Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tashi mutane suka shiga dariya har da tsuntsire wa shi kansa alkalin da ya shiga camber fadawa yayi kan kujera yana dariyar mai doya yace lallai wannan dan iskan kauyene bayan komai ya lafa an bar kowa yayi dariyarsa ya gyatsr mai shari a ya sake dawowa yaje yasa akayi tsit aka kira wata shari a sannan sai tasu safuwan lauyan malam nasiru mai suna mustafa dauda sai mai kare safuwan shine ya mike mai suna bala ali aka shigo da safuwan alhaji muazzam rudewa yayi ganin muguwar ramar da dansa yayi bashi ba har sauran mutane da suka san shi sun san yana cikin damuwa mai tsanani mai sharia yace ina safuwan?
.
yace gani yace kotu tana tuhumar ka akan silar mutuwar mallam nasiru da batan yarsa wacce kayiwa fyade kayi mata ciki" yayi shuru mai sharia yace kotu tana sauraron ka yace a gaskiya nasan ni nayiwa rufaida fyade a sakamon yaudararata da abokina sulainman yayi yaje gidansu yace bani da lafiya duk dai yasan maganganun daya gaya mata ta yarda da hakan ta amince akan inta sami lokaci zata neme shi a waya ya dauketa ya kai ta ta dubani muna zaune ta bugo masa waya ta sanar da shi inda zasu hadu ni kuma naji haka ni da mubarshir muka sami lemon kwalba muka sa kwayoyi muka bata shine nayi abinda zanyi da ita ba tare da sanin taba ban sani ba ko a lokacin cikin ya shiga lauyan mallam nasiru ya mike ya roki ai maaa uzuri yayi wa safuwan sasu tambayoyi aka basa lauya mustafa yace mallam safuwan ina ganin zaka fi kowa sani ina ma ba naka bane kai kasan yadda ka same ta? yace a gaskiya a cikakkiyar budurwa na same ta bata taba harka da wani ba mai sharia ya dakatar dasu yayi ya dan rubuce rubucensa yace an gama da wannan yace sai tuhuma ta biyu maibya faru tsakanin ka da mallam nasiru? yace tsakanina da mallam nasiru yazo ya same ni a majalisa mu muna zaune muna hira law mustafa ya sake mikewa yace da kai da wada wa? lauyan safuwan ya mike yace ai wannan tambayar bata cancanci wannan lokaci ba law mustafa yace ai ko dole ne ya lissafo wadanda suke wajen dan dukkanin su muna bukatansu anna law bala ali yace ba lalle ne yasan su gaba daya ba law mustafa yace akan me bazai san suba bayan kullum tare suke law bala yace ina rokon kotu ta duba wannan tambayar bazai yiyu ya iya lissafo suba saboda yana cikin rudani law mustafa yace ba wanda zai manta tunda tare suke shedancinsu da abokin tsiya dana arziki ba'a nemansu mai shari'a ya buga abin hannunsa yace kotu tana san safuwan ya lissafo abokansa dake wajen kuma kotu nasan su bayyana nan da mako biyu safuwan ya fara lissafosu sulainman,auwal,musbahu,nura,ali,da mubarshir habib nurandi,hashim,muhannai,auwal,musa da sunusi nasidi kai harta ni abba sanda ya kirani yace suke wajen.
.
ci gaba da yadda ku kayi da mallam nasiru bayan ya kirawo ni na durkusa zan gaisheshi yace bashi ne ya kawo shi ba daga wajen ubana yake ya sanar da shi abinda na yiwa yarsa amma da yake bashi da mutunci sai ya ci mutuncinsa nace shi yayi maka? ai bashi yayi mata fyaden ba gurina zakazo kuma wallahi har ka yarda ka zagan min uba shi ne ya kai min mariya mare ni na juya zan rama........
safuwan yasa kuka mai karfi sannan yaci gaba da cewa ina kai masa mari ya kauce yaci da baka ya fada kan bishiya kan sa ya fashe muka dauke shi mukayi asibiti da shi kafin mu karasa ya mutu kukan da yake ya sake tsananta ta cikin shashshekar kuka yace wallahi bani na kashe shi ba alkali yace ya isa sai kuma tuhuma ta uku ina rufaida? ya shiga yin kuka mai tsanani marar misaltuwa yace wallahi bani da masaniyar batan ta kuma har ga Allah nima inaa bakin cikin rashin ganinta kuma ina addu'ar Allah yasa a gan ta dan ni har yanzu son tada kaunar ta suna nan a dashe a zuciyata duk wannan abu da ya faru Allah yayi shi ya faru kuma nine sila mai shati'a yace na daga shari'a zuwa ashirin da uku 23 july a koma dashi gidan maza da sauri ya dafe kansa da hannunu biyu lokaci guda ya ji wani bugun zuciya kafin yan sanda su karaso inda yake har ya fadi kasa babu wata gaba da take motsi a jikinsa lokaci daya alhaji shima ya kwalla wata kara shima ya fadi kasa tsawar ce ta gigitani biron dake hannuna ya fafi kasa.ALHAMDULLILAH
shin za'a ga rufaida kuwa? idan an ganta a wani hali za'a sameta?, shin ya hukunci safuwan zai kasance?
ku saurareni a littafi na biyu da kuma littafina mai fitowa nan gaba mai suna..........
,
GODIYA da yabo sun tabbata ga Allah subahanahu wata ala mai kowa mai komai tsira da aminci su tabbata ga annabi muhammad (s.a.w) da alayen sa da sahabbansa sa masu girma da daraja.
.
KARSHEM DAN ALHAJI LITTAFI NA 1 SAI KARASHEN ZUWA MASU MAKONNI IN MAI DUKKA YA KAIMU
.
Jinjina ga marubucin wannan littafi M. A Gana, Allah yakara basira..
.


sai ni kuma jabeer rabi.u idris dana kawo muku ke cewa ku huta lafiya


whatsapp 07034488635.......... Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment