Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Imirana kan ruwan cikinta za ta hau a gabana" Inna ta faɗa tana sauri ta yi taku ɗaya biyu sai gata a gaban gadon a sukwane, aikuwa ta shiga kiran Imran da ƙarfi tana cewa.


"Imirana kai, kai Imirana tasata (Ɗaga ta) tasa ƴar mutane, wallahi ban bari ka yi wannan aikin da na sani, azo ayi abun kan ji alawo, sai daga baya ake wallahi tallahi" Ta faɗa tana jan rigarsa, amma Imran ko gizau be yi ba, cikin sauri ta juya ta bar ɗakin har tana haɗawa da gudu -gudu ta yi tsakar gida gabaɗaya a gigice take.

Imran kuwa ya ɗauka kunya ce ta sanya Inna ficewa daga ɗakin dan haka sai ya fara ƙoƙarin tashi, ai sai ya fara jiyo ƙaran gudun Inna kidif-kidif kamar an biyo ta, da sauri ya koma yadda yake ya yiwa Sadiya rumfa.

"Bari dai na yi maganinka na yi maganin sheɗan ɗin da ya rufe maka ido kake neman aikata aikin da na sani" Cewar Inna da ta dawo ɗauke da taɓaryar da ta ɗakko a kicin, ɗaya hannun kuma muciya, Sadiya da yake ita ce a kwance Imran kuma ya baiwa Inna baya bai ga abin da ta ɗakko ba, sai Sadiya ta ce cikin ƙaraji.

"Abban twins tashi taɓarya" Ta faɗa tana turashi da ƙarfi da hannunta dan ta san kaɗan daga aikin Imna ta ɗaga taɓarya da muciyar nan sa rafkawa Imran dan tsaf za ta sauke masa su a gadon baya ta je ta lahantashi a shiga uku a zo ana a'i ina indo. Imran turawar da Sadiya ta masa sai gashi a gafe rigingine a kan gadon, hango Inna ɗauke da madokai ta iyu kukan kura za ta hau kansu ya sanya ya yi wata adungure ya dira daga gadon sai gashi ba shiri tsaye a kan ƙafafunsa. Sadiya kuma da sauri ta tashi zaune ta miƙe tsaye dan dama ita dan ya mata nauyin kuka ne kuma ya hana ta ƙwatar kan ta amma dama da ba za ta yarda ta yi wannan abin kunyar ba a gaban Inna ta barwa kanta abin gori da abin faɗa marar iyaka a wajen Inna Azumi.

Ita ma Sadiya dirowa ta yi daga kan gadon ganin duk da Imran ya ɗaga ta amma Inna kamar bata fasa abin da ta yi niyyar yi ba, ganin da gaske tana shirin farmusu da taɓarya da muciyar ya sanya Imran yin wani uban tsalle ya bi ta bayan Inna ya fita daga ɗakin a sukwane, Sadiya ma da gudunta na bara ta fice suka bar Inna a ɗakin tana sababi tare da rufa musu baya cikin gudu -gudu sauri -sauri.
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment