Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahaukaciyar dariya kana yace kunzu gidan sauk'i


Gawannan. yabasu maganin dazasuyi amfani dashi.


Yace wannan inza,akaita tayi wanka dashi sau ukku tana Kiran sunansa. Wannan Kuma turare zatayi. Wannan Kuma matsashi zatayi se yayi awa 3 ajikinta kana tawanke tazo tayi turaren tsugunno da wannan.


Yabasu Kuma Wanda za,awatsawa hafsat afuska yace yanda ruwan zusu bushe afuskarta haka soyayyar datakeyiwa Dr F A zata bushe azuciyarta.


To Amma dasharad'i. To boka wanne irin sharadine?


Sharadin kuwashine in tayi amfanin da wad'annan kayan to atabbatar yaganta domin inbegantaba har,aka,kwana to memakon so tsanarta zeji Kamar mutuwarsa.tsana Kuma ta har,abada.


Wannan kayan matan kuwa kitabbatar yasadu Dake inkinyi amfani dasu domin inbeyi amfani dakeba Zaki fuskancin latsala. Inkuma yayi besake jindad'in kowace mace aduniya seke.


Hhhhh gimbiya suwaiba tasaka dariya ay indewannan ne sharadin aymesauk'ine agida d'aya famuke dashi.


Nasaduwa kuwa dolene kiyiyanda zakiyi yakusanceki amatsayinki na mace balema ayda yaganki magana tak'are shizekawo kanshi.


Dariyar suka saka dangani sukeyi harsunyi nasara.hakasukajuyewa tsofon mushirikin dukiya suka tafi.




Achan masarauta kuwa yasmeen tahana Dr ganinta tashige kichen itada jekadiya tadage tana shiryawa mijinta da iyayensa abunci sallah me Rai da lpy Dan suntaga tafarantamasa wannan ranar me albarka.


Dr kuwa sauri kawai yakeyi yashirya yafito domin k'annen sa nesuka shigo suna jiransa sutafi tare.




A masallahci kuwa yrm Ali ne da yrm sadam sukacewa liman suna da daurin auren dasukeso ayi kamin lokacin sallar idi yayi domin sunsancewa da,an idarda sallah bawani uzzurin da,aketsayawayi ashari,ance se angabarda hadaya.


Badamuwa limandin yace anan yrm Ali yabayarda sadaki yayiwa Dr walilci shiko yrm sadam yayi Samira.


Akadaura auren *Dr F A da Samira* akan sadaki dubu d'ari.


Cikin matsanancin tashin hankali Dr F A ke kallon k'annen mahaifin nashi dansun tabbatarda abunda kunnesa sukajimasa. Hakama su yrm muneer da yaransu duk kallon tuhuma sukeyiwa yanyen nasu.


Amma Basu kulasuba .memartabane ya,iso yanzu damashikad'ai akejira atada sallah.cikin tashin hankalin fawas yatareshi yanafad'in "takawa kajimikefaruwane annan.


Ganinshi agid'ime yasa sarki habibullah rike hannusa kana cikin dattako yafara magana "banjiba fawas Amma kominene kayi hak'uri kanatsu har,agama sallah mukoma gida seka gayamin. To kawai yace sa,Annan kowa yatashi akatada sallah.




Bayan anidarne akyi adu,o,in da,akeyi kana linman yayi yanka sa,Annan kowa yakama gabansa.anadawowa cikin masarautar su yrm Ali sukacewa memartaba sunaso suyi maganadashi da iyalansu duka.ummurni yabasu na ya,amince


Atake akahada mitin din gaggawa. Koda sak'o ya,iske Fulani alh Abdul Kareem yafalka Kamar ba,abunda yasameshi. Ahaka akashiga d'akin taron


Memartaba ne yayi gyaran murya kana yace yrm Ali sugabatarda abinda sukeson fad'a


Runsunawa yrm Ali yayi cikin tsintsar ladabi dabiyayya gamahaifin nashi yafara daneman afuwar sarki narashin Neman shawararsa kana yabada lbr auren dasuka daura yanzu. yak'ara dacewa nayi hakanne da musamu Dan uwanmu yak'ara kusanci damu domin inamejin bak'in cikin ace bama ganin Dan uwanmu acikinmu munzauna Kamar haka sedai daga shekara ,seshekara Kuma Gaya dukshine babba acikinmu bamusan yazamuyiba danshi nayanke shawarar aurawa Faisal y'ata Dan shiyakasance Yana,acikinmu kowani lokaci Kuma sanin na,Isa da yaron Dan uwana me shi yasa nayanke hukunci banshawarcekaba yaya.


Ya,iyda zancen Yana zubda kallah.




*Tirk'ashi waigobara bisa gemon sarki.*




Tashin hankali rud'ani fargaba duksunrufewa Fulani da ummty jidagani hakama alh Abdul Kareem da k'annen shi domin dukansu sunsan wani makircinne akahad'a


Shiko memartaba bawan Allah farinciki Kamar yataka rawa.


Gyaran murya yayi cikin dattako yafara magana Kamar haka. "Hak'ik'a najidad'in wannan lamarin Kuma hakan dakayi Allah yasa shene mafi alkhairi arayuwarsu .kaiko Faisal Allah yabaka ikon yin adilci ga matanka.ameen duk aka amsa.


Kallon Abdul Kareem memartaba yayi yace babana kasawa y'ay'anka albarka acikin aurensu kaji. To abbah Allah yazabamasu abunda yafizama alkhairi arayuwar aurensu. Duk akace ammen .nande kowa saka albarkacin bakinshi kana sukayi abunda akasaba akwatse.


Dr F A kuwa sashen Fulani yawuce jiki amace hakama Fulani da ummty.


Yrm Ali yanafita yanufi sashesa. Zuwansa yayi Dede da,dawowarsu daga gidan boka.nan yacewa gimbiya suwaiba ayiniyya ashirya amarya akaita sashen mijinta domin ta,Ida sallah acan tunda an daura auren.gud'a tasaki cikin farinciki sukafara shirin Da boka yabasu.sund'au lokaci kamin sukammala komai.har matsin daya Bata tayi. Akashiryata cikin shiga ta alfarma akanufi sashen Dr F A.




Yasmeen nacan batasan mikefaruwaba tagama duk girkinta tasaka jekadiya takai sashen Fulani acewarta yau acan suci abunci cikin iyayensu. Tayi wankanta tayi kwaliyarta kwanin Sha,awa tafito perlon tazauna zaman jiran shigowar mijinta.


Kamar daga sama taji sallamar mutane Koda tadago Kai sekawai taga Mata su hud'u gawani mugun yahaki abayansu memasifar wari natunkaro kofar shigowa perlonta ay amugun razane tamik'e tana fad'in......














Autar alheri......✍️✍️


🤴🎷
🇳🇬
🤴🎷


*IZZAR MULKI*🇳🇬


🤴🎷
🇳🇬
🤴🎷


By yasmeen Ahmad




(🥰 Autar alheri🥰)




*ALHERI WRITERS ASSO*


A*W.A






https://www.facebook.com/10798008594602?referre,whatsap




Page 47 & 48




___tamek'e tana fad'in kaisuwayeku? Minene zakushigomin dashi? Kamin subata amsa takai bakin k'ofar. Hayak'in dataganine taga Yana komawa binsa tayi dakallo taga wannan bala,in daga inayafito.


Magana sukemata Amma batajinsu domin Wannan hayak'in mebala,in wari yafirgitata. Kallansa takeyi sosai ayko setaga Yana bacewa cikinjikin mutum Wanda takasa ganin fuskarsa baletasan kowaye. Sosai take kallon hayak'in cikin matukar mamaki da alajabi. Kuma Taki jayewa daga bakin k'ofar dantafahimci ko,ajikinwane hayak'in kefita perlonta yakesan shigowa.shiyasa takafa ta tsare


Cikin wani sabon mamaki take kallon fuskar data bayyana bayan b'acewar hayak'in.itama me fuskar yasmeen take kallo cikin Isa da tak'ama tace "dan Allah malama kiban hanya inwuce kinzo kinwani tare hanya sekace gidanku..itade yasmeen tayi mutuwar tsaye ganin wannan mugun hayak'in dagajikin Samira yakefita..tunaninta ne yakatse jin d'aya daga cikin matan dasuka Fara shigowa tariko hannuta tanafad'in Y'arnan zokizauna kibasu hanya suwuce Kinji.k'anwar kice muka,kawomiki. Ina zasuwuce? bade Nan gidan ba wlh. Tafad'a cikin waro ido😳.


Ah,ah kekuwa kamarya bade nangidanba. Cewar wata acikinsu? Eh ba,anan gidan zasushigoba Kamar yadda kikaji. Tooo🤔 watasabuwa.akace inji y'an caca.keko baiwar Allah taya kikega kin,Isa kihana awuceda amarya cikin gidan mijinta.


What? Amarya cikin gidan Nan..eh Mana gatakuwa munkawo maku. Hhhhhh yasmeen takece da dariya. Tanafad'in to wacece amarya Kuma wanene angon? Kamin suyi magana. Sukaji muyar Samira daga bakin k'ofar tanafad'ar"nicenan amaryar Kuma yayana shine angona. Watomijinki Kuma Baki,Isa kihanani shigowa gidannan ba kodako ba aurena yakeyiba. Kinganeko.


Kallon bakida hankali tayi Mata kana tace "tonaji amaryar Faisal se,asamidamar juyawa akoma inda akafito.


"Ay wlh Baki,isaba Dan allah mubamu hanya muwuce.


"Kinga Y'arnan yihak'uri kibasu hanya sushigo kinji.cewar wata dattijuwa cikin way'an dasukafara shigowa.


Babah "kezanbawa haku domin Dan innaganin mutuncin shekarunkine nabarki acikin perlon nan bance kifitaba. Amma wlh babah bawani mahaluki da,ya,isa yashigomin da Wannan Bala,in dakejikinta acikingida kowayeshi kuwa.takarashe maganar cikin fad'a.


Tooo🤔ikon Allah lallaiko kinsha k'arya danko Samira Kamar tashigone tagama. Kuma kisani kece bala,i ba y'ata ba. Wata k'anwar gimbiya suwaiba ce kewannan furucin. Tanakawowa nantaja hannu Samira zasu kutso cikin perlon.


Cikin hanzari yasmeen taturasu baya dakarfi.tanafad'in to ay sekushigo mugani wlh kowane mugun abune kikazo dashi dashi zakikoma bade ananba zakikawoshiba.


Keee rashin kuya Zaki mana kinsan koni wacece? dazaki bankomu haka? Kyaleta anty Mina nice Dede ita danyanzu zanyi maganin rashin kuyar..batak'arasaba taji yasmeen nafad'ar wacece ke Banda mushirika dangin matsafa ay ayadda kuka shigo da Y'artaku tun anan kinnunamin wayeke. Tobara kuji wlh kodami kukazo ni yasmeen nafik'arfinku dagani har mijina Kuma wlh ko atsirara kuke yawo da dare da Rana ayafamuku Dan kanfai bazaku shigomin gidaba.


Samira cetayo cikinta zatadaketa "k'anwar maifiyarmu zakizaga to wlh Senaga uban daya tsaya Miki anan.tafad'a tanakaimata duka. cikin hanzari tarik'e hannunta tayi Bata dashi tana fad'in"waike ahaka Kinga wurin dukana tobara kiji ba k'anwar mahaifiyarku kadai nazagaba har itakanta mahaifiyar taku da iyayenta dasuka kasa bata tarbiyar dazata kiyaye dokar Allah da manzonsa harsu nazaga inda abunda zakiya sekiyi inajiranki.


Tak'ara she zancen tana wulgata wajen barandar su sedatafad'i. Tajuya takalli matan dakecikin perlonta tace duk wadda kesan muyi rabuwar mutunci tafitomin aperlo kamin nadena ganin mutincinta na tumurmusa shekarunta nawatsota waje..aytunkamin tarufe bakinta suka soma fitowa. Sunagama fita tajawo k'ofar perlonta tarufe tanarufewa.


Gimbiya suwaiba na isowa domin ankaimata lpr haryanzu ba,ashiga da,amaryaba.fadama kamar,akaga anayi awurin.cewar wata kuyanga. Shiyasa hankali atashe tabiyobayansu.


Yasmeen najuyiwa da Samira da k'anwar gimbiya suwaiba sukayo kanta gadan,gadan zasudaka yayinda gimbiya suwaiba ke k'ok'arin tayasu. Kuma awannan lokacinne aljana bilkisu tayiwa wurin dirar mikiya domin duk,abunda akeyi dazun yasmeen ce. *Kunsan takunfa akwai tsiwa*




Ay suna Kai hannusu jikinta tayi wata iriyar hajijiya dasu duk segasu baje ak'asa.atake kamannin yasmeen suka sauya.


Dukkansu bawanda ya,iya motsa Koda yatsarsane dumin muguwar faduwace sukayi sukai tsowon minti 15 ahaka bawanda yatashi.kamin sukamike dakyar .bilkisu natse tana kallansu shek'ek'e kamin tafara matsawa tana fad'in waike Naga alamar bakya gane kowane yare Sena duka ko tuzaki samu.




Amma kaminnan zankawo karshen wannan iskancin,na nawannan masarautar. Tanarufe bakinta.


Tawagar mazan na isowa.danyanzu Suma sukasami lbr tak'addamar da,akeyi sashen Faisal.


Yrm Ali,yrm sadam,yrm maneer,yrm khamil,se alh Abdul Kareem da Kuma galadima se y'ay'an su. Amma Banda gogan Dan Yana sashen Fulani haryanzu.




Yrm Ali ne yafara magana fad'a,fad'a "kaimikukeyi anan? lpy bakushigaba da amarya cikin gidan mijinta ba?


Inafa lpy cewar wata dattijuwa cikin way'anda sukazo da,amaryar. Miyafarune to? Wannan Karan yrm sadam ne yayi tambayar.


Lbr wannan dattijuwar tafara Basu tiriyan tiriyan duk abunda yafaru tunzuwansu haryanzu.. gimbiya suwaiba ce tasharb'e zancen dacewa Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment