Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwa ba, tun da faɗar ba'a kan ƴaƴa bane tsakaninsu da ƴar uwarsa ce yana da damar saka baki ya tare mata, da ace faɗar a kan su Khadijah ne to fa bashi da bakin magana, amma a kan ƴar uwarsa yana da bakin magana. Aikuwa ya tare mata a in da ya ce wlh in dai Haidar ya ɗaura hannunsa a jikinta yau sai ya gwada mashi banbancinsu, jahili wanda bai san me yake yi ba, angaya mashi ana taɓa matar aure ne? Matar mutun kawai kasa hannu kace zaka daketa, ai ko kotu aka je in dai shari'ar musulunci za'a bi sai a ɗaureka har igiya ta yi saura a kan hakan.

Da farko Haidar ɗin ya so kama Sadiq ɗin da kokawa. Amma ina Sadiq ya nuna mashi ya fishi hankali da sanin ciwon kansa a in da ya ce da maman Zee ta wuce cikin bedroom ɗinta ta rufe kofa ta rabu da su, idan suka gama hauƙarsu ba'a kulasu ba za su kama kansu.

Da sauri ta wuce cikin room ɗinta, ta bi maganar ɗan uwan nata. Tana jiyo muryar Hajiyarsu tana cewa to ai ba gidan ubanki bane da zaki shige cikin ɗakin, ki fito ki tafi gidan ubanki marasa kunya marasa tarbiya, wlh sai kin bar gidan nan tun da ku baku da albarka dangin matsiyata, dole ya zo ya sakeki ki wuce gidan ubanki tun da har da ni zaki yi wa rashin kunya, dan kin rai'na taki uwar.

Wato ita fa Hajiyarsu bata san cewa yanzu fa baban Zainab bayan Hauwa baya jin maganar kowa ba, har da wani cewa zata sa ya saki maman Zainab, wlh ana show a wannan gida, ana rikici, ko ya tsohuwar nan zata ji lokacin data ga Hauwa na juya mata ɗa? Mu dai ana yi muna shan Maltina.

Ko juyowa maman Zee bata yi ba bare ta kallesu har ma ta kulasu, tana jin hajiyar tasu ta ce kada ta yarda ta shiga cikin bedroom ɗin nan ta zo ta wuce gidan ubanta, amma ina ta wuce ciki ta banko masu kofa da karfi tare da murza key abinta, irin bata da lokacin sun nan.

Shi ma Sadiq sa kai ya yi ya wuce ya fita abinsa, dan bashi da lokacin biyewa haukarsu a cewarsa, shi a mahaukata ma yake kallonsu, idan sun ga dama su kwana a cikin parlourn suna surfa masifa su dai suka sani, shi dai ya kama kansa abinsa. Baban Zainab ma yanzu ba samun damar ganinsa zasu yi ba bare har su ce ya saki maman Zainab ko su gaya mashi ta yi masu rashin kunya, idan ma sun sami damar ganinsa to ko kallo basu isheshi ba, shi da yake ta Hauwa ina ruwansa da su? Idan ma suka yi wasa sai ya haɗa masu da zagi da kuma duka koma ya ce bai san su ba. Tirƙashi, ana cakwakiya a gidan baban Zainab fa sosai.

Haka suka yi ta surfa uban masifa mai isarsu, da dai suka ga ba mafita sai suka kama kansu, dama shi Haidar already ya bi bayan Sadiq da nufin ya je ya kama shi da faɗa, amma ina Sadiq ɗin yaki biye mashi, dama yaga zai takura mashi sai ya ɗauki wayarsa ya fice daga cikin ɗakin, ya bar masu gidan ma gabaɗaya, sai dai bai yi nisa da gidan ba, dan yana tsoron ya yi nisa kada su yi wa maman Zainab ɗin wani abin.

Haka suka yi ta haukarsu har suka gaji suka hakura suka tafi. Ita kuma maman Zainab tana shiga cikin ɗaki ta ɗauki waya ta kira mamanta dan ta sanar da ita halin da ake ciki na batun Zainab. Khadija kuwa wadda tun da taga ƴan uwan baban nata sun zo ta gudu ta shige cikin room nasu ta rufe kofa kamar basu a gidan, dan haka Sadiq ya gaya mata, ya ce kada ta sake tsayawa a wajen da ƴan uwan babanta suke faɗa da mamanta, idan taga sun zo ta shige cikin ɗakinsu su rufe kofa babu ruwansu.

Bugu ɗaya mamarsu ta ɗauki wayar, ƴar dattijuwa tana zaune a saman dadduma, kullum cikin yiwa ƴar tata addu'a take yi a kan Allah ya kawo mata mafita.

Bayanai ta kora mata dan gane da halin da Zainab take a ciki kamar yadda Sadiq ya ce ta gaya mata. Ajiyar zuciya maman tata ta yi tare da kara yi mata nasiha mai ratsa jiki sosai, daga karshe ta rufe fa ce mata. "A duk in da kike Aisha ki kasance mai jin tsoron Allah, in ma a lokacin kaɗaicewarki ko a cikin mutane, ki sani idan kowa baya ganinki to shi Allah yana ganinki kuma baya barci, dan haka kada ki ji tsoron kowa ki ji tsoron Allah shi kaɗai, sannan ita kuma Zainab ki samu ganyen magarya guda bakwai, ki daka shi a wajen da babu ya ji, sannan ki zuba shi a cikin ruwan da zai ishata wanka, sai ki karanta mata suratul baƙra aya biyar ɗin farko, ki haɗa da ayatul kursiyu kafa ɗaya, sai wattabau ma tattlusshayaɗini ala mulki sulaimanu waman kafara sulaiman har dai zuwa karshen ayar, sai amanarrasulu kafa ɗaya, sai ayoyin sihiri wato wa auhaina musa zuwa karshe, sai kala musa attakiluna maja'akum sihirulhazakulyan shi ma har karshe, sai kulhuwallahu kafa uku, falak da nasi kafa uku uku, daga karshe ki rufe da fatiha ki tufa a cikin ruwan ganyen magaryar, a bata ta yi wanka da shi".

Wannan duk girman sihirin da aka yi wa mutun manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce in dai ka yi hakan to ba shakka wannan sihiri duk girmanta sai ta warware, koda kuwa da me aka haɗata wlh sai Allah ya kwance ta, sai ta warware, so wannan ba iya Zainab na bama ba, gabaɗaya al'ummar Annabi na bawa, Allah ka tsaremu da tsarewarka, ka shiga tsakanin nagari da mugu. Idan kin ji daɗi kafin ki wuce ki mun addu'a ko wace iriyace in dai ta alkhari ce a gareni ina so.

Godiya maman Zainab ɗin ta yi mata tare da yi mata fatan karin samun lafiya, sannan suka yi sallama.

Shiru ta yi bayan ta ajiye wayar a gefen gado tana tunanin da zata samu ace baban Zainab ma ya yi wanka da wannan haɗi da zata yi wa Zainab ɗin, ai da shikenan kashin Hauwa ya bushe, asirin zai karye asirinta ya tonu, komai da zai dawo daidai, amma ina babu halin ta yi wa baban Zainab ɗin, ina ma ta gan shi da ido ma bare har ta haɗa mashi wannan haɗin? Ai bata ma ga alama ba, hakuri kawai zata yi ta cigaba da addu'a har Allah ya kawo mata mafita, ita kuma Zainab da izinin Allah zata samu lafiya komai ya wuce ya dawo normal.

Gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike taf da tunanin mafita, sai addu'a take yi na Allah ya kawo mata saukin al'amura da haka barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN EMPIRE.🌼

Sosai Leesharh take yin aikinta na gyare gyare kamar yadda aka umarceta, sai dai tana taƙa tsantsan da ƴan gidan sosai.

Kwance take a saman bed ɗinta daga ita sai doguwar riga mara nauyi, hular rigar ce a kanta, ta yi shiru tana tunani, ta kammala aikinta na yamma, ta yi sallar la'asar.

Ta yi nisa cikin tunanin da take yi kamar daga sama ta ji wayarta ta ɗan yi kara alamar shigowar sako, wayar da tun da ta zo gidan bata taɓa amfani da shi ba bayan duba time, ba'a taɓa kiranta ba, sai ga shi yau saƙo ya shigo ciki. Cikin hanzari ta janyo wayar har hannunta na kerma, a ƙage take da taga wani saƙo ne?.

Unknown number ce wadda aka rufeta da kyau, da ita aka turo mata sakon. Cikin hanzari ta fara duba saƙon ba tare da damuwar sai ta kalli number ba, ita dai me saƙon ya ƙunsa kawai take son sani, ba wani karatu sosai can can ta iya ba, amma dai ba laifi.

Jikinta har yana kerma wajen buɗe saƙon, miƙewa ta yi daga kwanciyar da take ta zauna tare da fara karantawa. Saƙo ne da aka turo mata a kan su Sharifat, ya tabbata dai duk wani motsinta suna sane da shi, rubutu ne kamar haka. A'isha tun da Sharifat ta nuna tana son samun kusanci dake to dama mu haka muke fata, dan haka ki saki jiki da ita ta yadda zaki shiga jikinta sosai, ta hanyarta ne kawai zaki iya samun damar isa wajen da Ramish yake, domin kuwa ta hanyar mutun ɗaya zaki samu kusanci da Ramish, ta hanyar Omar ne kawai, shi kuma dole sai ta kasancewarki kusa da Sharifat, idan kika shaƙu da Sharifat tabbas shi ma zaki shaƙu da shi, dan su ɗin abokai ne, idan kuma kika shaku da shi to tamkar kin shaƙu da kowa na cikin gidan ne, kin ga kuwa zamu samu abin da muke so, kema zaki kammala aikinki da wuri ki zo ki koma ƙasarku, ammafa ki kula sosai, kada ki saki baki, ki dai shiga jikinta sosai, kuma kin yi ƙoƙari taimakon Omar da kika yi, hakan ma wata dama ce da zata sa ki samu kusanci da shi, ko na ce ma yanzu ma kin samu kusanci da shi tun da har ya kulaki, ki cigaba da dagewa saura kiris mu isa in da muke so.

Wannan shi ne saƙon da aka tura mata, shiru ta ɗan yi tana nazari a kan waɗan nan maganganu, ita sam ta ƙasa ganewa mutanen nan, addu'ar da yazo bakinta kawai ta karanta tare da miƙewa ta sauƙo kasan gadon, wajen drawer kayanta ta nufa ta ɗauki ɗan ƙaramin hijabi ta sanya a jiki, ta nufi waje, dan ta je wajen Sharifat su ɗan yi hira, dama tana son biye mata su yi hira saboda Sharifat ɗin ta nuna ra'ayin hakan, amma saboda dokar da take tafiya a kai yasa take shareta bata kulata, yanzu tun da ta samu dama ai shikenan kuma, yanzu ne zata shiga jikinsu da kyau ta samu ta yi aikinta da wuri ta bar gidan a cewarta. Ni kuwa na ce akwai cakwakiya kuma sosai. Wai ma ta ina mutanen nan suke sanin motsinta ne?........🤔

Muje dai zuwa.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/8/2024.....✍️📚🌹




For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






E____________41🔥






🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥

Shiri sosai Chuchu ta yi, ta tsantsara kwalliya, kun san halinta dama da iya tsara shegen kyalliya kamar me, part ɗin Momman Zunaira ma ta je ta kwaso wasu perfumes ɗin masu zafi, ita da kanta ta yi wa kanta kyau, ta tsaya a gaban mirror tana ta kallon kanta, ta yi wa kanta kyau, sai murmushi take yi ta kasa dai'nawa, kamar wata wadda take ba ita kaɗai ba.

Doguwar riga haɗaɗɗiya mai bala'in tsada na ƴaƴan manya manyan sarakuna ta sanya a jikinta, launin pink color ce rigar, sai dai akwai ratsin white color kaɗan, and kuma duwatsun jikin rigar ma white color ne, daga ta sama rigar ta kamata dai'dai da jikinta, daga ta wajen ƙugunta kuma zuwa ƙasa ya yi wani irin bala'in buɗewa sosai da sosai. Alkyabbarta mai bala'in kyau launin white color ta ɗaura a saman kayan tare da sanya hular alkyabbar a kanta, ta haɗu kam ba karya, ta gyara gashin kanta sannan ta cigaba da tsayuwa a gaban mirror tana ganin kanta, ta mance da cewa ya ce idan ta kammala shiri ta kirasa, ta tsaya kallon kanta.

Almost 10 mins tana tsaye shiru tana ta kallon kanta, sai kwashe kyan nata take yi da idanunta, ga wani ƙamshi da take zubawa mai kwantar da hankalin mai shaƙa.

"Ba sai kin kalla kin sake kallan kan naki ba, kin yi kyau sosai na wuce misali ai my sister" kamar daga sama ta jiyo voice ɗinsa ta bayanta.

A hanzarce ta kai kallonta a bakin kofar shigowa. Yana tsaye cikin shigar ƙananan kaya, da alama shi ma ya yi wanka ya shirya, ya yi kyau sosai. Murmushi ta yi tare da kai tafukan hannunta ta rufe face ɗinta.

"Ina auta?". Ya yi maganar hankalinsa na'a kan wayarsa dake hannunsa.

"Bata dawo ba tun da ta tafi shiryawa". Ta bashi amsa.

"Okey ku sameni a wajen Aunty MieMie idan kun kammala, ta ce nazo yanzu". Yana kai karshen maganar ya juya ya nufi wajen elevator dan ya yi ƙasa ya je ɓangaren Gimbiya Aunty MieMie wato first born na King Zuhair kena, yar mummyn Gimbiya Chuchu ce kada ku manta, yayar Chuchun kenan.

Da kallo ta bishi da shi har ya ƙurewa ganinta, Yah Jawad ɗin nan yana yi mata kyau, ta faɗa a cikin zuciyarta tare da sauke nannauyar ajiyar, sannan ta nufi bakin bed ɗinta domin ta ɗauki ɗayar wayar tasa.

Auta ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama tana rike da wayar mommanta a hannunta, da alama video call take yi da wani daga cikin ƴan uwanta. Ta yi kyau sosai cikin shigar riga da sket Indian dressing, da wani katon mayafinta da yafi karfinta har yana jan ƙasa, kayanma gabaɗaya kamar sun ɗan yi mata yawa, dan sket ɗin ma yana jan ƙasa, amma ta yi kyau matuƙa, kamar ka saceta ka je ka ajiye ka yi ta kallonta kawai.

A kusa da chuchun ta zo ta zauna tana faɗin. "Ai Yah Jaish ne ya hanani zuwa da fa zan zo, nima na yi kewarku sosai Allah kuma".

Daga ta cikin wayar ya ce. "To yanzu ai baki gaya mun ina zaki je ba da kika yi wannan kwalliya haka? Kin yi kyau sosai".

Ƴar dariya ta yi kafin ta ce. "Yah Rizwan kai da ka ce aiki kake yi kuma ka biye mun ko? Ni kam dai babu ruwana ga shi ma Yah Omar ɗin ya gudu ya haɗamu ya dakatar maka da aikinka".

"Omar bai gudu ba, ga shi can a kwance a gadon Raj, ya barmu ne mu yi hira".

Ya yi maganar tare da ɗan juya mata wayar izuwa kan Guyson dake kwance a saman katafaren bed ɗin Dr Raj ya yi ruf da ciki tare da sanya pillow a wajen kirjinsa yana danna laptop ɗin Dr dake a saman bed ɗin, shi kuma Rizwan yana zaune ne a saman sofa set dake a cikin room ɗin na Dr Raj ɗin, gabansa shi ma laptop ɗinsa ne yana aiki yana kuma shan cappuccino mai zafi dake cikin wani haɗaɗɗen cup dake a gabansa. Su dai a duniyarsu suna kaunar coffee da cappuccino, sun ma fi son cappuccino a kan coffee gaskiya.

Gabaɗaya su Rizwan sun san auta, kuma suna kaunarta kamar yadda suke son Omar, su chuchu ne dai basu sani ba, domin idan baku manta ba ita fa auta tana zuwa Dubai sosai, kuma Abu Abdussalam bin Badeen uncle nata yayan mommanta, duk idan aka yi hutun school a can wajen dangin mommanta take hutu har sai an buɗe makaranta, wannan karon ne kawai aka hanata zuwa, su Chuchu kuwa dama basa zuwa sai jefi jefi, ko sun je kuma a gidan kakansu King Badeen suke zama, basu cika zuwa wajen sauran ƴan uwa ba, ko sun je ma basa wuce su wuni su koma gidan kakansu, ko kwana basa yi bare har su saba da sauran ƴan uwan nasu, so su gaskiya su Rizwan basu wani sansu sosai ba, ko shi Bilal da yake uwa ɗaya uba ɗaya da Chuchun ba wani saninta sosai ya yi ba, rabonsa da ita ya kai shekaru 10, Gimbiya Aunty MieMie kawai suka yi wa farin sani kuma suke waya da ita a koda yaushe, dan ita ɗin babbar yarsu ce, ta girmesu dukka, kuma tana yawan zuwa Dubai wajensu, su Chuchu kam shiru ne, kunga kuwa ai ko Bilal ɗin ba ya shaidata ba, auta kam ai dole ma su santa, ita take zuwa har in da suke ko basu nemeta ba.

"Kai Yah Omar har da tafiya ya kwanta, tom muma dai unguwa zamu je". Ta faɗa tana bin Chuchu dake ƙoƙarin kwanciya a saman bed ɗin da kallo.

"Ina zaku je?". Rizwan ɗin ya tambayeta.

"Nima ban sani ba, Aunty Chuchu ce ta ce na shirya Yah Jawad zai kai mu wani waje".

Jin ta ambaci sunan Chuchu yasa ya kawar da kallonsa daga kan laptop dake a gabansa izuwa kan wayar da kyau, shiru ya ɗan yi yana tunanin sunan Chuchu, can ya ɗan tuna ashe ita ce wadda Mammie ta zaɓa mashi.

"Ina Chuchun take?". Ya tambaya tare da zame farar glass da yake face ɗinsa, dama ɗazun bai wani duba hotunanta da Mammie ta turo mashi da kyau ba, aiki yake ta fama da shi, yanzu ma dan auta ce yasa ya tsaya yake hira da ita, video call Omar ya shigo yana yi da ita, shi ne ya zauna kusa da Rizwan ɗin, da ta gansa kuma sai ta ce. "Yah Rizwan inawuni". Daga haka suka fara hira ya karɓi wayar daga hannun Omar ɗin, shi ne yasa kuka ga suna waya, amma hankalinsa dukka yana a kan aikin da yake yi.

Juyar da wayar ta yi izuwa kan Chuchu dake kwance tana cigaba da yi wa Yah Jawad bincike a cikin wayarsa kamar ya aiketa. "Aunty Chuchu ga Yah Rizwan yana magana".

Da sauri ta juyo da fararen idanun nan nata tare da miƙewa zaune. "Ina wuni Yah Rizwan". Ta faɗa tana kashe wutar screen ɗin wayar Yah Jawad.

Shiru ya ɗan zuba mata idanu kamar mai tunanin wani abin, ta yi mashi kyau sosai, ga shi kuma ya yi sa'a gani ta ci kwalliya zasu fita, ai dole nema kowa ya ganta ya ji yana sha'awar cigaba da kallonta.

Sai da ta sake maimaita mashi kalmar inawun sannan ne ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta tare da amsa mata da lafiya lou Alhdulillah. Sannan ya ɗaura mata da tambayar cewa ita ce Chuchu daman?.

E ta bashi amsa da shi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tambaye ya school da kowa da kowa?.

Miƙa mata wayar auta ta yi tare da miƙewa ta koma gaban mirror ta zauna, kwalliyar face ɗinta ta fara gyarawa, dan Omar ya ce mata da ta sanya janbaki bata yi kyau ba, ta bar launin kalar lips ɗinta haka sun fi kyau, ta sanya lips balm kawai, to shi ne ta je gyarawa.

Ita kuwa Chuchu karɓar wayar ta yi suka cigaba da yin hira da Rizwan, dan shi dama yana da saukin kai sosai ba kaman su Dr Raj ba, shiyasa ma Sharifat take zuwa wajensa suke shiri, dan bashi da zafi sosai. Dan haka sai ya biyewa chuchu suka shiga hira, har da tambayarta ya yi ina wayarta, ta ce mashi yana hannun Yah Jawad.

"Me ya kai wayarki hannunsa kuma?". Ya yi tambayar yana matsar da laptop dake a gabansa ya miƙe tsaye.

"Kwace wayar ya yi dan na cika ɗaukar hoto dayawa". Ta bashi amsa tana ɗan turo baki, domin ta tuna da abin da Yah Jawad ɗin ya rinƙa yi mata a kan ɗaukar hoto.

Shiru ya yi a cikin ransa yana faɗin Jawad ka cika cin zali sosai, dan kawai tana ɗaukar hoto sai ka kwace mata waya?. A fili kuma sai cewa ya yi. "Tom shikenan idan ya dawo maki da wayar sai ki karɓi numberta a hannunsa ko a hannun auta ki kirani da numberki".

Okey ta amsa mashi da shi tare da tambayarsa ina su Yah Bilal.

Cikin zolaya ya ce mata. "Bilal kawai kika sani ba?".

Da sauri ta fara girgiza mashi kai tare da cewa. "A'a nasan su Yah Ramish mana, nasanku dukkanku ai".

Nufar hanyar fita daga cikin room ɗin ya yi, jikinsa na sanye da farar arab jallabiya, dukkansu dai kalar Akka ɗin ne, kyawawan gaske, soft skin kamar madara, sai ka rantse da Allah basu fita waje, saboda yadda skit ɗinsu yake sun ji hutu sun ƙoshi.

Cikin zolaya ya sake cewa. "A'a baki sanmu ba kam, Bilal kawai kika sani, dan ga shi shi kaɗai kika tambayi ina yake? To ya baya ƙasar ya yi tafiya".

Murmushi kawai ta sakar mashi, dan tasan zolayanta yake yi, ai babu bambanci a tsakanin ƴaƴan King, duk da cewa iyayensu basa shiri, to su dai basa faɗa, dan haka ita da yayanta Bilal da su Ramish ƴaƴan mama duk ɗaya ne a wajenta.

"Aunty Chuchu kizo mu tafi mana, Yah Rizwan kai da ka ce mun aiki kake yi ɗazun shi ne kuma ka sake biyewa Aunty Chuchu ko? Idan ka biye mata ba zata barka ka yi aiki ba". Cewar auta dake dake a saman mirror chair ta gama gyara kwalliyarta, ita dai kafarta na mata kaikayi, su tafi kawai, burinta taga sun je wannan yawon.

"Auta ai chuchu ta rigada ta hanani yin aikin ma, baki ga ma na fito waje na bar aikin ba? Sai kuma dare zan ƙarisa, yanzu dai bari mu ɗan yi hira da ita ko my sister?". Ya faɗa yana tsare Chuchun da waɗan nan idanun nasa wanda da ka gansu ba tambaya kasan tsatso ɗaya suka fito da Jawad, dan kuwa wlh idanunsu iri ɗaya sak, kamar Akka ta samu sabo ta basu tsoho..........😅

Murmushi ta sakar mashi tana ƙoƙarin yin magana auta ta rigata da cewa. "Ni gaskiya Yah Rizwan ban yarda ba, nifa nagama shirina tafiya kawai zamu yi kace zaku yi hira? Wlh idan ba so kuke na fara kuka na kai karanku wajen daddy ba Allah ku bar hiran sai mun dawo".

"Wai ina zaku je nema?". Rizwan ya tambaya.

Chuchu ce ta bashi amsa da. "Nima dai ban sani ba, kawai Yah Jawad ya ce mu shirya mu same shi a part ɗin Aunty MieMie....."

Katseta auta ta yi da cewa. "Wai dama Yah Jawad ya ce mu same shi a wajen Aunty MieMie ne kika zauna a nan ban sani ba, baki gaya mun ba, to ni dai na tafi". Tana kai karshen maganar ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita daga room ɗin mayafin kayan na jan ƙasa, ta tattaro ƙasan sket ɗin da hannunta ɗaya kamar dole.

Da sauri ita ma Chuchun ta miƙe tana faɗin. "Yah Rizwan in tafi ko?".

Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai tsareta da ido yana ta kallonta. Katse kiran ta yi ba tare da ta sake yi mashi magana ba. A hanzarce ta rufawa auta baya tana murmushi.

Kai tsaye ƙasa suka yi tare da nufar part ɗin Aunty MieMie, suna tafiya suna hira, kamar wasu taurari. A kan hanyarsu na tafiya ta wajen tsakanin part ɗin uncle Abbas da part ɗinsu suka ci karo da commander ZAFAR tare da Sadauki Hoorain da kuma wani jarumin mayaki ɗaya suna tsaye suna tattaunawa, da alama magana mai mahimmanci suke yi.

Cikin girmamawa Sadauki Hoorain da wannan mayaki suka ɗan dukar da kansu ƙasa tare da yi masu sannu, shi kuma commander Zafar bai duka masu ba, amma cikin mutunci ya yi masu sannu tare da tambayar ina zasu je?.

Chuchu ce ta basu amsa da cewa part ɗin Aunty MieMie zasu je, ita kuwa Auta tuni hankalinta ya koma kan mutuminta wato Sadauki Hoorain, ta tsaya ne ma tana tambayarsa wai ina yake shiga ne kwana biyun nan bata ganinsa sosai?.

Cikin girmamawa ya yi ƙasa da kai, da wannan sanyayyar muryar tasa ya amsa mata da cewa. "Kece kika dai'na fitowa lambu ranki shidaɗe, shiyasa baki ganina, amma ina nan".

Kallon commander Zafar ta yi kafin ta ce. "Abbu kai ma fa na dai'na ganinka

Please Login or Register in order to submit comment