Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

ο»ΏπŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³

*BOYAYYEN MUTUN* πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³



*Maman Abd Shakur*


Documents By AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels


_Aisha Muhammad Sani Oyiza!!! Na sadaukar miki da wanan littafin, this novel is for you my humi darling, my sister, my support system, my rock, i love you_


1⃣

Bishiyoyin dogon yaro ne guda shida dasuke zagaye haka a dajin da ba datti alamun ana gyara wajen, kowani bishiyan an makala shooting target vector ajikinshi sai wani babban dan table haka dake filin wajen daba komi akai, jiinnjinjinnn karan power bike yacika wajen, daga kai nayi danna kawo muku rahoto da kyauπŸ˜‚.
Daga dan nesa da bishiyoyin black powerbike din ya tsaya batare da an kashe machine dinba sai kuka machine din yake mai kara as usual irin na power bike dinan, daga kafa nafara kallon mutumin kan bike din, black hermes covershoe ne akafanshi dake sanye da bakar safa, yasaka bakin straight leg trim trouser, sai black Versace greco hoodie ne ajikinshi, hannunshi sanye cikin wani irin hadadden black safan hannu na maza, bayanshi goye dawani hadadden black bagpack, ahankali ya daura hanun akan key machine din ya juya hakan yasa machine din ya mutu, da kafarshi na haggu ya taba break din machine din ya tsayar da ita da kyau kafin yay wani irin tsalle ya dirgo daga kan machine din ya tsaya yana wani irin jan rigar jikinshi yana gyara tsayuwa, dogone sosai cikakke dan yacika kayan dayasa fam, duka hannayen shi ya daga ya daura akan hamlet din dake kanshi, ahankali ya cire ya rike a hannu yana jujjuya hamlet din yana kallo, gabaki daya kanshi da fuskarshi nacikin wani irin safar fuska baki ya sanya wani irin bakin glass dake manne ido sosai irin wanda sojoji ke sawa, baka hango bakinshi baka ganin hancinshi sai tudun hancin da dan raga raga ta wurin hancin, ajiye hamlet din yayi akan power bike din, ya daga hannunshi na haggu yana kallon screen din wani hadadden agogon dake daure a wutsiyar hannu akan safan hannunshi, sakin hanun yayi ya tura a aljihun wandon jikinshi dayan hanun kuma na lilo ya juya yafara tafiya kaman zaki yay wajejen bishiyoyin, awajen table din tsakiyar wajen ya tsaya yana bin bishiyoyin da wurin da kallo kafin sauke ya jakar bayanshi ya daura akan table din, zage zip din jakar yayi yaciro wasu bindigogi guda biyu kirar berreta M9 yana dan jujjuya su kafin ya gyara zaman su ahanunshi ya fara tafiya kaman zaki har yakai wajejen bishiyoyin, gyara zaman shooting vector din daya daga cikin bishiyoyin yayi kafin ya juyo ya dawo ya tsaya agaban table din, gyara zaman bindigar yayi ahanunshi yana kallon shooting target vectors dake jikinshi bishiyoyin wurin tacikin bakin glass din dake kan fuskarshi, ahankali ya ijiye bindigar ya tura hanunshi cikin jakar yaciro earmuff, saka earmuff din yayi suka rurrufemai kunne kafin yadau daya daga cikin bindigogin ya saiti target din vector din, pulling trigger yayi yay harbin bindigar tai kara bam aiko ya sami target din daidai, kara saita bindigar yayi yacigaba dayin harbinshi kara kawai ke tashi adajin, saida yay kusan one hour kafin ya hada komi ya maida jakan ya sake kallon agogon hannunshi sanan yadau jakar ya goya, yatako dawanan tafiyar kaman zaki yahau kan bike din yatada dawani irin azababben gudu yabar wajen.

Gaban wani babban gida anan cikin dajin yay parking wani irin dirowa yayi daga kan mashin din yay cikin gidan, babban gidane sosai ga manya manyan mota daban daban a compound din, gakuma babban masallaci ata gefe, wani babban part yabude kofa ya shiga.....



*************************

Babbar mace ce dake cikin shiga ta alfarma zaune acikin wata bakar mota kirar lexus da driver ke gaba yama kunna motar amma baija ba, agogon hanunta na gwal takalla ta dafa kai tace "ohhh yarinyar nan saitasa nai missing flight ko? Kaga Adamu jeka kiramin ita tafito" dan dariya direban da aka kira da Adamu yayi yace "to hajiya" ya kashe motar ya bude kofa harya fito da kafa waje wata yarinya doguwa haka brown skin budurwa dake sanye da fararan uniform tafito tana sanye da black cover shoe, white dogon wando dayasha karin guga, da farin riga daya tsaya mata a gwuiwa shima agoge, sai dan hijabin ta fari daya wuce kirjinta kadan, bayanta goye dawani bakin jaka babba na student, saikuma hanunta rike da after dress dinta baki da bata sakaba, murmushi tama Mum dinta dake cikin mota tana hararanta, da dan gudu takaraso wajen motan ta zagaya ta dayan bangaren zata bude kofan motar ta shiga, wani saurayi matashi dake sanye cikin suit da necktie a wuyanshi dabai gyaraba yafito rike da dan karamin food flask ya tsaya a barander ya kwala mata kira. "Nadeera" da sauri budurwan dake shirin shiga mota ta dago kanta, hannu tadaura akan karamin bakinta tace "laaaa" da gudu tai wajen barander ta tsaya ta mika hannu zata karbi kulan aka bude kofa, wani namiji babba ne yafito shima sanye da suit dawasu files a hanunshi saidai shi yafi wanan dake rike da kulan girma, idanunshi sanye cikin bakin glass babu alamun wasa akan fuskarshi, da sauri ta hadiye dariyan datake ta karbi kulan tace "thanks Ya Ahmad bye, aje banki lafiya my accountant" hararanta yayi yakai hannu zai mata rankwashi da gudu tai wajen mota tsawa aka daka mata hakan yasa ta tsaya ta kwalalo ido. "i think I've said it time without numbers banason guje gujen nan right" da sauri ta juyo ta kallai tana kara kankame kulan hanunta tsabagen tsoro, ahankali tace "bazan karaba Ya Muhsin, am sorry" daga ta chan mota Mum ta kwala mata kira. "Nadeera waisai nai missing flight dina hankalin ki zai kwanta ko" da sauri ta juya tana ma Ya Ahmad dake mata murmushi bye bye asace ta wuce wajen motan zagayawa tayi tabude kofa ta shiga driver yaja yay horn mai gadi yabude musu babban gate din gidan suka fita.

Hanun Mum ta rungume tightly ta lumshe ido, hakan yasa Mum dake daddanna waya ta ijiye wayar ta juyo murmushi kan fuskarta tadago kanta hakan yasa hawayen datake makalewa suka zubo da sauri Mum ta share mata hawayen tana girgixa kai tace "zaki fara ko, ke kullum idan zanyi tafiya saikin yi kuka bakisan yanzu kinyi girma ba u are 22 fa, stop it princess, bazan dade ba this time i promise you" fadawa tayi jikin Mum din ta kankameta sosai tasaki kukan da kyau tana shesheka ta yanda Mum ce kadai zata iyaji, cirota Mum tayi ta riketa saikuma ta bude hadadden crock handbag dinta dake gefenta taciro handky dake kamshi sosai tace "oya ya isa kinga karki bata white dinki, i said bazan dadeba kinji my Nadee" gyada mata kai tayi hakan yasa Mum ta shiga share mata hawayen da kyau kafin ta ijiye handky akan cinyarta, maida kanta tayi kan kafadar Mum ahankali tace "yaushe zaki dena tafiye tafiyen nan Mum? Banaso kina tafiya kina barina ni kadai, kinga Ya Muhsin yacika min fada barinma in bakinan, Ya Ahmad da Daddy ne kawai ke sona, Mum please kidena tafiyan nan d house is boring anytime u are not around, Mum please kidena" murmushi Mum tasake yi kafin ta dagata daga kan kafadar ta ta fuskanceta da kyau tace "don't worry bazai miki komiba, and if u need anything koda Dad dinki baya nan ask any of your brothers zasu baki, akwai some designs ne dasuka kare a boutique kuma akwai high demand akansu so dole nai tafiyan nan, just do one thing for me, take care of yourself okay" gyada mata kai tayi zatai magana wayan mum yay kara hakan yasa mum tadau wayar ta kalli screen din sanan ta kalleta tace "hold on baby business call ne lemme answer it" gyada mata kai tayi ahankali ta mayar da kanta kafadar mum din tana tunane tunane, Mum bata tabayin cikakken wata daya a gida ba kullum tafiye tafiyen kasashe saro abubuwa take, tanada manya manyan super market, tanada boutique, tanada babban plaza na interior designs, koma tana nigeria baka ganinta agida tana shagunan ta, neman kudi bala'i ne da Mum gashi basu rasa komiba amma tarasa mesa takasa daina business, matse hanunta akayi hakan yasa ta farka daga tunanin datake yi ta kalli Mum din dake mata murmushi tace "tell me tunanin mekike?" murmushi itama tayi daya bayyana white hakoranta tace "bakomi Mum kawai am feeling somehow ne yau tunda natashi as if something is going to happen to me" "did you pray?" gyada mata kai tayi tace "nayi Mum" shafa gefen fuskarta Mum tayi tana murmushi tace "My Nadee girl i know missing dina kike tun yanzu, anyway! Tunda kinyi addu'a am sure Allah will protect my baby girl for me, nothing is going to happen kinji" gyada kai tayi daidai lokacin direba yay parking agaban wani babban asibiti mai suna St. Edward teaching hospital, kofa Mum ta nuna mata tace "oya ayi practical lafiya my nurse, kardai akarya allura a duwaiwai patient, ur momma love you " dariya tayi tafada jikin mum din tace "i love to Mum, please come back soon" hawaye yataru a idonta, peck mum tamata akumatu tace "i promise, oya go go karki latti" murmushi tayi tabude kofan motar tafito kafin Mum tamika mata jakarta da food flask, karba tayi ta goya abaya ta rike kullan a hannu, sanan mum ta mika mata after dress din karba tayi ta maida kofar tarufe sanan ta daga mata hannu tana bye itama mum haka Adamu yaja motar sukai airport.

Motar tabi da kallo dasauri ta share hawayen daya gangaro mata ta sauke jakarta, linke after dress din tayi ta saka ata zip din bayan jakan, ta sanya flask din kuma acikin jakan sanan ta goya jakan tawuce ahankali kaman kwai yafashe mata aciki ta shiga cikin asibitin.

*team masoya BM*
*one luv*
πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³

*BOYAYYEN MUTUN* πŸ•³ πŸ•³ πŸ•³ πŸ•³


*MAMAN ABD SHAKUR*

2⃣

Tana shiga some students mate dinta guda biyu tagani zasu shiga ward da sauri ta taresu cikin innocent voice dinta tace "ammm please ina Fauzy taje ward ne?" atare suka "no yanzun nan ta shigo, taje common room" da sauri tai hanyar common room dinsu kafin HOD dinsu takamata ta turata ward, bude kofan common room din tayi wani irin ihu budurwan dake zaune tana danna waya tayi atsorace tazaci HOD dinsu ce, hararanta tayi ta kulle kofan da sauri tana daura hannu akan lips tana hararanta tace "banza anhana zuwa da waya kina zuwa da waya ko?" ajiye wayar fauzy tayi ajaka ta tashi ta rungumeta tana dariya saikuma ta saketa tace "banza maisa kikai latti yau?" kaman zatai kuka ta sauke jakarta ta ijiye tace "Mum ce tai tafiya fa Fauzy, daga ni yanzu saisu Abba dasu Ya Ahmad fa sai mai mana aiki and ita bata kwana da yamma take tafiya kullum" takara she maganan hawaye na taruwa a idonta, Fauzy tace "sorry kinji yar Mummy kema ai dazaran miji yafito kiyi aurenki ki barmusu gidan su kinji saikinga dama zaki dinga zuwa" dungure mata kai tayi tana hararan ta tace "ke komi aure aure, to dan kiji sainayi school of Post Basic nursing nai specializing a anesthesia ko midwifery kafin nai wani aure" tabe baki Fauzy tayi tace "kya rube agida bokoko" itama tabe baki itama tayi tace "rubaben tumatir yafi dadi" kama baki fauzy tayi tace "laaaa Nadeera yar air cefake, rotten tomatoe" hararanta tayi zatai magana Fauzy tace "dalla nidai dau kayan aikin ki da log book dinki mu wuce baniso na biye miki rotten tomatoe" dariya kawai tayi bata karace mata komiba duk duniya fauzy ce kadai kawarta, yarinyar kawar Mum ce, bakatabajin tsakaninsu, bude jakarta tayi taciro statoscope dinta da log book, ijiye jakukunan sukayi suka wuce suka tafi sukai signing in, dayake wanan week din tana female surgical ward ne itakuma fauzy na pediatric ward hakan yasa ko waccen su tawuce ward dinta danyin aikinsu kafin da azahar su hadu su tafi masallaci, ward dinta ta shiga tana gaida matayen marasa lpy tana duba drip din da aka makala musu, kafin tawuce nurse desk dinsu ko zama batayi ba, senior nurse din dake wurin tasa taje tai taking vital signs din all d patients din ward din hakan yasa ta wuce.


***
Babu kowa afalon hakan yasa yay stairs da dan gudu gudu yay sama, wani daki yabude ya shiga, computers ne kusan uku adakin akan wani dogon table saikuma macbook akan wani dogon lumtsatsen kujera, jakar dake bayanshi ya ijiye akan table din kafin yadau MacBook dake kan kujera ya zauna akan kujeran ya bude yafara aiki, yakai kusan 30min yana danne danne, knocking kofar akayi hakan yasa ya dago kai yana kallon kofan, agogon hanunshi ya danna saiga hoton samari biyu dake bakin kofan nan ya bayyana ta jikin agogon kaninshi ne, Abdullah wanda yake karmi da Omari daya girmeshi, ajiye MacBook din yayi yatashi yay wajen kofan ya bude kofan yakoma inda yake yadau MacBook dinshi ya cigaba da abinda yakeyi, shigowa dakin sukayi suka zauna kusa dashi suka sakashi a tsakiya, na gefen daman shi ne yace "Ya Marwan were you able to hack his system?" wani irin wahalallen tsaki yaja maiyar kara ya ijiye MacBook din akan cinyar Omari dake gefen haggunshi yajuyo ya kalli Abdallah dayamai maganan, cikin wani irin murya irin na terrors dinan dakakkiya yace "no, dole saina sami kwayar idonshi, eye scanner yake amfani dashi, don't worry i know how i will get it, i have to go hospital din da aka kwantar dashi, kun mini abinda nace?" yana maganan irin dole dole dinan kaman wanda yasha wani kwaya yana kallon na gefen shi Omari, Canon camera hanunshi ya mikamai hakan yasa ya karba yana dubawa, hotunan plate number mota ne na motoci guda uku hakan yasa ya gyada kai tareda ijiye camera a gefen shi yace "gud, wat time jirgin su zai sauka da daddare?" Omari yace "10:45pm, suna tare da 8 bodyguards, 3 drivers, zasu shigo kuma da kudin" gyadakai yayi batare dayace komi ba, sai chan yace "su kamal fa hope suna various post dinsu" Abdallah yace "Eh, zasusan yanda zasuyi su makala device din a logage dinsu once sunyi landing" murmushi yayi mai sauti kafin ya kalli Omari yace "kuje ku huta, zanyi wasu ayyuka" murmushi Omari yayi yace "okay Genius, Abdallah muje kadafamin dat ur pasta, am hungry" murmushi yayi tacikin mask dinshi yana kallon kanin nashi, Abdallah ya harare shi yace "bazan yiba ai we have kuku because am d auta ai am not ur kuku ko Ya Marwan" yay maganan yana kallon Marwan dake kallonsu tacikin mask, zaiyi magana Omari yace "don't take side Ya Marwan, Abdallah baida kunya kwanan nan ya rainani wlh me acikin dafa pasta" "Ya Marwan wlh shine ya rainani, he's 28 am 26 but saiya dinga treating dina kaman wani under 12, duk inmun fita operation he always take my post, and dazaran mun dawo gida he will be begging me to cook for him, am only cooking for Ya Marwan kaje kaci na kuku bazanyiba" "saikayi, i said saikayi naughty spoilt brat" "nine spoiled brat?" yay maganan yana mikewa daga kan kujeran kaman zai daki Omari, hakan yasa ya daka musu tsawa tareda daga hanunshi sama. "enough!" natsuwa dukansu biyun sukayi, tashi yayi ya rungumosu duka zuwa kafadun shi batare dayay magana ba, sunkai kusan one minute ahaka kafin ya nisa yace "kudena fada, i hate it, my heart break anytime daga kunayi, Omari have you forgotten Momma's last words?" girgiza kai yayi ahankali jikinshi yay sanyi, hakan yasa yace "good! we are one, we only have each other awanan duniyan, i love you two" murmushi dukansu biyun sukayi atare sukace "we love you you more Ya Marwan" Abdallah ya mika hannunshi yace "and we are" Omari ne yadaura hanunshi akan na Abdallah, ahankali shima ya sakesu ya daura nashi akan na Omari atare sukace "The BM's" ihu sukayi atare suka rungume mai safan fuskan suna dariya kafin su tureshi da karfin bala'i yay kasa suka daddaneshi duk suna dariya, murmushi yayi mai sauti baice komiba dan kansu suka dagashi yay kaman zai kamasu da gudu suka fita suna tafi Abdallah hardamai gwalo suka fita. Ahankali yatashi daga kasan yana gyara zaman bakin glass dinshi yakoma kan kujera ya zauna yadau MacBook dinshi ya cigaba da abinda yakeyi.



***
Sunayin la'asar suka fito daga masallacin ita da Fauzy suka wuce common room jakunkunan su suka dauko, Fauzy sai tsaki take, dan dariya Nadeera tayi tace "wai menene kiketa tsaki?" tsaki takara tace "ba wayan nan nurses din bane badaman suga yan practical saisu dinga barmana aikinsu duka, wlh suna zaune watsapp suketayi nida su Aisha ne muka dinga aiki bakiji bayana ba kaman zai rabe" "sannu lazy babe" turo baki Fauzy tayi suka fita tare suna hira har suka iso gate, Adamu na jiranta itama Fauzy anzo daukan ta hakan yasa sukama juna sallama suka shige mota, Adamu ya kunna suka dau titi, ko minti biyu bata karaba ta bingile da bacci dan itama tagaji wlh har aka kai gida batasaniba, parking Adamu yayi a parking space yajuyo yace "hajiya hajiya mun iso" ahankali ta bude ido waigawa tayi ganin suna gida yasa tai murmushi tace "ok nagode" daukar jakarta tayi tabude kofa tafito ahankali kaman kwai yafashe mata a ciki tai ciki, kofa ta bude ta shiga cikin falon su, hadadden dakine da komi milk da black, ajiye jakarta tayi akan daya daga cikin royal kujeran dake falon ta cire after dress dinta ta ijiye, tacire karamin farin hijabin uniform dinta ta yar kan kujeran, nan dogon gashinta da aka mata kalaba kanana ya bayyana sai lilo suke, fuskarnan tai fayau idanun sunyi zuru zuru dan shegen yunwa takeji, wajen fridge tayi dake nan dining ta bude cold bottle water taciro tasha kafin ta kalli dining ganin bataga kuloli ba yasa tai kitchen da sauri kaman zata tashi sama, Yaya Muhsin tagani agaban fridge yaciro banana yanaci yana sanye da dan 3 quarter da white singlet da alamun bai dade da dawowa daga aikiba shima, kaman zatai kuka tace "Ya Muhsin ina wuni" tai maganan tana kalle kallen kitchen din ganin bataga any kula na abinci ba, hararan ta yayi saikuma ya mika mata dayan bananan hanunshi yace "have this, dat woman batazo ba yau, go and freshen up kizo kimana girki am hungry nima" gyada kai tayi hawaye na taruwa a idonta dan masifaffen yunwa takeji, karban ayaban tayi daga hanunshi tawuce tafita tadau jakarta da after dress dinta tai corridor dazai sadata da dakunan su kafin ta bude wani kofa ta shiga dakinta da akai komi pink ko ina a gyare tsaf tsaf sai kamshi yake.
Wanka ta shiga bayi tayi da ruwan dumi ta fito ta shirya cikin wani simple gown na atampa blue, ko mai bata shafa ba tasaka hula black, fitowa tayi ta tsaya tana kallon kofar dakin Mum, ahankali ta bude dakin ta shiga gani take kaman zataga Mum tafito daga bayi ko tana zaune akan gado tana danna waya sosai take missing Mum, maida kofar tayi ta fita tana jin wani iri Mum itace annurin gidan idan bata everything looks dull, dudda su Ya Muhsin mazane basa nunawa amma suma basajin dadi in batanan, kitchen ta wuce tafara girkin, simple jellof rice tamusu da salad, ta jera akan dining lokacin karfe shida, fita tayi dan zuwa kiran Ya Muhsin dan yazo suci daidai lokacin aka bude gate, ganin motar Abban sune yasa tai wurin parking da gudun ta. "oyoyo Abba" bude kofa magidanci da zaiyi 57 years yaci farin shaddan gizna sai kamshi yake zubawa ya fito yana mata murmushi yace "princess na missing Mumyn ta daga ganin dis eyes" dariya tayi ashagwaban ce tana bubbuga kafa tace "ah'ah ni bazanyi missing dinta ba, Abbana sannu da zuwa" "yauwa princess, ya kewan Mummyn ki?" kaman zatai kuka tace "lpy lau" murmushi yasake mata yace "dauko tsaraban ki acikin mota dawasu files dina kibiyoni dasu" gyadamai kai tayi tace "to Abba" yawuce yay ciki itakuma tabude motar ta dauko jakar coldstone ice cream data gani tana murmushi sanan ta dau files din data gani ta rufe motar ta wuce ciki itama, afalo ta tarar da Abban zaune da Ya Muhsin suna magana zama tayi gefen Abba bayan ta ijiye file din akan center table ta bude jakar zatasha ice cream din, Ya Muhsin ya watsa mata harara yace "ba abinci za'aci ba bazaki bar ice cream din zuwa anjima ba akwadayya" gyadamai kai tayi asanyaye, Abba ya daure fuska yana nunashi da yatsa yace "kaga kabar min auta tahuta, koma metake so tasha ubanta yasai mata ai, bakaga maman ku batanan bawai bakasan ajiki yakamata kajataba, sha abinki kinji Princess" Abba yay maganan da sigan lallashi, girgiza kai tayi dan tasan inhar tasha ice cream dinan sai Ya Muhsin yaci ubanta ko wlh tace "Abba anjima zan sha muje kaci abinci dana dafa kaji" tashi tayi yana murmushi yace "iyye my princess harta girma ta iya girki" suka mike sukai dining suka zazzauna shida Ya Muhsin, saka ice cream din tayi a fridge tadawo ta xuba musu abincin itama ta zuba nata aka shiru anacin abincin, Abba yafara gama cin nashi ya kalleta yace "iyye princess ke kika dafa abincin nan kuwa?" gyadamai kai tayi tana murmushi, dan dariya yayi yace "masha Allah my princess is now a big girl, sai aure, gaskiya u deserve a reward" dubu goma ya kirga daga uban kudin daya ciro daga aljihu ya ijiye mata kusa da plate dinta yace "naki ne karki raba da kowa d only nurse in my house" akunyace tace "thank you Abbana" tashi Abba yayi daga dining din ya kalli Ya Muhsin dakecin abincin kaman bashi a wurin yace "hurry up son mutafi masallaci" kaman mara son magana yace "to Abba" Abba yawuce ciki yana gyara malummalum dan dauro alwala shikuma yature plate din yabar wajen, bayanshi tabi da harara ahankali tace "dadin abin Abba dai yace abincin yay dadi and see my reward" ta nunama bayanshi kudin kafin ta mike ta atttare plate din takai kitchen ta wanke ta dawo ta gyara dining din ta wuce dakinta danyin salla.

Bayi ta shiga ta dauro alwala tafito tai salla kafin ta zauna tafara karatun Al Qur'ani ana kiran isha kuma ta tashi tayi tai shafa'i da wuturi sanan ta linke dadduman tahau kan gado ta dauko wayarta kirar Samsung A70 tahau watsapp tana duba groups kafin ta bingile da chatting da Fauzy ahaka bacci yay awon gaba da ita.

πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³πŸ•³

*BOYAYYEN MUTUN* πŸ•³ πŸ•³ πŸ•³ πŸ•³




*Maman Abd Shakur*

3⃣ - 4⃣


Misalin sha biyu da kusan rabi na dare wasu motoci guda uku suke tafiya akan titin hanyar airport ta wajejen daji dajin gefen hanya, titin shiru sosai babu wasu motoci dake wucewa banda su, benz guda biyu ne suka saka wata jeep din Brabus a tsakiyan su, kaman daga sama wani power bike ya yanko daga cikin dajin yahayo kan titin da wani irin fitinannen gudu, rike hanun bike din yay da hannu daya ya janye dayan hanunshi daga dayan hanun bike din yakai hanun tabayan wandonshi ya ciro karaman bindigar shi daya saka mata silencer abakin sabida kartai kara, saita bindigar yayi ya harbe tayan benz din baya, ya harbe na jeep sanan ya harbe na benz din gaba kafin yakara wani irin azababben gudu ya gaba, wani irin juyi motocin sukayi sakamakon fashewan tayan suka bubbuge juna kafin direbobin su tsayar da motocin

Please Login or Register in order to submit comment