Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikata irin abinda suka mata agarin to sune dalaifi, suka ware, atake ciwo yaƙare, daganan suka koma sojojijon dole acikin rugarsu masu gadin ƴammata, Hakan yasa kowacce budurwa tasamu inci acikin rugar tasu.


MASARAUTAR MAHAR

yau dai wannan matar samu damar aiwatarda mummunan ƙudurinta akan sarki Habibullah domin tabawa wata baiwa maganin datakeson ayiwa sarkin anfani dashi tasaka acikin abincinda jekadiya zata kai masa, wannan hadimar kuwa bakowa bace face amin tacciyar hadimar me babban ɗaki wanda ita kaɗai jekadiya ta yadda da Ita kasan cewarta dattijuwa kamarsu, hadima hajjo kenan munafukar tsohowa me fuska biyu... lokacinda tazowa da matarda tasaka aikin da labarin ta aiwatarda saƙonta kuma har memartaba yaci baƙaramin Farin ciki tayiba, atake tafaɗa turakarta tareda ɗauko wani walki ta ɗaura kana tarufe idonta tana karanto wasu laziman tsafi kawai taɓace daga wurin segata ta bayyana acikin wannan ƙugurumin jejin memasifar tsoratarwa...tana sauka wurin ya ɗauke da wata mahau kaciyar dariya cikin ɗaga murya me dariyar ke faɗar "aikinki na kyau Fulanin sarki habibullah yanzu Seki zuba ido kiga yadda komai ze kasance. "Murmushi tayi cikinjin daɗi tace "godiya nakeyi yakai wannan dodo, sedai inada tambaya wadda nakeyima kullun koyanzu itace zanyi, akan babyn da gimbiya halima tahaifa shekarun baya, wai haryanzu baka gano muna wanda yaɗauke shiba dakuma inda yake? Tafaɗa cikin damuwa...ɗan shiru wurin yaɗauka nawani lokaci kafin taji saukar mummunar muryar dodo yana cewa "tabbas bamu gano komaiba gameda wannan baby domin bamuma samu tahanyar dazamu gano wani abinba atare dashi abu ɗaya nasani shine duk inda yake yana raye kuma acikin aminci da kariya ta musamman tabbas kinrigada kinyi sake Fulani dama tarigida tawuceki, yanzu sedai kishiryama yaƙarshi aduk lokacinda ze bayyana agareki domin tabbas dashirin yaƙarki zeshigo masarautar MAHAR, hhhhhh, hhhhhh,,hhhhh Hakan yariƙa ɓaɓɓaka wannan dariyar merazana duk wani meji alokacinda yakeyinta kafin kuma wurim yayi tsit kamar ba'abinda yafaru, Hakan itama Fulani taɓace kamar yadda tazo takoma turakarta sedai duk kwakwata nakasa gane wacce Fulani ce acikin matan sarki domin taƙi bada damar aga fuskarta.

US

Zaune yake acikin tangamemen office ɗinshi yasaka computer agaba yana aikinshi cikin mutsuwa da kamala, kyakkyawan dattijo mecikar haiba dakuma kamala fari tass kamar ka kwanta shi jini yafito, ahankali yake aikin yanayi yana kurɓar tea ɗin dake gefenshi, wayarshice tayi ƙara wanda yasakashi saurin dubawa domin wayar family shi daban take sabida be haɗa komai da ahalinshiba dudda baya taredasu amma yanajin sonsu harcikin ɓargon jikinshi, dubawa yayi yaga me kiran nashi afili ya furta "Ameer sekuma yayi picking yakara wayar akunne tareda sallama, "Abba inawuni. "Murmushi yayi wanda yaƙara Mishi kyau kana yace "lpy qalau Ameer sedai fa nan kam hantsine ya kuke y gidan ya memartaba? "Duka lpy qalau alhamdulillah Abba. "Masha allah, miyake faruwane Naji muryarka wani iri? Yajefawa Ameer tambayar..ajiyar zuciya Ameer yasauke kana yace "Wlh Abba akwai matsala ne, Anan yashiga bashi labarin yadda sukayi da abbey dakuma yanayinda princes keciki sedai yaƙara da Cewar amma yana Ganin ba wannan maganar ce tafi ɗagawa princes ɗin hankaliba domin tun kafin abbey yayi zancen suka ganshi wani iri....cikin tashin hankali Alhaji Abdallah yamiƙe tsaye yana faɗar "subhanallah inayake shi Sameer ɗin? "Yana bedroom Abba. "Okay bashi wayar yafaɗa aƙagare. Aiko Ameer yamiƙe zuwa bedroom ɗinshi koda yashiga yana zaune ya jingina kanshi dajikin bed sedai ba bacci yakeyiba, bece mishi komaiba yaƙara Mishi wayar akunne domin yasan koyayi magana ba tanka Mishi zeyiba... ɗagowa yayi yana hararar ameer ɗin kafin yayi wani motsin yaji saukar muryar abbanshi yana faɗar "Sameer Mike damunka? Yafaɗa hankalinshi duk atashe, jin muryar abbanshi ne yasa yariƙe wayar tareda lumshe kyawawan idanuwanshi, yana sauke ajiyar zuciya...Ganin Hakan yasa Ameer ficewa daga bedroom ɗin...shikuwa shiru yayi bece komaiba kusan minti 5 seda yaƙara jin muryar abban nashi yana faɗar"kanajina kuwa sameer waimike faruwane a,nan? Yaƙara jefo wata tambayar. Daƙyar ya haɗiye Yawun dasuka tokare maƙoshinsa kana yabuɗe baki daƙyar yace "Abba, sekuma yayi shiru. "Na'am yarona miyasameka? Naji muryarka Hakan? Mi akayima? Wani abunne yafaru? Duk ajere yake jefomishi tambayoyin. Yarima Sameer kam yakasa bashi amsa ko ɗaya daƙyar ya iya buɗe baki yace "Abba aljana gamo nayi Abba Wlh aljanace, yafaɗa yanajan wani irin numfashi wanda yakeji kamar zuciyarshi zata fasa ƙirjinshi ne tafito....ido Alhaji Abdallah yawaro cikin mugun tashin hankalin daya ƙara yimai dirar mikiya yace "aljana dai Sameer a'ina? Kai baradai ganinan zuwa zanshigo Nigeria nanda ƙarfe 6 nasafiyarku, daga Hakan ya yanke wayar tareda kwashe takashenshi ko kashe computer ɗin beyiba yabar office ɗin hankali amatuƙar tashe....!


END BOOK 1

kuma Anan free page yaƙare semun haɗu a book 2 wanda yakasance paid ne.

Humm yanzune za'afara asalin wasan acikin wannan book ɗin metaken👉 *AL'AJABIN MASAURATA*

Shin wacece HUSNAH? Miye alaƙarta da pappi?
Wacece wannan Fulanin dake neman mutane da sharri acikin masarautar MAHAR?
Shin ina labarin jinjirin da aka sace?
Miyasa aka kashe gimbiya halima?
Mi zuwan abban princes ze haifar?
Miyasa PAPPI kezuwama HUSNAH da kamannin yarima sameer?
Minene yatadawa HUSNAH hankali acikin masarautar MAHAR?
Shin minene asalin faruwa wannan abubuwan al'ajabi dake cikin masauratar MAHAR? Humm duk kobiyoni semun haɗu a page nagaba in sha Allah.



Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal 👌 zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp.









Autar alheri ✍️
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment