Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yaba da hankalin Usman ya

kuma san mahaifin Usman shiyasa yayi saurin amincewa da su turo ayi maganar aure suna sanar da Usman Yaji

dadin jin haka dan haka ya turo iya yan Sa aka saka ranar aure wata1 Alhaji nasir yace baya son lokaci me tsawo

Hajiya na zaune a falo tareda su Abu Binta da Amal suna hira Aqeel da Arif suka zo suka zauna

Aqeel yace mommy me kuka fara yine akan maganar auren Amal dawani abinda zamu taya Ku

Hajiya dariya tayi tace munyi komai ranar kawai muke jira Da kuma fatan Allah ya kaimu da rai da lpy

Atare suka ce Ameen

Arif yace dama mun yanke shawarar kaisu su zabo abinda sukeso ne mommy shine mukazo muji ko kina da sako

A'a ni banida sako idan matan kune gasu nan Ku dauke su Ku tafi yanda kuke Sosa keyar nan nasan abinda ya rage ku tam baya kenan

Arif yace A'a mommy da bamuyi niyar tafiya da suba tinda kince suje shi kenan Ku taso ba komai

Hajiya tayi dariya "to shi kenan kuje Ku kadai su kuma Ku bar su Anan tinda badasu kukayi niyar tafiya ba

Aqeel ya za bura " mommy kinriga kin Sa musu rai ki barsu muje kawai idan kika hanasu baza suji dadi bafa

Amal Abu da Binta dariya sukeyi jin ga abinda suke so sai suce hajiya ce tace haka

Arif yace Ku taso mu tafi Abu da Binta kamar jira suke suka mike Aqeel da Arif na ganin su suka mance da hajiya da Amal

suka koma wa matan su suna tafe suna musu magana cikin rada suka yi hanyar fita ganin basu da niyar juyowa suyi wa Amal magana

Hajiya tace Amal din ta fita kenan

Aqeel a kun yace "kinga yarin yar nan ko mommy kina kallo ita na fara yiwa magana da magana nata da wan nan zaman da tayi yaci ace ta kai waje amma dube ta ki gani

Arif yace gaya mata wan nan san jikin naki ba inda ze kaiki gwanda ma ki dena gidan wani zaki yanzu idan kinje gidan Usman abinda zakiyi kenan

Amal baki ta saki tana kallon ikon Allah yanda suke shirin Dora mata laifi tana ji tana gani

Amal tace yaya dan Allah kun manta dani abinda zakuce kenan hasa Lima bada ni kuka yi niyar fitaba shiyasa suna tashi kuka tafi

Aqeel ya dawo kusa da ita ya zauna "Amal taso mu tafi zaki iya tafiya kona Goya ki abinda kike so mu muki kenan kadai

ba karamar yarin ya bace da zamu dinga yi miki magana cikin rarrashi idan zaki ki taho idan baza kiba gaba ta kaimu

Arif yace baza taba tace taho mu tafi tana bata mana lokaci

Injiwa yanda ba kwaso naje kamar naje na gama kome za ayi ko a siya nima a siya min

Arif yace kinga Usman Anan ne da zakice haka ba abinda zamu siyar miki idan kin bimu yarin ya kinje a banza

Bakomai nayi gaba Ku biyoni a baya

Amal ta bisu badan sun so ba haka Aqeel da Arif sukaita hade mata rai ko a kanta ita da Kansu suka gaji suka koma

yanda suke Kaya suka siya musu bana wasa ba daga Abu Binta har Amal suka biya ta gidan cin abinci sukaci Aqeel

da Arif sun zagaya dasu guri da ban daban dasu hakan ya kara saka sha kuwa tsaka ninsu da matan su suka fahimci junan su sosai

hakan yasa Amal ta dena jin kewar rabuwa dasu sai dare suka koma gida har dakin su Aqeel da Arif suka rakasu

suma suka wuce nasu dakin bayan sunyi sallah suka Ciro littattafan su suna karan tawa saura kwana 5 su fara waec


Bayan sun karan ta suka kwanta bacci saida safe suka Ciro kayan da maza jensu suka siya musu suna dubawa

Kayan nan sunyi kyau ko Binta

Sosai ma wai yau lpy kuwa Amal bata shigo ba ko duk baccin ne

Zo muje suna zuwa suka samu kofar dakin a Bude suka shiga kan gadon suka dira Amal a tsorace ta Bude ido

Abu da Binta suka Sa dariya suna ce mata matsora ciya

Cikin muryar bacci tace ba batun tsoro Anan koku nayiwa haka saikun tsorata ina nan lokacinda kuka zo dokan Ku su

yaya sukayi a kafa kuka ce barayi barayi Amal Allah ya Baku hakiri gidan Ku muka zo

Au abin yar Tina baya ne to ai shi kenan kije gaban yayyunki ki fadi haka Abu na gama fada tasa dariya daga ita har Binta

Binta tace dafa munyi hauka wauta iya san ranmu kunyi hakuri damu

Amal tace ni kanhin tiraren nan nafi so dama kunga biki ya maso yakamata kufara tanadin tirare na musam man danni da mutane tirare da ze fasa taro yasa a to she hanci

Suka kara fashewa da dariya
Abu tace wai na gode Allah na da na dena Wannan haukan koyan zu ya zanyi idan kanhin na Jikina

Amal tana dariya "gaskiya zan g
aya miki inda kina shiga suna to she hanci yanzu kam daki zasu miki su kulle ki saida mu Tsaya daga waje mu gaisa harda ke Binta

Bakomai tinda za kuzo mu gyai Sa meye a ciki kanhi rahamane ga Almiski a bakin mu

Tana gama fada suka Sa dariya

Amal tace dan Allah Ku barni haka kar cikina yayi ciyo kuzo muje muci abincin nasan kuma Baku Ciba

Yasin kuwa kamar kinsani ke muke jira mutafi

Amal tace Yasin din nan baze fita daga bakin Ku bako

Binta tace bama fada sai in munason Tina baya

To shikenan mu tafi

Suna tafe suna hira har suka karasa dining Suka ci abinci saiga Asibi da kande

Asibi tace Amal zamu fita bazamu dade ba zamu dawo ko zaku temaka kukula da girkin dana Dora

Abu da Binta kai a kasa

Amal tace Eh zamuyi sai kun dawo

Mun gode

Amal tace bakomai

Suna tafiya

Binta tace ni gaba dayama kunyar su nake ji wlh

Abu tace ke koni manya damu saboda qazantar mu su suka fara mana Wanka daga nan muka fara sabawa

Amal dariya takeyi "to meye a ciki kila masu sun manta da zancen kune dai Baku mantaba

Binta ta girgiza kai "ya zakice sun manta bayan muna tare saidai matan nan akwai karfi wlh wani riko da suka mana haryau mun kasa mantawa

Aqeel ne yakatse musu hirar su da cewa mommy gaskiya abinda ake mana a gidan nan be da ceba

Hajiya mariya fito warta kenan taji abinda yace saida ta samu guri ta zauna "da aka yi me fa

Suma zama sukayi
Arif yace mommy ya dace da auren mu da komai amma haryanzu muna tare daku kamata yayi ace muma muna gidan mu ko

Hajiya cikin jin kunyar maganar "Arif ban gane inda ka dosa ba fa ka fahim tar dani

Aqeel yayi gyaran murya "mommy kamata yayi wan nan abincin da muke ci Anan a gidan mu ake dafawa gaskiya ana hukun tamu da yawa

Sarai hajiya ta gane abinda suke nufi saita shashantar da maganar da cewa Amal Abu Binta horan yunwa kuke musu shiyasa naga suna rama amma a sanina ana dafa abinci kowa na samu garin yaya haka tafaru

Mommy bafa haka muke nufi ba fa muna nufin yakamata matan mu su tare a gidan mu horon ya isa haka

Ko to gaku gasu

Mommy ba haka ba fa munaso ki amince su tare yau

Hajiya tace yaushe kuka zama marasa kunya ne Aqeel Arif yanzu dan bakuda kunya ni kuke fadawa haka to kunjawa kanku bazasu tareba duk abinku

Aqeel a mairaice "mommy karkice haka mana ba dadi fa shikenan zamu zama masu biyayya a gareki duk sanda kuka ce keda daddy su tare dai dai ne

Arif yace amma gaskiya zamu horu da yawa kafin su tare wai ace ka gama da wata matsalar sai wata ta kunno kai

Aqeel yace taho mu tafi suka bar gurin rai a hade Abu da Binta kunyar ce ta rufesu Suka kasa cewa komai ahankali suka tashi Suka tafi Hajiya na kallon su ita dariya ma suka bata

Akwana a tashi yau ya kama Abu da Binta zasu zana jara bawa waec da sassafe suka shirya a dining suka samu

hajiya suka gaidata ta amsa sukaci abinci Aqeel da Arif suka kaisu makaranta haka sukai tayi har suka gama zanawa wa gaba daya suna jiran saka mako

*An daura Auren* Amal da Usman ansha biki bana wasa ba Amal taga gata sosai Amal gidan da zata zauna na Abuja

tayi nisa da gida Abu Binta Aqeel da Arif saida suka kaita har Abuja sannan suka dawo Washe gari kafin Amal ta fafi

tayiwa Abu da Binta nasiha sosai wanda ya kashe musu jiki Aqeel da Arif baki har geya dan sunsan matan su zasu tare

koda suka dawo yan biki basu gama watse waba hajiya tayiwa Abu da Binta nasiha itama yamma nayi tasa wasu daga

cikin yan bikin su kaisu gidan maza jansu tin kafin su dawo daga Abuja hajiya mariya tasa aka gyara musu gida jen su da

zasu tare babban gidane me part 2 gidan yaci Ado da kayan Alatu kowan nansu aka kaishi ban garen sa sannan suka koma

gida yayiwa hajiya girma sosai ban garen Ango Aqeel da ango Arif kuma baki yaki rufuwa suna ganin akai musu matan

su suka baro gidan Hajiya rantsatsen gurin gasa kaza suka je kowan nen su ya siyowa matar sa suna dawo wa

gida kowa ya wuci gurin matar sa Aqeel da Arif sun kasa boye inrin farin cikin da suke yi sallama sukayi sannan suka shiga dakin

Abu ta amsa cikin miryar kuka Aqeel ya zauna a gefen Gado "zainab meye na kuka kuma keda zaki godewa Allah daya nuna mana Wannan ranar da ranmu da lafiyar mu

Ba kuka nake yiba kukan farin cikine gaskiya zamuyi kewar Amal sosai

Aqeel ya matso kusa da ita ya janyota jikin shi "idan kinyi kewar ta baga niba ni zan debe miki kewa

Abu ta dago jajayan ida nunta da suka cikuka suka gaji Aqeel ya kashe mata ido da sauri ta sun kuyar da Kai

Murmushi yayi " da alma cewa kunyata kike ji bakomai dai je Kiyi alwala kizo muyi sallah jiki a salube Abu ta shiga bandaki

Bangaren Binta da Arif ma haka

Binta ta fito bayan tayi Alwala Sukayi sallah raka'a2 sukayi Addu'oi

Arif ya dauko kazar daya siyo mata da lemu ka ya ajiye a gaban ta binta kura jiki ba kwari ta kalla ta dauke kai

Arif yace Amarya bakya laifi nakine na siyo miki Eh kici iya cinki

Nakoshi hasalima bazan iya cin komai ba

Saboda me

Saboda na koshi

Ba a gidana ba ki daure kici Kinji

Ganin bazata Ciba yasa shida kanshi yake bata abaki saida ya tabbatar ta koshi sannan
Yabar ta

Da suka gama sukayi shirin wanciya ina ganin lbr ya fara sauya wa dagudu na fito har tintibe sanda nayi

πŸ™„πŸ€” wai yau Kazamai ne a jikin Aqeel da Arif harda🀐

Amare da Angwaye ASIBA TA GARI

Garin Allah na waye Aqeel da Arif kamar su hadiye mata nasu suko sai shagwaba suke zuba musu

Hajiya tayi kokari wajan gyara yaran nata sunsha gyara da jiki shiya Aqeel da Arif Suka Hauka ce akan matan nasu

Haka suka cigaba da rayuwa cikin soda qaunar juna

Harsu Abu suka samu ciki suka haihu

Abu yan2 dika maza

Binta yan2 mace da namiji

An yi suna an kuma nunawa yaran gata sosai

Inda yaran Abu suka ci suna kamar haka
Samir
Salim

Inda na Binta suke amsa
Maheer
Macan kuma taci sunan hajiya Mariya

Abu da Binta sunyi karatu me zirfi da suka gama suka nemi aiki

DARAUDAU suka je suka Bude makaranta da Asibiti da masallatai suka Bude kun giyar tallafawa yara mata DARAUDAU na Alfahari dasu mahaifiyar Binta tayi aure bayan bikin Binta

Koda suka dawo gida kano Abu ta Bude gurin da za a dinga yiwa Amare KWALLIYA da kawayan su ta zuba ma aikata

Binta ta Bude gidan abinci kamar yanda ta fada

Amal ta hafi danta na miji wanda yaci sunan Alhaji Nasir

Yaya Nura yayi aure ya zama babban ma ai kaci matarsa ta Haifa masa yan2 mata ya maida sunan qannen nasa 2
Zainab
Fatima

*Alhamdulillah*


GODIYA GA DUK WANI MASOYIN NOVEL din πŸ’„πŸ’… *'YAR KWALLIYA* πŸ’…πŸ’„bansan wana irin godiya zan muku ba kunmin komai na gode kucigaba da bani goyan baya ta yanda zan ci gaba da suburbudo muku novel din da ze dinga saku ni shadi πŸ˜€ Allah YABAR QAUNA 😘😘

Ina ganin sakon ninku koda ban kama suna ba godiya ga kungiyar maru buta da kuka yaba da novel dina har kuka su na zama 1 daga cikin Ku nagode Wannan ma wata alamace nacewa inawutaπŸ”₯😜
Nagode da kula warku gare ni
Ana tare🀝


Masoyan *HUSBA'AHFAMA* ina muku Albishir cewa ina nan zuwa da sabon novel dina me sunaaaaaaaaaaaπŸ€”πŸ˜€


Yana nan tafe nan bada dadde waba

Love you All πŸ˜˜πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©


😎😎 *BANYAR DA WANI KO WATA YAJUYA MIN NOVEL* *DINA BA DUK WANDA YAYI NABAR SHI DA ALLAH HAKAN* *HAKA BAYA NUFIN BAZAN DAUKI MATA KIBA* πŸ‘¨β€βš–πŸ˜Ž
*A KIYA YE* 😎😎









New writer's

Hakan Take
Hakan Take
Hakan Take *husba'ahfama* πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹

Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment