Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan nawa kusan minti biyar sai gashi ta fito karan bude kofar ne yasa ya san ta fito daga kai da zaiyi dukai ido hudu ita da shi.






Gaban kuwa sai da ya fadi kallon juna suke wanda kowa yana tambaya kan san wannan wace irin kama ne muke haka?? duk kan su basu da amsar da zasu ba juna kusan minti goma suna kallon-kallo can dai Deeyana tayi kasa da idon ta kirjin ta na wani irin bugawa shi din ma haka ne.






Tambaya yake ma kansa wacece wannan kaman mu ta baci to ko dai aljanna ce k'ara kallon Deeyana tayi wanda yanzu ta far bakin kofar ta koma bakin Bed ta zauna ita ma tunani fal ranta, ya rasa mai zaice mata ma sai kawai yace, "kece Deeyana??" Shuru tayi kaman bata ji abunda yace ba dan hankalin ta ya gama tashi bata tab'a ganin mai kama da Abban ta irin Dameer ba shi kawai zai nuna mai fari ne da kuma gashin shi da yake kaman na larabawa amma komai na abban ta irin na Dameer ne.






Shurun da yaga tayi ne yace, "maybe ke d'in kurma ce Amma in kece Deeyana ki shirya ga break d'in ki cen a Parlour" kallon shi Deeyana ta k'ara yi a karu na biyu sannan tayi sauri ta saukar da idon ta kasa gaban ta na cigaba da faduwa.






Murmushi gefan baki yayi ganin yanda duk kaman ta tsorata sai kawai ya fita a dak'in da tambayoyi fal ranshi kuma bashi da mai amsa mai sai dai mafita daya ya kira Ammin shi, bedroom d'in shi ya shiga sannan ya fito da wayan shi ya fara kiran Ammi ringing biyu ta dauka, "Ammi na ya kike ina missing d'in ki".






Murmushi tayi jin muryan dan nata sannan tace, "lafiya lau dan Ammi ya yata tana lafiya" yace, "lafiya lau Ammi na" "to madallah" cewar Ammi.






"Hmmmm Ammi kin san wani abu" gyara zama Ammi tayi sannan tace, "A'a lafiya dai ko??" "Ummmmm Ammi yariyar nan muna kama da ita sosai Ammi" "wacce yariya kenan Dameer??".




"Ammi yariyar nan mana da aka had'a ni da ita" jin zancen Ammi tayi wani iri sannan tace, "ni fa Dameer har yanzu ban gane mai kake nufi ba ya zaka ce kana ma da yariya bayan kuma kace Ba'a masarautar yariyar take ba".




"Ammi baza ki tab'a gane mai nake nufi ba amma Ammi insha Allah zamu zo saudi a satin nan dan kwata-kwata ban gane wannan abun da Momma ta had'a ba a zancen da take min tace, ita ma bata san yariyar ba wai makarantar su taje anan ta fara ganin yariyar to Ammi kaman da muke da ita fa sannan jiya baban yariyar ya fad'a min wata kalma da har yanzu inq tunanin ta a zuciya ta".






Tashi tayi tsaye sannan tace, "Dameer gaskiya kam ina buk'atar ganin ta sabida akwai wani abu da mu bamu sani ba Allah ya kawo ku lafiya" "Ameen" yace nan dai suka cigaba da tattauna maganar.








Yan uwa Amma kuwa haka suka koma gida suna yabon karamcin masarautar mure barin ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya sunfi mata addu'a kowa yace tana da kirki sabida ta musu hidima Amma taji dadi sosai dan daman addu'ar ta kenan Allah ya ba yarta kwanciyar hankali da hutu to gashi ta samu sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya.






Misalin karfe sha-biyu gimbiya Aisha da sarauniya maimunatu suka shigo part d'in Deeyana dan shirya ta za'a kaita fad'a kuma za'a zagaya da ita masarautar gaba daya a bedroom d'in ta suka samai ta, tana zaune sai tunane-tunane take sallaman su da taji ne yasa ta tashi da sauri ta gyara hijab d'in da yake jikin ta tana musu sannu da zuwa.






Da sauri sarauniya maimunatu ta rungume ta tana fadin, "my sister kin kwana lafiya ya bakunta?" Murmushi Deeyana tayi sannan ta dan dungusa ta gaishe su tace, "lafiya alhamdullh" gimbiya Aisha tace, "kinci abinci ko?".






Daga kan ta tayi alaman "eh" wanda zata shirya tane ta matso ta fara mata kwalliya su kuma suka fita zuwa parlour, sosai mai kwalliyan ta tsarata sannan ta miko mata kayan da gimbiya Aisha ta bata tace, shi zata ba Deeyana ta sa, masha Allah tana gama saka kayan mai kwalliya ta fara feshe ta da turaruka masu kamshi da daukar hanci.






Alkebba ta miko mata sannan ta fara sanya mata, kai bazan iya tsayawa lissafo muku kyau da Deeyana tayi ba, murmushi matar tayi sannan tace, "gaskiya kinyi kyau gimbiya" ita ma Deeyana murmushi tayi sannan tace, "nagode" sarauniya maimunatu ce ta shigo taga ko an gama mata tana yin arba dq Deeyana ta tsaya cak ta kasa ko k'wak'waran motsi ganin Deeyana take kaman k'anwar ta a hankali ta fara takowa in da Deeyana take sannan tace,




"My sister kinyi kyau masha Allah" kasa da kai kawai Deeyana tayi taba murmushi a hankali sarauniya maimunatu ta kama ma Deeyana hannu suka fito parlour, gimbiya Aisha ma zaro ido tayi tana mamakin kaman da tagani a fuskar Deeyana sakin ta tayi sannan ta shiga bedroom d'in Dameer dan ya fito su tafi, har lokacin jikin sarauniya maimunatu a sanyaye yake ta rasa mai zata ce ma, Dameer tayi ma ma mgn sannan ta fito.






K'ara shiryawa yayi sannan ya fito samun su yayi a Parlour kowa shuru kowa da tunanin da yake a ransa, suna ganin shi suka miki sarauniya maimunatu ta mai shi gun Deeyana sannan tace, "doki ne zaku hau ka rike ta".






Kai kawai ya d'aga mata sannan ya sanya hannun shi cikin na Deeyana dan bega fuskar ta ba ta saki hulan alkebban, a hankali suka fara takawa har suka fito harabar part d'in nasu fadawa ne suka iso gare su da sauri janye da dokuna.








Jikin Deeyana ya fara rawa dan bata tab'a hawa doki ba wani fari aka matso da shi gaban su sannan aka ce wannan na gimbiya ne ana nufin na Deeyana kenan, gyara mata akai sannan aka ce ta hau ai bata san lokacin da ta kara tamtsi hannun shi a nata ba kallon ta yayi sannan yace, "lafiya?".






"Muryan ta na rawa tace, fadowa zanyi in na hau" dariya yayi har hakuran bakin shi na beyana yace, "daman kina magana ai nasha kurma ce" shuru Deeyana tayi kuma taki sakin hannun nashi sarauniya maimunatu da take karasowa tace, "mai kuke jira my Bro's?".






Beyi magana ba sai ganin kawai da sukai ya dauka Deeyana ya daurata a dokin cike da tsoro Deeyana ta rike mai hannu tana girgiza kan ta, gyara wajan hawan yayi sannan ya hau dokin kin, gaba daya fadawa sukai kasa da kai gimbiya Aisha kuwa tsayawa tayi tana kallon ikon Allah murmushi sarauniya maimunatu tayi sannan ta d'aga mai hannu.








Haka suka fara tafiya a kan dokin Deeyana ta rike shi gam, shi abin ma dariya yake bashi jin yanda jikin ta ke rawa, fada suka nufa fadwa wasu na gaban su wasu na baya sai busa da ke tashi, suna isa fada shi ya fara saukowa sannan itama ma ya taimaka mata ta sauko hannun shi cikin nata suka shiga fada guri na musanman aka nuna musu suka zauna mai-martaba sarki Fahad Abdullah yana zaune a kujeran shi.




Gaisuwa Deeyana da Dameer suka kai ga sarki sannan suka koma suka zauna addu'a sarki Fahad Abdullah yace, ayi sannan ya fara musu nasiha ya kuma sa ma Deeyana albarka, sun dan dade a fada sannan suka fito yanzu ma haka akai doki daya suka hau part d'in gimbiya mabaruka suka nufa.






Gimbiya mabaruka tun da taji zuwan su ta fito dan ta tare su, suna saukowa a doki tazo ta rungume Deeyana da fara'ar ta shiga suka ta zaunar da su a Parlour ta nasiha ta fara musu mai ratsa jiki sannan ta sanya musu albarka sai da suka tashi zasu tafi sannan ta bude hular alkebban da ta dan rufe mata fuska tace, "bari in ga jikar taw... "






Bata karasa ba ganin Deeyana da tayi gimbiya mabaruka tayi shuru ta sai kallon Deeyana take kuma kallon ta Dameer yayi ganin kallon yak'i karai wa sai kawai ya kama hannun Deeyana suka fita a dak'in,a zuciyar shi yana cewa lallai akwai wani boyayan sirri tunda gashi ita ma gimbiya mabaruka taga Deeyana ta kasa magana.




Haka suka kara hawa dokin akai ta zagaya dasu masarautar suna gaida da mutane, part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya yanzu suka nufa, duk da bata jin karfin jikin ta hakan be hana ta zuwa tarbar su ba tunda haka ake in dai za'a zo gaishe ka to sai ka fito kayi tarba ita da jakadiya suna tsaya har su Dameer suka karaso doki guda taga Deeyana da Dameer haushi ya kara kamata jakadiya ta tafo ta tace,






"Uwar gijiyata kalle abun mamaki yanzu yarima ko kunya baya ji" cizan bakin ta tayi sannan tace, "jakadiya wannan yaron in banyi da gaske ba bakin cikin shi zai kashe ni barshi kawai nasan maganin shi".






Sankowa Dameer yayi a dokin sannan ya kama Deeyana ta sauko rungume ta yayi a jikin shi ya fara cewa, "sannu kiyi hakuri dan wannan tafiyan ya zama dole ne amma da baza kiyi ta ba sabida nasan ba dadin ta kike ji ba".






Kallon mamaki Deeyana tayi mai tana xancen zuci, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta zuke fuska sannan matso kusa da su tace, "to mara kunya dan yanzu sunan ka kenan a gurina sai ka sake ta ko" "la Momma baza ta iya tafiya da kanta bane shiyasa" yayi maganar kaman zaiyi kuka.






Hmmmmm kawai gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace, da karfi sannan ta janye Deeyana suka shiga kilisarta, murmushi yayi sannan yabi bayan su magana gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fara ma Deeyana sannan tace, "ki dauke ni kaman mahaifiya duk wani abu da Dameer ya miki ki gaya min kinji"








Kai Deeyana ta daga a hankali jakadiya ce ta shigo da kayan motsa baki sannan ta aje tsakiyan su tace, "to sarauniya gashi a dan tab'a" "ummmm" kawai Deeyana tace murmushi gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "my daughter cire hular ki sha iska"




Murmushi Deeyana tayi sannan ta cire shi dai Dameer na zaune na danna waya abun shi, gimbiya Haleematun-Sa'adiya na kallon Deeyana gaban ta ya fad'i fuskar yarima ALIYU ne kawai ya fadu mata k'ara kallon Deeyana tayi a karu na biyu nan da nan zufa ya rufe ta jakadiya da taga gaba daya uwar gijiyata ta burkice sai take mata mgn da ido akan menene.




Kallon in da take kallo jakadiya tayi da sauri ta zaro ido dan kaman Deeyana da yan masarautar ya baci, kusan minti goma suna zaune haka can dai Dameer ya tashi yace, "Momma na zamu huce" bakin ta na rawa tace, "to Dameer" kallon ta yayi sannan ya kama Deeyana suka fita.






Jakadiya ce ta matso kusa da gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace, "uwar gijiyata mai zamu gani kin ga abun da na gani kuwa lallai ba shakka wannan yariyar jinin masarautar mure ne sabida su jinin su baya boya".






Zufa gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta share sannan tace, "na shiga uku ni Haleematun-Sa'adiya mai yasa duk abun da zanyi baya tafiya min dai-dai wannan yariyar jinin waye kenan a cikin masarautar nan na had'a ruwan dafa kaina".






"Aliyu" shine abun da kawai wata murya tace.....








*πŸ€”πŸ€”to fa wacece wannan kuma*






*Aunty baby ce✍*
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🀱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚








🀴🏻 *IZZAR SARAUTA*🀴










🌐
*_ALHERI WRITER'S*
*ASSOCIATION_* ✍
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*








*ALHERI SAI DAN AlHERI* πŸ‘Œ








*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍








*DEDICATED TO..*
*TO MY SON AREEF*🌷






*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*








*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*










πŸ“ *page* 4⃣3⃣⏩4⃣4⃣












*___________* πŸ“– "Aliyu!! wannan yariya da kike gani jinin Aliyu ce dan kallo daya nayi mata na tabbatar da haka Haleematun-Sa'adiya ya kamata ace yanzu kin girma kin daina duk wani makirci sabida wallahi gaba nake jiya miki kuma ni bazan tab'a tona miki asiri ba duk sanda Allah ya tona miki shikenan dan rayuwar na abun tsoro ce" gimbiya mabaruka kenan matar sarki Abdallah.








Wani mugun kallo gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta zuba ma gimbiya mabaruka sannan tace, "daman fa ke ba sona kike ba duk cikin masarautar nan shiyasa yanzu zaki zo kina min wasu banzan maganganu to wallahi ina miki kashedi na karshe karki kara shiga hurumin da ba nake ba a cikin masarautar nan karki ga wai ke matar uban mai-martaba ne hhhhhh ba raga miki zan ba".










Murmushi gimbiya mabaruka tayi sannan tace, Haleematun-Sa'adiya kenan yanzu ko wannan abun da yake shirin faruwa be ishe ki ishara ba yaron da kikai sanadiyar fitar shi a masarautan nan shi kuma yanzu a rashin sanin ki da muguntar ki kika kara shigo da shi..".






"Dakata! Dakata!! Wallahi in dai ina raye Aliyu bazai tab'a kara shigowa masarautar nan ba" Gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fad'a tana shiga bedroom d'in ta fuuuuuu, Hmmmm kawai gimbiya mabaruka tace sannan ta fita a dak'in, jakadiya na tsaye sororo ta kasa tafiya! tana shiga bedroom d'in ta ta fara zagaye dak'in tana zantuka.








"Ni gimbiya Haleematun-Sa'adiya zan saka abu a gaba ban cin ma buri na ba wallahi karya ne" shigowa jakadiya tayi da sauri sannan ta tsugunna gaban ta tace, "kiyi hakuri ya uwar gijiyata Allah ya huci zuciyar ki in dai ina raye baza ki tab'a shiga damuwa ba".








"Huuuuuummm jakadiya wani bala'i ne yake shirin tinkaro ni yanzu y'ar Aliyu tana cikin masarautar nan komai na ya gama lalacewa ya zanyi yanzu?" ta fada tana zauniya a bakin Bed d'in ta dafa kanta tayi dan ji take kaman zai fashe, jakadiya ta gyara zaman ta sannan tace,








"Ummmmm uwar gijiyata sai kace ba ke ba wannan Dan matsalar har zata kwance miki kai abu mai sauki" matsowa tayi kusa da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fara gaya mata magana a hankali sannan ta kare da cewa, "haba uwar gijiyata ai ki daina damuwa wannan shine hanya mafi sauki da zamubi".








Daga kai gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "shikenan kuwa jakadiya shiyasa nake sonki wallahi sabida k'wak'walwar ki" murmushi kawai jakadiya tayi.










Ko da su Dameer suka fita dak'in da jaddah take suka shiga ita ma ta saka musu albarka sannan ta k'ara musu nasiha ko da taga Deeyana tayi mamaki sosai amma bata ce komai ba dan ita a zaton ta duk yan uwa ne gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta had'a, sosai taji Deeyana ta shiga ranta nan dai ta dunga tsokalan su irin na jika da kaka ita Deeyana ba wani fahimta take ba dan larabcin Nigeria da Saudi ba iri daya bane shiyasa sai dai tayi ta murmushi.








Sai bayan sallah Asr suka tafi nasu part d'in, Deeyana tana shiga bedroom d'in ta alkebba ta fara cire wa sannan ta cire kayan jikin ta ta shiga toilet wanka tayi sannan ta fito kaya mara su nauyi ta sanya sannan ta zauna bakin Bed tana tunanin iyayan ta dan wani irin kewar su take gashi bata da waya bare ko Amman ta ta kira.






Shima dai Dameer wanka yayi sannan ya sanya jallabiya ya fito parlour ya zauna yana danna waya tunani yake gobe kawai zasu wace saudi amma mai-martaba kuma shine ko zai bari su tafi a gobe oho, kiran Ammin shi yayi ya sanar da ita cewa yana so su taho gobe amma yana tunanin ko mai-martaba zai bari, Ammi tace, ya gwada tambayan shi yaji amma barin masarautar nasu shine mafita tunda duk ya bata labarin yanda sukai da gimbiya Haleematun-Sa'adiya.








A haka dai suka tsaya zaije yama mai-martaba magana, tashi yayi ya shiga bedroom d'in shi ya canja kaya sannan ya shiga na Deeyana tana kwance kallon ta yayi ganin yanda tayi shuru, dan sosa giran shi yayi sannan yace, "akwai abinci a Parlour ki fita kici".








"Bana jin yunwa" shine kawai abunda Deeyana tace, tayi kasa da kanta lumshe kyawawan idon shi yayi sannan yace, "hhh ina ga d'ure kike son na miki d'aga kafadun shi yayi sannan yace, "in hakan kike bukata dan Allah ki bari na dawo baki ci abincin nan bq kiga yanda zan miki" yana gama fadar haka ya fita a dak'in.






Kwalla ta share sannan a hankali tace, "wayyo Allah na wai dan mugunta yace zai min dure wannan daman daka ganin shi bashi da imani" tashi tayi a hankali ta fita a bedroom d'in ta huce parlour, abincin ta taran a cikin basket an rufe shi da farin kyalle mai Kyau zaunawa tayi sannan ta bude flast daya ta bude sannan ta dauke plate ta dan zuba abincin kad'an sannan ta koma kan kujera ta fara ci kaman tana cin magani.






Yana fita fada ya huce lokacin ana kokarin sallahn maghrib shima alwala yayi sannan yabi jam'i ana idarwa sarki ya huce kilisar shi dan ana sallah maghrib zaman fada ya k'are kuma sai gobe, jakadiya yasa tayi mai iso mai-martaba yace, ya shiga sannan ya shiga cikin ladabi da biyaya ya gaishe shi sannan ya fara mai bayanin abun da ya kawo shi.








Sarki yace, "be kamata ace daga yin biki jiya ba gobe su tafi wata kasan amma tunda shi hakan ya zaba shikenan sai ya sanar ma fulani a shirya musu tafiyan sannan kuma ya kai yariyar gidan su tayi sallama da iyayan ta" sosai Dameer yaji dadi dan be tab'a zaton mai-martaba zai amince ba nan ya mai godiya sannan ya tashi ya fita.






Kilisar fulani ya huce dan yasan iyanzu tana can yana shiga ya tatda ta ita da jakadiya suna firan su tashi jakadiya tayi tana mai fadanci sannan ta fita dan ta dan basu guri su zanta, zaunawa yayi kusa da gimbiya Haleematun-Sa'adiya da ke kishingid'e tana cin tufa lokaci zuwa lokaci kallon ta yayi sannan yace, "Momma na sannu da hutawa".








Murya a had'a tace, "yauwa" murmushi yarima Dameer yayi sannan yace, "Momma na insha Allah gobe tare zamu huce da jaddah Saudi Arabia" washe Baki tayi dan azaton ta zai bar Deeyana ana sai tace, "to madallah amma my daughter zatayi kewar ka amma ai ba wani Abu tunda gani".






"A Momma na tare zamu tafi daga jiya zuwa yau nayi sabon da bazan iya rabuwa da ita ko na minti daya ba" ya fad'a tare da basarwa kaman bashi yayi maganar ba, zaro Ido gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi sannan tace,






"Dameer yariyar da aka kawo ta jiya kace zaka tafi da ita wata k'asar ai be dace ba kuma kasan a k'aidar masarautar nan ba'a fita da yariya har sai tayi shekara amma ita jiya jiya ai sai kaja mana zage ace dan ita ba Yar kowa bace shiyasa".






Kallon ta yayi ganin yanda ta dage tana magana sai kace da gaske sannan ya cizai labb'an bakin shi na k'asa yace, "Momma na pls kiyi mana addu'a kawai amma naga ai ba komai bane dan na tafi da ita tunda duk gida ne kuma yanzu na sanarwa da Abba yace, ba komai".






"To bazai tab'a yuhuwa ba kuwa dole ka barta ana ka tafi kai daya" "hmmmmm Momma kenan to ai Naga dai matata ce kuma Ni ke da iko da ita dan haka ni dai tare zamu tafi".




Huci ta fitar Mai zafi sannan tace, "wato Dameer ban san ranar da raini ya shiga tsakanin mu ba ni da Kai na daya dai ni ba wasa nake da Kai ba, ba wani abu ba kuma ko da uwarka ban taba wasa balle Amma Ina daga maka kafa baka sanni ba ko hhhhhhhh Dameer kenan to Wallahi ka kiyaye kanka sannan kuma matar ka ce baza ka tafi da ita d'in ba sai Naga yanda za'a yi".








Tashi yayi sannan ya zuba hannun shi cikin aljihun wandon shi ya fara takawa a hankali sai da ya kai bakin kofa sannan yayi dariya mai sauti yace, "hmmmmmm Momma na kenan" sannan ya fita a kilisar.






Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi jakadiya ce ta shigo da sauri jikin ta har rawa yake gurin zubewa gaban gimbiya Haleematun-sa'adiya tace, "Allah ya huci zuciyar ki Dan nasan wannan shegen yaron sai da ya Bata Miki rai ya fita Amma ki kwantar da hankalin hakan mu ta kusa cin ma ruwa".






Shuru gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi dan ko kalma daya baza ta iya fad'a ba tashi tayi da sauri ta fita fuuuuuu kilisar mai-martaba ta huce ko iso bata nema ba ta shiga, kallon shi tayi sannan tace, "Allah ya baka yawan rai Dameer ya zo min da wata magana wai gobe zai tafi da yariyar nan kasar su baka ganin da cutarwa a ciki ai ba'a mata adalci ba".






Shayin da ke hannun shi ya kurba sannan ya kalle ta sai huci take sannan yace, "fulani ki barshi ya tafi tunda hakan yaga yafi mai kila uwar shi ce take son ganin ta" kallon mai-martaba tayi sannan tace, "lallai sai yau na tabbatar Daman in dai ba Kai ka haifi d'a ba to baka da iko da shi in ba Haka ba duk abunda nake ma Dameer baza Yi abunda na saka shi ba sannan har ka goya mai baya".






Murmushi su na manya yayi sannan yace, "to yanzu na riga nace mai ya tafi hakan nan za'a barshi ya tafi d'in dan kin san bana magana biyu sai a kori gaba kuma" hawaye ta fara sharewa "shikenan, dan ban haifi da namiji bane shiyasa da Ina da d'ana Nima ai ba Wanda ya Isa ya mai wani abu a kan shi bazan Kara shiga shirgin dan ka ba" tana gama fadar haka ta fita fuuuuuu.








Girgiza Kai kawai mai-martaba yayi yaci gaba da shin shayin shi, tana shiga D'akin ta ta fara zagaye shi tana tunanin mafita wata zuciyar tace, kije ki samu yariyar kice karta amince ta bishi wata kuma tace la karki haka za'a gano ki da wuri rasa ma wani tunani zata yi tayi.








Yana fita daga kilisar fulani part d'in shi ya shiga parlour ya zauna duguwar kujera yana ta tunanin maganar gimbiya Haleematun-sa'adiya ciza labb'an shi yayi sannan yace, "Wallahi Momma baki san Dameer bane Ina ga lokaci yayi da zan nuna miki real color na".






Deeyana tana zaune a kan Bed d'in ta tunanin Amma da Abba sun damai ta ta rasa yanda zatayi tayi magana da su tunda dai ita ba waya gare ta ba tashi tayi a hankali ta leka parlour kwance ta samai shi a duguwar kujera idon shi lumshi da alaman bacci yake a hankali ta lallaba ta fito tana tafiya a hankali har ta k'arasa kujeran da yake dubawa tayi ko zata ga wayan shi bata gani ba ta lika bayan shi ana ta hango duk wayoyin nashi.




Ta bayan kujeran ta sak"ala hannun ta zata dauka daya daga cikin wayoyin nashi zurun ya rik'e mata hannu, kulle idon ta tayi gam sabida ba k'aramin kunya taji ba kallon ta yayi sannan ya dawo da ita ta gaban shi ya zaunar da ita kan kujeran sannan ya shima ya gyara zaman shi, Kara kallon ta yayi a karu na biyu ya kafe ta da lumsassun idon shi.






Kaman tasan yana kallon ta ta k'ara kulle idon murmushin gefan Baki yayi sannan yace, "Kai wannan yariyar akwai wayyo mai zakiyi da waya?" Toro baki Deeyana tayi sannan tace, "ai Abba da Amma zan Kira".




Shima kwaikwayan muryan ta yayi sannan yace, "shine kuma baza a gaya min ba kawai za'a kwashi min waya" kara tura bakin tayi sannan tace, "ka matsa to in tashi" "Aa an fasa kiran Abba da Amma ne?" Ya fad'a yana lakatan hancin ta sauri tashi tayi a zuciyar ta tana cewq "shi wannan baya jin kunyar taba mata".






Kaman yasan tunanin da take kenan ya mika mata wayan a hannun ta sannan ya dauka sauran ya tashi ya shige dayan part d'in, tabe Baki Deeyana tayi sannan ta mik'e ta shiga bedroom d'in ta, sai da ta zauna a kujeran bedroom d'in sannan ta sanya number Abba ta fara Kira, ringing kusan uku sannan Abba ya dauka.




Cike da murna Deeyana ta fara gaishe shi yana jin muryan Deeyana yayi murmushi sannan suka fara gaisawa yace, Ina ta samu waya sai tayi shuru ta rasa abunda ma zata ce can dai tace, "na na hmmm ynnn yaya ne" murmushi Abba yayi sannan ya k'ara mata nasiha sosai nan dai sukai Sallama.




Murmushi tayi sannan ta fara kiran Amma ringing daya Amma ta dauka cike da murna Deeyana tace, "Amma na" Amma tana jin muryan Deeyana tace, "Deeyana

Please Login or Register in order to submit comment