Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ne gari hadari ya had'o sosai sai walk'iya da cida wato tsawa ake yi ga wata irin iska mai k'arfi da take kad'awa sosai, nan Sabeer ya shiga mugun tashin hankali sosai don yasan idan ruwa ya tsinke babu shakka sai yayi mishi jagab musamman idan mai feshi ne, kawai sai ya fashe da wani irin kukan tausayin kanshi, yana cikin kukan ne ruwa ya zuge kamar da bakin kwarya kafin Sabeer ya ankare ruwa ya jik'e shi jagab tunda kanshi har k'afafun shi.

Tak'urewa yayi waje d'aya ya had'a kai da gwiwa yana faman shashshak'ar kuka da rawar sanyi, ga ruwan sai zubo mishi yake jikin shi amman ya kasa tashi daga wajen toh idan ma ya tashi ina zai je bashi da wajen zuwa a yanzu wanda ya shige inda yake zaune.

Tun da aka fara walk'iya Suhaima ta farka tana zaune tsakiyar gado ta zabga tagumi duk ta rasa abin da yake mata dad'i, don tasan irin yanayin zauren gidan nasu ruwa zai jik'a mutum Yah Aliyu yana da niyyar gyaran shi cikin satin nan, amman tasan halin Yayanta sai yak'i gyara shi saboda Sabeer, kasa jurewa tayi ta sakko daga kan gadon ta nufi bakin window wanda za'a iya hango filin tsakar gidan zuwa cikin zaure.

Hannu ta sanya ta yaye labulen window wani irin mugun sanyi tare da feshin ruwa ne ya ratsa ta, bata hango Sabeer sosai ba saboda duhu sai kyallin farin kayanshi da ta hango, sakin labulen tayi tare da dawowa ta zauna kan gado kusan har aka gama ruwan gabannin asubah Suhaima na zaune ta kasa komawa bacci, da yake tana da toilet aciki ya sanya ta yin alwala tayi sallah tana idarwa ta fara addu'a tana cikin yi ne wani bacci mai k'arfi ya d'auke ta.

"Suhaima! Suhaima!! Ki tashi haka baccin ya isa "
Cewar Aunty Aliyah tana bubbuga k'afar ta, cikin nutsuwa take bud'e idanunta akan agogo ta d'ora eyes nata taga har 10:40 da sauri ta mik'e zaune daman haka lokaci yaja lallai tayi bacci mai nauyi.

"Aunty gaskiya nayi bacci mai nauyi haka lokaci yaja "

"Naji shirun yayi yawa har mun karya shine nazo duba ki ko lafiya?"

D'an murmishi tayi sannan tace
"Lafiya qlau Aunty kawai bacci ne "

"Kiyi sauri ki shirya kizo ki karya don ina son mu gama aiki da wuri zan fita suna da yamma "

"Laaa Aunty zan raka ki don Allah "
Cewar Suhaima cikin shagwa6a, 'yar dariya tayi kan tace
"Waiii rufa min asiri sai dai ki tambayi mijin ki tukunna "

Had'e fuska Suhaima tayi kan ta mik'e da sauri ta shige bathroom da kallo Aunty Aliyah ta bita kan ta girgiza kanta kawai fita tayi daga d'akin.

Agurguje Suhaima tayi wanka ta shirya cikin wata blue d'in jallabiya ire iren kayan da Yayan ta ya siya mata ne tunda bata taho da kaya ko d'aya ba, bata yi wani kwalliya ba wet lips ne sai powder kawai ta shafa duk da haka tayi kyau kuwa, d'an perfume ta shafa kan ta had'e gashinta da ribbon ta fito daga d'akin.

Hankalin ta akan hanyar zaure amman bata hango shi ba nan taji hankalin ta ya d'an tashi kaddai ya tafi, har tana yin tuntu6e saboda lek'e ashe Aunty Aliyah na kula da ita girgiza kanta tayi kawai tana murmishi don tasan Suhaima nason Sabeer haka shima yana sonta don haka zatayi bakin kok'arin ta wajen daidaita su.

"Lek'en me kike har kina yin tuntu6e "
Wani kunya ne ya kama Suhaima sai kawai ta sunkuyar da kanta tana shafa kai ta wuce kitchen don d'auko abin karyar ta tana cewa
"Ni babu abin da nake kallo fah Aunty "
Murmishi kawai Aunty Aliyah tayi, fitowa tayi daga kitchen ta zauna kusa da ita tana kok'arin zuba kunun tsamiya a cup tace

"Aunty ina Yaya ne? "
"Ya tafi makaranta yana da lecture d'in safe gashi zasu yi test ma "

Suhaima tana bud'e wani k'aramin flaks wanda kosai yake ciki tace
"Ayyah Allah ya taimaki Yayana "
"Amin "
Cewar Aliyah tana murmishi, kafin kuma tayi bismillah ta fara cin abincin cikin nutsuwa bayan ta gama ta wanke hannun ta tana kok'arin d'auke kayan da ta karya dasu don ta kaisu kitchen Aunty Aliyah tace

"Bar wannan aikin Suhaima ki rik'e min Ameer don kuwa sauri nake son yi "
Shagwa6e fuska Suhaima tayi kan ta ce
"Kaiii Aunty nima fah na iya wannan saurin gashi ke kadai kika had'a abin kari "

"Ni na isa na fad'i hakan ke dai zo ki rik'e min shi idan ba haka ba yana wannan rarrafen nashi zai hanani saurin aiki "

D'aukan Ameer tayi tana cillashi tare da cafe shi tana dariyar shima Ameer d'in dariyar yake mata da 'yan hak'oran shi, tana cikin haka ne taji tsayuwar mutum akanta da sauri ta d'ago kanta ido 4 tayi da Sabeer wanda yake tsaye ya hard'e hannun shi yana kallon ta cike da so da tarin sha'awarta don sosai ta birgeshi ji yake kamar ya kamota ya gudu da ita, d'auke kanta Suhaima tayi daga barin kallon shi ta cigaba da yiwa Ameer wasa amman jikinta ya bata har yanzu bai tafi ba kallonta yake lokaci d'aya taji wata kasala ta lullu6e ta har takai ta kasa d'aga Ameer sama sai kawai wasan da take mishi.

Fitowar Aunty Aliyah daga kitchen ne ya sanya shi katse kallonta, kallon shi Aliyah tayi kafin ta girgiza kanta ganin lokaci d'aya ya rame gashi kayan shi sunyi datti sosai tace

"Sabeer kana buk'atar wani abun ne? "

Cikin dashashshiyar muryar shi wadda mura tayi mishi mugun kamu yace
"Auntyn mu wanka nake son yi sannan ina son bak'in tea da lemon tsami aciki "

"To amman wannan murar taka ko chemist zaka je kada ta ssukar maka da zazza6i "

Cikin murmishin yak'e yace
"A'a basai naje ba zata warke "

"Anya kuwa Sabeer za'a yi haka kada fa ta baka matsala? "

"Auntyn mu kada ki damu zata warke nagode da kulawar ki, wadda ya kamata ta nuna damuwa akan ciwon bata damu ba sai ke don haka ki share zancen zuwa chemist "

Da sauri Suhaima ta d'ago kanta ta kalli shi har zata yi magana kuma sai kawai ta d'auke kanta tana murgud'a baki, duk abin da take yi akan idanun Sabeer, yayin da Aunty Aliyah tace

"Yanzu sai kayi wankan zaka sha tea d'in? "

"Eh "
Ya fad'i a takaice
"Ka shiga d'akin Suhaima akwai toilet aciki sai kayi wankan ka aciki "

Daga Suhaima har Sabeer da sauri suka d'aga kansu tare da kallon Aliyah, gid'a kanta tayi sanann tace
"Kada ka damu kaje kayi "

"Aunty amman...... "
Cewar Suhaima sai dai bata k'arasa fad'in abin da zata ce ba taja bakin ta tayi shiru ta had'e fuska.

"Aunty nayi kawai a wannan toilet d'in "

"A'a bazai yiwu ba, Suhaima kije ki had'a mishi ruwa nace idan har na isa na sanyaki abu kiyi "

Tashi Suhaima tayi tana 6a66ata rai zata wuce d'aki taji tana cewa
"Dawo ki d'ebi ruwan zafi tun da garin da d'an sanyi gashi yana fama da mura ".

Kitchen ta shiga ta d'ebo ruwan zafi ta wuce d'akin ta tana cika tana batsewa don me Aunty Aliyah zata ce yayi wanka a d'akin ta, ko ta mance da irin yanda ya koreta daga gidan shi ne.

"Auntyn mu 6atawa Baby nah rai fah? "
Ya fad'i hakan bayan wucewar Suhaima.

"Kyaleta Sabeer sakkowar Suhaima daga fushin da take da kai shi zai sanya Yayan ta ya huci daga d'aukan zafin da yayi maka, kai dai kayi kok'arin shawo kan Suhaima "

Gid'a kanshi yayi kan ya wuce zuwa zaure ya d'auko bag d'in kayan shi ya wuce d'akin Suhaima, yayin da Aunty Aliyah ta cigaba da aikinta bayan ta goya Ameer.

Yana shiga cikin d'akin wani k'amshi ne ya fara mishi sallama mai dad'i har sai da ya lumshe eyes nashi, tsayawa yayi yana kallon d'akin cike da sha'awar shi yayi mishi kyau duk da ba wasu kaya ne masu tsada ba sosai amman yanayin yanda aka tsara d'akin ne ya birge shi, daga gado, wardrobe sai dressing mirror k'asan kuma carpet ne sai kayan kallo gashi d'akin babba ne sai labulaye masu kyan tsari gadon nan an gyarashi sosai tamkar ba'a ta6a kwanciya akan shi ba.

Yana nan tsaye Suhaima ta fito daga toilet d'in ba tare da ta kalli inda yake ba ta fara kok'arin fita daga d'akin, hannun ta ya rik'o cikin sanyin murya yace

"Baby nah kiyi hak'uri please ki daina fushi da ni "

Bata ko kalle shi ba ta fara zame hannunta daga nashi sannan ta fice daga d'akin, da kallo ya bita kafin kuma ya nufi hanyar da ta fito ya shige toilet d'in.

Suhaima tana tsaye kusa da Aunty Aliyah tana mata mitar yanda ta sanya Sabeer shigar mata d'aki, yayin da Aunty Aliyah take murmishi kawai yaro yaro ne idan ban da haka yaci ace ta yafewa Sabeer don ita kanta Suhaima ya kamata ta baiwa Sabeer shaidar yanda yake nuna mata so da kulawa abu ne ya gifta a tsakanin su wanda mak'iyan su da basa son su gansu tare suka yi amfani da abin da Sabeer yafi so suka had'a makirci shi kuma laifin shi d'aya da ya biyewa zuciyar shi ya yanke hukunci cikin fushi sai dai kuma yayi kok'arin controlling din zuciyar shi tun da bai sake ta ba.

Sallamar da suka ji anyi ne ya sanya Suhaima da Aliyah zabura gaban su ya hau fad'uwa lokaci d'aya kafin su ankare ya shigo gidan, kallon su ya tsaya yi cikin mamaki ganin yanda suka zuba mishi ido kallo d'aya yayi musu yasan basu da gaskiya.

Tsarguwar da suka yi da yanda yake kallon su ne ya sanya su sakin murmishin yak'e tare da yi mishi sannu da zuwa, amsa musu yayi kawai yana sake bin su da kallon ban yarda daku ba.

Zuciyar Suhaima da ta Aliyah tamkar zasu faso kirjin su ta fito saboda yanda take bugawa sam basu yi tsammanin ganin Yah Aliyu yanzu ba sun sakankance sai da yamma, musamman Aunty Aliyah tafi kowa tsorata tayi dana sanin sanya Sabeer shiga cikin d'akin Suhaima yanzu idan ya fito daga d'akin batasan hukuncin da Aliyu zai d'auka ba akanta don itace da wannan shishshigin, gashi kafin ya fita sai da tasha gargad'i kada ta sake tsakanin Sabeer da Suhaima magana ta had'a su, nan ta fara addu'a Allah ya sanya kada Sabeer ya fito.

"Wai lafiyar ku qlau kuwa? "

Cikin sauri Aunty Aliyah tace
"Me kagani? "

"Gani nayi kunyi wani tsuru tsuru sai rarraba ido kuke kamar marasa gaskiya "

"A haba ba komai, lafiya ka dawo yanzu? "

"Nayi mantuwa ne "
Yana gama fad'in haka ya wuce d'akin su da sauri don kuwa sauri yake, bai dad'e ba ya fito daga d'akin ya fice daga gidan, sai lokacin suka saki ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali.

"Aunty kinga abin da nake tsoro koh da yanzu ya gane fah "

Aliyah wadda jikinta ya mutu saboda tsoro ta aro dauriya tace
"Kai dai Allah ya kiyaye kawai ba don haka ba da yau zanyi bayani don nice da laifi "

Suhaima dariya ce ta kubce mata ganin Aunty Aliyah na goge zufa tace
"Haba Aunty kinsan Yah Aliyu bazai iya ce miki komai ba sai dai kisha harara da mita "

"Ke kyale Yayan nan naki kawai idan ya fusata "

Cup d'in da ta had'a wa Sabeer tea ta mik'o mata tare da cewa
"Gashi ki kai mishi da zafin shi yasha kada ya huce gashi jiya fah bai samu cikakken bacci ba don nasan ruwan nan ya jik'a shi sosai "

D'an ta6e baki Suhaima tayi kan tace
"Allah Aunty kina son wanann guy d'in ya rainani da yawa bakisan haushin shi nake ji ba wallahi "

"Hakuri zakiyi Suhaima kinsan kowanne d'an adam da irin tashi k'addarar Allah ya riga ya tsara hakan sai ya faru tsakanin ku"

Kar6a tayi kawai ta tafi tana zum6ura baki Aunty Aliyah ta bita da kallo tana murmishi kawai.

Tana shiga d'akin ta ajiye cup d'in tea saman drower na gefen gado ta jiyo da niyyar fita daga d'akin taji an janyo hannun ta da d'an k'arfi wanda ya sanya d'an kwalin kanta mai santsi ya zame lallausa dogon gashin kanta ya tarwatse, bata tsaya ko'ina ba sai saman faffad'an kirjin shi har sai da d'an kanta ya bige kad'an, kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce mata kallon junan su kawai suka tsaya yi cikin wani irin shauk'i da tsananin kewar junan su............

Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻

*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*

Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ

ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ

♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*

*PAGE 106-107*

Kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce mata kallon junan su kawai suka tsaya yi cikin wani irin shauk'i da tsananin kewar junan su tare da wata irin zazzafar kauna, sun d'auki wajen 5 minute suna aikawa da junan su kallo yayin da Sabeer ya kasa jure kallon da suke aikawa junan su ya fara matsar da fuskar shi saitin fuskar ta da niyyar yayi kissing d'in cute pink lips nata wanda yayi tsananin missing d'in su a lot.

Jin saukar numfashin shi kusa da hancin ta sosai ya sanya Suhaima dawowa cikin hayyacin ta ta daddage ta fiske jikin ta daga jikinshi, sai dai yanda ta fisgi jikin nata ne ya sanya ta tafiya baya da d'an k'arfi kamar zata fad'i k'asa yayin da Sabeer wanda gaba d'aya kasala ta baibaye shi ya biyo ta shima.

Sauran kad'an Suhaima ta saki ihu na tsoro sai taji ta fad'a saman bed yayin da Sabeer ya biyo ta shima cikin jikinta, lokaci d'aya suka sauke wata ajiyar zuciya sai dai kowannen su da banbancin ajiyar zuciyar tasu Suhaima ita ta jin dad'in bata fad'i k'asa ba shi kuma Sabeer na jin shi rungume da Babyn shi a jikinshi wanda ya d'auke tsayin lokaci da su had'u kamar haka.

Kok'arin tashi take amman ya wani rik'e ta k'am kamar wanda za'a kwace mishi itaa haushi ne ya ishe Suhaima ta d'aure fuska cikin fusata tace

"Malam wai me kake nufi ne haka ni ka d'aga ni wallahi ko nayi maka ihu "

Murmishi Sabeer yayi kafin yace
"Haba Baby nah kinsan nayi missing d'in ki da yawa ki barni ko na samu kwanciyar hankali da nutsuwa cikin zuciya ta "

Haushi ne ya k'ule Suhaima don haka tace
"Kada ka mance da bakin ka kace min ka tsane ni me yasa zaka zo inda nake nima kasani na dad'e da tsanar ka tun lokacin da ka furta min haka "

Jikin Sabeer ne yayi wani irin sanyi wanda Suhaima har ta samu ta ture shi daga jikinta ta mik'e tare da d'aura d'an kwalin kanta ta wani kalle shi taja tsaki ta fice daga d'akin gaba d'aya.

Tana fitowa suka had'a ido da Aunty Aliyah da take zaune can gefen kitchen tana aiki, sake d'aure fuska Suhaima tayi don duk ita taja gashi ba don tayi kok'arin yakice shi ba da tuni ta bada kai bori ya hau, don haka ta samu waje ta zauna kawai ko kula Aliyah bata yi ba, sauran kad'an dariya ta kubce wa Aunty Aliyah amman ta danne ta kada ta janyo tayi mata kuka da rigima don kad'an daga aikin Suhaima don haka taja bakinta tayi tsit ta cigaba da aikinta.

Wani zafi da zugi ne yake ji cikin zuciyar shi kalaman Suhaima ne kawai suke fad'o mishi a rai da jan tsakin da tayi mishi don yaji ta ya dad'e kwance a haka yana tufka da warwara tare da yin d'unbin nadamar abin da yayi dakyar ya iya shiryawa cikin wani jeans blue da T-shirt fara mai k'aramin hannu ya d'an fesa perfumes kan ya zauna ya sha tea d'in da ya fara sanyi ma.

Yana gama sha ya mik'e ya d'auki kayan shi ya rik'e mai dattin a d'ayan hannun ya fito waje kallon Suhaima ya d'an yi kan ya kalli Aunty Aliyah yace

"Auntyn mu nagode bari na d'an fita waje ko zanga Ashiru don bamu had'u ba tun da nazo "

"Toh Sabeer sai ka dawo, amman ina zaka tafi da kayan nan masu datti haka a hannu? "

D'an murmishi yayi yana cewa
"Anjima zan wanke su ne zan ajiye su a inda nake kwana "

Tausayin Sabeer ne ya kama Aunty Aliyah tasan bai ta6a tsammanin zai yi irin wannan kwatankwacin rayuwa ko zuwan da yayi na farko baya yin wanki Yah Aliyu ne yake had'a wa ya wanke musu da nashi.

Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*

"Sabeer kabar shi Suhaima zata wanke maka "

"A'a Auntyn mu kada na wahalar da Mata ta "
Ya k'arasa maganar fuskar shi d'auke da murmishi wanda ya k'ara mishi kyau.

'Yar dariya Aunty Aliyah tayi kan tace
"Mata manya ni ai ban ta6a ganin matar da take gudun mijinta ba akan wani abu da ya faru bisa kuskure "

"Kaiii Auntyn mu kada mu yi haka da ke waya gaya miki tana gudun mijinta? "

Ya fad'i yana satar kallon Suhaima wanda ta cika tayi fam,
"Ai abin a fili yake K'anina "
Daga jin dai yanda Aunty Aliyah ke maganar kasan ta tsokana ce, sai akayi sa'a Suhaima bata tanka musu ba, ajiye kayan Sabeer yayi kusa da k'afar Suhaima kan yayi wa Aunty Aliyah sallama ya fita daga gidan.

"Allah Aunty ki daina yi min haka taya ina zaman hutawa na ki had'a ni da wanki don Allah "Cewar Suhaima cikin turo baki.

"Haba K'anwata bansan ki da fushi mai yawa ba ki d'auka ki wanke mishi na tabbatar Allah zai rubuta miki lada tunda da auren shi akan ki "
Cewar Aunty Aliyah cikin rarrashin Suhaima.

"Aunty kawai naga alama yanzu kin fi son shi da ni "

"Tabd'i kinsan dai Suhaima son da nake miki na daban shak'uwar mu da ke ma ba d'aya ce da ta Sabeer ba dukkanin ku matsayin k'annena ba don na girmi Sabeer ba, ina son ku had'a kanku da Sabeer ne da zarar Aliyu yaga haka duk fushin da yake dashi zai daina, Allah ya gani ina sonki da Sabeer wallahi gashi yana ban tausayi jiya da dare ji ruwa da aka tafka amman kusan akanshi ya k'are ga sanyin waje da duhu dalilin da ya tashi da mura kenan don tun da na tashi da asuba nake jin tarin shi da atishawa yana yi kuma duk wannan abun yana yi ne saboda A DALILIN SONKI Suhaima ya kamata kiyi tunani sosai kisan Sabeer masoyin ki ne na gaskiya "

Tana gama fad'in haka ta tashi ta wuce don cigaba da aikin ta yayin da tabar Suhaima cikin wani irin yanayi wanda lokaci d'aya ta fara jin haushin Sabeer yana raguwa cikin zuciyar ta.

Cikin sanyin jiki ta tashi ta fara wanke mishi kayan fes ta wanke su ta shanya saman igiya sannan tayi alwala ta tafi d'aki don yin sallah, bayan ta idar ne tana nan kwance saman abin sallahr Aunty Aliyah ta shigo cikin shirin tafiya suna tace

"Suhaima ni zan tafi idan Yayan ki da Sabeer sun dawo ga abinci nan a foodflaks ki zuba musu "

"Kaiii Aunty yanzu ki fasa tafiya dani? "

"Kiyi hak'uri Suhaima bazai yiwu mu tafi tare ba saboda baki tambayi mijin ki ba amman zan dawo da wuri kafin mangarib insha Allah "

"Toh Aunty adawo lafiya "

"Yawwa K'anwata haka nake son ji kin fad'a "

Tashi tayi suka fito har k'ofar zaure ta rakata ta tafi sannan ta rufe gidan ta wuce ta zuwa d'akin ta, kwanciya tayi kawai maganganun Aunty Aliyah ne suke dawo mata, da taga tunanin ba mai k'arewa bane ya sanya ta tashi taje ta had'a wuta a dutsen guga ta zauna ta gogewa Sabeer kayan shi tsaf ta d'auke su taje ta ajiye mishi saman jakar shi.

Tana zama kenan taji ana

Please Login or Register in order to submit comment