Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya ƙara ƙanƙame micijin ya cigaba da yin baccinsa abinsa. Da yake wajen sha biyu da wani abu ne Inna ta yi masa wannan aiki, wajen ƙarfe haɗu da wani abu na asuba sai ya ɗan yi juyi kaɗan ya miƙa hannu idanunsa a rufe ya ja bargo ya rufe ƙafarsa da ta buɗe. Gefen kan micijin ne a wajen hancinsa dan haka da kan micijin ya dan dunguri hancinsa sai ya ɗauka Sadiyarsa ce a cikin baccin aikuwa ya ƙara ƙaƙumeta tare da ƙara gyarawa hancinsa zama a saitin kan micijin yana cigaba da baccinsa. Ƙaran wayarsa na alerm ɗin da ya sanya shi ne abu na farko da ya farkar da shi daga bacci, dafe micijin ya yi da hannu ɗaya duk zatonsa Sadiya ce dan a bacci -bacci yake ya ma manta cewa Sadiya ta haihu kuma Inna tana ZAMAN WANKA babu ma dalilin da zai sa su kasance shi da Sadiya a katifa ɗaya har ma a bargo ɗaya indai Inna tana nan.

Ɗayan hannun ya miƙa ya lalumo wayarsa da ke neman ɗauki, har lokacin idanunsa a rufe ruf, sai da ya ɗakko wayar ne ya ɗan buɗe idanunsa cikin yatsina fuska ya kalli screen ɗin wayar, alerm ɗin ya kashe yana shirin maida wayar ya ajiye ya tashi sai kawai hasken fuskar wayar ya sauka a kan micijin, da mamaki ya ji hannunsa ɗaya rungume da abu, ƙwaƙwalwarsa ce ta fara kai masa tunanin me Sadiya take yi a jikinsa bayan Inna tana gidan, dan son ta addabi mutane da sababi, idanu ya ware fesss a kan micijin wani uban ihu ya ƙwala ya buɗe bargon yana ƙoƙarin tashi zaune dan gabaɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, gabansa sai faɗuwa yake, hannu ya kai yana son yakice micijin daga jikinsa amma me sai ya ji a manne suke da juna a cikin singlet ɗaya wacce dama ta ɗan masa faɗi kuma sai micijin ya ƙara taɓata tare da buɗata duk da hakan dai a ɗame take a jikinsu sun zama kamar tif da taya.


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Wace ƙarar kwana ce ta sanya wannan tsautsayin kasancewa da ni" Ya faɗa a zuciyarsa wasu hawaye da bai san da su ba suka fara yiwa fuskarsa tsinke. Dakyar ya samu ya tashi zaune yana jin jelar micijin a kan cinyarsa, haka ya tashi yana kiciniyar ɓanɓaresa daga jikinsa amma sanyin da jikinsa ya yi ga kuma karkarwa da kuma tsabar fargabar da yake ciki ya kasa yin haka. Tsaye yake so ya miƙe amma ina hakan ya gagareshi, dan haka kawai sai ya yanke hukuncin ta tafi bedroom neman ɗauki dan bashi da ƙwarin gwiwar da zai iya yin ihu a jiyo shi har a taimaka masa, gashi kuma ya ga da alama ma micijin bacci yake dan haka ba ya so ya tashe shi a samu matsala dan haka sai ya yanke hukuncin tafiya ɗakin ko da, da rarrafe ne. Hannayensa duk biyun ya ajiye a ƙasa yana ɗan lallaɓawa ya saukar da gwiwoyinsa daga kan katifar a haka ya fara rarrafawa micijin na cikin singlet ɗin kamar dama a nan aka halicce shi.

"Yiiiii, wayyo Allah, yau kuma haka na tashi ni Imran" Yake kukan cikin ɗan ƙasa da murya yana tsoron kar kukan nasa ya tashi micijin.

A haka har ya je tsakiyar bedroom ɗin yana ɗan rarrafawa kamar wanda aka cirewa laka, dan ko kaɗan bashi da ƙarfi gwiwar tasa ma idan ya ɗaga ji yake kamar wanda aka mata dabaibayi da igiya.

"Sadiya, Sadiya,Sadiya" Cewar Imran cikin raɗa-raɗa, kamar wanda aka shaƙewa wuyansa. Inna da tun falkawar Imran tana jin yadda yake ta tutumurtu da miciji a cikin singlet, dan hatta shashshekar kukan da yake duk tana jin sa. Bare kuma yanzu da ya zo tsakar ɗakin da suke ji take kamar ta tashi ta taka rawa dan murna saboda kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Tun yana kiran da bakinsa har ya dawo yana ɗan buga jikin gadon a hankali dan shi ba ya so ko kaɗan ya tashi micijin ya je ya sare shi a samu matsala, hakan ne ma yasa yake lallaɓawa ya tashi Sadiya domin ta kawo masa ɗauki dan ya san ita kaɗai ce za ta taimakeshi. Ganin dai Sadiya da shegen nauyin baccinta ba za ta tashi ba dan har ƙafarta yake ɗan ja amma shiru sai ka ce wata matacciya. A hankali ya lallaɓa ya koma wajen setin da Inna take kwance, dan ya tashe ta, ta taimaka masa duk da ya san karon su da Inna ba daɗi amma yaya ya iya dole ce uwar naƙi za ta sa ya nemi agaji a wurin Inna dan ko kusa bai kawo cewa ita ce ummul aba isin shigar da micijin cikin jikin nasa ba.
"Inna! Inna!! Inna!!!" Ya faɗa yana ɗan ɗaga murya kaɗan dan ji yake tsabar tsoro fitsari na neman kuɓuce masa dan har cikinsa ma murɗawa yake ba ya so kuma a yi abi kunya dan ya san dai matasawar aka ɗauki wani lokaci ba a rabashi da micijin ba to ba kallon fitsari da kashi ba da a ce maza na haihuwa to ya tabbata har haihuwa sai ya yi ko da kuwa hanji ne zai haifa.

Inna kuwa da dariya ke neman kunya tata ta ƙara danne dariyar ta shiga sakin wani munshari kamar wata jakin dawa, ita a dole bacci take, amma kawai Imran lura ne bai yi ba da ace ya lura har cikin Inna zai ga yana loɓawa irin na ƙyaƙyata dariyar nan.

"Innarmu, Innata, Innar Malam, ɗaya tamkar miliyan a wajen Malam ki tashi ki taimake ni kar in mutu in bar iyalina, dan ko micijin bai sare ni na mutu ba to tsabar fargaba za ta sanya zuciyata ta buga in mutu" Ya faɗa cikin kuka yana jijjiga ƙafar Inna.

"Kai duniya , wato wuya in ji tsula, wa ya faɗa maka barno gabas take, yaro ya ga uwar bari, to da wa ya ce maka karo da Azumi abu ne mai kyau, wai Imirana ne ke cewa Innarmu, kai har da Innata ma, wai ni Azumi da ya rainawa hankali da wayo ni ce Innarsa" Ta faɗa a zuciyarta tana dariyar mugunta.

"Wayyo zan yi gawa" Ya faɗa yana sakin kuka a hankali. Wani juya Inna ta ɗan yi ta koma ɗaya ɓangaren tana sakin munshari, so take sai ta gama wana shi sannan za ta tashin, a haka ya cigaba da magiya har dai ta ɗan tashi tana murtsuka ido duk da ba haske a ɗakin amma kuma kana iya hango hasken farin wata ya ɗan shigo ɗakin ga kuma asuba ma da ta kawo ki masallatai sao kiran assalatu ake.

"Waye wai ya dameni da shegen kira kamar wanda na ci bashi ban biya ba" Cewar Inna cikin muryar bacci wai ita ala dole yanzu ta falka daga bacci"

",Inna jikan ki ne Imran" Ya faɗa cikin sanyin murya yana addu'a da fatan Allah ya ɗora shi a kan Inna ta taimaka masa kar ta ja masa rai.

"Wa ka ce sunan naka, ba Imirana bane?" Ta faɗa dariya na son fito mata.

"Eh Imirana ne" Ya faɗa kamar yadda take faɗa masa dan shi gabaɗaya fatansa kawai su rabu lafiya dan ba zai iya da sabgar Inna ba gwara ya lallaɓata su rabu lafiya.

"Wai menene halan, ciwon ciki ne ya koro ka gabannin assalatun nan?"

"Dan Allah Inna kunna fitila ki ga, wallahi Hassan ne a cikin rigar jikina"

Murmushi Inna ta yi tare da tashi ta sakko ta kunna fitalar aikuwa haske ya gauraye ɗakin.

"Meye wai ka wani surƙusa kamar mai naƙudar da ke yinƙurin haihuwa?" Cewar Inna tana danne dariyarta ganin yadda Imran yake kallonta idanu a gwagwgwale.

"Inna kalli ki ga cikin rigata" Ya faɗa yana daga durƙusan hannayensa a ƙasa haka gwiwoyinsa ma.


Ɗan yatsina fuska ta yi, sannan ta ɗan ranƙafa ta leƙa wai ita a dole bata ga micijin ba daga yadda take a tsaye. Ganin micijin da ta yi sai ta wani taɓe baki tare da sakin wani tsaki da ya matuƙar ɓatawa Imran rai, ta ce.

"Wai dama a kan ɗanka kake ta ƙwala min kira ka katse min baccina na gabannin asuba mai daɗi tsiya? Kana ta rafka kuka kamar an aiko maka cewar Amina ta mutu, wai me yasa kake da ɗan karan raki ne kamar mace"

Wani haushi ne ya turnuƙe Imran amma haka da daure ya ce.

"Wallahi Inna kawai ina tashi daga bacci na ganshi a jikina ban san yadda aka yi ba, ki taimaka ki fitar min shi ko ki taya ni tashin Sadiya ta fitar min da shi dan na tashe ta bata tashi ba"

"To sai me dan ya je wurinka, ina ce dai ita kaɗai Sadiya ke riƙitu da shi kuma dan ya je ya shiga rigarka shi wani abu wataƙila so yake ka karɓeta ma'ana nono yake so ka bashi...

"Nono kuma Inna?" Ya katse Inna da tambaya cikin tsoro

"Nono mana baka ga inda ya shiga ba kawai ka bashi ya tsotsa ka bani shi in kwantar da shi"

"Haba Inna wace magana kike haka wai? Nono kuma sai ka ce wata mace, baki ga ba yau d bai dawo mutum ba ko ita ma uwar tasa bata shayar da shi ba sai ni da ba nono nake da shi ba za ki ce wai na bashi"

"Ya baka da nono ɗin nan, kuma wanda Allah ya halitta maka fa?"

"Inna!!! Wai me yasa kike haka dan Allah ki bar faɗa ma kar ki sa ya kafa min haƙora a ƙirji yana neman nono in bai samu ba ya cije ni in shiga uku"

Wata dariya Inna ta fashe da ita ta ce

"Imirana ni ka sanya wa ɓawon ayaba?"

Wani irin zare ido Imran ya yi jin furucin Inna.

"Ba dai matar nan bace ta sanya min micijin nan ba saboda ƙarfin hali...

"Na ce ba ni ka sanya wa ɓawon ayaba ya kada ni ba??? " Muryar Inna ta katse masa zancen zucin da yake.

"Inna ni ba da niyya na ajiye ba ban san ma na jefar ba kuma tsautsayi ne ya kawo kika faɗi"

"Ni ban san miciji ma ya je wurinka ba, kawai dai na ga kana buƙatar taimakona shi ne nake faɗa maka ta yaya zan taimaka maka bayan kai ma ka sa na faɗi"

"Dan Allah Inna ki taimaka min"

"To zan taimaka maka amma sai ka yi abin da nake so dan ka san ko a nan Kano ba a aikin banza, idan kuma ka ƙi to dan wannan matar taka mai kamar mesa ba tashi za ta yi ba gwara ma ka min abin da nake so"

"To Inna faɗi" Cewar Imran cikin ƙosawa da maganganunta da ya matsu a raba shi da micijin nan da ya masa ƙabe-ƙabe.

"So nake ka min rawa"

"Rawa kuma Inna?"

"Rawa mana in ba haka ba, ba zan cire maka ba"

"Ni da bani da ƙafa da me zan taka rawar"

"Gurguncewa ka yi ne?"

"A'a amma ba zan iya tsayuwa da ƙafafuna ba saboda gudun matsala" Inna ta fahimci me yake son faɗa dan haka sai ta ƙudurta ko ta ina ya biyo tana da hanyar ɓullewa.

"Ka min rawar a durƙushen nan da kake"

Shiru ya yi sai kuma ya ga mafita yake nema dan haka sai ya shiga rawa daga tsugunnen da yake yana ta rausaya kai. Kallonsa kawai Inna take dariya na cin ta.

"Haba Imirana rawa haka salam -salam babu ko kiɗa"

"Haba Inna da gabannin asubar nan wane irin kiɗa kuma ni da nake so na je na tafi masallaci"

"To jeka masallacin da micijinka ma gani ina ƴan masallacin basu dare sun barka ba, kowa gudu zai ke kamar ya ga fatalwa"

"To ai ban san ya zan yi kiɗan ba"

"Waƙa zan ke maka kana yin rawar"

"To" Ya faɗa kamar ya fashe da kuka
In na faɗa sai kana min amshi, kana dawa kana cewa maliyo"

"To"

"Ɗan maliyo maliyo"

Shiru ya yi bai ce komai ba takaici duk ya cika shi tsohuwar na son kaishi bango.

"Ba za ka yi ba?"

"Maliyo"

"Ya je ina ne"

"Maliyo"

"Ya je ilori"

"Maliyo" Cewar Imran yana amshi yana rawa ransa sai ƙuna yake yana jin kamar ya mammake Inna ga takaicin nauyin baccin Sadiya da ya addabeshi.

"Kake zazzakuɗa wa mana" Cewar Inna da ke ɗan tafi ƙasa-ƙasa.

Ɗuwawu ya shiga zazzakuɗa wa yana yi hawaye na zuba gashi ba ya so micijin ya tashi, amma ya fahimci da gangan Inna fa sa yake rawa wai har da wani zazzakuɗa wa kawai dan ta sanyashi a bala'i.

Yana cikin rawar sai jin inna ya yi ta sauya baitin waƙar.

"Mu kama sana'a mata macen da bata sana'a aura ce, lale-lale maraba da ke zinariya"

Ai kawai Imran da ya lura Inna dan ta yi ta sanya shi rawar ne ba wai za ta rabashi da micijin bane sai kawai ya saki wani kuka mai ƙarfi wanda hakan ya sanya Sadiya tashi ba shiri, ta tashi a firgice jin kuka Imran tana tashi ta yi arba da Inna da ke tsaye kan Imran ta daddage tana tafi da waƙa.

"Ikon Allah yau kuma me yake faruwa wane irin dogon bacci na yi ne da ake wannan bidirin ban sani ba" Ta faɗa a ranta tana saurin sakkowa daga gadon.


*Masu fitar min littafi ku sani haƙƙina ne, ku ma masu karantawa baku biya ba haƙƙina ne, kowa ya san Allah na gafarta zunubai gabaki ɗaya amma ba ya gafarta haƙƙin wani a kan wani! dk mai so ta biyabta karanta 300 kacal*

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375




Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134




*I* ➡️ *J*




" Subhanallahi Abban twins lafiya" Cewar Sadiya lokacin da ta sakko idanunta a kan Imran. Kafin Imran da ke kukan zuci da sarari ya yi magana Inna ta yi karaf ta ce.

"Haba Halima yo kya yi maganar lafiya ma kina ganjn mijinki a wannan hali na durƙuso, ƙura'ani ni duk tunani na naƙuda yake ashe wai duk labarin ƙanzan kurege ne mutum a dudduƙe ya zo cewa yake Innarmu, Innata" Cewar Inna tana sakin dariya. Da mamaki Sadiya take kallon wani uban gumi da hawaye ratata a fuskar mijin nata.Ga miciji a cikin singlet ɗinsa sai wani nishi yake fitarwa kamar wanda aka biyo da gudu.


"Ya Allah ni dai ina ganin abubuwan da na kasa gane ko fahimtar inda suka dosa shin wai meye tsakanin Inna da Imran ne?" Sadiya ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta tana miƙa hannu za ta fara ƙoƙarin cire masa Hassan ɗin.

"Haba Sa'adiyya wai me yasa kika raina ni ne ya za a yi in yi ta maza in bar baccina dan in taimaki mijinki kina can kina baccin asara, muka ƙayyade zai min rawa da amshi ina masa waƙa amma yanzu ki zo za ki cire masa micijin nan salin alin, so kike ki barni da haƙƙin rawar da ya mini ban cire masa micijin ba ai ni ya kamata na cire masa...

"Sadiya umarni nake baki idan kina son ki shiga aljanna ki cire min micijin nan dan Allah" Imran ya katsewa Inna maganarta dan ya ga jan maganar za take ta yi shi kuma numfashi ma dakyar yake iya yi dab komai yake da faruwa da shi.

"Ke dan Allan can bani wuri ni ɗin da ya rainawa hankali ni zan cire masa, in banda ma fallasa auren bashi ai da tuni ma an yi komai an gama ba tare da kin sani ba, amma saboda girman kai rawanin tsiya irin na Imirana ya ƙi taka rawa da kyau, saboda ya gama ganin makwancina wato ga ƙaramar danga me daɗin tsallaka shi ne yanzu kuma ya ce ki cire masa" Cewar Inna tana ture Sadiya gefe. Sadiya tana shirin magana amma Inna bata, bata dama ba, ta hana ta, hannunta ta kai bayan Imran ta daddage ƙarfinta cike da mugunta ta sanya faratanta ita ala dole singlet ɗin za ta cire tun daga farkon bayansa ta fara karta faratan ta har wuyansa tana ɗago singlet ɗin haɗe da farcen nata, ta kusa gama ɗago singlet ɗin wani uban raɗaɗi ya ratsa Imran na farcen da Inna ta karta masa amma haka ya daure dan burinsa kawai a rabashi da micijin.

Haka ta haɗo da micijin da singlet ɗin ta cire amma ko lokacin da ta zo cirewa daga wajen kunnesa sai da ta haɗa da kunnuwan duka biyu ta murɗe yadda zai ji a jikinsa ba tare d Sadiya ta lura ba, haka dai ya danne har wani ɗan daddaurewa yake.

" Yanzu na san na yi wai mahaukaci ya taka kashi, to Halima sai gareki kuma tun da an cire ai ta faru ta ƙare an yiwa me dami ɗaya sata, har a ce ina nan a bar Imirana cikin damuwa ai idan da kara akuyar gidan sirika ma iya ce da ke dashi ai duk ɗaya ne a wurina ba banbanci" Ta faɗa tana miƙawa Sadiya Hassan da singlet ɗin gabaɗaya.

Wata uwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin raɗaɗin bayansa da Inna ta kartawa farce da kuma kunnuwansa suna zafi amma babu yadda zai yi sai dai ya ƙuduri wani abu da ban, sai yanzu ya gama fahimtar cewa babu makawa Inna ce ta kai masa micijin nan.

"Lallai tsuhuwar nan al'amarinta ya girmi tunani na "Ya faɗa a ransa yana mamakin irin ƙarfin halin Inna.

" Yau dai na ga abin da ya turewa buzu naɗi yo banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika wai yau ni Imirana ke kira Innata" Ta faɗa tana dariya.

Wani takaici ne ya ziyarci Imran lokaci guda abubuwan da ya sha faɗa cikin gushewar hankali da tsananin tsoro suka rinƙa dawo masa haushin kansa ya rinƙa ji da kuma hashin nauyin baccin Sadiya ai da ta tashi da wuri da bai nemi taimakon Inna ba wanda hakan gashinnan ya zame masa abin gorantawa. Amma dama ya san duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa.

"Yo kuma ai sai ka tashi daga tsugunnen ka tafi masallaci tun da dai ka yi abin kunya yau" Cewar Inna.

"Dama tashi zan yi" Cewar Imran yana ji kamar ya kwaɗe Inna.

"Ba niyya ango ya kwana da wando, yo kana durdurƙusar da kai alamun kunya ka kasa tashi za ka ce wai dama tashi za ka yi, ai fa ka sanyawa zuciyarka dangana Imirana faɗan da ya fi ƙarfinka kake midashi wasa sai ka zauna lafiya da mutane, ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki"

"Wai kamar ya Inna" Cewar Sadiya da ta fara fuskantar wani abu kenan dai Inna ce ta haddasa komai.

"Abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro, wato ke uwar ƴan son miji shi ne kike bin ƙwaƙƙwafi, kawai ki barni da Imirana dan kura ce kaɗai ta san gidan mai babbar sanda" Ta faɗa tana niyyar fita daga ɗakin.

"Sadiya miƙo min riga a drower" Ya faɗa yana jin haushin Inna na ƙara azalzalashi a kan ƙin yin da na sani a kan abubuwam da ya aikata mata a baya da ma wanda zai aikata mata nan gaba, duk da dai ya san ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma rana dubu ta ɓarawo ɗaya ce tak ta me kaya.
"Maza miƙo masa rigar ya tafi masallaci kar ya yi saki na dafe, na ga sai wani hararata yake abin da na masa bai gode ba yo Allah na tuba ban da dai abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake duk taimakon da nake yiwa Imirana a gidan nan ba ya gani kawai dan na sa ya min rawa na ce yake ɗan zazzakuɗa mazaunai yana kaɗa kai shi ne laifin da na masa" Cewar Inna tana kallon Imran fuskarta da alamar dariya, wata uwar harara ya doka mata.

"Wai tsohuwar nan ni za ta yiwa kissa, amma ba komai ki dai bi a hanakali kar tura ta kai bango, dan wanda bai ji bari ba zai ji hoho" Ya faɗa a ransa. Sadiya kuwa Hassan ta mayar kan gadonsa ya ɗakkowa Imran rigar dan gabaɗaya kanta ya kulle da abubuwan nan ko kaɗan Inna da Imran babu wanda ya ke tunanin halin da Hassan ke ciki, wai yana cikin halin ne ma har ya zama ana ɗaukansa dan cika wani buri, gashi kullum cikin ka ce suke ta ka gane dalili musamman ma shi Imran da, ko damuwa da bai yi ba da yawan magana amma yanzu sai take jin har magana yake yadawa Inna a wayance ta kasa gane bakin zaren.

Inna dai juyawa ta yi ta fice daga ɗakin ta je ta ɗauro alwala. Ta dawo tana ɗakko abin sallarta daga cikin jakarta sai ga Imran ya fito daga bedroom ɗin.

"Masallacin ne Imirana sauka lafiya" Ta faɗa tana ƙushe dariyarta ganin ya fito sai muzurai yake. Bai tanka mata ba ya cije leɓe ya sanya kai ya fita ya ɗaura alwala ya tafi masallaci dan zuwa lokacin ma har an kusa kaiwa raka'ar farko.


*HAJIYA*


Tun da ta baro gidan Imran bata zame ko ina ba sai gidan wani Malam Isuhu mai almajira ta daɗe tana jin labarinsa to da yake ma babu nisa sosai daga gidanta amma can sama da su yake. Tana zuwa ta tambaya aka ce yana cikin gidan da sallama ta shiga gidan bayan sun gaisa da matan aka faɗa masa ya yi baƙuwa, bayan an mata iso ta nufi ɗakin nasa tare da matarsa uwar gidansa ita ce ta raka ta har turakar Malam ɗin. Ɗakin cike yake da manyan qur'anai da littattafan addini a gefe guda, ga wasu carbuna manya manya da ƙanana hawan hawa. Zaune yake a kan darduma ya sanya gabansa gabas ga wani ƙaton carbi yana ja. Matar da ta rako ta tana shiga ɗakin ita kuma ta koma. Malam kuwa da ke ɗaura rubutu a leda rubutun cikin bokitin fenti babba, wanda ruwa ne kawai aka zuba tawada a ciki sai a ƙulla a leda ana baiwa mutanen da suka bayar da kuɗi a musu rubutu.
Dan haka ba ya rubutun tawafa kawai yake zubawa a ruwa yana ƙullawa jin an ce ana masa sallama shi ne ya rufe bokitin ya ɓoye wanda ya ƙulla ɗin. ya koma ya zauna a darduma ya fara jan carbi yana mismis da baki.

Sai da ya kai ƙarshen carbin Hajiya tana zaune sannan ya juyo gareta ta fara gaishe da shi tana masa ya fama da kuma ƙoƙari da jama'a, nan ya masa komai lafiya.

"Malam dama wani aiki ne nake so ka min a kan iska...


"Ai mun gama sanin me yake tafe da ke, duk na gani cikin mafarki tun jiya na san da zuwanki, dan haka indai ƙwanƙwamai ne babu abin da ya gagaremu ku da su sai dai ku ji ana labari" Ya katse Hajiya daga abin da take son faɗa masa a kan Hassan da take so ta ce ya je ya masa addu'a ko za a dace ya dawo mutum amma kuma shi sai ya nuna ya san komai ya hana ta ta masa bayani.

" To babu komai nawa ne abin sadaka?"

"Ai abin sadaka sai mun je muke faɗa, kuma yau ina da baƙi ba zan samu zuwa ba sai gobe da yamma"

"To babu damuwa, Allah saka fa alkairi"

"Amin" Cewar Hajiya, tana jin daɗi za a yiwa jikan nata magani.

"Ai kar ki damu mu nan fitar da mutsa mutsai ba komai bane indai muka karanta ayoyin qur'ani to tabbas Allah zai amsa"



Please Login or Register in order to submit comment