Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗar gaskiyar dalilin da ya sa ta kwana a ƙasan gado dan har yau bata daina jin tsoron aljanin ba kuma har yau tana ganin kamar dai yana kallonta a gidan.

"Sanyin garin nan ya sa na kwana a ƙasan gado" Ta faɗa tana ƙara gutsurar goro fuskarta ɗauke da damuwa.

"Sanyi fa Inna, lallai sanyi bai kyauta ba" Ya faɗa yana dariya dan ya fuskanci bata faɗi gaskiyar abin da ya sa ta kwana a ƙasan gadon ba dan daga yadda ta faɗa ya san ta faɗa ne kawai, ga kuma
yadda take bada labarin ma kaɗai abin dariya ne.


"Sanyi mana, ai ba fa shi ne abin da na fuskanta ba kaɗai, ka san Hassan ya zo da baiwa a jikinsa wato haka kawai sai yaro ya ringa saɓaɓa-saɓa ya bar ainihin halittarsa ya koma ta miciji"

"Miciji Inna" Ya faɗa da yana son tabbatarwa dan ya san dai Imran ya xe fatar bayan yaron ta miciji ce.

"Miciji mana, ai a washe gari da haihuwarsa ya koma miciji da kan mutum amma saboda rashin imani na Imirana haka ya garƙameni da micijin nan a ɗaki tun ina neman ɗauki har na gaji, ya sanya na rinƙa karanta alif an baki waw zal, kai daga ƙarshe dai sai ga Azumi a saman drower na hau can tsililiko ina reto"

Dariya kawai yake, da jin labarin ya san dama tabbas a rina wai an saci zanin mahaukaciya dan ba za a ƙarƙe ƙalaw ba da Inna da Imran saboda basa jituwa.


.

"Lallai Inna kin yi ƙoƙari" Ya faɗa had lokacin ya kasa tsaida dariyarsa, Ashrof ma sai tayashi take duk da Sadiya ta bata labari amma sai ta ji kamar yanzu ne ake farkon jin labarin.

"Kai Abida baka cin ribar zance ne, ka tsaya ka ji yadda ta kaya mana tsakanin ni da Imirana ai bai fa ci bulus ba, mutuminka na sanya Sadiya ta ƙwala masa kira lokacin ya sha dariyarsa ya more, a raina na ce bakin dariya shi ne na kuka, ai yana shiga ɗakin na shammacesa a janyo Halima muka fito na bankeshi a ɗakin, kira yake Inna ki buɗe dan Allah, aikuwa na yi kunne uwar shegu na ce sai na rama sai da ya horu sosai a ɗakin na buɗe, ka san ya na ga Imirana" Ta faɗa tana dariya, su ma dariyar suke har Sadiya da ta kasa riƙe tata dariyar, hakan ya sanya Imran ya shigo yana ta sallama basu ji ba da yake bai wani ɓuga maganar ba dama jikinsa ya bashi ana cin namansa a gidan tun da ya ga motar Abid a waje ya san Inna tana nan tana bada labarinsa.


"Yana laɓe a jikin bango yadda ka san ƙadangare ya rakuɓe a waje ɗaya sai maƙyarƙyata yake kamar kazar da bazai ya kamata" Ai gabaɗaya suka ɗauki dariya har Inna a dai dai nan Imran ya shigo falon sai haɗe rai yake kamar zai kai musu duka.Ɗif suka daina dariyar sai Abid da ke ƙoƙarin danne dariyar taƙi tsayawa har ruwa idanunsa suka kawo saboda dariya sosai yake hango yadda abokin nasa ya yi, a rakuɓe a ɗakin ga kuma miciji a gefe, tsaf Inna ta iya bada labari yadda mai sauraro zai ji kamar a gabansa ake yi.

"Abokina ka dawo? Ka ganni kamar an jefoni daga sama ko ban maka waya ba" Cewar Abid yana goge ƙwallar idonsa da dariya ta sa ta taru. Wani mugun kallo Imran ya masa wanda ya sanya wata dariya ta ƙwacewa Abid aikuwa ya sakikayarsa dan ya kasa riƙeta.

"Ai abin akwai abin dariya Abida dan ma ba a gabanka aka yi ba" Inna ta faɗa tana dariyar dan ganin Imran ma sai ta sake ƙara ƙarfin dariyarta dan ta ƙular dashi tun da shi bai san abin arziƙi ba.


"Yo da kana siyo min ɗan goro da turmin zane, ai da na ɗan rangwanta maka ka san zuciya tana son a kyautata mata" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Kallai abin arziƙin da abokinka ya kawo min, wancan na gaban Asharofa kuma ya ƴaƴanka ne da matarka"

"Ta faɗa tana kallon Imran da ke ƙoƙarin ajiye ledojin da ya shigo da su.

"An gode" Kawai ya ce tare da juyawa zai fita.

"Amma kuwa yau nan tabbatar ta mugun halin ka Imirana ace a kawo wannan uban kayan kuɗi amma ka yi godiya ƴar mitsitsiya, ina laifin ma ka ce an gode madalla Allah amfana Allah saka da alkairi ya bar zumunci, ka ƙara da cewa kai amma kayan sun yi kyau sosai har da Inna ma aka kawo wa to madalla, amma dan baƙinciki kake min kuma da baƙin halinka Imirana shi ne ka ce an gode a takaice" Cewar Inna tana gatsinen gefen hanci.


"Haba Inna ai tsakaninmu ba godiya" Cewar Abid a fili yana ƙara maƙe dariyarsa. A zuciyarsa kuma ya ce na tabbata Imran ya ji Inna tana bada labari amma babu yadda zai yi da ita, kuma gashi magana take faɗa masa a kan ƙin doguwar godiya kuma ba yadda zai yi da ita lallai Inna ita ce maganin Imran.


"Ka ji ɗan arziƙi irin albarka, wallahi kana birgeni Abida...

"Idan ka gama neman maganar ka same ni a waje" Imran ya katsewa Inna maganarta yana kallon Abid tare da ficewa cikin ɓacin rai.

"To ina fitowa " Cewar Abid yana bin bayan Imran da kallo dariya na cinsa.

"Kai rabu da shi yana ta ƙuncin rai ka yi zamanka a nan mu sha hira in maka abin ban faɗa maka ba" Cewar Inna tana kallon Abid.

"To Inna"

"Ashrof miƙa masa yaran ya gan su" Sadiya ta faɗa cikin sanyin murya dan yadda ta ga Imran na harararta da ya shigo hakan ya sanya ta gane bata kyauta ba da aka zauna da ita ana bada labarinsa suna dariya.

"Lah ta barsu ma tun da bacci suke kar a tashe su, ai ni nan tunda gidan zuwa na ne na gansu wata rana"

"Kana ji ko Abida jiya kurman abokin nan naka ya kawo abokinsa Sojojo"

"Inna meye kuma Sojojo ko suna ne?"

"Ina kai ka, baka cin ribar zance"

"To ina jinki Inna"

"Nake faɗa maka Sojojo ne dan bana kirashi Soja ba saboda ragwantarsa"

"Ragwanta kuma Inna"


"I mana" Inna ta faɗa tana kwashe duk yadda aka yi da Abdallah da ya zo barka da matarsa.


"Inna haka aka yi ashe haɗe su kika yi, kai abokina ba dama" Ya faɗa yana dariya

"Kai dai bari yo shi ma Imiranan ranar nan fa suma ya yi saboda Hassan ya sawaya ya zama miciji a jikinsa" Ta faɗa tana dariya. Haka suka sha ta dariyarsu har cikin Abid yana ƙullewa dan ya ma manta Imran na jiransa a waje. Sai can ua tuna ya musu sallama ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko dubu ɗaya ya miƙawa Inna. Hannu ta sanya ta karɓa tana washe baki.

"Haba Abid ai da ka barshi hidimar ai ta yi yawa " Cewar Sadiya cikin jin nauyin Abid.

"Lah ba kamai ai...

"Rabu da ita kawai in banda baƙinciki meye wata dubu ɗaya dan ya bani kyauta zaki wani haƙiƙice kina cewa ya yi hidima ai dama kowa ya san ya yi hidima musamman da ya fi mijinki da bai san ya siye zuciyar mutane da kyauta ba sai baƙin hali da na zuciya fal ransa" Ta faɗa tana sanya dubun a cikin ƴar pos ɗinta.

Dariya Abid ya yi jin abin da Inna ta ce haka kawai shi ds a ce za a barshi da Inna da ya huta d shiga damuwa ko ɓacin rai, saboda ita bakinta ba ya shiru kuma bata gajiya da abin dariya duk da ita tana yin komai dan raha ne.


"To Inna sai kwana biyu"

"Kwana biyu fa Abida sai ka ce an maka baki, yanzu sai ka iya kwana biyu baka zo mun gaisa ba, ai baka ji daɗin da na ji ba da ka bani bugun Abujar nan"

" To Inna idan na samu dama da lokaci zan ke leƙowa "

"To nagaode sosai" Ta faɗa lokacin da ta fito har ƙofar falon Abid ya sanya takalminsa ya fita.

"Oh ɗan nan da kirki yake Sa'adiyya ya fi min mijinki Imirana sau miliyan ma" Cewar Inna lokacin da ta zauna a kan kujera tana ƙara ganin atamfarta.

"Inna dan Allah kike iya bakin ki idan abokan Imran sun zo kin ga ko a fuska ya nuna ba ya so kina shiga shirginsu" Cewar Sadiya cikin lallaɓawa dan ta san Inna hukuma ce sai da lallashi.

"Ikon Allah, lallai Halima wuyanki ya fara isa yanka sauran kuma a gwada wuƙa a tabbatar, yanzu sabibi da Allah ni kike faɗawa wannan maganar to ni da banda ma gaisawa da muke a ɗan taɓa hira ina ni ina su, ni fa kawai dan na ɗaukesu ɗaya da ku ne tamakar jikokina in ba haka ba me ma zai haɗa ni da su, in kuma baƙincikin ɗan abin da zan ke samu kike yi to duk da babu wanda ya taɓa bani wani abin arziƙi in ba Abida ba"


"Abid Inna" Cewar Ashrof.

"Ke ki kiyaye ni, in ma Abu zan kirashi ina ruwanki"

"Ki yi haƙuri Inna" Cewar Sadiya.

"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bani?"

"Allah baki haƙuri"

"Haƙuri kaya ne naɗa gammo ki ɗauka"

Bayan fitar Abid Inna ta ce ta gaji da zaman cikin gidan fita za ta yi ta zagaya ƙafadunta dan ciwo suke mata, gidan Hajiya Amina za ta je. Haka ta musu sallama ta fita ta sha wata atamfarta mae kyau, ta saka ɗan madinanta ta kama hanya ta fita, har Sadiya ta bata kuɗi ta hau ɗan sahu amma ta ƙi karɓa wai ita ta fi son tafiya a ƙasa saboda kalle -kalle.

Hanyar gidan Hajiya Amina ta kama, har sai da ta je gidan bayan ta gama kalle -kalle da ratse -ratse. Haka ta je gidan Hajiya Amina suka gaisa ta ɗan jima sai kuma ta kamo hanya ta taho gida dan Hajiyar ma sai da ta yi ta yi da ita a kan ta zauna idan aka yi sallar magariba ta yi sallar sai ta tafi, amma Inna fafur taƙi zama dan ta fi so ta taho ido na ganin ido. Saboda ta fi so ta taho ido na ganin ido dan ta ga gari gari ma ya gan ta.

dan haka ta kamo hanyarta ta taho riƙe da ledar da Hajiya Amina ta zuba mata bakilawa. Tana tafe tana kalle-kallenta tana ƴar waƙarta a hankali, tana cewa.

"Carman dudu carman duduwa , carmagade, akwai wani baƙo a gidan mai gari, carmagade, ba duka ba ya lakuci, carmagade, in duka wa zai bashi ne, carmagade, aradu ta Allah ba zan bashi ba" Tana cikin yin waƙar ne ta hango wani ƙerarran gida mai shegen kyau tun daga nesa gidan ya birgeta. Dan dama ba ta hanyar ta bi ba a tafiya yanzu kuma sai ta canja hanya dan ta sake ganin wasu sabbbin abubuwa ba irin wanda ta gani a tafiya ba.

"Ikon Allah masu gidan nan kuwa sun san ana wahalar kuɗi kuwa a duniya, an ya kuww sun san sunan wani abu wai babu, ace wannan gida kamar ba a duniya ba" Ta faɗa tana tsaye tana ƙarewa gidan kallo.

"Oh ni Azumi ina can a ƙauye ina fama da ɗaki ɗaya a gidan Malam kullum ana bala'i da Tasalla to ina kuma ga na ganni a gidan nan ina ga kuma sai an mana tsakani da Tasalla dan kar take faɗawa mutane ita kaɗai ce matar gidan" Ta faɗa tana ƙarasawa ƙofar tangamemen get ɗin da ke buɗe, sai da ta tabbatar babu kowa mai gadin ma ba ya nan...

Masu son a tallata musu hajarsu MMN AFRAH 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

"Aikuwa dai sai na shashshafa gidan nan da hannu na, a saka a baka ai ya fi a rataya, ko da a ce baka da rabon zama a cikin waɗan nan gidajen a duniya to kafin mu je aljanna mu samu rabonmu gwara dai na taɓa in ji, ai da hanau gwara mannau" Cewar Inna tana dosar wajen, hannunta ta kai jikin ginin ta shafa shi da hannu biyu kamar wacca ta samu ka'aba har da jingina fuskarta a jiki ta goga fuskarma a jiki hagu da dama.

"Na taɓa ka da alkairi gidan ƴan gayu" Tana ƙara shafawa. Haka ta rinƙa bin wurin tana ganin ginin tana gyaɗa kai alamar mamaki.

"Oh ni ƴasu mutane masu kuɗin nan ko a ina suke samun kuɗaɗe haka su yi ta baje hajarsu a duniya son ransu, ko kuwa rijiyar haƙo kuɗin garesu irin wannan gida, to mu da bamu dashi haƙuri ya ganmu, dan ma dai da daɗi saboda Malam ya faɗa mana cewa ko a lahira sai talaka ya riga me dukiya shiga aljanna, yo kai da baka da kuɗi ina ka ga tarin tambayoyin da za ka amsa dangane da ina ka samo kuɗi kaza, ta wace hanya ka kashe su" Ta faɗa tana kama haɓa har lokacin kaɗa kai take kamar ƙadangaruwa. Leƙa cikin get ɗin ta ɗan yi daga inda take tsaye ta yi dogon wuya tana so ta ga ko za ta hango me gadi, amma babu abin da take hangowa sai tarin fulawoyi masu matsanancin kyau.

"Ni Azumi da a ce zan samu shiga cikin nan ɗin ma ba tare da na zauna na yi rayuwa a ciki ba, da wallahi tallahi iya hakan ma na godewa Allah kuma na ji daɗi, yo in ban shiga na gani ba na kashe ƙwarƙwatar ido na ba me aka yi da maza, kawai shiga zan yi komai ta fanjama fanjam" Ta ce tana takawa a hankali cikin sanɗa ta durfafi get ɗin, tana shiga sai ta ga ashe ma babu abin da ta gani a waje motoci ne gasu nan wasu a lulluɓe wasu a buɗe.

"Ikon Allah na kwance ya faɗi wato dai a duniya ma akwai aljannar duniya, lallai masu gidan nan kun huta amma duk da haka ba za mu shiga sahun ƴan Allah baku mu samu ba" Ta faɗa tana leƙa cikin wata mota tare da shafawa.

"Tabbas idan na koma garinmu duk mai son in bashi labarin gidan nan sai ya biya ko da kuwa Malam ne, Tasalla kwa ko a da kuɗinta bata da rabo dan ba zan bata labarin nan ba" Ta faɗa tana ɗaga kai sama tana ƙarewa benen kallo ga wasu hazbiya a saman suna ta waricinsu. Haka ta rinƙa kutsa kai cikin farfajiyar gidan tana ta kallo abinta.

"Ni ai yau ta waru wallahi yawon buɗar ido dai da wasu ke biyan kuɗi suna hawa jirgi su tafi ƙasashen waje, to ni ga nawa yawon buɗar idon a nan babu ko sisina bare taro, yo da na san akwai gidaje masu kyau kamar wannan a kusa da gidan Halima ai nan da gidan Halima babu nisa da nan zan ke tahowa in na gaji da zaman gidan, da dai in ke zama da wannan Imiranan me baƙar zuciyar tsiya ga mugunta ai gwara in zo nan in wanke dauɗar idona" Ta faɗa tana bin bayan gidan daga can ciki.

"Anya kuwa Azumi kya ke fitowa kina barin Imirana daga shi sai Halima a cikin gidan, bakya ganin wani abu zai faru" Wani ɓangare na zuciyarta ya tambayeta.

"Kuma fa da hakan ne wallahi, kar in je in fito yawon buɗar ido shi kuma ya je ya buɗe ƴar mutane a gida ya je ya rugurgujeta son ransa ya farke mata ɗinki a shiga uku" Ta faɗa a fili tana saurin juyowa dan ji ta yi ma kallon ya fita daga kan ta duk da akwai Ashrof a gidan kuma ƴan barka na zuwa amma sai take ganin Imran zai iya aikin Ashrof wani wuri dan ya cimma burinsa.

"Dole in yi maza ma in koma gidan dan yanzu komai ma zai iya faruwa amma in ina kusa dolensa ya ɗauki dangana ko ba ya so" Ta faɗa lokacin ta dawo hanyar fita, tana shirin ficewa ta hango wani wuri na shaƙatawa an jera faraen kujeru ga falawoyi kewaye da wurin.

sakin baki ta yi ya layar me tafiya tana dosar wurin a ranta tana cewa.

"Ai kuwa yau sai na ɗosana ɗuwaiwukana a kan kujerun nan" Haka ta ƙarasa wajen ta zauna a kan kujerar har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jin una ma nan gidan Malam ne da kuwa kakarsu ta daɗe da yanke saƙa.

Daga can wajen gidan wata mota ce ta faka a ɗan nesa da gidan, wasu maza matasa majiya ƙarfi suka fito su biyu, suka bar wanda ke tuƙawa a ciki.

"Kar fa ku yarda wani ya gan ku, ku bi a sannu, kun ga dai yanzu da sauran haske a gari magriba bata kai ga yi ba, dan dai ma unguwar masu hannu da shuni ce kowa yana cikin gidansa tun da shi me gidan ba ya ƙasar shi da matarsa, kuma Oga ya sanya an zo an ɗauke me gadin to ku tabbatar kun ɗakko tsohuwar nan kar ku bari a samu matsala, daga it sai ƴan aiki a cikin gidan, wallahi kar ku bari a samu matsala dan Oga ya ce ba ƙaramin kuɗi za a karɓa ba idan muka kawo masa tsohuwar nan domin Alhajin zai iya bayar da ko ma nawa ne idan ya ji an kama mahaifiyarsa dole ya bada kuɗin fansa idan ya ji za a aikata barzahu in bai bada kuɗi mai tsoka ba" Cewar wanda ke mazaunin direba cikin muryar dabanci

"An gama za mu yi duk yadda za mu yi mu kawo ta" Suka faɗa tare da juyawa suka nufi gidan, ta baya suka zagaya suka fara leƙen gidan daga wasu ƴan ƙofofi da aka yiwa gidan kwalliya da shi suna so su samo yadda za su shiga, duk da ba me gadi dan Ogansu ya sa an kama shi dan ma kar su zo ɗaukan tsohuwar su tafi ya kira me gidan ya faɗa masa, a kira ƴan sanda a sanar da su amma in suka ɗauketa kafin a gano hakan sun sanar masa sun kuma gargaɗeshi a kan kar ya sanarwa ƴan sandan. Hango Inna suka yi zaune kan kujera a wajen shaƙatawa ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

"Baaba ai ka ga tsohuwar ma a araha tana zaune ba sai mun sha wahala ba wajen shiga can cikin gidan"

"Wallahi kuwa ai kawai mu gewaya mu shiga gidan" Ɗaya ya faɗa, haka suka gewayo dan zuwa su shiga ta get ɗin gidan.

Inna da ke zaune ta ɗakko alkakinta ta gutsura ta mayar a ranta ta ce.

"Kin ga Azumi tashi ki tafi, kar masu gidan su fito ki shiga uku dan ba makawa sai yadda hali ya yi" Ta faɗa tana tasowa dan ta tafi.

"Kai dakata mu laɓe gata nan ma za ta fito daga gidan, tsuntsu daga sama gashashshe" Cewar ɗaya yana janyo rigar ɗaya suka dawo suka laɓe.

Inna da ke tafiya hankali kwance tana ƴar waƙarta
"Duniya ba wurin zama ba, da ka cuta ƙwara a cuceka, yau taka gobe ta ɗan...

Raf ɗin da aka yi da Inna da bata ma lura da samarin ba shi ya dakatar da ita daga ƴar waƙarta, bakinta suka danƙe da hannunsu suna waige-waige irin n marararsa gaskiya, cikin azama suka rinƙa ƙoƙarin kai Inna inda motarsu take, amma Inna sai turjewa take tana neman gagararsu. Idanun nan nata kwa ya fito ƙulu-ƙulu sai son tofa albarkacin bakinta take amma riƙon da bakinta ya sha ba na wasa bane.

"Kai Baaba wannan tsohuwa da shegen ƙarfi take, ka ga yadda take neman gagararmu" Cewar ɗayan yana huci kamar wanda yake kokawa da doki.

Sun kusan zuwa inda motar take ai Inna da ta ga sun doshi mota sai hankalinta ya tashi dan duk tunaninta ƴan yankan kai ne za su tafi da ita su yanke kan nata.

"Wayyo Allah na, wayyo Malam wayyo Tasalla ku kawo min ɗauki gani a hannun ƴan yankan kai, Malam da Tasalla duk da na san kun min nisa amma dole in kira sunanku dan na san idan na kira Sunan Imirana sai dai su gundule min har ƙafafu dan wallahi baƙin halinsa ba zai sa ya taimaka min b mutumin da ya tsane ni, bari in ƙwaci kaina dan ba zan yarda a cire min kai ba in mutu in barwa Tasalla Malam ta zauna ita ɗaya" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ja wani uban birki, aikuwa aka shiga turumurtu ita da su, har sai da na cikin motar ya ga Inna na neman ta gagaresu ya taso cikin hanzari rai a ɓace yana zuwa cikin ɓacin rai ya ce.

"Wai dalla malamai meye hakan sai kun sa asirinmu ya tonu yanzu ban da abin kunya har wannan tsohuwar ce kuka kasa kawo ta mota tana ta mayar da ku baya " Ya faɗa yana hucin ɓacin rai a zuciye ya kama Inna wai shi nan mai ƙarfi aikuwa ta daddage ta cije a wuri ɗaya ta ƙi gaba ta ƙi baya ganin wankin hula na son kai su dare su uku amma sun kasa jan tsohuwa sai laya ya ce su mata cali-cali aikuwa cikin lokaci guda mutum biyu suka kamo ƙafar Inna sai gata an mata cali-cali biyu riƙe da ƙafar ɗayan kuma da saman kan har lokacin hannunsa a riƙe da bakin Inna, a haka suka saka ta a motar biyun suka saka ta a tsakiya, ɗayan ya shiga ya ja motar da uban gudu a sukwane suka bar layin. Tuƙi yake amma Inna sai uban bige -bige take a bayan motar ta hana samarin nan biyu sakat duk ta tara musu gajiya kamar wanda suka yi dambe. Sai da suka daddafeta da iya ƙarfinsu sai haki suke sannan ne suka ɗan samu salama amma kuma sun ƙulle mata idanu, da wani ƙyalle bakin kuma ɗayan ya rufe mata da hannunsa.

Hanyar bayan gari suka nufa duk ta tara musu gajiya, ba dan uban kuɗaɗe da Ogansu ya ce za a samu idan sun kamo tsuhuwar nan da na jaki za su lakaɗa mata su jefar da ita.

Tafiya suke amma Inna hankalinta a matuƙar yashe yake dan tana gani lokacin barinta duniya ya yi domin kuwa ta haɗu da waɗanda za su fille mata kai.

"Allah na tuba, ka yafe mini kura kuraina, ka sa ni a aljanna, ka haɗa fuskokinmu a gidan aljanna da malam, amma banda Tasalla ita ma a kaita aljannarta da ban amma ba wacce za mu zauna da ni da Malam ba " Cewar Inna a zuciyarta hawaye zubo mata gashi babu damar ƙugawa dan an yiwa bakinta rub.

A haka dai ta shiga shirya abin da za ta musu duk da tana ganin mawuyaci ne ta kuɓuta amma za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta musu wani abin ko da zai ita kasancewa bata rama ba. Dama dai ta san zai yi wahala a ce ka rama abin da wanda ke shirin rabaka da duniya zai maka. Ganin ta tuno abin da za ta musu sai ta fara tunanin aiwatarwa. Hannun damarta da ke gefen wanda ke damarta, kuma a wajen cinyarsa hannun nata yake duk da ya riƙe ra amma kuma wajen kafaɗarta ne ya kama ya maƙalƙale, dan haka tsintsiyar hannunta ba a riƙe take ba, dibara ta yi ta miƙa hannun wajen inda al'aurarsa take.

"Yau zan yiwa mazaƙutarka (Al'aura) Damƙar da tun da ka zo duniya ba a mata ba, kai ko wanda ya maka shayi lokacin kana yaro ai ba damƙarta ya yi amma yau za ka gwammace kiɗa da karatu" Cewar Inna tana lallaɓawa da hannun har sai da ta ji ta je saitin inda za ta samu abin da take so, amma ba wai tana ɗora hannun a wurin bane, tunda hannun baya kai ga ɗorawa a wurin ba dan haka babu wanda ma ya san ƴar tsohuwa akwai abin da ta shirya, kawai tun da sun ga sun samu lagonta na maƙureta a tsakaninsu sai basu kawo komai ba.

Laɓɓanta na baki ta

Please Login or Register in order to submit comment