Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

numfashin ta na kaiwa yana kawowa da sauri ya ƙaraso gurin ta.
ɗago mai hannu tayi tace '' basai ka taɓani ba zan iya tashi...,
dafa bango tayi dakyar tana tafiya limshe danuwanta, tayi da suka cika da kwalla bata so ta zubarwa da altab hawaye domin hawayen ta masifa ne a rayuwar'sa biyota yayi tace '' wallahi tun kafin ranka ya ɓaci ka kawshe matan da kakawo cikin gidan nan ban da iskanci da wulakanci gidan auren ka zaka kawo mata kuna shaye shaye..,
to shikkenan ummi zan kwashe su amma bazan je na tawo da matata..
da sauri ta juyo jin zancen da ya furta anya kuwa kan'sa ƙalau lallai, ɗazu ma da ta mara mai baya dan dai Hajiya rukayya ta nuna mata rashin mutunci ne amma ko dukan da yayi wa samha bata ji dad'i ba duk da itama da laifin ta idan mace za tayi aure komai barin sa take yi a waje ta shigo gidan mijin ta da kyakkyawar niya amma ita bata san wannan ba ta dinga tara matan banza kuma bata kunyar wani ya gani suna shaye shaye ajiyar zuciya ta sauke tace '' ga hanya nan tafi wallahi yan uwanta sun shirya tsaf kana zuwa zasu kama ka haka kurum ka kama yar mutane ka naɗa mata duka ita , duk abin da ake aikatawa me take maka..? wallahi ko da wasa kar na kara ji ka saka hannu ka daki yar mutane mace da kake gani daraja ne da ita..,
shiru yayi har ta gama zancen ta , ta fita da sauri hany ta biyo bayan sa tace '' Man what is happening..?,
shafa gefen fuskar'ta yayi yace '' no bakomai ke da su mufee ku tafi zan neme ku ko wacce ta turo account number din'ta..,
da sauri ta riƙe mai hannu tamkar za ta shiga jikin sa tana mai wani irin kallo tace '' amma didn't you say we would spend the night here today? How many of us are even here?,,
matsar da ita yayi daga jikin sa yace '' Please hany kuyi abin da nace kafin raina ya ɓaci idan kuka kika ce ba in da ki tafi wallahi sai na farfasa miki jiki da duka ba ku ga abin da take shirin faruwa ba oh da ba mahaifiyar ki bace shine ba abin da ya dame ki to duk iskancina ina son mahaifiyata bana so na rasa ta..,
bata ce komai ba ta juya ta bar gurin samin su mufee tayi suna zaune sun yi ɗare ɗare akan gadon sa suna busa shisha tace '' maman My man ta bashi umarni ya fitar damu daga cikin gidan nan ku taso mu tafi yace ko wacce ta turo mai account number din'ta...,
ransu be so ba suka tashi suka bar gidan bama suyi mai sallama ba..

*OSOKORO........*
*STUDY ROOM....*

tunda ya shiga yake aikin office da ya tarar mai kwana biyu da yake yayi busy ba ya ƙasar sai yanzu ya samu yake rage wa kan'sa ne ya dauki chaji gaba ki ɗaya wayoyinsa ya kashe su, yana bukatar hutu da kaɗaici domin yayi aikin sa ba kuskure..
ji yayi an yi knocking kofar sa yasan wace dafa goshin sa yayi yace '' abu ɗe yake..,
jin haka da sauri ta murɗa handle din ta shigo zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun da suke study room din tace '' ummi ce ta bugo duk layin ka a kashe yake ce maka..,
ajiyar zuciya ya sauke shi ya amshi wayar tare da karawa a kunne yace '' Assalamu alaiki ummi barka da yamma...,
JAWAD riƙe gaisuwar ka bana so bana so wallahi ai baka mai dani mutum ba wayancan Mutanen da na raba ka dasu sune mutane har ka iya zuwa yola baka zo gurina ba ina matsayin mahaifiyar ka , ka kyauta dole suyi min abin da suka ga dama su nuna min ban isa da kai ba sai su, suka isa dakai ban ce maka ba , na rabaka da duk ahalin ɗan buzu musamman ma Hajiya farida bani da wata wacce na tsana sama da ita dan haka kai gaggawar mai da mata da yar ta , wallahi wallahi wallahi JAWAD idan ka sake kayi abin da na ke zargi to bani ba kai ban da iskanci tun wuri ka rabu da ita mana to wallahi alkali mudassir ya taro abin da yafi karfin sa domin duk abin da yake faruwa ina sane wato za su fage da guzuma su harbi karsana ko to sunci karya bakai ba jinin Hajiya farida da Alhaji Sharif..,
kifa kansa yayi akan table rasa ina zai saka kan'sa yayi anya kuwa Mahaifiyarsa, tana tsoron Ubangijin'ta me wannan baiwar Allah tayi mata tun da ya taso be san dadin uwa ba , watan sa takwas ita da mahaifinsa suka rubu dan haka bata tafi dashi ba ta bar shi ba ruwanta ya mutu ko yayi rai sai bayan ya kammala digree dinsa na farko yana shirin tafiya egypt ƙaro karatu ta bayyana be rayu da ita ba , tun daga bayannara ta zuwa yanzu kullum cikin saka shi take a damuwa da farko da ta bayyana yaji dadi be taɓa zaton ba hajiya ce mahaifiyar sa ba suma haka su NAJLAH sai a lokacin suka san me yake faruwa ajiyar zuciya ya sauke yace '' ummi insha'Allahu zan kiyaye duk abin da kika shinfiɗa min wallahi bawai haka kurum naje yola ba a'a na can na sauka gobe nake so na zo mu gaisa..,
kashe wayar tayi saboda ai ta riga da ta isar da sakon'ta miƙa wa jawaher yayi,
amsa tayi tace '' amma sweet lafiya ko ba wani abu ne ya faru ba..?,
bece mata komai ba ya nuna mata hanyar fita sum sum ta fice tana danne dariyar ta ,
ci gaba yayi da aikin sa bayan ya gama ya tashi ya fito ba kowa a parlour kai tsaye bedroom din sa ya nufa tana kwance tana waya tana ganin sa ta katsai wayar tace '' badai la gama ba ? Amma kuwa idan haka ne kayi saurin gamawa...,
zama yayi bakin gado yace '' eh na gama kije kice NAJLAH ta haɗa min coffee..,
tashi tayi tana cewa to an gama oga kiss tayi mai a kumatu tace Allah ya bar min kai ya makantar da idon yan mata akan ka...,
dan murmushi yayi mata yace '' amin...,
da sauri ta dawo ta zauna riƙe hannun sa tayi tace '' idan har hasashena ya faɗa min gaskiya kamar akwai abin da yake damun ka amma kaki sanar min idan ma tafiyar ce baka so nayi sai na fasa shikkenan magana ta ƙare amma wannan haɗa ran ban saba da shi ba kullum na fiso mu ɗore cikin so da kaunar juna da fahimtar juna shekara biyu da auren mu bamu taɓa samin matsala ba kar yanzu akan tafiyar nan mu samu beb idan haka ne ni wallahi na hakura ma da nayi tunani ko wani abu ummi ta faɗa maka da na kuma ƙara wani tunanin sa naga ita uwa ce me son farin cikin ɗan ta ba za ta taɓa faɗa maka abin da zai saka lokaci kali lan ba ka shiga cikin damuwa , ina kyautata zaton nice sanadin komai,
saukowa tayi ƙasa ta damƙe hannuwansa idanuwan'ta ya taru da kwalla fal sakin hannuwansa tayi ta haɗe hannuwanta biyu alamar ban hakuri ta ci gaba da cewa.
Dan Allah ka yafe min mijina bana so ka kwana kana fushi da ni bana so na zama sillar bakin cikin ka , ka dawo daga tafiya kamata yayi na faran ta maka be kama ta na bakan ta maka ba...
Kwantar da kan'ta tayi yasha kan'ta yayi yayin da wani sanyi yake ratsa zuciyar'sa hakika annabi yayi gaskiya da yace idan namiji ya dace da mace ta gari to kamar ya samu rabin addini ne yana kaunar jawaher yana son ta fiye da son da yake wa kan'sa baya iya kallon ko wacce mace a matsayin mace , Hakika jawaher rabin jikin'sa ce.. cikin daddaɗan sauti yace '' wallahi baki yi min komai ba idan ma kwai na yafe miki sweet stress ne yayi min yawa ina bukatar hutu amma ni baki min komai ba jeki, ki faɗa mata , ta haɗa min kafin na fito daga wanka..
Hmmm ku biyoni dan jin wanne darasi wannan labarin ya kunsa
# KURUWAN CIKIN GIDA
EPISODE 3
Ɗago idanuwan'ta tayi cike tab da hawaye share mata yayi yace '' bana so na ganki cikin damuwa..,
Murmushi tayi ta tashi, ta karasa share hawayen ta , fita kai tsaye bedroom din NAJLAH ta shiga turawa tayi ba tare da tayi sallama ba , tana kwance wayar ta na hannun ta taɓe baki tayi ta kalle tace '' sweet yace ki haɗa mai coffee..,
ajiye wayar hannun ta , tayi bata ce mata komai ba ta miƙe ganin haka ita mata fita, tana shiga tarar dashi tayi ya shiga wanka zama tayi tana charting da wayar ta fitowa yayi yana tsane jikin sa batare da ya kalli inda take ba yace '' kin faɗa mata..?,
ajiye wayar ta , tayi tace '' na faɗa mata amma bata ce min komai ba bama ta kalli inda nake ba balle nasan taji me na faɗa..,
ajiye towel din hannun sa yayi ya fita a hankali yake saukowa cikin nutsuwa kamar ba sauri yake ba yana sauka kai tsaye bedroom din NAJLAH ya nufa murɗa handle din kofar yayi da sauri ta dago tare da ja da baya tun da take dashi a rayuwar'ta bata , taɓa ganin sa acikin makamancin wannan yanayi ba ko exercise zai yi da dogon wando yake tafiya balle wannan daga shi sai towel a ɗaure a kugu lallai auren da yaya yayi ya mai dashi wani iri,
ƙasa tayi da kan'ta tace '' yanzu zan kawo maka..,
okay ita da kikai mata shiru kenan raina ta kika yi..?,
ya jefo mata wannan tambayar bata , taɓa tunanin jin wata magana makamancin haka abakin sa ba. turi ƙaramin bakin ta , tayi tace '' nace mata to..,
karya kenan take miki..?
da sauri ta ɗago kwallah har ta fara taruwa a idanuwanta ja da baya tayi tana sauke ajiyar zuciya ganin ya matso kusa da ita tamkar zai shige jikin ta da sauri ta, tashi tace '' bara naje na duba kar ya gaji da tafasa..,
ratsawa tayi zata wuce riƙe hannunta yayi da sauri ta juyo anya kuwa yaya Jawad lafiyar sa qalau ko kallon ta ya ke kamar jawaher ta shiga uku da sauri ta saka ɗaya hannun nata , zata cire hannunta da ya riƙe wani irin shock yaji ajikin sa da sauri ya cika mata hannu kasa koda motsi yayi dakyar ya iya ɗaga kafar sa ina yaga abin ba zai yiwu ba hannun sa ya saka ya kashe switch din fitilar dakin a gigice ta ɗago da kan'ta sai dai kafin ta gama tantance wanne yanayi take ciki ya hanka ɗata kan gadon ta yunkurawa tayi zata fita aguje amma ina be bata damar haka ba , domin ya danne ta kuka ta sakar mai , sosai ta shiga kici niyar kwace kanta amma ina ya ƙi bata damar haka.
ji tayi an buga mata pillowcase agigice ta , tashi tana zabga uban gumi ganin shine gaban tane ya faɗi tunowa da tayi da abin da ta gani a cikin mafarkin ta , da sauri ta ja baya gaban ta na faɗuwa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa yace '' NAJLAH sannun ki na saka ki aiki shine , kika zo kika kwanta har kikai bacci daman ai tace baki bata amsa ba ..,
cikin sanyin murya tace '' nace mata to wallahi ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba na ɗora akan gas Allah ya saka me kone ba bara na tafi na duba kafin yace wani abu ta fita cikin sauri,
ko ina na jikin ta rawa yake daman ya lafiyar kura balle tai hauka, tana tafiya a hankali jikin ta na motsawa balle yanzu da ta fita da sauri zama yayi ya ɗora ƙafafuwan'sa ɗaya kan ɗaya ciro wayar sa yayi daga aljihun kayan baccin da ya saka farare tas dasu fara operating din ta yayi har ta kawo ta ajiye mai be ɗago ba.
cikin daddaɗar murya me dadin sauraro tace '' yaya gashi nan na kawo maka a ina zan ajiye maka..?,
akaina zaki ajiye..
da sauri ta ɗago ganin ita yake kallo sai tai sauri ta ajiye tare da matsawa daga gurin zama tayi agefe tana wasa da gefen mayafin'ta so take yi ya dauki kayan sa ya fita.
wayar tace tayi ringing da sauri ya kalli gefen sa BLOOD LINE sunan da yaga tayi saving number din dashi ajiye coffee ɗin hannunsa yayi ya dauki wayar tata ya soma juyawa nan ɗanan ɓacin rai ya bayyana afuskar sa kallon ta yayi yace '' wanne wannan...?,
bakin ta na rawa tace '' yaya muneef ne..,
ɗaga kan'sa yayi ya kalli agogo ƙarfe goma saura minti uku kallon ta yayi yace '' lokacin nan ya kira ki daman kun saba waya kenan..? kenan ba karatu yake ba tun har yakai lokacin nan be kwanta ba be kuma ya zauna yana karatu ba ya kira ki..?,
NAJLAH bata da wuyar kuka dan haka a yanzu hawaye ne suka soma sintiri a kan fuskar'ta bata son wani issues ya haɗa ta da yaya Jawad saboda ya dinga tambaya ya saka mutum a kwana ko dan aikin sane amatsayin sa na alkali ya dinga bin diddigi sai yaga ya aka haihu a ragaya shi ya saka kaf Yaran Ɗan buzu suke tsoran sa har da wasu manyan ma bakin ta na rawa tace '' a'a yau ne kawai ya kira ni da wannan lokaci...,
au daman kun saba waya son ki yake da sauri ya ɗago tace '' ya muneef ne fa..?,
miƙo mata wayar yayi yace '' buɗe min..,
karba tayi ta buɗe ƙara cewa yayi yace '' cire password gaba ki ɗaya..,
jikin'ta na rawa ta amsa ta cire mai daukan coffee din yayi ya fita, tamkar an tsoma kaza cikin ruwan zafi haka jikin'ta yayi banda uban gumi da yake yanko mata.
ba abin da take tunani sama da video's da tayi wani zubin da towel, wani balle ita tana son saka English wears duk da idan ta saka, sai ta saka hijabi amma wajibi ne tayi video ko photo wani zubin har da rawa, daman wannan ranar aunty hafsa take ji mata , tace duk randa Jawad ya karbi wayar ki , sai ya hanaki riƙe waya cewa zai yi tiktok kike yi be san cewa iya kan wayar yake ba.
Shikkenan tayi mata baki yau gashi ya kamata a inda ba annu balle ta tare mata tasan gunduwa gunduwa zai yi da ita ya Jawad ba dai zafi ba.
Bayan fitar sa kai tsaye baranda ya nufa tura glass door yayi ya shiga wani guri da flower's abin sha'awa ga wasu fararen kujeru da table a tsakiyar su bangaren hannunsa na dana wani lilone zama yayi akan lilon tare da ajiye tray din hannun sa akan center table daukan magazine yayi ya soma dubuwa ya dan daɗe,
yana dubuwa sannan ya ajiye ɗaukan wayar Najlah kai tsaye gallery ya shiga da sauri ya cire glasses ɗin sa gani yake ba dai-dai ya gani ba a hankali ya furta NAJLAH da sauri ya shiga hannun sa har rawa yake buɗe video yayi daga ita sai wata riga me karamin hannu ta lafe ajikin ta , da wando three-quarter skiing tight tana rawa ta , tana bin wata waka..
fita yayi ya dauki wayar sa ya danna wata number ya kara akunne ba a dade ba aka dauki wayar sallama yayi.
Tace '' wa'alaikis'salam JAWAD ya mutuniyata kardai kuka tai maka sai ta dawo kasan Najlah ba dai rashin yadda ba..,
cije lips din'sa yayi na ƙasa yace '' aunty hafsa kinsan NAJLAH tana tiktok naga kun fi good time da ita..,
dariya tayi tace '' a'a bawai tiktok take ba kawai tana yin sa ne prevent kasan Najlah akwai son English wears amma bata tiktok..,
hmmmm kareta kike yi nagani a wayar ta.
murmushi tayi tace '' a'a wallahi ko dai abin ne ya motsa nidai ina ta zuba ido naga big result..,
kashe wayar sa yayi bece mata komai ba ci gaba yayi da binciken wayar ta be ga wani abu ba , banda dai wannan video ajiye ta yayi ya ci gaba da shan coffee ɗin'sa sai karfe sha ɗaya ya tashi dauke kayan yayi ya kai kitchen.
bayan ya ajiye ya fito kai tsaye dakin ta ya nufa murɗa handle yayi ya shiga tana zaune a yadda ya barta tana jin shigowar sa da sauri ta , tashi jikin ta na gumi taja baya miƙa mata yayi ƙin amsa tayi domin bata san ko yayi haka ne domin ya kafa mata tarko ɗaka mata tsawa yayi yace '' ba Magana nake miki ba..,
da sauri tace '' dan Allah kayi hakuri..,
haɗe rai yayi be ce mata komai ba ya ƙara miƙo mata jikin ta na rawa tace '' to ka ajiye akan bedside drawer zan dauka..,
limshashshun idanuwan'sa ya buɗe masi kama da me jin bacci ya kalle ta mai da wayar aljihunsa yayi yace '' good lallai ma yarinyar nan kin raina ni ko..?,
da sauri ta girgiza kan'ta tace '' a'a kai hakuri..,
okay zo ki karɓa kafin na kifa miki mari...
jikin ta na rawa ta karɓa sai dai hannun ta ya riƙe be bata wayar ba , kuka ta rushe dashi tace '' wayyo Allah hannuna ya Jawad zai karye..,
murmushin mugunta yayi ya cika ta tare da miƙa mata wayar ta kin amsa tayi ta kifa kan'ta a gado tana kuka ita , ta dade da sanin cewa ya Jawad zuwa gidan sa da tayi hmmm akwai matsala Allah ne kaɗai yasan irin kalubalen da zata fuskanta, ta nunawa su Hajiya amma sun kasa fahimta.
ajiye wayar yayi akan gado ya fita ta dade a haka sannan ta kashe fitilar dakin, ta ta kwanta..,
yana fita kai tsaye bedroom ɗin ya nufa jawaher tana kwance tana charting tana ganin sa ta ajiye wayar tace '' sweet ka dade ko bata ɗora bane..?,
zama yayi yace '' na zauna a abaranda ne nasha iska..,
hannunsa ta riko ta kai bakin ta za tai mai kiss da sauri ta ɗago jin kamshin turaren NAJLAH a jikin sa bakin ta na rawa tace '' sweet kamshin me nake ji..?,
da sauri ya kalle ta yace '' ban fahimta..,
kwallace ta , taru a idanuwanta tace '' ya kake abu kamar baka gane me nake nufi ba , JAWAD kamshin turaren NAJLAH naji a hannun'ka me ya kai hannun ka har ta shafi turaren NAJLAH wallahi nayi trusting ɗin ka amma yanzu kana neman jefa ni cikin zargi kar mu fara rayuwar zargi a cikin gidan nan...,
what jawaher kanki ɗaya kuwa kike faɗar haka..?,
ɗam tayi ta buga kan'ta tabbas bata cikin nutsuwar ta , amma abin da taji bashi da nasaba da abin da , tasha, batayi tunanin zai shigi yanzu ba , tasha totalling syrup zama tayi a ƙasa kan'ta na juyawa tashi tayi tana tan gaɗi da sauri ya riko ta ya taɓa kan'ta yace '' sweet yanzu daga wannan magana sai ki shiga wannan hali..?,
limshe idanuwan'ta tayi bacci ba fusgarta ganin haka sai ya lallaɓa ta tayi bacci
dai-dai ta mata kwanciyar ta , yayi ya tashi ya dauro alwala zama yayi ya fara karatun Alkur'ani mai girma bayan ya idar misalin ƙarfe 1;20 yayi Sallah sannan ya kwanta
************
1:30
CLUB
Motocine jere tamkar ba dare bane gurin wasu ma yanzu suke zuwa wata motace tayi parking yayi dan ta toshe wa masu fita hanya saboda a ƙan hanya ta ajiye motar fitowa tayi tamkar bayar musulma ba wani irin mini skirt ne a jikin ta wanda ake wa kira dashi gwara babu kanta yaci kalbar attachment sai wura hanci take fuskar nan tamkar zata gasar sarauniyar kyau duk uban adon nan da taci kallo ɗaya zakai mata , kasan cewa ranta a ɓace yake saboda idon ta yayi ja taku take ɗanɗai shiga cikin gurin tayi tamkar zai tsaya saboda ƙiɗa ratsawa tayi ta shiga ko wa yana sabgar gaban sa ba wanda ya lura da ita, itama kai tsaye table ɗin da ake sai da giya ta nufa zama tayi ta dauki guɗa, ɗaya ta kai bakin ta da sauri mutumin yace '' a'a gaskiya yau billahilazi kika shamin baki biya ba kika taɗa hankalin karya to yasin sai na yi miki rashin mutunci..,
ajiyewa tayi sai ta tashi saboda abin da take nema ta samu gyara zaman p-cap ɗinta tayi ta dauki kwalbar ta bar gurin binta ya dinga yi da sauri ta hau sama a guje ya biya har sama dakin da taga ya shiga da wasu yan mata nan ta shiga a kuje ta buga kofar dakin duk wannan abin da yake faruwa bama su san ana yi ba , saboda sheɗan ya buga musu gangarsa ɗaukan kwalbar tayi ta buga akan wata marashiyar budurwa ƙara ta saki da ta dinga amsa kowa a club ɗin..,
da sauri matashin nan ya riƙo ta yana cewa nailah anya kuwa lafiyar ki kalau kin ga abin da kikai mata fa..?
ɗurƙusawa tayi tace '' DAZ aza ton ka ni irin banzayen yan kwalta din nan ne da za'a ɗinga cik su daga ƙarshe a jefar da kwallon mangaro to kayi kuskure wallahi wallahi wallahi wannan abin da nayi maka kaɗan ne daban caccaka mata wuƙa ba a ni zaka yaudara ka baro ni da gidan iyayena ka kawo ni bariki kake tunanin barina kuma to kayi kuskure DAZ kayi Kuskure wallahi..,
wanda ya biyo ta ya tsaya yana kallon ikon Allah gaskiya nailah yar bala'ice ga jini sai mulala yake ko a jikin ta da sauri yace '' wallahi bara na kirawo yan sanda wannan ta'asar da ki kayi ba'a san a inda zata tsaya ba..,
dalla can rufe min baki ka bari masu abin faɗa su faɗi kudin ka kake ji ko ..?
shiru yayi jikin sa na rawa kar shima ta lumamai kwalba domin ya lura bata da imani lokacin da aka raba shi tayi bacci Dala ta ciro a bayan wayar, ta ta cilla mai tace '' matsiyaci dauki nafi karfin naci maka abu wallahi...,
Wannan matashin tallafo kan wacce aka fasa yayi ya ɗauke ta suka fita zama dirshen tayi zuciyar'ta na tsananin bugu ya tafi ya barta bata san yadda za tayi ba shima dayan tafiya yayi ya barta da sakakken baki.
dakyar ta , tashi ta fara tafiya ranta duk a bace fita tayi daga gurin gaba ki ɗaya samu tayi mutane na ta jiranta saboda tayi parking da dai-dai ba..
Copy is not allowed 🚫

EPISODE 4

Tana zuwa ba wanda tayiwa magana ta shiga motar ta tayi baya , sannan ta fita da gudu Allah ya rufa asiri Bara buge wani ba tamkar zata tashi sama haka take gudu a daidai wani gida tayi parking din motar ta , fitowa tayi ta soma buga gate din gidan ma mallakiyar gidan ta buɗe kofar gate din cikin mamaki tace '' Nailah kice cikin daren nan...,
kallon ta tayi tare da tabe bakin ta tace '' hmmm wallahi deeyana raina a ɓace yake..,
okay shigowa daga club kike ne..?
shugowa tayi ta jingina da bango tace '' daga can nake budurwar DAZ na fasawa kai , wallahi deeyana namiji ba dan goyo bane dan kunama ne ki kalli irin halarcin da nayiwa DAZ amma har ya iya saka min da wannan abin..,
dariya tayi ta riko hannunta suka shiga ciki shisha ta ɗauka ta fara sha bata cewa nailah komai ba sai da ta sha kashi isarta tace '' barki nayi ki wuce nailah gaki mace har mace amma kin tsaya wani banza irin DAZ yana ɓata miki rai ki shiga harkar sahun manyan mata kin ganni nan ba ruwana da tension ɗa namiji mijina tamkar photo yake a gurina dan dai bana son idon mutane ya komo kaina da tuni na dade da yanka mai ticket ya kama gaban sa , to ta wani fannin aure suttura ne kuma mutuncin ɗiya mace ne amma banda haka da tuni labari yasha bamban Na'ilah mace tafi namiji iya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment