Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Umar mu iyayenka bazamu hango maka abinda zai cutar dakaiba na baka. Nan da kwana biyu ka kawo min matar da zaka aura ko yar waye inbakada ni inada wadda zan gadaku aure tare Salma na fahimci tana tsananin kaunarka Kaine dai kake yi mata wulakanci ,Dan haka na yanke hukunci matsawar baka kawomin surukata ba to ka shirya tarbar Salma a matsayin. Bride dinka ,what? Salma fa kikace Hajiya yes ita Salmar dai dakasani meye bata dashi ba mace bace ko kafitane so go an think before na sake kiranka , Faruuq ya mike idonsa sunyi jajir kamar gauta zuciyarsa kamar ta Faso kirjinsa ta fito yama rasa mezaice da kyar yakai Kansa room dinsa har wani jiri yake gani hava yaza amasa haka bayan yanxu ne yake so yafara budewa Kansa sabuwar Rayuwa shida angel dinsa kamin wani lokaci zazzabi mai zafi ya rufeshi shi da kyar ya iya kiran abokinsa Dr. Khamal Dan ya Duba sa wan nan kenan.
A bangaren su Rukayya kuwa tun da suka fita unguwa basu dawo ba sai bayan la,asar sunsha yawo kam Dan sunga gari sosai har kasuwa saida suka shiga mummy tayi sayayyar kayanda take bukata daga nan suka dungumo cikin Adaidata sai gida A falo suka zube Dan dayake daddy yadawo suka gaidasa ohhh shine kuka fita harda patient din idan kuka kwaso mata rana fa gashi yau anyi rana, lah daddy ai taji sauki sosai cewar Sajeeda kedai kunason yawo daine ba wani sauki karfin hali dai gabaki dayansu sukayi dariya Rukayya tace Allah Daddynmu nasamu sauki sosai tau Baby Allah yakaro sauki yabaki lfy mai amfani aka amsa gabaki daya da amin after All Daddy tace sai Ku huta muyi shirin zuwa cikin gari again da murna sukace a shirye muke ai ohhh kajisu sarakan son yawo to da boys dina kawai zani ko my boys suka CE yes Daddy bazamu dasuba tunda mummy da Girls ta fita dazu muma da Daddy zamu fita yanxu ,mummy tace jealousy kukeyi to nima ai sai mun sake fita dasu watarana Daddy ya kashe mata ido daya basai na bari ba murmushi tayi zama ka bari ai duk Kansu kowa dariya yakeyi cike da so da kaunar yan uwansu bayan magrib daddy ya daukeso zuwa yawon shakatawa Dan dama already duk Friday sai sun zaga gari Dan su Debe kewa sunkan sha garin Dan suyi yawo sosai basu suka dawo ba sai 10 :pm kowa da sayayyarsa a hannu dashigarsu gida kowa room dinsa ya fice bayan sun yi sallar insha suka watsa ruwa sai bacci dayake sunci sun koshi asuba tagari Sajeeda& Rukayya 'yan biyu. Mummy da Daddy

Maman Ussee=

I REALY THANKS FOR UR CARE MY FANS LUV U ALL=


=N YAR BAIWAH =N 2 5

Maman Ussee=

Washe gari tun da safe su Rukayya suka tashi bayan sun idar da Sallah suka fara gyare gyaren gida koda mummy ta fito har sun kammala da komai dayake yanxu tana barin su su Dora breakfast danshi ba wuya kegareshiba suyan arrish daine sai Dora ruwan zafi sun saka komai a mu halin da ya dace suka koma room dinsu Dan suyi wanka bayan sun gaida mummy da kuma Daddynsu, fitowa sukayi da shirin zuwa islamiya kai tsaye dining area suka nufa basu wani bata lokaci ba suka kammala cin abinci kai tsaye suka fice dakin mummy sallama sukai mata suka fice zuwa islamiya.

A bangaren Umar faruuq kam abin yayi worst sosai Dan da kyar ya iya tashi yayi sallar magrib da isha wani zazzafan zazzabi ne ya keji duk da anyi treatment dinsa Amma ji yake kamar baisha komai ba bacci kam a ranar sai dai barawo har abinci kasa cinsa yayi washe gari haka ya tashi jiki ba kwari yadanji sauki dai irin nasa Dan har sallar asuba yaje bayanda gari ya waye yaje cikin gidansu gaida Hajiyarsa ba laifi ta amsa masa batare da wata damuwa ba kana ta CE INA fatar kana nan kana yanke disition din da ya dace dakai ko eah kawai ya bata amsa gud haka yanada kyau breakfast dinma bai wani ci abincin kirkiba yadan tsakura kadan yatashi ficewa yayi daga gidan Dan kwata2 baya jin dadin zama gidan garinma ya isheshi yakusa barin garin gaba dayama ya huta haka ya wuni a ranar ba dadi dayan bangaren zuciyarsa yana mararin ganin RUKAYYAH ga kuma Hajiya ta taso shi gaba.
Rukayyah da sajeeda. Basu dawo daga makaranta ba sai 12:pm da zuwansu falo suka zube suna hutawa mummy ta fito daga room dinta sannu da gida mummy yauwa yaran Daddy kuna lfy a makarantar to Alhmdllh suka amsa mata to masha Allah haka akeso bayan sun gama hutawa sukaje dakinsu suka ajiye kayan su sukan Dan kwanta su wuta kamin time din sallah yayi basu farka ba sai 2:pm koshima mummy CE ta tayar dasu Dan karfe ukku zasu koma Islamiya bayan sun idar da sallah abinci sukaci suka sake ficewa zuwa islamiya Dan daukar karatun marece sai 6:pm suka dawo gida a gajiye basu wani dadeba magrib tayi suka fice zuwa dakinsu Dan gabatarda sallah.
Haka Rayuwarsu ta kasance har weekend ya kare Monday morning ko waccensu ta shirya tsaf cikin uniform dinta suka dauki skull bags dinsu zuwa makaranta Dakin mummy suka shiga sukayi mata bye bye daddy ya dauke su zuwa skull dasu da su Abdallah da Fadil bayan ya ajiyesu ya ficewarsa zuwa gurin aikinsa bayan an kare Assembly kowace student ta nufi class dinsu do daukar darasi dayake ma text za,a fara musu yau Dan sun kusa fara exams yauma kamar kullun zaune yake cikin staff office ya rasa abinda ke masa dadi abubuwa duk sun cakude masa kwata kwatama ya manta yau yanada Class dinsu Rukayya before break yayi zurfi cikin tunani sai jin murya wata student yayi uncle muna da kaifa yanxu munta jira munji shiru shine mukazo muyi biko dago Kansa yayi OK Fateema ganin zuwa kice su shirya yau text zan muku kinji ta amsa da to yabata sauran kayansa ya CE ta fice masa dasu kamin yazo.

Bai wani bata lokaci ba yabi bayanta Rukayya na zaune a sit dinta hankalinta kwance fuskarta daka ganta. Ba wata damuwa a tartare da ita da shigarsa class din ita ya fara tozali da ita baisan lokacin da ya saki wani Kayataccen murmushi ba= a zuciyarsa cewa yake Alhamdullah my Angel taji sauki bayan an gama gaida shi shap shap yafara rubuta a saman white bord questions ya rubuta kamin nan yace every body should take a sheet of paper we are going to write, a text yes uncle suka amsa Rukayya batace komai ba Dan ita har yanxu bata huce dashiba duk da Sajeeda ta roketa da tabar komai everything ,yazama normal , bayan ta Rubuta name dinta a paper bata wani. Bata lokaci ba ta fara rubuta text dinta saidai duk dagowar da zatayi sai sun hada =@ dashi abin har ya soma gundurar da ita shikuma gogan ya kifa mata manyan Idanuwansa ko kiftawa bayayi ciki da so da kulawa wani sabon kaunarta yakeji yana ratsashi duk wani motsinda zatayi yana lura da ita dayaga ta dagoshi sai ya Ciro phone dinsa ya fara latse latse nan kuwa pics ne yake snapping dinta. Batama saniba yayita daukata pictures sunfi a kirga itace first data fara somiting din text dinta ta koma sit dinta ta zauna ita duk ta kagara yan class dinsu sukare text din Dan bama tason zama sa a class din nasu shikuma jiyake kamar suyita zama a haka after an kare text din karbar papers dinsu yayi ya fice daga ajin cike da shauki koba komai dai yau zuciyarsa zata samu sawaba kuma ya dauki pics dinta zasu debe masa kewarta.

Maman Ussee=

=N 'YAR BAIWAH =N2 6

Maman Ussee=

Zaune suke a gurin da suka saba zama domin. Yin break shikuma Faruuq yana cikin staff room yana hango ta sai dariya takeyi da murmushi abin ya matukar kayatar dashi har a cikin zuciyarsa wani sabon farin ciki yakeji yana matukar kaunar Rukayya bayaso yayi missing din ganinta koda na minti dayane haka ya wanzu da kallon ta har suka koma Class Ya Salaam! Ya ambata Wai wace irin soyayyace haka yakasa fada mata and kuma a kullun ji yake soyayyarta na kara ratsa zuciyarsa. Bai wani jima a skull din ba ya fita Dan dama sabida ganinta ne yake daukar time a skull din direct gidansu ya nufa da motarsa da shigarsa cikin gida yar gdn sa ya tarar a Falo tawani hakince kallo daya yayi mata ya dauke Kansa tasowa tayi da niyar yi masa magana hannu ya daga mata ke dakata look Salma na fada miki tun ba yauba nidake bamu daceba and u still don't understand me, plzz ina rokonki 4 d last time let me alone karki hadani da Iyayena Dan indan har kika kuskura kika shigo Rayuwa ta u wll regret, smiling tayi kamin nan tace ai kuwa baka isaba umar Faruuq weather u like it or not u wll marry me am yours,you're my and only me mtseww yaja tsaki it seem like you're not in your sense ,shiyasa kike maganar abinda bama zai ta ba yuyuwa, ai kuwa. Baka Isa ba Dan nice mahaifiyar ka kuma dolene kabi umarnina abinda nikeso shi zakayi yau kwana ukku kenan banji komai daga gareka ba saboda haka na yanke disission and it is Final , saboda haka kawai ka saurari zuwan Amaryarka Salma. Cewar Hajiya Kubrah tunda ta fara magana umar mutuwar tsaye yayi kasa motsa yatsansa yayi ji yayi jiri na Neman ka dashi kasa saurin rumtse idonsa yayi nawasu mintuna yasake budewa jiyake kamar a cikin marfarki Salma yagani zaune akan ciyar Hajiyarsa tana mishi murmushin mu gun ta , dakyar ya iya saita zuciyarsa Dan idan baikai zuciyarsa nesa ba kila a yanda yakeji zai iya kashe salmar kowama ya huta room dinsa yashiga yadade yana tunani kamin nan wani nannauyan bacci yasace shi,
Rukayya dabatamasan meyake faruwaba tana zaune Class dinsu hankalinta kwance har aka tashi daga skull suka fice warsu gida itada Sajeeda .
Haka Rayuwarsu ta kasance har akayi Holiday tun ranar kuma bata sake ganin faruuq ba duk da tanaso ta daina tunanisa Dan bataga dalilin da yasa take sha,awar ganisaba a yanxu Dan tasan ba shiri sukeyi ba itadashi amma meyasa nake muradin faninsa oho tabaiwa kanta amsa kawai mantawa zanyi dashi Dan ba abinda ke tsakanin ni dashi haka kurun tunanina yarasa Wanda zai tunano sai wanda na tsana bayan anyi musu Hutu bada dadewa ba Daddy ya shirya musu tafiya Raba itada Sajeeda Dan acan zasuyi hutunsu hakan yayiwa Rukayya dadi ba kadanba koba komai zataga mamanta da Baaba dakuma Abbanta kasa boye murnarta tayi har Ranarda suka daga dayake su biyu kadai Zasu Daddy sarkin tsaraba a kullun baya gajiya da lalurori haka ya shirya musu tsaraba mai tarin yawa yatafi dasu domin yakaisu gida murna gurin Baaba kamar me taga jikarta ta kara girma gwanin sha,awa nan nan kawai tayi da ita Daddy kuwa yasha Addu,a kamar me Dan kuwa malan Sa,idu harda kwala yayi gurin iya Daddy godiya bakomai ai yiwa Kaine Rukayya tamkar 'yace a gareni nadauketa tamkar Sajeeda basuda wani banbanci a gurina Salame kam saboda kunya kasa magana tayi saidai murmushi bataso ta zake da yawa saboda Rukayya yar farice a gurin ta ,kwanan Daddy daya ya juya zuwa sokoto Dan aikinsa yakuma gaya musu ranarda zaidawo daukar su ba laifi yasha Tsaraba shima irin tasu ta mutanen k'auye shike da mutunta juna aka Rabu ana murna da farin ciki saidai duk da Zamansu a can din bai hanata tunanisaba har mamakin kanta takeyi lol Ruky an kamu da son uncle F=== Sajeeda takanyi mata kirafi akan yawan tunane tunane but sai kawai tace mata bafa tunani komai nakeyiba kawai dai INA kewar mummy da Daddy ne haka zata kyaleta but itama kanta tasan akwai abinda yake damun sister dinta batason fada ne kawai kuma zata kyaleta inayi tsami saji cewar Sajeeda

Umar kam tun ranarda yakoma gida yahadu da baccin rai yayi alkawarin barin kasar kozai samu sawaba ga jiya sai shirye _shiryen aure sukeyi Alhaji Basheer kawai take jira aje asaka rana a biyawa diyan ta sadakinsu Dan kam harta hada lefe nagani na fada duk ta zauce ji takeyi kamar ma ace gobene saurin auren Dan kuwa Hajiyarsu Salma asiri taketa banka musu itada danta ganin ko anyi ma Umar baya tasiri shiyasa suka maida kambun yakinsu zuwa ga Hajiyarsa ba laifi a gurin su Dan kwalliya ta biya kudin, sabulu hakonsu na gamda cinma Ruwa. Shikan Faruuq BISA yayi ta zuwa umara Dan acewarsa gara yakaiwa Allah kukansa kozai rage zafin ra dadin da zuciyarsa ke masa bada dadewaba ta fito bai fadawa kowaba sai randa zashi yayi musu sallama ya fice yayansa ya ajiyesa airport jirginsu yadaga sai kasa mai tsarki haka ya wanzu ba dare ba rana yana Addu,ar samun Rukayya Allah yasa ita alkhairi CE agaresa Alhmdllh addu,arsa ta karbu Dan kuwa yanxu Rukayya batada wani aiki saina tunanin sa kwata2 wan nan hutun a Raba bata wani yi enjoying dinsaba.


Maman Ussee=


=N 'YAR BAIWAH =N 5 7


~Maman~ ~Usseey~=


& Masha Allah Abu yayi kyau Domin An Daura aure Lami lafiya komai yatafi yanda yadace Yayinda Yan Daurin Aure suka nufo Hanyar Dawowa Sokoto Dan Can Ne Bidirin Yake Dayake Daurin Auren. Ne kawai Malam Sa'eed yace azo Gida ayi sauran komai Yabarwa Baban Amarya wato Shugaban Biki Daddy=
Wanda Yayi Alfahari da Hakan,, da Baban Rukayya yamasa.

" A bangaren Amarya kuwa tun Safe aketa shagalin Biki Amarya wanka ,, kawai take Dauka na mutunci Ba karya kam Sosai tayi kyau misalin . Karfe Hudu aka Fara walima Wanda Akayi Nasiha mai Ratsa jiki game da zaman Aure da yanda Hakkin miji yake akan matarsa. sosai Abin ya ratsa Jama,a Sai gab da magrib Aka yi Addu,a Allah yabawa Amarya zaman lafeeya da Samun zuri,a Dayyaba ,,Aka watse tun Kare walima Rukayya da Sajeeda keta Kukan Rabuwa Duk Wanda yagansu sai sun Basa tausayi Saida . mummy Ta nuna Baccin Ranta kamin Suka Hakura Dan Dolene su Rabu dama Sabo akewa kuka.


& Uwargida kam tun da FAROUQ yayi Fushi ya tafi taketa jin Badadi a Ranta,, Haka yaturo mata Sakon cewa Zai turo Ta Dauki abinda Takeso Yau zasu Tare a Sabon Gidansa Komai ya zuba mata aciki kawai Dai ta tattare abinda takeso Dan By 3:pm Zai turo adauketa ,, Tana kare karanta massege din Ta Fara tattara yan komatsan ta Zuciyarta sai Zafi take mata . Haka Yan uwanta da Danginta suka Zauna tare da Ita bamai Bata shawaran Kirki Duk zuga. Ta kawai Akeyi Wanda Hakan kara Ingiza Zuciyarta kawai yakeyi . Maman ta batazo ba Acewarta sai An gama Biki Zata Zo da Sabon Tuggu Dan Tasamu labarin cewa Salma Nada Juna biyu yanxu sun samu Gidin zama . A gidan Umar Farouq . (ohhh kuji min Mata 'yarta fa ke Auren Farouq din Amma ita Dukiyarsa,, CE kawai A Ranta Allah kashiryar Damu kasa mufi K'arfin Zukatan mu Ameen) Haka suka wuni Har Gurin 3 din kamin Yaturo aka Dauki Salma da Sauran K'awayenta Da yan Uwanta yan Kore masu Rakiya .
& Ba,a Zarce dasu Ko,ina ba Sai Gidan Farouq Dake Unguwar Guiwa lowcost ,,, Gidane Babba nagani Nafada An kawata gidan Ba karya indan Nace Zan Iya Fayyace muku Yanda tsarin Gidan yake Yazama ,, Waist of Time . = Lol . part Biyu ne A gidan sai Garden da Kuma Dan karamin swimming pool ,, da Filn Wasan Ball kusan Irin Ukku Basket Bolly da Kuma Hand Ball. Sai shuke shuke da kuma parking Space . Wanda yake da isowarka ,, Gidan Mutuwar Zaune Salma tayi ta sake Baki tanata Kallon kayyatuwar ,, gidan A Ranta take cewa Ohh All This is myn Wata ,, Zuciya kuma take cewa Ku biyu fah mtseww..... Taja Tsaki Wallahi dai Kishiya batayiba Acid CE Hava ,muna Zaune kalau a Hadani da ,, yar bakin Ciki zaki Ganene inkin Shigo Gidan Wata kawartace tadan bugetah tace .
 ke Ki fito Mana kin wani hakince a Cikin mota ni na matsu naga ,, ya cikin gidan yake Dan gaskiya Salma ur lucky kinga yanda gidan ya Hadu kuwa Sakowa tayi ta Nufi Dayan part din taga A Rubuta kamar Haka  This Belongs' to RUKAYYAH!!! A Ranta Tace ,,, Ohh Farouq Dan Rainin Hankali ne jifa Ko gidan ban saniba gashi ,, Duk Nama Rasa INA ne Nawa part din Mai gadine ya iso Gun da Take ya ,, Rusuna yace Hajiya ,, Ga makulin Part dinki gaya can Karba tayi bayabo ba Fallasa ta nufi Dayan Part Din sauran Jama,artah suka Rufa mata Baya ,,Ta bude ta Shiga  Ni ma dai Sauri nakeyi na Shiga na ganewa Idona Menene Acikin Gidan Dan gaskiya Ba karya fah ,, Wow na Furta A Hankali. Dan A gaskiya ,, Ba,a cewa komai wani Makeken Falone. Na Hango D'auke da Wasu Kayyatattun Kujeru komai Na Falon Black ne da White ,, Kai harma pent din Jikin Bango ,,, Dan Kara min koridor nagani Wanda Zai sadaka da Store da kuma Kitchen daga ka zagaya kuma Ga Dinning nan sai kuma wata yar Hanya ,, Wanda Zata sadaka da can Cikin gidan Dayan bangaren kuma Dakuna ne kusan ,, Guda Hudu a Jere sai Daya kuma A ,, Gefen Wadan nan da Alama Guest Room ne wato D'akin Bak'i . Sai kuma Wata Hanya Daga gefe Can na nufa ,, Wani Katon Falon nagani A gurin ,, Shikuma an masa Kwaliyar Pink komai pink da White color Fantastic na Fada ,, Tare da Zuba Idanuwa na Dan nabasu Abincinsu Shikuma Kofa Biyu ne nagani da Alama Dakin Mai Gidan ne Wata Hanya nabi naga kuma ta sadani da Dinning anan Nan ,, Ne Nafahimci Falon Maigidane Dana Salma Sai aka Sanya Kitchen a Tsakiyarsu dakuma Dinning Area ,, dawowa nayi nashiga Kifarda Naga su Salma sun Bude sun Shiga ,,,Zaune nayi Dana Hango wasu Mayyun Leader sit, Kut=I mai kud'i ya More Wan nan Dukiya haka da aka zuba a Gidan nan Kuryan Room din wani Gadone Hadararre mai Rumfa!
& Suna Tafe ina binsu a Baya ,, Kowane Room sanda muka Shiga ba karya gaskiya Dakin , mai gidane kawai banmu shigaba Dan a kulle yake Falon suka Dawo nima nasamu Gurin zama ,,, sai Kallonsu nikeyi yayinda my Usseey. Yaga Ana shan Juice kala2 yaje yadauko Daya yafara sha banma lura ba sai Ganin shi nayi yanata zukar lemu ,,, Zare Ido nayi nace Kai =D Rufa mana Asiri da shegen kwadayi gobe ma Bazan taho tare dakaiba Dan kar ka k'ara Kwasamin = lol.

& Yan Daurin Aure sun ,iso lafeeya yayinda Ango da Abokansa basu Zarce ko,Inaba sai sabon Gidan FAROUQ . Dan anan zasuyi liyafarsu . yana isowa Kota kan Salma baibiba kawai Wuce ta yayi ya Shiga Dakin sa,, kawayenta sai tsokanar sa sukeyi suna Ango kasha Kamshi Murmushi kawai yamusu ya fice abinsa Salma ,,ta bisa a Baya yana Shiga itama ta Shigo Zatayi Magana yadakatar da ita da Hannu Durkushewa tayi ,,tafara mai kuka Abinda Bayaso kenan Dole ya Rarrasheta ,, Harsuka shirya kunsandai Mata da Miji sai Allah ,, Haka ta Daure suka Gaggaisa da fans Dinsa yayinda aka Bata kyata kala2 Kawayenta ke karba suna godiya,, yayinda Bakin Farouq yaki Rufuwa Har Gab da magrib kamin suka watse Dan suje akai Ango gurin Wankisa =.

& Shirye2 aka farayi na zuwa wajen Wanke Amarya ,, Wanda ba,a Bata lokaciba ,,, Aka kaita bayan an karene Aka dawo da ita gurin mummy kuzo kuga. Kuka anxo Rokon gafara Haka mummy ma sanda tayi kwallah saboda sabo ,, kakar Amarya sai Baaba sai tsokanar Rukayyah take . haka taje Gurin Daddy dakyar ta Rabu dashi Dan Saida yamata wayo ta Hakura haka suka nufi ,,Gidansu FAROUQ aka damka Amanar Rukayyah a Hannun Hajiyarsa sosai tayaba takuma karba ta sanya Alkhairi Kamin aka wuce da ita Zuwa Gidanta Wato Gidan Ango FAROUQ .

" Salma najin tsayuwar motar kawo Amarya Hankalinta ya matukar tashi ,,Jitakeyi wani. Abu na taso mata kamar Zata mutu . haka ta Daure ta Gimtse har aka Shigo da Rukayyah Lullebe da Mayafi ,, Aka Damkata Hannun Uwargida Sarautar mata Dakyar Salma tayi control din kanta Dan,, jinsu kawai takeyi haka suka karaci Surutunsu ,, suka Ja Rukayyah Zuwa part dinta Wanda komai Dayane Dana Salma saidai ita Kalar na Rukayyah Pupplene da White ba laifi Daddy yakashe mata Kunya Dan itama an zuba mata dukiya wane Diyar wani Shahararren mai Kudi ,, Rukayyah Bata taba Tunanin Zata kasance Haka A Rayuwarta. Ba wan nan wata BAIWAH ce daga Allah Da Addu,ah a Bakinta tashiga har kuryan Dakin ta suka ajeta Saman Bed. Yayinda kowa yaba tsarin gidanta yakeyi wasu kuma Cewa sukeyi Rukayyatu tayi dace mudai Fatanmu Allah yabada Zaman . lafeeya da Zuri,ah Mai Albarka.


~Maman~ ~Usseey~=


 Special Thanks to you my Beloved oneces ,,Bazan taba mantawa dakuba Nagode Sosai da Kwarin Guiwarku a gareni 

& Maman Khairy Allah ya Raya mana Ummul-khair.=
& Ummu -Alkhairi B. B=
&Bintu Tijjani Zaifada =

& And my Lovely Aunt Sister Zainab Mai Kano Allah yakawo yan Biyu Ameen=.
Thanks much more Luv u all my Fans Lodi-Lodi=.


=N 'YAR BAIWAH =N5 8

~Maman~ ~Usseey~=

& Gidan Amarya ya Rage daga Sajeeda sai Afra da Afnan da wasu Fans Dinsu mutun Biyu ne su Biyar kenan. Yayinda Rukayyah ke lullub'e a Mayafi Zuciyarta sai duka takeyi ,, Wai yau itace a gidan Aure gidan Umar Farouq abu kamar Almara .
"Sajeeda tace wai yaushe ne Zasu kawo wan nan Angon ne 10:30 fah Afra tace kin San sai anmasa Huduba kuma kinga Sai sun tsaya Dan Kinga dakwai masu so Su yi masa Naseeha Dan Rike macce Biyu sai jarumi Sajeeda tayi Dariya tace Tab kenan . Yayanku Jarumi ne ko Afnan tace sosaima ,, kinga zai nunawa Sistern ki Jarumta irin tasa Aisha tace kai kudaina Tsoratata mana kufa zolayace daku Safeena tace No way Ai dolema ya Hakura saboda Sabon Shiga CE Sajeeda tace Ohhh kukan Allah yashiryaku kunga kamar naji Tsayuwar mota may be gasu nan sunzo Suka kara feshe ko,ina da Turare kamin suka sami Gu suka zauna Rukayya Hawayene kawai ke zuba a Idan nuwanta Dan yanxu ne yakara tsinkewa lol=.

& Bayan an kare wankin Ango Gidansu aka nufa Dan Ayi masa,, Hudu ba sosai Alhaji Basheer ya Masa Nasiha mai Shiga jiki yayi Adalci a Tsakanin su karya nuna musu banbanci Kuma ya Rike su Amana,, Ya tsaya tsakani da Allah karya fifita wata akan wata ya kwatanta Adalci . Haka aka kaisa gurin Hajiyarsa Itama dai Fadan tamasa na a Rike Aman da Adalci ,, daga nan aka Daukeshi zuwa gidansa Abokansa sai tsokanar sa sukeyi ,, Shikuma sai Dariya kawai yakeyi yana Wani jin Dadi har suka iso Part din Salma suka nufa dashi ,, Suna Zaune itada Kawayenta daketa zugata da Sallama suka ,, Shigo aka tsaya Akayi jawabin na Salma ta zauna lfy da yar uwarta Kuma Farouq ya kwatanta Adalci ,, Akayi Addu,a Kamin aka Baiwa Salma Kayanta na tande tande ,, Ba yabo ba fallasa tayi masa saida Safe shima ya mata ya lura sosai Bata cikin Kwanciyar Hankali,, amma bayanda ya iya haka Suka Ja Farouq zuwa part din Gimbiya Amarya .

& Da Sallama suka Shiga yayinda wani Daddad'an kamshi mai sanyaya zuciya ya doki Hancinsu da Sanyi mai Dadi ya Ratsa su har Kuryan Daki inda Rukayyah take suka kai Farouq

Please Login or Register in order to submit comment