Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi kuma ya zauna kan tabarma ta kusa da
Shadad yana shafa masa kai, na kawo musu ruwa cikin
jug, na nemi kujera 'yar tsuguno na zauna. Na gaishe
su suka amsa, sai dai shi daya kafe ni da ido yana
kallona, duk da ba wuta sai hasken farin wata, ya ce,
"Ni ba zaki gaidani ba?" Na kalleshi irin hararar masoya,
na maida kaina kasa. Ya ce, "Shine na kiraki dazu wai
kike cewa baki gane ni ba." Shiru nai ban tanka ba Ya
ce, "Ka gani ko Hashim ta gane ni." Sagir yayi dariya,
"Kila bata gane ka din ba." Abubakar ya ce, "Bani aron
hankalinki nan. Shi yasa na kwaso abokaina dan su
zama shaida, da farko ina sonki, kuma ki ban amsa. Ta
dago ta ce Abubakar bana sonka, ba aibu bane dan
kince baki sona, in yaso sai sonki ya zama ajalina,
amma daga yau idan har kinki amince min ba zaki kara
ganina ba koda cikin mafarkine.
Gabana ke faduwa, na ce, "To ai ban ce bana sonka
ba." Hashim ya ce, "Pls Hafsa, magana daya zamu yi
tunda kina da hankali tin taba aure bai kamata mu
tsaya muna wasa da hankulan juna ba." Abubakar ya
ce, "Magana daya ce Malama, kina sona?" Kalma daya
ce da Hashim ya fada ta dagan hankali, wai na taba
aure? Inama na taba auren ai da bazan damu ba, sam
banji maganar da Abubakar yake min ba, su duk sun
dauka aure nayi na haihu, to tun kan na samu matsala
gwara na rabu da shi, sai dai sonsa ya zama ajalina, na
ma rabu da iyayena ballantana shi?
Tsawar da ya dakamin ita ta dawo dani daga tunanin
da nake ya ce, "Kin maidani dan iska ne ina magana
kin min shiru?" Hashim ya ce, "Ki yi magana mana
Hafsa."
Muryata ta soma rawa irinta masu kuka, "Lallai ina son
ka har ba zan iya kwatanta son da nake maka ba. .....


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 2-08
Posted by ANaM Dorayi on 11:28 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Domin sonka ya shigeni ne a lokacin da nake tunani na
ha'ka dogon rami na saka so a ciki na rufe shi, ina fatan
kowa ya mutu ya huta. Amma abin bakin ciki sai da ya
fito har ya zo ya kama ni, a bisa adalci Abubakar bai
cancanta na zam matarka ba, matsayinka na kamili, kada
ka so kaji dalili ko ka matsa min na fada maka." Na kifa
kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka irin wanda yake sa
jiki motsi, gidan ya yi tsit, gidan shiru kamar ba
mutane.Abubakar ya ce, "Malama ki nutsu ki fiddamu
daga tunani." Hashim ya ce, "Baiwar Allah ki nutsu ki
mana bayanin komai, da kin san irin son da wannan
bawan na Allah yake miki hakika da baki masa haka ba,
ni abokinsa ne kuma dan'uwansa ne na jini, Mahaifina
wan Mahaifinsa ne, tare muka taso kamar 'yan 2, ya san
sirrina haka na san nashi, tunda muke da shi ban taba jin
ya ce yana son 'yan matan da suke nacin sonsa ba, na
kosa na ganki mai sa'a." Na dube shi na ce, "Ina son sa,
kuma ina matukar farin ciki ace na samu mutum kamar
Abubakar ya zama Uban 'ya'yana, amma kash!!!" "Amma
kash me?" Sagir ya ce, "Dan Allah ki daure ki fada mana
Insha Allahu za'a samu mafita."
Na mike tsaye, "Ba wai ka aureni ba, da zarar ka ji
matsalar, sirri ne zan fada muku." Na yi shiru, na yi ajiyar
zuciya cikin kudurin gaya musu, "Amma ina so na gaya
maka Abubakar ina sonka, kuma duk lokacin da ka tuno
da ni ka tuna cewar na soka, zan ci gaba da sonka har
karshen rayuwata."
Na kalli Hashim na ce, "Za ka so dan'uwanka ya auri
karuwa? Wadda ta bar gidan iyayenta saboda cikin
shegen da tayi? Ta shiga duniya tana zaman kanta?"
Abubakar ya mike zumbur ya ce, "Cikin in, in, wa? Wa
kenan kina nufin ke karuwa ce? Cikin shege kika yi kika
haifi Shaddad?" Na ce, "Kwarai kuwa, ciki nayi."
Ban ankara ba naji saukar mari wanda idanuwana suka
daina gani na wucin gadi, ya ce, "Tur da haihuwarki, kin
cuceni da kika bar ni na fada son ki, Allah ya isa!" Ya
fice fuuu!!! Sagir da Hashim suka bishi.
Shadad ya farka a gigice sakamakon kukan da na fasa,
na zauna kasa ragwab, ya zo ya fado jikina muna kuka
tare da ina fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha."
Mun yi kuka ya ishemu, amma har daga bisan Shadad ya
yi bacci, ni kuwa tuni zazzabi ya rufeni hakanan hawayen
idanuna bai kafe ba, abin da nake tsoro kenan rabuwa da
Abubakar gashi nan kuwa, Ya Allah! Ya ma aka yi na
fada masa zancen a baibai?
Kafin safe ko motsi na kasa yi don zazzabi da ciwon kai,
Ga fuskata ta kumbura sumtum saboda marin da
Abubakar yayi min, ga kuma kukan da nayi, haka muka
kawan gidan ko sakata ban iya samu na sa ba saboda
azabar ciwo.
Da asuba da kyar na iya tashi nai alwala, a zaune na yi
Sallah, Shadad ma Sallah kawai yayi dan ba zan iya yi
masa wanka ba, har 8 ina kudundune ban san me zai
biyo baya ba.
Shin Abubakar zai iya rabuwa da Hafsat? Ko Munnir yana
sane da cikin da yayiwa Hafsay? Baba fa da bangaren
Inna kuwa suna ganin Hafsa?
Duk amsar tambayoyin nan
Sae kun biyo mu a littafi na 3
Godiya gareku




Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment