Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata uwar kwana a sukwane ko lanƙwasa babu.

Dariya Inna ta yi idanunta a kan motar Abid ta juyo ta dawo ciki tana ƙoƙarin rufe ƙofar sai gasu sun fito Imran da Abid.

"Innna har ya tafi baƙon naki?" Cewar Abid yana maida dariyarsa.

" Ya tafi mana amma dai ba baƙona bane baƙon Hassan ne kuma ya sallame su dan kuwa sun sha baƙar azaba kwakwa dai yau an sha ta a wajen miciji" Ta faɗa tana washe baki.

"Na gane Inna" Ya faɗa yana daria.

"Ba dai tafiya za ka yi ba?" Cewar Inna da mamaki.

"Ba tafiya zan yi ba kaya za mu ɗakko a mota kin san kayan rabawa ne gobe muka siyo"

"Ikon Allah wato ka ji kaɗan ka ji da yawa, yanzu baƙin halin Imirana har ya kai haka, a ce zai tafi siyayyar amma ina garin nan muna gida ɗaya ɗaki ɗaya amma ya kasa gayyata ta na raka shi sai ya je ya ɗakko ka".

Wani kallo Imran ya jefa mata irin na kina kai kan ki inda Allah bai kai ki ba, kafin ya raɓa ta ya wuce wurin motar.

"Au Allah wato ina maganar ma ka wuce ka bar ni wato ga karya yo in ba karya ba waye ake bari yana haushi shi kaɗai" Cewar Inna tana bin bayan Imran da harara.

"Rabu da shi Inna ba gani ba zan tsaya mu yi hira abin mu kuma kwantar da hankalinki indai kina nan to kuwa kafin ki tafi xan kai ki yawo a mota ta mu yi siyayya ki zaɓo abin da kike so in biya kuɗin" Cewar Abid yana kallon yadda fuskar Inna ta saki lokaci guda kamar an mata albishir da gidan aljanna.

"Allah Abida ka ce akwai zaɓar abubuwa masu yawa to aikuwa har sa kishiya kuka da sa kishiya tagumi zan ɗakko a wurin siyayyar"

Galala Abid ya yi jin furucin Inna dan shi dai ya ji ana cewa sa kishiya kuka ko tagumi maganin mata ne amma kuma mai Inna za ta yi da maganin mata.

"Inna sa kishiya kuka da tagumi za ki ɗauka in mun je siyayya...

"Oh Abida rufani ka saya ni, dan Allah kuke bari sai mutane sun mutu kafin ku binne su.

, yo in ba fallasa auren bashi ba har na tsaya yin maganar maganin banza da kai(Maganin mata) Magano na ce magano, to indai abin da ka yi zato to Allah tsari gatari da saran shuka, to ni ina nufin kayan ƙwalam wato kayan ciye-ciyen ne zan ɗakko sa kishiya kuka da tagumi, abubuwa ne zan ɗakko masu daɗi wanda ba za su lalace ba har lokacin da zan gama ZAMAN WANKANA in tafi da kayana gidan Malam sai in ke ɗakkowa ina ci ina jefar da takardar ko ledar yadda Tasalla da ta gani za take rafka uban tagumi da hannu bibbiyu, idan ta shige ɗaki kuma ta yi ta rusar kuka saboda baƙinciki, shi na ce zan ɗakko kar ka kai ni inda Allah bai kai ni ba ka sa ni a bakin duniya" Ta kai ƙarshen maganar tana kallo Abid da ke ta faman dariyar maganar ta.

"Na gane manufarki Inna, sai Inna ta mu ta Malam bada kan ki a sare ki je gida ki ce ya faɗi"

"Rass kuwa Abida ai ni ce ɗaya tamkar da miliyan a wajen Malam, kuma wallahi da ka ce Inna tamu sai ka sani wata ƴar bazawarar dariya dan ka tina min da daren jiya" Cewar Inna tana ƴar dariya tana kallon Imran ta gefen ido dama ganin ya kwaso kaya a mota ya taho ta faɗa.

"Mai kuma ya faru daren jiya Inna?" Cewar Abid yana dariyar shi ma

"Hummm kai dai bari Abida wallahi daren jiya ne abokin ka Imirana ya shiga wani hali na a zo a gani, sai ji ka yi Imirana yana, Innarmu, Inna ta" Ta faɗa tana sakin dariya irin mai ƙular da mutum ganin Imran ya zo wajensu zai fice, wani irin haɗe rai ya yi tare da wurga musu wata uwar harara. Abid kwa kawai dariya yake dan har ya hango abokinsa tabbas ya san Imran ba ƙaramar wuya ce za ta sa ya ce Innarsa ba.

"Hehehehe na dawo in ji ɗan yawon duniya, to wallahi ban san ana yi ba kunu a maƙota, kuma ban san harara ba sai ido ya faɗo ehe" Cewar Inna tana jefawa Imran hararar ita ma har da gatsi ne.

"Ƙyaleshi Inna" Cewar Abid dariya har kasa magana yake.

"Yo dama ai ba biya shi zan yi ba da ina biya Imirana ai da zamana a gidan nan bai kawo yanzu ba, ni kuwa na faɗa masa zama daram, kuma nan gani nan bari farar tunfafiya, labari kwa dole na bayar tun da ya yi abin da za a faɗa dan labari sai ma na koma ƙauyenmu in samu abin da za mu ke maimaitawa ni da aminiyata Tsahare muna darawa yo labarin abubuwan da Imirana ya yi daga zuwana zuwa yau ai abin a bayar da labari ne, dan ba tsoronsa nake ba, bada labari kuwa farillah ne tusa a masallaci, dan wallahi ina sane wai karuwa ta taka matar aure, dan kuwa ni na san karambanin akuya yasa ta leƙa ɗakin kura" Ta kai ƙarshen maganar tana wani juya ido tare da gatsine kamar wata matashiyar budurwa.

Abid kawai dariya yake a haka ya je ya buɗe motar ya ɗakko wasu kayan da wata leda mai ɗauke da apple mai yawa fari da kore ya miƙawa Inna, ta karɓa tana ta godiya kamar ta ari baki, a haka suka baro zauren dan dama a can ne tun da ya same ta za ta rufe ƙofa suka tsaya suke maganar. Ko da suka dawo ma haka ta zauna tana ta baiwa Abid labari dan haka kuwa ya zauna yana ta dariya har da riƙe ciki, amma kuwa saboda soyayya da kuma kyautatawar da Abid ke mata, Inna bata bari Abid ya ga miciji ba, dan ƙofar ma ta kulle bayan ta maida Hassan ɗin kan gadonsa dan kar Abid ya gani ya firgita dama hausawa sun ce zuciya na son mai kyautata mata.

Bayan tafiyar Abid Inna ta buɗe jakar kayanta ta ɗakko wani abu ta saka a cikin ɗan tofinta (Siket da tsofaffi suke sakawa daga ciki wand ake ɗinka musu har da aljihu a jiki) Bayan ta sanya a aljihun ɗan tofin nata ta cewa Sadiya za ta fita ta ɗan zaga ƙafarta dan ita ta gaji da zama wuri ɗaya, Sadiya kwa ta ce a dawo lafiya dan ita ma so take Innar ta fita saboda ko kaɗan in tana gidan sai an samu wani akasin. Baki ta taɓe ta ɗauki mayafinta ta yafa sannan ta ɗauki goro guda ɗaya take ci abinta ta fita. Tun da ta fito hanyar da Malam Isuhu ya bi ta nan ta bi tana yi tana kallon sawun ƙafarsa da ya yi ta sheƙa gudu ɗazu dan sawun har wani nitsewa yake a cikin ƙasa saboda yadda ake taka shi da ƙarfi, kalla kawai ta yi tana dariya wai mai sittin wata kan wata sai gashi ko izifi ɗaya bai karanta ba a ɗakin Hassan. Tafiya take abinta hankali kwance, tana cikin tafiyar, wata mota mai baƙin gilashi da wasu ke ciki suna kallon hoto a waya ɗayan ya kalli ɗayan ya ce

"Ita ce"

Aikuwa da uban gudu motar nan ta sha gaban Inna dama wajen duk ba mutane Inna da ta tsaya kallon ikon Allah ganin mota ta sha gabanta kafin ta gama tunani sai gani ta yi an fito daga ciki an fisgeta an shiga da ita motar an banke ƙofa an kwasa da uban gudu...


Masu fitar min littafi ki sani haƙƙina ne, dan haka ke ma da kike karantawa haƙƙina ne kuma baki biya ni ba.



09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375




Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134



3️ 4️⃣5️⃣➡️4️⃣6️⃣


Tun da suka saka ta a mota ta fara wurwurga idanu, mutum huɗu ne a cikin motar gabaɗaya suna sanye da kayan sojoji, ɗaya yana jan motar shi kaɗai ne bashi da kayan sojoji. Mutum biyu ne suka sanya Inna a tsakiya kallonsu take tana so ta ga ko ta taɓa ganin wani, amma babu wanda ta gane, baki ta buɗe za ta yi magana amma ɗayan ya ɗaga bindiga ya ɗora mata a kan ta hakan ne ya sanya Inna ta ja bakinta ta yi shiru dan duk abin ta bata wasa da rai da lafiyarta.

Gum ta yi da bakinta bata sake yinƙurin yin magana ba su ma kuma duk cikinsu tun da ta shigo motar bata ji wani daga cikinsu ya yi magana ba.

Wata unguwa suka nufa da babu hayaniya sosai a ƙofar wani get suka tsaya horn aka yi mai gadi ya zo ya buɗe ƙofar suka shiga ciki Inna kuwa sai rarraba ido take yi dan ta kasa gane dalilin da ya sa aka ɗakko ta. Tunani ta fara yi ko ƴan yankan kai ne suka ɗakkota, duk da dai ta gansu da kakin soja a jikinsu amma hakan ba zai hana ta zargesu ba saboda yanzu ƴan bindiga suna kashe sojoji su ɗauke kayansu suke sanyawa, dan dai ta san wancan karon da aka ɗakko ta daga gidan masu kuɗin wannan jeji aka nufa da ita saɓanin yau kuma da aka nufo cikin gari kuma ƙeraren gida na gani na faɗa.

Haka dai ta daure saboda bakin bindigar da ke kanta. Suna fitowa ita ma haka ta bi ayari ta fito bisa bin umarnin da aka bata, tun da suka fara tafiya zuwa ainihin cikin gidan take ta kalle -kalle har suka samu nasarar shiga cikin wani falo madaidaici mai shegen kyau. Su duka wuri suka samu suka ƙame babu wanda ya nemi wurin zama Inna kuwa ganin tsayuwar ba za ta mata ba sai ta zauna a ƙasan kafet gudun kar ta hau kujera a harbeta.

Suna nan, sai ga wata yarinya ta fito cikin wasu ƙananan kaya tana riƙe da abin wasanta, Tun da ta fito Inna ta ƙura mata ido tana mata kallon sani sai dai ta kasa tuna inda ta san yarinyar tana ta kiciniya da ƙwalƙwalwarta a kan ta barta ta tuna ina ta san yarinyar amma kafin hakan sai ganin mutum ta yi ya fito daga cikin wani ɗaki shi ma sanye da kaya amma ba na sojoji ba. Kallo ɗaya Inna ta masa ta gane shi a take ta tuna da inda ta san yarinyar ma.

"Sojojo kai ne dama nan gidan ka ne ina tsohuwar matarka mai shegen tsoron nan kamar farar kura, ko da yake ma ba ita kaɗai ce matsoraciyar ba har da...

Wata uwar tsawa da ya daka mata ita ce ta hana Inna da ta washe baki tana ta kauɗi da karaɗi ƙarasa maganar, dan tun kan ya ƙaraso ma tsakiyar falon ta fara zuba.

Cikin ɓacin rai ya ƙaraso tsakiyar falon gabaɗaya suka shiga sara masa kujera ya nema ya zauna har lokacin ransa a matuƙar ɓace yana aikawa Inna wani mugun kallo. Ƴar tasa ce ta zauna a kusa da shi tana ta raɓewa a jikinsa da alama dai bata manta da inda ta ga Inna ba.

"Ke inyamura ina uwaki take, yo ina so in miki magana amma na san bakya jin hausa, ina so in ce ki kira min uwaki tsohuwa mu gaisa ko yau ma tana can tana kwalliyar tana shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa sai...

Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙara yiwa Inna tsawar da ta sanya ta yi shiru sai dai yanzu tun da ta ga abokin Imran gaba yake da su, wato ogansu ne sai ta ji duk bata tsoronsu dan ta san dai duk tsiya ba lallai su harbe ta ba.

"Oh ni Azumi Allah ya tsaga min bakina amma ku hana ni magana, na rasa ma mai yasa kuka ɗakko ni duk da dai na san ruwa ba ya tsami banza amma dai da walakin goro a miya"

Babu wanda ya mata magana dan abokin Imran ya ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.

Kallon su ya yi cikin bada umarni ya ce

"A kai ta wannan ɗakin" Da kallo Inna ta bishi tana mamakinsa amma sai ta miƙa hannunta ta taɓo saitin aljihun ɗan tofinta ta ji abin da ta ajiye yana nan hakan ya sanya ko gardama bata musu ba suka tafi da ita. Har sun je ƙofa za su fita ta juyo ta ce

"Gobe sunan Hassan dai mutuminka ina fatan za ku je" Wani haushi ne ya rufe shi yana ayyanawa a ransa tabbas tsohuwar nan yau sai ta banbance tsakanin aya da tsakuwa, dan sai ya tabbatar ta gane akwai banbanci tsakanin kiɗa da karatu. Ƙeyarta suka tisa har ɗakin da aka bada umarni a kai ta, ɗakin a can bayan gidan yake kuma a rufe yake sai da suka buɗe ɗakin suka shigar da ita ciki wani daga cikinsu wanda ya zo a kujerar mai zaman banza lokacin da suka taho a motar har ƙeya ya tallewa Inna, amma bata ce komai ba sai dai ta ayyana za ta rama ne.

Sai da suka gama harare -harare da wani tsawace -tswacensu sannan suka fito suka rufe Inna a cikin ɗakin suka sanya mukulli sai dai basu cire mukullin ba daga waje suka barshi a jikin ƙofar.

Sai da suka yi kamar minti goma da fita Inna ta tashi ta yi dibara ta ɗan buɗe windown sai da ta tabbatar babu kowa a kusa sannan ta buɗe windown duka, wani dogon icce da ta samu a ɗakin ta ɗauka ta sanyo shi ta windown a hankali cikin dibara ta saƙala iccen a jikin ƙarfen key holder na jikin mukullin, cikin dibara ta cire mukullan daga jikin ƙofar sai dai tana ƙoƙarin shigo da iccen ta windown sai mukullin ya zame daga jikin iccen ya faɗi ƙasa.

A haka ta rinƙa yin dibara har dai ta ci nasarar ɗakko shi a jikin iccen, daga ƙasan ta shigo da shi cikin ɗakin, jijjiga kai kawai take tana dariya ta ce

" Ta yaro kyau take bata ƙarko, tabbas yaro bai san wuta ba sai ya taka, lallai yau allura za ta tono garma, su a ganinsu sun garƙame ni, basu san na fisu wayo ba ko dan dogaye ne dan bashaushe ya ce dogo da hankali dace ne" Cewar Inna tana ta ƙoƙarin cire mukulli ɗaya daga jikin key holdern dan gabaɗaya mukullan iri ɗaya ne hakan ya nuna duka na ɗakin ne.
Bayan ta cire ɗaya sai ta sanya a cikin aljihunta, bayan ta ɗakko wata ƙaramar farar leda ƙulle da wani abu, tana gyaɗa kai alamar za ku gani. Sai da ta adana mukullin da ta cira ta yi murmushi ta ce


" Mu je zuwa da ni Azumi kuke zancen ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha"

A hankali ta lallaɓa ta sake leƙawa har lokacin bata hango kowa ba kuma bata ji motsin kowa ba ga la'asar ta yi lis haka ta sanya mukullin ta buɗe ƙofar a hankali ta fito daga ɗakin, tana fitowa ta maida ƙofar a hankali ta rufe bayan ta rufe sai ta bar mukullin a jiki, cikin sanɗa ta fara tafiya tana ta waiwaye abinka da marar gaskiya ko cikin ruwa gumi yake. Cikin ikon Allah har ta ƙaraso ɓangaren da suka fara zuwa ita da sojojin nan wato inda ogan nasu yake abokin Imran. Shigewa ta yi dan a hankali ta tura ƙofar har ta ƙaraso falon babu wanda ya lura da ita. Laɓewa ta yi a jikin bango wani ɗan loko take leƙo falon yana zaune ya rungume ƴar sai matar ita ma daga ɗaya gefen nasa ta zauna ta kwantar da kanta a kafaɗarsa ta yi wani turum da tsohon cikinta.

" Wai da gaske an samo matar nan ta gidan abokin ka?" Cewar matar cikin gurɓayacciyar hausarta.

"Eh wallahi har nan aka shigo da ita amma saboda ƙarfin hali har tambayarki take tana miki wulaƙanci wai ko kina can kina shafa jambaki bakin ki kamar akuya...

" Haba wato kaima maimaita abin da ta ce za ka yi, tabbas yau bayan ka hukunta tsohuwar nan sai ni ma na mata hukunci mai tsanani za ta san da ni take magana"

"Ayyo to ke ma ashe shegiyar kan ki ce da ban yi niyyar miki komai ba shi kaɗai zan yiwa to tun da ke ma mummunan ƙudiri ne a ranki har ke zan haɗa, ƴar taku ce dai ba zan yiwa ba saboda ƙanƙantar ta, dan kar in ɗau alhaki" Cewar Inna a zuciyarta.
"Ayya ba dan na ɓata miki rai ba na yi baby, amma tabbas yau za ta karɓi hukunci dan kuwa zan ɗauke idanuna daga kallon tsufanta in manta alaƙarmu da Imran duk da shi ma ya ce min ta addabeshi, amma yau sai ta san wa ta yiwa abin da ta yiwa ranar nan wai dan wulaƙanci ni take cewa sojojo sai ka ce wani ɗan ƙwaya" Ya faɗa cikin gurɓatacciyar hausarsa.

"Ai kawai ka bari tsohuwar nan za ta gane kurenta, ai na gode Allah da ka aamu hutun sati biyun nan jiya gwara da ka sa aka ɗakko ta mu ga tsiya" Cewar matar tana dariya.

"Za mu ga wanda zai gane kurensa ni da ku ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, kuma iya gani iya ƙyalewa ni Azumi zan nuna muku ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu" Cewar Inna a zuciya.

A hankali ta since farar ledarta wacce ta zubo ƙaiƙayin hatsi ta haɗa da barkono ta daka ta zuba a leda ta ƙulle. Ya daɗe a ajiye a cikin jakarta dan tun kafin cikin Halima ya tsufa ta ajiye saboda idan za ta je ZAMAN WANKA ta ajiye saboda shirin ko ta kwana. Ledar ta since ta lallaɓa cikin falon da suke da yake sun baiwa ƙofa baya ne basi san me ke faruwa ba idanunsu a kan TV. Sai da Inna ta je bayansu kawai sai ta ga matar za ta juyo da sauri ta durƙusa Allah ya sa ma matar bata ganta ba sai da ta bari ta ɗan jima ta ji suna ta hirar yadda za a azabtar da ita, ta tashi ta zuba musu ƙaiƙayin nan mai barkono a cikin wuyan rigarsu sai da ta barbaɗawa mata da mijin ta lallaɓa ta fice. Ta baya ta bi tana yi tana laɓewa dan so take ta gano inda sauran sojojin nan suke wanda suka ɗakko ta. aikuwa ta hangosu zaune a kan benci sun bata baya suna cin wani abu haka su ma ta lallaɓa ta je sai da ta zubawa kowane a cikin wuyan rigarsa cikin hanzari ta bar wajen ta koma ɗakin da aka ajiyeta. Ta maida mukullin yadda suka ajiye shi a jiki ta rufo ƙofar sai dai bata kulle ba.

Sojojo suna kallo bai ankara ba sai ganin ya yi ya miƙe tsaye zimbet yana zazzare ido dan raɗaɗin barkonon da ya ziyarci fatar bayansa ya haɗe da ƙaiƙayin ya bashi wani azababben zafi da raɗaɗi. Yatsina fuska matar ta yi tare da taɓe baki ganin abin da mijin nata yake yi kamar wani mahaukaci sabon kamu. Tana shirin masa magana sai ita ma a take ta ji wani raɗaɗi ya ratsa fatarta kamar wanda aka tsatstsaga mata fatar bayan da wuƙa ko reza aka zuba gishiri ko yaji haka ta ji a take ita ma ta miƙe suka shiga zarzage -zazzage sai idanu take zarewa kamar ta yi ƙarya an zo mata cakar ƙarya.

A take suka shiga zirya a falon babu wanda ke iya taimakawa ɗan uwansa kowa ta kai ta kai yake kowa ɗauki yake nema sai ife-ife da soshe-soshe suke kamar za su karce fatar jikinsu amma kuma ƙaiƙayin ƙaruwa yake . Su sa suke hannu bibbiyu dan shi mijin ma ya yi xaman ƴan bori a ƙasa sai susa yake amma kamar ya yi hauka ga ƙaiƙai ga raɗaɗi , ita ma matar da ta gaji sai zaman dirshan ta yi ta miƙe ƙafa tana sosawa shi ya kalli gabas ita ta kalli yamma sun raba jaha mijin da matar, can ya gaji ya kwanta a ƙasa yana gurza bayansa a ƙasa amma ina jin abin na neman wuce gona da iri sai ya fara kiciniyar cire riga, yana gama cirewa ya cigaba da soshe soshe ƴarsu na musu sannu.

Hakan bai masa ba sai da ya tuɓe kayansa duka daga shi sai gajeren wando, tashi tsaye ya yi sai zagaya falon yake yana wani dira ƙaƙafu, matar ma kiciniyar cire riga ta fara ganin tana neman cire kayan ya doka mata wata uwar tsawar da ta sa ta suka shige ɗaki ita da ƴarta shi kuma ya yi hakan dan kar wani cikin yaransa ya shigo duk da dai basa shigowa sai ya musu izini amma dai idan wani uzurin ya tashi zasu iya shigowa bare yau da ya san ya ajiye Inna a gidan ya san ba za a rasa nono a ruga ba.

Suna shigewa ɗaki da ya ji bala'in ya yi bala'i a sukwane ya fito daga part ɗin nasa ya fito yana ƙwalawa yaran nasa kira, daga inda suke suna ta tutumurtu suka rugo wurinsa a guje cikin son cila umarninsa ganinsu su duka a tuɓe da gajerunan wanduna kowa hannu a jiki kowa na susa kamar su yi hauka.

Shi ma yana susar ya kalle su yana wani zare idanu.

"Meye hakan kuma kuke yi kuna min yawo a gida a tuɓe?" Ya jefa musu tambayar yana soshe soshe. Sara masa suka yi suna ta susar kowanne idanunsa jajur.

" Oga wallahi kawai muna can baya a zaune sai kowa ya fara jin ƙaiƙayi da raɗaɗi mun rasa menene" Suka haɗa baki wurin bashi amsa har lokacin kowa susar yake har ogan.

Yana shirin yin magana ai da ya ji wani azababen ƙaiƙai sai ya manta da basu amsa tun yana yi a tsaye har ya kwanta reran a ƙasa sai birgima yake su ma maimakon su taimaka masa sai ƙaiƙan ya ci ƙarfinsu suka kwanta a ƙasan daga gefe duk da halin da suke ciki amma sun san Ogan su ne basu jeru da shi ba, yana gefe yana birgima da gurza bayansa a ƙasa suma suna gefe suna yi kamar yadda yake, sai da suka ji ƙaiƙan ya ɗan lafa suka dakata Oga ne ya fara tasho sai wani cin magani yake yana wani harare-harate shi a dole kar a kawo masa raini cikin haɗe rai ya ce.

"Ina tsohuwar nan?"

"Tana ɗakin da ka ce a kai ta"

"Kun kulle ta kuwa"

"Eh Oga da mukulli ma"
Sai lokacin ya ɗan ji ya daina zargin Inna dan ya san dai babu yadda za ta yi ta fito ɗaki a kulle amma da ba zai taɓa yadda ba ita ce silar shigarsu halin da suke ciki ba sbd ya san za ta iya yin komai sai dai ai babu wanda ya ga wanda ya aikata wani abu kowa ya tsinci kansa ne a halin dan haka sai aka dangana hakan da ko aljannun gidan ne suka musu hakan.

Ɗakin da Inna take suka nufa domin a je a mata hukunci tun yau za ta fara karɓar hukunci dan ya yi alƙawarin sai ta kwana uku suna azabtar da ita sannan za a maidata sunan da damun mutane da shi ma ba za a yi tana nan ba

Please Login or Register in order to submit comment