Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su daga na fadi gskya?" xagawa da ita cikin kasu yyi gaba daya, sae tabe baki take, ita a dole bae mata ba daga karshe tace "ni dae sir na gani, mu tafi kawae" yyi murmushi yace "to mu je tudun wada ki ga polytechnic dinsu na science?" Tabe baki tayi tace "ni bn san wajen ba" yace "ae nuna maki xan yi" tace "tohm mu je" polytechnic din art dake unguwan rimin ya fara nuna mata yace "akwae wani a barnawa ma, but ynxu na tudun wada xa mu" suna isa junction road yace "kalli can ki ga stadium dinsu" juyawa Afeefah tayi da sauri tana kallon inda yake nuna mata ta xaro ido tace "wnn dan wurin sir?" Dariya yyi ssae yace "don baki shiga bne" ta tabe baki tace "um ni dae dan karami ne" kwafa yyi yace "bbu ruwan sir dae, bari yan kd su ji ki su kama ki" dariya tayi tace "ni ina ruwana da su" ta sardauna crescent ya shiga sbda traffic, ta ce "Sir Dubi fa titin mu ma ya fi nasu girma da kyau ssae" yyi murmushi yace "eh mana" cikin mintunan da basu wuce goma ba suka isa poly road, Afeefah ta xaro ido tace "Sir nn ne polyn nasu?" Yace "yea" tace "kai shine yayanmu ke wani cewa makarantun kd sun fi namu ashe ba hka bne" dariya kawae Dr Sharif yyi ya nufi main gate din k.p.t, ya karbi gate pass ya shiga, dariya kawae Afeefah ta dinga yi ita a dole ta raina polyn, Dr Sharif ya girgixa kai yace "kin san shekaran polyn nn nawa?" Ta girgixa kai, yace "uhm ki bar raina sa, babban makaranta ce yarinya," tace "bn yadda ba, ka gaya min shekaran sa nawa!" Yace "this polytechnic was founded in 1956! Ki lissafa shekarunsa ki ga tun kan Independence, ya fi north west din nn naku da kike brag da iyakacinsa shekara biyar, kin manta slogan din kadunan ne wae? 'Center of education! Let me remind yhu" Afeefah ta saka dariya tace "kai Sir" murmushi yyi ya xaga da ita cikin polyn gaba daya snn suka fita ya shiga da ita ostrich bakery dake wajajen ya siya mata snacks kala kala, suka kama hanyar U.rimi, ya juya yana kallonta yace "its almost 6 pm da mun shiga gamji in ji cmmnt din ki, nd beside ma it's nt decent mu shiga da yamma" Shiru tayi bata ce komae ba, murya can kasa ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je muyi hoto?" Shiru tayi kmr me naxarin abinda yace, sunanta taji ya kira, ta dago manyan idonta tana kallonsa a hnkli yace "Mu je studio muyi hoto nace?" Dauke kanta tayi, sae kuma tayi murmushi ta gyada masa. Hadadden studio ya nufa yana gama parkin ya juya yana kallonta yace "mu je" bude kofar tayi ta fito shima ya fito, yana gaba tana biye da shi suka shiga studio din, Afeefah taji baxata iya hoton ba bayan Sun shiga sbda kunya, ma'aikatan wajen duk a tunaninsu pre wedding pics suka xo yi, Dr Sharif yyi murmushi yace nml pic suka xo dauka, da kyar Afeefah ta iya tsayawa suka yi hoto da Dr Sharif tsabar kunya sae wani rurrufe fuska take, kala hudu kawae suka yi ya biya kudin suka ce su dawo gobe su karba bayan sun tura ma Dr Sharif a wayarsa, kasa kallon Dr Sharif Afeefah tayi har suka shiga mota, Eatry taga yyi parkin ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo ya shiga motar ya mika mata ledan hannunsa, ta karba ba tare da ta kallesa ba, ya tada motar suka nufi gida, Dr Sharif na gama parkin bayan sun isa gida Afeefah ta bude motar ta riga sa fita da sauri tayi cikin gida, Amina dake kitchen ta fito tace "sannun ku da dawowa" Afeefah tayi murmushi kawae ta ajiye ledan hannunta tace "ina Fadil Anty?" Amina tace "tare mu ke girkin a kitchen ae, gashi can cikin kekensa" dariya Afeefah tayi ta mata sannu da aiki ta nufi sama da sauri kafin Dr Sharif ya shigo.
Bayan isha Ma'aruf yace da Dr Sharif "ya mgnr daxu Dr, mu tafi gun dad din ne ynxu? naji kace gobe xa ka koma!" Dr Sharif yace "to mu tafi frnd" takwas da kusan rabi suka isa can gidan, Dr Sharif yace "look captain kunyan dad nake wllh, just go in and explain to him" Ma'aruf ya hade rae yace "kaga matsala ta da kai koh" Dr Sharif ya marairaice masa yace "don Allah ka rufa min asiri kai ka shiga I just cnt go in" tsaki Ma'aruf yyi ya bar sa cikin motar ya nufi cikin gidan, ba karamin farin ciki dad yyi da xancen da Ma'aruf ya xo masa da ba, dad yace "ae wnn ba matsala bne in har uwar tawa tana so, kaga sae a hada da nasu jamila kawae, ka xo min da ita gobe mu ji ta bakinta" Ammi dake xaune falon tayi shiru dae tana kallonsu bata ce komae ba, dad ya juya yana kallonta yace "ko ya kika ga Uwar gida?" Sauke ajiyar xuciya tayi tace "Amma kuma Alhaji naga ae yana da kyau a fara jin ra'ayin iyayenta na kano ka ga ba wajen mu take ba bare kayi saurin yanke hukunci hka!" Dad ya hade rae yace "ji wani xance don Allah, da nan da can din ba daya ba mne, kuma nasan baxa su ce don me ba, don duk abinda na yanke tamkar su suka yanke ne" Ammi tace "To Allah rufa asiri, amma Dr Aliyu kam mutum ne, Allah dae ya xaba abinda ya fi alkhairi" Dad yace "yauwa xancen knn, Ameen ya Allah" Ma'aruf ya sallami iyayen nasa ganin ya bar Dr Sharif a waje snn ya bar gidan, Yana shiga motar ya sakar ma abokin nasa murmushi yace "In'sha Allah kmr ka samu Zainab frnd" murmushi Dr Sharif ya mayar masa yace "I trust yhu captain" goma saura suka isa gida, Amina tayi masu sannu da xuwa snn ta dauko masu abinci ta ajiye masu tsakiyar rug din falon ta nufi sama, Afeefah na shirin kwanciya Amina tace "kaddai har xa ki kwanta" Afeefah tayi murmushi tace "um bacci xan yi" Amina tace "to baki tafi kin ma Sir sae da safe ba yace baxae kwana nn ba" Afeefah ta kauda kanta a hnkli tace "toh" dariya Amina tayi ta fita daga dakin, Afeefah ta mike ta sa hijab dinta har kasa snn ta fita daga dakin ta sauka downstairs. Xaune ta samesa da Ma'aruf, ta karaso cikin falon kanta a kasa ta xauna daga kasa, cike da xolaya Ma'aruf yace "kin sakko fira knn" bata fuska tayi tace "A'a" yyi dariya ya mike yace "bari to in baku waje." Sae dae Ma'aruf ya haura sama snn Dr Sharif ya juya yana kallon Afeefah yace "har kin gama jin Kunyan" rufe fuskarta tayi da sauri yyi murmushi yace "to dawo nn" bata masa musu ba kanta a kasa ta dawo gefensa ta xauna daga kasa. Wayarsa ya mika mata yace "kin ga hoton da kika ki gani daxu" murmushi tayi ta karbi wayar tana kallon hoton nasu, ba karamin kyau suka yi ba barin Dr Sharif, tace "um bayan ka fini kyau!" Yace "kin dae fini" sunkuyar da kanta tayi tace "bn yarda ba" Ma'aruf ne ya sakko downstairs ya shigo falon da sallama yana mika ma Afeefah waya yace "ga yayanki" ba karamin faduwa gabanta yyi ba, ta karbi wayar da kyar, juyawa Ma'aruf yyi ya koma sama, sarae Dr Sharif ya lura da halin da Afeefah ta shiga, wayar na soma ringing ta daga a sanyaye tace "yayanmu!"

Eeshatullah Goni๐Ÿ˜˜

๐ŸŒธ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป 'Ya mace kyautar Allah๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป๐ŸŒธ

A true life love story

By Ashmaad

42___43
Shiru Afeefah tayi jin ya Aliyu bae ce komae ba, can ta kalli screen din wayar ta ga bai kashe ba kuma, a hnkli ta kuma cewa "yayanmu!" Yace "ina jin ki, ykk" jin yanayin muryar tasa yasa da damuwa tace "baka da lfya ne yayanmu?" Yace "lfyata qlau, I called daxu ma'aruf yace kin fita da matarsa" Afeefah ta gyada kai da sauri tace "uhn!" Yace "Shknn gud nyt, just called to say hi" murmushi tayi murya can kasa tace "am missin yhu yayana" shiru ya dan yi sae kuma a sanyaye yace "No yhu are nt Zainab! nasan haushi na kike ji ynxu kina ga kmr ina takura ki koh? Kiyi hkuri with tym xa ki gane meyasa nake maki hka kuma xan daina kin ji" shiru Afeefah tayi ita ma jikinta yyi sanyi, kmr xata yi kuka tace "yayanmu wllh ni bna fushi da kai, kaga ae bn da waya ne ynxu shi yasa bana kiran ka" ya Aliyu yyi shiru bae ce komae ba, a hnkli tace "Allah nayi missing dinka yayanmu, I missed yhu a lot" dan murmushi yyi bae dae ce komae ba, kmr xata yi kuka tace "ka ji!" Murya can kasa yace "naji! Kina son gani na to?" Xaro ido tayi da sauri tana kame kame tace "Lah ae to kila ma na kusa dawowa ko yayanmu, mun kusa komawa sch ka tambayi su Anty jiddah" yace "toh shknn, Allah dawo da ke lfya" a sanyaye tace "Ameen yayanmu" katse wayar yyi lkci daya, duk sae ta ji ba ddi abinda ta ce masa, da da ne kullum cikin kiransa take in ta xo kd wani lkcn ma har cewa take ya xo ta gansa, amma wnn karan har bata son ya kira, juyawa tayi a sanyaye tana kallon Dr Sharif taga kallonta yake, dauke kai yyi da sauri, ita kuma ta sunkuyar da kanta, ya mike ya karbi wayarsa a hannunta yace "je sama ki ce masu xan tafi" tace "har xa ka tafi sir" yace "yea" mikewa tayi a sanyaye ta nufi sama. Ma'aruf ne ya sakko tare da Amina yace "wato dae da gske baxa ka kwana nn ba ko Dr" Dr Sharif yace "abokina na jira na tun daxu, so I have to go," Amina tace "to amma yaya don Allah ka xo kayi breakfast a nn" yace "xan xo in'sha Allah" Makullin motar Ma'aruf ya dauka yace "da motar ka xan tafi, gudnyt" juyawa Ma'aruf yyi yana kallon Afeefah da ke tsaye yace "Baxa ki masa rakiya ba" Amina tayi dariya tace "to kai kaji ya mata sae da safe shi din?" Dariya Ma'aruf yyi yace "wae nn kunyar surikinsa yake" juyawa Afeefah tayi da sauri ta nufi sama, Amina tayi dariya tace "Ina kuma xa ki Anty yana fa jiran ki ne a waje" sae da Ma'aruf ya sa baki snn Afeefah ta sakko a kunyace ta nufi kofa ta fita. Har Dr Sharif ya tada motar ta karasa kanta a kasa tace "Sae da safe sir" yace "Allah ya kai mu" bae kuma jiran jin abinda xata ce ba ya ja motar ya bar wajen, jikinta yyi sanyi ta bi sa da kallo, juyawa tayi da sauri tun kan ta fara hawaye ta nufi cikin gida da gudu ta haura sama ta shige daki, sae a snn ta fada kan gado ta fashe da kuka, tayi mai isarta daga karshe bacci ya dauketa nn kwance. Washegari misalin Karfe sha daya Afeefah na kwance daki kmr mayya taki fitowa har Amina ta gaji da xuwa cewa ta sakko ta kyaleta, bude kofar dakin aka yi ta daga kai don ganin waye, Amina ce ta tsaya daga bakin kofa tace "to ae kya fito ynxu tun da sir ya xo koh?" Murmushi kawae Afeefah tayi, Amina ta juya ta bar dakin, mikewa Afeefah tayi da kyar ta sa hijab dinta ta fita daga dakin fuskarta a daure, yana xaune falo yana shan coffee, ta karasa kanta a kasa ta xauna kan rug din falon, kin cewa komae tayi shi ma hkn, can dae a sanyaye tace "ina kwana sir" yana kallonta yace "lfya Zainab," har yyi shiru sae kuma yace "wat made yhu cry?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, ya ci gaba da shan coffeen sa, mikewa tayi xata bar wajen yace "ina kuma xa ki?" Girgixa masa kai kawae tayi sae ga hawaye, dauke kai yyi ya dauki envelope karami dake kusa da shi ya mika mata yace "ga hotunan! ur copies" risinawa tayi ta karba murya can kasa tace "ngdd" "sit" yyi instructing dinta, ba musu ta xauna, yace "kar ki min kuka" gyada masa kae kawae tayi, ya dauko wani leda ya mika mata, kin karba tayi da farko, amma ganin ynda ya tsare ta da ido yasa ta sa hannu ta karba duk da bata san meye ba, ajiye mug din hannunsa yyi yace "xan koma kano" dago dara daran idanuwanta tayi tana kallonsa, a hnkli tace "to ngd sir Allah tsare hanya," yace "Ameen Zainab!" Kira min Amina, mikewa tayi ta nufi sama, tare suka sakko da Aminan ya mike yace "sae kin xo meenah, I will b on my way ynxu" Amina tace "kai yayana baxa ka jira Abban Fadil ba," yace "mun yi waya da shi, nace baxae same ni ba, beside mun ma hadu daxu da safe ae" Amina bata so hka ba a sanyaye tace "to shknn yaya ina xuwa" sama ta nufa, ya juya yana kallon Afeefah, murmushi yyi ganin ynda ta bata fuska, yace "me ya faru kuma?" Kmr xata yi kuka tace "ni ma wajen Mami na nake son komawa" dariya yyi yace "ae nn da few dayz xa ku koma sch," Amina ce ta sakko rike da leda ta mika masa tace "gashi yaya ka kai ma teemah" hararanta yyi yace "wa xa ki hada da kaya?" Marairaice masa tayi tace "ba jirgi xa ka bi ba yayana" karba yyi yace "shknn sae mun yi waya" Juyawa Zainab tayi ta haura sama da sauri, Dr Sharif yyi dariya yana kallon Amina yace "xa ki sha lallashi yau knn" dariya tayi tace "wae baxa ka tafi ba?" Yace "wae xata koma kano ita ma" dubu goma ya ciro ya daura kan fadil ya shafa kan yaron , yyi pecking dinsa yace "gudbye son" godiya Amina tayi masa ta raka yayan nata har gate, snn ta dawo cikin gida, dakin Afeefah ta shiga ta sameta xaune tana rusa kuka, dariya ssae abun ya bata, ta dake ta shiga lallashinta amma kmr dada tunxurata take hkn yasa ta bar dakin. Da yamma misalin Karfe biyar Afeefah ta bude ledan da Dr Sharif ya bata, waya iPhone 7 ta gani, tuni ta kwalalo ido a dan tsorace tana kallon kwalin wayar, mikewa tayi da sauri ta bude jakarta ta saka kwalin da ganinta kasan ba karamin tsoro ta ji ba.

After Magrib Ma'aruf ya tafi da Afeefah can gida, a hanya take gaya masa wayar da Dr Sharif ya bata, yace "iyye, lallai Aliyun nn na ji da ke, to kin gode, idan mun koma gida sae ki kirasa kiyi masa gdya, gobe sae in siyo maki sim" Afeefah tace "toh yaya"

ba karamin kunyar tambayar da dad ke mata Afeefah tayi ba, taki dago kanta don ji tayi da ma ta nutse wajen kawae, Ammi tayi dariya tace "ka bar ni da ita kawae Alhaji, xata gaya min gskya" dad yyi dariya yana kallon Afeefah yace "to tashi ki tafi" mikewa tayi kanta a kasa ta bar falon, dad yyi murmushi yace "Allah ya ji kan Umar ya gafarta masa," Ammi tace "Ameen ya Allah" snn ta mike ta bi bayan Afeefah, bedroom dinta ta kai ta ta xaunar da ita gefen gado tace "kar ki ji kunya ta dota, ki gaya min gskya kina son Aliyu wan matar yayan ki?" Afeefah ta sunkuyar da kai bata ce komae ba, sae da Ammi tayi da gske snn a hnkli ta gyada mata kai a kunyace, Ammi tayi murmushi tace "toh shknn tashi ki yi tafiyar ki" mikewa tayi da sauri ta bar dakin ta shige na su Ilham. A hanya xa su koma gida Afeefah ke ce ma Ma'aruf "yaya amma don Allah kar a gaya ma su Mami, kasan Abbanmu karatu yake son muyi, ni sae na gama karatuna" kmr xata yi kuka ta kare mgnr Ma'aruf ya dan tabe baki yace "na ji" duk da kawae amsa mata yyi don shi ya ma fi son a aurar da ita da karatun hofin. Hka Afeefah ta karashi hutun ta a Kaduna duk ta kagu ta koma kano ta rasa dalili, ana gobe xata koma Abba ya sa ya saleem ya yankar mata ticket, tsaraba ssae Ammi tayi mata, hka ma Anty Amina, ya Ma'aruf kuma laptop ya siya mata, Saleem kuwa da ya tambayeta me take so kawae Ca tayi yar karamar Nokia xae siya mata, da yamma Ya Ma'aruf da Anty Amina suka rakata airport, suna nn har jirgin yyi take off snn suka koma gida. Adnaan ne ya tare ta a airport din kd, Afeefah tayi mmkin da ya Aliyu bae xo tarar ta ba as usual. Bayan sun kama hanya tace "ya Adnaan yayanmu fa?" Adnaan yace "yana gida" shiru tayi bata kuma cewa komae ba har suka isa gida, bata damu da murnar dawowanta da yan uwanta ke tayi ba ta nufi sama da sauri ta shige dakin ya Aliyu, yana tsaye waya na kare kunnansa alamar waya yake, da gudu ta rungumesa tsam cike da farin ciki tace "yayanmu" da farko dakewa yyi, tana dago dara daran idonsa ta daura kan nasa kawae ya kasa, lkci daya ya sakar mata murmushinsa Mae kyau ya ja kumatunta yace "Welcm" bata fuska tayi tace "shine baka xo daukana a airport ba ko yayanmu" ajiye wayar hannunsa yyi yace "kin gaya min xa ki taso yau?" Ta wara ido tace "yaya ka manta bnda waya" yace "na tuna," tace "amma ya saleem ya siya min yar karama bn fara amfani da shi ba" gyada mata kai kawae yyi, ta juya ta nufi kofa tace "bari in je in gaida Mami" bin ta yyi da kallo har ta fita. Tana fita dakinsu ta nufa da sauri ta bude jakarta ta ciro wayar da Dr Sharif ya siya Mata ta shige bayi da sauri ta shiga kiran layinsa, yana dagawa tace "Sir na dawo" yace "haba, yaushe kika dawo" tace "ynxun nn" yace "welcm dear, result din ku ya fito" xaro ido tayi tace "da gske sir? Ka duba min nawa?" Yace "yep na duba, Allah ya taimake ki a course dina kadae kike da carry over" dafe kirji tayi sae kuma ta saka masa kuka, yyi dariya ya katse wayar. Ta ci kukanta ta koshi ta fito daga bayin. Cikin jaka ta boye wayar da sauri. Da daddare Afeefah na fiddo da tsarabar su jiddah wayarta dake cikin jaka ya soma ring, xaro ido su Jiddah suka yi jin Ringtone din, da gudu Afeefah ta nufi jakar don mancewa tayi bata sa a cylnt ba, kashe wa tayi gaba daya ta mayar jakar, Jiddah tace "iPhone Afeefah? Wa ya siya maki" bata fuska tayi tace " ya Ma'aruf" bata jira cewarsu ba taje ta ci gaba da abinda take, Sadiya ta sauke ajiyar xuciya har da su Sumayya. Hka Afeefah ta dinga kaffa kaffa da wayar kar yayanmu ya gani, laptop kuwa da ma ta kai ma Mami tace Ma'aruf ne ya bata, wayar kuwa bata nuna mata ba sae wnda saleem ya siya mata, ana gobe xa su koma sch da daddare Afeefah na xaune ita kadae daki ta shige cikin bargo ta gama waya da Dr Sharif knn tana danne dannenta, ya Aliyu ya turo kofar dakin ganin tun yamma bata sakko falo ba, tsayawa yyi yana kallon bargon, ko kadan Afeefah bata san an shigo dakin ba, ya karasa kan gadon ya yaye bargon a hnkli yana kallonta, a kidime ta mike xaune tana kallonsa, lkci daya ta shiga kkrin boye wayar hannunta, fixgewa yyi yana kallon wayar da mmki, kuka ta saki ta mike da gudu ta fice daga dakin ta shige dakin Mami, Mami da fitowarta daga bayi knn ta bi ta da kallon mamaki, kuka ta fashe mata da tace "wayyo Mami ki ce ma yayanmu dady ne fa ya siya min wayar" korarta Mami tayi daga dakinta a fusace, Afeefah tayi dakin Adnaan shi ma ta fashe masa da kuka tace "kaga ya Adnaan, dady ne ya siya min wayar fa" Adnaan yana kallonta da mmki yace "wani waya?" Cikin kuka tace "yana hannun yayanmu je ka gani kar yace ba shi ya siya min ba ya min duka" dariya Adnaan yyi ya mike ya fita ya samu Ya Aliyu dakin sa a kwance, kallon iPhone 7 din kan gadon Adnaan yyi ya karasa ya dauka yana dariya yace "Wae kaji dady ya siya mata tace" wani mugun kallo Aliyu yyi masa can yace "naji, ae ni bn ce mata komae ba kai mata wayarta" Adnaan ya fita da wayar ya kai Mata dakinsa, mikewa ya Aliyu yyi ya fice daga dakin ya nufi dakinsu jiddah, jakar kayan Afeefah ya nufa ya xuge ya shiga fiddo kayan ciki can kasan jakar ya ga kwalin wayar ya bude bae ga receipt ciki ba, kan farin envelope idonsa ya sauka ya dauki envelope din ya bude ya ga hotuna ne ciki, yana cikin fiddo hotunan aka bude kofar dakin ya daga kai suka yi ido hutu da ita ta shigo, mutuwar tsaye tayi bakin kofar cikin rawan murya tace "yayanmu" bae kuma kallonta ba ya ciro hotunan gaba daya yana kallo, mikewa Aliyu yyi da sauri ya dafa bango tsabar wani mugun jirin da ke neman kada sa daga durkushen da yake kansa na juya masa.

Eeshatullah Goni๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
?
?[5/23, 08:34] Umar Dalha: ๐ŸŒธ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป 'Ya mace kyautar Allah๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป๐ŸŒธ

A true life love story

By Ashmaad

44.....
Afeefah ta fasa ihu a tsorace ta durkushe wajen tana kallonsa lkci daya ta fashe da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kiran Mami, da kyar Aliyu ya iya jan kafarsa ganin tsayuwar ya gagaresa ya koma can gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi ssae, Adnaan ne ya shigo dakin da sauri ya kalleta snn ya kalli Aliyun, su Jiddah ma suka shigo suka yi cirko cirko a bakin kofa su kalleta su kalli Yayanmu, Mami ce ta shigo dakin ita ma tace "me ya faru? Wa ke min ihu a gida?" rasa me bata amsa aka yi, Afeefah kam sae kuka take daga durkushen da take, kallon Aliyu dake xaune gefen gado har lkcn yana rike da kai Mami tayi ta ja tsaki ta juya ta fice daga dakin, Adnaan ya karaso cikin dakin ya karasa kusa da Aliyu yace "me ya faru bro? Me tayi maka" ganin Aliyu bae da niyar tanka sa yasa ya juya ya fice daga dakin shima, su Jiddah suka bi bayansa. Mikewa Afeefah tayi ta fice ita ma da sauri jikinta na rawa, dakin Adnaan ta shiga ta xube gabansa cikin kuka tace "ya Adnaan ka taimake ni yayanmu xae kashe ni yau" Yace "me kika yi ne wae?" Muryarta na rawa tace "Ni ma bn sani ba" hka tayi ta xama dakin Adnaan taki fita sae kuka take. Ganin gyangyadi take daga xaunen da take yasa Adnaan yace "ki kwanta Zainab" bude ido tayi, tayi shiru tana kallon bakin kofa can ta mike kmr warce kwai ya fashe ma ta fice daga dakin ta nufi dakinsu, su Jiddah na shirin kwanciya Afeefah ta shigo dakin ta nufi kan gado a sanyaye, duk suka bi ta da kallo, sae da ta kwanta snn Jidda ta karasa kusa da ita ta xauna tace "Afeefah me kika yi ma yayanmu" hawaye ne suka gangaro mata bata ce komae ba, daga karshe ta kauda kanta, mikewa jiddah tayi ta bar wajen. Har asuba Afeefah bata wani rintsa ba, ta rasa me ke mata ddi a duniyar, tasan a da ko da wasa bata tsallake duk umarnin da yayanmu ya bata amma tun da ta fara higher institution take disobeyin dinsa ta rasa dalili, sae da su Jiddah suka dawo daga gaida Abba snn ta mike jiki ba kwari ta fita don xuwa gaishesa, Abba na xaune falonsa ya Aliyu

Please Login or Register in order to submit comment