Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasani bana gayyar dangin mayu acikin zuri'ata."

kan zahra mummy tashafa dacewa "kuje hanan kujirani amota inazuwa,zahra saida tasake ballawa gwaggo rabi harara hada yar kwafarta da girgiza kai sannan tayi gaba.duk abinda takeyi akan idanun mummy sai dai tasan wata jikakkiyace zata wakana tsakanin zahra da gwaggo rabi tabbas!

har bakin mota zahra taraka su mummy tana daga masu hannu saida taga bacewar motarsu tanufi wajen megadi dake zaune yana sauraren radio yana hangota yakashe radion yana dariya da tsokanarta "amarya megida barka da fitowa,zhra dake kyalkyala dariya tace"kai baba me gadinnan bafa nice amaryar yaaa ishaq ba yaya aneesa ce."

baba megdi yace "waya gayamaki aikece amarya kuma uwargida awajen megida."
tasake kyalkyalewa da dariya tace "tokace kwarankwatsa"
shima dariyar yakeyi yace a'aha aibama saina rantseba."

sundade suna fira zahra harta fara hamma sannan baba megdi yace taje ta kwanta,
bata musaba tanufi cikin gida tana yan wake-wakenta.

cik tatsaya hango inna delu tana gogar kubewa,harzata wuce ta tuna da gwaggo rabi,ahankali ta lababa sotake yau tayi maganin fitinar gwaggon.....







*wash typing is not easy ooo*☺





*mum Nass nd meenat*😍

*MIJIN 'KWAILA🤦🏽‍♀*








*Chapter 36*









*Written by maman meenat*







*Edited by Aisha Abdullahi T.fulani*






*Mum meenat fans nd mijin kwaila fans dama duk fans na mum meenat wannan chapter nakune,yanda kukesona Allah yasoku fiye dahakan yanda kuke garkuwa ga mum meenat Allah yazama garkuwa agareku kunada yawan gaskefaaaa inama inzayyanoku gaba daya,kai namasan koban fadaba kunsan kanku much luv*😍






Sando taci gaba dayi tana wurga idanuwanan ko ina na bangaren gidan,saida ta tabbatar bakowa ta'isa inda inna delu take tana dariyarta me sauti tace"inna mezaki dafamana,"

inna delu dake juya kubewa tabata amsa"tuwone zanma gwaggo kinsan tafison tayi kalaci da tuwo."


wata dariya ta tu'ke zahra har saida tasaka tafin hannunta takulle bakinta,saikuma ta gyara fuska sosai tace,nima ianason inkoyi girki irinnaki inna"

inna delu tafadada murmushinta tana cewa"Aiko gyara kidage ai girki shine mace."


hakan kuwa ce takasance zahra ta tile iya karfinta tana zabga aiki,sai daifa tafakaici idanun inna delu tazabga masifaffaen gishiri hakanan ruwan da suka wanke kubewar daukarshi tayi ta fakaici idanun inna delu tasheqashi akasan hanyar shigowa kitchen din.

ta gyada kai tana hararar kofa aranta ta ayyana,tasan jarabar gwaggo rabi bazai barta tazauna jiran agama tuwon sannan akaimata ba.zata takone tazo dakanta tace zata karba.


Tunaninta yakatsene lokacin da hancinta yajiyo mata lallusan kamshin turaren yaaa ishaq dake tahowa,hannunshi sakale cikinna anee saika rantse sudin wasu raurarine saboda yanda suke sheki dazuba kamshi.


zahra data saki baki harma da hanci tana kallonsu saitaji sun mugun burgeta,sai dai aranta tana ayyana yaa aneesa mara wayo data yarda yaaa ishaq yakama hannunta.


dayake tasan aika-aikan datayi akofar kitchen din dasauri ta tsallaka ta'isa wajensu tana washema anee baki.

Anee dake zabga mata harara dakyar ta'iya amsa gaisuwae da zahran kemata shima naganin idanun ishaq dinne.

zahra jitayi jikinta yayi sanyi sosai,kallo daya zakamata ka fahimci hakan.

juyawa tayi danufin komawa kicin din ishaq yarike hannunta tabaya,tajuyo da fuskarta ahankali idanunta sunnuna alamar damuwa saikuma tashagwabe fuska dacewa"nibanayi dakai......"

takasa karasa maganar hango gilmowar gwaggo rabi dake tafe bakinta mai-maita ina delun takene?

Tahowa take da mugun zafinnama danufin takarema inna delu tijara,

zahra tuni dariya takamata amma saita dake.



*Manage😍😍*

[10:06AM, 4/24/2018] maman meenat😍: *MIJIN 'KWAILA*🤦🏾‍♀






*36 to end*




*written innar Amunatu*








*Sadaukarwa ga dukkan fans nawa a ko'ina suke*😍






*Gwaggo rabi datataho takwal-takwal tana zuba ruwan tijara wani azzalumin santsine yakwasheta jikake yuuuu....tif.*

wata razananniyar kara tasaki wadda tadauki hankalin iahirin jama'ar gidan ciki harda masu gadi damasu bama flowers ruwa.
afin kace kwabo mutane sun zagaye gwagwo rabi dake zube akasa bata motsi ko alama.

sai alokacin hankalin zahra yatashi musamman ganin ishaq ya sunkuci gwaggo kace baby ce yasunkuta.

Aguje yafice aneesa tarufa masa baya.bema saurari driver ba yashimfideta kujerar baya anee tashiga yafisgi motar da matsanancin guda yacilla bisa kolta,gudu sosai yake shekawa mintuna ashirin suka sadashi da asibitin mummyn tasu wato *KHADO'S HOSPITAL*
bai tsaya sauraren anee ba don gaba daya arikice yake yasunkuci gwggo rabi kace jaririya yadauka anee ta rufa masa baya suka nufi emergency da'ita.
Nurses na hango ishaq sukayo kanshi da gadon tura mara lfy aka shimfide gwaggon akai suka.shige da ita ciki.
banda kai kawo da shafar sumar kai lokaci xuwa lokaci babu abinda ishaq yakeyi saikuma addu'a data kasa katsewa daga bakinshi.

suna a wannan halin mummy tazo asukwane tawucesu jikinta dakayan tiyata saikuma likitoci akalla guda biyu tare da nurses uku suka rufa mata baya, tun anan jinin jikin ishaq yatsinke zufa mai zafi tasoma kwaranyowa daga cikin kanshi tana diga a kan fatar jikinshi zazzabi yakejin yna neman kayar dashi.
shi kanshi besan yanama tsohuwa gwaggo irin wannan sonba sai yanzu.

abangaren oganniya zahra kuwa data kyalla ido taga halin da gwggo tashiga saita rude tanufi daki aguje tsalle daya tayi tadare bisa saitin akwatinanta tasoma watsosu waje duk a kokarinta nason nemo hijabin dazata saka tabaza dagudu gidan umma tun kafin su gwaggo rabi sudawo suyankata danyarta.


Awanni uku cir suka kwashe akan gwaggo rabi wanda zuwa lokacin asibitin tagama dinkewa da jama'a ciki kuwa harda su yaya Aliyu wanda dirarshi kenan akasar shida matarshi Anty faheesa saikuma broda dinta Aliyu AA wanda shine mutumin daya kade zahra acan ranar aurenta wanda yazuwa yanzu yagama macewa akan soyayyarta duk da baimasan ina zai sameta ba amma koma menene yasan tanada relation da khados family.
babban lauyane me zaman kanshi akasar america dukansu sunzo hutun karshen shekarane anan gida nijeria.

Bayan wani dan lokaci dr.rukayya tafito tana sharar zufa sai dai kallo guda zakama kammalalliyar fuskarta kagane babu alamun nasara a aikin dasuka gudanar.

Daddy da baba delu kanwar gwaggo suka nufeta suna tambayar lafiya yamai jikin? hawayen dataketa kokarin dannewa suka ziraro tacikin tabarau din dake dofane akwayar idanunta.

Kasa jurewa tayi tafada jikin dady tasaka kuka mai fitar da sauti, ahankali tace" we lose her" Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.shine kalmar datake fitowa daga bakin kowanne mahaluki dayake harabar wajen.

kuka sosai jama'ar keyi musamman ishaq dayake ganin mutuwar kamar almara.anee data d'aga murya sosai tana kuka tare da sambatu tna cewa"shikenan zahra kinkashe gwaggo meta aikata agareki dazafi haka meta tsaremaki zahra why?

kuka yafi karfinta tafada jikin ishaq duk jikinta yana tsuma kamar mazari.

kowa awajen shanye hawayenshi yayi suka soma tambayar anee dalilinta na laqama zahra kisan gwaggo.anee dake sharar hawaye tace"lokacin danaxo daukarma ishaq plate akicin zanzuba mashi fruit naga zahra da idanuwana tana zuba ruwan yankakkiyar kubewa me yauki bisa tiles tana dariya dacewa yau zatayi maganin jarabar gwaggo rabi.

kuma alokacin damukazo nida ishaq munyi kokarin taka wajen amma saitayi saurin rike hannun ishaq tahaashi karasawa gurin.

sannan alokacin da gwaggo tazo wajen zahra dariya tasoma kasa kasa tanamata gwalo."
[10:01AM, 4/24/2018] maman meenat😍: ishaq gyada kai yakeyi cike da gamsuwa saiyake tunano komai ahakan.
yakuma tuna wacece zahra,wani mayatar tsanarta taji ta mamaye mashi ranshi jikinshi yasoma tsuma sai alokacin hawayen takaici da kaicon sanin zahra suka ziraro daga kwayar idanunshi

mutannen dake wajen kuwa babu wanda beyi tofin Allah tsine akan zahra ba sai A'A daya tsurama anee idanuwa tunda tafara maganar yana karamin murmushi kawai.
dr.rukayya dake hawaye tace"nayi kaicon saninki zahra nabaki amana kinci.nayarda dake.kin zalunceni na daukeki diya kinyi butulci kije Allah ya isarmana daga kaidi dakuma akircinki.

daddy kiran police yayi yace suzo yanzu anyi kisan kai.

kafin kace miye motarsu tacika asibitin da jiniya, nan sukaji case din cewa sumkayi atafi da gawar gwaggon. bamusu aka dauko gawar aka saka amota duka mutanen suka rufa masu aya.

zahra dake makale jikin tagar windo tana leken tsakar gida aitana hango motar ishaq tadad tsurewa.jama'ar duk suka fito anan dpo yabada iznin cafko zahra wanda fitsari harda zawo suka kufcemata tasakesu awando.

burari take tana cewa wlh ya ishaq bansakaba wlh banice ba wayyo ummana da babana ayyo ummilolo kizo kitemakeni.


wawan marin da ishaq ya dauketa dashine yasaka bakinnata fashewa take jini yayi wata irin tsartuwa yabugi saitin zuciyar AA dake tsaye yagoya hannuwa abaya idanunshi sunkada jajur soyayyar zahra da tausayinta yasakashi kasa katabus.

zahra da take idonta guda ya kunbura yasoma tsiyayar da wani yellon ruwa da rarrafe tarike zanin mummy sai dai takasa furta koda kalma daya illa zubarda hawayen datakeyi kawai.

itama mummyn angijeta tayi taja.baya da sauri tana matsar hawaye'ishqq da jikinshi ke kyarma nunata yayi da yatsa yace"kije ni ishaq saifullahi na sakeki zahra Adam saki biyu"bana kuma fatan Allah yasake hada fuskata dataki har abada."

zahra sake rushewa tayi dakuka tanacewa"wlh banibace banice na kashe gwaggo ba wayyo ummana."

marin da Daddy yazuba matane yasata zubewa jikin AA dake tsaye yasaka duka hannayenshi ya taryeta ahankali yasoma nade hawayen nata da babban yatsanshi dan Ale yana girgiza mata kai alamar tayi shiru tadena kuka.

cikin kuka zahra ke fadin"yaya don Allah kace dasu banice na kashe gwaggo ba banice ba kukaini wajen ummana banasonku dukanku bana sonku."

Anee dake harararta tace todama wake gayyar bakar ja'iba agidanshi muma bama kaunarki kijecan akasheki yanda kika kashe rai tsinanniya baqa me baqar aniya almura azzaluma.kllonta kawai zahara takeyi ahaka aka tisa keyarta zuwa police station.

Duk yanda su Abban zahra sukaso susamu damar ganin zahra abun yaci tura don dai police sun basu tabbacin insunga zahra tafito daga cell tofa kotu zasu kaita.

umma dasauran yan uwan zahra sunyi kuka da kaico akan halin zahra sai dai abunamasu karamin karfi bayanda suma iya.

satin zahra guda acell aka kaita kotu alokacin duk me imanin dayaga zahra saiya tausayamata.tarame matukar rama tasake yin duhu kanta duk ya aske saboda bala.i sai idanuwa kamar na aljana.

Akotu tana ganin umma da Abba anty lubnah dasu anty murja saita fashe dakuka'kuka sosai take tambayar duniya idan Alkali yayi amsar zahra itace e...

kekika kashe gwaggo ...tace..ee.kekika sakamata rywan kubewa..ee.e
[10:31AM, 4/24/2018] maman meenat😍: Ganin tagama amsa laifinta yasaka alkali yanke mata hukuncin daurin shekaru tamanin agidan yari kukoma su daukaka kara awata kotun.

saboda shekarunta basukai na ayankemata hukuncin kisa ba.

babu wanda bai tausayama zahra a kotunnan ba'tanaji tana gani zata qare rayuwarta a magarkama.

su umma duka rungumeta sukayi suna kuka sosai sunamata fatan Alkairi dafatan Allah yashiryi masu hali irinnata dukkan yaran musulmi Allah kashiryamanasu kamaana tarbiyyarsu badan iyawar muba.

Anan dai aka tasa keyar zahra akayi prison da ita,nikuwa nace karshe tika-tika tik!

*Tafaru taqare anwa me dami daya sata.Abunda kashuka.shizaka girba in hairan hairan i.shararran sharran.*

Allah ka'iyama don Alfarmar fiyayyen halitta.

*Ni maman meenat anan na sauke labarin mijin kwaila wanda nasan ba lallai karshen ya kayatar ba.Amma saboda yanayin rayuwa gayanda takasance*.Zunubanmu Allah kamana aikin gafara..


*Me bukatar jin labarin zahra A prison saiya saurareni😆don Allah banda zagi bakar magana dakuma kausasa harshe duka basa cikin tsarin mutanen kirki.*


*millons greatings to my Beautiful fans naboye dana bayyane my enemies and yar gidan mqguzawa duka mum meenat na kaunarku acan kasan ranta.saimun sake haduwa nan kusa ko nesa qila*

*Don Allah wanda nabatamawa suman aikin gafara zaku iya jin tabakina through my whatsApp no.or phone no.08130859084 luv u guy's*😘
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment