Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

21-25




✍✍




Haneefah tayi kukan har ta gaji,bakin cikine kawai yake yawo a ranta,tunanin dawowar mai martaba kawai take,yadda yake ganin hankalinta ace ta saci waddan nan makudan kudin,daga tayi wannan tunanin sai ta fashe da kuka,sannan ta tuna asalin ita wacece nan ma hankalinta ya kara tashi,tun yamma haneefa take kuka har sai da lokacin sallar magrib yayi,dakyar ta tashi da shiga toilet yayi alola bayan ta fito tayi sallah,haneefa bata tashi daga kan sallaya ba ta fara mika kukan ta wajen ubangiji kamar yadda ta saba.




Hannu biyu ta daga sama👏 ta fara addu'a kamar haka a fili.




Ya Allah ina rokonka ka bani ikon cin wannan jarabawar,Allah kai kace mu roke ka bani da wanda xan roka bayan kai,ya Allah ka karamin hakuri da juriya,ka kuma kareni daga sharrin mutum da aljani,da masifar gabas da yamma kudu da arewa,ya Allah ka bani mafita,ka kawomin farin ciki na har abada.




Ya Allah ka kareni daga sharrin dake cikin wannan ranar,nan fa kuka yaci karfin haneefa😭 ta cigaba da cewa Allah ka sadani da alkhairan dake cikin wannan ranar,Allah ka sakawa iyayena da alkhairi,Allah ka sakawa mai martaba da alkhairi.




Banda kuka ba abin da haneefa take😪 ,momy da Amal kuwa suna can sai faman hada wa haneefa tuggu suke.


Haneefah tana idar da addu'a ta wuce wajen baba mareeya,tana xuwa ko magana bata iyayiba ta xauna akusa da baba mareeya,sautin kukane kawai yake fita daga muryar ta,baba mareeya tayi sauri ta dago tare da matsar da kwanon da take kadi daga gabanta,haneefa kiyi hakuri insha Allahu wannan yanayin baxai taba dawwama ba watarana xaki sami canjin rayuwa insha Allah,shi kudi da sarauta da suke ji dashi mai karewa ne,gaskiyar ki kuwa baxa ta taba karewa.




Har alokacin da baba mareeya take magana haneefa kuka kawai take,ta cigaba da cewa nasan cewa baxaki taba iya daukan ko da tsinke na mutum ba,balle makudan kudi haka,haka kuma duk ma'aikatan gidannan kowa yasan baki dauka ba dan dai bamu da iko ne ba yadda xamuyi.




Haneefa tace baba mareeya mai martaba ya rikeni tamkar 'yar da ya haifa komai yana yimin,idan yaji ance na dauki kudi baxai taba jin dadiba ni dai kawai barin gidannan xanyi,baba mareeya tace a'a haneefa idan kika tafi nima ai baxanji dadi ba saboda bansan hannun wanda xaki fada ba kinga ba wanda kika sani,dan haka kiyi hakuri Allah ya kaimu goben muga abinda xai faru idan mai marta ban ya dawo.




Suna cikin wannan tattaunawar ne sukaji ankira sallah,haneefa tace baba mareeya bari na shiga ciki nayi sallah baba mareeya tace to amma dan Allah ki kwantar da hankalinki insha Allahu ba abin da xai faru,haneefa tace toh tare da goge hawayen dake xubowa daga idon ta.






Haneefa tana da hankali sosai gashi ta dace hankalin nata ya hadu da addini,ko kadan bata wasa da sallah,tana ganin girman naga ba da ita komai talaucinsa,bata da yawan magana barkatai sai ta kama,shiyasa ta shiga ran yaya Abdul sosai saboda baya son mutum mai rawar kai da yawa.Allah sarki haneefa baiwar Allah.




Sukayi sallama da baba mareeya,haneefa ta shiga cikin gida,tayi sallar isha,ranar ko karatu bata iyayi ba,gashi da safe tana da test,danma akwai brain ko batayi karatu ba bata tunanin shiga test ko exam,haka ta kwanta dakyar bacci ya sace ta.






Asuba nayi haneefa ta tashi tayi sallah,tana kallon Amal sai sharar baccinta take,har xata tasheta kawai sai ta fasa saboda tasan ba tashi xatayi ba,bayan haka kuma masifa ce kawai xata sha.




Haneefa tayi kyau sosai,amma kana kallon fuskarta kasan akwai damuwa mai tarin yawa,ta nufi sashen momy don ta gyara kamar yadda ta saba.




Tana shiga dakin momy ta daka mata tsawa,what are u doing here?? Muryar haneefa cike da tsoro tace momy dama xan gyara dakin ne,cikin masifa momy tace ok,to banason gyaran,yau kuma idan na barki kika shigomin daki brief case din gabadaya xaki sace ai,haneefa tayi shiruuuuu kamar ruwa ya cinye ta.




Momy tace to bari kiji infada miki daga yau banaso ki kara shigomin daki,keee falo na ma haka,barauniyar banxa barauniyar wofi,ciki shouting tace "oya get out of my room stupid"....






Haneefa kam sai hawaye,jikinta a sanyaye ta bar dakin.




Tana fitowa ta nufi hanyar part dimsu,kanta akasa ta wuce ta gefen yaya Abdul dake kan dining yana break fast,saboda bacin rai bata ma san yanan ba.






Yaya Abdul ya kira sunan ta,haneefa,tajuya slowly ta fara kokarin,seta kanta,gashi ya riga yaga hawayen dake fuskarta.




Yace xo nan,ta karasa kusa dashi,yace haneefa what's wrong?? tayi shiru,ya sake cewa meya faru kike kukane haka?? Still batayi magana ba hasali ma hawane ke kara xubowa daga fuskar ta,cikin yana yin damuwa yaya Abdul yace ehhnn ina jinki,muryar ta na rawa tace ba komai,yaya Abdul yace,no no no no no,banyarda ba,haneefa tace mo"..momy ta katseta,tace dalla can rufawa mutane baki,Abdul yarin yar nan sata ta koma a gidannan,250,000,naira ta dauka jiya a brief case dina,a fili kamar baxata aikata ba.




Abdul yace haba momy,me haneefa xata dau kudi tayi dashi?? Momy tace ok dama ka saba bin bayanta ai,yaya Abdul yace bahaka bane amma dai gaskiya momy kisake duba kudinnan da kyau,ko kinyi misplacing dinsu.






Momy tace ba wani misplacing danayi,gatanan ka tambayeta inda ta kaimin kudina,momy ta juya ta shiga part dinta tare dayin murmushin mugunta aboye...😊😊.




Tausayin haneefa ya kama yaya Abdul,yace take heart haneefa,kije school idan kin dawo sai muyi magana karki makara.






Haneefa tace to ta shiga daki ta tauki jakarta da mayafi tasa takalmi ta wuce school...






Luv yhuuuu ol💞






By
Hauwa s.Ahmad&
Maryam y.Ahmad📚






Luv yhuuu ol..💞
[10/16, 7:58 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺
2016


26-30




✍✍




Tunda haneefa ta fita yaya Abdul yake tunanin ta,yana matukar tausayin ta,yadda momy take treating dinta a cikin gidan,kamar batasan ciwon haihuwa ba.




yana cikin wannan tunanin yaga kiran mai martaba na shigowa wayar shi,yayi picking call din sannan yace Hello Abba,mai martaba yace Abdul ya gida ya su momy?? Abdul yace lafiya kalau Abba,maimartaba yace,yace karfe 4:00pm jirgin mu xaiyi landing,sannan yace,,Abdul na matsu nasaka a kwayar idona,Abdul yace Abba ni kaina ji nake kamar kayi shekara da tafiyar nan,sarki salahuddeen yace wannan ne karo na farko dana farayin tafiya babu kai,haka kuma itace tafiya ta farko da batayi min dadi ba.




Mai marta ya kula cewar jikin abdul a sanyaye yake yace Abdul kodai baka da lafiya ne?? Naji muryar ka sabanin yadda nasabaji.




Abdul yace a'a lafiya kalau Abba,mai martaba yace Abdul karka manta nifa mahaifin kane,nine komai naka arayuwa,dan haka idan kana da damuwa ni yakamata ka fara fadawa.




Abdul yace daddy ba komai,mai martaba yacewa Abdul ka shirya idan na dawo inason nasan menene damuwar ka,Abdul yace to Allah ya dawo dakai lafiya.sukayi sallama.






Yadda marmartaba yaji yanayin Abdul yasan cewa kwarai yana da damuwa,fadamasa ne kawai bayasonyi,yana son Abdul sosai shiyasa komai kankantar damuwa yake fahimtar ta daga gareshi.




Ko kadan mai martaba bayason abin da xai batawa Abdul rai,ya dau son duniya ya dora masa,haryanajin idan Abdul baya tare dashi kamar babu wani babban sashene a jikinsa.Alokacin yaji kamar yayi tsuntsuwa ya dawo dan kasancewa tare da Abdul.






Tuki kawai haneefa take amma hankalinta baya duba yanayin yadda xata seta motar akan titin,bata ankaraba sai gani tayi ta kade wata yarinya da mamanta.




Da sauri haneefa ta fito a gigice,kafin kace meye wannan har mutane sun taru awajen,a rikece haneefa ta durkusa agaban wannan matar tana cewa sannu kinji ciwo?? Haneefa ta daga yarinyar,ganin hankalinta ya tashi sosai maman yarinyar tace yarinya karki damu banji ciwo ba,sai dai ni ta yarinyata nake,kalmar da matar ta fada ta tunawa haneefa inda yake mata ciwo,a ranta tace da ina da mahaifiya nima nasan xataji xafin duk wani abu daxai sameni.




Yarinyar tayi xumbur ta mike tace mama nima fa banji ciwo ba,haneefa taji wani irin dadi ganin yarinyar ta ware,tacewa yarinyar sannu,sannan tace baba ina saurine wallahi ban kula ba,tabasu hakuri sannan ta dakko 5000 a jaka ta basu ganin cewar suna da karamin karfi.




Motar da Naseer yake ciki na karasowa wajen driver'n shi ya yunkurin fita don yayima haneefa magana saboda tayi blocking hanyar,Naseer yace bari na fita da kaina,driver'n yace to.


Naseer ya fito cikin wata bakar suit,ya daura red neck tight ne a wuyanshi,yayi kyau sosai,Naseer kyakykyawan saurayine maiji da kanshi,shine first born wajen mai girma governor'n kano Alhaji muhammad salees.




Ya karasa kusa da haneefa ya nuna ta yace ke wannan wanne irin sakarci haka? Kinxo kinyi blocking hanya,ta sama kike so mutane subi ko yaya??




Haneefa ta watsawa naseer kallo da kyawawan idanun ta,tace malam kayi hakuri bawai nayi hakan intentionally bane,bata sake magana ba ta juya kawai ta shiga motar ta ta nufi makaranta.




Naseer yayi mamakin yadda haneefa ta bashi ansa cikin masalaha,yadda yaga tsananin kyan halittar ta ya dauka xatayi girman kai,gwiwar sa tayi sanyi yaji kawai ta gama birgeshi,yayi wani shegen murmushi ya ciji gefen lebensa kadan ta gefe daya,sannan ya koma cikin mota.


Haneefa na shiga school tayi roushing xuwa class,kowa yayi tsit sun fara test din wasu ma har sunfito,5ive minute ya rage ayi submitting gabadaya,lecturer'n bai hana haneefa shigaba,kawai cemata yayi tym na cika xai karba, he will not wait for her,haneefa ta yarda tayarda akan hakan.




Haka tayi test din cikin minti biyar,kowa yayi sunmitting.




Already hidaya ta fita dama,haneefa na fitowa daga hall din ta wuce wajen da suka saba xama ita da hidaya,tana tuwa ta xauna,hidaya ta jefo mata tambaya kamar haka.


Haneefa ya akayi kika makara sosai haka?? Haneefa tace wallahi na dan bige wasune a hanya shiyasa,sai da na tabbatar da lafiyar su sannan na taho,hidaya tace eyyyahhh Allah ya rufa asiri,haneefa tace amin ya Allah.Daganan haneefa bata sake magana ba,tunani kawai ta tafi wanda har ya kaita ga immagination,harta hasko a idan xuciyarta mai mar taba yace ta kwashe nata ya nata ta bar masa gida,ita kuma sai kuka take.






Ashe har a fili hawane ke xubowa daga idon ta.


Hidaya ta xuba mata ido har tsawon 2minutes abin yana bata mamaki,amma inaaaaa haneefa batasan tanayi ba.




Hidaya tace hanny me yake damunki?? Haneefa tayi firgigit ta dawo daga immagination din da take,tace ba komai.




Hidaya tace haneefa wanne irin tarayya mukeyi?? Ace abu yana damunki amma inaji ina gani bani da matsayin daxaki fadamin,nasha ganin yanayin ki cikin damuwa idan na tambayeki sai ki nuna ba komai.




Ni ina ganin bai kamata ba.




Haneefa tace am sorry hidaya cikin kuka take maganar,tace it's a personal problem.




Hidaya ta bata rai tace haba haneefa,gaskiya am highly disappointed,☹☹ banyi tunanin xaki iya boye min wani abuba,aganina munxama daya kuma ko ban miki maganin abinda yake damunki ba xan iya baki shawara kuma nayi miki addu'a,wallahi haneefa ba abinda xan iya boye miki atare dani.




Jikin haneefa yayi sanyi,tace hakane hidaya.






Haneefa tace,hidaya yaune ranar farko da xan fara bayyana sirri na ga wani mutum,ina nufin kece ta farko data fara saninin sirrina bayan 'yan gidan mu.




Xan baki labarin da xaki dade kina mamaki,magana haneefa take amma ta kasa tsayar da hawayen da yake xubowa daga idonta.


Hidaya tasa handkatchief ta gogewa haneefa hawayen dake fuskarta.tace dan Allah haneefa ki daina kuka ina jinki meyake faruwa???






Luv u more guys💞



By
Maryam y.Ahmad
Hauwa s Ahmad.




For call
08033660286
08063495753.


💞💞💞
[10/16, 7:58 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺
2016


31-35




📚✍




Haneefa tace,hidaya ni da kike gani ba 'yar mai martaba salahuddeen Adam bace.


hidaya da haneefa tare sukayi secondary school,shiyasa maganar da haneefa ta fada ta bawa hidaya mamaki,tace kina nufin ba Abban kune ya haifeki ba??




Haneefa tace hakane bashi ya haifeniba,ta fashe da kuka,😭idon ta yayi ja kamar barkono,haka fuskarta,saboda haneefa farace tasss ko yaya ranta ya baci sai fuskarta tayi ja balle idan tayi kuka.


Hidaya tace ki daina kukan nan haka pleassssse kanki xaiyi ciwo,haneefa tace dolene nayi kuka hidaya😭😭.




Saboda bansan ko daya daga cikin iyayena ba,tun ina da shekara biyu wani bawan Allah ya tsince ni a bakin titi rike da takarda a hannuna wadda take tauke da rubutu kamar haka.


Don Allah ga 'yatanan amana duk wanda ya tsince ta ina mai rokonsa da yariketa amana,bansame ta ta hanyar fasikanci ba,dan Allah a taimakeni wajen bata tarbiyya mai kyau.




Kamar yadda mahaifina ko mahaifita ta rubuta a jikin paper,inaji ajikina ni ba 'yar da akayi fasikanci aka samenibace,😭😭.


Ina bakincikin yadda iyayena sukayi abondoning dina,kullum addu'a nake Allah ya bayyana munsu,ya ganar dasu dan su dawo gareni,tun bani da wayo amma har yanxu shiru ba labarin su.😭




Hidaya tace insha Allahu Allah xai bayyana su.


Haneefa ta cigaba da cewa,hidaya anyi sanarwa gidan radio,television ba iya jaharnan ba har other states amma iyayena sunki bayyana kansu.Daga karshe mai martaba ya yanke shawarar rikeni a hannunsa,alokacin bani da wayo ko sunana bana iya fada idan aka tambayeni,alokacinne mai martaba ya samin sunan matarsa ta farko da Allah yayi mata rasuwa,hajiya maryam,ake kirana da haneefa agida,a school kuma da maryam salahuddeen Adam.




Hajiya maryam itace matar mai martaba ta farko,danta daya wato yaya Abdul Allah yayi mata rasuwa,sannan Abba ya auro maman Amal.




Lokacin da aka kaini gidan yaya Abdul yana da shekara bakwai,Amal kuma tana da shekara uku,tare aka samu a makaranta,komai tare mai martaba yake mana baya ban ban tamu ni da Amal,wanda momy ko kadan batason hakan,tun bani da wayon daxan gane har naxo na fahimta.




A lokacin da ya wuce bakiga yadda muka shaku da Amal ba muna yara,Amal tana sona sosai amma momy ta hana mu wasa tare daganan ta cusawa Amal tsana ta kuma ta nuna mata cewar ni ba 'yar gidan bace.


Momy ta mai dani kamar mai aiki haka kawai xata kirkiri aiki ta bani har wanda yafi karfina,burinta kawai nasha wahala.Bayan akwai wadatattun bayi da masu aiki agidan.




Duk abin da momy take yimin maimartaba bai sani ba saboda yawancin lokaci yafi xama a fada,idan ya gama da fada kuma bangarensa yake komawa momy tasameshi acan.
Haka muma idan muna da bukata ko xamuje wani waje can muke xuwa mu sanar dashi.




Tun bansan bani da iyaye ba sai da momy tasa na sani,kulawar da maimartaba yake bani yasa duk inda naje sunansa nake kira.




Wata rana ina waya da wata kawata sai take cemin banason xuwa gidan su,sai nace mata xan tambayi Abbana insha Allah xanxo.kawai sai ji nayi momy ta katseni.


Abban ki a ina?? Kije dai can duniya ki nemi ubanki,maimartaba bai haifi shegiya ba kin gane ai?? Kike wani iyayi wai Abban ki mtswwww.


Nasa kuka bata bari nayi magana ba ta wuce part dinta.


Dama nasan ba momy ce mahaifiyata ba,amma duk a tunanina maimartaba mahaifine,na fita da sauri naje wajen mai martaba ina kuka nafada masa,yasa aka kirata yayi mata fada sannan yace damme xata fadamin a tym din,sannan yace idan lokacin daxata sani yayi ai xansa ki fadamata ko ni nafadamata da kaina.
Momy harda kukan munafurci,ta fara bawa mai martaba hakuri.




Ni kuma na kasa jurewa,na ringa kuka,nace dole sai mai martaba ya nunamin iyayena shine ya kwashe labari yabani.




Da farko yaya Abdul ma bai fahimci momy tana yimin mugun riko ba sai kwananan,saboda ba akasarnan yayi karatuba,kuma tana kuntatamin ne ta hanyar da baxai fahimta ba.


Ina primary six nasan cewa mai martaba ba mahaifina bane,Abba yace daga ranar bayaso yaji ankara tayar da maganar.




Daga lokacin ba wanda ya sake,sai yau dana fada miki.


Kuma na yanke shawarar guduwa na bar gidan,saboda tun ban isa yin saurayi ba ake xuwa kamun aurena sai momy ta xage tace ni 'yar cikin shegece,😭😭daganan baxa'a sake maganar auren ba.


Jiya kuma cewa tayi na satar mata kudi a brief case dinta har 250,000 Naira.

Fuskar hidaya ta gama jikewa da hawaye jin labarin da haneefa ta bata,tace a'a haneefa karkice xaki bar gidan,watarana gaskiya xatayi halinta dan Allah ki kara hakuri.


Haneefa tace kiyi hakuri hidaya gaskiya baxan iya jure cigaba da xama a gidannan ba.


Hakadai hidaya tai ta bawa haneefa hakuri,sai karfe 6:15pm suka bar makarantar.




By
Hauwa s.Ahmad&
Maryam y.Ahmad💞




💞💞💞💞
[10/16, 7:59 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺
2016


36-40




📚✍






EMIR IS ON HIS WAY BACK...✈


Motoci goma shabiyu Abdul ya umarci sarkin gida da'a shirya don xuwa taro mai martaba.




Kamar yadda Abdul ya fada hakan sukayi,sarkin gida yaxo ya gurfana a gaban Abdul wanda ke xaune fada kan kujerar mai martaba,ya dunkule hannu ya daga sama alamar jinjina,yace Allah ya taimaki magajin sarki angama shirya motocin.


Abdul yace ina ganin xamu iya tafiya,fadawan dake tsaye a gefe suka xagaye Abdul ya mike kamar maimartaba,sai faman kirari suke a haka har suke raka Abdul jikin motar da xai shiga,aka bude masa kofar motar, sai da suka tabbatar ya shiga ya xauna sannan suma suka koma wata motar.






A layi motocin suke tafiya,daya daga cikin motocin mai jiniya ce,sai faman yi take,nan danan jama'ar kano suka fahimci ranar ne mai martaba xai dawo,har wani farinciki suke da nishadi,kokadan basason suji mai martaba xaiyi tafiya,saboda suna tsananin jin dadin mulkinsa tamkar na mahaifinsa da yayi murabus ya bashi,saboda adalcinsu da tausayin talakawa.




Haka sukayi parking motocin a airport suna jiran isowar mai martaba.




Ba'a jima da yawa ba jirgin da mai martaba yake ciki ya sauka,mutane sai daga masa hannu ake,fadawansa kuwa da sauri suka karasa matattakalar jirgin.


Abdul ya tafi da sauri ya rungume mai martaba,sarki salahudden ya shafa kan Abdul sannan ya rike hannunsa fadawa suka raka sarki da Abdul mota majesticallay,wanda har suka shiga motar hannun sarki da Abdul a rike yake.




Hhhmm lallai akwai kauna mai tsanani da shakuwa tsakanin sarki salahudden da dansa Abdulrahman💞💞




Haka suka nufi gida drivers din sunayin tuki cikin nutsuwa,duk unguwar da suka wuce munane suke dagawa mai martaba hannu saboda tsananin kaunar da suke masa.




Motocin na tsayawa a harabar gidan,fadawa suka xo suka baxa manyan rigunan su dan kare mai martaba kar aga fitowar sa,bayan ya fito suka rakashi fada,bayan ya xauna sukayi masa sannu da xuwa tare dayi masa fatan Allah ya bashi lafiya,yace amin,haka sauran bayi da ma'aikatan gidan suma suka gaisheshi tare da yimasa sannu da xuwa.






Baifi minti goma a fada ba ya wuce part dinsa inda ya tarar already momy tana jiransa,da sauri tayi hugging dinsa tare da yimasa kisss🙈 tace sannu da xuwa maimartaba,sarki yace yawwa uwar gida sarautar mata,ta kama hannunsa suka karasa ciki,tacire masa glass din dake idonsa ta rage masa kayan dake jikinsa,sanna ta mika masa towel,ta kalle maimartaba cikin kissa da kisisina tace sweetheart kafarayin wanka sai kaci abinci ko? Yace hakane dama nagaji hakan will be more better.


Kafin ya fito daga wanka hajiya fatee ta fito masa da kayan da xaisa da sauran abubuwa na amfani daxai bukata idan ya fito.


Bayan ya fito hajiya fatee tayi wa maimartaba dumping ruwan jikinsa,ya shirya cikin wasu kaya na sarauta amma basu da nauyi ko kadan,hajiya fatee tayi masa jagora xuwa dining don cin favourite dinsa data tanadar masa,sakwarace miyar agushi da ganda with fish and meat,sai papper chicken,dambun naman xabi da drinks.mai martaba na xama kafin ya faracin abinci yace ina Amal da haneefa suka shigane?? Momyn Amal ta danyi murmushi hade da yatsine fuska kadan tace uhhmm suna school gaba dayansu.




🌺'YAR MULKI🌺
2016




41-45


📚✍






Haneefa na dawowa daga school,tasa kafarta a hanyar falo kenan dai dai corridow taji an jawota a hankali tare da rufe mata baki da hannu,da yake magriba tayi corridow din akwai dan duhu bata gane waye ba,sautin muryar baba mareeya taji,tace haneefa kinsan cikin gida bashine wajen aikina ba,shiyasa na labe anan nake jira kidawo,nasan watikil sai gobe xamu hadu,shiyasa najiraki anan,so nake nace miki mai martaba ya dawo kuma idan aka kiraki akan maganar kudi karkiyi nuku-nuku kicewa mai martaba ke baki dauki kudiba nasan xata iya tilastaki kice kin dauka karki sake ki ansa laifin da bakiba kinji? Cikin tsoro kar wani ya kamasu haneefa tace to baba mareeya,nagode xanyi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment