Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai Aliyu da Suhaima suka yi lokaci d'aya, kafin Aliyu ya iya cewa
"Babaa Lantana kiyi hak'uri ki bar mu a wurin Innar mu "
Itama girgiza kai tayi tare da cewa
"A'a Aliyu kayi hak'uri ku je waje "
Dakyar Babaa Lantana ta shawo kan Aliyu ya kama hannun Suhaima suka fita waje, suna waiwaiyar Innar su, da batasan halin da take ciki don ta fara fita a hayyacin ta.


Bayan fitar su ne Babaa Lantana ta fara yiwa Fatima dabarin su irin na zamanin da, ganin abin yana kok'arin gagarar ta ne ya sanya ta fito waje inda Aliyu suke raku6e waje d'aya, kallon su tayi wani tausayin su ne ya kamata dakyar ta iya cewa
"Aliyu kayi sauri kaje ka kirawo Ladi ungozoma "
Gid'a kanshi yayi sannan ya fita da gudu, ita kuma Babaa Lantana ta koma cikin d'akin wajen Fatima, ta bar Suhaima anan zaune tana kuka.


Babu dad'e wa Aliyu ya dawo Ladi ungozoma tana bin shi a baya, d'akin da Fatima take ciki ya iya nuna mata da d'an yatsan shi, Ladi ungozoma kuwa wadda ke d'auke da k'aramin buhu a hannun ta na kayan aikin ungomanci irin na zamanin da, ta shige cikin d'akin.


Duk yanda suka yi kok'ari wajen kada cikin Fatima ya zube, sai da cikin ya zube sai dai jini yak'i tsayawa sai zuba yake, nan dai ungozoma ta bayar da maganin da za'a jik'a mata ta sha, sannan Babaa Lantana ta biya ta kud'in ta, ta had'a kayan nata ta tafi.


Babaa Lantana sai da ta gyara jikin Fatima tsaf da d'akin, sannan ta kirawo Aliyu da Suhaima don su zo wajen ta, sannan ta tafi gida don d'ebowa Fatima abinci don ba k'aramin gala6aita tayi ba sosai, tun da ba wani abincin kirki take samu ta ci ba, da sannu Allah zai saka ita da yaran ta a wajen Umaru, tabbas yaci amana bai rik'e amanar da Allah ya bashi ba ya azabtar da su, duk don son rai irin shi nashi.


Suna shiga d'akin wajen Fatima suka nufa, zama suka yi a gefen ta gaba d'aya sun zuba mata suna kallon ta tamkar yau suka fara ganin ta.


Kallo d'aya mutum zai mata yasan bata da ishashshan jini a cikin jikin ta, saboda yanda tayi wani fari sosai, gashi ta rame sosai dakyar take iya motsi ma, kallon yaran nata tayu tana daga kwance, wani tausayin sune ya kamata, a hankali wasu hawaye suka shiga zubowa daga idanun ta, bud'e bakin ta tayi wanda ya bushe saman le6en yayi fari tace
"Aliyu ga Suhaima nan koda na mutu ka rik'e ta cikin amana, ina horan ka da ka tsaya tsayin daka ku nemi ilimi, don zama da jahilci bashi da amfani, sannan kada ku ce zaku ji haushin mahaifin ku, ku cigaba da yi mishi biyayya koda ya dawo wajen ku, ku kasance cikin yi mishi addu'a Allah yasa ya gane gaskiya, yasan 'ya'ya rahma ne, komai runtsi ina son ka kasance da Suhaima kada ka guje ta, duk laifin da tayi maka kayi hak'uri kai babba ne "


D'an dakatawa tayi ta had'iyi yawu sannan ta d'an yamutsa fuska saboda jin yanda marar ta take wani murd'awa wa, cikin kuka Aliyu ya kamo hannun ta yace
"A'a Inna baza ki mutu ba, zamu rayu tare da junan mu, don Allah ki daina wannan maganar Inna, hankali na yana tashi wani tunani yana d'arsuwa a zuciya ta sannan gaba na yana fad'uwa "


Wani d'an murmishi Fatima tayi tare da cewa
"Kayi hak'uri d'ana ni kaina bansan dalilin yi maka wad'annan maganganun ba, ina son duk lokacin da mahaifin ku ya dawo ku sanar dashi na yafe mishi duk abin da yayi min, nima kuma ya yafe ni idan nayi mishi wani laifin a zaman mu, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya raya min ku ya baku ilimi mai amfani ya kuma kare min ku a duk inda kuke 'ya'yana, ku rik'e Babaa Lantana da Baba Adamu a mataayin iyayen ku, don mutanen kirki ne kuma zasu rik'e ku tamkar Aliya 'yar su, duk abin da suka baku shawara kuyi amfani da ita don nasan baza su baku mummunan shawara ba Allah yayi muku albarka "


Fatima ta k'arasa fad'in haka tana hawaye sosai, nana Aliyu da Suhaima suka sake fashe wa da kuka sosai, ana cikin Babaa Lantana ta shigo d'akin turus taja ta tsaya ganin su da tayi suna kuka, jikin ta ne yayi sanyi sannn wasu hawaye na tausayin su ya zubo mata, wayance wa tayi tare da fakar idon su don kada su ganta ta goge nata hawayen sannan ta k'arasa inda suke tace
"Haba Fatima taya zaki na saka su a gaba kina kuka suna yi, ke da zaki rarrashe su ki kwantar musu da hankali "
Murmishin yak'e kawai Fatima tayi, nan Babaa Lantana ta rarrashe su dakyar suka yi shiru, sannan ta basu abincin suka fara ci hannu baka hannu kwarya.


Sannan ta d'ago Fatima a hankali ta kara mata kofin madarar shanu mai d'umi a bakin ta, a hankali Fatima take kur6a har ta gama shan kusan rabin kofin, sannan ta zame bakin ta a bakin kofin tana girgiza wa Babaa Lantana kai alamar ya ishe ta.


Sauke kofin tayi a k'asa ta ajiye, tukunna ta d'auko kofin maganin da aka jik'a ta bawa Fatima tasha, bayan ta gama ta kwanta tana mai mayar da ajiyar zuciya, ita kad'ai tasan abin da take ji cikin jikin ta.


Babu dad'e wa bacci ya d'auke ta, fito wa suka yi zuwa tsakar gidan gaba d'ayan su don kada ayi hayaniya ta tashi, Babaa Lantana da Suhaima suka fara kimtsa gidan da yake Fatima bata sangartar da ita ba, tana d'an sata aikace aikacen da zata iya wanda baifi k'arfin ta.


Aliyu kuwa fita yayi a gidan don zuwa neman wani aikin da zai siyo wa Inna lemo da kankana don tasha, tun da yasan mara lafiya yafi son cin kayan itatuwa fiye da komai.


Babaa Lantana tana wanke wanke ne Aliya d'iyar ta ta shigo gidan, nan ta kar6i aikin da Babaa Lantana take yi ta cigaba da yi, gefe d'aya Suhaima nayi mata dauraya.


Lokacin da Farima ta farka daga baccin jikin ta da d'an dama don ta iya tashi taje band'aki da kanta, sai dai har zuwa lokacin jini yana zuba a jikin ta, amman ba mai yawa sosai ba, sai bayan ishsha Babaa Lantana ta tafi gida, ta bar Aliya anan wurin Fatima ko zata na taimaka mata da wani abin a yafi k'arfin Suhaima.


Bayan tafiyar kenan Aliyu ya dawo gidan da yankan kankana a hannun shi k'arami sai lemo mai 6ayo guda biyu, dakyar ya same su bayan yasha wahalar ferar lemo mai tarin uban yawa da mai siyar da lemon ya bashi, sannan ya bashi wannan kankanar da lemon tare da nera ashirin, cikin farinciki ya taho gida.




Bayan ya shigo gidan duk suna d'aki don haka ya shiga kitchen ya d'auko silver da wuk'a ya yanka su k'anana sannan ya shiga d'akin da sallama, Fatima, Aliya da Suhaima suka yi amsa mishi, da sauri Suhaima ta mik'e tana rik'e shi cikin shagwa6a tace
"Yaya shine kayi zaman ka ina ta jiran ka, kasan bana son ka fita ka dad'e "
D'an murmishin yak'e yayi tare da shafa kanta yace
"Yi hak'uri 'yar k'anwa ta aiki ne ya tsare ni "
"Toh Yaya na "
Fatima kallon su take kawai, kafin wasu hawaye su zubo mata, da sauri ta sanya hannun ta, ta goge su don kada su Aliyu su gani, don ma babu wadataccen haske a d'akin.


K'arasa wa yayi inda take ya zauna tare da mik'a mata silver d'in yace
"Inna gashi kisha, ya sauk'in jikin naki? "
"Da sauk'i Aliyu nah, nagode Allah yayi muku ya albarka "
"Amin Inna"
Aliyu ya amsa, nan ya fara bata a baki a hankali, bayan ya d'an sanwa Suhaima don Aliya k'in kar6a tayi.


A hankali yake bata har ta shanye tas, sannan ya d'auke silver d'in ya bawa Aliya takai kitchen, shi kuma ya fara jera wa Fatima tambaya akan yanda take jin jikin nata, Fatima kuwa amsa mishi kawai take da sauk'i, har zuwa lokacin kwanciya bacci, har ya tafi Fatima ta kirawo shi tana dad'a yi mishi nasiha tare da k'ara bashi amanar ya kula da kanshi da Suhaima, jiki a sanyaye Aliyu ya fito ya shige d'akin shi.


Can cikin dare wajen asuba ne jini ya tsinke wa Fatima kafin kace me tuni ta fara fita daga hayyacin ta, aikuwa Suhaima da gudu ta shiga d'akin Aliyu ta taso shiga, daman ba baccin yake ba, don gaba d'aya ji yayi baya jin bacci a idanun shi, ganin Suhaima tana kuka ba k'aramin d'aga mishi hankali yayi ba, ko tambayar ta bai tsaya yi ba ya fito daga d'akin nashi ya fad'a d'akin Fatima.


Yana shiga yaga abin da ya gigita shi, ya rud'u iya rud'ewa kamar wani babban mutum, da sauri ya k'arasa wajen Inna Fatima ya rik'e ta yana fashe wa da kuka yace
"Inna don Allah kada ki tafi ki bar mu, ki bud'e idanun ki "
Ya fad'i hakan ganin yanda take lumshe ido tana jan numfashi da dakyar, gashi ta kasa magana sai kok'arin bud'e baki take tayi magana ta kasa bud'e shi, kallon Aliyu kawai take da Suhaima.


"Yaya Aliyu ka kirawo Babaa mana "
Yaji saukar muryar Aliya a kanshi, sai lokacin ya tuna hakan, aikuwa ya ajiye Inna a hankali ya fita da wani irin gudu.


Fatima bin shi da kallo tayi Sannan ta mayar da kallon ta kan Suhaima, sai kuma a hankali ta bud'e bakin ta zata yiwa Suhaima magana, amman sai kawai taji ta tsinci bakin ta da furta kalmar shahada, a hankali ta k'arasa fad'a sannan Lokacin d'aya kuma numfashin ta ya tsaya da aiki, idanun ta kuma a lumshe suke har zuwa lokacin da zuciyar ta tabar bugawa komai na jikin ta ya tsaya cak da aiki ya daina motsi, ta koma tamkar wadda ta mutu ko irin ta suman nan.


Da iyakacin k'arfin shi yake bugun gidan Babaa Lantana yana d'aga murya da k'arfi yana kiran Babaa Lantana da Baba Adamu, sam kamar Aliyu baya cikin hayyacin shi yama mance da wani dare ne Saboda tsabar rud'ewa.


Da sauri Babaa Lantana da Baba Adamu suka fara rige rigen bud'e kofa, jin muryar Aliyu, Baba Adamu ne yayi nasarar bud'e kofar saboda Babaa Lantana zaninin jikin ta da kunce yana kok'arin sullu6e wa k'asa.


And rikice Aliyu ya rik'e hannun Baba Adamu yana cewa
"Ku taimaka min Inna ta "
Abin da ya iya furta kenan, aikuwa tsakanin Babaa Lantana da Baba Adamu tare da Aliyu suka kasa tsere don shiga gidan.


D'akin Fatima suka fad'a dukanin su, kallo d'aya Baba Adamu yayi wa Fatima yasan bata numfashi, ganin haka ya sanya korar Aliyu, Aliya da Suhaima daga d'akin.


Suna fita Baba Adamu ya kalli Babaa Lantana ido jawur yace
"Sai dai mu yi hak'uri Lantana Fatima ta rigamu gidan gaskiya "
Hannu Babaa Lantana ta sanya a kanta dukka hannun tare da zaro ido tace
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Malam da gaske Fatima ta mutu ko suma tayi ne "


Cikin dauriya Baba Adamu yace
"Haba Lantana ki kalle ta da kyau, ai kina kallon Fatima kinsan gawa ce "


Lokaci d'aya Babaa Lantana ta rushe da kuka sosai, yayin da Baba Adamu ya sanya zani ya lullu6e ta tun daga saman kanta har k'afar ta, Sannan ya kamo hannun Babaa Lantana suka fito waje tsakar gida, ina Suhaima da Aliyah suka yi tsuru tsuru suna kuka, yayin da Aliyu ya kasa zama waje d'aya sai safa da marwa yake yi.


Ganin fitowar Babaa Lantana da Baba Adamu jikin su a sanyaye ga Babaa Lantana tana kuka, yasa Aliyu tahowa wajen su da sauri yana cewa
"Ku fad'a min meke faruwa, ina Inna ta, kada ku ce min ta mutu don Allah "
Babu wanda yayi karfin halin yi mishi magana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai d'akin Lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai......


Sai kun yi hak'uri da wannan page d'in banyi editing ba.




Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝


Written by
Aishat A Muh'd


♻£xclusive Writer's Forum


Dedicated to my Sadeey SaNaz




PAGE 7-8








Babu wanda yayi k'arfin halin yi mishi magana a tsakanin Baba Adamu tare da Babaa Lantana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai cikin d'akin, lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai.




Aliyu yana sanya k'afar shi cikin d'akin idanun shi suka hango mishi Umman shi kwance an lullu6e da zani, da sauri ya k'arasa wajen gaban shi na tsananta fad'uwa, hannun shi na rawa ya sanya akan zanin ya fara janye shi a hankali, fuskar Fatima ce ta bayyana kamar an kirata ta amsa, sai kace ba matacciya ba, tuni Aliyu ya durkushe tare da sakin wani irin kuka yana cewa
"Umma ki tashi don Allah kada ki tafi ki barmu a wannan duniyar mu kad'ai"


Kuka sosai Aliyu yake yana sumbatu, ganin haka ya sanya Baba Adamu ya janye shi daga gaban gawar Fatima dakyar don shima hawayen yake yi, Babaa Lantana kuwa da Aliyah Suhaima kuka suke yi sosai.


Daga k'arshe Baba Adamu ya fita don sanar wa da jama'ar gari, cikin k'ank'anin lokaci mutuwar Fatima baiwar Allah ta zagaye cikin k'auyen nasu, sosai mutane sun jimanta rasuwar ta tare da yaba kyawawan halayen ta, da irin yanda take hak'uri da jure irin rashin mutunci irin na mijin ta wanda sam kanshi ya sani.


Babu jimawa mutane suka taru akayi wa Fatima wanka aka had'a ta cikin likkafani, sannan daga k'arshe aka sadata da gidan ta na gaskiya, gidan da shi muke jira Allah ya jik'an wad'anda suka mutu mu kuma Allah yasa mu cika da imani Amin.


Aliyu da Suhaima sun sha kuka kuwa, musamman Aliyu don yafi Suhaima hankali sai yafi jin rad'ad'in mutuwar fiye da ita, su Baba Adamu da Babaa Lantana ne suke tausar su tare da yi musu nasihar yarda da k'addara, lokacin Fatima ne yayi don haka Allah ya d'auki abarshi, kowanne mutum da iyakacin lokacin da Allah ya d'ibar mishi yanzu Fatima addu'a tafi buk'ata fiye da komai, Allah yasa mu dace duniya da lahira Amin.


Haka Aliyu da Suhaima suka rungume maraicin su, sun koma abin tausayi, bayan sadakar bakwai ne 'yan uwan Fatima suka nemi tafiya da Suhaima shi kuma Aliyu ya zauna a wajen 'yan uwan uban shi, amman k'ememe Aliyu ya yak'i yarda da tafiya da Suhaima, anyi rarrashin sunyi fad'an amman ina yak'i aminta dole suka damk'a amanar su hannun Babaa Lantana da Baba Adamu, tukunna suka tafi bayan su bawa Aliyu wani d'an taimakon da zai nemi wata sana'ar ta domin kula da kansu.




Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda Aliyu da Suhaima suka sake shak'uwa da junan su, komai Aliyu ya samu zaka ji bakin shi na ambatar Suhaima, kulawa sosai yake bata don shi yafi tausayin ta fiye da kanshi, sai dai ita Suhaima ta koma gidan Babaa Lantana da zama sai dai tana shigowa wajen Yayan nata tana tayashi 'yar hira.


Aliyu ya dage da yin sana'a kowacce iri ce indai zai samu halal d'in shi, aiki yake yi sosai na k'arfi kuma, haka ya dunga tara kud'i har ya sanya Suhaima a makarantar primary tana nan cikin k'auyen nasu tare da islamiya, babu dad'e wa Suhaima ta fara zuwa makaranta hankali kwance, kullum shi zai kai ta a tsohon keken da Baba Adamu ya cika mishi kud'i ya siya, haka idan aka taso su zai zo ya d'auke ta.


Ganin Aliyu ya fi karkata akan son yin noma da kiwo yasa Baba Adamu bashi aron gonar shi guda d'aya don yana yin amfani da ita, shi kuma ya rik'e guda d'aya, da yake gonakin nashi guda biyu ne manya, gashi gonar da ya bawa Aliyu aro a kusa da gidan su Aliyun take, idan ma mutum bai kula ba ya d'auka kamar gidan a tsakiyar gonar yake, sosai Aliyu yayi murna da wannan karamcin da Baba Adamu yayi mishi.


**** **** ****
Haka lokaci ya cigaba da tafiya watanni da shekaru na wuce wa kamar kiftawar ido, Suhaima an fara zama 'yammata an don har ta kammala makarantar primary sun zana commen interest tana gida ana jiran fitowar result sai makarantar islamiyya da take cigaba da zuwa.


Yayin da Aliyu an zama matashin saurayi, ya zama cikakken manomi a yanzu, don ya rik'e sana'ar noma da kiwo, da wannan gonar da Baba Adamu ya bashi aro yake noman shi and cikin ta har zuwa yanzu da ta zama mallakin shi, don tuni Baba Adamu ya siyar mishi da ita, bayan aikin noma kuma yana yin kiwo irin su kaji, awakai da shanu sai kuma yana siyar da kwan kaji sosai yake samu bud'i a harkar shi, ga taimakawar wani amintaccen yaron shi da Baba Adamu ya sama mishi yana taimaka mishi.


Ya gyara gidan su sosai yayi kyau, inda a lokacin kuma Baba Adamu ya nemi da yayi aure, babu 6ata lokaci ya sanar musu da Aliyah d'iyar shi yake sosai, babu wanda bai yi farinciki da hakan ba don haka babu 6ata Lokaci akayi aure amarya ta tare a gidan ta, nan kusa da gidan su tun da Aliyu a asalin gidan su ya zauna, a lokacin kuma Suhaima ta dawo hannun Yayan ta da zama, zaman su suke cikin kwanciyar hankali da farinciki, Aliyu ya mayar da hankalin shi sosai kan sana'ar tashi, ya dad'a zama wani babban mutum musamm da yanzu yayi aure.


Kamar yau ne ranar laraba ranar da kasuwar garin nasu take ci, tun safe Aliyu ya bar k'auyen nasu ya tafi cikin birni kai wasu kwai masu yawa, wajen mutumin da yake kaiwa ya siya a kan machine d'in shi, don haka gidan ya rage daga Aliyah sai Suhaima a ciki.


Ranar Suhaima cikin farinciki take saboda Yayan ta baya nan, zata je cin kasuwa don haka da wuri tayi wanka ta ci gayun ta cikin wata atampa mai kalar milk da brown a jiki, ta sanya hijab d'in ta k'arami kalar brown, sannan ta fito daga d'akin ta zuwa wajen da Aliyah take.


Aliyah tana zaune tana gyaran kayan miya don tana son gama girki da wuri kafin Aliyu ya dawo, ta hango Suhaima tana tahowa zuwa wajen ta, fuskar ta d'auke da murmishi tace
" Suhaima wannan gayun fa ina zuwa? "
Cikin dariya Suhaima tace
"Yaya Aliyah nayi kyau ne?"
Itama Aliyah tana dariya tace
"Sosai ma 'yar k'anwata kinyi kyau, ina zuwa? "
"Cin kasuwa zan je "
Zaro ido Aliyah tayi tare da cewa
"Haba Suhaima kin mance Yayan ki baya son kina zuwa koh, yanzu idan ya dawo bakyanan nasan fad'a zai mana ni da ke "
Shagwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa
"Haba Yayah Aliyah kafin ya dawo fah na dawo, ba dad'e wa zanyi ba "
"Toh shikenan amman don Allah kada ki dad'e "
"Yawwa Yayah Aliyah nagode, kuma bazan dad'e ba "
Murmishi suka yiwa junan su, sannan Aliyah ta d'auko kud'i ta bata, godiya tayi tukunna ta tafi cikin zuciyar ta fal farinciki.


Tana fita waje ta tarar da k'awayen ta suna jiran ta, nan suka tafi kasuwar suna tarar ana tacin kasuwa ga mutane daban daban har da na maraya ma suna zuwa cin kasuwar.




Suhaima bata dad'e ba tace wa k'awayen ta zata tafi gida, don kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata dawo ba yayi mata fad'a, aikuwa suka ce sai dai tayi gaba su ba yanzu ba, haka Suhaima ta kamo hanya tana tafiya ita kad'ai cikin sauri.


Sauri sauri take gaba d'aya hankalin ta yayi gida, tana tsoron kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata nan.


D'ago kan da zatayi ta hango wata kyakkyawar yarinya a tsaye kusan sa'ar ta, sai dai zata ba Suhaima wajen shekara biyu, sai wani dattijo a tsaye shima a gefen ta a tsaye da alama sun k'agu da tsayuwar da suka yi.


A hankali Suhaima ta k'arasa inda suke tsaye har zata wuce su, da sauri yarinyar nan ta k'arasa wurin Suhaima tace
" 'yar uwa idan baza ki damu ba don Allah muna son ki taimaka mana da ruwa zamu sanya a mota "


D'ago kanta Suhaima tayi ta kalle ta sannan tace
"Toh ba matsala bari na k'arasa gida na d'ebo muku"
Murmishi yarinyar tayi tare da cewa
"Idan baza ki damu ba zan bi ki don na gaji da tsayuwar "
"Ba komai mu je "
"Ngde 'yar uwa "


Kallon dattijon nan tayi tare da cewa
"Malam Habu bari mu je gidan su mu kawo ruwan "
Sai da dattijon nan da yarinyar ta kirawo da Malam Habu yayi d'an jim kad'an kafin yace
"Toh amman kada ki dad'e kinga kada yamma tayi mana a hanya "
Gid'a kanta tayi sannan ta juya wajen Suhaima tace
"Mu tafi koh? "


A nutse suka fara tafiya yarinyar tana yiwa Suhaima hira sai dai bata fiye bata amsa ba daga ehh sai a'a, can sai kuma tace
"Ni sunana Hauwaa amman 'yan gidan mu na kirana da Jiddah saboda sunan kakar mu ne "
Murmishi Suhaima tayi tare da cewa
"Sunan ki mai dad'i "
"thank you, ke fah what's your name? "
"My name is Suhaima Umar"
"Wow nice name, daman kina jin turaci? "
"Yeah but kad'an kad'an."
"Good, kin gama primary ne "
"Ehh na gama ina jiran result ya fito na cigaba "
"Amman kin birge ni Suhaima, zamu iya zama friends? "
"Why not "
Cewar Suhaima, nan kowacce ta bada d'an yatsan ta suka k'ulla friendship, tukunna suka k'arasa shiga gidan da sallama.


Gaban Suhaima ne ya fad'i ganin Yaya Aliyu a tsaye yana safa da marwa, ga Yaya Aliyah ma a tsaye fuskar ta d'auke da damuwa da alama dai ita ake nema.


Suna ganin ta gaba d'aya sukayo inda take Aliyu ya sanya hannun shi saman kafad'ar ta ya rik'e da d'an k'arfi yace
"Ina kika zauna Suhaima, ba na hana ki fita kasuwa ba "
Idanun tane yayi raurau kamar zata yi kuka, batason ganin damuwar Yayan nata ko kad'an, don haka sai tace
"Kayi hak'uri Yaya bazan sake ba "
Kallon ta kawai yake bayason wani abu ya samu tilon k'anwar tashi.
"I'm so sorry Yayah bazata sake ba "
Aliyu da Aliyah suka ji saukar muryar Jiddah, da sauri suka kallo inda take don sam basu kula da ita ba hankalin su gaba d'aya yana kan Suhaima.


Kallon Suhaima Aliyu yayi irin na neman k'arin bayanin ina ta samu wannan yarinyar, fahimtar hakan da Suhaima tayi ne ya sanya ta bud'e baki tayi mishi bayanin had'uwar su.


Ba wanda yayi magana sai da Jiddah ta gaida su sannan suka amsa, kallo d'aya zaka yiwa Jiddah kasan ta samu tarbiyya mai kyau a wajen manyanta.


Babu 6ata lokaci Aliyu ya samu jarka ya zuba ruwa taf a ciki, sannan ya d'auko ta Suhaima da Jiddah na bin shi a baya har zuwa wajen da motar su tayi parking.


Bayan sun k'arasa ne Aiyu suka gaisa da Malam Habu sannan ya kar6i ruwan ya zuba a mota yana godiya, mik'a wa Aliyu jarkar ruwan yayi yana sake godiya, girgiza kai Aliyu yayi tare da cewa
"A'a ka barshi a wurin ka idan buk'atar hakan ya taso muku a gaba kwayi amfani dashi "
Malam Habu cikin girmama karamcin Aliyu yace
"Mun gode d'an samari Allah ya saka da alkhairi "


Daga haka Malam Habu ya shiga cikin mota yayi mata key ya tasar da ita, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Jiddah da bata da alamun shigo wa motar yace
"Jiddah taho mu tafi yamma nayi "
Maimakon ta bawa Malam Habu amsa, sai ta juya wajen Aiyu ta rik'e hannayen shi duk biyun tace
"Don Allah Yaya Aliyu zan na zuwa nan ganin Suhaima, Allah tun da na ganta naji ina sonta sosai, gashi mun k'ulla k'awance da ita, kuma ina son ka zama Yaya nah "
D'an murmishi Aliyu yayi shi duk wanda yake k'aunar 'yar k'anwar shi, to shima yana

Please Login or Register in order to submit comment