Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dauke ta tsawon minti goma ba wanda yayi magana yace to ni ya zanyi na shawo kanta?
.
suka hada baki suka ce ya kake yi da sauran yan matanka" munarshir ya kama kunnensa ya rada masa wata magana yace kwarai da gaske suka dau dariya gaba daya suka tafa gaba daya sulainman yace kabar min komai a hannu na kai dai ka dauke kafarka kwana biyu ka kuma hakura da yi mata waya ko da kuwa ta kiraka a waya ka kaheta ku dai ku bani lokaci dana daukar maka za kaga aiki da cikawa ya girgiza kafadarsa yace Allah ya kaimu gaba dayan su suka amsa da ameen ni dai nace allahumma a'a kwana biyu bata ji duriyarsa ba hankalinta ya tashi soasai ko ta name shi a waya baya dauka ta ringa turawa da message amma shiru ba amsa ba karamin tashin hankali ta sake shiga ba abin duk ya biya dameta ta ringa tunani anya lafiya kuwa ita dai a iya sanin ta ba abinda ya shiga tsakanin su shihowar wani yarone ya katse ta daga tunanin wanda ya zame mata abincinta a kullum yace "Assalamu alaikum wani ana sallama da rufahda inji wani a waje dakwa tayi kamar bata jiba umminta tace baki ji abinda yace bane? tace iye iye? tace ana kiranki a waje ki leka ki gani mana tace jeka kace wane ne?
.
yarobya dawo yac sulainman ne abokin safuwan wani tashin hankali taji ya dada karuwa ta tabbata ba lafiya ba.tana fita ganin sulaiman yasa ya taji wani faduwar gaba ta karasa inda yake suka gaisa duk ta matsu taji halinda safuwan yake ciki yace baki tambayeni mutumin kiba? tace shine abinda nake so ji yace to mutumin an binciko file dinsa ta dafa kirjinta tace bashi da lafiya mai ya same shi? wallahi zazzabi ne oai zafi ya kamashi ko abinci baya ci a gaskiya zazzabi bai kama shi da wasa ba shine naga ya dace na zo na sanar `a ke dan kar kiji shiru tace hakan yayi kyau na gode shi kuma Allaj ya bashi lafiya yana gida ne ko .......?
.
yace a'a suna da likitansu a gida shi yake buba shi gashi bansan gidan su ba inji ta sulainman yace gidansu ba boyayye bane ko kuma kar na baki wahala kawai ki gaya min ranar da zaki sai na zo mu tafi tsaya na baki lambata idan kina da bukatar hakan sai ki neme ni tace ba damuwa in haka ta taso na neme ka sukayi sallama ta shige gida ta sanar da ummin ta safuwan bashi da lafiya sosai shine abokinsa yazo ya gaya mata habiba tace aiya shi yasa kwana biyu baya zuwa Allah ya bashi lafiya tace ummi dan Allah ki barni naje na duba shi tace kin san dai bazan mu tunkari abbanki da wannan maganar ba ta sake sasaauta murya ummi har naje na dawo ba tare da ya sani ba tare da halima abdullahi ta raka ni hakan yayi kyau sai ki shirya ku tafi nan da nan ta shirya cikin wani leshi madan karen kyau gashi ta tsara kwalliya mai daukar hankali tayi kyau sosai abinka da kyakywa ta sake tsokano shi ita da kanta da ta duba madubi sai data firgita gashi kayn fitet ne ta dauko mayafi ta yafa tana fitowa umminta tace baza ki tafi a haka ba ita kanta kyaun rufaida ya firgita ta duk dacewa kamar su daya sai dai ta fita haske.ta koma daki ta kuma duba madubi ta tabbatar umminta tayi gaskiya kamar ta cire sai wata zuciyar taba ta shawarar dora after dress akan kayan ta after dress mai ratsn ja gashi jan less ne ta saka zaka zata wata yar india ce tafito tace ummi haka yayi?
.
tace ko kefa to je ki daki ki dauko min wannan karamar jakata ta dauko ta mika mata ta dauko kudi naira dubu uku tace ki sai masa kayan dubiya tace mai zan sai masa? tace abinda kika gaya dace ta rataya jakarta tace sai na dawo habiba tace af! kin kira habiba a wayar kin ji tana nan?


*** DAN ALHAJI 6 ***
.
Na manta bari in kira ta ta dauko wayar ta a cikin jakarta ta kira halima sau uku shiru wayr taki shiga ummi kin ji wayar taki shiga ina ga maysalar bata da cajine bari naje gidan suna gani tace to dai dan bata anan ki dawo kar ki tafi ke kadai kuma ku kula da kanku ku tsare kan ku ku kila da mutuncin ku ku dawo da wuri kafin ya dawo tana zuwa ta tarar gidan su halima a rufe jikinta yayi sanyi tasan uma idan ta koma gida shikennan babu tafiya gashi ta matsu taga yadda jikin nasa yake da dade tana tunani ko ta koma gida ummi baza ta barta ta tafi ita kadai ba uma gashi batsan ranar dawowar su halima daga garinsu ba indai kika ga sun kulle gidan gaba daya to sun fita gari ta kuma dada sanar da ita sun kusa tafiya gashi bata da wata kawa da umminta ta yarda da ita bare ta dauke ta,
.
sai kawai ta ynke shawarar tayi tafiyarta tana isa bakin kasuwa tayi masa siyayya ta kira sulainman tayi masa kwatancen inda take akayi sa'a lokacin suna gidan safuwan da suka tsara yadda za suyi inta zo a zuciyar sa sai ya ji tausayinta amma ina shedan ya rinja yeshi wani hadaddan lemon kwali suka bude suka zuba wasu kwayoyi masu sa maye suka rufe suka mayar firij ya sami wani shinfideden bargo ya lullubu ya kwanta a kan gado ba wanda zai ce ba mara lafiya bene.ayya Allah sarki rufaida,bai fi awa daya ba ta dawo hayyacinta a gigice ta tashi ta ganta akan gadon sa wata kara ta saka marar misaltuwa hade da wasu zazzafan hawaye suka ringa fitowa mata tayi zinbir ta mike ta dau kayanta tasa shi kuma ya zuba mata ido yana kallon kyakykyawan surar da Allah yayi mata a cikin mata da banbanci duk iya neman mata irn nasa bai taba gamuwa da irin taba ko tima bata kama kafartaba ya kudiri niyyar kota halin kaka sai ya mallaketa a matsayin matarsa cikin rudani ta juya ta kalle shi tasana mara misaltuwa da tsiya wacce baza dada son komai kama dashi ba tace
.
KA CUCE NI!!! KA YAUDARENII!!! KA BATA MIN RAYUWA!!!! KA CUCI IYAYENA!! KA DAU ALHAKINSU!! KA ZALINCESU!!! ALLAH YA ISA!!
.
kukan da keyi ya sake tsanan ta tacu gaba da cewa sun dauki shekaru da dama suna tarbiya ta amma sa'a daya ta tashi a banza cikin kuncin zucita tace Allah ya isa! tsakanina da kai yadda ka sani cikin takaicin rayuwa in Allah ya yarda kai ma haka zaka kare da sari ta fice daga dakin ta nufi hanyar fita waje
duk tausayinta ya dame shi da na sanin da bata da amfani tashi yayi ya ringa zagaya dakin ya rasa abinda yake masa dadi can hangin jakarta da hanzari ya dauka ya bita ya kwalla mata kira amma ina ko kallo bai isheta ba motarsa ya hau ya bita har titi ya tsaya dai dai inda ta tsaya yace ga jakarki ba tare da kallon shiba tasa hannu ta fisge tayi gaba bitaa yayi da kallo yana cewa ta shiga ya kaita gida yana kallo ta tayi wata mota tayi tafiyarta ta bar tsaye sai ga sulainman nan suka tyaya suna tambayar sa ya DAN ALHAJI da fatan ka rubuce ka wanke ko kallon su baiyi ba yaja motarsa ya barsu a nan tana shiga gida ta tarar umminta na bacci lallabawa tayi ta shiga bandaki ta gama abinda zatayi tata gyara fuskarta sannan ta koma dakin ummi tayi sallama tace ta dawo tace yaya jikin nasa tace da sauki ummi tace ninaji a jikina dk ba dadi shine na kwanta ina kuma halima?
.
tace ta wuce gida ita sauri take wai zasu tafi garin su yau kwana da kwanaki tana cikin bacin rai ta kasa gayawa kowa ta bar abin a zuciyarta yana damuntako baccin arziki batayi ga wani sauyi da take ji a jikinta ta kara razana.kullum sai yayi mata waya data gaji ta babbalata ta watsar duk wani abu da tasan inta kalle shi zata tuna da shi ta rabu dashi kullum yazo sau hudu ko biyar taki fita duk umminta na lura da hakan tace wai ke me yaka hakan to?
.
da taga hakan gudun kar ta takura mata sai taji abinda yake faruwa idan yazo sai tayi kamar ta fita sai ta shige wani daki a sororon gidan ta kifa kanta tana kuka bata zata umminta ta ganta bata shigo daukar itace ba karamin faduwar gaba tayi ba tace me kike yi anan? kuma kukan me kike yi? zaki gayamin abinda yake faruwa ko sai ranki ya baci na lura lura da ke tun ranar dakikaa je duba yaronan kike cikin kunci to me ke faruwa in baki gaya min ba wazaki gayawa? ko dole akace ki saurareshi? ai dama ke kika ce kina sonsa cikin shekar kuka tace ummi ba komai ji nayi bana son sa akwai wani abu haka kawai baka ce baka son mutum sai da dalili shike nan dga yau idan yazo sai kin boye a nan nba kawai kice bakya nan rufaida inkin huce inda rabo sai ku shirya tashi ki shiga gida ta bita da kallo tana murmushi a zuciyarta inadai fada ne irin na saurayi da budurwa nawa akayi aka shirya ta dauki itacen ta tashiga gida itama kawana biyu a tsakanin haka laulayi ya bayyana tashin zuciya da tsirtar da yawu amai da sauran sauransu Rufaida ta fara hankalin habiba ya tashi data lura da halin da yar take ciki tace ke! gaya min gaskiyar abinda yake faruwa dake? yau rabonki da ganin al'adar ki wata nawa?
.
*** DAN ALHAJI 7 ***
.
Tayi shuru ta sake zare mata ido cikin fada tace zaki gaya min ko saina ci miki mutinci cikin raway murya tace wata biyu batasan lokacin data makureta ba tana cewa ni zaki bawa kunya duk irin tarbiyar da muke miki a banza ashe duk wannan abin da suke akan idon mallam nasiru cikin tsawa yace saketa aikin gama ya riga ya gama cikin wata mahaukaciyar tsawa ya sake cewa zaki sake ta ko sai kinyi kisan kai tana sakinta ta fadi a sume cikin gigita akayi asibiti da ita bayan an gama aune aune da dube dube da kuma bugun zuciya da suka gani suka kira mallam nasiru.suka tabbatar masa tana da ciki na wata biyu da kwana goma sannan matsalar duk sanda wani abu ya faru wanda zai fadar mata da gaba zata iya rasa tunaninta in dai ta razana suka sallameta suka bata magunguna a haka suka bar asibitin a sabule bayan sun je gida ne ta tambayita wanda yayi mata ciki bata boye musu komai ba a lokacin a lokacin habiba ta sha fada dan me ta bar ta taje buba wani saurayi?
.
to iyaye mata ayi hattara akan irin wannan tabargazar kobuba saurayi ko zuwa gidansu ko a gaiyace ki party koh gidan aboki,to dai yan mata ayi hattara iyaye musa ido akan shige da fitar yayan mu yan mata a guji karbar abuna shi kona ci a wajen samari,ayi hattara mutunci daya ne idan ya zube rayuwarki ta shiga ibtila'i dan Allah mu kula Allah ya kare mana har kukan dan kan daru YANCIN KU GIDAN MAZAJEN KU.
AMEEN!!!!}
.
gidan Alhaji muazzam ya nufa yayi sa'a ya same shi aja yo masa sallama da shi ba dadewa yana tsaye wanda ya aiki yafito yace wai waye yace kace bako ne yake son ganinsa ya ske dawowa yace an ce ka shigo wani falon alfarma aka shiga da shi yana shiga ya tabbatar alhaji ba karamin mai kudi bane amma hakan bai sa zuciyarsa ta karaya yaji tsoron fadin abin da yake tafe dashi ba suka gaisa yace na zone na sanar da kai cewa dan ka safuwan ya yiwa ya ta fade saboda haka har ciki ya shiga zirbir Alhaji ya mike yace au ta haka kuma ka bullo? kana ganin hakan zai sa na yarda ya aure ta? to tsaya na gaya maka har yanzu ina nan kan bakata ka nemi wannda ya yiwa yarka ciki tun da wuri kuna sakin yayan ku kamar awaki sai sun dauko muku abin kunya ku rasa yadda zakuyi ku ringa kame kame idan kun sami warsali sai ku lika masa kawai in so kake a taimaka maka a baka kudin dazaka zubar sa a baki ba sai kazo kana soki burutsu ba duk wannan maganganun nasu kamar da almara da yake malam nasiru yana tsaye jikinsa sai tsuma yake dan tsananin bacin zuciya tashi yayi ya dauko kudi masu yawan gaske dan a kalla za suyi dubu dari biyar ya mika wa malam nasiru ya fisge ya yayyaga su ya watsa wa Alhaji yace karya kake kace zaka siyi mutuncin yata baka da kudin da zaka girgizani.
.
"hmmm toh mata masu kwadayi a kiyaye,cikin zafin nama yayi kan malam nasiru ya ce kan har ka isa ka zo har gidana kaci min mutunci hajiya bilki data shigo taga Allah yayi kan mallam nasiru ta shiga tsakanin su da sauri shi ko nasiru ko zagesu Alhaji yaci gaba da fada sai naga wanda ya tsaya maka a garin nan ko wayene wallahi baka isa ka jada niba kawai talauchi yana damunka zaka zo kayiwa mutane hauka ga kanan babban mahaukaci kana ganin yata ko ta rasa wanda zata aura zata auri dan kane? zan bari ta saurareshi ne kaine baka isa da danka ba amma nina isa da yata banza shashasha banZa, ya ringafizgewa yana ki bar nina nuna masa matsayina ta juya tace da mallam nasiru dan Allhah fita kayi tafiyarka kayi hakuri ya fita yana cwa da kin bar shi ya dau raina tunda bani da galihu ta zaunar da shi tace kaga abinda nake gaya maka ka barshi ya auri wacce yake so kaga yanzu ya jawowa mutane abim kunya yace au ke kin yarda shi yayi mata?
.
kunya kuma su suka ji tunda ba a jikin sa cikin yake ba duk abinda namiji yayi adone kuma sai na dau mataki a kansa zai sa yazo har gida yaci mutunci na sai na sa an daure shi ya raina kansa hajiya bilki tace haba yallabai a cuce shi a hana shi kuka kasan fa duk abinda ya fada gaskiya ne kawai dan bashi da kudi a danne masa hakki, a fussace yace ke tunda kina da kudi basai ki tsaya masa ba wannan ai maganar banza ce kina ganin abinda mutum nan yayi min ya nuna kudi a kaaa an yaya gasu gutsi gutsi baza su taba moruwaba tace ai bai rama ba na riga na cuceshu ya harzuka yace walllahi ran ki zai baci saboda tashi ki ban waje ya sake daka mata tsawa ta mike ta fice ya zauna yana ta kunfar baki yana hada gumi yana ganin tunda yake bawanda ya taba ci masa mutunci irin wannan zaune suke a majalisa suna ta shewa duniya tayi musu dadi mallam nasiru ya hango dan marakin zuciyarsa ta kuma yi masa zafi tafiya yake kamar zai fadi har ya karaso kusa da inda suke ya tsaya jikin wata bishiya da aka sare cikin daga murya yace kai safuwan wainwayo yayi da sauri kiran da yaji kamar daga sama ganin malam nasiru yayi a tsaye yana ganinsa ya taso cikin faduwar gaba haka kawai yaji bugun zuciyarsa yana karuwa.




** DAN ALHAJI 8**
.
Yana karasowa inda yake ya sunkuya zai gaishe shi yace dakata daga wajen ubanka nake naje dan mu sami masahaal akan abinda kayiwa rufaida har ciki ya samu shine ya nuna min bashi da mutunci kafin ya sake wata magana safuwan yace ya za'ayi kaje wajen sa o shi yayi mata cikin?? malam nasiru yace rashin kunya zakayi min har kana da bakin fadamin wannan maganar yace an fada maka kai kake niyyar zagin ubana to wallahi kar ka yarda ka zagar min uba yace idan na zage shi me zakayi? yace rama masa zanyi uba bai fi U.
.
kafin ya karasa mallam nasiru ya kai masa mari fau!! yan majalisan ganin haka suka taso da sauri shi ko safuwan ganin haka yana juyowa shima ya kai masa wani wawan mari anan da nan mallam nasiru yayi sauri ya kauce kaucewar da zaiyi yaci tuntube ya fada kan wata reshen bishiya yana fadowa kansa ya fashe kafin wani lokaci mutane sun taru kowa na fadin albarkacin bakinsa,wasu nace wa shi ya tura shi wasu nacewa tuntube duk yabi ya rude ganin halin da malam nasiru yake ciki nunfashin sa sama sama wasu na cewa ya mutu wasu na cewa da ransa aka dauke shi akayi asibiti duk wanan abinda yake faruwa akan idon iyatu a kusa da gidan su rufaida take aiki gidan wani wai Alhaji kabiru tana gani malam nasiru ta dauka fa da sauri ta nufi gidan sa tana shiga ta tarar da habiba zaune tana bawa kamal nono ta labarta mata batasan lokacin da ta ajiye kamal din ba ta dauki mayafi bata tsaya daukarsa ba tayi waje da gudu ba takalmi rufaida ta rufo mata baya suka bat iyatu a tsaye yaro an dagwar dashi yaga fitar yan gidan su ya daga ido yaga baisan iyatu ba ya barke da kuka tasa hannu ta dauke shi ta ringa rarrashin sa yaro yaki bi sutayi da shi suna isa wajen da abin ya faru suna kokarin tsallaka titi lokaci da ake kokarin sa shi a mota jini yana tsituwa habiba ba tare data duba titi ba ta tsallaka mai mota yana tayi mata horn rufaida tace wa ummi ga wata katuwar mota nan tsaya ta wuce ina motar nan tazo tabi ta kanta take ko shurawa batayi ba.tab!
.
Ana wata ga wata ga kuma wata Allah ya sawwaka dai,ana barin wajen da aka sa mallam nasiru a mota kallo ya koma titi gawar habiba kwance ita ko rufaida tunda ta kwallara wata uwar kara ta nufi wata hanya (abinda likita ya fadi ya tabbata) mutane suna ta habiba ba wanda ya kula da ita iyatu na karasawa da kamal a hannunta taga abinda ya faru jikinta ma rawa yake tana ta kuka tana cewa itace matar mutumin nan dya fada kan bishiya mutane sunyi jugun jugum sai ga motar data dauki malam nasiru ta nufi gidansa dashi kafin su karasa asibiti ya cika a ranar mutane unguwar da dukkan wanda abin ya faru a idonsu koya jiyo labari ba wanda bayi kuka ba alhaji kabiru ne komai ke hannunsa banda kukkan ba abinda yake shi da matarsa sun shaku sosai anyi zaman mutunci aka sitirtasu aka sallace su aka kai su makwancinsu bayan dowowarsu ne kowa ya nutsu aka tuna ba'a ga rufaida ba mutane da yawa sunce tare suke lokacinda abin ya faru iyatu ce ta bada shaidan hakan kmal sai kuka ya ke yana dube dube mutane yana neman uwarsa gashi ba'a ga yayarsa ba karamin tada hankali mutane yake ba alhaji kabiru ne ya dauke shinyayi waje dashi yana rarrashinsa har bacci ya daukesa jikinsa yayi zafi sosai saboda kukan daya dade yanayi Allahu Akbar! Alllah ya jikan malam nasiru da malama habiba
.
Gashi ba wanda inda yan uwasa suke ba irin bakin cikin dasu alhaji kabiru da abokan aikin sa ba suyi ba rufaida ko jin wanda ya ga mai kama da ita ba'ayi ba mutane unguwa sunce sai sun dauki mataki akan safuwan wasu nace wa abar shi da Allah tunda yanzu ina mallam nasiru da mai dakinsu da yar tasu da abin ya faru saboda ita wannan kawa ibtila'i ne daga Allah yan sanda ko tunda abin ya faru suka tsar keyar safuwan Alhaji duk ya rame yayi baki hajiya bilki ko tunda taji abin daya faru da iyayen rufaida bata cikin hayyacinta tana kwance a asibiti jininta ya hau sosai safuwan ko in ba kyakyawan sani kaya masa ba baza ka gane shi ba yan sanda sun hana ganin shi ko Alhaji ma sau daya ya ganshi.kamal har ya fara sabawa da mutanen gidan alhaji kabiru ba irin sabon da basu yi da Alhaji ba barcine kawai yake rabasu kullum zai tafi kasuwa sai da dabara suke rabuwa wani lokacin ma boye shi akeyi sai nono ko dama ba'a kara bashi ba tunda dama ya isa yaye gashi Allah ya jarrabi Alhaji kabiru da hajiya naja son sa Allah ne ya basu dama basu taba haifuwaba kusan shekara ashirin da aure Allah bai basu haifuwa ba yaro yasake wani girma da wayo Allahji muazzamu duk wa babba wanda yasan mai fada ajine ba wanda bai gani ba akan a bashi safuwan hakan ta gagara saboda duk wani abin da yake makama da shi gaba da gabanta Alhaji kabiru yafi shi idon ko batun kudi ne yayi masa fintinkau ba yadda baiyi ba akan suyi masahalaha da alhaji kabiru abin yagagara yaune ranar zuwa kotu duk wani wanda abin ya shafa ba wanda bai halattaba yan kallo ko kamar kasa ba wanda ke jin tausayin safuwan ko mahifinsa kusan mutane unguwar su murna suke suna cewa ai dama gaba da gabanta duk iskancin da yaron kayi ubansa baya kwabarsa.
** DAN ALHAJI 9**
== == == karshe == == ==
.
Komai yayi daidai dan tunda abin ya faru ko kare a cikin unguwar ba wanda yaje masa jaje hakan yan uwansa wannan abin ba karamin tayarwa da alhaji muaZzam hankali yayi ba duk sai yaji ya tsanni halayensa yasan shi ya jawa kansa halinsa na wulakanta talakawa ga irinta nan tun daga yanzu hatta yan uwansa sun tsane shi lokaci daya ya gane kuskuransa ga kuma dana sani da yake tayi akan malam nasiru ga shi cikin lokaci kankani ya bar masa duniya gashi ya rataya akan dansa kai! duniya abin tsoro ce daga wannan lokacin yasan lallai ya yarda kaki naka duniya taso shi kaso shi duniya taki shi gashi dai ta faru akan Alhaji muaZzamu ya gani tun kafin aje ko ina duk kowa ya natsu ana sauraron fitowar mai shari'ah waje ya cika makil can tsayin wasu yan mintuna sai ga shi mai shari'a ya fito kowa ya tashi ana fadin kotu ya zauna sannan kowa ya zauna waje yayi tsit ba wanda ya sake ko tari sai can ga wani mai sayar da doya ya doso get din kotun ganin mai gadin baya wajen ya zagaya ya hango mutane da yake babbar kotu ce wajen kotun biyar ce ya fito yana a sayi doya wani mai tsaron kotu number 2 yace ka bar wajen nan ba wajen talla bane mai shari'a ya shigo banza yayi masa yaci gaba da fadin a sayi doya mai shari'a ya daka tsawa yace waye mai mana tallan doya anan wai?
.
yan sanda sukayi kansa da yake mai taurin kai ne sai ya zagaya yaci gaba da tallansa mai shari'a yace aje a shigo da mai doyar nan b bata lokaci suka cika aikin su kafin su shigo dashi ya tsaya zai yimusu taurin kai ya sha kulki kotu mao shari'a yace kai na ce maka nan wajen talla ne kuma ba anje an yi maka magana ba? saboda kai dan taurin kai ne kaki maza ku ajeshi sata daya ya durkusa yace dan Allah yallabai kayi hakuri yace an kara maka sati biyu ya sake cewa wallahi talla na fito ban barwa iyalina na komai ba yace sati uku shigo ku tafi dashi ya tsaya ya sake cewa dan Allah ayi hakuri alkali yasake cewa idan baka shige ka tafi ba in ka sake magana sati hudu ya sake cewa in kun kulleni yayana da matata zasu shiga damuwa alkali ya sake cewa kar ka kara magana sai ko cewa yayi tunda ka dauke ni ta karkarewa yai ya ringa cewa asai doya! asai doya! asai doya! ba wanda abun bai bawa dariya ba amma ba hali mai shari a ya mike yana cewa ya shiga cember aka yi gaba da mai doya a na ganin mai shari a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment