Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

full, alhamdulillah Kanon Dabo ta yi zarrah a jihohin Nigeria gaba daya, wajen albarkar Al’ umma”.
Rayhanah ce ta bude masa kofar motar ya shiga ta rufe,
“Sleep well Daddy.....”
Ta fada tana daga masa hannu har ya bar get dinsu yana daga mata shima. Maigadi ya kulle, ita kuma ta koma cikin gida.
Nan ta ga wayar Daddyn a nan inda ya tashi santin faten waken Inna Juma ya mantar da shi. Ta ce,
“Lah! Inna kinga Daddy ya manta wayarsa”.
Inna ta ce,
“Sai ki adana gobe ya karba”.
Ta ce, “Ba lallai ya zo gobe ba, karshen wata ne zai je Takai. Bari dai na ajiye din”.
Ta yi dakinta da ita ta sanya a kan lokar gadonta, ta fada bayan gida don ta yi alwalar sallar magariba.
Kafin lokacin magariba ya cika, Rayhanah na zaune kan sallaya da carbinta a hannu cikin kyakkyawar shiga da ta ware musamman don yin ibada, doguwar Abaya ce kirar Kuwait da farin Hijab wanda ya tsaya iya gwiwoyinta, tana yiwa Ubangiji tazbihi.
Har aka kira magariba ta tada sallah, a lokacin da wayar Daddy dake kan lokar gadonta ta soma dan kida ba mai cika kunnuwa da gigita mutum ba.
Don haka a nutse ta ci gaba da sallarta har ta idar, mai kiran bai hakura ya daina kiran ba sai kira yake akai-akai-akai. Yana yi yana karawa.
Ta mike ta kwanta a gefen gadonta ta dauki wayar Daddy don ta kashe, a ranta tana kunkuni cikin fadin “these so-called AKTH emergency unit, will not leave my Dad to live in peace ........haba! Ko inji ai yana son (service) kafin ya ci gaba da aiki balle mutum dan-Adam.
Amma shi Daddyn baya gajiya, ko ya kwana da an kira shi komin dare zai tafi. Ni gara ma da ya bar wayar, yau daya dai ya huta”.
Amma ga mamakinta sai ta kasa kashewa, ta zubawa lambar ido, domin ba ta yi kama da normal lambobin da ta saba gani ba. Lambobi ne rankacau (International).
Haka nan ta samu kanta da faduwar gaba, mutuwar jiki da sanyin gwiwa, wanda suka dage da cewa lallai suna son amsa wannan wayar, ta gayawa mai su Daddy baya tare da wayar, don ganin yawan kiran mai nuna mai ita a matse yake da son magana da Daddyn daga kololuwar duniya ba kiran asibiti bane.
A dai-dai lokacin da kiran ya kara shigowa, sai ta kishingida ta amsa.

“Dacta baya tare da wayar fa! Be patient mana!!”.

Wata irin sassanyar murya ce mara amo da karsashi, sannan kuma mai taushi, yarinyar ta yi amfani da ita wajen yi masa wannan kalamin, wadda ta tsirga har cikin kwakwalwarsa, ta haifar masa da macewar jiki, at the same time, ta tada tsigogin jikinsa.
Da ta ji anyi shiru kawai sai ta katse wayar ta ajiye. Ta dau remote ta kunna A.C ta soma addu’ar kwanciya barci.
Ibraheem ya yi shiru yana kallon wayar hannunsa, tsaye yake a balcony din gidansa (terrace) a saman bene yana kallon yadda ruwa ke tsiri, yana zuba cikin furanninsa korra sharr.
Akwai wani abu extraordinary cikin muryar yarinyar da bai taba ji a muryar wata diya mace ba, mai sanya sanyin jiki da kasala.
Me ya hada Daddy da budurwa har wayarsa ta je hannunta? Yana da kyakkyawan zato a kan mahaifinsa, amma wannan ba Abida ba ce ba Jawahir ba, ba kuma Azizah ba.
Idan ma sune ba yadda za ai wayar Daddy ta zo hannunsu. Don haka ya ji yana so ya tambayeta ita wace ce? Me ya hadata da wayar mahaifinsa?
Don haka ya sake kira, ta kuwa sake amsawa don yau cikin nishadi take, don Daddy ya ce za ta tafi Singapore jibi in Allah ya kaimu ta dora karatunta kafin Ibraheem ya nemi gida.....
“Wace ce ke?”
Abinda ya tambaya kenan a gintse, da makalalliyar hausarsa mai fita a doron harshe, cikin tsananin takaitawa.
Ita ma a takaicen ta samu kanta da amsawa.
“Sunana Juma”.
“Juma? What kind of name is this?”
Ta amsa da cewa, “Sunan da iyayena suka rada min kenan”.
A muryarta kamar ta ji zafin tambayar da ya yi mata, shi kuma a rayuwarsa bai iya muzanta dan adam ba. Sai ya yi saurin cewa,
“Ki gafarce ni plz, ina so in san yadda akai wayar Dr. Mansur ta zo hannunki ne?”
“Am the Nurse on duty, and he left it at the ward”.
Ibraheem ya gamsu da bayaninta har ga Allah, ita kuma kawai cikin nishadi take kan wannan albishir mai dadi da Daddy yayi mata na tafiya Singapore (Informatics-Singapore) ta rasa da wanda za ta yi sharing nishadin nata, sai ya fada a kan Ibraheem.
Ya ce, “Alright, zan kira zuwa gobe. Thank you”
“Don’t mind”. In ji ta.

Karfe biyar na Asubahi tana tsaka da barci sai ga kira again, ta yi dan tsaki ta mika hannu ta dauko wayar tana ganin laifin kanta da ba ta kashe wayar ba tun jiya, ga shi an katse mata barci mai dadi da take yi bilhakki.
Sai dai ita kanta ta san ba laifinta bane, laifin yatsunta ne, sun kasa kashe wayar kada mai Turanci mai dadi ya bugo bata dauka ta sake gillara masa karya ba.
Ai tana ganin lambar ce sai ta nemi barcin da ya cika mata ido ta rasa. Ta amsa da sallama cikin muryar barci, wannan karon tasirin da muryar ta yi a jikin Ibrahim Mansur, Allah ya yi yawa da shi, ta yadda biro na bazai iya rubutawa ba.
Har ta kai ga Ibraheem ya fada cikin wani yanayi na daban. Muryarshi can kasan makoshinsa ya ce,
“Ki yi hakuri na tashe ki daga barci”.
“Don’t mind”. Ta sake cewa.
“Jumah!”
Ya kira sunanta da murya (which is deeply suffering).... Sai ta ji jikinta ya kama rawa, ta yi magana cikin sarkewar harshe.
“Doctor is not yet at office!”.
Ta kashe wayar hannunta yana rawa, gangar jikinta ma gabadayana yi. Irin wadannan mazan sune masu yin zinar murya, me yasa zai rika yi mata magana da irin wannan sauti mai kassara gabban jiki kamar wata matarsa ko budurwarsa? Ba za ta kuma amsa wayarsa ba. Batasan cewa murya ce da Ubangiji Subhana ya halicce shi da ita ba.
Sai kuma ta baiwa kanta dariya, sanda wani bari na zuciyarta ya tambayeta,
“Wa ya gaya miki haka miji ko saurayi ke yin magana da budurwarsa ko matarsa Rayhah?Tunda ke baki da saurayin ko mijin? Babu kuma wanda ya taba yi miki magana hakan including Yaya Khalipha?”
Oho!”
Ta fada tana kyabe baki tareda shigewa cikin lallausan bargonta tana cewa,
“A to, haka dai na ga Daddy na yiwa Mami magana, ita ma in ya yi tafiya tana waya da shi ai haka take yi mishi magana”.
Barci ne mai karfi ya dauke ta. Hasken rana da ya hudo ta farin labulen da ya zagaye dakin barcin nata shi ya ratso ya dallare mata fuska. Ba shiri ta tashi tana mittsike ido ta fada toilet ta yi wanka ta yi brush da yake ta yi sallar Asubahi ta fito falo.
A kicin ta jiyo motsin Inna, don haka ta tasarma kicindin. Can ta iske Inna Juma tana kwabin Alkubus, ta ce,
“Allah ya ja da ran Inna ta, yau Alkubus zamu ci haka?”
Tana buga fulawar ba tare da ta juyo ba ta ce,
“Ni ba ke nake yiwa ba, Baba Likita nake yiwa don jiya ya gaya min yana son shi”.
“Ba kya jin magana Jumah.......! (ta fada da sauti irin na Ibraheem) wanda ita kanta ba ta san sanda muryarta ta karye ta canza ta koma haka ba. Na gaya miki yau ba zai zo ba zai je Takai Asabar din karshen wata ce”.
Inna ta yi dan jim, sannan ta juyo ta dubeta. Abubuwa biyu ne suka sa Innar yin shirun da juyowar.
Na farko kiran sunanta da Rayhanah ta yi da wani irin amo (tune) da ba nata ba, na biyu kuma ba ta ce mata Inna ba kamar yadda ta saba.
Gani ta yi Rayhanah na rawar dari, ta kankame hannunta a kirjinta, murya na rawa idanunta na lumshewa, suna budewa ta ce,
“Inna sanyi nake ji”.
Sai ta tsame hannunta daga cikin fulawar ta rufe ta don ta tashi, ta wanke hannunta ta kama Raihanan, ta soma tofa mata duk addu’ar da ta zo bakinta, domin a tsammanin Inna aljanu ne suka shiga jikin jikar tata yanzu-yanzun nan.
Tabbas muryar da ta yi mata magana da ita, ba tata ba ce.
Daki ta maida ita ta ce ta kwanta, bari ta je asibiti ta kira Dacta (da yake ta san ofishinsa ya taba kaisu).
Rahane ta ce, “Wai Jumah........! (ta kara yin magana da irin sautin dazu) sau nawa zan gaya miki Daddy baya nan ne?”
Inna ta ci gaba da tofa mata addu’a. Haushi ya kama Rahane, don ta ga Inna ta mai da ita mai aljanu kawai don ta ce da ita tana jin sanyi.
“Kinga Jumah..... (ta kara fada da sautin Ibrahim da tune dinsa na yin magana) jeki ki yi Alkubus dinki, ki rabu dani don Allah bana son wannan tofe-tofen da kike mini, fever ne kawai ke son shiga na, rufa min bargo, jeki don Allah”.
Inna ta ce,
“Ba zan tafi din ba, aljani ke son auren ki. Bari Baba Likita ya zo a daddale magana, idan dan American nan baya sonki, to ya sahale miki ki yi rayuwar ‘yanci ki samu wani mai sonki ki aura.
Wannan ba aure bane, watanni goma fa! Ana shirin shiga na sha daya. Babu miji ba dalilin sa”.
Inna babatu take ba ta san cewa Rayhanah ba jinta take ba. Zazzabi mai zafi ya rufeta ruf. Ina ma ba ta kashe wayar nan dazun ba, da watakila ta ji sunan mai wannan poisonous murya wadda ta dura mata virus ta cikin kunnuwanta ta haifar mata da zazzabi mai zafi.
Ita dai fatanta Inna ta fita ta ji da abinda ya sameta, amma Innar ta ki. Sai da ta hada da magiya sannan Inna ta fita tana ta mita, ita wannan aure ya isheta, ba ta san irinsa ba. Bata taba gani ba!
Bayan fitar Inna kira ya sake shigowa, Rayhanah ta daga, duk da ta ce ba za ta kara dagawa ba, zuciyar da gangar jikin sun ki amincewa, cewa suke;

“........ ba zamu samu sauki ba in bamu ji shi ba, ba zamu barki ki zauna lafiya ba sai mun ji ko shine IBRAHEEM!!!
[12/25/2019, 15:42] Takori: Ya tabbata ta amsa kiran, amma ba ta yi magana ba.
Ya dade shima bai ce komin ba, sai da ya saisaita kansa ta hanyar yin ajiyar zuciya akai-akai, sannan a sanyaye ya ce,
“Am now not to ask for Doctor, (yanzun ba Dr. Zan tambaya ba) don haka don Allah kar ki kashe min waya.
I want to know more about you..., Concerning you. ...”
Ta ce, “You can ask me anything (za ka iya yi min kowacce tambaya) insha Allahu ba zan kashe ba”.
Ta fada da muryar da ta kara kassara Ibraheem.
Ya ce, “Meye alakarki da Doctor Mansur?”
“Likita da mai taimaka masa”.
Ta amsa kai tsaye.
“Wannan matsayin da kike ikirari bai yi isar da zai sa ya baki wayarsa ba. Don Allah!Ke wace ce dinsa???”
Tunda ya ce ALLAH! Sai ta ji ba za ta iya yi mishi karya ba. Kuma jikinta yayi wani irin sanyi, da wata muryar again da Ibrahim ba zai taba mantawa ba, ta ce,
“Kafin in amsa maka, nima ina so in tambayeka don ALLAH! Ko kai ne IBRAHIM.....???”

Shiruuuu! Ya bakunci kunnenta. Da ta duba sai ta ga cajin wayar ne ya mutu. Don haushi sai raunanniyar zuciyarta ta ce da ita,

“Ki rushe da kuka........”

Shi din kuwa ta shiga yi mai yawa, sai da ta yi ya isheta. Wannan mutumin da take waya da shi, da matsayin da zuciya da gangar jikinta suka baiwa muryarsa, suka kuma karbeta, da tasirin muryar cikin gangar jikinta da kwakwalwarta, da wata tsoka guda daya dake tsakiyar kirjinta (zuciya) ya fi gaban na wani mutum kawai, wanda yin waya da shi kawai zai haifar da wadannan emotions. He must be the HUSBAND.
Ba ta tantama ko shakkar cewa shine mijinta IBRAHEEM MANSUR TAKAI....
Zazzabin na karuwa, sanyin da take ji na daduwa. Har Azahar ba ta fito ba kuma ta ki bude kofarta kada Inna Juma ta dameta sai ta ci alkubus.
Ita yau ko naman Dawisu (Peacock) aka gasa aka kyafe mata aka ce ta ci da gida da mota (in return), baza ta iya ci ba.
Muryar Ibraheem kawai take son sake ji, da son ganinsa a zahiri. Wata murya data haifar da wasu bakin abubuwa agareta da bata taba ji ba a rayuwarta, ba kuma zata iya fassarasu ko fasaltasu ba da kowacce irin siga don wani ya gane ko ya fahimta.
Zazzabin kuma sai ta ji yana sauka a hankali, a saboda lallashin da zuciyarta ke mata da cewa,
“Watakila shine angon Rayhanah! Amma anya Rayhanah baki kamfato da yawa ba?
Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki?
Idan kuma ba shi bane hatta wannan tunanin da kike da bari da kike muryarshi na tasiri a gangar jikinki da zuciyarki, kina aikata haramun ne fa, a matsayinki na matar aure!!!
“Astagfirullah!”
Rayhah ta fada a hankali. Ta debo kuzari da karfi ta zubawa jikinta, ta mike cikin zafin nama, ta bude bed-side fridge dinta ta dauko gorar ruwan FARO mara sanyi ta soma kwankwanda. Sai da ta sha rabin doguwar robar sannan ta ajiye.
Ba ta mantawa wannan horon Mami ne, ba ta bari su karya kumallo sai sun sha fresh water sun koshi. Sannan ta adanawa Daddy wayarsa, ta bude kofa ta nufi falo wajen Inna.
Ba ta falon, don haka ta wuce dakin da ya zan mallakin Innar a kasan benenta.
Sanda ta shiga Inna na sallar Azahar, sai ta shiga bayin Innar ita ma ta yi alwalar ta fito ta tada sallah.
Ko da Inna ta idar ba ta kulata ba laziminta ta ci gaba da yi kasancewarta mai son ibada, ba ta zama haka kawai, inda abokin hira ayi hira ayi dariya, in babu a yiwa Ubangiji tazbihi ayiwa Annabi salati.
Ta gane lamarin na Inna yau har da fushi a cikinsa. Ko don ta rufe kofa ne ko don ta ki cin Alkubus ita ba ta sani ba. Sai ta ji ranta ba dadi, ta gurgusa ta kwantar da kai a cinyoyinta, cikin murya mai ban tausayi ta ce,
“Inna idan laifi na yi miki don Allah ki yi hakuri”.
Girgiza kai Inna ta yi alamar a’a. Sai da ta kai laziminta ta ja addu’a ta shafa ta shafawa Raihanan, sannan ta ce,
“Ni baki yi min laifin komai ba, auren nan ne dai nake so a kawo karshensa in ba mai nasara bane”.
Rayhanah ba ta gane abinda Inna ke nufi ba, cikin mamaki ta ce,
“Inna kamar ya ya idan ba mai nasara bane?”
Inna ta ce, “Eh, idan ba mai nasara bane, abin nufi idan yaron baya so, ba zan zuba ido ki kare kuruciyarki a haka ba har jinnu su soma kokarin auren ki.
Daga yau daki daya zamu dinga kwana. Bari Baba Likita ya zo, wannan zaman jiran tsammanin warabbuka ya ishe ni”.

Fushi ne sosai ya bayyana cikin idanun Rayhanah, ba ta san sanda ta dagawa Inna sauti ba.
“Ko zaman shekaru ashirin ne Daddy ya ce in yi zaman auren dansa, kuma dan baya sona, ba jinnu ba, ko ifritai ne za su aure ni ba zan taba ce da shi ya kawo karshen auren ba. Tunda daurawa ce tashi, amma igiyar aure ba a hannunsa take ba balle ya tsinka ta.
Sama da wannan ni abin ikonsa ce sai yadda ya ga dama dani, don na san ba zai taba yin abu don ya cutar dani ba. Shi ya mai dani -MUTUM....... Wani kwayar halitta guda daya da ya tsaya ya maidani MUTUM!!! (Cewar Rahma Abdulmajid ). Ba don shi ba ban san ya ya rayuwata ta baya za ta kasance ba, a lokacin da na budi ido babu kowa nawa a duniya.
Don haka Inna don Allah kada ki yi masa wannan maganar hankalinsa zai tashi, ni na ce na-ji-na-gani INA SON IBRAHEEM.......!!!
Ina darajja igiyoyin aurensa da suke kaina, ko da baya sona. Koda har abada bazan ganshi ba, balle mu zauna tare.
Baku sani bane, baku san rawar da Daddy ya taka a rayuwata ba. Kun budi ido ne kawai kun ganmu tare. He is someone I cherish and respect most! Ko me zan yi masa ba zan iya biyansa hidimar da ya yi dani da rayuwata ba. Inna gaya miki ne ban taba yi ba, amma har nakasa nayi; babu ji dungurungum!”
Ta yi shiru tana share hawaye cikin TUNA BAYA. .....sannan ta ci gaba da cewa,
“Shi ya nema min magani na warke, da lafiyarsa, da iliminsa da lokacinsa da aljihunsa. Shi ya bani ilimi irin wanda ya baiwa ‘ya’yan da ya haifa dama wanda bai basu ba.
Duk wannan bai isa ba, ya dauke ni ya aurawa dan da ya fi so cikin ‘ya’yansa. A lokacin da aka so rayuwata ta tozarta Don na fito daga karamin asali, na taba yin cuta.
Sai kawai don yaron ban yi masa ba ya ki zuwa sai ki ce Daddy ya raba ni da auren dansa?
A’a, Inna kada ki fara, na zabi in mutu, in kare kuruciyata da rayuwata gaba daya da igiyar auren Ibraheem, ina mai darajjata da kare martabarta. Don haka don Allah Inna kada ki kara tada wannan magana za ta tada hankalin Daddy”.
“Sai na yi!”
Abin da Inna ta ce kenan.
“Fito fili kawai ki yi mana gori, bamu tallafi rayuwarki ba kina karama, a nan kam bani da bakin musa miki. Amma ina da shi a wajen Allah, wannan kyautayi da alherin da ya yi ai sakayyarsa na gurin Allah.
Ba zai zama hujjar cewa sai kin biyashi da tauye kuruciya ba, babu inda musulunci ya yarda da wannan, sai in dama ya yi ne ba don Allah ba sai don ya aurawa dansa wanda baya so.
Mene ne dole? Babu dole!”
Amsar Rayhanah cikin rurin kuka ta bata mamaki.
“Inna in dai kin gaji da tayani zaman jiran Ibrahim ne..... kina iya komawa Takai ni in zauna ni kadai. Babu abinda zai cinyeni cikin gidannan da yardar Ubangiji....,In har ba za ki taimaka min in yiwa Daddyna biyayya ba.......!’’
Sai Inna ta mike a hasale tana fadin
“Haka kika ce ko? To shi kenan”.
Ta soma ciro kayanta daga cikin kwaba tana dannawa a (Ghana Must Go) din da suka zo a ciki.
Kan ta gama kukan tuni Inna ta gama cika jakarta ta yi lullubi ta kinkima ta daura a kanta ta yi waje.
Kamar an yiwa Rayha allura haka ta bita da gudu, ba ta cimmata ba sai a kofar fita daga falon, ta kama jakar ta kankame tana kuka kamar na fitar rai. Inna na ja Rahane na ja, a haka Allah ya kawo Dr. Mansur, saboda bacin ran junansu ko karar shigowar motarshi basu ji ba.
“Subhanallahi-Subhanallahi!”
Abin da yake fada kawai kenan. Inna Juma ba ta ko kalli kwayar idanunsa ba don ita kanta ya yi mata kwarjini. Sai ta kasa cewa komai ta sunkuyar da kanta kasa, ya yin da Rayha ta dauki jakar da kyar sabida nauyin ta, ta maida ita ciki.
Tana ji yana bai wa Inna hakuri da lallami da lallashi cikin girmamawa, sai haushin Inna Juma ya kara kamata, da kyar ya lallabata suka koma falo.
Ya zauna a kan kujera yana fuskantar tsohuwa Juma, wadda ke zaune kasa kan kilishi ta rasa daga inda za ta dauko masa zaren bayanin da ya bukata, wanda ya sata yin fushi haka, har za ta iya tafiya ba tare da ta neme shi ba,.
Ko me Rayhanah ta yi mata ai yarinya ce, shi ya kamata ta jira ya zo in na fada ne ya yiwa Raihan, in na tsawatarwa ne ya tsawatar mata. Yara yanzu ai ka haifesu ne kawai amma ba ka biye musu sai ku taru ku zama yaran dukkanninku.
Inna ta yi shiru dai-dai lokacin da Rayha ta iso da tray shake da jus da ‘ya’yan inibi, peach da pear ta ja karamin tebur din dake gefen kujerar da Daddy ke zaune ta dora ta matsar dasu gabansa.
Hankalinsa kwance ya soma cin kayan marmarin yana sa mata albarka kamar ba shi ya sayo da kudinsa ba. Ta koma daki ta dauko masa wayarsa ita ma ta dora a kan tebir din.
Ya shiga hamdala yana cewa, “Ashe a nan na barta, kai! Batan waya babu dadi, ba wayar ce abin ji ba, al’amuran da suke ciki. Ke Rayhanatu jeki daki zan yi magana da Inna”.
Ta ce, “To Daddy”. Ta mike ta nufi bed room dinta.
Ya sha tambulan din ruwa mai sanyi, ya

Please Login or Register in order to submit comment