gidan Chief shugaban masu kuɗin garin Jos" Sai kuma ta ƙara fashewa da kuka har da kwanciya a ƙasa, taɓe baki Najmeer ta yi "Wai ke Mamu meye haka ne? idan na ga dama sai na ce ba inda zamu tafi" Zumbur Mamu ta miƙe kamar zararra "Amma kin cika ƴar baƙin ciki me mugun hali, da farko kin cewa Cheif baza ki daina halayyarki ba yanzu kina faɗin za ki fasa zuwa gidan, idan kin fasa bakya wa Allah" "Haka ki ka ce ko? shikenan na fasa zuwa" "Au da gaske ki ke kenan? har da ƙara maimaitawa" "Dama a zatonki ƙarya ne, yanzu ma zan bar gidannan sai na yi kwana uku kafin na dawo akwai wani suger Daddy wanda nake son mu shaƙata da shi" "Waye kuma Sugari Daddyn?" "Suger Daddy aka ce ba Sugari Daddy ba, saurayina kenan amma kuma ya haifeni a shekaru" Najmeer ta faɗa tana mai jifa da hijab ɗin jikinta dama ya dameta sosai. Bata jira abin da Mamu zata ce ba ta nufi room ɗinta tare da juya hips kamar wadda ke yin hakan da saninta. ........... Tun a harabar gida Dad ya hangi Mom riƙe da ƙugu sai huci take har motocinsa suka tsaya, ba tare da ya ce uffan ba ya nufi hanyar parlour fuskarsa a ɗaure, ganin ba wanda ke biye da shi ne ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana mai bin bayansa, "Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya" "Da ban dawo lafiya ba za ki ganni?" Dad ya faɗa a taƙaice. "Laifin me na yi haka? da ake ƙoƙarin sauke haushi kaina" A fusace Dad ya juyo fuskarsa babu alamar wasa ya nunata da yatsa "Ki maida hankali ki saurareni da kyau Salma, na lura daga jiya zuwa yau akwai abin da ke damunki wallahi ki shiga hankainki bana cikin irin mazan da matansu ke juya su, idan har kina son zaman lafiya dole za ki girmama duk wanda na kawo gidannan a matsayin nawa" "Amma Alhaji......." Saurin ɗaga mata hannu ya yi "Ban son jin komi daga gareki, in kina son zaman lafiya ki tabbata cewa gobe idan baƙina suka zo ki kama girmanki a matsayinki na uwa" Barin gurin ya yi cike da takaicin hali irin na matarsa, a rauwarta bata ƙaunar talaka balle wani ya zo gidanta. Saukowar Sultan ne ya sa ta maida kallonta gurinsa, sanye yake cikin jallabiya fara me kyau gashin kansa ya sha gyara tamkar ba shi ba, ƙamshin turarensa ne ya baje gaba ɗaya parlourn har ya ƙaraso inda Mom ke tsaye kamar an dasa ta. Ƙarar bell ɗin ƙofar ne ya sa Sultan faɗin "Majeed come in" Shigowa Majeed ya yi bakinsa ɗauke da sallama, gaida Mom ya yi ta amsa sama-sama tana mai barin gurin jiki na rawa, dan har yanzu ba wani sakewa da Sultal ɗin ta yi ba. Hannu Majeed ya miƙa ma Sultan suka tafa, "Guy wallahi yunwa nake ji please a kawo min wani abun kafin a kira sallar magrib" Sai da Sultan ya hararesa kafin ya ce "Zan yi maka dan Allah ba dan ka isa ba" Kichen ya nufa Majeed kuwa ya haura ɗakinsa yana dariya. A hankali ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama jikinsa ne ya hau rawa bakinsa kuwa ya shiga ɓari kamar wanda aka kunnawa lantarki ganin Zakanya zaune tsakiyar ɗaki tana mai kallon ƙofar, suna haɗa ido da Majeed ta yi saurin ɓacewa daidai lokacin da Sultan ya ƙaraso gurin da gudu hannunsa ɗauke da basket, da ƙarfi ya janyo Majeed ta baya, a mugun tsorace Majeed ya ja dogon numfashi gami da sumewa jikin Sultan. A kiɗime Sultan ya shige da shi ɗakin yana mai faɗin "Sai da na ce kar ki zo amma kin kasa saurara yanzu kalli abin da ki ka janyo kuma kin tafi kin barni da aiki" Dariya Sultan ya rinƙa ji amma baya ganinta abin da ya ƙara ɓata masa rai kenan ya nufi frigde a fusace, ruwan roba ya ɗauko me sanyi, ɓalle ruwan ya yi tare da kwara ma Majeed a jiki, sai da ya kwara masa ruwan so uku amma be farka ma, hankalinsa ne ya mugun tashi kar dai Majeed ya mutu, Sultan ya faɗa a ransa yana mai zama gefen bed, "Ba mutuwa ya yi ba yanzunnan zai farka kawai ka sake zuba masa ruwan da ke hannunka" Zakanyar ta faɗa cikin muryata me rikitarwa ba tare da Sultan ya ganta ba, a hanzarce ya ƙara watsawa Majeed ruwan sai kuwa ya ja numfashi da ƙarfi, ɗagowa ya yi yana mai faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wallahi Zaki a ɗakinnan" Yunƙurawa ya yi da niyar gudu Sultan ya damƙo shi "Kai amma marar hankali ne, mafarki ne fa ka ke yi tun ɗazu nake zuba maka ruwa amma sai ihu ka ke cikin bacci wai Zaki ya biyo ka" A mamakince Majeed ya zauna tare da dafe kansa "Mafarki kuma? na zata gaskiya ne amma ai bansan lokacin da na yi baccin ba" "Ka aje duk tambayoyinka ni banada lokacin amsawa, ya za'a yi ka ga Zaki a ɗakina kamar dai a Jeji, malam ga abincinka can sai ka ci dan an kusa kiran sallah" Sultan ya faɗa yana mai barin gurin. Abincin Majeed ya fara buɗewa yana mai gazgata abin da ya gani, dan shi kam ya san ba mafarki yake ba gaba ɗaya ya kasa yarda da idanuwansa. ....................... Misalin tara na dare ne Najmeer da Meera suka fito cikin shigar ƙananan kaya kamar yanda suka saba, yau Najmeer ta ce za su tafi Clup na ƙarshe tun da gobe za su koma gidansu Junaid, ba ƙaramin kyau kayan jikinta suka yi ba doguwar riga ce red me adon duwatsuna daidai cinyarsa, daga saman na shanunta rigar ta kama sai ƙasan gurin manyan hips ɗinta da ke ƙarawa jikinta kyau, duk taku ɗaya sai mazaunanta sun juya hakan ya ƙara fitar da tafiyarta. Ko da suka fito ba kowa a parlourn hakan ya sa su ficewa cikin sanɗa tun kafin Mamu ta ankare. Najmeer ce me driving Meera na waya da Saurayinta a gefe har suka iso Clup, a ɗan tsorace Meera ta ce "Wai anan zamu zo? ko kin mance abin da ya faru wancan lokacin" "Dan wani abu ya faru sai a hana min zuwa Clup, ko wannan lokacin idan ya shigo sai na......" Tun kafin ta rufe baki ta ji kamassssss an daki motar da suke ciki, da sauri Najmeer da Meera suka fito dan ganin waye. Motocin Sultan ne guda goma jere da juna masu tsadar gaske, gurin da aka daka Najmeer ta duba sai ga glup ɗin bayan motar ya fashe, "Kambala'i.........., wallahi ba ka isaba sai ka gyara min motana" Inda Sultan ɗin ke tsaye ta nufa tana mai zuba masifa, tana isa bata yi wata-wata ba ta wanke shi da mahaukacin mari "Allah ya tsinewa gadara da nuna isa, na ci uwarka a iskanci" Ta faɗa tana mai kama kwalar rigarsa, a mugun fusace Sultan ya damƙo gashin kanta tare da jinginata bayan motarsa da ƙarfi cikin tsantsar mugunta, jikinsa ne ya hau rawa bakinsa ya shiga neman kalmar da zai fara magana kusan mintuna biyu a lokacin riƙon da ya yiwa Najmeer ya fara yi mata zafi dan har gurin ya soma yin ja, "Ki ka mareni....?" Sultan ya faɗa muryarsa na sarƙewa. Itama Najmeer cikin ƙarfin hali ta ce "Yes ammareka kai waye? kuma sai ka gyara min motana" Meera da ke gefe ne ta shige motar da mahaukacin gudu ta bar Clup ɗin tare da nufar gida, dan ta san yau kam akwai bala'i. "Na lura tun ranar da na fara haɗuwa da ke ki ke raina min hankali yau zan koya miki ladabi" Cewar Sultan yana rufe mata ido, umarni ya ba Drivern sa da ya ciro masa wani ƙyalle a mota, nan kuwa Driver ya kawo masa, da sauri Sultan ya rufewa Najmeer ƙwayar idonta saboda da shi take samun damar canja halitta, idan har idonta na rufe bata iya komawa Mage. Buge-buge ta fara tana ƙoƙarin janye ƙyallen amma Sultan be bata damar hakan ba, dan ƙarfinsu ba ɗaya ba. Cikin Clup ɗin ya nufa da ida wanda kowa ya fito waje sai shi ɗaya, sai da ya shige kafin mutane suka rufa masa baya ana koɗa shi da yi masa kirari. A wani haɗaɗɗen ɗakin ya nufa da ita a lokacin Najmeer ta fara ganin jiri saboda bata jure rufe mata ido da wani abun, ɗaki ne me masifar kyau da ɗaukar ido wanda Sultan ke sheƙe ayarsa a ciki idan ya zo Clup. Duk iya ƙoƙarin Najmeer na ganin ta janye wannan ƙyallen ta kasa saboda ya riƙe mata hannu, cikin salon mugunta ya ce "Yau zan kawo ƙarshen rashin kunyar da ki ke min tun da na lura cewar ke marar kunya ce" Ya faɗa yana haɗa kanta da ƙofar ɗakin, wata irin razananniyar ƙara Najmeer ta saki wadda ta sa ɗakin amsawa tana mai zubewa ƙasa a sume. Ba tare da jin tausayi ba Sultan ya saki dariyar mugunta yana mai fara rage kayan jikinsa, ƙofar room ɗin ya saka ma key sannan ya dawo inda take kwance ya tallafota zuwa kan bed, a hankali ya ƙura mata ido yana mai kallon kyakykyawar fuskarta me ɗauke da ɗan ƙaramin bakinta be san lokacin da ya haɗe bakinsu guri ɗaya ba yana mai sakar mata hort kiss me rikita tunani. Sosai Sultan ke sarrafa bakinsa cikin nata har ya fara ficewa a hayyacinsa, tun da Allah ya halicce shi be taɓa jin daɗin kiss ba sai wannan karon har ya mance wadda yake tare da ita, a haukace ya shiga sarrafata yana mai yamutsata har ya cire ƴar ficikar rigar da ke jikinta, wani mugun numfashi ya ja ganin halittar jikinta tamkar ita ta yi kanta, sannu a hankali ya fara shinshina wuyanta da ke fitar da ƙamshin turare. Gaba ɗaya Sultan ya ruɗe ya fice a hankalinsa har ya fara ƙoƙarin shiga hanyarsa amma abun ya gagara, duk iya yinsa na ganin ya shige amma ya kasa, yanda ya rinƙa yi ne ya sa Najmeer jan numfashi saboda jin kafurin zafi na shiga ta ƙasanta, ba ƙaramin razana ya yi ba ganin ya kasa tafiya, mamakin duniya kuwa ya ishe shi, duk da cewar baya hayyacinsa amma sai da ya gane cewar Najmeer bata taɓa kwana da wani namijin ba, cikin sanyin jiki ya koma gefe yana mai dafe mararsa da ƙarfi, "Ya Allah......" Ya faɗa cikin sanyin murya, lokaci ɗaya ya miƙe a galabaice ya maida kayansa tare da ficewa ɗakin. Sai da Najmeer ta kai mintuna goma a haka kafin ta fara motsi gami da dafe kanta, a rikice ta kurma ihu tana mai kiran sunan Mamu jin zafin da ke bi ta ƙasanta, ƙyallen da ke fuskarta ta cire sai yanzu take tunano abin da ya faru a tare kuma ta saki wani irin kuka me ban tausayi duk a tunaninta Sultan ya keta mata haddi, kuka take sosai wanda duk yanda ka kai ga rashin imani sai ka tausaya mata, ta jima tana kukan gami da zaginsa da saka masa Allah ya isa buhu-buhu, wata tsanarsa ce ke ƙara dira a ranta lokaci ɗaya ta saki ihun da ya sa gaba ɗaya Clup ɗin girgiza, nan take ta zama wata jibgegiyar Mage wadda ta lunka girman yanda take zama so goma, mutanen da ke Clup ɗin ko sun tarwatse jin yanda ƙasa ke girgiza kamar zata rufe da su. A hankali ta dawo halittar mutum sanye cikin kayanta, takalmanta da ke gefe ta saka tare da ficewa daga room ɗin ta nufi titi kamar wadda ke ciyon jiki, tafiya take amma hankalinta baya jikinta hawaye na sauka tsiri-tsiri kan haɗaɗɗiyar fuskarta, a ranta take faɗin shikenan Sultan ya gama da rayuwata ba bu wani abin da ya dace face na kashe kaina a yanzu. Jin ƙarar mota ne ya sa ta saya ba tare da ta juyo ba, motar na tsawa Nameer ta cigaba da tafiya sai kuma ta ji an ƙara yin horn a bayanta, a hasale ta juyo dan ganin waye amma hasken motar ya hanata gane wanda ke ciki. Ta kai mintuna biyu a haka me motar be tafi ba ita kuma bata matsa ba, Allah ya sa titin ba kowa dan sai can ba'a rasa ba motoci ko mashin ke giftawa, ba zato ba tsammani taji an ja hannunta tare da matsar da ita gefe, ɗago kan da zata yi suka yi ido huɗu da shi, bakinta na rawa idonuwanta kuwa hawaye ne cike take furta "Prince...." Sai kuma ta rungumeshi tare da fashewa da kukan da ke tsaye a ranta, sosai take kukan gami da ƙara matse shi a jikinta ko zata samu sassaucin zafin da zuciyarta ke yi, ganin yanda take kukan ne ya sa Prince kasa cire ta a jikinsa amma hannayensa a ƙasa ba tare da ya taɓa ta ba, rawanin da ke fuskarsa ya gyara kamar kullum ƙwayar idonsa kawai ake gani, cikin sanyin jiki ya janyeta daga ƙirjinsa "Malama lafiya za ki wani manne min a jiki? bayan na ga inda ki ka fito yanzu" Rikitattun idanunta ta ɗago "Kaima ka san abin da ya faru da ni ne?" Najmeer ta faɗa muryarta na sarƙewa. "Me ya faru da ke?" Kasa bashi amsa ta yi sai kawai ta cigaba da tafiya, hannunta ya kuma riƙowa tare da faɗin "Ke tsaya ina zuwa haka? da alama kin yi shaye-shaye a Clup ɗin da ki ka tafi mu je na kaiki gida kafin mota ta kaɗe ki a hanya" "Bana buƙatar taimakonka" Najmeer ta faɗa cikin wata irin muryar da ta firgita shi, duk da cewar ya ji tsoro amma hakan be hana shi haɗe fuska gami da watsa mata mayatattun idanuwansa ba, da sauri ta sunne kai dan ƙwarjinin da ya yi mata. Mota ya nufa da ita tana cijewa har ya shigar da ita a gaba. Kasancewar yau ba Dogarai ne ya sa shi ke jan motar da kansa, tun da suka fara tafiya Najmeer ta kasa cewa komi haka shima Prince har suka iso ƙofar gidan, ganin bata da niyar fita ne ya sa shi fitowa ya janyowa waje, da mamaki ya ga ta nufi wata hanyar ba tare da ta shiga gidan ba, "Na shiga uku wai me ke damun wannan yarinyar ne?" "Ya faɗa a hasale. Bayanta ya bi da sauri ya riƙota "Ina zuwa kuma ga gidanku can" "Mun canja gida na ɗan wani lokacin" Najmeer ta faɗa tana mai rufe ido alamun jiri na ɗibarta, ganin haka ya sa Prince faɗin "Faɗa min addrees ɗin sai na kai ki" Da ƙyar ta iya ƙarasa faɗa masa tana gamawa ta zube jikinsa a sume, cikin tashin hankali ya rungumota jikinsa yana istigfari, a bayan mota ya kwantar da ita sannan ya nufi gidan da ta faɗa masa, kasancewar akwai number a gidan ne ya sa be bashi wahala ba, horn ya yi gate man ya buɗe masa. A harabar gida ya tarar da su Mamu da Meera a tsaye kamar masu jiran sadaka, ba tare da ya kallesu ba ya fito da Najmeer kwance kan ƙirjinsa, Meera ce ta yi masa jagora har room ɗinsu, Mamu sai kuka take tana faɗin an kashe mata jikanya hankalinsu ya kwanta. Shi dai Prince be amsa mata ba dan ya san maganarsa zai sa Mamu ta zage shi tassss. *Wai waye ya turo neman auren Najmeer?* *Wacece wannan Zakanyar?* *Menene dalilin da ya sa Najmeer ke canja halitta?* *Waye Prince?* *Ya zaman Najmeer zai kasance a gidansu Sultan?* *Meyesa Sultan ke zama Kada?* *Menene dalilin da ya sa suke son kashe Najmeer?* *Sultan, Junaid, Prince, a cikinsu waye zai auri Najmeer* *Wanne mataki Najmeer zata ɗauka saboda zargin cewa Sultan ya lalata mata rayuwa?* *Ya Mom zata yi idan su Najmeer suka dawo gidansu da zama?* *Me ku ke ganin zai faru idan har Sultan Junaid da Mom suka gane cewar Najmeer ce ƴar fashin da ta zo gidansu kuma wadda Dad ya mayar a matsayin ƴarsa?* *Duk amsoshin wannnan tambayar tana cikin cigaban littafin Shalelen Alhazawa, idan kuna buƙatar sanin abin da zai faru sai ku biya 500 kacal domin karanta wannan littafi me tattare da nishaɗi da kuma ban al'ajabi. Alhamdulillah Allah abin godiya a nan na kawo ƙarshen free pages na littafin Shalelen Alhazawa, duk me buƙatar cigabansa akwai account number a saman page ɗinnan tare da number ta shaidar biya, thank you all* Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels