Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai Zayyad ya shayar da ita gubar mamaki bata taɓa zaton haka yake ba, jiki a sanyaye ta koma kitchen ta ɗiba breakfast ɗin soyayyen arish da kwai ta fito ta nufi wajen maigadi Zayyad yana tsaye tazo ta wuce, ta miƙa masa yana zabga mata godiya, Safna tace.


Anjima akwai sauran tuwo zan kawo maka, sannan in ka samu almajiri ka yi mini magana shima na saka masa dan yana da yawa kuma kar ya lalace.


To 'yar baba nagode Allah ya saka a mizani.


Ta amsa da amin ta zo ta wuce su lokacin yaran sun fito sun shiga mota ga Anisa tana yi musu bye bye, ta shiga ɗakinta ta rufe da key ta ɗauko sauran abin karin tazo ta zauna, da kyar ta iya cin kaɗan ta mayar da sauran ta koma ɗakinta ta kwanta ta shiga karanta wasiƙar jaki.


A takaice haka Safna ta fita girki Zayyad bai ci abincinta ba, sannan tunda Rashida ta amsa girki in ya leƙota da safe to bata sake ganinsa sai wata safiyar, tayi kuka har ta gode Allah ga ciki ga ciwon kunne da har lokacin yana mintsilinta ga damuwar Zayyad, bata iya cin abinci sai ta tilastawa kanta sai yawan shan ruwa, nan da nan ta rame ta yi wani haske, taƙi faɗawa kowa halin da take ciki face Allah dan shine kaɗai gatanta.


****


Bayan kwana biyar.


Wanda ya kama ta amsa girki ta fita, Rashida ma ta amsa hatta fita itama, Safna ta kuma tq amsa har tayi kwana ɗaya jiya, kuma har lokacin Zayyad bai daina fushi da ita ba kusan mako guda suna abu guda, a ranar ne ta yanke shawarar tunkararsa da maganar dan ta bashi haƙuri su shirya, saboda ita ce ke cutuwa saboda shi yana walwalarsa a sashin Rashida wacce har ta ji sauki Anisa ta tafi gida sai Zaliha ce ta rage tana ɗan tayata aiki. Ranar ta tura masa text akan tana so a kawo mata fulawa zata yi ɗan wake, duk da in ta tura saƙo baya yin reply amma yana aikowa. Can wajen ukun rana ya aiko da fulawa haɗe da kwai da mangyaɗa, nan ta soma haɗa ɗan waken saboda bata ci komai da rana ba shi take jira, kafin La'asar ta gama dan haka ta zuba taci haɗe da kayan miya data yanka da kwai data dafa, taci sosai kuwa dan ta jima bata ci abinci haka ba, ta tsame sauran a matsami akan anjima zata ci in kuma yace zaici duk sai ishesu tunda har lokacin baya cin abincinta, ta samu ta gabatar da sallar La'asar sai ta zauna a adduna tana jan hasbulallahu wa ni'ima wakil ƙafa 450, Ya hannu Ya mannanu ya bidi'assamawati wal ardi ya zaljaluli wal ikram shima ƙafa ɗari, tare dasu salatin annabi dubu da Bisimillahi dubu, haka ta kai kusan ƙarfe biyar tana lazumi daga bisani ta yi addu'a ta miƙe ta fito falo ta kwanta a doguwar kujera ta soma kallon MBC bollywood.


Yauma kamar kullun Zayyad bai shigo sasshinta ba koda ya dawo sai wajen ƙarfe tara da rabi, ya shigo ya sameta a falo tana kallo tana ganinsa ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa, ya amsa ba yabo ba fallasa sai ya wuce ɗakinsa ita kuma ta wuce kitchen dan shirya masa abinci, ta gama haɗa komai a babban tire ta fito dashi falo ta ɗaura a table sai ta wuce zuwa ɗakinsa, koda ta shiga taji saukar ruwa alamar ya fara wanka, sai ta zauna gefen gado tana jiransa amma me? ƙarar saƙon WhatsApp ya cika mata kunne dan datarsa a buɗe yake, kamar ance ta ɗauki wayar taga saƙonni yana shigowa ta sama, abinda idonta ya gani na saƙon Saima sai da taji kamar anbuga mata guduma a kai, wanda yasa aljanunta motsawa saita samu kanta da danna PIN ɗinsa wanda ita bata sansu ba amma aljanunta sun yi amfani da hannunta sun buɗe mata, ta shiga WhatsApp ɗinsa tare da shiga number ɗinta Saima nan taga hirarsu na batsa da yawa, sai ta fito ta shiga duba sauran numbers ɗin, nan taci karo da Zuby itama dai kusan hirar da yake yi da Saima suke yi, sai dai yadda suke roƙonsa da magiyar yazo su haɗu ya bata mamaki, kuma a hirar taga yasha tura musu kuɗi, sosai gumi ya gama rufeta dan hankalinta yayi mugun tashi. A lokacin ne Zayyad ya fito daga bayi ɗaure da towel ga wani ƙarami a hannunsa yana goge kansa, Safna ta ɗago tana kallonsa cike da tuhuma shi kuma wani faɗuwa gabansa yayi ganin wayarsa a hannunta, da sauri ya yarda towel ɗin hannunsa yazo ya kwace wayar yana hucci.


Uban waye yace ki taɓa mini wayata.?


Ya ƙare maganar yana kifa mata mari cike sa borin kunya, Safna ta miƙe jikinta babu inda baya rawa tama kasa magana, ta fashe da matsanancin kuka tare da dafe mararta data ɗaure mata, nan take kuma jini ya ɓalle mata.


Last freepage.


_Labari ne ƙirƙirarre mai taɓa zuciya za kiji tamkar kina kallon tv in kina karanta shi, wataƙila kuga labarin yayi kama da labarinki ko na wata to arashi ne, amma na tabbatar irin haka yana faruwa musamman a cikin rayuwar Bahaushe. So da dama matsalolin da mata suke fuskanta acikin gidan aurensu to mata sune suke jefa su a ciki, mu da kanmu muke cutar da 'yan uwanmu mata bisa son zuciya da son kai. Idan kuka bibiye ni a wannan tafiyar akwai faɗakarwa da yawa wanda zaku ilmantu dashi sosai akan zaman aure, tare da ƙarin wasu abubuwan da zaki amfani gobenki._


Don samun cigaban labarin ku biya ₦400 discount daga nan zuwa ranar Lahadi In Sha Allah duba da mutane sunata niman ragi da rokon in duba halin da kasar ke ciki, normal group update sau biyar a sati Monday to friday. VIP ₦1000 zasu samu update duka 7days tare da yuwuwar samun 2pages amma ba kullun ba.


Pay ₦400 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.


Masu matsalar turawa ta Opay saiku tura ta nan.
0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank
[27/09, 10:10 pm] null: *AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 19.


Ght products me Maida Bora mowa💃🏻💃🏻💃🏻 Mai maida mazaje jarumai uwar gida da Amarya suyi ta alfahari da shi shima na alfahari da su🙈😂


Wai haryanzu kina zaune baki gwada ba? Kaima kana zaune baka gwada ba? mata da Maza nata k'ara martaba da kima adalilin ght products, wai kun tsaya kallo? Shin ko sai gwad'o yayi muku k'afa ne?🤔🤥


Yar uwa da d'an uwa ku garzayo in hada muku kayan gyara iya kudinku iya shagalinku.


Mrsjmoon bata tsauwalawa ku dai ku zo musa labule in gyaraku ciki dawaje kuyi tsaf tsaf kuyi cif cif kuyi zaqwai zaqwai kunsan dai zaki na zuma baya illah😋 hakkun duk wanda bai tab'a amfani da kayan GHT ba anbarshi a baya Maza da Mata kada ku bari a barku a baya dan dan Allahb👏🏻 ku ka sance a kan gaba wurin mallakan naku ba jiran ana baku labari ba😍🏃‍♀️🏃‍♀️ Mai so zai iya tuntubar wannan number 08132166848 a Whatsapp ko kira. Nagode sosai.👏🏻👏🏻 Indiawa suka ce bahut bahut shukhriya🥰🥰


Zayyad a kiɗime ya isa gareta yana niman kamata amma Safna ta saka wani irin ƙarfi ta ture shi wanda yayi baya taga taga zai faɗi sai yayi saurin dafe bango, ita kuma falo ta fito ta duƙa a ƙasa tana wani irin marayan kuka kamar ranta zai fita, tun daga zuciyarta kukan ke ratsowa ya fito saboda haka shine kaɗai zai sa ta samu sauƙin zafin ta data ke ji a ƙirjinta, daga jin wannan kukan ma ba ita kaɗai ke yinsa ba, ga jinin bai daina zuba ba har ya ɓata tiles jajir da shi tsinkakke.




Don samun cigaban labarin ku biya ₦400 discount daga yau zuwa ranar Lahadi In Sha Allah, duba da mutane suna ta niman ragi akan In duba halin da kasar ke ciki. Normal group update sau biyar a sati Monday to friday. VIP ₦1000 zasu samu update duka 7days tare da yuwuwar samun 2pages amma ba kullun ba.


Pay ₦400 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.


Masu matsalar turawa ta Opay saiku tura ta nan.
0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank
[02/10, 9:25 pm] null: https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA








Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??


Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??


Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??


Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.


Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955




*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG
Wattpad @rahmakabir


Page 22.


Suna tsaka da cin abinci taliya da miyar ganye da kifi, suka ji bugun ƙofa da sauri Zayyad ya miƙe yaje ya buɗe sai yaga Ilham da Aslam.


Ilham yaya?


Mun zo ne.


Abinda yarinyar ta faɗa kenan sai Zayyad ya matsa musu suka shiga, nan ko wanne ya kame a kujera ba tare da gaishe da Safna ba, Zayyad ya koma ya zauna yana cewa yaran.


Ku baku iya gaisuwa bane? Kun shigo ba zaku ce mini sannu da zuwa ba balle ku gaishe da antynku.


Ina wuni, ina kwana.


Cewar Ilham da kuma Aslam a lokaci guda, Safna ta amsa ta cigaba da cin abincinta, shima Zayyad bai ƙara magana ba ya cigaba da ci, haka yaran nan suka ƙura musu ido kamar basu taɓa ganin abinci ba, Ilham ta baza kunne tana ta record ɗin hirarsu kamar yadda uwarsu ta saka ta, ga dai tv suna kallo amma hankalinsu baya tv, Zayyad ya miƙe bayan ya gama ci yana cewa zai yi wanka yazo, Safna tace masa to ya wuce ita kuma ta zubawa yaran abinci a plate ɗin da suka gama ci tace su sauko suci, haka suka sauko suka fara ci kamar waɗanda basu ga abinci ba sai ta miƙe ta bi bayan Zayyad, da ido ilham ta rakata. Safna koda ta shiga tuɓe kayan jikinta tayi gabaɗaya ta kutsa toilet ɗin Zayyad, lokacin ya watsa ruwa ya goga sabulu ya kaiga wanke fuska, ta shiga a hankali duk da yaji motsinta sai ya cigaba da wanke fuskar, Safna tazo ta rugumeshi ta baya tana shafa jikinsa da santsin sabulun, wani irin saƙo ne ya sauka a jikin Zayyad ya juyo da ita nan suka fara yiwa juna wasa...


Don samun cigaban labarin ku biya ₦300 final discount, Normal group update sau biyar a sati Monday to friday. VIP ₦1000 zasu samu update duka 7days tare da yuwuwar samun 2pages amma ba kullun ba.


Pay ₦300 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels






Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ ************************** Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment