Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana gauraye jikin ta. Yayinda wani farin ciki ke cika zuciyarta tamkar kumfar omo a cikin aton bahon wanki. Yau itace yaranta ke faWa mata suna son yin magana da itane iya su kaWai babu matar can a tsakkiyarsu. Ya rabba, ita kam mizatace da UBANGIJI yau. A zahiri kam sai ta dake babu wani alamun komai a fiskarta ta dawo ta zauna. Babban Yaya ne ya fuskanceta da yau cikin nutsuwarsa.
 Mamy akan Ajwaad ne dama muke son dan ALLAH kisa baki a tsakanin rikicin Abah da Oum. Dan ALLAH ki taushi Abah akan ya bari Maanal ta tare a Wakinta gobe idan ALLAH ya kaimu, dan gani yake kamar Oum ta kasa fahimtarsa ne saboda soyayyarmu ta rufe idonta, Auta na buatar matarsa a kusa da shi ya fahimci Oum dan ALLAH .
Sosai kalmar soyayyar nan ta daki zuciyar Mamy, dan saida ta maimaitata a zuciya yafi sau uku. A fili kam sai ta sake raunana fuskar tata ta ce,  Oh dama wani abune ke faruwa? Ai ni na zata dan bashi da lafiya ne kawai bata tare Win ba. Yau gajiya tasa sau Waya kawai muka haWu da Oum Win. Amma gaskiya ai Abahn naku ya faWa, Mamanku ta cika rigima akan al'amarinku.....
Cikin ar dariya Fawzan ya ce,  Kai Mamy kema haka zaki ce .
 Ai gaskiya ne Fawzan, ita idan kaga tana fushi a gidan nan abu ya shafi Wayanku ne. Karku damu zan sameshi muyi magana in sha ALLAHU. Itama zuwa da safe zan zauna da ita. Ni bara naje na Wan kwanta nima kamar Nibras Win gaSSaina duk ciwo suke min .
Godiya sukai mata da sai da safe. Fitarta babu jimawa Oum ta shigo itama. Su duka miewa sukai sukai kanta ganin har yanzu fiskarta a cinkushe, ga idannunta kamar wadda tayi kuka. Take suma duk fuskokinsu suka sauya. Murya a rauanne Babban Yaya ya ce,  Oumna Please ki cire damuwar nan, kin san fa Abah wani lokacin dan kawai ya kunnaki ne bawai abinda ke ransa kenan ba.
 Amma Fadeel ya tausaya masa mana, kwance fa yake baida lafiya. Shin ALLAH ma ba muna masa laifi ba ya kuma gafarta mana saboda rahamarsa .
 Hakane Oum shima zai huce . Cewar Fawzan yana mata murmushi da kama hannunta ya sumbata. Haka sukaita lallashinta har sai da tayi murmushin itama. Kafin su nufi bedroom Win AA Win. Ganinsa zaune a bakin gado yasa ta arasa shiga ciki da sauri, kusa da shi ta zauna tana mai rio hannunsa daya dafe kansa da shi, dan yaji duk zancen Mamy da su Babban Yaya. Mamakin Mamy da halinta ke sake raunana masa zuciya, amma yana mata fatan shiriya kafin lokaci ya ure mata. Yasan duk abin nan fa Abah keyi daga cikin shirinta ne, zai kuma bama kowa mamaki in sha ALLAHU cikin saui.
 Auta yaya akayi? Kanne har yanzu dai? .
Karan farko ya kalla Oum ya sakar mata murmushin arfin hali, sai kuma ya kwantar da kansa a saman kafaWarta.  Ya daina Oum .
Ya faWa acan an maoshi.
 To Alhamdullah, ALLAH ya ara lafiya baby na kaji, yanzu mi kake son ci? .
 Oum tea kawai .
 To ba damuwa bara Fawzan ya haWa maka .
Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya kalla Babban Yaya da Fawzan. Murmushi yay musu kaWan, suma dake kallonsa suka maida masa murtani suna tambayarsa yaya jikin nasa. A samman laSSa yace da saui. Daga haka Fawzan ya fita haWa masa shayin. Kallon Oum ya Wanyi, har ya janye idanun sai kuma ya tsira mata su, kafin tai oarin dai-daita fiskarta har ya furta,  Oum kinyi kuka .
 Kukan lafiya Auta  . Ta faWa tana Wan harararsa cikin yanayin son basarwa. Ina bai gamsu ba, cikin rashin kuzari ya zamo asan lallausan carpet Win gaban gadon ya zauna yana mai zuba mata idanunsa dake a shanye. Zatayi magana ya girgiza mata kai,  Oum Please ki daina damuwa, nasan a kaina ne ko? Dan ALLAH ki bari naji saui fa, ki tambayi babban Yaya ma . Ya are maganar yana kallon babban yaya a raunane.
Cike da tabbatarwa babban Yaya ya jinjina kansa shima yana kaiwa zaune kusa da Oum Win, Fawzan ma yazo ya miama AA kofin tea Win daya haWa masa suka zagayeta kowa na mata nashi daddaWan kalamin, idan ka gansu abin sha'awa da birgewa sojojin yaanta zagaye da ita, basu barta ba har sai da fiskarta ta washe da fara'a kamar yanda suke so. Shima AA sai oarin arfafa kansa yake yanda hankalinta zai ara kwanciya. Ganin dare yayi Oum da babban Yaya suka baro sashen suna ara tattaunawa aka bar Fawzan da zai kwana da shi. Bayan wucewar tasu ne Fawzan ya zayyanema AA komai dake faruwa ana rikicin da Abah keyi akan tarewar Maanal kamar yanda ta buaci ji. Murmushi AA yayi mai faWin da har ya saka Fawzan zuba masa idanu baki buWe.
 Oh abin ma kai nishaWi ya baka kenan? .
Cewar Fawzan cike da mamaki. Murmushin AA ya sake saki a karo na biyu, sai kuma a hankali ya jingina da fuskar gadon yana kai hannu ya Wan shafo gashi kumatunsa.  To yaya Fawzan in bai sakani nishaWi ba kuka kake son nayi, banda ma abin Oum minene abin Waga hankali anan, ta bar masa arsa mana .
Dariya Yaya Fawzan yayi da faWin,  Oh hakama zakace? ALLAH yasa ya jika, kaga idan sati Waya yay niyyar horaka sai ya maida shi wata uku kadai san halin Abah .
Murmushi kawai AA yayi kaWan batare daya sake cewa komai ba. Fawzan kuwa ya tasashi gaba da tsogumi...

__________&

Washe gari da safe Alhamdullah Oum ta tashi da sauin damuwa ba kamar jiya ba. Dan tunda ta kira Mah-mah a Wazun da asuba ta sanar mata sai Mah-mah Win ta tausheta da mata nasiha akan ta sakama Abah Win ido, ta bashi damarsa matsayin mahaifi dan ko yaya shima bazai yi abinda zai cutama Ajwaad Win ba ai, sannan kuma tunda a gida Waya suke ai babu wani abun Waga hankali in dai yaran yanzu ne masu arancin kunya, shi da kansa ma zaice ya Wauki matarsa basai ta Satama kanta rai ba. Ji tai zuciyarta ta rage jin haushin Abah Win, ta kuma Wau alwashin daidaita komai a tsakanin AA Win da Maanal ta yanda Abahn da kansa zai tattarasu ya kora sashen nasu batare da alwashin nasa ya cika ba.
Yau Win yanda Manaal take ta faman sinne-sinnen kai ya saka Oum kamata ta duddungure da faWin,  Wai Auta ni kike son maidawa surukarki a gidan nan, jiya na saka miki ido ne kawai naga iya gudunki, to kar naji karna gani. Maza tashi muje kitchen ki haWama mijinki abinci yau kije ki duba jikinsa dai kada mu take doka .
Murmushi Maanal tayi tana Soye fuskarta a jikin Oum Win, itako Oum na mata dariya. Atare da Oum suka shirya abinci mai saui ma AA Win har kala uku, sai wanda suma zasu ci, dan yauma Abah a sashen Mamy zai karya. Suna kammalawa Oum tace taje tai wanka, yayi da masu aiki keta faman kimtsa sashen kamar yanda suka saba. Ba wata kwalliya Maanal tayi ba, ta dai gyara fuskarta ta Wan saka kwalli da lipsgloss, sai tai simple Waurinta daya zauna mata Wan kwantaccen gashinta ya Wan fito ta gaban goshi kaWan. Tana oarin saka turare kiran Amaal ya shigo mata. agawa tai cike da shagwaSa dan haushinsu take ji a Kano sunce zasu dawo amma sukai mata wayo. Dariya Amaal Win taita mata, sannan ta kwantar mata da hankali akan ai next week in sha ALLAHU suna nan tafe da sauran kayanta, dan Daddy yace sai zuwa arshen sati za'a kai kayan gararsu ita da Huznah. Duk da dai Oum tace a Wan saurara akwai sauran biki da zasu yi anan Abujan shiyyasa ma bata tare ba. Sosai ita Maanal ma abin ya bata mamaki, yanzu duk wancan kaikawon da akasha na Kano bai kuma isa ba. A fili kam sai suka cigaba da maganar su da Amaal. Tana ajiye wayar mai aikin Oum ta shigo tai kiranta, mayafi ta Wauka ta sanya, dan haka kawai taji tana jin kunyar fita a haka matua. Tayi yau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan amshinta daban ne, ga unshinta raWam yanata Waukar ido daga bain har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autanta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai Worewa kuma. ALLAH ya kawo zuri'a masu albarka..........
'




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'4


______________


.......Basket Win da aka shirya masa kayan abincin Maanal ta Wauka, kai kace wani anguwa zasu je ba cikin gidan ba. Sun fito gwanin sha'awa daka gansu kaga uwa da Wiya ba uwar miji da matar Wa ba. Oum tasan Mamy na sashen Abah dan haka bama tace Maanal taje ta gaida su ba, shiru ma gidan alamar kowa na sashensa, sai ma'aikata dake ta oarin kimtsa ko'ina, sunta gaishesu har suka isa sashen AA. Haka kawai Maanal ke jin kamar tace bazataje ba, amma bazata iyama Oum musu ba duk tsanani. Kai tsaye Oum ta shige dan tasan bazasu sami kowa a falon asan ba, Maanal dai biye da ita zuciyarta na mata wani nauyi. Dan kana shiga da sallamar sabon fenti dana sabbin kaya zaka fara cin karo. Tabbas dole ne mai kallo ya furta Masha ALLAH, dan kuwa dai Daddy yayi matuar oari, daga Maanal Win har Huznah ya zuba musu dukiya. Duk da asace Maanal ke kallon komai sai da taji hawaye sun cika mata ido sosai, wata irin aunar Daddy da Ammie na ratsata, falon asa ma kenan, bata san yaya kitchen yake ba, kuma su Didi sun sanar mata daga saman har asa Daddy ya cika mata su da kaya. Zuciyar Maanal bata arasa fashewa ba sai da suka hawo upstairs Win, ya subahannallah komai yaji, a hakan ma nan ba'a kammala aikin ba dan ga manyan kwalaye nan a ajiye gefe an tule, zama sukai a cikin kujerun dan su an riga an shiryasu, dai-dai nan Fawzan ya shigo shima da alama yaje sashensa ne.
Cike da tsokana yace,  Inyee kaga Lilly amaryar Auta .
Da sauri Maanal ta Wan waro masa idanu, sai kuma ta Sata fuska. Dariya Fawzan yake yi, Oum dake tayashi ta ce,  Ni ban taSa ganin yaya irinka ba Fawzan, anya kuwa bazan turaka hutu Kano ba ka bar min yara su shaata .
Dariya sosai Fawzan yake yi, ya kai zaune kusa da Oum Win yana gaisheta, itama Maanal Win sai ta gaisheshi. Oum ce kawai ta tambayi yaya jikin Autan nata, Maanal kam kunya ta hanata yin hakan. Fawzan ya ce,  Da saui sosai Oum, dan tare mukaje massallaci ma da asuba yau. Ku shiga mana ai ya tashi .
Murmushi Oum tai da faWin,  Alhamdullahi . Sai kuma ta juya ta kalla Maanal da kanta ke'a asa. Cike da kulawa ta ce,  Auta tashi ki shiga masa da abincin gamu nan zuwa . Kai kawai Maanal ta iya Waga mata, sai dai ji take kamar tace ma Oum Win a'a amma babu dama. Haka ta Wauka basket Win kanta a asa, Fawzan ne yay mata nuni da Wakin yana tsokanarta, ita dai yau babu bakin maida murtani sai Oum ke kare mata. Sai da tai Wan jimm a tsaye kafin tai knocking da yatsanta Waya kamar mai jin tsoro, tabbas badan bazata taSa iya musu da Oum ba komi za'ai bazata je inda yake ba, duk da kuwa har cikin ranta tana jin damuwa da rashin lafiyar tasa. Jin shiru ta sake yin knocking Win, sai kawai jitai daga falo Fawzan nace mata ai ta shiga kawai ba lallai yajita ba. Nan ma jitai kamar ta saki hawaye, amma haka ta danne kamar mai tsoron shiga wuta ta tura ofar Wakin a hankali. Sai da ta Wan rumtse idannunta taja numfashi kafin ta saka afarta a hankali lips Winta na motsawa alamar sallama. Bata kalla cikin Wakin ba ta maida ofar ta rufe, yayinda wani sassanyan amshi ya daki hancinta, Wan sanyin acn da aka saka kaWan yay wani shiga jikinta. Sosai ta saki ajiyar zuciya a cikin irjinta. Sai kuma ta shiga bin Wakin da kallo jin alamar kamar babu mutum, babu kowa kam, sai dai gadon babu gyara alamar yanzu aka tashi a kansa, Wakin ya tsaru matua, ga komai dai-dai misali babu wani tarkace, duk da safiya ce babu yawan haske a Wakin, dan labulayen duk a sake suke, fitulun kuma a kashe sai mara haske sosai kalar blue. Hakan ya saka launin Wakin sake zama mai Waukar hankali. Nanma ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma ta cigaba da takawa a hankali kamar mai sanWa da nufin ajiyewa ta fice abinta tunda ALLAH tasota baya Wakin, sai dai kuma da'alama shirin nata zai bi ruwa, dan tana gab da isa tsakkiyar aton bedroom Win ofar bathroom dake daga can cikin closet Winsa da zaka iya hangowa ta cikin Wakin ta buWe, harga ALLAH da farko tsorata tayi dan haka ta kalla wajen, sai dai kuma da gudu ta Wauke idanun nata zuciyarta na wani kalar bugawa saboda saukarsu a kansa. Ba aramin jin ta gama rikicewa tayi ba, dan daga shi sai aramin towel daya Waura a ugunsa, buWaWWen jikinsa jie da raSar ruwa alamar wanka yayi, dan hatta sumar kansa a jie take itama dai da alama wanketan yayi. Shima dai cak Win ta tsaya, dan ganin nata ya saka shi jin shock na rashin zato dan tunda suka dawo bai gata ba, duk ciwon nan bata shigo dubashi ba. Kamar zai Wauke kai dan jin haushi. Sai dai ganin yanda tai tsammm kanta a asa ya sakashi sakin wani shegen murmushin gefen baki yana Wan yin luuu da idanun nasa kamar zai lumshesu. aramin towel ya cira dake rataye a jikin wani yayyawan hanger dake gab da ofar bayin, dan an tsara su ne a wajen kala-kala ta cikin closet Win gwanin birgewa. Saman kansa ya kai towel Win kafin ya fara takowa harya fito daga closet Win gaba Waya.
Bedroom slippers ne a afarsa masu taushi, duk da ba ara sautin takun nasa ke badawa ba sai take jin sa ita har tsakkiyar kanta, karo na farko a rayuwarta da taji wani mashahurin tsoron kasancewarsu su biyu kacal a waje, da ace zata iya da Sacewa kawai zatai a Wakin ta huta. Amma babu damar hakan gareta tunda ita ba aljana bace. Yana isowa gab da ita batama san wani arfi yazo mata ba tai saurin juya masa baya tana sake arfin rumtse idannunta hannayenta biyu data rie basket Win na ara dame shi da yau. Cak ya tsaya shima dariya na neman cika masa zuciya, dan yanda ta juya Win da saurinta sai ka Wauka wani kumurcin maciji ta gani ko zaki. Da yar ya iya danne dariyar dake cinsa a rai ya matsa jikinta sosai, tsabar neman magana sai ya zagayo da hannayensa ta gefe da gefenta ya Waura akan nata hannayen dake rie da basket Win, badan ya rie hannun nata da yau ba da sai basket Win yayi faWuwar da abincin zai tarwatse a wajen. Yanda ta takure jikinta waje guda ya sake bashi damar manne jikinsa da bayanta sosai tare da duo kansa saman kafaWarta yana busa mata numfashinsa a saman dokin wuya da cikin kunne, sannu a hankali ya sake matsar da fuskarsa jikin tata idanunsa a lumshe, kwantaccen gashin kumatunsa dake da damshin ruwa na gogar gefen fuskar tata. Da sauri ta zame hannunta dake rie da basket ya koma nasa hannun gaba Waya. Karo na farko ya saki Wan murmushi mai sautin da har taji, har yanzu kuma idanun nasa a lumshen suke yana shaar ni'imtaccen amshinta. Cikin matuar raWar da koda wani ne a kusa da su da wahala yaji miya faWa a hankali can asan maoshi ya furta,  Good morning Bestie .
Tsabar yanda maganar tashi taima Manaal shigar zuruff bama tasan ta zabura ba tana oarin tureshi, dolensa ya bata damar fita a jikin nasa, dan duk ta daburce har tana neman kaSe basket Win abincin hannun nasa. Hanyar fita ta nufa da sassarfa, muryarta na rawa, harshenta na sarewa ta furta,  Su Oum na falo . Kafin yay wani yunuri harta fice. Kansa kawai ya girgiza yana mai sakin murmushin da har sai da hawaransa suka bayyana, a ransa kam ayyanawa yake (Zamu haWe ne ai yarinya).

=Tace maka ita ba yarinya bace yanzu kana sake maidata baya<

& Sarai Oum ta lura da yanda Manaal ta dawo kamar wadda aka biyo, sai dai batai magana ba har sai da Manaal Win ta sanar musu cewar ya tashi. A dai-dai nan ma kiransa ya shigo wayar Oum Win. Basu ji abinda ya faWa ba, Oum tadai mie tana murmushi tace su shiga.
Fawzan ne ya fara shiga, Oum biye da shi, itace arshen shiga dan maalewa tayi a bayan Oum.Sosai Oum ta nuna farin cikin ganin yanda jikinsa yay saui yau sosai fiye da kullum, shima ganin fara'a a fuskarta sai zuciyarsa ta masa sanyi. Fawzan kam ya tasashi gaba da tsokana shi da Maanal data zauna a cikin yanayin takura, dan tun haWa idon farko da tayi da AA ta Wauke kanta bata sake kallon sashen da yake ba. Yanzu ma da Fawzan Win ke tsokanarsu kanta a asa sai Oum ke kare musu. A dai-dai nan Saheeba da Nibras sukai sallama. Kafin a basu iznin shigowa Naufal da Anum sun shigo. Kai tsaye yaran inda AA yake suka nufa cike da farin cikin ganinsa a zaune, shima fuskarsa da Wan sakewa ya Waga Anum ya zaunar a jikinsa, Naufal kuma ya zauna a kusa da shi.
Da kai kawai ya amsa gaisuwar da Saheeba da Nibras sukai masa. Ba haka Nibras taso ba, amma har ranta taji daWin ganin jikinsa da saui sosai yau Win. Wani gefe na zuciyarta kuma najin zafin ganin Maanal a tare da shi, gashi data kallesa sai taga idanunsa akan Maanal Win suke, ita kuma ar ranin hankalin sai wani latse-latsen waya take yi ita adole ga mai aji. Oho ita Maanal bama tasan tanai ba, hasali ma jinta take duk a takure, da Oum zata barta ma da tuni ta wuce abinta ta koma sashenta ita kam.....

________&

A lokacin da anan ahalin gidan ke sashen AA a Sangaren Mamy tana can tana waya da babbar yayarsu akan batun auren AA Win da Nuratu da sukaji su Abah sunyi shiru suni cewa komai ga shi har yau laraba, a yanda tsarin nasu yake kuma daga gobe alhamis ya kamata ace biki ya fara musamman tasu Sangarensu, amma sunji Wif babu wani bayani. Shine tai kiran Mamy Win dan jin mike faruwa. Bayanin da Mamyn ke mata rai Sace yasa tace yau zatazo Abujan dan tana Kano. Da wannan sukai sallama.
Zama Mamy tai tana mai dafe kanta. Eh lallai taci nasara akan Abah na hana Maanal tarewa a sashen AA, sai dai tana jin fargaba akan tunkararsa da batun bikin nan kuma. Musamman idan akai dubi da halin da AA Win ke'a ciki na ciwo. To amma kuma itama fatanta ai ayi bikin ne. Numfashi mai nauyi ta sauke sosai, tana mai tattara batun gefe ta jingine har isowar yayar tata dai, dan gara su tunkari Abahn tare zatafi samun warin gwiwa....

Kusan arfe uku na rana kuwa yayar Mamy ta iso gidan. A lokacin kusan kowa yana a sashensa, dan hatta AA yana sashen Oum, daga sallar azhar daya samu iya fita yau shi da sauran yan uwansa suka wuce sashen Oum Win. Manaal dai na Wakin tunda taji motsinsu tai fitowa, sai ma tayi kwanciyarta barcin dole, daga baya na gaskiyar ya Wauketa.
Mamy da kanta ta fito ta tarbi ar uwarta, kai tsaye kuma sashenta suka wuce, suna dai-dai gifta window Win Oum dake kallon sashen Mamy Win sautin dariyar su Fawzan ta shiga kunnunwansu, kasa hauri sukai sai da suka lea. Aiko idanunsu suka gano musu zaratan mazajen aan na Oum zagaye da ita tana bama AA abinci a baki, dai-dai kuma lokacin Babban Yaya shima ya buWe nasa baki wai ta bashi, shine suka saka sanya dariya, shima Fawzan yace bazai yarda ba ya je aka bashi. Kai da kaga fuskar Oum kasan cike take da farin ciki, haka suma su babban Yayan, farin cikin Oum Winsu ya saka fuskokinsu bayyana murmushi na musamman, musamman ma shi da AA da ba cika son yin dariya sukai ba sai sun so. Fuuuuu Mamy ta wuce sashenta zuciyarta na tafasa. Koda suka shiga Waki saita sakar ma yayarta kuka. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga irjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu Wan zane. Dan tabbas ta rigada ta gama mallake zukatan yaran nan da salon makirci (kamar yanda suke fassara soyayyar Oum Win akan su AA. Sai dai kuma wannan nasu mummunan zaton ne kawai, dan ita dai baiwar ALLAH Oum har cikin zuciyarta ne, hasalima takan manta da cewar ba itace ta Wauka cikin su AA tai naudarsu ba saboda yanda ta sakankance matua).........
'


_Dangin Mamy ina gaisuwa =D>q<_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =-=O_*
*_Typing=_*








*_=؞AJIYA A DUHU....=؞_*




*_Bilyn Abdull ce ><_*


*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._

*_My TikTok account =G_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=G<_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama==<<_

*_BOOK 2_*
<'5


______________

5


......Sun tattauna sosai kafin su yanke shawarar yayar ta tunkari Abah da batun bikin cikin hikima. Hakan kuwa sukayi, bayan sallar la'asar Abah ya dawo gida Mamyn tai mata rakkiya har sashensa. Bayan sun gaisa cikin mutunta juna dan akwai ar kunyar surukuta a tsakaninsu duk da kuwa Abah ya girmeta sosai, amma yana kawaice mata saboda dattako. Cike da kissa tana murmushi take faWin,  Kukam kamar a kanku aka fara aurar da auta, yanzu bayan shagalin Kanon bazaku barmu mu huta ba wani satin kunce zakuyi wancan kuma? .
Cikin danne takaici da yar Mamy ta aaro murmushi tana Wan laSe baki,  Ai jikinsu ne zai gaya musu dan nikam dai nayi na ALLAH da naje muku Kanon ma. Amma da zaku tausayama kanku da kun barshi ku haWe duka .
Cikin rashin damuwa Abah yay ar dariya shima da faWin,  Ai ku kwantar da hankalinku bikin ma Saturday Win dama da wahala ya yiwu. Dama yau nake son zama daku akan zancen dan yau da safe Baba ya kirani, ya kuma tabbatar min zuwa gobe shima zai samu mutanen gidan naku dan bammayi zaton Aunty Babba zatazo Win ba . Ya are maganar yana kallon

Please Login or Register in order to submit comment