Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ce in naki fa? Ya ce
ki gamu da Allah. Ya fada kan gadon shi ya ci gaba da
bacci. Ina ta neman makullin ina sanda, amma Allah
baibani ikon ganin sa ba, don haka naje nayo alwala
nayi sallah. Ina zaune ina tunanin anya kuwa wannan
dan tahalikin cutata zaiyi?
Amma bari ya tashi na gwada yi masa dabara duk da
naga shima kar yake kallo na, amma da macucci ne da
tuni ya aika abinda zuciyarsa take so.
Daf da la'asar ya farka, ya shiga bayin nake zaton ruwa
ya watso da naga ya jima kuma ya shiga da wasu
kayan, ya fito yayi sallah, sannan ya ce nifa ina jin
yunwa. Na hada rai na ce to ni ina ruwana, ya ce ke
mijinki yana jin yunwa zaki ce ina ruwanki? Na ce ni dai
ka bude ni in tafi. Ya kira waya wai a kawo masa jalof
din shinkafa da farfesun koda.
Ya dube ni me zaki ci? Na ce nidai burin in bar nan, ya
share ni. A raina na kudurce ana kawo masa abincin
zan fice koda tsiya, amma ana danna kararrawar kofar
sai naga ya zuge gilas din window yayima ma'aikacin
magana ya amsa, ya zauna yana ci yana waya da
Hashim cikin fillanci jifa jifa yakan sako hausa, anan ne
na gane zancena yake yi, lokacin da yake cewa Allah
Hashin in zamu shekara anan sai randa ta saurare ni
zata fita, ya sake juyowa ya ci gaba da fillanci.
Ni kuwa nayi zugum kamar wacce take neman gafara,
ganin yamma tana kara yi bansan abinda zai biyo baya
ba idan dare yayi, don haka na ce bari na saurare shi,
kafi sannan bari na gwada dabarata ko da lalata yake
sona.
Sai da ya gama wayar na ce to naji zan saurare ka,
amma banda yau. Don yau ina azumi ne, in ma jiki na
kake so ka bari gobe zan baka. Ya dube ni da sauri,
jikinki? Ina jikin kin yake? Ya ja tsaki banga jiki anan ba,
ni ke nake so, zatinki na ke so ba jikin ki ba, kin tsaya
kina zabga min karya wai kina azumi.
Ki tsaya muyi magana shine mafita, amma har wani jiki
kike dashi? Na ce in ba jikina ba me kake so? Ya ce
halayenki da ke kanki nake so, inna sauraroka, yi
batunka. Ya ce tashi ki matso nan dan bazan iya daga
murya ba kamar fada.
Na dan matsa ya ce bana bukatar sai kince kina sona,
na riga naga sona a idon ki, fada min inda su Baba
suke in tura magabata na, nayi shiru, tunani nake ga
garin zuwa amma babu zanin daurawa, lallai zanso
haka sai dai nasa in Abubakar yaji labarina bazai aure
ni ba. Sannan in shi ya yarda iyayen shi baza su yarda
ba. To ni da na shigo duniya ma yaya za'ayi mutum
mai mutunci ya aure ni? Yanzun ma ina zan san inda
iyaye na suke?
Tunda nasan ba gidan kanshi yake ba, gidan haya ne
kila yanzun ya tashi...
"Ba ki bani amsa ba." Ya katse ni. Na ce ni fa kaga ka
kyale ni, bazan aure ka ba, ya ce nasan kina tunanin ki
fada min kin taba aure kada in ce bana son bazawara,
to kin min kuma zan aure ki a haka. Shike nan? Takaici
ya sa wasu hawaye zubo min, nace a raina da na taba
aure me zai hana ni fada?" Ya ce ki fada min
damuwarki bana son kuka.
Na ce, ina rokon wata alfarma a gurinka, don Allah ka
zauna a matsayin yayana, mai bani shawara in bukatar
hakan ta taso, ka zam mai min fada a duk lokacin da
nayi ba daidai ba, na dube shi in nayi abin duka ma ka
doke ni....." Na fashe da kuka tare da sa kaina cikin
hajabi.
Ya zo ya tsuguna a gabana, ban sani ba sai da naji
muryarsa dab dani. Abin zaifi armashi idan kika amince
na zama mijinki majibancin lamuranki, mai saki cikin
farn ciki, mai kare lafiyarki da mutuncinki, hanyar shiga
aljannar ki.
Hafsat ina so da kaunarki, ki amince. Wallahi nasha
alwashin zama dake har karshen rayuwata, bazan sake
ki ba yanda mijinki na baya yayi, zan rike danki tamkar
ni na haife shi."
Na dago ina kallon shi, shi zatonshi na taba aure mijina
ne ya sake ni, ina ma ace haka ne? Da tuni nayi
magana. Na ce kayi hakuri duk ba wannan bane, don
Allah ka kyale ni kawai yanda ka ganni." Shima shiru
yayi. Can ya ce. "To naji, yanzun ki fada min inda
mahaifanki suke kawai." Na ce ban sani ba, wallahi ban
san inda suke ba. Ya ce to shike nan share hawayen
naki in maida ke gida.
A cikin mota ni dashi kowa tunanin shi daban. Motar
tsit kamar babu kowa a ciki. Shi a tunaninshi kila bayan
nayi aure baban Shadad ya sake ni nabar gida, kila
Iyayena suna son in koma gidan mijina ni kuma naki.
Ni kuma tunani na shine zanso matuka Abubakar ya
zama mijina, don wannan gata ne Allah yayi min in dai
na same shi a matsayin miji. Amma nasan da wahala in
zai ji labarina ya aure ni. Ya tsaya kofar gidan mu jikin
sa sanyaye, ya kifa kanshi a sitiyarin mota. Na bude
kofar motar tare da cewa sai anjima.
Ya zaro wayata daga aljihunsa na baya ya mika minn ni
na manta ma ina da wata waya, na karba jiki babu
kwari na shiga gidan sukuku, nayi sallolina na zauna
cikin tagumi , Allah nake roko ya zaba min mafi
alkhairi.
Misalin karfe takwas suka shigo shi da Shadad, yau har
cikin dakina ya shigo, Shadad ya zauna a jikina shi
kuma ya tsaya da leda a hannun shi. Ya ajiye min
ledar. "Kici wani abu zan kira wayarki anjima. Gobe da
safe zan wuce kila na biyo."
Sai naji har raina bana son tafiyar tashi, sai dai bani da
izinin hana shi. Na bude ledar kaza ce da madara mai
sanyi, rabona da cin kaza tun lokacin Hajiya Hindu
Likita, Allah ka yafe mata har in gushe bazan daina
mata addu'a ba.
Na ci na koshi, Shadad dama da guntun baccin shi ya
shigo, yana zuwa yayi bacci. Nayi shafa'I da wuturi na
kwanta. Sam bana jin bacci zuciyata ce ma take ta
azazzala ta tare da fada min bazata juri Abubakar ya
subuce mata ba gara ma in san abin yi. Na kosa ya kira
ni, sai gurin sha daya da rabi lokacin na debe tsammani
da kiran sai ga wayata na ruri.
Na daga da sauri don marmarin jin muryarshi.
A tare muka yi sallama, sannan muka kara hada baki
gurin amsawa. Ya ce kin fara bacci ne? Na ce a'a" ya
ce ki fada min tsakani da Allah ki kasa bacci saboda
menene?" Na ce bazan iya ce maka ga dalili ba." Yayi
shiru, can yace sona ne ya hanaki bacci kamar yanda
sonki ya hana ni.
Muna son juna mezai hana ki bani hadin kai muyi aure?
Duk abinda kike so zan maki Don Allah ki tainake ni
Hafsat."
Muryata can kasa, jikina yayi lukwi nayi juyi zuwa ruf
da ciki. Sannan na ce in nace ba jin wani abu mai
kama da so a tare dakai, hakika nayi karya. Sai dai in
na saki jiki zuciyata tazame da sonka, a karshe zan sha
wahala, duk ranar da kasan who I am.
Ya ce ki fada min komai, bazan taba gudar ki ba, don
kin sami wata matsala ko kina da matsala da iyayenki
zan fahimce ki sosai. Na ce zan fi so in kabar batun
aurena, ya ce in yi yaya da sonki to?"
Na ce hakuri mana, nima hakuri zanyi." Ya ce amma da
gaske kina sona? In na duba wasu abubuwa zan iya
yarda cewa ina sonka, kai kadai ne kasa ni in manta
alkawarin da na dauka na cin mutuncin duk wani namiji
da yayi min kallo fiye da daya.
Kaine kake sani inyi abinda ban niya ba. Ya ce har kin
sani naji sanyi a zuciyata, don Allah ki taimaka muyi
aure. Gidan mu an matsa min in fito da mata, yanzun
haka an bani lokaci." Na ce dama baka da mata? Ya ce
ina da mata, na ce to bazan taba auren ka ba don na
san wata rana zata yi min gori.
Da saure ya ce bani da mata wasa nake maki. Na ce
duk da haka kayi auren ka ni bazan iya aurar ka ba,
hirar mu daga jayayya sai zance soyayya, tare da
magiya. Abin al'ajabi sai na jiyo kiran sallar farko.
Na ce, "Sadeek kaji abinda naji kuwa? Ya ce me? Na
ce, kiran Sallah fa." Ya dubi agogo yanzun nan fa muka
fara magana, na ce shi ne nima na gani, to zaka shigo
kafin ka tafi? Ya ce bazan shigo ba, kuma bazan sake
zuwa kano ba tunda kince baza ki aure ni ba, kin kuma
ki fada min dalili. Bance komai ba har lokacin da yace
min sai wata rana, ya kuma kashe wayar shi.


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sanadin Boko 2-7
Posted by ANaM Dorayi on 11:27 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Munir ya dubi mahaifiyar shi, fuskar shi babu walwala.
Ta ce ya akayi? Ya mika mata takardar hannun shi,
sakamako ne na gwaji ya amso, da sauri ta mike tsaye
HIV? Subhanallah! Muje wani asibitin, ya ce Momy tun
daga Dubai suka fada min ban yarda ba, sai da nazo nan
na sake yi har kashi biyu, ta dauki waya jiki na bari ta
kira Dady a waya.
Kuka ta saka masa tana fadin Munir yana da kanjamau.
Shima Munir din kuka ya saka, a sukwane Dady ya baro
ofishinsa zuwa gida, ganin su cikin halin damuwa harda
kannan shi, sai hankalin Dady ya kara tashi.
Ya ce ku kwantar da Hankalin ku zan shirya mana zuwa
America za a duba shi."
Momy ta ce, zan fi son haka. Shi kadai ne ya rage min
yanzun tunda yayanshi suka yi fada suka kashe kansu a
Maleshiya, yanzun kuma a ce shima yana da kanjamau?"
Cikin kankanin lokaci suka shrya suka tafi. Sai dai kash!
Can ma sun tabbatar yana dauke da ita. Sai dai sun basu
wasu maganguna cewa ya dinga sha, sannan idan sun zo
nan ma ya dinga shansu.
Jiki babu kwari suka dawo.
Sannu a hankali ya hakura ya cigaba da zuwa aikin sa,
yana shan magani. Sai dai koda yaushe yana zargin
mahaifansa sune suka ja masa wannan halin, SANADIN
BOKO. Da sun bari yayi aure ya tabbata baza ya zama
daya daga cikin masu neman mata ba, gashi yayyanshi
sun mutu su biyu. Shi kuma ga halin da yake ciki.
Ya hadu da wata yarinya 'yar mutunci, Usataziyya a rufe
cikin hijabi da nikabi, ya ce yana sonta. Tuni ya fara
zuwa shira.
Yarinya mai suna Nanah A'isha ta amince dashi, sam bai
fada mata yana da ciwo ba, kuma ya gama sheke
ayarshi, kuma yanzun 'yar mutunci yake son ya aura don
cuta.
Iyayenshi ma basu nuna masa abinda zaiyi bai dace ba,
sai ma suka shiga lamarin suka yi dumu dumu suka yi ta
barin kudi aka sa bikin.
Wani daga cikin abokan Munir yayi mata text ta waya
wai Munir yana da kanjamau, ko ya fada mata? In kuma
bai fada mata ba to ta sani yanzun. In kuma tana musu
to ta gayyace shi suje ayi gwajin jini.
Nanah ta firgita kuma ta sanar da mahaifanta. Sune
suka nemi Munir da ya zo suje ayi gwaji, nan da nan ya
zuke daga nan kuma sai ya samu Nanah yana borin
kunya, wai ya fasa tunda iyaynta basu yarda dashi ba.
Ta ce to menene don sunce muyi gwaji, ai ba sai ta
mummunar hanya ba ake dauka, ko malamai sunce ba
laifi bane don anyi gwaji.
Ya ce shi ya hakura, ta ce Allah ya hada kowa da
rabonsa.
Gida uku yana neman aure amma ana dagaoshi, bakin
cikinsa ya karu. Dole ya koma wajen tsohuwar
budurwarshi wadda suke rigima suna zargin junan su.
A nashi tunanin ita ce ta sak mishi, ita ma tana tunani
shi ya saka mata. Ya ce mata suyi aure kawai tunda
suna shan magani, ta amince nan dai iyayen su suka
shiga barin kudi tunda duk suna dashi.
A yawon amarcin su ne suka je America aka duba su in
da Likita ya tabbatar masu zasu iya zama indai suna
shan magani, sai dai yana gani da wuya su sami
haihuwa.
Su basu damu ba, amma da suka zo gida Momy ta
damu. Ta fadawa Dady cewa ita yanzun ba za ta samu
jika ba a wurin yaranta maza?
Ya ce kada ta damu, tunda ga 'ya'yanta mata. Haka suka
ci gaba da zama shi da matar shi a unguwar Kinkinau.
Sai dai kullum yana cike da bakin cikin ciwonshi, wanda
yake danganta shi da iyayenshi duk SANADIN BOKO.
***************
Baba ya dubi Umar ya ce, "Tunda ka yi aure ka kwashe
kannanka baka son zuwa duba ni, gashi bani da lafiyar
da zan fita nema.
Ya ce "wallahi Baba bana son zuwa ne in ban sami dan
abinda zan riko muku ba, yaran nan kuwa na kwashe su
ne dan kuji saukin kudin haya.
Nima can kasan buga buga ce kawai. Bus din tawa
kwanan nan kudi kawai take ci kullum sai nayi gyara,
Allah ya taimaka.
Umar ya ciro dubu daya ya bashi tare da cewa "Ga
wannan sannan ga doya nan" ya ce na gode Allah ya
saka da alkhairi"
Baba ta shigo ta ce, "Mun gode Umar Allah ya ba da
lada."
Har ya mike zai fita, ya ce Umar zomana" Ya dawo ya
zauna. Baba ya yukura, Babah ta kama shi ta sa mishi
filo a bango ya jingina.
Ya dube shi dakyau.
"Umar wai har yanzun babu labarinHafsatu ne?" Umar
ya daure fuska, shi kam in karatune wannan tambayar
to ya jima da haddace ta.
Babah ta ce "Malam kai ne fa da kanka ka kore su, ba
dole suyi nisan kiwo ba? Gara ma innar su sunsan inda
take, amma Hafsa yanzun wayamasan tana mace ko a
raye oho.
Umar ya mike tare da cewa, "In da rabon ganawa za a
gana." Baba ya ce, "Umar ina cike da nadamar abinda
na aikata.
Hakika ina zaton nine na yiwa Hafsa baki har kaddara
ta fada mata, da ina mata addu'a da bata shiga wannan
halin ba, ko dai zaka sa cigiya ne?
Umar dai gani yau Baba yafi kullum rudewa akan batun
Hafsat, sai ya lallaba shi da cewa.
"To Baba, za a cigita kada ka damu" ya ce to Umar, a
cigita. Allah yasa a dace."
Tabbas tun bayan rabuwar shi da innar su Hafsat yaga
matsaloli kala kala, ga ciwo ya sa shi a gaba, wai suga
ya kwanta a asibiti har sau biyu.
Umar ne ke ta fama dashi, don ma Allah ya taimaka
Innar su ta sa shi ya saida mashin din ta cika masa ya
sai Bus ya diban lodin kasuwa daga Rigasa.
na dama ta shige shi yanzu tun da ya rasa matar shi
fatansa ya samu yar. Cikin haka ne umar yaga yar uwar
inna mai suna murja a wata ziyara da ya kai
munanfashi. Yace yana sonta itama ta amince, nan aka
kare komai inda aka sha buki,tare da dan madaidai cin
gidan da ya kama mai daki 3 don haka ya kawo kannan
shi zuwa gidan. Tun baba yana dan fita har ta kai baya
iya fita din ma, ga ka‘idojin abinci, gashi ba kudi. Yanzu
baba bashi da burin da ya wuce yaga hafsat, shikam
umar ya kance bai san inda zaije yaga hafsat ba, domin
yayi bakin cikin abin da ya faru. Kuma hafsat itace silar
rabuwar iyayen su, shi sam bai ga laifin baba ba, tun
da dai dai gwargwadon ilimi ta samu, sun dage sai tayi
jami‘a, to ga abinda ya biyo baya yanzun.
**************
Haka inna anata ban garen tana zaune lafiya gidan
mijinta, da yayan taguda 2. Kuma duk sanda umar yazo
takan tambaye shi ko ya sami labarin hafsat. Yace,
inna ki daina batun hafsat, babu inda za‘aje nemanta.
Ita tasan inda muke, inda muna ranta kamar yanda take
ranmu da tuni tazo koda zamu kashetane. Kum inna ya
kamata ki sauwaka ma kanki batun ta, dubi yanda
tabaki kunya, ta zubar da kimanki ta kashe aurenki,
dan kawai kin tsaya mata ta sami gishirin zamani, wato
ilimi. Ta miki sakamako da haka. Inna tace, ina zaton
kadarace ta fadawa hafsat, yanzu da tatafi ba asaniba
ko tana raye ko tana a ma ce, kilama ta mutu gurin
haihuwa. Umar yace, to muyi adu‘a kawai Allah ya yafe
mata. Inna tace, amin. Amma nafi dora laifin kaina.
Don da lokacin da mahaifinku yace bayaso tayi boko da
na hakura da yanxu ban bar yaya na ba. Da yanzu bata
gudu ba. Umar yace duk mu bar wanan ga kadara,
Allah shine mafi sanin da lilin da hakan ta
faru,tsakaninta da mijinta akwai mutiny's juna, haka
nan ya yansa ta hada da nata yayan ta sunguma.
*********
Abubakar ya dawo gida cike da rashin kwarin gwiwa.
Cikin kwanakin duk ya canja ba kwanciyar hankali.
Ummi ita ce ta fara gano haka acikin gidan su, ta
dunga matsa mashi da son jin matsalar shi. Yace, kinyi
kan kanta da in fahimtar dake halin da nake ciki. Tace
zan gane hmma. Yace nida hafsat muna son juna, sai
dai a kwai wani dalilin da take ganin zai hana mu aure
wanda ban san dalilin ba. Kiyi shuru da bakinki kada
wani a gidan nan yaji wannan zancen. Ummi tace,
hmma ina tunanin zaka iya shawo kan kowace matsala
da zata hanaka auren anty hafsa. Tunda ka iya shawo
kan lamido ya yarda ka aure ta. Abinda ko iyayenmu ba
zasu iya kwatanta hakan ba. Kai sadauki ne, kana da
nasara a kan duk abinda kasa a gaba.ina ji ajikina zaka
auri anty hafsa. Dadin kalaman ummi sun karfafa mishi
gwiwa sosai, har ya bata kyautar wayar da take ta
nacin ya bata. Da yace sai ta gama secondary. Amma
yana bukatar ya kara natsuwa kafin yagane ta in da zai
shawo kan matsalar. Ko da ya fada ma Hashim cewa
hafsat taki, tace ba zata aure shi ba saboda wasu
dalilai nata. Hashim yace, kada ka damu zamuje tare
kuma zata yarda. Amma yanzu abinda nafi so ka
nutsu, iyayanmu su san ka karbi fadi. Dan haka yau
dadadare zamuje zance. Daga ofis super market ya
wuce inda ya siyo kayan shafe-shafe da tande-tande
dan suyi tsaraba. Lokacin da fadi ta nufo su abubakar,
ya zuba mata ido. Gaskiya tana da kyau, sai dai baya
jinta a rai kamar hafsa. Ta zauna suka gaisa, tace ya
dawo lfy? Yace lafiya lau. Hashim yace, mun zone
dama mu dan gaisa. Amma yanzu bari in matsa ku
zanta ke da yallabai. Abubakar yace kaje ina, kamar dai
zamu shekara? Bai saurari Abubakar ba, ya fita.
Fadi tace, don baka sona shi ne zaka ce wai sai kace
zaku shekara? Ni to ina son ka. Ya dube ta kin ji
abakina cewa bana sonki? Tace, banji ba, amma naji
yanda kaita kokarin doje ma aurana. Ni kam ko wane
lokaci nayi sallah ina fada ma Allah cewa ya bani kai
amatsayin miji na, gashi ya amsa. Ranar da aka kawo
mintin bai kon mu da sa rana ban iya bacci ba don
murna, gani nake daga bacci ya debe ni zan farka in ga
cewa ba gaskiya bane. Zugun abubakar yayi yana kalon
kasa, wannan al‘adar tana cikin al‘adun da ya tsana a
mata. Ba wai haramun bane mace tace tana son namiji,
amma a kalla kijira ya fara furtawa. Shi yasa yake son
hafsa, don tana da kamun kai. Shi a nashi ra‘ayin in dai
mace zata fito tace tana son namiji ba mijinta ba, ko
kuma shine yazo da da‘awar son shi gurinta ta amsa
mashi ba. To wannan bata cika mace ba a nashi
ra‘ayin.........ta katse shi. Na san waccen yarinyar da
kake nema ta kano din tafi ni kyau ne ko? Ya dago kai,
please ki muyi maganar da ta shafeni da ke, bana so
kina saka hafsat. Tayi dan diM, can tace shi kenan.
Yanzu wane shiri zamuyi? Ya kamata bukinmu yazo da
sababin salo na burgewa acikin zuri‘ar mu. Yace, ko?
Tace, sosai kuwa. Yace, to ki rubuta duk abinda
kikeson ayi, in yaso in nazo zan gani. Ya mike zan tafi
gida, ga yar tsaraba nan. Ya nuna mata lader. Cikin
doki tace, amma na gode. To yanzu har zaka tafi
bamuyi wata fira ba sosai. Wani lokacin in nazo zan
dade. Ta rako shi har bakin gate in da hashim yake
tsaye da jamilu yayan fadi. Suka gaisa da jamilu, inda
ya shiga jin jina masa da cewa ya gode da wanan
jahadin da yayi a gurin lamido, inda ya samo musu
yanci. Abubakar yace au! Kai ma kayi farin ciki ne?
Jamilu yace, ba dole ba, don yarinyar da nagani
zuciyata ta so ba yar zuri‘ar mu bace. Son yarinyar ya
shige ni a kudu muka hadu da ita lokacin da muka je (N
Y S C) Allah ya shi maka albarka bayan bukinka zanyi
maganar tawa. Abubakar yace Allah ya taimaka, mu
kam bari mu tafi.
sati 2 tsakani da zuwan shi kano, lamido ya kirashi to
kasan lokaci yana gabatowa, don ha sai kafadi inda
iyayen yarinyar nan suke saboda aje a kammala da su
suma. Zufa ce ta soma tsatsafo ma Abubakar, amma
sai yace, am.....dama mahaifinta yayi tafiya ne shi
yasa. Amma idan ya dawo sai in fada muku saboda ya
riga ma ya san da maganar, kuma su a shirye suke.
Lamodo yace, to cike da damuwa ya fito, dole ne ya
koma kano gobe sai sai ya takurawa hafsa don yasan
abinda take ikirari zai hana auren su. Ya kira phone din
hashim yace, ka shirya gobe juma‘a zamu shiga kano,
sai mujuyo ranar sunday. Hashim yace, to
*******
Nikam tun ranar da abubakar ya tafi na shiga halin
kunci da damuwa. Na rasa dan ragowar farin cikin da
ke tare dani. Ina zuwa makaranta da gurin aiki, amma
bana iya cin wani abu. Ban amince ina son abubakar ba
sai yanzu. Har shadad yafini hakurin rashinsa, duk da
cewa sun shaku matuka. In nayi kamar in kira lanbobin
da ya bani sai in fasa. Nace, kai gara in koyi yanda
zanyiwa kaina fada, in hori zuciyata ta saba da rashin
sa kada in zurma da yawa in kamu da ciwon zuciya a
banza. Don nasan babu mai hankali da zaya aureni. Kai
akwai daran da na rabashi ina kuka. Ba zance irin
kukan da na saba bane, wannan kukan son abubakar
ne. Yau satin mu 2 rabon mu dashi. Ina zuwa ne cikin
aji, duk da hankalina yana gurin malamin amma har
yayi ya gama ba zance ga kalma 1 da yake fadi ba.
Tunanin Abubakar sadeek kawai nake yi. Na san abaya
na so munnir amma ban shiga irin wannan ma
tsanancin halin ba. Wani irin abubuwa nake ji game
dashi, waddanda ba zan iya fasrasu ba. Kenan da ba
son mannir nayi ba. Kenan da shirme nakeyi. Ya
rintace tasa nake ganin kamar son shi nake. Karshe ya
cuceni, shima dama ba sona yake yi ba sha‘awa ce.
Gashi dalilin abin da yayi min yasa na rasa abubakar
sadeeek.
har aka watse cikin aji ban sani ba. Da yake ni ba kawa
ko aboki gareni a makaranta ba, babu wanda ya kulani.
Kasancewar ko yaushe cikin daure fuska nake, masu
son kulani ma tuni sun watsar dani, saboda rashin
fuska. Ringing din wayata ne ya dawo dani daga
tunanin da nayi zurfi acikin sa. Jikina lakwas na dauka.
Nasan rahama ce, tunjiya take min nacin inje tana
nemana, ba tare da na duba fuskar wayar ba na kaita
kunnena. Muryar da tayi min sallama ce tasa naji na
watsake. Bansan na mike tsaye ba, ina cewa.
Wa‘alaikumus-salam. Yace, ina kike ne? Sai na samu
kaina da wani jan aji, ina tambayar wanene? Da sauri
yace, kina nufin baki ganeni ba ko? Nace, eh. Yace,
good! Ki fada min inda kike sai inzo in sameki. Nace,
ban gane kowanene ba ya za‘yi in fadi inda nake? Sai
kurum ya kashe wayar shi. Take naji haushin kaina,
mutumin da nake son gani ruwa a jallo amma yanzu na
tsaya salo. Da sauri na fita na nufi gida, ko in biya in
dauki shadad wai ina zaton yana kofar gidanmu. Ganin
bashi na juya da sanyin jiki na nufi makarantar su
shadad na daukoshi muka nufo gida. Hashim ya kali
sagir yace, kaima kazo muje mu 3 don mu sami
galabarta. Sagir yace, nifa shaknar hafsat nake ji, gashi
tana bani girma kada taga zamu matsa mata. Rahama
tace, ka daure kuje, kila ganin idonka ta sausauta.
Abubakar yace, nifa hafsat nasani tana sona. Dalilin da
take fadin cewa ba zai bari muyi aure ba shine nake
son ji. Sagir yace, to ku tashi muje. Suka mike yana
mitan cewa dan miskilanci irin na hafsa waima nine
bata gane ba yau. Hashim yace, kai dai wannan abu
yayi maka ciwo. Kasani ko kila bata gane kadin bane?
Sagir yace, wannan yanuna kai kadai kake sonta, ita
bata sonka kamar yanda kake zato. Abubakar yace
tabbas tana sona, amma ku muje dai.
Misalin karfe 8 na dare, Shadad ya yi barci, muna kan
tabarma a tsakar gida, ni kuwa lokacin zuciyata ta
kekashen idanuna sun bushe ina ta tunanin ina cewa,
"Ya Allah, dama haka so yake?" Na tashi zaune, na
mike tsaye, na jingina da bango duk banji dadi ba dai,
zuciyata tana tuhumata da cewa nice na bar dama ta,
me yasa na nuna ban gane shi ba? Sai kuma wata
zuciyar tace ki daina saka kanki cikin matsala, ba zai
aureki ba, keda kika yi cikin shege?!!!
Na koma na kwanta, hawaye na sintiri a idona daga
gefen idona zuwa kumatuna, so matsala ne, dama ban
san Abubakar ba, dama ban zo Kano ba, dama ban je
bikin Rahma ba.
Bugun kofar ne ya sani na dawo cikin hayyacina, da
sauri na mike cike da fatan shine, ba tare da na saka
takalmi ba na nufi kofa, ban bukaci na san waye ba na
bude kofa. Ganin shi tsaye ya sa na sauke wata
nannauyar akiyar zuciya, sai kuma Miskilanci ya motsa
na ce, "Daga ina? Ka canja ne ba kace ba zaka kara
zuwa ba?" "Au korata kike? To shike nan bari na koma."
Da sauri na ce, "Ni bance ba, ai ance bakonka
Annabinka, ka iya shigowa." Ya ce, "Zaki ji da gulmarki.
Hashim ku shigo." Na shimfida musu tabarma suka
zauna,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment