Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum na farko dana taba kae qaran shi wurin daddyna bae amshi korafina ba. Tundaga ranar asabar din daya dira gidanmu Abuja,van qara samun kwanciar hankali ba.A qarshe shine daddy ya daura min aure dashi a ranar asabar kuma. Kalli wannan abin doctor,ta yaya zan yafemasa wannan zunubin?
[8/23, 10:28 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�7⃣Salis yayi qoqarin danne dariyar da ke qoqarin kufce masa,sannan cikin zolaya yacee "gaskia yayi babban zunubi". Ismail kam dariyarsa yayi harda qwalla.sannan yace, "Mimi kenan ,kiyi haquri,don nifa haka nake, duk inda nashiga sae nayi nasara akan duk mae ja dani, saboda na dogara ga Allah.kinsan duk Wanda ya mika lamuransa ga Allah,to fa Allah ya Isar masa.kinci sa'a ma wannan guntun labarin naki agaban likita kika fada,ba agaban alqali ba, da sae ya daureki.Domin babu abinda ya hada labarin nan da halin dakike ciki.ni na hanaki bin umurnin mahaefinki? Ni nace miki ki gudu? To, in baki sani ba kisani,bijirewa mahaifinki da kuma gudun dakikayi kika bar iyayenki sune silar shigarki wannan Hamlin. Likita have, wai-wai-wai kin gudu ne dama? Ta sunkuyar da kai, hawaye ne kawai ke zuba. Lallai kinyi babban laifi. Ko dani ba alqali bane. Kamar yadda Ismael yace, amma na yarda gudunki ne ya jawo miki wannan halin da kk tsinci kanki a ciki. Ta soma tuna yadda suka auna arziki a gudun farko. Ashe gargadi ne suka tsallake. Na biyu kuwa shine masoyinta ya mutu, ita kuma gashi ta kakkarye, Burinta in ta warke ta sake guduwa inda iyayenta da danginta ba zasu ta6a jin labarinta ba. To kenan mezai faru in ta sake guduwa? Duk zatonta a zuciya takai qarshen maganarta. Ashe a fili ne. Sai kurum taji yace, in kk sake guduwa na uku, qila qafafunki da hannayenki su gutsire, ki koma gundulmi, kinga kenan sai bara. "Bara? " ta zaro ido. Likita cikin son firgita ta yace, "bara kuwa" sabon kuka ta dora, tare da cewa, " Allah ya dauki raina in huta. "
Canjin rayuwa.
5�8⃣Ismail yace kinata burin mutuwa, an fada miki sauqi zaki samu in kin mutu a haka? Na tambayeki guzurin da kkyi na zuwa lahira, amma baki ban amsa ba. Kk yarda kk mutu a haka, ai kwanciyr kabari ma kawai ya isheki. Ta Runtse ido cikin tsoro, tana tunanin kalmar likita. Wai tayi bara, Nan ta tuna wani English novel data karanta yadda Yarinyar cikin labarin 'yar sarauta, sakamakon son zuciya, ta qare da gutsurarrun qafafu kuma a gidan yari. A firgice ta dago ta Kalli likitan, sai taga ya yagi kwalin magani ya ciro biro a gaban aljihunsa ya soma rubutu. Ya gama, sannan ya miqa ma Ismael tare da cewa, duba ka gani, kasan wannan magani? Ismail ya kar6a tare da cewa to, Ya soma karantawa kamar haka. "Ismail inason ka sauke duk abinda ke ranka game da Yarinyar nan. Ynxun na san bata san tunanin da zatayi ba. Amma ni da kai in mun hadu zamu saita mata tunanin ta. Ismail ya dago kai, ya kalli likitan sannan ya kada kai, na san shi. Likita yace, to kasai mata shi a hada cikin magungunan. Ba damuwa, inji Ismail. Likitan ya sake kusantar gadon mimin, "yanxun, menene tunanin ki a gaba, ko ince burinki? Inason in taimakeki ne matuqa. Mimi cikin kuka tace, banda wani sauran tunani, tunda malam ya dage wai mutuwa ma ba hutu bace a gareni. Da farko na daura aniyar dana warke zan gudu, in nesanta kaina da mahaifana, yadda baza su sake samun labari na ba. Inason su manta sun haifi 'ya irina. Kai in mutu ma yadda zan nesanta dasu gaba daya. Amma ynxun kunce haka. Likita kai ka taimakeni ka nesanta ni dasu mana.
5�9⃣Doctor salis yace, "yi shiru daina kuka, in miki abinda kk so, ta tsagaita saidai ajiyar zuciya da takeyi. Yace, na tabbata in kin kwantar da hankalinki, Ismail dinnan zai nesanta ki dasu, kamar yadda kk so domin shi mijink... "Ta katse likitan da cewa, bana buqatar yaci gaba da zama mijina. Doctor salis yace, dukda haka zai iya, zaka iya ko? Ya kalli Ismail. Yace zan iya matsawar zatayi min alqawari guda daya, sannan zata kwantar da hankalinta tare da bani hadin kai, to zan nesanta ta da mahaifanta, sannan ba aanci gaba da zama mijin nata ba, in ta buqaci hakan. Tace, menene tabbacin, zaka bar gari dani ko qasar? Ya ce, kina cikin garin katsina amma ba dole ku hadu ba, ko susan inda kk. Ta danyi shiru, sannan tace, fadi alqawarin inji. Yace, zaki dauki alqawarin cewa, ba zaki gudu ba, duk wuya, duk runtsi. In kinyi haka, ni kuwa zan 6oyeki, tare da yi miki duk abinda kk so, iyakar iyawa ta. Haka kuma in bakya buqatar inci gaba da zama mijinki, sai in koma wanki. Likita yace, bakida wani za6i sama da wannan. Kuma asirinki rufe. Tace, in kuma hajiya ta kirashi fa ko Alhaji don jin inda nake? Yace daga yau zan kwafe duk numbers din dake wayata banda nasu, sai in baki sim din ki karya, ki zubar. Tace, to in akazo gidanku fa? Ai kafin mubar asibiti zan nemi haya a wata unguwa daban, kuma ko 'yan gidanmu ba zasu sani ba. Dama basu san gidanmu ba. Dama Hamisu direba ne kawai ya sani. Tayi shiru, domin qaramar kwanyarta ta yarda da abinda akace. Ta kalli Ismail, kenan daga ynxun kai ba mijina bane? Ismail yace, a'a wannan shine zai zama a qarshe, ko yaya kace likita? Likitan yace, wannan hakane.
Canjin rayuwa


: 6�0⃣Ta girgiza kai, tare da dan yatsina fuska, sbd dan radadin da ciwonta keyi mata. Tace ban fahimta ba. Likita yace, kinsan za'a bi abin daki-daki ne. Farko dai zamu fara ta lafiyarki. Zanso ki bada hadin kai gurin ganin anyi jinyar ki cikin sauqi. Ki dinga cin abincinki, kina shan magani har a sallameki. Kinga wannan ne farko. Sai mu koma kan abu na biyu, bayan an. Sallameki ki zauna dashi tamkar 'yar uwa, kiyi haquri da duk abinda ya samo ya baki na abinci, ko na sutura, ki kuma nutsu, babu batun guduwa, don kamar yadda yace, zai zamar miki wa. Ko ince kun riga da kun zama daya ma, domin jininsa ne aka zuba miki yake hade da naki. Ta dago ido ta Kalli Ismael, sannan ta Kalli hannunta mai lafiyar. Ta runtse tafin hannunta tana kallon tsintsiyar hannunta, kamar mai kallon jinin yana haduwa. Likitan shiru yayi, daya ga tayi hakan, don yasan zantukan nasa sun shigeta sosai. Ta katsewa likitan tunani da cewa, Doctor in nayi haka fa? Ina nufin sai menene a gaba? Yace, sai batun raba auren ku dashi. Ismail yace, kuma in kin samu wanda kk so, ba zai hana muyi miki aure dashi ba.
[8/24, 10:56 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�1⃣Da sauri ta Kalli Ismael. "Ni bazan qara soyayya ba. Nayi ta na gama, don na haqa rami na binne ta. Zan rayu ne ni kadai. Ismail yace, duk wannan babu matsala, matsawar zaki cika alqawarinki na qin guduwa ko ina. Ni kuma zanyi miki duk abin da kk so. Ta soma qoqarin zamewa don ta kwanta. Sai dai amma ta kasa. Likitan yace, yayanki ya taimaka miki? Tace a'a likita, bana so ya dinga kai hannunsa jikina. Likita yace, wannan babu matsala. Ya miqe ya nufi waje, nurse ya kira yace tazo ta taimaka mata. Sannan ya kira Ismail, zo mana, mu danyi wata magana. Sun jera tamkar abokai. Likitan yace, Ismail banaso ka damu da duk abinda Yarinyar nan zatayi. Ka ceci Rayuwar ta ta hanyar kyautata mata don kar tace zata sake guduwa. Kabi da ita ta hanyar da muka sata akai. Sannan kayi mata qoqarin nesanta ta da mahaifanta na wani lokaci, sbd a samu ta nutsu, ta kuma saba daku. Ismail yace, Allah yasa ta iya. Domin in kaji labarin gatan da take ciki zaka sha mamaki. Allah dai ya shige mana gaba. Doctor salis yace, Ameen. Sannan inason duk lokacin da kk buqatar taimakona a game da wannan matsalar taku, ka kira number ta, sannan ya ciro katinsa ya miqa ma Ismael, "akwai numbers dina a jiki, ko da bana nan a asibiti. Ismail yace, nagode sosai Doctor.
Canjin rayuwa


6�2⃣Na'ima kuwa, yadda taga rana, haka taga dare, sbd mijinta yana samanshi tare da wata mace, wadda ba halalinsa ba. Tayi kuka ta gaji, idanunta sun kukkumbura sunyi jajur. Maimakon Na'ima ta tashi cikin darennan ta miqa kukanta ga Allah, madadin kukan da takeyi. Saidai kash ba zata iya yi ba. Tasan ma anayin hakan. Allah ka ganar damu, Ameen. Bata qara tsurewa ba saida gari ya waye kusan goma da wani abu tayi wanka ta fito. A tunaninta sun bar Gidan. Ta nufi kicin ne don tasa masu yi mata aiki su hada mata abin kari. Cak ta tsaya sakamakon ganin karuwar tare da angon nata suna hada abin da zasu karya. Batasan sadda zuciya ta kwashe ta ba, ta qarasa kicin din cikin fushi ta daqumi wuyan 'yar best din da Jennifer ta saka, tana kuka tana cewa, "zo ki fita a gidana, shegiyar karuwa. Saukar marin da taji ne ya sata sakin Jennifer cikin sauri, ta tallabe kumatunta. Ta kalli Abbas, wanda yake cewa, kinsan dawa kk son yin fada? In baki sani ba, to tsaya in sanar dake. Sunanta Jennifer kuma itace ta musamman dina. Ko da ace mimin da nakeso ce na aura, dole ta barni da ta musamman dina, bare ke wadda baki cikin ra'ayina! Karki sake ki sake kai wannan baqin hannun naki jikinta. Sannan ya juya gurin Jennifer, wadda ta koma gefe, ta 6ata rai matuqa, ya janyo ta jikinsa. Kar ki damu da wannan 'yar wahalar kinji ko? Banida lokacinta.
[8/24, 10:57 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�3⃣Na'ima tace, cikin kukan takaici, Akan wannan zaka mareni? Yace kadan na miki na gargadi. In kin sake kuma, zaki bada bayani. Sannan ki fita anan, in mun gama, mun fita kina iya shigowa kiyi abinda zakiyi, haka Na'ima ta fita, ta koma daki, cikin nadamar auren Abbas. Bakin gado ta zauna, tare da daukar waya ta soma kiran layin momi, tare da fadin cewa, ko momy bata zo ta tafi dani ba, yau na gama Rayuwar gidannan. Momy tana dagawa, kafin Na'ima tayi magana, ta katse ta da cewa "ga daddyn ku kiyi masa sannu da jiki, kafin mu gaisa sbd Jikinsa yayi zafi yau. Na'ima ta fahimci tayi hakane sbd ta sanar da ita tana tare da daddy. Sbd batason daddy yaji wannan matsalar. Muryar daddyn ce ta katseta da cewa, "Na'imatu. Tace, Na'am daddy ina kwana? Yace lafiya lau Na'imatu, yaya kuke da maigidan naki? Tace, lfy daddy yaya jikinka? To da sauqi kenan za'ace tunda ina gd. Amma sugar din yaqi sauka sam. Tace to Allah ya sauwaqe daddy, sai nazo duba ka. Yace a'a Na'imatu karki soma fitowa da wuri haka, in dai ba mijinki bane yace kuzo tare. Tace to daddy, Allah ya qara maka lfy. Yace Ameen. ga Momyn taku. Ta amshi wayar, sannan ta nufi fita. Alhajin yace, kizo ki bani maganin. Tace to Alhaji ina zuwa. Alhaji bashir ya kwanta shiru, yana tunanin yadda sukayi da likitansa daya fita ynxun. Bayan likitan ya auna shi ne yace, "Alhaji meyasa sugar dinka bata sauka? Alhaji yace kuma ina qoqari gurin shan magani da kuma kiyaye duk abinda aka hanani. Doctor yace, to kuwa kana tare da wata damuwa. Saboda shima sugar haka yake, kamar hawan jini 6acin rai yana tayar dashi.
Canjin rayuwa


6�4⃣Alhaji yace, ni bana tare da 6acin ran komai likita. Likitan yace, to ynxu zanyi maka allurar da zata saukar da sugar din inqha Allah. Sannan kasha wannan maganin. Ya dago daya daga cikin magungunan ya nuna masa. Sannan yace, Allah ya qara sauqi. Kuma yana da kyau kadan qara samun varci.
Momy Nafisa ce ta katse masa tunani da cewa, "Alhaji ga ruwan kasha maganin. Ta dauki kwalin maganin ta bude masa tare da cewa, likita fa yace, ka rage wannan tunanin. Wai tunanin me kkyi ne Alhaji? Saida ya afa sannan yace, ko na fada bakida maganinsa. Amma ni burina ynxun in dan samu sauqi inje katsina. Inason ganin sauda sosai, don tana buqatar lallashina. Na tabbata ban kyauta mata ba. Nafisa ta ta6e baki, ka 6ata mata rai, ko mimi ta 6ata mata rai? Shawarata dai a gareka Alhaji. Ka kauda kanka ga komai din lafiyar jikinka ta samu. A tunanina tunda Na'ima ta share maka Hawaye, bai dace ka tsaya tuna wata damuwa ba, wadda zata hana ciwonka sauka, "hannu ya daga mata, alamun tai shiru. Sannan yayi mata alamun cewa ta fita daga dakinsa kurum. Rigingine yayi, tare da dora qafafunsa wadanda sukeyi masa zafi tamkar ana hura musu wuta akan filon, ya kalli qafafun nasa wadanda ciwon sugar din yasa suke masa radadi, ya mai da kansa gefe, yana tuna sai zuwa yaushe kenan zai rabu da wannan ciwon? Domin kuwa damuwa agurinsa ta zama dole. Bai ta6a tunanin cewa, don ya yi wa mimi abin da yayi mata zai dameshi ba. Duk da qoqarin da yakeyi na tanqwasa kansa don fada da zuciyar sa. Mimi ce dai, har ynxun sonta a zuciyar sa bai canza ba.
[8/25, 8:47 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�5⃣Harma wani sashen na zuciyar sa yana fada masa cewa, bai yi wa 'yar tashi adalci ba, domin yasan har ynxun mahaifiyar ta kawai yake yiwa tsantsar SO. Sai yaji tamkar ya daga waya ya kirata, ko kuma ya tashi yaje gurinta. Amma in ya tuna qudirinsa, sai ya fasa, ya lallashi zuciyar sa da cewa, lokaci baiyi ba da zan nemeta. A fili yace, ynxun sauda ce babbar damuwa ta. Yakama in je inyi mata bayani, yadda zata fahimci dalilina. Ya karkata kansa, ya kalli wayoyinsa dake saman durowar gefen gadon. Cikin qarfin hali irin nasa, ya kai hannu, ya dauko qaramar ciki, wadda itace ya tanada don iyalinsa kawai, mata da yara. Ya shiga Numbers, sannan ya danna, kai tsaye yayi qasa, ya latsa masoyiyata sauda. Sunan da duk cikin matansa ba wadda bata nuna kishinta tsantsa akanshi ba. Domin su ya rubuta musu matata wance dukkansu.
Yayi guntun murmushi sbd tuna hakan, sannan ya latsa kira. A ringing na uku, ta daga tare da yin sallama. Yayi shiru na kamar qiftawar ido, sannan ya amsa. Sakamakon duk lokacin da yaji muryarta, sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Yace "sauda." tace Na'am Alhaji. Mun tashi lfy, ya kuma jikinka? Yace da sauqi sauda, amma fa ciwo yananan. Koda yaushe likita ya gwadani sai yace sugar yana qara sama. Kila ma ciwon bana tashi bane. Ji tayi wani abu ta tokare mata qirji, sbd fargaba. Tace Alhaji bakaje asibiti bane? Yace na gaji da zaman asibiti. Kinsan bayan taron nan, na kai kaina asibiti an bani gado. Tace ynxun a gd kk a kwance? Yace eh. Likita yana zuwa dubani. Kar kijini shiru sauda, kina raina. Da naji 'yar dama zanzo in wanke kaina a gurinki


Canjin rayuwa
6�6⃣Zugum tayi tunda suka gama wayar da Alhaji. Kalmarsa ta qila ciwon ba na tashi bane ta tsaya mata arai. Ta san cewa, mutuwa dole ce, amma gsky batason rabuwa da Alhajin ta. Bata san yaya zatayi ba, in har hakan ta kasance. Kurum sai taji Hawaye na zuba daga idanun ta. Hasina ce ta katse ta da cewa, menene hajiya? Cikin sauri ta share hawayen, tare da cewa, babu komai hasina. Ta zauna kusa da ita, shine kk kuka? Ba kuka nakeyi ba Hasina, tunanin rayuwa nakeyi mai cike da canje-canje. Yau fari, gobe tsumma. Hasina bata fahimci hausar ba, don haka sai tace, sis mimi ce? Eh, kawai hajiya tace, don kawai Hasina ta rabu da ita. Miqewa tayi ta nufi gefen masu aiki, sbd aiken da zatayi ayo mata niqan dan waken da muktar ko Abba zai tafi dashi Abuja Anjima.
Momy nafisa kuma, lokacin da taje dakinta ta saurari koken Na'ima sai tace, ta jira, bari ta bawa dadyn su magani. Bayan yace, ta fita ne ta koma dakinta ta soma kiran Na'iman. Cikin sauri Na'ima ta daga har lokacin kuka takeyi. Na'ima wai kkce Abbas ya mareki? Tace eh momy marina yayi akan karuwar daya kawo suka kwana tare. Gsky momy zan dawo gida bazan jure ma wannan cin kashin ba Allah. Momy tace, kai wannan abu ya isheni. Aure ko sati daya baiyi ba, amma matsalarsa tafi ta shekara daya. Amma ba komai, ki qara haquri. Zan turo Aminiyata anjima, zatazo da mayukan da kuma qwayar da zakiyi amfani da ita. Munyi waya tun jiya. Ni kinga dadynku ba zai barni in fita ba sbd baijin dadi, amma kome kenan ki fadawa hajiya nana din kinji? Na'ima tace to.
[8/26, 8:37 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�7⃣Suna gama wayar, ta budo grp chat dinsu na wtsapp. Qawayen ta suna ganinta tayi musu hello, shikenan suka shiga shewa. Ga Amarya! Ina ango? Amarci ya 6oye ki. A turo mana sababbin hotunan da aka dauka cikin amarci. Kowa da kalar tambayar da yake mata. Kasa cewa uffan tayi a group din sbd hawayen da suke zubo mata. A fili tace, da ace kun halin da nake ciki, haqiqa da baku tambayi Amarci ba. Tana kashe data dinta ta jiyo qwanqwasa qofa. Tayi kamar ba taji ba, sbd tana zaton ko sune da suka fita suka dawo. Kusan minti uku ana buga qofar, sannan ta tashi ta nufi qofar da zummar taga ko waye. Tana budewa, sukayi ido hudu da surikarta Hajiya Bilkisu da qawayen ta. Ta hau raba ido tana kallon su. Sannan tace musu, "sannunku da zuwa. Ku yi haquri. Wlh bansan ku bane. Hajiya Bilkisu ta harareta, cikin 6acin rai tace, "au dama in kinji a ta6a qofar bazaki bude ba, sai kin san ko wanene? Hum kuzo mu shiga hajiya ladi. Suka shiga Na'ima ta zauna a gabansu tana cewa, kuyi haquri momy. Sannan ta miqe ta nufi kicin don kawo musu abin sha. Zuciyar ta cike da nadamar rashin bude qofar akan kari. Hajiya ladi ta kalli hajiya Bilkisu, Yarinyar nan tanada tarbiyya kuwa? Hajiya zuwaira tace, banga alama ba. Hajiya Bilkisu tace, ai kuwa ba zan dauki rashin tarbiyya ba. Kusan minti uku muna buga qofa kina ciki kina yauqi, sai kace gidanki.
Canjin rayuwa


6�8⃣Har Na'ima ta kawo musu abin sha da cincin, su diblan, da alkaki, irin wanda amare ke ba ma baqinsu, amma basu daina maganar ba. Kai kurum Na'ima ta sunkuyar, suka yi mata tatass. Har kuka saida tayi tana bashi haquri, amma basu daina ba. Sunyi kusan minti talatin, sannan suka ce zasu tafi. Har gurin mota ta rakasu, sannan ta dawo cikin damuwa da takaici mara misaltuwa. Alamu sun nuna sam ba zata ji dadin dangin mijinnan nata ba. Tun kafin motarsu tabar harabar gdn, hajiya ladi tace, hajiya Bilkisu gsky bakiyi sa'ar sarakuwa ba, alamu sun nuna zatayi rowa. Kin tuna lokacin da muka raka hajiya mairo gdn danta mansur? Wace irin kyauta tayi mata harda mu? Hajiya Bilkisu tayi tsaki. Abinda ke raina kenan ladi. Mu kanmu surukar hajiya mairo ta bamu turaruka masu tsada, ita kuwa lesuka ta bata da atamfa. Hajiya zuwaira tace, ko qannensa da sukaje yini, sai da ta hado su da kayan shafa. Gsky hajiya Bilkisu ki taka birki tunda wuri. Domin in kk bari wannan rowar da rashin son jama'ar nata yayi nisa, to kuwa nan gaba shi kansa dan naki, kina ji kina gani, zai tsani danginsa, ya kuma qanqame abin hannunsa.
Ran hajiya Bilkisu ya qara sosuwa, ta ce, ina zai yiwu! Gobe zan turo su Aisha da samira, har Azima da jamil, in gani suma rowar zatayi musu. Hajiya ladi ta saka dariya, kinji hajiya Bilkisu, kema tayi miki rowa ballantana wasu yaranki? Kawai danki zaki tasa a gaba ki nuna masa cewa, yayi mata tarbiyyar kyuta da son jama'a tunda an kasa yi mata gidansu. Hajiya zuwaira tace, zancen kenan. Tafdijam! Wannan shine gaba kura baya damisa. Na'imar da bata samu kwanciyr hankali daga Abbas ba, ta yaya zata san yadda zatayi abida ya kamata? Muje dai zuwa.
6�9⃣Haka kuwa washe gari sai Na'ima ta sake jin bugun qofa, guraren qarfe dayan rana. Bata yi qasa a gwiwa ba, ta tashi ta nufi budewa don kar ayi irin na jiya. Su Aisha ne da samira da kuma Azima harda auta jamil. Cikin 'yar fara'a mai kama da yaqe tayi musu sannu da zuwa. Suma suka amsa cikin isa, musamman samira da Azima. Sun zauna, ita kuma ta nufi kicin don kawo musu abin sha da dan na ta6awa sannan ta sanar da masu aiki cewa, ga baqi a dora musu abinci. Taje ta kawo musu hotunan biki. Sannan ta zauna. Jin basu gaisheta ba tace musu, ina yininku? Suka ce lfy. Aisha tace, ina bros Abbas fa? Na'ima tace, ya fita tun safe, don tana daki taji fitarsa. Samira tace, sis Aisha kin manta jiya bros daya zo yace, zai koma aiki? Aisha tace, haka ne, Na'ima tace, eh ya koma aiki yau. Ta fadi hakane kurum, sbd kar su fahimci irin zaman da sukeyi. Sun wuni cur, amma bataji dadinsu ba. Komai cikin isa da nuna mata iyakar ta sukeyi. Sannan Abbas ya shigo kusan shida na yamma. Tana dag cikin daki tana jiyosu yana ce musu, kunci kunsha duk abinda kk so, ko kuma anyi muku rowar? Samira, wadda tafi kowa rashin kunya, tace, an ma isa? Bros muzo gidanka ayi mana rowa? Za ma mu jira kenan. Kowa abida take so, shi tasa masu aiki suka dafa mata. Yace, kunyi daidai. Bari inyi wanka inzo in kaiku gida. Aisha ce ta shigo tana ce mata. Bros fa ya dawo. Tace to, sannan ta taso daga kan gadon, ta nufi samanshi, cikin fargaba, sbd kar qannensa su fahimci wani abu.
Canjin rayuwa


7�0⃣Ta tura qofar falon ta bude. Na'ima ta shiga cikin fargaba. Yana zaune kan kujera yana ciro wasu takardu daga cikin jakarsa. Tace sannu da zuwa. Baiji shigowar ta ba, sai magana kawai yaji. Ya dago a fusace, "lafiya? " A tsorace kuma cikin faduwar gaba tace, dama Aisha ce tace min ka dawo, kuma su baqi ne dai, kada su gane cewa akwai wata matsala Tsakanin mu. Ya watso mata harara. Don Allah fitan min anan! An dade ba'a gane cewa, Tsakanin mu akwai matsala ba. Waton ma jiya da Momyn mu suka zo shine kkyi musu wulaqanci ko? Na'ima ta riqe kanta sbd wani sarawa da yakeyi. Tace, ai dai na basu haquri ban zaci sune suka zo ba. Na zaci wannan matar ce data biyo ka. Yace, in itace sai kiqi bude qofa tunda gidan babanki ne? To bari in sanar dake, in baki sani ba, ta fiki matsayi. Ke har iko ta fiki a gidannan. Sbd haka kibi a sannu. Sannan duk lokacin da 'yan uwana suka zo wani yayi kuka dake, na rantse miki sai na zane ki. Fita! Wawiya kawai! Na'ima ta dubeshi rai 6ace, kai bakasan darajar dan adam ba. Ka sake ni kawai, don ba zan iya da wannan wulaqancin ba. Yace, fita nace kiyi. Da kuka ta fito, sbd 6acin rai har ta manta da baqin da suke gidan. Gadonta ta fada tana kuka. Samira, suka kalli juna da Aisha, lokacin da ta wuce su a falo. Har suka shiga dakin, sallar magriba tana kwance tana kuka. Aisha ce ta tambaye ta ko lafiya? Sam Na'ima bata tanka ba har zuwa lokacin da suka gama shirinsu suka ce, mun wuce, Na'ima bata daina kuka ba bare ta amsa.7�1⃣Sun isa gida cike da dokin labarin kaiwa mahaifiyar su. Aisha tana jinsu tana kallon su, samira Tana sanar da mahaifiyar su cewa, Bros Abbas yasa Na'imar kuka. Qila ma dukanta yayi. Azima kuma tace, sannan munyi abinda muka ga dama a gdn. Aisha tace, ku dai bakuda hankali, ina ruwan ku da kukan ta?shiyajiya Bilkisu tace, yayi min daidai! Ai shiyasa jiya daya zo na fada masa abinda tayi, sbd ya kwa6a mata. Samira tace, mu ma da zamu

Please Login or Register in order to submit comment