Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan be hanashi daukan ka ba ya samaka albarka...naga baƙar rana guna dawo min da kai yayi ya damkamin amanar ka da ta Khadijah da kuma jakar da ya dawo da ita ya cika da kalmar shahada..




Iya firgici na shiga haka Khadijah itamana tana ji ya mutu ta bishi haka mu ka kawo gawarsa gida su nanne sun shiga tashin hankali domin iya shi suka mallaka binciken likitoci bayan harbinsa da akai har wata guba an bashi a hankali take mamaye jiki sai dai kawai aga mutum ya mutu




haka na dauki ragamar komai ta rayuwar ka domin ban bawa su nanne kai ba ni na ke kula da kai ba ruwan saudatu da kai.....akwai lokacin da har sakin'ta nayi sakamakon ture ka da tayi ka waɗi shine sanadiyyar ɗingishin nan da kake



Kabi a hankali Asharaf bance lallai sai ka faɗa min abin da ke faruwa da iyalanka ba amma jikina ya bani akwai wata munufa da yasa mahaifin nadeeya ya baka yar'sa bayan baya son mahaifin ka da haɗin bakin sa aka kashe da wasu manyan ƙasar nan na fara bincike abun ya faskara direct daga aka aikomin da takarda daga fadar shugaban kasa cewa in janya hannuna daga batun kisan kanal Muhammad maɓaya ba daddara ba na ci gaba sai da sukai min barazana da kai sannan na haƙura



Mutanan gidan nan ma ba abin yarda bane saboda ko su nasan suka sami dama wallahi sai sun aikaka lahira ASHARAF wata irin sarkakiya ke tare da banso Ka shiga siyasar nan ba Asharaf saidai na fahimci burin kane



Iɗagowa yayi idon'sa yayi ja jijiyoyin ƙansa sun fito rada rada da kyar ya iya buɗa baki yace



"Abba jininsa bazai taɓa tsulwan'ta a banza ba insha Allah sai duniya tasan wayan da suka kashe shi ƙasar nan an gina tubalinta a rashin gaskiya duk wanda zai gaskiya ɓatar da shi ake.....,


Fito da wani littafi yayi duk yayi kora yace




"Ungo wannan shine mahimman abu da sa mahaifinka yace abaka wannan akwati in Ka girma kaje kai bincike akai...,


Amsa yayi hannu bibbiyu ya riƙe yace



"Insha Allah komai zai zamo karshe nima akwai wasu ayoyin tambaya da nasawa mahaifin nata da ita kanta saidai duk abin da suke ina lura da su yanzu ainiyin wasan zai fara...,




Kai ya jinjina yace



"Allah yayi maka albarka ka cika ɗa na ƙwarai..,



Amin yace sun ɗan tattauna wasu batutuwa akan takarar sa yayi mai sallama ya fita kai tsaye gurin hajiya sauda ya nufa dan mutuncin abbansa badan halinta ba




Saminta yayi a zaune ta ɗora kafa daya kan ɗaya baƙinsa dauke da sallama ya shiga sauran yaranta suka amsa mai kadaran kada ham suka gaishe shi gaishe'ta yayi cikin mutun tawa




Ɗan yatsuna fuska tayi ta amsa mai

a guje wata sanye da riga da wando ta fito ƙanwar hajiya sauda ce yar autar su cikin so da kauna tace




"Ya ansh barka da warhaka...,




Tashi yayi cikin halin ko in kula yace







"Yauwa ya juya yace na tafi ba wanda ya tamka maganar'sa ya fita shima ko kuwa ko a jikin sa dan adam yasan hali



Komawa gun abba yayi ya dauki akwatin nan





yafita kofar gida yayi tuni ya cika damƙam da mutane da yake duk sanda zai ziyarci mahaifinsa sai sun taro kuɗi ya bawa john yana rarrabawa





Dakyar suka barsa ya huce tafiya me nisa sukai kafin suje inda gidansa yake



Gaban wani tabkeken gida suka tsaya John yayi horn me gadin ya buɗe




Parking space ya shiga inda ya ajiye motar ya fito ya buɗewa uban gidan nasa ya fito cikin izza yake tafiya John biye da shi har izuwa kofar da zata sada shi da shashinsa




Amsar akwatin yayi John ya juya shi kuma ya shiga ciki


*******




Sai yamma liƙis suka dawo gida a kofar gidan su me a napep ya kawo ta sauka tayi ta biyashi kuɗinsa ya ƙara gaba da baraka.....sanadin program ɗin nan da tayi gwamna ya cika mata jaka da kuɗi dan haka yau ji take tana shawagi a sararin samaniya



da yar wakar'ta ta shiga gidan kahu hamisu ta yi kicibus da shi a tsakar gida cikin baƙin ciki ya kalle'ta yace




"Yanzu jidda abin da kikai ya dace to wallahi bazan boye miki ba A.I.GEZA yasa inyi bincike akanki yace zai yarda ba wallahi in yayi miki wane daurin ko su wayan da suka saki basu isa su kunto ki ba....,



Wani takaici ne ya kamata tace





"Kahu wallahi siyasa yanzu na fara faɗuwar gaba a sarar na miji kasani sarai bana jin tsoro wallahi in ya fasa shi ba ɗan halak bane....,




Tau ya dauke'ta da mari da sauri ta kama kuncin'ta tace



"Ni ka mara to wallahi yau kowa na gidan nan bazai kwana cikin kwanciyar hankali ba MUZU BA MUGA NI ( shin KO kinsan me littafin MUZU BA MUGA NI nace kin sani ko kema ambarki a baya....?) tana kaiwa nan ta shiga ɗaki gwaggo ce ta fito cikin kumfar baki tace





"Wallahi hamisu ka fita a idona in rufe kowa na gidan nan ya tsani marainiyar Allah nan..,



Cikin takaici yace





"Gwaggo yarinyar nan siyasa fa tashi ga .....,




Turo daurin ta gaba tayi tace





"To sai mai hamisu karkai ma ka fara yi mata hassada ne dan kaji muryar ta a gidan rediyo tab wallahi ka shiga hankalin ka tun kafin Ubangiji yayi mak kunar baƙin wake dan kaga shi wancan me fubfar kafurawan farko ba shi take ba ta tafi siyasar su tsula tsiya ka gama lafiya yo kululu akwai wayo ba ta tsaya fagen su yan kuci ku bamu ta tafi sama ɗoɗar...,




Wani kululun takaicine ya tukare mai ma ƙogaro yace



"Gwaggo ina jiye miki ranan na dama wallahi domin kar jidda ta ɗebo abin da yafi karfin ku...,







Tub aniyar ka ta bika masaharranci ba ruwan ka da ita

Fita yayi domin bazai iya zaman gidan ba shi yanzu besan me zai fadawa oga ba jidda ta cuce shi wallahi





Cikin gida kuwa tana shiga ta cire kayanta zama tayi daga ita sai daurin kirji tana lissafa kuɗin da ta samu dubu hamsin cas gwaggo ce ta shigo ta washe baki tace


"Kululu duk wannan su suka baki....?,


Ajiye su tayi a gefe tace



"Eh wallahi zan ware kuɗin motar tafiya kamfen sannan in baki ke da malam...,



Buɗa tasaki tace



"Ta gaban mota insha Allahu wata ran sai kinyi Kwamishina....,



Cikin farin ciki tace



"Amin gwaggo...gobe ma da huri xan fita zan raka gwamna kamfen...,


Tashi tayi ta fita gun tattabarun'ta ta shiga buɗe su tayi fur suka fito suka tsagaye'ta gero take watsa musu suna ci suna hawa jikin'ta takan shiga farin ciki inhar tana tare da su ji take bata da wata damuwa.....baba lami ce ta fito tace




"A'a woman leader kin dawo...?,



ɗaga gira tayi tace



"Ga shinan kuwa kin gani..,


Ɗan dam baba lami tayi tace




"Kululu yar gidan gwaggo nace ko zan sami rancan dubu wallahi jarina ne ya karye..,





Wani kallon up and down tayi mata baba hansai ce tafi to hannun ta rike da buta da alama makewayi zata shiga Cikin dan habaici tace



"Allah ka kara bamu da haifar ya'yan kuka...,


Yaron'ta ne ya tsala ihu da yake sabuwar haihuwa tayi da sauri ta ajiye botar cikin sauri ta koma dakin'ta


Kallon baba lami jidda tayi ta saki wani banzan murmushi tace



"To jeki zuwa safiya zan baki rance amma Wallahi duk randa na bushi iska baki biyan ba tofa duk abin da nayi miki ke kika jawa kanki....,


Da sauri tace



"A'a zan ma biya ki nagode..,



Banza tayi mata ta ci gaba da watsa musu hatsi Allah Allah take baba lami tabar gun aikuwa ta gaba yan abun da za ta yi ta bargun da sauri jidda ta watsar da hatsin hannun'ta ta shiga ɗaki


Kullun wani abu ta dawo da shi cikin sanda ta buɗe wannan butar ta hansai ta juyai tsidugu tas a cikin ruwan nan kusan rabin leda fara a inda ta ajiye ta sa shi.....ai daman da tasu da mijinta dazu har shi zai mare'ta ya manta da


Wacce jidda woman leader wanka ta shiga fitowar ta kenan hansai na tsaye tana jiran'ta yi tayi kamar bata ganta ba


Ta bangaje ta ta shiga makewayin jidda bata kulaba ta koma ɗaki daman tayi al'wala jira take a kira sallar magariba tayi


Wani irin wahalallan ihu hansai ta saki.........✍️





*Oum yasmeen*




*HAUWA KULU WOMEN LEADER*


*Banyar da wani ko wata ya mai da min wannan book audio ko document ba bazan fitar da document ba kuma ban bawa wani ko wata document na wannan littafin ba*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

🔞book 1



*Typing..................*


Wani irin wahalallan ihu hansai ta saki da sauri kowa na gidan ya fito ban da jidda da take kwance tana dariyar keta

Fitowa tayi tana dafe bango tana tale kafa dafe kirji gwaggo tayi tace



"Na shiga uku badai yaran da suke haurowa gida suna yiwa matan mutane ba sun kamaki hansai ji yadda kike tale kafa yawa wacce akai wa fyade...,




Cikin yanayin azaba tace



"Gwaggo barkono aka zabamin a ruwan da zan shiga bayi da shi....,



Tunu gwaggo ta harbo jirgin me ya faru amma saboda bata ganin laifin jidda tace



"Ke hansai bana son shashancin banza wa zai zuba miki barkono a ruwa...kidai nemi wani abun badai wannan ba,



Kahu hamisu ne ya shigo yace



"Lafiya nagan ku anan kunyi cirko cirko..,



Tsaki gwaggo tayi tace




"Wannan alimar matar ka ta tara mu inban da iskanci ta zuba barkono a buta tace zuba mata akai wata kila wata shegiyar ce zata ce maganin gyaran gaba ne..... saboda ita tazama me kan dosa ta dauka dan kaji zam-zam ai gashi ita taji a jikin'ta....,



Ƙasa yayi da kansaa yace




"Hansai shige mu shiga....,


Cikin takaici tace




"Wallahi jidda ce tayi min wannan aikin ba ɗazu ka mare ta ba....,



Da sauri jidda ta ɗaga labulan ɗankin'su tace




"Innalillahi wa'ina ilaihir raji'u ni kuma kiji tsoron Allah kuka tasa harda shashsheƙa tace



Yanzu gwaggo kina gani ana cin zarafina dan anga bani da uwa wallahi yau bazan kwana a gidan nan ba gun inna ta gabas zani



Kamo jidda tayi ta rungumi tasa kuka tace




"Wallahi Allah zai saka mana yanzu dan rashin mutunci a gabana kuke cin zarafin yarinyar nan kai sokon banza kana tsaye kana jin baka ɓarar mata da haƙoraba ta rasa na zawarcii...,



Ransa ne yayi matsifar ɓaci yace





"Inna Dan Allah kiyi haƙuri.....,



Kahu musa ne ya shigo yace




"Jidda gani na dawo zo ki bani kaso na duk inda nayi a garin nan cewa ake kinyi kuɗi nima figa min nawa kason....,



Turus yayi ganin abin da yake faruwa yace




"Lami me yake faruwa....?,



Ina zan sani me gida hansai ce da wani abu wai jidda tasa mata barkono shine gwaggo take kuka


Ai kafin ta ƙarasa wani zancan ta suka wasai sakamakon karurnuƙan mage da suka shigo da alama ya dawo ga yawan nasa


Ihu ya saki yace



"Dawa dai malam sai Ni uban mafarautan garin nan sai Ni wan kulu annuba cau cau cau an ja dani an barni..,



Jidda ce ta fito ta saki buɗa tace



"Duk wanda yace zai ja damu tofa karshan sa yazo....mukan hana mutum bacci..cau cau Ni RABEBE ARNAN DAJI...,



Da sauri kahu musa ya fito har yana harɗewa da rigarsa yace





"RABE anya kuwa kana da hankali..? kullum kana girma kana ƙara shiga dawa yau kwanan ka nawa rabon ka da ga gidan nan...wallahi Rabi'u dole in gyara maka zama a gidan nan..,


Muciji ne ya fito ya tsaya ya saita kahu Musa mage yace




"Kahu Allah yayi maka tambaya to kai bashi amsa danni bani da lokacin ka.....,



Zare idanu ya shiga yi yana waige waige yace



"Dan girman Allah jidda mage ku yi min rai....,








Dariya jidda ta sheƙe da ita tace



"Kahu yanzu zan dauke maka shi amma gum ba ruwanka da shiga sha'anin da ba'a saka ba...,


Da sauri ya ɗaga kai yace



"Na yarda kululu yar gidan gwaggo...,


Danna remote control ɗin mucijin yayi na ruwaba ne ai kuwa tuni ya dawo kusa da shi ya hau jikin'sa da sauri kahu musa ya bar gun dariya jidda ta shiga yi tace



"Ya mage ina ka samu wannan mucijin roba me kama da na gaske....,




Dariya ya sheƙe da ita yace





"Kar inji abakin wani kiyi shiru yau mutan gidan nan sun shiga uku a tsakar gida zan ajiye shi duk wanda ya fito yayi farin gani....,




Kai ta gyaɗa mai kasancewar an kira sallar magarib duk abin jidda tana da roƙon ibada da sauri ta shiga ɗaki tace



"Ya mage tafi masallaci an kira sallah...,



Idanuwan'sa ya zaro da yasha kwalli yace


"To tasallah in nayi lokacin da na gadama kar ki amsa..,


Girgiza kai tayi ta shaga ɗaki



*******




Tafiya yake cikin natsuwa sai ka kula zaka san yana motsa baƙin'sa tasbihi yake ga ubangiji madaukakin sarki ɗan taƙi kallan yayi ya zo gida


Da yake tsakaninsu da masallacin ba nisa tura get yayi sai ya tarar a buɗe da sauri ya shiga cikin gidan ko ina me gadin gidan ya shiga......



Tarar wa yayi baya nan da sauri ya koma ya rufe kamar ance kalli can megadin ya gani tare da nadeeya yana binne mata wani abu saurin komawa ciki yayi ya zauna a floor sa aiki ya shiga yi


Sai guraran goma sha biyu ya tashi lokacin yasan nadeeya tayi bacci cire kayan'sa yayi ya sa marasa nauyi tare da face mask ya fita


Cikin sanda yaƙe tafiyar har ya ƙarasa gun nan tuna gun ya shiga yi sunyi haƙa me zurfi tukun na ya gano fukafikin kaza da alama da ranta aka sata an rufe bakin'ta cikin rashin tsoro ya buɗe baƙin cin karo yayi da laya zurawa yayi a ajihun'sa ya rufe gurin ya wullar ga ƙazar a waje abin duniya ne ya ishe shi be gane yayi zaɓen tumun dare ba


Sai a wayan nan kwanaƙin waje su neme shi haka gida ma to da me zai ji .....


Komawa yayi shashinsa toilet ya shiga tuɓe ƙayan'sa yayi cikin kyam kyami ya shiga wanke hannunsa duk kuwa da safar da yasa ya daɗe yana wanka tukunna ya fito daure da towel



Gaskiya ansh ba ƙaramin ingarman namiji bane jikinsa duk a murɗe yawa ɗan dambe ji yayi an turo kofar be joyo ba ci gaba yayi da jafa mai ta maya ta rumgume shi tace




"My man kai hakuri nasan na ɓata maka wallahi nakasa bacci...,


Ture hannun'ta yayi daga jiki sa ya ci gaba da shiryawa akan mararsa ta ɗora hannunsa tasan wannan ɓangaran bashi da sauran zaɓi wanda ya huce ya bita


ɗan murmushi yayi a zuciyarsa yace



"Yau nadeeya zan shayar dake ruwan mamaki....,



Kunce towel ɗin tayi saurin roƙo towel ɗin yayi cikin i don't care...yace




"Nadeeya me kike yi haka yanzu bani da wani interest akan wannan abun Please ki barni na gaji....,



Cikin sauri ta ɗago kai ta kalle sa bakin'ta har rawa yake tace



"What.....my man me kake faɗi to aini ina da shi...,


Idanuwan'sane suka kaɗa sukai ja cikin tsawa yace




"Nace ni bani da shi ko ana dole ne....,


Zancan da kullum take faɗa mai kenan in ya kawo kansa gare'ta


Cire yaloluwar rigar baccin da tasa tayi kau da kansa yayi yace




"Please fita zan yi sallah...,



Kallon agogo tayi karfe ɗaya har da rabi cije lips ɗinta tayi tace



"Okay...ta zura rigarta futa tayi ko rufo kofa batayi ba gama shiryawa yayi ya zura jallabiya ya kullo kofar'sa shin fiɗa prayer mat yayi ya tada kabbarar sallah


A sujjadar'sa ta ƙarshe ya dade yana neman zaɓin Allah akan mulkin nan da Allah in ya bashi ya bashi inƙon sauke nauyin da ya daukarwa kansa sannan yayi wa ƙasar tashi addu'a tare da iyayensa ɗagowa yayi yayi sallama sannan ya ƙara ɗaga hannunsa ya miƙawa Ubangiji kukansa


Tashi yayi ya kashe ko mai ya cire jallabiyar sa addu'a yayi kusan karfe uku da rabi ya kwanta ya ja blanket me uban taushi


******



Washe gari da sassafe kahu hamisu ya amsa kiran A.IGEZA a office ɗinsa ya tarar da mutane dan adan haka kuma sai da ya jira shi bayan ya gama sallamar mutane ya shiga gaisawa sukai cikin mutum'ta juna haka babban amininsa Shuram Abubakar suka gaisa

ANSH yace




"Ka binciko wace ita....,



Gabansa ne ya waɗi besan da wannan baƙi zai faɗamai jidda a matsayin ya'take a gunsa kauda wannan tunanin yayi koma mene ai ita ta jawa kan'ta yace



"Yar wanace...,


Da sauri shuram yace



"Yar wanka...?,


daga kai yayi alamar tabbatar wa yace



"Gwaggo ita ce silar taɓarɓarewar jidda bata son lefin'ta ko kaɗan daga dan girman Allah ina nemawa jidda afuwa yarinya ce yar yanzu ko sha shidda bata rufa ba..marainiya ce bata da uwa..,



Shiru ANSH yayi yana juya biro tukunna yace



"Bakomai Malam hamisu kafi karfin haka a guna..,



ya dan dade tukunna ya bar office ɗin yana bari shuram yace



"Man kaji wani abun takaici daga yaron da bashi da uwa ko uba yayi abu sai ace marayane shi besan bashi da gata ba yake aikata abin da ya gadama ni wallahi banga dalilin da zanbar ƙaramar yarinya tana shiga siyasa ba ko gujin daukar muguwar ɗabi'a basa yi...,



Ajiyar zuciya ya sauke yace



"Allah ya kyauta,


shuram yace




"Amin...ya nadeeya...?,


Cije lips ɗin'sa na ƙasa yayi yace




"Ba canji jiya i yau...,



Dan jim shuram yayi tukunna yace



"Ga shawara me zai hana ka ƙara aure hakan zai sa ta gyara halin'ta...,



da sauri ansh ya daugo yace



"Aure kuma...?Ni yanzu bani da burin ƙara aure..,



wallahi in har kana buƙatar farin ciki dole ka ƙara aure ka auri ƙaramar yarinya wacce kai zaka koya mata yadda kake so ta zama me zai hana ba zaka auri wannan WOMAN LEADER ba ka jefi tsuntsu biyu da dotsai ɗaya ka gasa mata aya a hannu ko daga baya ka sake ta kaga kai maganin'ta ta cikin ruwan sanyi a kullum jifan ka take da mugayan maganganun in wani be dauka ba wani zai dauka kai tunani



Da sauri yace




"Shuram kana da hankali kuwa....me zanyi da wannan yarinyar bayan kuma ba mutuniyar kirki bace yarinyar da take yawa tsakanin maza ba kunya ba tarbiyya kana dai ji abin da dan uwanta yace akan'ta...,

Dafa kafaɗar'sa shuram yayi yace



"Calm down man ka yi tunani hajadi fa zakai..,



Sakar baki Ansh yayi yana kallonsa yace



"To kai kai jahadin mana....,



Tashi yayi yace



"Kaga tafiya ta kai tunani irin wayan nan yaran sune kadangaran baƙin tulu....,




Dariya yayi yace





"In Allah ya nufa zan zama shugaban ƙasa wallahi bata isa ta hana ba kai ko wayan nan mutanan ƙarya suke wallahi...,





Hakane amma kai fa tunani me kyau na barka lafiya


Mai da hankalinsa yayi kan system ɗinsa ya ci gaba da aikin gabansa


Bayan kwana goma



Wannan program ɗin da jidda tayi shi ya daga martabar ta ko ina in kaje sai zancan saboda yar gwagwarmayar siyasa da aka samu ake musamman yan jam'iyyar NBB me alamar gona


Kahu hamisu kuwa ya zuba mata ido haka mahaifinta saboda gwaggo har cewa tayi zata tsine musu hakan kuwa ba ƙaramin dadi yayi wa jidda ba ta ƙara miƙe ƙafa tana abin da taga dama


Yau ita da gwamna za su fita campaign dan haka tun safe ta shirya


cikin material baƙin da adon flower ha sosai yayi mata kyau dauko mayafi tayi ja tasa ta rataya jakar'ta tace



"gwaggo ni na tafi sai magariba zan dawo..,


To yar albarka Allah ya temaka ya bada sa'a



Murmushin jindadi tayi tace




"Amin gwaggo ta...,


Tasa ƙafa ta fita a tsakar gida ta tarar da hansai da lubabatu sai lantana suna gyaran zoɓo duk sunyi bututu ɗan ya tsuna fuska tayi ta dauke kanta sarai sun ganta amma ba wanda ya kula ta dan yanzu jidda ta ƙara koyo rashin mutunci yan zunan zata ɓadawa idon'ta toka ta ci uban mutum ba me magana

Saboda yanzu da yan daba take yawa

har taje kofar soro ta tsaya tace



"Baba lubabatu malam yana ciki...,


Wacce aka kira da baba lubabatu tace



"Yana kasuwa yau kinsan kasuwar garin nan ke ci..,


dafe kanta tayi tace



"I for get ta saka kai ta fita ɗan isiya yana ganin'ta ya burga mashinɗin'sa yace


"Tun dazu nake kijaranki...amma kin tsaya kina taku daddai...,


Ƙara Sosa tayi tace



"Wallahi bansan kana jirana ba ina baraka take...?,


Cije baƙi yayi irin na yan daban nan yace


"Owo mata ai gab nake da inci kut...,


Ai kafin ya ƙarasa ta ɗaga mai hannu tace



"Haba dan isiya wannan fa kawata ce kuma aminiyata duk abin da muka zama ita ce sanadi kawai yanxu na lura so take tayi baya baya dani....,



Wata mahaukaciyar dariya ya sheƙe da ita yace



"Ba dole ba baki san iliya ya kai kuɗin ta ba....,



Ƙasa hawa mashinɗin tayi tace



"Wanne iliyan....?,



Wanda kika sani


Ji tayi duniyar na juya mata ta dafe kanta daman shiyasa jiya taji su hansai suna magana ƙasa ƙasa har suna dariya lallai BARAKA ta cuce ta tace



"Ɗan isiya yanzu kasan me....,



Nida ba akuya ba ya za'ai in san mee..


cije lips ɗin'ta tayi tace



"Please yanzu ba lokacin wannan maganar bane kai ni gidan su BARAKA dole in tauna tsakuwa dan aya taji tsoro..,



A'a ba haka za'ai ba yanzu dai kinsan gwamna bazai tsaya jiranki ba akwai wayan da suke neman damar ki basu samu ba dan haka sai mun dawo ko karfe tara ne sai muje gidan su zan sa yarana su shirya mana makamai shegiya kinsan fa yanzu ta dena harkar siyasar nan ita zatayi aure maza sun gama kwakule'ta...,


Kai ta jinjina tace



"Haka ne kuma hawa tayi tace



Muje tafiya sukai ba wanda ya ƙara cewa qala yayi da zuciyar jidda take cin kushe bata taɓa zaton ILIYA zai ci amanar ta ba haka BARAKA to wai ma ya akai ILIYA ya yarda da BARAKA


bata san zancan zuci ya fito fili ba sai ji tayi dan isiya yace



"Wai an ce ita da zulai kanwar'sa suka haɗa abun iyayen'sa suka ce bazai aure marajin magana ba....,




Kwafa tayi tace



"Aikuwa za suga rashin jin magan ganin idonsu...,

Dariya yayi yace


"Yauwa tawan....,


Cikin ikon Allah suka isa gidan gwamnati har na fara taron shiga tayi ya tsaya agun ya jagaliya samin guri tayi ta zauna kiran sunan ta akai da sauri tashi ta isa gana table ta amshi speaker tace



"Jama'ar gurin nan barka da warhaka da fatan kowa yana lafiya a gurguje duba da yanayi na lokaci zamu fara abin da ya kawo mu


GEZA SAi.....?



Tuni mutanan gurin suka ce sai SA'EED MAI GORO


Gyara mayafin ta tayi da ya zafe tace


ƊURMA sai....?,


Haɗa mutanan gun sukai suka ce sai



YUSUF JIRGA..... 🔊


To kununa mana soyayya ta haryar zaɓar mu a 2025 nan da sati biyu kenan mu kuma mu baku tallafi kala kala zamu inganta hanyar tsaron ƙasar nan tare da huta sai ruwa da tallafin lafiya inhar kuka zaɓe mu kowa zai makaranta kyauta Zaku yarda ku zaɓe gurgur mage....?



Haɗa baki sukai suka ce



"A'a....,


Yauwa ai daman ku masu tunani ne sannan zamu raba muku dubu biyu kyauta RANAR ASABAR sha biyu ga watan Oktoba 2025 ku fito tsakin ku da kwarkwatar ku ku zaɓe jam'iyar NBB me alamar gona...


Ran gwamna ne yayi fari tas da jawabin jidda komawa tayi ta zauna


Wani ne ya ƙara fitowa yayi magana da ga shi aka rufe taro sallama me tsoka gwamna yayi mata daga nan ta tafi gidan Radio GEZA akwai program ɗin da zata yi


********

Shigowa tayi riƙe da kofi a hannunta miƙa mai tayi amsawa yayi a hankali yace



"Thank..,


Kai ta ɗaga mai ta koma ta zauna a kafaɗar'sa ta kwantar da kanta gyara mata kwance yayi ta hanyar kwantar da kanta a cinyar sa sosai yanayin na yau yayi mai dadi kasancewar ba wata sa'insa da ta haɗa shi da nadeeya kafa kofin yayi abakin'sa da sauri ya zare ya dube ta yace



"Sweetheart wannan me kika kawo min....?,


tashi tayi ta ɗan haɗe rai tace



"Abin da kasa nayi maka yayi dad'i ko fiye da wanda kake order ko..?,


Ajiyar zuciya ya saki baya so ya sace Mata gwuiwa amma wannan abin da tayi be yi kama da coconut juice ba yace


"Yayi....,


murmushi ta saki ta rungume shi tace



"My man ina mutukar son Ka Allah ya barmu tare har abada....,


Ajiye kofin yayi ya rungume'ta yace



"Amin my dear....,


wallahi my man duk macan da tayi gagganci kula ka Allah ranar lahira zata yi baƙuwa.....,



Zare ta yayi a jikin sa ya zuba mata lumshashshun idanuwan'sa yace



"Me isa kishin ki yayi yawa in Allah ya ƙaddara cewa a rayuwa zanyi mata biyu ba yadda zanyi dole inyi saboda yana ɗaya ga cikin ƙaddara'ta....,


Wasu hawaye ne suka kwaranyo mata tace



"Wallahi ranar zan kashe ka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment