Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan dukanin abunda kasa a gaba." Ya amsa da "ameeen.'' Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza, Garba ya take masa baya.

Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Ma'aruf a can tsallake a fake.....ranta duk a bace ta karasa bakin motar.....'Dan kwankwasa jikin motar tayi Camas! da Alhaji Ma'aruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur! ya bude mata motar yana fad'in" Ya akayi *'Yar gaske* Allah yasa kin aiwatar da komai." Rai a 'bace tace" Wallahi ya'ki bada had'in kai d'an iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba."

Alhaji Ma'aruf yace."Kai! wannan d'an iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji sha'awarki ba? anya ma kuwa yana da lafiya? duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji sha'awa ta kamashi." Ya 'karashe maganar yana bin jikinta da kallo.

Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas! take kwance a kai! Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka she'ke! Allah ya kyauta.

Hijab dinta ta sanya tace"Alhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku.

Alhaji Ma'aruf ya kunna motarshi yana goge gumi yace."Maganar ki gaskiya ce *'Yar gaske* shiyasa muke 'kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin."

Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Ma'aruf na fada musu yanda suke dauki ba dad'i a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kad'angare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai kar'beshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya.

Wasila tace"Ka rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kad'ai ya isheshi sai nayi fata-fata da rayuwarshi."

Alhaji Ma'aruf yaji dadi maganar ta yace.''Mu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya *Yar gaske* zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu."

Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa *(Ba iyak ka)* har sai taga abunda ya turewa buzu nadi.


'Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen........


'Yar 'kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana dakon dawowar 'yar tata.

Wasila ta mayar da 'kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu! kamar ba dare ba.

Uwani da Rashida suka fito a guje! Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshi.....Uwani na ganin Sabbin 'yan dubu-dubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu! ta rungume! 'yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar gud'a ta dinga rangadawa tana sakarwa 'yar tata kirari......Ita kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya.


Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige ru'babbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu 'kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga had'ddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya, wai! yaushe rabon duniya da ayya raye."!! Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannunta........Wasila tace"Yanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa.

Uwani tace"Ki d'an gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh! duniya kenan."

Wasila tace"Uwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga." Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fad'in"Ai dama ni nasan jari na haifa ke ba 'karamar mace bace idan ba'aso ki dan komai ba a so ki dan 'kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina."

Wasila tace"Uwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sana'a muka fita mukayi ko ba haka ba Camas!." Tafada tana kallon Camas! dake irga kudinta.

Camas tace"Kwarai kuwa sana'ar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba."

Uwani tace"Kai amma wannan sana'a ta karbeku wallahi Allah ya bada sa'a ya taimake ku."

Suka amsa da "ameen." Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada ha'karkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita *Sana'a*







_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/13, 1:07 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange


*Free Pege6*
Da safe suka tashi da wurwuri sukayi wanka tsaf suka shirya tuni Uwani ta ta fasa musu shayi Rashida ta siyo su madara da milo da bread har da su kwai Uwani ta soya musu yau karin kullamo sukayi rigijib suka karasa cinye sauran kajinsu na jiya....Wasila ta kalli Camas! dake gyara daurin dankwali tace"Ya kamata kije gida mamanku ta ganki kafin mu tafi ko." Camas! tace"Ke kin san idan na shiga gida yanzu babanmu nanan ba zai bari na sake fita ba kawai ki kyalesu idan na dawo ma had'u."

Tace"Shikkenan ke Rashida zan bada dubu talatin ayi aikin gidanan a sanya kokafi data waje data bandaki saboda bana so in doso layin nan wallahi in hango ku kamar tumaki a akurki wai sunan kuna cikin gida a zaune amma jama'ar dake waje na ganinku wannan gidan ai sunansa kango ba gida ba.

Uwani tace"Naji kinyi maganar dubu talatin duk a aikin gidan anya kuwa basuyi yawa ba." Tace"Na fiso ayi komai da inganci a sa kofofi masu kyau insha Allah yau ma idan mun fita zamu samo kudi.' Uwani tace"To Allah yasa." Wasila ta irga dubu talatin da biyar ta bawasu Uwani talatin na gyaran gida biyar kuma tace su dan auno kwanan shinkafa suyi cefane kafin ta dawo.......Haka sukayi musu sallama suka kama hanya suka tafi can guest house din Alhaji Ma'aruf dake a can yace su had'u.


Suna shiga harabar gurin suka wasu gugun matasa rukuni rukuni! amma 'yan daba da shaye-shaye sunfi yawa.....Alhaji Ma'aruf da wani mutumi suna tsaye a kansu suna magana dasu.

Kai tsaye can suka nufa Alhaji Ma'aruf na ganinsu ya washe baki ya kalli Alhaji Tasi'u "Yawwa kaga 'yan halak! ko yanzu yanzu mu ka gama zancensu ashe suna tafe.

Wasila tace" Aikuwa dai muna hanya wallahi kun san matsalar abun hawa sai a hankali." Alhaji Tasi'u ya kalli abokinsa yana nuna Wasila da bakinsa yace"Ko baka fada mun ba na gane wannan ce *Wasila 'Yar gaske!"* Yace."Kwarai kuwa Alhaji kayi mamakin ganinta 'yar karama ko." Yace."Dai-dai kenan duk da kankantar ta nasan zata bamu gudumawar da muke bukata daga gareta Wasila naji kina maganar abun hawa da sauransu ki kwantar da hankalinki zan siya miki mota ta kece raini ke dai kawai ki bamu goyon baya domin zamuyi amfani dake domin cimma manufarmu.''

A dake! tace"Kar ka damu Alhaji a shirye nake wallahi domin harkar na shigo gadan gadan duk inda nasan zan samu nan zan nufa in zaku sakar min kudi magana ta 'kare."

Alhaji Ma'aruf da Alhaji Tasi'u suka fashe da dariya suna tafawa, Sai bayan sun tsaigata da dariyar ne Alhaji Tasi'u yace."Kunga wad'ancan mutanan dake zazzaune ko."? Suka ce."Eh." yace."To zaku fita dasu yawon kamfen saboda mun samu labarin *Ahamadu (Ba iya ka)* zai fita zagaye gari domin yad'a munufarsa a kan talakawa to muna so duk inda suka shiga suna yad'a manufarsu su shi ku soke! ku watsa jama'a akwai kayan aiki a tare dasu Lauje karkuji komai kuyi aiki sosai mune muke da mulki a hannunmu babu wani abu da zai same ku."

Wasila tace"Kar ka damu alhaji nayi maka al'kawari bakin rai bakin fama." Alhaji Ma'aruf ya kalli Camas yana lumshe mata ido yace."Kefa baki ce komai ba."

Tace"Haba karfa ku damu nima na dauki alkawari insha Allah sai mun rusa shirin *Ba iya ka."*

Alhaji Tasiu ya nunawa matasan nan su Wasila yace sune abokanan tafiyarsu su kula dasu a matsayinsu na mata, har bakin mota suka rakasu suka shishhiga a'kalla sai da suka cika motaci hud'u irin na haya saboda yawansu sun kai su ashirin da wani abun....Kai tsaye suka dauki titin da zai futar da mutun cikin gari.


Cikin shadda fara kal ya fito yana daura agogon silvar a hannunshi hularshi ya kar'ba daga hannun Garba ya d'ora a kanshi *Ba kano* zallah yayi kyau har ya gaji ya zaune gefan gujera yana sanya safa Garba ya gama goge masa takalminsa sawu ciki ya mika masa ya sanya a kafafunsa yana mikewa Khalifa babban amininsa ya shigo shima yana sanya da manyan kaya shi harda babbar riga cikin kamala da mutumta juna suka gaisa kai kana ganin mu'amularsu zaka gane masu ilimi ne suna kuma aiki dashi........suna fita harabar gidan suka tadda matasa sun kai su goma duk suna jiran fitowarsa....Aikuwa ya dinga amsa gaisuwarsu yana daga musu hannu su kuma sun rud'e da fad'in" Sai kayi Ko garin ba kowa mu muna tare da kai kane za'bin talakawa, Kano sai *Dan Musa."*
Ahamad ya d'aga dukanin hannuwasa biyu sama da 'karfi yace." *CPC."!* Suka amsa da *"Sa'a!!!"* Yace."Sa'a ta mai rabo ce." Sukace "Kaine kake da Sa'a mai Sa'a." Ya saki murmushi da fad'in "Allah ya bawa mai rabo Sa'a." Suka amsa da "ameeen."!!!" Da sauri Garba ya bude masa bayan wata had'addiyar mota ya shiga Khalifa yabi bayanshi Garba da Dan uwanshi Hadi suka shiga sai direba ya shiga mazauninsa.....Kafin kice kwabo kin nemi jama'ar gurin nan kin rasa duk sun shisshige motocin dake fake a gurin domin su raka dan takararsu yad'a munufarshi.....Kai tsaye titin da zai sadaka da wata unguwa a cikin gari suka nufa mai suna *Jakara* nan yake so ya fara zuwa saboda yanda yake jin labarin unguwar babu kyau ga ta'bar'barewar al'amura da yawa tarbiyar yara matasa ta lalace babu sana'ar yi sai jagaliya da harkar gwan-gwan da sauransu yana so ya fara zuwa unguwar ya yad'a munfarashi kafin ya shiga sauran unguwanni.


A kan idonsu motocinsu suka dinga parking, dake duk rabin unguwar Jakara kasuwa ce kafin kice kwabo guri ya hargitse da kaya-kaya jin cewar ga d'an takarar gwamna nan yazo yad'a munufarshi masoya *Ahamdu Musa Ba Iya ka* suka dinga turereniya domin suje su daga masa hannu.....Matasan nan suka fito da tarin pastocinsa suka fara aikin mannawa a bango da shagunan mutane gefan titi suka dinga bi suna mannawa guri ya cika ma'kil! Khalifa ya bude masa samar mota ya fito da jikinsa ya daga hannuwansa biyu yana fad'in" *CPC."!* Sai gurin ya rud'e! da fad'in" *Sa'a!!!!!* Su Wasila suka keto gurin da motocinsu a guje!!!! A take mutane suka watse kowa na ceton ransa.....Parking din motocin sukayi suka fito a fusace! ko wanne da makami a hannunsa.....A sai guri ya hargitse ihu!! kawai kakaji da gudu radadada!!!!!

Hankalin Ahamad ya tashi sosai gashi Police guda biyu kacal ya dauka kuma suma al'amarin yafi 'karfinsu domin 'yan daban gidan gwamnati suna da muggan makamai!! Ya ware murya sosai yana fad'in"Kowa yayi takansa ya tsira da rashi."!!!! Wani *Dan daba* ya 'bullo daga wata hanya dake da maraba da wata katuwar kwata hannunsa rike da wata shar'be'biyar addah! sai kartar ta yake a 'kas! yana sakin wani uban ihu! da fad'in" *Sai kayi ko garin ba kowa."* Eh! yane! mu za'a kawo wa raini a unguwar tamu! ashe yau sai an zubar da jini wallah!!!! Huhhhhhh! ya kurma wani uban ihu! yayi kan 'Yan daban Gidan gwamnati yana sararsu ta ko'ina!!!

Wasila dake can aikin Ya'bawa Fastocin Ahamad kwata da 'bakin mai!! ta hango abunda ke faruwa Abokanan tafiyar ta sun suna shigewa mota saboda *'Kumd'um!* dan daban nan ya soma fitarwa da wasu jini sai suka razana suka soma shiga mota.....Da gudu tazo shiga mota *'Kumdum'* ya fuzgo hijab din jikinta ta dawo baya 'Kara ta 'kwallara! ganin yana 'kokarin kai mata sara da 'katuwar addar dake hannunsa ta rintse ido gabanta na buguwa fat! fat! fat! shikkenan ta mutu!!! Shiru taji gurin yayi ta bude idonta a hankali tana bin mutanan gurin da kallo......Shi ta gani tsaye a gabanta hannuwansa cikin aljihu yana mata wani mummunan kallo still ga *'Kumdum* rike da shar'bebiyar addarsa a hannu.!!

Kallon juna suke ita dashi! tsaf! ya gane yarinyar nan ce da shigo masa gida jiya tabbas ga maganar Garba ta fito ashe da wata manufa ta ziyarceshi ya gode Allah da bai sanya masa kwad'ayin mata ba da badan hakaba da tuni bukatarsu ta biya a kansa.

Ya kalli 'Kumdum dake zare ido yana ciccije baki!!! Yace."Rabu da ita kar kayi mata rauni ko ka zubar mata da jini! taci albarkacin sunan mace da ta amsa mace duk inda akasanta mai daraja ce da kame kai Astagafurullah wannan yarinyar ta 'batawa mata sunansu idan ka daketa ko ka zubar mata da jini duk a banza tunda na lura da akwai bakin iyaye a kanta so ka kyaleta taji da abunda ke damunta zamu dai cigaba da yi mata addua idan mai shiryuwa ce kuma insha Allahu muka samu mulki a hannunmu duk zamu tattara ire irensu mu samu mu had'asu da mazaje dai-dai dasu muyi musu aure babu shakka za'a samu sassaucin wasu abubuwan."
'Kumdum! ya saki hijab d'in Wasila dake damke! a hannunsa yana fad'in"Eh! Yanda kace haka zakayi mahadi mai dogon xamani insha Allahu kano ta kace ko ana ha! maza ha! mata sai ka tuge! wancan wawan! da bai iya komai ba sai hauka.''!!!!!! Jama'ar dake gurin suka sa ihu! da fadin""Maganarka haka take 'Kumdum Kano ta d'an Musa ce ko ana so ko ba'a so sai yayi."""!!! Wannan damar da Wasila ta samu ya sanya tayi wuf! ta bar gurin can inda motocinsu suke ta nufa ta tarar duk an ragargaza gilashin motocin Camas! ta bude motar ta shiga da sauri wani matashi ya daki motar da kafarsa yana musu ihu!!! Sai da suka yi nisa da gurin sai suka saki wa'kar gwamnan dake ci a yanzu Mai taken *Munyi muku fintinkau!!!!!! Kano sai kallo daga nesa mai raba gardama yazo Enginer Lawan Rabo, duk wanda zai ja dakai shine wawa!!!!!* Wasila ta fito da jikinta ta saman mota tana watsawa Ahamad da'kuwa! da dukanin hannunta tana sake fad'id"
*Wanda zai ja da Engener Lawan Rabo shine wawa!!* Ahamad yana kallon sanda take watsa masa hannayenta da sunan da'kuwa! *{Zagi!}* ransa ya 'baci sosai lallai yarinyar nan bata da kirki ya lura yar adawa ce mutuka dole ne ya sanya ayi masa bunkice akanta domin abun nata ya wuce gona da iri.

Mota ya shiga tare da jama'arshi jama'ar gurin sai daga masa hannu suke suna masa fatan alkairi yana amsa musu cikin sakin fuska amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin zaka tarar tayi ba'kikkirin sakamakon zagin da Wasila tayi masa wanda ba kowa ne zai fahinta ba sai shi wanda akayi dominsa.






_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/13, 4:15 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko Orange_

*Free Pege7*
Wani irin gudu motocinsu sukeyi kan kwalta, suna sakin ihu!Wa'kar injiniya Lawan Rabo ta tashi a motocinsu jama'ar gari suma suka dinga ihu! da fad'in "Ba mayi!!! insha Allahu kano ta d'an Musa ce! su dinga jifan motocinsu da duwatsu suna ihu!!! Su Wasila da kyar suka sha amma dai hakan yayi musu dadi tunda dai sun rusa shirin *Ahamadu* sun hanashi aiwatar da nufinsa wannan ya nuna musu suke da nasara a kanshi.

Khalifa ya kalli fuskarshi ya ganta a murtuke! yasan ranshi a 'bace yake gyaran murya yayi yace." Wai wannan cin maganin da kakeyi na menene dole fa ka fuskanci irin wannan 'kalubalan al'amarin siyasa sai addua komai mutuncinka sai ya zube kauda kanka kawai zakayi.

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya d'an gyara zamanshi yace."Khalifa sam abunda mutanan suka turo ayi mun bai dameni ba saboda nasan sunyi abunda yafi wannan......Shin wai baka ganin zagin da yarinyar tayi min ne."!?
Khalifa ya dan gyara zaman hularshi yana sakin murmushi a hankali yace."Duk akan idona al'amarin ya faru sosai nayi mamakin tsaurin idonta na fahimci kuma harkar takeyi da gaske so kar ka damu da wannan Siyasa ce a gabanka ma sai a zage ka a jefe ka kai dai tunda kace za kayi to sai ka daura d'amara!

"No!!! Karya ne wallahi." Yafada a zafafe! ya kalli Khalifan da jajayen idanunsa da suka rine da 'bacin rai! yace."Khalifa Siyasa ba hauka bace kamar ni wannan yarinyar gantafalfala ta zageni! kai kanka kasan halina bana ya fiya mutukar mutum ya shiga gonata ban hanata tayi min komai ba na yarda siyasar 'kasa ce amma banda zagi sai na ci mutuncinta wallahi."!!!

"Clm dwon mana ka nutsu fa ba'a saurin yankw hukunci da gaggawa ka kyaleta kawai idan ta sake sai ka dauki mataki a kanta amma yanzu kana yi mata wani abu zasu 'kulla maka wani sharrin kasan halin su dai."

Ya rintse ido yana sake hango lokacin da take watsa masa hannuwanta da sunan zagi! Ya bude ido yana sauke numfashi idan fa bai rama abunda yarinyar tayi masa zuciyarsa zata iya tarwatsewa mutum ne shi mai bala'in kishin kansa da 'kaunar iyayensa ya tsani na 'kasa dashi ya raina shi ko ya zageshi baya daukar irin wannan rainin shiyasa yanzu hankalinsa ya tashi mutuka duba da yanda yarinya 'kankanuwa wacce bata wuce 'yar cikinsa ba ta zageshi dole yayi bunkice a kanta.

Khalifa ya dinga tausarsa da kalamai masu sanyi yana nuna masa haka lamarin siyasa yake dole fa sai ya kauda kansa ga dukanin abunda 'yan adawa zasuyi masa idan ba hakaba kuwa zai 'bata rawarsa da tsalle kawai ya share yarinyar ya bari kawai duk sanda ta sake to suma baza su kyale ba.

Garba Da Hadi suka ce "Sir da ka bari wannan 'dan daban ya koya mata hankali wallahi yarinyar bata da mutunci ko kadan muma munga abunda tayi maka wallahi munyi rantsuwar duk sanda ta sake maimaita abunda tayi sai munyi mata tsirara sai mun tujara ta a gari karyar iskanci takeyi.

Ajiyar zuciya ya sauke ya dan ji sanyi cikin ranshi Yace." Na rabu da ita saboda maganganunku ammafa ku sani duk sanda ta sake kwatanta zagina wallahi ranar sai ta raina kanta sai tayi nadamar zuwanta duniya babu ruwana."

Khalifa yace."Yawwa mai girma Governor haka ake son shugaba da daukar shawara insha Allahu kai ke da nasara a kansu" Hannu ya bashi suka rike suna sakin dariya Ahamadu yace." *CPC."* gabad'anyansu suka amsa da *"Sa'a!* Ya sake fadin." *CPC."* Suka amsa da *"Sa'a."!* Yace." Mulki na Allah ne."! suka amsa da fad'in "Insha Allahu kai Allah zai bawa." Ya amsa da "Allah ya bamu Sa'a." Suma suka amsa da "ameen."


Wasu Wasila kuwa kai tsaye gidan Governor suka nufa domin su alhaji Ma'aruf nacan gidan suna meeting sai sukace su samesu a can, suka samu wata katuwar rumfa suka zazzauna kamar wasu almajirai suna jiran fitowarsu.....Can sai gasu sun fito daga wani dakin wanda yake nuna alamun dakin taro ne sun kai su goma wannan yana wane wannan sun sha lafiyayyun shaddodi sai motsi takeyi tana she'ki masu Cot a cikinsu kad'an ne......Kai tsaye rumfar dasu Wasilar suke suka nufa ta ganinsu sun doso gurinsu sai ta mike da saurin gaske ganin harda Governor ya sanya ta fara masa kirari da bambad'anci! dama Wasila akwai shegen za'kin murya tsiya Governor tun kafin su karaso yake murmushi babu shakka wannan yarinyar za'aje da ita irin wannan washi haka!!!! Gabadayansu suka mike tsaye ganin sun iso gurin Lauje dake jin haushin abunda Wasila takeyi ya buga mata tsawa da fad'in"Ai sai ki saurara haka domin mai girma governor ya iso ki bamu damar magana." Wasila tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

Gaisuwa suka mike garesu suka amsa sosai Alhaji Ma'aruf ya kalli Lauje yace."Kaine wakilin tafiyar ya akayi alamu na nuna mana cewa akwai nasara a tafiyar." Kafin Lauje yace komai Wasila tayi karaf! tace"Alhamdullihi muke da nasara insha Allah domin tun zuwanmu gurin muka watsa shirinsu muka tashi hankalinsa dana jama'arsa ni da kaina na dinga bin pastes dinsa da suke mannawa ina yagewa ina watsa masa ruwan kwata da bakin mai! da 'kyar! nasha a hannun wani d'an daba."!

Governor Ya kallesu yana fad'in"Da gaske maganar haka take."? Duk suka amsa da "Hakane ranka ya dad'e."! Lauje yaji tamkar yaje ya sha'ke wuyan Wasila shin wai me take nufi ne? yarinyar fa ta za'ke da yawa anya ba sai ya taka mata burki ba kuwa."

Governor Ya kalli Wasila yana murmushi Yace."Dama tun kafin na ganki na samu labarinki gurinsu Alhaji Ma'aruf gaskiya ne *'Yar gaske!* kin cancanci ayi miki komai zamu zauna dake insha Allahu ki fada mun dukanin bukatunki." Wasila aka saki murmushi ana gyara tsayuwa farin ciki duk ya isheta tace"Godiya nake mahadi mai dogon zamani governor da ba ta'bayin irinshi ba ba za'ayi ba insha Allah." tana gama maganarta Ta koma ta zauna inda take kana ganinta zaka gane tana cikin farin ciki babu shakka bukatarta ta kusa biya sun kusa yin hannun riga da talauci.

Alhaji Tasi'u ya kalli Lauje dake faman cin kunu babu shakka katsalandan din da Wasila ke masa akan harkarsa ya isa har yaushe ta shigo harkar da zata dinga za'kewa da za'kalewa kan komai kafin zuwanta shine yake jagoranta al'amura da suka shafi harkar jagaliya amma ya lura yarinyar idanunta kar suke zata iya komai bayan haka kuma macace dole tafi shi samu power a kanshi

Yace."Duk wasu bayanai munji su daga bakin *'Yar gaske!* kuma kun tabbatar da maganarta babu shakka munji dadin kasancewarta a wannan tafiya tamu, domin ta nuna mana ita jaruma ce kuma mai alkawari zata iya fansar da ranta a kan wannan harkar Kai Lauje daga yau Wasila *'Yar gaske* itace shugaba a wannan tafiya taku abunda tace muku shi zakuyi kai kuma in yaso sai ka zama mai take mata baya.

Lauje wani irin gumi! ya shiga yanko masa kai!!! 'Karya ma kenan! wannan afiruwar yarinyar itace za'ace zata jagorance shi aikuwa da sake!!! wallahi ba zai yarda ba. Cikin ranshi yake wannan zantukan amma a fili sai yace."Gaskiya ne Yallabai dukaninmu mun yaba bajintar yarinyar dan haka zamu bata hadin kai dari bisa dari mu dai fatanmu mulki ya cigaba da dawwama a hannunmu."

Governor Ya kalli Alhaji Ma'aruf yace."Ayiwa *'Yar gaske* kyauta ta mussaman Kafin mu zauna da ita.....Lauje da sauran yara suma ayi musu kyauta dai-dai gwargwado ai sun faranta min rai mutuka."

Aikuwa Alhaji Ma'aruf ya d'auko daurarrun kudi 'yan dubu dubu sabbi fil fil ya mikawa Wasila dauri hud'u....Kana ya mikawa su Lauje dauri hud'u kwatankwacin na Wasilan Ita kuma Camas aka bata dauri d'aya.....Wannan al'amari yayi masifar 'batawa su Lauje rai!! lokaci guda sukaji sunyi masifar tsanar Wasila daga zuwanta zata zo ta kar'be musu fada lallai da sake sai sun dauki 'kwakkwaran mataki

Please Login or Register in order to submit comment