Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazata iya boyeshi ba,duk sai suka tayata darawa suna tuna rigima irin tata
"Komai zanyi inayinsa ne saboda rayuwarku,na godewa Allah da ya nuna min hadin kan ahalina gabanin mutuwata".



Haidar na murmushi yace
"Bamu da abinda zamu saka miki dashi hajjanmu sai fatan gamawa da duniya lafiya,kije ki tadda mijinki cikin aljanna madaukakiya kuci gaba da rayuwa"addu'an fatan alkhairi sosai ya dinga jera mata zahra na amsawa da amin,zuciyar hajjan fari qal kamar tasu ta fita tabar dakin,bayan ta tunawa zahran ta shirya ta fito haidar din ya kaita a sake tabbatar da lafiyarta,ta fita tana sake godewa Allah kan tarin baiwa da ni'imomi da yayi mata.


*_TAMMAT BI HAMDILLAH_*


_Kada ki sake,kada ki bari damuwar wani d'a namiji ta hanaki sukuni,kada ki bari damuwar wani saurayi daya yaudareki tasa ki tsaida taki rayuwar cak,bayan shi yana can yana tashi rayuwar_

_rabu dashi,manta dashi,nuna masa bashi da muhimmanci cikin rayuwarki,kamar yadda ya nunawa duniya hakan a kanki_

_kada ki manta,idan dubu sun qika....dubu ke sonka suke kuma jiranka_

_sau tari abinda kake so saiya zamana ba shine alkhairi a tattare dakai ba,abinda kake gudu kuma shine alkhairi a tare dakai ba tare daka sani ba_

_zama mai hankali ta hanyar zurfafa tunaninka,kada ka yarda ka yankewa wani dan adam hukunci ba tare daka mu'amalanceshi ba,kada ka yarda ya fadi halin wane bayan baka zauna dashi zama na gaske ba_

_koda yaushe ka zama mai kyautata zatonka ga mutane,sai gobenka tayi kyau_

_MAZA kuji tsoron Allah,nasan bazan aureki ba,to bazan soma tsayawa zuwa zance wajenki ba,kona bata lokaci kan layin waya ina qona miki kati ko ina qona nawa katin ba,ina bata miki lokaci,ina dauke hankalinki daga kula maza 'yan gaske masu niyyar aurenki ba,KADA KU MANTA KAI YAYA NE,WATARAN KUMA UBA NE!,ZAKA HAIFA KO A HAIFA MAKA!,AKWAI KUMA HISABI,ALLAH BAYA QYAKE HAQQIN WANI AKAN WANI TUN NAN GIDAN DUNIYA_


*_muna miqa saqon godiya da jinjina a gareku masoya kuma makaranta litattafan zafafa,wadanda a kullum basa gajiya da sanya kudadensu su siya rubutunmu,ubangiji yabar qauna_*


*_muna neman afuwan wanda muka batawa,ko wanda muka yiwa ba dai dai ba,ko labarinmu ya batawa,ko bai masa yadda yaso ya kasance ba,dukkanmu ajizai ne,duk inda ajizi yake kuwa saiya nuna ajizancinsa_*🙏🏽


*_kurakuran dake cikin rubutunmu muna fata Allah ya yafe mana,ya bamu ladan dake ciki_*

*_ubangijin ya sadamu a rubutu na gaba,ya bamu aron rai da lafiya,yaci gaba da riqo da hannyenmu,ya kuma bamu damar rubuta abinda al'ummar annabi muhammadu zasu amfana dashi_*

*SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASHHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA*🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment