Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

dani. Tace, ba zaka bari kadan qara samun sauqi ba? Yace, karki damu, can ma zanci gaba da ganin likita. Shida daidai suka sauka a filin jirgin sama. Sun samu direba na jiransu, domin kafin su taso daga Abuja, Alhaji yasa Abba ya kira direban hajiya sauda, batasan da zuwan Alhajin ba tana zaune a falo tana ba Zainab magani, don yau kwananta uku babu lfy, kullum suna hanyar asibiti. Sai kurum taji Sallamar su. Bata zaci Alhaji bane, don muryar Abba irin ta Alhajin ce. Saida taji yaran suna Oyoyo daddy. Da sauri dago tace, sannu da zuwa Alhaji. Ta miqe cikin sauri bayan ta kwantar da Zainab, tace, Alhaji baka sanar dani cewa kana tafe ba. Yace karki damu tu tunda mun iso lfy. Sun gaisa da Abba sannan ya nufi gidansa.
Canjin rayuwa

9�6⃣Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki. Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti. Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan sha. Tace, a'a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa. Ya tsura mata ido, "sauda nayi miki laifi ko? Ta kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi. Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai ta6a son wani cikin 'ya'yansa kamarta ba. Amma dole ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa. Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share hawayen sa, saida tace "na shiga ukuna! Alhaji kukan me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani babban al'amari.9�7⃣Ta kama hannunsa. "Na roqeka karka 6oyemin komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa hannunta, "sauda karki tada hankalinki ba wani abu bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan cewa, na sa6a miki da yawa. "qara firgita tayi, gani takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, "sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani. Tunda munyi sallar isha'i, sai inje in sallami yara na inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin plate, tasa a gabansa. "in baka a baki?" yadan karkatar da kai, "bana tuna shekaru na matsawar ina gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.9�8⃣Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam. Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano maganar Mimi ce damuwarsa. Batun 'yan uwanta ta dauko masa na auren 'ya'yan sa'ade 'yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu. Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai. "sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai yarda ba shiyasa na haqura.
Ya qura mata ido na 'yan kakwanni. Ta shafi kumatunsa, "wai wannan kallon fa? Yace, karki tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. "wlh tsoron kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya. "sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a'a sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin 'ya'yanki su samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin samun tarbiyyarki. Ma'anar in na mutu kuyi farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane.

9�9⃣Hajiya sauda, cikin mamaki tace, kana da wani hali ne na daban? Domin in da za'a tambayeni halinka, zan bada shedar cewa, kai mutum ne na gari. Yace, "sauda kowane dan Adam ajizi ne, in dai ba ma'asumi bane. Harkoki na sunsa bana samun yin sallah akan lokacin ta. Harkokina sunsa 'ya'ya na basu samu soyayyata ba. Harkokina sunsa 'yan uwa maqota ban basu nasu haqqinba. Shawararki da nayi ta guje mawa ynxun na gano itace mafita. Zan aje tunani na na kullum, wato maida Naira ta zama Dala, ko ko taro ya zama sisi. Ta kamashi, tashi ka koma kan gado, bari in kwashe kwanukannan, in kuma tabbatar da yarana suna cikin makwancinsu. Ya miqe tare da komawa kan gadon. To karki jima maman yara. "Bayan fitowar ta ne ta tsaya bakin qofar, sannan ta daga hannunta sama, "Alhmdlh, ya Allah ka qara sa mijina akan hanya madaidaiciya.
Kamar kullum daga dakin su Abdullahi ta soma har zuwa dakin su Zainab dasu Hasina. Nan ta dan 6ata lokaci don sai da taba Zainabu magani sannan ta fito. Zata shiga dakin su usaina saiga su sun fito. Tace, ina zakuje? Suka ce munason mu sake yiwa daddy sannu da zuwa, sannan muga jikinsa ne. Tace, to kuje yana ciki, ina zuwa nima. Dakinta ta shige don ta dan sake kintsawa cikin kayan varci. Su Hasana suka shiga dakin daddyn su bayan sunyi sallama, ya kuma basu izini. A hannun kujera suka zauna suka gaida gaida shi tare da sake tambayar jikin sa. Ya tashi zaune daga kishingidar da yayi. "kuzo nan yarana! Suka kalli juna cikin mamaki, sannan suka nufeshi. Ya ce, ku zauna bakin gado kyawawan 'yan biyu na. Suka zauna. Ya dora hannunsa akan kafadar ko waccensu. 'Yan biyu kuma fa kun girma, masha Allahu. Hajiyarku tace min zakuyi jamb da Waec ko? Suka sake kallon juna, sannan sukace "eh daddy mun kusa mu fara. Yace, to Allah ya baku sa'a. Suka ce Ameen.
1�0�0⃣Ya sake cewa, me kuke karantawa ne? Ina nufin Art ko science? Usaina ta kalleshi "'Hassana ce take science class, ni Art nike. Yace, Hassana zamu doctor kenan? Ta kalleshi cikin Jindadi tace, eh daddy inason in zama medical doctor. Yace, Usaina fa? Tace, daddy nikam 'yar jarida nakeso in zama, ina sha'awar haka, shiyasa mass com zan karanta. Cikin farin ciki yace, nagode ma Allah. Allah ya cika muku burinku yara na. Daidai lokacin Hajiya sauda ta turo ta shigo da sallama. Ta kallesu da fara'a " 'yan biyu azo aje ayi varci ko? Suka miqe, sannan suka sake cewa, daddy Allah ya baka lfy. Yace, Ameen nagode. Suka ce, Hajiya saida safe. Tace, mu kwana lfy karku manta da Addu'a. Suka ce, to. Ta zauna tana kallon fuskarsa, "sun dameka da surutunsu ko? Yace, inason su saki jikinsu dani. Tace, ya kamata kam. Yace, "ynxun wace shawara zaki bani? Ta kalleshi "tame? Maganar da nayi miki dazun, ta damqa harkoki na ahannun yara, kamar yadda kike ta bani shawara tuntuni. Tace, ynxun kwanta kasha magani fa, in ka samu varci, gobe idan Allah ya kaimu, sai muyi maganar ko? Ya kwanta tare da cewa, Allah ya kaimu. Itama ta kwanto masa, tare da kashe fitilar dakin.
Alhaji Bashir ya jima bai samu varci kamar na yau ba. Yaji dadin jikinsa daya farka, har masallaci yaje. Sannan da gari ya dan yi haske, sai yace, ki fitomin da kayan motsa jikina, zan dan fita. Likita yace, in dinga motsa jiki sosai, zufar da zan fitar tana fita da cutar.
Canjin rayuwa

1�0�1⃣Hajiya sauda tace, tunda yarannan suna hutu, to ka fita dasu Abdullahi mana da Sadiq da Ameen da Umar. Take ya yarda sbd ynxun kam burinsa bai dara kusantar duk 'ya'yan nasa ba. Suka fito cikin kayan motsa jiki. Yaran sun sa gajeran wando da riga mai gajeran hannu, yayin da uban yasa mai dogon hannu da kuma dogon wando. Yaran cikin murna, domin suna son fita motsa jiki sosai, Hajiya ce take hanasu, wai tace, batasan da wadanne irin abokai zasu hadu ba in sun tafi can gurin motsa jikin. Alhaji ya dube ta, "sai mun dawo." Cikin salon tsokana tace, "to Alhajina. "Ta kalli Abdullahi, "Yarana masu albarka, ku lura min da mijina. Gaba daya suka sa dariya. Tace, da gske nakeyi Abdullahi, kar yayi gudu, tafiya kawai zakuyi. Suka ce "To" suka jera suka fita, biyu nan, biyu nan, suka sa mahaifinsu a tsakiya. Kafin ya dawo tuni ta dama masa kunun alkama da qosai. Qarfe takwas suka dawo, duk yayi zufa, yaran suka nufi dakinsu don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka masa tayi tayi, yayi wanka don nuna kulawa. Bayan yaci abinci, yasha magani, sai yace, ki shirya zamu fita. Tsaf tayi kwalliya cikin koriyar super da hijabinta wanda kyansa ya nuna tsadarsa. Qamshi take yi, ta bar sallahun komai gurin masu aiki tare da sauran yaran, sannan suka fita. Direban shi ya taso, Alhaji yace, je ka huta. Nine zanja motar. Saida ta zauna a gidan gaba, sannan ta kalleshi da murmushi. "kai da baka da lfy?1�0�2⃣Yace, sauda kowane lokaci in muna tare bana son mu samu na uku. Sai inga tamkar mu kadai ne a duniyarmu. "Tasa dariya, daidai lokacin daya tada motar. Tace, to kaba ni in tuqa mu. Kaifa jiya kazo. Yace, baki lura ina ganinki na samu sauqi ba. Ynxun ma kinsan ina zamuje? Tace, a'a. Sai da ya hau titi sosai, sannan yace, gidan saukar baqina. Inason muyi hirar da muka dade bamu yi irin ta ba. Sannan mu tattauna muhimman zantuka. Murmushi tayi batace qala ba.
Kwance suke a tsakiyar gadon na dakin baqin, suna fuskantar juna, yace sauda na buqaci muzo nan ne musamman don in baki haquri, sannan in fada miki dalilaina. Sauda nasan cewa, na sa6a miki lokacin dana rabaki da 'yarki na kaita ga wata, wanda harga Allah lokacin soyayyar Mimi ta rufemin ido har na aikata haka. Amma kika yi haquri. Sannan na biyu kece kadai zanyi wa 'yarki abinda nayi mata, wato aurar da ita ga talaka ba tare da kin dagamin hankali ba. Da wata ce, cikin sauran matan, na tabbata da ranar aurenmu da ita zai mutu. Sai na qarshe kece kadai 'yarki zata samu hadari, in hanata zuwa, kuma ta hanu. Sauda duk inda ake neman mace ta gari, kin kai. Ina roqon Allah yasa ki zama shugabar matana a gidan Aljannah. Cikin murmushin jin dadi tace, Ameen Alhaji. Ya tashi zaune. "sauda dalilina na aurar da Mimi ga malam Ismail, tare kuma da yanke duk wata alaqa da ita tare da cire ta cikin ahalina shi ne........
Kashhh! Mu hadu cikin littafi na hudu, kuma na qarshe. K. Mashinku ce, sai na jiku a 08081165107 Downloaded from GNOVELS.COM.NG

This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

Please Login or Register in order to submit comment