Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koda baki sani ba kai tsaye,kuna karbar wayarta,kuna kuma shiga inbox nata,idan akayi katari kika karanta to kamar na rage wani nauyi dake zuciyata,na kuma isar da saqona,don yawancin lokuta tana gayamin yadda kike nuna zallar mamaki idan kikaci karo da daya daga cikin saqonnin dana tura matan.....bazan boye miki ba....nayi missing zahra'u,na kuma shiga tashin hankali na haqiqa sanda na rasata,har nakejin ma kamar bani bane....kamar zan zauce....na jima....na jima ina dorawa kaina alhakin mutuwarta,saboda ta rasu ne a sanda naje makaranta ganinta,da wani yammaci,na dawo daga gwambe,na tsaya ta wudil ganinta,saboda munyi waya tun ina hanya.


"Sanda na shiga makarantar na sameta shuru,kamar irin anyi hutu dalibai sun kokkoma gida,to amma nasan ana tsaka da zangon karatu ne,ba lokacin hutu bane,waya na daga na kirata da zummar bata mamaki,don batasan da zuwa na ba,na gaya mata inda nake tsaye,cike da zumudi da mamaki tace gata nan fitowa,saina maida wayar aljihuna ina duban inda nake tsayen,wajene mai yalwar bishiyoyi dogaye da kuma tarin ciyayi mai tsaho,tunda nake zuwan mata makarantar lokaci zuwa lokaci bamu taba tsaiwa a wajen ba sai ranar,ina cikin karantar yanayin wajen naga bullowarta ta gefena,kamar kowanne lokaci cikin hijabinta,tana tafe tana murmushin ganina,saina bata dukka hankalina harta qaraso.....
"Me ya faru yau naga makarantar taku yau so silent" tambayar dana fara mata kenan
"Wallahi tun jiya da aka samu fitowar macizai ne,sai kowa ya tsorata ya lazimci zaman daki,don yau ko lactures ma ba'ayi ba" kai na jinjina sannan nace
"Amma da kin gayamin da bazan shigo ba bare na fiddoki daga daki" dariya tayi
"To na godewa Allah da ban gaya maka ba bare ka haramta min ganin fuskarka....komai muqaddarine ai daga ubangiji,koda ina daki duk abinda ya qaddara zai sameni saiya samenin"basai na gaya miki sauran abinda tace min ko nace mata ba...saboda tsaro ba don tsoro ba" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi tana girgiza kanta,idanunta a kanshi,ajiyar numfashi yayi
"Yau soyayya ta sani dogon magana.....a taimakamin da ruwa" hannunta ta sanya ta bude masa gorar ruwan sannan ta ajjiye masa,ya dauka a nutse ya soma sha,yana sha yana ajewa yashaqi numfashi har ya gama,ya aje robar yana sauke numfashi tsahon minti daya sannan ya dora.


"Bari na samo maka abun sha a wani kanti nan" ta fada ta soma takawa,da hanzari na tsaidata
"A'ah....ni ganinki kawai nazoyi,bana buqatar ci ko shan komai" kafada ta maqale
"Ban yarda ba....saboda nima irin karamcin nan naka nakeso na koya,saboda haka saina samu ladan baqona" daga haka ta soma takawa ta cikin ciyayin nan tayi gaba,a cikin zuciyata inason tsaidata amma kamar wanda aka daurewa baki na kasa,inasin ince kada tabi ta wannan ciyayin amma na kasa fada mata,inason ince mata ta tsaya na rakata amma dukka kamar wanda aka daurewa baki duk na kasa fada,ashe ajali ne,ajali ne ya kirata,don batayi wani nisa da idanuna ba naga gilmawar wani abu ta bayanta,na fuskanci maciji ne,idan nayi magana kuma zata iya rudewa,don haka na fara takawa da wani irin hanzari da zafin nama,dai dai sanda ta waiwayo tana kallona,sai fuskarta ta nuna mamakin ganina ina tahowa inda take da mugun gudu,bansan ya akayi ba saijin ihunta nayi ta durqushe cikin ciyayin.


Sanda na isa na sameta riqe da qafarta,ta hada gumi sharkaf tana juye juye,dana dauke hannunta saiga inda macijin ya sareta nan,na bata taimakon daya dace,na riqeta zuwa asibitinsu na cikin makaranta,saidai abun haushin abun takaici basu da allurar kashe gubarsa,raina ya baci sosai,amma ban tsaya biye musu ba,saboda kada bata lokaci ya jawo asarar ran da naketa gudu,na sanyata a mota kawai muka wuto zuwa kano.


"Irin gudun dana dinga tsalawa ni kaina nasan Allah ne kawai yayi motar ba itace ajalinmu ba nida ita gaba daya,tana cure waje daya set din gaba taba murqususun ciwo da azabar dafin daya zuba matan,hankalina rabi ga titi rabi a kanta,qarin abun haushin asibiti manya guda biyu mukaje suma basu da allurar a dai dai lokacin ta qare,sanda muka dauki hanya zuwa asibitin mu a sannan ta kalleni,launin idanunta yana canzawa
"Kayi haquri ya haidar....kayi haquri,kuma naga ranka ya baci,duk abinda Allah ya shiryawa bawa bai isa ya tsallake mishi ba" saita maida kanta ta kwantar,kalamanta suka dagan hankali,na tsaya gefan hanya sanda naga yanayin jikinta ya saki gaba daya.


Nasan a sannan ta mutu don zuciyata tana gaya min haka.....amma idanuna a rufe suke,saina tashi motata da mugun gudun da yafi na dazu na nufi asibitin,saidai abinda nake tsoro dai shi aka gayamin,zahra ta rasu,dafin yaci jikinta yakai inda ba'a so yakai......"saiya tsaya da bata labarin yana duban yadda hawaye ke zuba a idanunta,a wancan lokacin sam batasan yadda mutuwar zahra ta kasance ba,kawai dai tasan saran maciji ne,hakanan tana ganin haidar yaqi daukan qaddara ne kawai,amma data kwatanta mutuwar masoyi ko aboki gaban idanun abokinsa sai taga abun ba mai sauqi bane,dole ya shiga irin yanayin daya shiga din,kasa jurewa tayi,sai tayi qasa da kanta kuka na kubce mata.
23/10/2021, 08:50 - 👍🏻👍🏻: 42


Murmushi ya saki,sannan ya taso daga inda yake zaune,yaja kujera dab da ita ya zauna har gwiwarsa na gogar tata,hannunsa ya sanya ya dago fuskarta gaba daya,saiya girgiza mata kai alamun
"A'ah"yatsansa guda daya ya sanya ya dinga dauke mata hawayen,murmushi kwance saman fuskarsa,har sai daya goge duk wani hawaye da yayi saura,saiya hada goshinsa da nata suna musayar numfashi,qamshin turarensu na gauraya da juna
"A wancan lokacin kinyi fushi....kin nuna kishi saboda ganina da wata balarabiya.....wadda nake ganinta da muni sosai idan na hada da kyakkyawar fusakarki,da kuma yadda zuciyata ta rayu da sonki......ta samu dukka fara'ata ne da kulawa saboda yabonki da tazomin dashi,ta shaidamin tunda taga shigowarmu taji mun burgeta.....tana son qawance dake,dalilin da yasa ta biyoni kenan har kika ganmu tare....saidai kuma a yanzun gashi kina kuka saboda wata da na taba so na baki labarin mutuwarta...me yasa bakiyi kishin xahra ba?" Ta rasa amsar da zata bashi,amma dole duk me imani yaji a yadda zahra ta rasun ya tabashi,ta riga data wuce zahra ba zata taba dawowa ba,kishi da ita tamkar abun nan da hausawa ke kira da ihu bayan hari ne.


Murmushi ya saka yana cewa
"Na fahimta....amma har yau kinsan ban samu makwafin zahra ba?" Cikin mamaki ta zare fuskarta daga nashi tana duban idanunsa,saiya dage mata dukka girarsa
"Eh....ban sake samun wadda tacemin ALIYYU HAIDAR INA SONKA BA,ban sani ba ko baqinjini gareni?" Dariya sosai ya bata,yanayin yadda yayi maganar ma abun dariya ne,sai tasa hannu ta toshe bakinta,yayin daya harde hannayensa a qirji yana qare mata kallo,dariyarta kadai ta sanyashi farinciki shima,gami da saukar masa da nutsuwa
"Aikam saidai idan har shin haidar din ne baiso a gaya masa ba,a iya sanina akwai daruruwa ko ince dubban mata dake ta dakon randa xai basu dama su furta wannan kalma a gareshi....." Tararta yayi ta hanyar watsa hannayensa,kamar zai saki kuka yace
"Ni dukkansu ban gansu ba,bansan da zamansu ba,zahran hajja kawai na sani,kuma ita kadai nake jira da dakon randa zata gaya min hakan....." Itama bata barshi ya qarashe ba yaji saukar kalaman kamar ruwan sama saman zuciyarsa
"Ya haidar kadai nakeso....shi nake qauna har abada" idanunsa ya ware cikin mamaki yana dubanta
"Say it again please"🙏🏽,duk kunya saita cikata,ta maida kanta wani sashen tana murmushi,sai ganinshi tayi ya koma inda ta maida kan nata
"Please....inason na sake ji" wani qwarin gwiwa ya bata daga cikin idanunshi,saita kalleshi sosai
"Ina son ya haidar,ina sonka...ina sonka" gaba daya ya tattareta cikin jikinsa,ya manta ma suna waje ne,sai data ankarar dashi,ta tabbatar da a 9ja suke da tuni sun tara 'yan kallo,da qyar yayi controlling kansa,ya komqa ya zauna dab da ita,muryarsa cike da wani irin softness ya kamo hannunta ya riqe tsam cikin nasa sannan yace
"Hakan yana nufin....kin mallakamin rayuwarki?,kin zama ni na zama ke?,zakici gaba kuma da kasancewa tawa har abada,munyi amanna wa juna zamu rayu da juna duk rintsi duk kin yarda da wannan?" A kunyace kan irin salon kalaman dake fita daga bakin yayan nata,da salon kallon da yake mata ta gyada masa kai,saiya girgiza kai
"Banison body language.....pls ki gayamin da bakinki"
"Amince.....na amince ya haidar" lightly yayi kissing saman hannunta,ya rasa da wacce kalma zai sake magana,kawai sai yaci gaba da riqon hannunta cikin nashi yana kallon kayarsa kamar za'a qwaceta,har sai da tayi waving hannunta saman fuskarsa
"Bansan me zance miki game dani ba,abu daya zuwa biyu kawai bakina zai iya gaya miki,da kanki zaki dinga bawa kanki amsar irin mijin da kikayi katari dashi,sannan ina miki albishir din cewa......zaki shiga sahun matan da sukafi dukkan mata sa'ar miji a duniya" daga haka ya miqe yana riqe da hannunta,itama saita miqe suka soma takawa cike da wani irin xallar farinciki dake yawo dasu a duniyarsu.


Kwan daya tak suka qara suka fara shirin dawowa,ya bata dama ta siya dukkan abinda take da buqata,siyayya me yawa da batasan me za'ayi dasu ba.


Kamar yadda suka tafi tare haka suka dawo,sun tadda 'yan Tarbarsu danqam suna jiransu,family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,babu wani bambanci da xaka gani tsakaninsu.


Tun a airphort din ta ankare da yadda 'yan gidan nasu keta gulmarta ita da ya zakin,saboda duk inda yayi yana maqale da abarsa,baya jin kunya ko nauyi sam,motsi kadan nata idanunsa da hankalinsa yana kanta.


Da zasu tafin bai bar kowa ya shiga tashi motar ba,zahran ta rasa dalili amma yayi fuska,ta sani dukkansu shakkarsa suke,saboda haka ba wadda ta iya tunkararsa,sai hafsat data rage bata samu waje ba,tayita zagaye tanason tace ya dauketa,amma ta kasa,sai zahran ce ta dubeshi
"Please ya haidar....maman khairat ce bata samu waje ba" ta fada cikin marairaicewa,wani kallo ya watsawa hafsat din ta window,ba shiri ta fara qoqarin juyawa tabar wajen,amma sai zahran ta yaficeta ganin baice komai ba.


Bai tanka musu ba har aka fara tafiya,basuyi nisa da airport din ba ya bawa driver umarnin ya tsaya,saiya fidda kudi tana ajema hafsat din fuska a tsuke
"Sauka ki tari napep ki hau....." Kallonshi duka suyi cikin mamaki,saiya hade rai tsam,zahra ta dubeshi a shagwabe
"Yayaaaaa"
"Shshshshhh...ba gida muka nufa ba,so take muyita yawo da ita?" Mamaki ya kamata,toba gida suka nufa ba ina suka nufa kenan?,tana ji tana gani hafsat din ta sauka ta tari napep su kuma sukaja motarsu suka wuce,sai tayi kicin kicin ita ala dole fushi take dashi,bai tankata ba,data kalli fuskarsa ma sai taga walwalarsa yake abinsa.


Tanata zuba ido tana ganin yadda suka shiga unguwar,mamakin wajen wanda zasuje take,daga dawowarsu daga doguwar tafiya irin wannan.


Bata samu amsar tambayarta ba har sai da suka tsaya qofar gidan,mai gadin madaidaicin gate din ya bude musu suka shige madaidaiciyar harabar gidan da zata iya cin motoci uku zuwa hudu ba tare da sun takura ba,da kansa ya fita,ya zagaya inda take zaune ya bude mata motar,fuskarsa dauke da murmushi yace
"Bismillah" dubansa tayi tana maqale kafada tare d zumbura baki,Ranqwafowa yayi saman kanta yana murmushi
"Beautiful.....wannan bakin naki...." Sai ya saka yatsunsa biyu ya kama labban nata ba tare daya qarasa fadar abinda ke bakinsa ba,janye bakin tayi da sauri saboda yawon daya fara da yatsunsa saman labban nata
"Ranki ya dade.....ina miki barka da shigowa gidan aurenki" ya fada murya can qasa kamar meyin rada,da sauri ta daga ido tana kallonshi
"Ya haidar....kada kayi haka,shi yasa ka hana kowa shiga motar mu....hajja fa" yatsansa ya dora saman lips dinsa yace
"Shshsshhhhh....banason kiran sunan kowa ba,bansan kowa ba sai ke,nan din duniyarmu ce ni dake,kema kuma zaki manta da kowa da komai soon" ba tare data shirya ko ta ankara ba taji gaba daya ya sunkuceta,ta Maqaleshi sosai,saboda ji da take kamar zata fadi
"Karki damu,a hannun soja kike" ya fada yana murmushi,saita maida masa martani itama ta maida kanta qirjinsa ta kwantar,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri,sai ta daga kanta cikin mamaki ta dubeshi,murmushi ya sake sakar mata
"My heart beat ko?,kada ki damu,sonki ne da zumudin kasancewa tare dake" wani farinciki taji yana ratsa zuciyarta,tanajin alfahari da kasancewarsa mijinta yana mamaye ruhinta,qaunar hajja ta sake fadada a ranta,tabbas ita din ba qaramar masoyiya bace,me yasa kaf cikin jikoki da 'ya'yan 'yan uwa bata zabi kowa ba sai ita?,ita kadai ta dauka ta mallakawa mutum mai tsada da daraja irin aliyyu?,a hankali a hankali take fuskantar komai,kamar yadda ta taba gaya mata cewa zata gane,zata fahimci gatan datayi mata,bata da bakin gode mata,bata kuma da abinda zatace mata face addu'ar gamawarta da duniya lafiya.


Tana daga hannunsa take qarewa gidan kallo tun daga hanya har shigarsu falo,ba'a cika masa kayan alatu na qarya da barnar kudi ba,amma ya qayatar matuqa ya kuma bada ma'ana,parlour,two bedrooms with toilets a qasa,dining area,kitchen,store da wani toilet din a falo,saman benan gidan ma falo ne da bedroom biyu,kowanne shima da toilet,gaban kowanne daki akwai qawataccen corridor da zai baka damar ganin gaba da bayan gidan,akwai dakuna daga bayan ainihin ginin gidan guda biyu masu falo daya da bandaki,sai wajen ajiye motoci matsakaici ha matsakaiciyar haraba don shan iska.


Dubansa tayi sanda taga yana aje kayansu a dakin daya direta
"Ina nawa bedroom din?" Wani kallo ya mata mai kwantar da zuciyar masoyi,saidai fuskarsa a dan hade take,saiya zare rigar shaddar jikinsa,jinsa yake gaba daya a takure,don bazai iya tuna rabonshi da saka manyan kaya ba,banda wannan tafiyar da hajja ta tubure kan lallai bashi ba saka fingilallu kuma damammun kayan yahudu,bayan garin ma'aiki zashi.


Sai daya qaraso dab da ita ya dagata tsaye yana riqe da qugunta da hannu daya,daya hannun kuma yana warware rolling din doguwar rigar dake kanta
"Banason na raba komai da matata,nafison komai namu mu dinga sharing....bawai saboda babu wadata ko ikon siya ba,a'ah.....inason mu samu kusanci qauna da shaquwa matabbaciya.....irin wadda a tarihin masoya kaf na duniya babu masoyan da suka samu shaquwa da fahimtar juna irin tamu" yakai qarshen zancan sanda yake fidda mata doguwar rigar jikinta,saiya zamana daga ita sai under wear da vest,kaman maye haka ya bita da kallon qurilla,yadan ja baya kadan ta yadda zai samu damar kallonta da kyau,saiya miqa hannunsa i zuwa muhallin dako yaushe yake tsone masa idanu,ya kumayi tafiyar ruwa da nutsuwarsa,gocewa tayi tana dariya,a 'yar tarayyarsu ta qididdigaggun kwanaki,ta gama fuskantar shi din mutum ne da yake qaunarsu,suka kuma matuqar tafiya da hankalinsa,cikin zafin nama ya bita zai cafko yana cewa
"Oh....no,don Allah,kada muyi haka dake pleasessssssss" dai dai nan ya samu nasarar kamotan,ya mannata da jikinsa yana sauke qatuwar ajiyar zuciya,tsayin minti guda kafin yace
"Duk sanda nake tare dake,nakan manta wanene ni....ashe dai da gaske kedin aljannar duniyata ce,don Allah....ki rayu dani,mu mutu tare" martani ta maida masa ta hanyar rungumeshi tsam itama,yadda takeji cikin zuciyarta bazai misaltu ba,a hankali take rada masa wasu kalamai cikin kunnuwansa,kalaman da suka sake rura wutar dake ruruwa cikin zuciyarsa,suka kuma sanya ya daina gane komai,cikin qaramin lokaci suka qwace dukka hankali da nutsuwarsa,wanda hankalin da nutsuwar basu dawo masa ba,har sai data kaishi wata duniya ta daban,duniyar da kullum yake bege da muradin tabbata a cikinta matuqar da zahran ne.


Kwance saman qirjinsa wanda tuni bacci yayi awon gaba da ita,yayin da shi kuma yayi nisa cikin duniyar tunaninta,duk da tana tare dashi amma baya gajiya da tunaninta,bai taba zaton cewa qaunarta a zuciyarsa tayi nisa har haka ba,bai taba tunanin zuciyarsa zatayi nisa da zurfi cikin soyayya har kamar haka ba,ashe ubangiji sonshi yake da rahama daya sanya matsaloli tsakaninta da manemanta a baya,ashe tanadinsa ce ubangiji yayi masa,shi yasa yake rusa dukkan wata alaqarta da wani.


Qarar da wayarsa tayi ita ta katse masa tunaninsa,sai daya miqa hannu sosai sannan ya iya lalubota,saboda fadawa da tayi gefan gado,yana duba sunan yaga hajja ce,saiya sauke zahran yaja mata bargo ya lullube mata jikinta,ya zura qafafunsa qasan gadon sannan ya amsa wayar
"Wai ina kuka tsaya ne haidar?,baka duba lokacine?,kusan awa uku?,hafsa tace a hanya kuka sauketa,kuna ina ne?" Ya bude baki zaiyi magana sai yaji muryar tasa a dakushe take,don haka ya danyi gyaran murya
"Banason qaniya....ka bude baki kayimin magana"
"Muna gidanmu.....,gobe ko jibi zamu shigo mu sake yi muku ban gajiya"
"Gidanku?,wanne gidan naku"
"Gida na na gaida gida dubu" salati hajja ta saki tana sallallami,jin haka sai kawai ya datse wayar,yama kasheta gaba daya,ya tashi ya lalubo wayar zahran itama ya kasheta,ya hadasu gaba daya ya watsa cikin sif sannan ya wuce bandaki yana murmushi qasan ransa,yasan za'asha daru da rigima,tana can qila ta tadawa kowa hankali,shikam bazai dauki wannan gantali da aure da hajjan keta yi musu ba,ana masa wasa da hankali kamar zahran bata gama zama mallakinsa ba.


Kamar kuwa yadda yace din,kwanansu uku cikin gidan su kadai,babu abinda suke banda morewa amarcinsu,gami da sake dasawa juna sabo da shaquwa mai qarfi a tsakaninsu,cikin kwanakin zahran tayi mugun sabo da soyayyarsa,wadda ya dinga koyar da ita salo salo cikin dabara da tsabar qwarewa,sau tari takan saki baki tana tambayar kanta
"Da gaske ya haidar ne wanann?" Duk inda ta motsa yana maqale da ita,tare suke komai,girki gyaran gidan,wanke wanke,kai hatta ma wanka bai bari ta shiga ita daya,idan ko ta sake tayi ita kadai to tayi aikin banza,don sai ta sake,suna aikin yana tsokanarta,wasan guje guje sam batasan a inda ya koya ba,ya qware a sosai a tsokana,idan mamaki ya cikata ta saki baki da ido tana kallonsa,saiya hure mata ido da iskar bakinsa,wani lokacin kuma saiya hade bakinsu waje guda,yace bari ya rage mata mamakin da takeyi,saiya tsotsi lips dinta iya son ranshi sannan ya saketa,ya dubeta yace
"Kairukum kairukum li ahlihi,wa'ana kairukum li ahly. خيركم خيركم لآهله وانا خيركم لآهلي,annabi yace mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalansa,sai annabi da kansa yace nine mafi alkhairinku ga iyalina,yana taya iyalansa dukka ayyukan gida da kika sani....ni din waye da bazanyi koyi da wanda akayi duniya da lahira saboda shi ba?" Maganganunsa sunyi matuqar burgeta ba kadan ba,da gaske ne duk wanda ya hukunta wani mutum bisa wai wai ko kuma kallonsa da yake daga nesa ba tare da ya mu'amalanceshi ba,zai aikata babban kuskure,ashe kalar abinda umminta keta mata kwadayi kenan?,lallai uwa uwa ce,a kowanne hali makomar rayuwar ahalinta na nan cikin ranta,komai runtsi komai wuya,Aliyyu miji ne ɗaya da ɗaya,mai tarin nagartar da kaso mafi yawa daga cikin mazan yanzu suka rasa irinta
(Idan baki samu ba,saiki roqi Allah ya gyara miki dabi'ar naki mijin,ya zama me koyi da sunnar ma'aiki,idan kuma kin samu,saiki godewa Allah,kuma kada kiyi wasa da damarki,koki wofantar da baiwar da Allah yayi miki,idan budurwa ce ke....kina da sauran dama,ki fidda so ko burgewar dukkan wani qyale qyalen duniya daga ranki,ki tsayawa sallar dare,kiyita gayawa ubangiji da roqarsa ya zaba miki miji na gari,ba mai arziqi ko kyau ba,miji na gari ya wuce dukkan wani irin nau'in miji daya mallaki dukiya kyau mulki ko sarauta,miji na gari shine abu mafi tsada da daraja cikin rayuwar diya mace kaf!!!,da zarar kin dace dashi,tofa matar du wani mai mulki kudi kyau ko sarauta saidai ta biyoki a baya,matuqar itama ba katari tayi da irin naki mijin ba,ubangiji ya wadata qannenmu 'yan uwanmu da 'ya'yanmu da nagartattun maza🤲🏽🤲🏽🤲🏽,dama daukacin matan musulmi gaba daya).



Cikon kwana na hudun suka shirya wajen sha biyu saura suka nufi gida,duk a kunyace take,saboda batasan da wacce fuska zata kalli jama'ar gidan nasu ba,musamman mama da umminta,har gwara hajja an saba gauraya.


Sai da suka shiga kowanne sashe suka gaidasu sannan suka wuce sassan hajja,ga mamakinta ba wanda ya tsokanesu ko ya tada maganar,bare ya nuna yasan me ya faru,suna sallama sukaci karo da akwatuna masu azabar kyau blueblack guda takwas cas,kowacce shaqe da kaya a cikinta,wasu daga cikin 'yan uwan hajja ne suka gama kalla,da alama tafiya zasuyi ma,don har sun miqe.


Ango da amarya suka kirayi sunansu dashi,itadai ta murmusa ta gaidasu cikin kunya,yayin da aliyyu ya fuske cikin salon miskilancin nan nasa,sai zahran ta dinga satar kallonsa ta gefan ido,ya zama aliyyun nan sak dake basu tsoro cikin gidan,suna hada ido ya kashe mata idonsa daya,ya mata nuni data rage kallonsa,yana taba zuciyarsa,saita janye idanun nata tana sakin murmushi,dai dai nan suka hada ido da hajja wadda ta gama sallama da baqinta suka fice
"Sannunku marasa kunya feqaqqu....bari na fara da babban rasa kunya beran tankan.....kaga....hade girar gefe da gefanka ba zasu tsoratani ko su hanani cima mutunci ba.....da zaka daukemin yarinya ka kaita gidanka da kanka anyi biki ne?,ko ce maka akayi ma ciniki ya fada ne?,ance maka ta gama zama taka?,aro ne na shekara daya shine zaka zaqewa mutane....." Tana tsaka da bambaminta ya miqe yana cusa wayarsa aljihun wandonsa
"Don Allah ki hutama ranki.....don ciniki ya dade da fadawa....ki godewa Allah da bata shigo tana miki amai bama....idan sadakinne ya miki kadan ki fadi dame kikeso a qara yawanshi" baki ta kama tana zare ido,yana ganin haka yasan ya soma maganin rigimar hajjan,saiya juya ya fara takawa zai fita daga falon,ba tare daya ma kalli kayan lefen da yasan shi ya bayar aka hadashi ba,duk da yaga akwati daya ta dadu akwai,har zai fita saiya waiwayo,xahra nata danne dariyarta,hajja na tsaye inda take tana binsa da kallo
"Kuma ga amanar matata nan....quda idan ya tabata saina ciki tara"
"Haidar....aliyyu,dani kake maganar" ta fada cikin daga murya sanda yake ficewa daga falon,cikin ransa tana qyaqyacewa da dariyar abinda ya yiwa hajja.


Guri ta samu tana zama tana hade ranta tsaf,duk da cewa zallar farinciki ne qasan ranta me tarin yawa,already sun riga sun gama magana dasu abba babba kan abarsu tunda har sun hada kansu sunma wuce gidansu,shi dama taron biki al'adace kawai,tunda an qulla auren yadda musulunci yace,kuma jama'a sun shaida shikenan
"Gafara kika tsareni da ido mara kunya....ja'ira kamar ba kece nan kamar zaki mutu ba saboda mun aura miki shi,ashe lambu lambu kikayi,qiris kike jira" wannan karon dariyarta kubcewa tayi,sai kuma tayi saurin mazewa
"To tunda nafi qarfina aina haqura na zauna ko?,badai za'a ce banyi biyayya ba" murmushi ne ya qwacewa hajjan itama,tasa hannu tana daga kayan,don ita duk yadda ake kallon lefan bata samu gani ba saboda gajiyar tafiya da take tare da ita,sai yanzu tadan samu ta warware.


Zahra dai bata sanya hannu ba har hajjan ta gama kalla tana daga gefe a zaune,har saida hajjan da kanta tace ta matso ta gani mana,saita girgiza kai alamun a'ah,hakan saiya burge hajjan,duk da cewa an riga da an zama daya,amma har yau akwai abubuwan da zahran ke kunyar yinsu,ba kamar 'yammatan yanzun ba,da wata ma randa za'a kawo lefan tana gidansu,masu kawowa ko qofar gida basa gama kaiwa take tsallen albarka ta fito aci gaba da gani da ita,tana gani tana comment,tana hanawa a tattaba mata wasu abubuwan,Allah ya kyauta.



*_BAYAN KWANAKI BIYU_*


Walima gagaruma haidar din ya shirya a sabon gidan nasu,ranar walimar aka taho mata da akwatunan lefanta,saiya zamana kamar itace a madadin yinin biki,sosai aka ci aka sha,aka gabatar da wa'azi da nasihohi ga mata kan zamantakewar auratayya,wadda ta ratsa zukatan mata da dama,dangi sosai suka halatta,gidan yayi cikar kwari,saidai anyi taro lafiya an kuma watse lafiya.


Rayuwa suka ci gaba da gudanarwa mai cike da tsantsar soyayya da qauna ta kwatance,idanu ko wanxuwar wani a waje baya hanasu nunawa junansu zallar son da sukewa juna,mutane da dama na mamakin haidar din,saboda kowa ya sanshi da miskilancinsa ya sanshi,sai gashi lokaci daya zahra ta sukurkutashi.


Tako wanne fanni

Please Login or Register in order to submit comment