Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi nai ina kuka! na takaicin sallama mai kaina danai domin sam ban shiryawa wannan rana ba ko kaɗan.
Sosai ya gasamin jikina wanda ya bani karfin bakina na soma surfa mai rashin kunya har ina cemai maye.
Shikam baya tankani se murmushi harya kammala kana yabarni nai wankan tsarki ina kuka!
Tattare zanin gadon yay ya shinfiɗa bargo sannan ya koma bakin rijiya ya wanke sa kunya kamar ta kashesa ya shanya saman igiya kana ya koma bayin tsiramin idanu yay.
"Kinyi na tsarkin?"
Tura bakina nai gaba.
"A,a sekaimin da kanka"
Nafaɗa da salon baƙar magana.
Dariya ya saki kana ya ɗage doguwar rigar jikinshi.
Idanu huɗu mukai nida abarsa wadda ashe bai saka komi ta ciki ba rigar kaɗai ya ɗora.
A firgice na saki ihun tsoronta.
Kana na rufe idanuna.
"Na rantse da Allah nayi nayifa Allah ya baka hakuri dan Allah"
Dariya yay sosai sabida yadda yaga ta haukace da ganin gidan daɗin shi dan haka rungumeni yay ta baya yana shafa gadon bayan nawa.
"Ammanata taga bebynta tana tsoro waya gaya miki ana tsoron kayan wasa?"
Zamewa nai ajikinshi ina kukan takaici na rabe agefe ɗaya na cure kaina.
Haka ya dibi ruwa yay wankan shi tare mukai alwala kana ya ɗagoni mukayo ɗaki.
Kwantar ni yay saman gado sannan ya ɗaukomin kayan sakawa da taimakon shi na saka kaya sannan shima ya saka jallabiya fara panadol ya ɗauko ya ɗauko ruwan pure water ya ɓallo ya mikon sabida yadda kaina keciwo yasa na amsa nasha sannan na koma na kwanta ina jin jikina yana mugun ciwo.
Shiko sallaya ya shinfiɗa ya tayar da sallar godiya ga ubangijin sa.

*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*15&16*


Sosai ya jima yana miƙa godiyar shi ga Allah maɗaukakin sarki, daya mallaka masa sanyin idaniyar shi Aishatul humairah, macen dayake so yake ƙauna yakeda burin ya kasance da ita muddin rai.
Har aka soma kiran assalatu yana saman darduma seda aka soma tayar da sallah a masallacin cikin unguwar tasu sannan ya miƙe gaban akwatin kayan shi ya nufa ya ɗauki turaren shi na element ya fesa a sassan jikinshi kana ya fita da sauri yana mai zira slipers ɗinshi a ƙafafun shi.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya buɗe ƙofar gidansu ya fita zuwa masallaci.
Sahun jam'i'n sallah yabi har aka idar anan suka haɗu da imran dasu baba suka gaisa a mutunce kasancewar duk anan masallacin sukeyin sallah.
Hanyar gida ya kamo cikin sauri sabida yadda ake azababban sanyi tura kofar gidan yayi kana ya mayar ya rufe sannan ya kama hanyar ɗakin innah wadda yake da yaƙinin tana saman abin sallah a zaune tana lazumi.
Aikuwa hakance ta kasance sallama ɗauke abakinshi ya shiga ɗakin.
Zaune ya tarar da inna a saman darduma carbi ahannunta daga cikin uwar ɗakin kwa ƴan bikine da sukazo daga katsina suketa faman haɗe kayansu waje ɗaya.
Agabanta ya zube gwiwarshi tare da sunkuyar da kanshi a ƙasa yanajin yadda innah ke kai kukanta wajan ALLAH maɗaukakin sarki akan ya shiga lamuran ɗan nata dama sauran musulmi baki ɗaya.
Sosai yakejin daɗin tarin addu'oin nata akan shi harta kammala a tare suka shafa.
Sannan ya soma gaisar da ita a kunyace kamar koda yaushe, itama a nata ɓarin amsa mai take a kunyace tare da alkunya irinta ɗan fari, tana tambayar shi ya kwanan humairah?
Sosa ƙeyarshi yayi batare daya ce mata komi ba ya gyara tsugunnon ya koma ya zauna a gabanta tare da tanƙwashe ƙafafunshi.
"Innah yanzu me kike ganin za,a shiryawa baƙin nan na karin kumallo? dana ce a sayo bread se a dafa tea, sannan a siyo ƙosai su haɗa dashi anjima zan saka salim ya samo musu tasin da zata kaisu tasha".
Yakai maganar a nutse kamar yadda maganar shi take a koda yaushe babu baragada.
Kallonshi tayi cike da ɗunbin tausayin shi acikin ranta, tana yabon ƙwazon ɗan nata haka nan tana jin tausayin shi matuƙa gaya sabida wahal halun da sukai mai yawa, bare yanzu da daɗin wasu suka ƙaru amman tunawa da Allah yasa taji sanyi a cikin zuciyarta.
"Yaro"!
Tafaɗa a hankali sabida sunan datake gaya mai kenan.
"Na'am innah"!
Ya faɗa shima a nutse.
"Kaga tun jiya na saka mairamu takai markaɗan gero na kwano biyu, sannan ga wake can shima na siyo za,a markaɗo se ayi ƙosai, amman yadda kagani tunda kayi niyyar alkairi ga ƴan uwanka bazan hanaka ba, asiyo kayan shayin inyaso geron semuyi amfani dashi agida".
Takai maganar a nutse.
"Tom shikenan innah".
Yafaɗa babu musu kamar yadda tun asali baya mata musu a dukkan umarninta.
Tashi daga gabanta yayi ya nufi ɗakin shi har lokacin humairah tana bacci kamar babu gobe akwatin kayan shi ya buɗe tare da zaro kuɗi acikin wanda abokanshi suka haɗa mai na jiya na gudun mawa.
Waɗanda sun kai kimanin dubu huɗu a waɗanda ya ɗebo ɗin sannan ya fita waje, shagon dake bakin layinsu ya nufa ya haɗo kayan shayi tare da manya manya biredi wanda iya na gida kawai ya siyo domin shi abokan shi sun haɗa mai nashi jiya.
Lokacin daya shigo gidan ya tarar da inna a tsakar gida tare da kanwarta suna ƙoƙarin haɗa wutar sanwa sedai yaga kamar suna magana ne akan shanyar zanin gadon da suka gani a shanye a tsakar gidan wanda shi sam yama manta dashi.
A kunya ce, ya ƙaraso gabansu yana gaisar da anty maimuna.
Cikin barkwan ci take amsa mai tana tsokanar shi.
"Kai, ka aje wannan zanin gadon anan waya gaya maka yanzu ana buɗar kaine?"
Kunya kamar ta kashe shi haka ya sunkuyar da kanshi yasan za,a rina sabida yadda yasan anty maimuna da muguwar zolaya.
Itako inna kasa tai da kanta tana sakin murmushin farin ciki.
Ledar hannun shi ya aje gabansu da sauri ya nufi gaban zanin gadon ya tattare shi ya nufi ɗakin dashi, kicin ɗinsu ya nufa ya ɗora ruwan tea, sannan ya dawo ɗaki ya tube rigar jikinshi yay saura dagashi se gajeran wando da singlet, sabida yadda Allah yayi shi da mugun jin zafi, yasa duk uban sanyin da ake tsulawa bai hanashi zagewa ba.
Zama yayi a bakin gadon tare da ɗaukar wayarshi ƙarama yana duba saƙonni.
Har lokacin daya kimanci shayin ya tafasa aje wayar tashi yayi tare da fita ya sauke sannan ya wanke tea flaks ɗin dayake sabo cikin kwalinsa ya zubo tean a ciki sannan ya kashe rishow ɗin yayo ɗaki da flaks ɗin shayin.
Komawa kicin ɗin ya kumayi, still ruwan wanka ya ɗora musu a ƙaton tukunya a tsaye yake wajan har ya tafasa sannan ya juyo rabi a bahon wanka rabi kuma a flaks ɗin ruwan zafi wanda yafi na shayi girma.
Wanka ya shiga bayan ya kammala ya fito.
Mai ya shafa sama-sama tare da mitsika turaren arabian udt, shirya kanshi yayi cikin ɗanyar farar shadda sabuwa dall se maiƙo take, lokacin wajan bakwai na safiya sauri yay ya daura agogon farar sliver a hannun shi kana ya ɗauko hula da bakin sau ciki.
Agaban gadon ya tsaya tare da zama bayan ya tura takalman gefe guda.
A dai dai kunnenta ya kai bakin shi yanajin feeling ɗinta na fusgarshi baiyi gigin matsata sosai ba sabida gudun kada ya ɓata lamarin shi domun sauri yake ya fita ya gaida baƙi suyi bankwana sabida yana da text yau a school ƙarfe tara.
"Ammatana! Ammanata!!"
Yake faɗin sunan ta a hankali kamar maiyin raɗa.
Mitsika idanuna nai a hankali ina mai yatsine face ɗina.
Sabida baccin dayake kaina.
Kafin na waresu a kansa yawani ranƙwafo saman fuskata kamar zemin rumfa.
Da baya naja jikina na matsa nesa dashi sannan nace.
"Miye ne wai baka san sunana ba se wannan munafukin sunan wanda nakeji yana tarwatsamin zuciyata da tsanarka".
Nafaɗa kaina tsaye.
Amai makon naga yaji haushi kamar kullum innai masa rashin kunya.
Senaga yay murmushi.
Ya miƙe tsaye tare da zube hannayen shi a aljihun shi.
"Allah yay miki albarka da wannan kyauta da kikai min a daran jiya ubangiji ya bani ikon riƙe ki amana Allah ya haɗa kammu,nasan bakida matsala ajikin ki tunda har harshen ki ya iya sarrafuwa wajan yimin rashin kunya, ga ruwa can a fulas ki ɗauka kiyi wanka ga tea nan da kaza kici naso na kasance dake a yau domin na baki kulawa sedai kash inada uziri a makaranta, wanda bazan shigo gida da wuri ba, kiyi kokarin gyara kanki sabida gudun jin zafi irin na jiya domin yau ma bazan ɗaga miki ƙafa ba".
Yafaɗa yana mai ƙoƙarin kama hanyar fita daga ɗakin.
"Inka dawo lafiya kenan? ina roƙon Allah akan yasa kai hatsarin mota kai mummunan nakasar da bazata barka kai wani abu ajikina ba mugu azzalumi kawai".
Amai makon naga ya dawo da baya ya ɗauki mataki akaina senaga yay ficewar sa batare daya nuna ma yaji mai nace ba.
Komawa nai na daki bangon ɗakin ina daga kwancen sabida takaici sau tari wannan halin shariyar nashi yana bani haushi ai abu yazama kamar kurma tun a gida inna guma masa takaici baya tankani kuma ko a fuska baze nunan ba, miskilin tsiya kenan.
Kuka nasaka mai cin rai kafin na tashi cikin ƙarfin hali na sauka daga gadon alwala nayo nazo na tayar da sallah ina kuka.
Har na idar kana Na koma gado na ƙara kwanciya sabida yadda ƙasana kemin zafi kamar an tsaga da reza.

Zuciyar shi babu abinda take se tafarfasa jinsa yake kamar ya mutu matarka ta sunna wadda ka amarce da ita a daran jiya itake maka wannan fata? seda ya tsaya ya dai daita nutsuwar shi sannan ya nufi ɗakin inna.
Zaune suke suna karin kumallon safiya..........


*Littafina na kuɗine naira ɗari 300 ta wannan asusun bankin 0078174806 starling bank, shedar biya ta nan 08142105218, Auren bare naira #500 ta accnt dake sama*
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*17&18*


Sallama yay cikin nutsuwa tare da shiga cikin falon ya zauna a saman tabarmar dake shinfiɗe a gefe ɗaya, Sosai suka gaisa shida ƴan uwansu na katsina har wasu na tsokanar shi da cewa.
"Ango kasha ƙamshi".
Mayar da hankalin shi yayi wajan iyatu kakarshi yana jin yadda take faman janshi da wasa, cike da sakin jikin sabon dayay da ita yake mayar mata da martanin tsokanar tata.
"Hamma umaru barka da safiya yaya amarya?".
Cewar nuratu wadda take sanye da shuɗiyar atamfa wadda akaiwa ɗinkin riga da skirt ta yafa mayafi a kafaɗarta gabanta ɗauke da trollyn kayanta tana mai danna wayar hannunta.
Tsira mata idanun shi yay batare dayace mata komi ba, seda ya ɗauki ƴan daƙiƙu kafin ya furta mata.
"Lafiya ƙalau Nur! amman mai yasa bakiyi break fast ba?"
Sunkuyar da kanta tai ƙasa tanajin daɗin sunan daya gaya mata, kafin tace.
"Ayyah hammana naci abincin nan kam, amai zanyi kafin mukai can bana break da safiya haka".
Murmushi yayi mata yana mai cewa.
"A,a kaga baturiya seki ɗauki bread ɗin ki saka a ledar in kinji yunwa kyaci a mota".
Dariya kurum tai mai batare data ce mai komi ba.
Miƙewa yayi yana mai zaro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa anty maimuna.
"To anty ga wannan ba yawa kwa rage na mota ni zan wuce makaranta ne amman akwai, abokina salim ze kawo mai tasin daze kaiku tasha".
Amai makon ta amsa seta ɗaga jakarta ta ɗauko damin kuɗi guda biyu kowanne ze kai dubu hamsin a daure.
"Ga wannan namu ne na dangi mahaifiyarka ni ina wakiltar ƴan uwana da basu zoba amman ga saƙonsu nan da nawa ba yawa, kasan anata aikin gona a ƙauye, gakuma na dangin mahaifinka da iyatu ta bani ɗazu na baka harda nasu harɗo duka suna aikin bazara ne, yasa basu zoba, sabida haka mu bazamu amshi ko kwabonka ba yadda kake hidimar mahaifiyarka da kanwarka ma ya ishemu Allah ya tsare mana kai umaru".
Tausayin ahalin nasane ya ɗarsar masa a basu da shiɗin basu kasa taimakon shiba, wani maƙwallaton abu mai nauyi ya haɗiye kafin yace.
"Nagode sosai amman suna fama da kansu ai basa bada kuɗi mai yawa haka ba".
"Kai kaci ubaka dan ubaka inda muna dashi bamu zamuyi maka auren ba, in kana dashi ai barema zakama bare naka, maye mahaifinka bai mana ba, shi kaɗai muka haifa amman ya share mana hawayen dubu, kai yanzu wani irin saƙone baka aika mana ta tasha? shi kansa arɗon bada irin kuɗin da kake bamu bane ya zuba amfani gonar bana ba?"
Cewar iyatu wadda take faman taunar goro tana zuba masa magana.
Murmushi ya sakar mata.
"Afuwan gimbiyar mata uwar gida sarautan mata na".
Gaba ɗaya dariya ƴan ɗakin suka saka masa kowa yana faɗin albarkacin cikin bakinshi.
"Yaro bakai karin kumallo ba zaka fita? ina humairan ita kuma?"
Inna ta faɗi hakan tana mai kallon shi.
"Inna innaje school zanyi ita kuma akwai shayi a ɗakin bacci take in ta tashi zata karya".
Yafaɗi hakan cike da soyayyar mahaifiyarshi aranshi inba uwa ba waze maka haka?.
"Badai wata matsala ko? naga fuskarka shigowarka kamar a damuwa?".
Sosa kanshi yayi.
"Inna zancen text ɗinnan ce ta sakani damuwa sabida kinsan mun kusan soma exam's wadda kuma daga ita zamu shiga lavel 4 daga nan kuma se service wannan shine damuwata".
Yakai maganar wadda sam ba haka take ba kawai danya ɓoye laifin da humaira tai masane a fitowarsa.
"Kaita addu' insha Allahu, ubangiji ze dubeka Allah yay maka albarka".
"Amin"!
Yafaɗa yana maijin sanyi aranshi, haka sukai sallama dasu iyatu yabar ɗakin kai tsaye gidan su humaira yaje a kunyace suka gaisa da baba again sannan ya wuce ɗakin anty.
Zaune take a saman tabarma tana haɗa kayan dake gabanta su anty uwani sunata shirin tafiya suma.
Gaisarsu yayi a kunyace kafin ya zaro kuɗi na daga cikin wanda ƴan uwanshi suka haɗa mai.
"Anty ga wannan ki basu na mota ni zan wuce school".
Fafur suma ƙin amsa sukai, sema albishir ɗin kayan gara da anty tai masa wanda baba ya haɗa komi yanzu za,a miƙa kafin danginsu na katsina su wuce.
"Haba anty duk irin hidimar da baba yayi mana sekuma yay wata gara dan Allah a bari ina da kudin kuma inada kayan abinci".
Cikin nutsuwa anty ta dubeshi.
"Kai ma kasan baya yi maka hakan domin humaira bane yayi maka ne sabida yana tausayin ka nidai fatana dan Allah ka riƙemin ita da amana kasan har yau akwai kuruciya atare da ita".
Sosai kalamin anty suka bigi zuciyarshi tabbas yanawa humaira so mai tsafta sedai halin dattako irin na mahaifanta yasa yaji ya kara mata ninki fiye dana da.
"Insha Allahu anty bani da bakin gode muku face nai muku addu'ar gamawa lafiya kun ɗauko ƴa kun bani batare da kun duba niɗin waye a halin yanzu ba, kun biyamin sadakin aurenta kunzo kun haɗani da kayan abinci, inama abba na yana darai da idanun shi sun nuna mai yadda amininshi ke lura da lamuran ɗanshi".
Yafaɗa idanunshi na sauya launi zuwa jajur!
Sosai anty take bashi baki tare dasu anty uwani harya mike ya fita daga ɗakin.
"Niko anty ina yabon umar ɗin nan gaskiya humaira tai dacen miji sedai muce Allah ya basu zaman lafiya".
Cewar anty zulfa kanwar anty.
"Hakane zulfa'u Umar yarone mai ƙwazo nagari baida matsala, sedai ƴar takuce take mai tsiya dan Allah in kunje can ɗin ku kara mata faɗa sosai"
Nan suka hau tattaunawa akan halin humaira har lokacin da akace su fito domin miƙa kayan gara.

Shikuma yana fita adai daita sahu ya samu direct BUK ya nufa yana duba agogon dake hannunshi, lokacin daya isa malamin nasu yazo dan haka bai tsaya bata lokaci ba ya wuce aji tare da mayar da hankali ga text ɗin dake gabanshi domin baida matsalar karatu sabida yana da naci wajan duba manyan littattafai.
Haka ya wuni a makaranta baya da wani time cikakke sabida zafafan text ɗin da aketa faman yi masu wanda ko abinci baiciba sedai sallah kaɗai ke fitar dashi, daman babu wanda yasan zancen aurenshi bare ai masa Allah sanya alkairi domin imran ba dp ɗinsu guda ba, sukuma su salim daman abokai ne na unguwa da aka taso tun ƙuruciya tare bare su faɗa, duk da shiya soma buɗe musu ƙofar aure acikin abokan nashi.

Lokacin dasu anty uwani suka isa gidan inna har su iyatu sun fito da kayansu gaban motar da salim ya samo musu, ganin karamar mota da kayan abinci ta tsaya a kofar gidan yasa suka dakata seda inna ta hango su zulfa kannan anty sannan taɗan saki ranta.
Suka karaso suka gaisa a mutunce.
"Ai daman tafiyar wuri zamuyi yanzu haka kayanmu muke sakawa a mota in mun fita mu biya muyiwa su malam yusufa godiyar karamci".
Cewar iyatu wadda anty uwani ke gaisarwa.
"To madallah muma kayan abinci baban nasu ya bada a kawo musu ne yanzu".
Cewar anty uwani.
Sosai iyatu tahau godiya kafin su rankaya zuwa cikin gidan kayan abince madai daita baba ya haɗo hardasu daddawa kubewa da sauransu, godiya mai yawa su anty maimuna kannen inna sukai kana suka dauko kudin tukwici zasu basu.
Fafur sukaki amsa suna cewa.
"Ai anzama ɗaya wallahi su bazasu amsa ba".
Rankayawa sukai ɗakin humaira gaba ɗayansu har su iyatu.
Maganganun sune ya farkar dani a kunyace na tashi ina cije bakina ina gaisar dasu.
Babu abinda iyatu take face tsokanata.
Haka na sinne kaina a jikin anty zulfa ina murmushin dole.
"Amaryarmu ina kwana?"
Naji zazzaƙar muryar wata farar budurwa a cikin kunnena tana min murmushi.
Kadaran kada han na dubeta.
"Ina gajiya"
Nafaɗa ina mai gyara kaina jikin anty zulfa ganin bata sami fuskaba yasa taja ta fita, ganin haka yasa su anty zulfa suka sakani na sako hijab ɗina muka fita waje har suka gama shigewa motocinsu muna tsaye har motar ta tashi wadda naji suna maganar sesun je sunwa babana godiya kafin su wuce.
Haka naji muryar iyatu a cikin motar tana cewa.
"Ke nuratu tashi ki koma gaban mota nan mun matsu".
Wannan ta ɗazun nagani ta fito ta shiga gaba tana ɗagawa salim hannu da murmushi har motar tabarmu
Wajan ya rage dagani se inna da maryam dasu anty muke awajan kafin muma mu wuce cikin gida......
Ɗakin inna naje muka gaisa tana tambayata yana kwana?
A kunyace nake amsa mata kafin na tashi nai ɗakina sabida su anty uwani suna ciki, abakin kofa na haɗu da maryam itama gaisawa mukai.
Na kama labule na zan shiga ɗaki naji dirin muryarsu anisa nafisa da kuma sadiya, haka muka rankaya cikin ɗakin dasu.............


*Littafina na kuɗine naira ɗari 300 ta wannan asusun bankin 0078174806 starling bank seki turo sheda tanan 08142105218, AUREN BARE kuma naira 500 maiso ya nemi numbern sama*
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*19 & 20*

NOTE: _Humairah tana da shekaru goma sha shida (16 yrs ) aka mata aure sedai ta'taso a mai girman jiki wanda tun tana da shekaru 12 ta zama mai jikin girma,haka zalika tana aji ɗaya a sakandire yanzu haka aji biyu zasu shiga, shikuma umar yana aji uku (lavel three) a jami'a wanda nan da ƴan watanni ze tafi aji huɗu ( lavel four ) haka zalika yana da shekaru ashirin da tara a duniya ( 29 ) dafatan makaranta sun fahimce ni_
*******
Da shigarmu muka tarar dasu anty uwani sunata faman gyaramin saitin jeren kayan ɗakin, su nafisa zama sukai a ƙasan leda nikuma na zauna a bakin gado ina ɗan cije bakina sun ɗauki kusan a wanni biyu suna gyaramin kayana na ɗakin domin hatta akwatunan kayan ya umar seda suka gyara musu wajan zama,Sannan anty zulfa ta ɗauko tsintsiya da abin kwasar shara ta share tsakar ɗakin tass sannan ta fita da sharar tazo da kaskon wuta.
Gaushine cikin shi se faman huci yake, haka ta ɗora a saman madubin da seyau suka ɗaura masa ruwan shi kana ta ɗebo turaren wuta ta zuba aikuwa nan da nan kamshi ya gauraye ɗakin.
Ita kuma anty uwani kicin ta nufa ruwan zafi ta ɗora seda yay ɗumi sannan ta zuba ɗan gishiri kaɗan sannan takai banɗaki sabida tun zuwansu suka fuskanci umari ya kashe arna a daren jiya.
Ina zaune ta shigo ɗakin lokacin anty zulfa ta shinfiɗa sallaya a ƙasan leda duk mun koma samanta mun zauna.
"Humaira sauya kayan jikin ki'kizo banɗaki ina jiranki, ku'kuma nafisa kutafi gida kucewa anty ta bani dahuwar nan danai ɗazu da duku dukun safiya".
Amsa mata sukai da.
"To"!
Sannan suka miƙe suka fita nikuma gaban siff da aka jeran kayana yanzu na bude, zani balle ɗaya na atamfa leda na ɗauka sannan na tube kayan jikina na ajesu a ɗan wannan kwandon na zube kayan wanki wanda yazo a saitin kayana na robobi.
Bin bayanta nai har cikin bayin.
Hannu taɗan saka a ruwan taji baya da zafi zau sannan ta dubeni.

"Tunda bakida jikin kirki maza zauna cikin bahon nan ki ware ƙafafunki ruwan ya game miki jikinki".
Banawa anty uwani musu, bare kuma yanzu daman abinda nake bukata kenan sabida yadda ƙasana yay kamar an tsaga da reza.
Fita tai tabani waje na tube zanina tare da shiga kamar yadda ta umarceni wani sayiyin ɗumi nakeji acikin dukkan ilahirin sassan jikina ina jin ruwan yana min daɗi fiye da yadda yay min a ɗazu wato shidayake ɗan koyone yasa bai ƙware sosai wajan gashin ba.
Tsirawa nippy ɗina idanu nai ina kallon yadda samansu, yay wani irin ja kamar an watsa wani abu mai ja gawani irin ɗan tashi dayay kamar wani abu ya mintsine shi, hawaye ne ya tahomin tunawa da yadda yay budiri dasu kamar wani jariri, ina zaune har ruwan ya salamce sannan na mike ina mai ɗauko butar ƙarfen danaji wani ruwan ɗumin ne acikinta wanda dashi na samu na kuma yin wankan sabulu, sannan na duba saman hangar banɗakin cikin ikon Allah naga sabbin makilin da burush guda biyu, ɗaya na ɗauka na matsi makilin ɗin sannan na soma wanke bakina ina gamawa na ɗaura zani na, nabar bayin.
Ɗakin na koma a zaune na tarar dasu gawani babban fulas a gaban anty uwani.
Gaban madubi naje na ɗauki man basilin na soma shafawa ƴar hoda na mitsika a saman fuskata sannan na lakato man na goga a leɓɓana, sif na bude na ɗauko pant da bra na koma ƙuryar sif ɗin na sakasu, sannan na ɗauko rigar material na rariya na sakata ɗinkin buba.
Bakin mayafi karami na yafa sannan na ɗauki humra na shafe jikina bayan na goga alumun a hammatana sabida gudun wari tare da daukewar gumi duk da ina shebin, amman hakan bai hana zufa taruwa a hammatana ba.
Seda na kammala sannan na ɗauki fulas ɗin shayin daya dafa na isa gabansu na aje.
Kayan shayi na haɗa musu harda kazar jiya na tura musu gabansu.
"Anty zulfa kuyi kari nasan koba kuci komiba".
Murmushi ta saki.
"Ga surukan banza ko? waya gaya miki mu sakarkaru ne? salon mijinki yazo yagammu a haka ai ba'aji, muba wannanne ya kawomu ba".
Rau-rau nai da idanuna zanyi kuka!
kafin na ƙaƙaro muryar shagwaɓa nai amfani da ita wajan yi musu magana.
"Kai anty zulfa,wai anty uwani bazakuci ba? nifa ba yunwa nakeji ba koma kun bari sedai yasan yadda ze dasu inya dawo".
Nafaɗa ina mai zama gefensu.
Babu wadda ta tanka abinda nike faɗa sema wannan fulas ɗin da anty uwani ta buden kana ta turomin shi gabana.
Wannan karan ba kaza bace.
Dafaffun ƴan shilane guda biyu waɗanda sukai wani irin baƙi na magani, domin har kaina nikejin kamshin magunguna waɗanda aka masu mis da kayan kamshi.
"Maza cinye tas ki bani fulas ɗin amman banda tauna kashi".
Banida bakin musu haka na amsa nacinye da ƙyar ina ɓata fuskana sabida yadda baurin maganin ke hawa kaina.
Dana kammala ta mikon haɗin zuma a wani babban cup amsa nai nasha, bayanshi ta bani wani haɗin na kayan ƴaƴan itace hardasu markaɗaɗɗiyar tufa da kankana acikinshi da madara cikina kamar ze fashe na shanye na mika mata cup ɗin.
"Amshi wanna farin miski ne wanda kika sha kuma na hadin zumar nan na sanyine dan haka ki kula bana son a kawon kararki".
Anty uwani ta kai maganar tana mai mikomin wata farar karamar kwalba amsa nai kamar kunya zata kasheni haka na sunkuyar da kaina kasa.
Kafin su cigaba damin nasiha akan zaman aure harda min gargadin kula da innah wanda sukace na dauketa kamar anty.
Daman inna

Please Login or Register in order to submit comment