Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan da nake ba a cikin hostel sai dai gidane na haya da yan makaranta ke kamawa.
Driver shi ya taimaka min da kayana har zuwa bakin gidan namu ya shiga min dasu sai dai bai shiga ciki ba kudi ya miko min yace gashi oga yace idan na sauke ki in baki.
Dan jimm nayi kamar bazan karba ba sai dai nasa hannu na karba tare da fadin kace nagode sai dai ban faye karban irin kyautar nan ba kallo na yayi ganin na fara jan trolley dina yasa shi wuce yana mamaki na a ran shi.
Dakina na bude wanda mijin ya Amina ne ya kama min hanyan shi dakine ciki da falo da bandaki a cikin sa sai inda mutum zai danyi girki daga waje haka dakunan suka a jere har dari da wani abu.
Dakin yayi kura dan sati biyar din da nayi ban ciki daga kofa na aje kayan da na dawo dashi na fara gyara dakin tukun sai da na sharo ko ina na dakin.
Na mayar da komai yadda nake son shi na fito ba zan iya fita ba haka yasa na kwanta don in sauke gajiyan dake jiki na a lokacin.
Ba wanda yasan na dawo do haka na rufe kofa na kwanta abina sai barci mai nauyi ya dauke ni a cikin barci sai gashi wai muyi mumunan fada da buzuwa mijin kuma na tsaye yana kallon mu baiyi magana ba.
Falkawa nayi don kiran wayana da akeyi na lalubu wayan da kyat saboda barci da yaci idona ya Amina takirani.
Ina dauka naji muryanta tana cewa ina kika shiga ne haka waya nata kara baki dauka ba cikin muryan mai barci nace wallahi barci nakeyi anty.
Tace yaya kuka sauka shine koki kirani hankalina ya kwanta nace wallahi lafiya kalau muka sauka tace badai wani matsala ko ke da buzuwan ki ?
Naja guntun tsaki nace suna can gidan su muka sauke su driver su ya kawo ni hostel ni komai bai hada mu ba a motan bayan gaisuwa.
Tace to barin barki ki huta an jima zan kira son naga yanzu barci yaci karfin ki nace ai na tashi yunwa ma nake ji yanzu tace to ki samu abinda kikaci kin san kina da ulcer nace yanzu zan tashi.
Baki sayo komai ba ma ke nan nace yau na gaji ne anty ba zan iya zuwa ko ina ba sai dai gobe idan na fito lecture.
Allah yakai mu tace muka kashe waya ina jin dadin yar uwa ta sosai saboda kulawan da take bani na musanman shiyasa nima nake mata komai kamar ita ta haife ni.
Mafalkin da nayi ne ya fado min a raina lokaci guda yake dawo min dan dariya nayi nace ikon Allah wanan buzuwar kamar manya ta tsaya min a rai haka ?
Sai a lokacin kudin da driver nan ya bani ya fado min a rai na jawo jakka na daga kwance na kirga kudin ido na zaro ganin har dubu hamsi ya bani nace wanan yasan zafin kudi kuwa ?

ZAINAB IDRIS MAKWA
SEENABU
Bai yi mamaki shigowa ya samu abinda ya gani ba a gidan don ba yau bane farkon yin haka gare ta don a duk lokacin da ta ganshi ya rabi wata mace ba aita ba ko kannen sa da suke uwa daya ko uba daya ba hakan take mashi wannan haukan a gida.
Don sani yadda suka rabu da ita kafin yaje office akan kawai mahaifiyar shi ta bashi umurni ya bi na su rage min hanya zuwa abuja kuma a motar shigan su.
A hankali ya kusa kai cikin falon su na sama ga tarin gajiya a jikin shi daya kwaso yau ga na tafiyan da sukayi ga ya zo ya samu aiki a office.
Hankalinshi yayi matukar tashi saboda ganin yadda tayi kaca kaca da falon komai ta har gitse ta fasa na fasawa ta watsar dana watsarwa a kasa.
Hatta tv bango ta tarwatsashi ga crystal glass da aka aje don decoration din falon a folon a kasa ta tarwatsa duk komai na falon a har gitse kamar ta haukace.
Tsayawa yayi a daga kofa yana bin ko ina da kallon mamaki a ranshi kuma yana mamakin irin zafin kishin Nafisa.
Wanan wani irin kishine haka shi bai da dama ya sake da wata mace a rayuwan shi sai ita duk da tasan neman mata ba halin shi bane.
Wanan wani irin rashin hankali ne ko kishi haukane kinshi Nafisa ba ba bai san yadda zai fasarashi ba don abin baiyi kama dana mai hankali ba.
Shi dai tun farko bai fada mata da ita kade zai zauna ba a rayuwan shi kuma tasan yana da mata tayi ta nacin sai da ya yarda ya aure ta.
Amma kuma shigowan ta ta hana shi zaman lafiya da iyalin shi da mahaifan shi gaba daya halin Nafisa idan ya motsa sai yaji nadaman auren ta dayayi.
Amma kuma idan komai ya wuce sai ta koma kamar ba ita ba shi dai wanan abin yana matukar damun shi wallahi.
Dakin barcin su ya nufa inda ya hangota takure a wuri daya tayi kuka tagaji ta ba kanta hakkuri jin an shigo dakin yasa ta dago kai cikin fushi don taga ko waye ya shigo mata daki.
Daga kofa ya tsaya ya kare mata kallo da kyat ya bude bakin shi yace wanan wani irin rashin hankali ne ko kishi haukani a garin ku ko kwakwalwan ki ya tabo ne da zaki min hassara irin haka don bake ke saye ba ko ?
Ya ka maganan cikin fushi yana hararanta a harzuke ta dago tana huci tana fadin eh hauka nake kuma a kan ka wallahi kadan ka gani duk kace zaka hadani da wata mace a duniyan nan abinda zan ma sai yafi wanan.
Yace oh ashe kina da aiki kuwa don dai ni namiji ne mijin macd hudu so zan iya aure a duk sanda nayi raayin hakan.
Cikin wani murya tace wallahi karya kake baka isa kace zaka hadani da wata kishiya can ba ni ni kadai ne matar ka, ka sani.
Oh dama tunanen ki ke nan amma kafin ki shigo kin samay ni da wata matar ko amma sabods zafin kishi irin naki ki hana mu zauna lafiya da ita.
Kaima kasan abinda ba zai yuyu ba ke nan ka hadani da wata mace may na rage ka dashi a duniyan nan wani irin kulawane baka samu a gare ni da sai ka hango wata a waje.
Cikin mamaki yace wana na hango a yanzu din kuma wa kika gana kula haukan ki dai ke nuna maki hakan mahaukaciyar banza kawai.
Indan kai ba baka hango ba ai mahaifiyar ka ta hango maka ita in bashi ba may ye nace wa sai wata ta biyomu a motar mo inba son hada fitina ba.
Yace Nafisa rashin hankalin naki har yakai ga mahaifiyata haka tanan kika biyo kuma Nafisa kan mahaifana tace in ba haka ba ne may take nufi yasa ta hado mu da ita ?
Yace cikin daka tsawa karki kuskura ki kara fadin wani maganan banza akan haka rakin zai baci sosai a gidan nan daga haka ya juya zaj bar dakin sai kuma ya juyo yace.
Ki tabbatar da kin gyara dakin nan da kan ki kuma ki mai da komai da kika fasa in ba haka ba wallahi zaki ga bacin rai na a yau din nan.
Sannan wani magana guda kada ki kuskura ki kira wani dan aiki yazo ya kwashe wanan barnan da kikayi ke da kan ki nake son ki kwashe shi daga haka ya fice ya shige wani daki a gidan.
Bin shi tayi da kallo don tasan ya hau sosai ga abinda tayi din sai yanzu nadama yazo mata a rai ga abinda ta aikata don tasan gaskiya ya fada mata kuma zuciyar tane kawai ya bata hakan ta hau ta zauna akai.
Gashi ta jawa kanta aiki don abinda ya fada har cikin ranshi ya fada duk dan aikin da takira ya gyara mata tasan abakin aikin maishi yake.
Gashi duk yan uwanta ne na jini babu wanda zata so a kora a cikin su haka yasa ta mike dole a cikin daren nan ta fara gyaran duk inda ta bata din.
Dakin yake yayi wanka ya sauya kayan shi zama yayi tare da dauko laptop din shi ya duba sai dai ya kasa aikin da yake son yi a lokacin tunane halin Nafisa yake yi.
May take nufi dashine ya tun haduwan su na farko da ita a bakin ma aikatasu yazo shigewa ta miko mai hannu tana fadin baba bani kuddi.
Kallon mamaki ya tsaya yana mata tare da waigawa baya ko da wani take magana bashi ba sai yaga babu kowa a wurin sai shi kadai tsakanin shi da mutane akwai nisa ta sake mika hannu tana fadin baba bani kuddi.
Yace kudin may zan baki tayi mashi alama da hannu abinci zataci alhalin su ke sai da abincin dayake shi mai tausayi ne kamar yadda mama ta koyar dasu na taimaka ma nakasa dasu sai ya ciro dari biyar ya mika mata da sauri ta karba har kasa tana mai godiya.
Ta nufi rufan sai da abincin nasu ta mika kudi yana kallo aka bata abinci ta koma gede tana ci a haukace kamar mai yunwa.
Tun wanan ranan idan yazo zai shige zata taso tana fadin baba bani kuddi sai ya mika mata dari biyar taje ta karya dashi.
Har shakuwa ya shiga tsakanin su mai karfi ko bai ganta ba zai aje mata dari biyar din nan kudin karyawanta yakawo mata yace ga kudin abinci nan.
Tsaki yaja ya rufe laptop din tare da kai kafadan shi saman gado ya kwanta rigingine yana ci gaba da tunane shi mutum na farko da ya fara warning din shi akanta shine Yusuf.
Yace kasan fa irin mutanen nan kudi suka fito nema ido rufe da maza ya kamata ka daina bata kudin nan kar mutane suyi zargin ka akanta.
Shiko tausayi take bashi baiga zai iya kin taimaka mata ba don taba bukatan taimako aa lokacin har yakai sun fara kyaabewa da ita.
Alokacin kallon yarinya yake mata don bai dauka ta haihu ba ma sai da yaje da zancen ta gida wurin su mama nason ya taimaka mata.
Mama ta kafe ba zai dauko mata fitina cikin zuri,anta ba anyi anyi da mama tace ba zata yarda ya dauko buzuwa ba yadda take ganin a na kwashewa dasu a gidaje da suke.
Ga fati bata rage shi da komai ba tana mishi biyayya don auren gata akai masu shida ita tun yana karami sosai saboda an ga taso yazo daya da ita aka dauka soyayya suke yi dashi aka hadasu aure tare.
Ido ya runtse a haka barci ya dauke shi cikin barcin ne yaji ta a jikin shi don bata zuciya dashi duk yadda ya iya fushi da ita bata yarda fushin nasu yai nisa.

Tea na tashi na hada don yunwa ke damu na na debo danbun da mama ta bani ina hadawa dashi ina jin kida na tashi a gidan alaman adawo da yawa ke nan hakan bai sa na fito ba don har na rufe kofana a lokacin.
Na gama nayi shirin kwanciya na don kada in makara da safe ina son shiga school tunda safe in gama komai don zan tafi shopping da yamma.
Washe gari bakwai na gama komai na fito don zuwa cikin makaranta ina rufe daki ne makwaciya na ta gani tace ashe kin dawo dama naga haske jiya a dakin ki sai kuma ba sake gani ba nayi zaton idona ne ke gizo kawai.
Nace eh nadawo jiya nan dai na tsaya muka gaisa sama sama da ita don ina sauri a lokacin na samu napep da zai karasa dani cikin school tunda ajike nake da kudi yanzu.
Naje na gama komai har na samu shiga lecture a lokacin sai karfe uku na juyo zuwa gidan mu a hanya na tsaya sai da na sai abinda zanci na wuce zuwa gida.
Sallah na fara yi don lokaci ya shige sosai koda na dawo wanka nayi na dan huta sai na shirya don zuwa sayo abincin da zanyi amfani dashi na wanan time din tunda ina da waddatacen kudi a hannu na saboda wanan tafiyan a saa nayi shi nake gani.
Don ga kudin da ya Amina ta bani wanda dama ita ke sallama na idan zan dawo sai dai kudin bai kan isheni sai na je gida na dan kara roro abinda ke akwai in kara kafin time ya kare.
Sai gashi wanan karon na samu a wurin mama da kuma dan su mijin buzuwa da ya driver ya bani dariya nayi don tuna sun da nayi nace jamgwangwan ke nan.
Ai sune maganin mazan dake ketare matan kasan mu su auro su don kawai ace buzuwa mutum ke aure ko may ko kuwa jaraba ne irin na mazan Nigeria oho ?
Na watsar da maganan su na mike na sabala jakata na rufe kofana na nufi bakin titi don samun abin hauwa a lokacin sahad yana tashe sosai a cikin abuja do haka na yanke shawaran zuwa can in sayo komai da nake so a saukake.
Ban samu wani matsala samun abin hawa ba ni kadai na dauki shata har can bakin sahad mai Napep ya aje ni na karasa shiga ciki.
Ban tsaya wani feleke ba abinda ya kawo ni na fara yi inda na dauki basket na fara zagayawa ban gare su indomie da taliya wanda shine abincin dan makaranta.
Sai shikafa karamin buhu dana dauka da su kayan miya yadda zai kai min time kada yazo ya kare in rasa mai taimaka min.
Bayan na gama da wayan nan sai na nufi bangaren kayan tea madaran Nidor na dauka na gari dan madaidacin gwagwani na juya zan sa a basket din da nake tara kayan a ciki .
Kamshin turaren mijin buzuwa ne ya daki hanci na kaina na kasa ban dago ba sai takalman mutumin da na gani bakake a kafan shi hakaya na dago kai na dan kalle shi.
Mijin buzuwa ne tare da Yusuf suke sayayya a shagon su ma dan daburcewa nayi da ganin su kamar ba zan gaida su ba sai wata zuciya tace min ko dan kudin da ya baki ai kya gaida su.
Sannu ku nace dasu tare da juyawa na fara tura keken kayana Yusuf din ne ya amsa min tare da fadin a a yar garin mu ke ce.
Ummm kawai nace dasu na wuce abina na karasa saura sayayyana na dungura keken zuwa wurin biyan kudi na aje a gaban wanda ke lissafi ina jiran inji ko nawa na kashe a cikin shagon in biya.
Ya gama lissafi kaina yana akan wayana ya dago yace thirtythree thousand five hundred nace OK na bude jakkan dake makale a kafada na zan biya kudin yace ai an biya maki kudin ga canjin ki ma ya rage yana miko min kudin.
Yana kokarin miko min ledojin yaron shagon ya mike da sauri yana karba da mamaki nake kallon shi ina kallon kudin da yake miko min din.
Waya biya nace mai duk da nasan ba wanda ya sani in ba mijin buzuwa da Yusuf dana hadu dasu yanzu ba a ciki.
Yace gasu can suna fita su suka bada kudin sukace indan kin gama sayayya a biya maki suka tafi da sauri nabi bayan su har na samu sun tayar da motan su suna ribas a lokacin.
Ganina Yusuf ya tsaya na dago da zuman fadar wani magana kuma sai na kasa yaya akayi yar garin mu nagan ki a sukwane ko hanya zamu rage maki ne ?
Nace murya a tausashe aa nazo inyi godiya ne mai shago yace kun biya min kudin kayan na mika mai canji nace ga sauran kudin daya rage nan.
Nuna min mijin bazuwa yaya yace bani na biya ba ogana ne ya biya maki albarkacin ki na yar mama mun yasa ya biya maki ban san sanda nace mijin buzuwa na gode ba.
Ido ya waro waje jin abinda na kirashi dashi shiko Yusuf dariya abin ya bashi yace kwarai kuwa mijin buzuwa ne abokiyar fadan ki ko ?
Sai nayi kasa da kai kunya ya kamani nace ga sauran canji ina mikawa Yusuf din kudin kai ya girgiza min yace ai shi bai kyauta ya karba jeki dashi Allah ne ya baki sai a kara ayi provition ko don naga alaman sayayyan yan makaranta kikayi.
Kallon ledan da yaron ke biye dani dasu nayi nadan yi murmushi nace na to gode kai mun godiya wurin mijin buzuwa zai ji yace dani.
Ai da kizo mu sauke ki don naga gaki da kaya dayawa abin hawa zai maki wuyan samu a nan da sauri mijin buzuwa yace amma dai kasan sauri nakeyi ko ?
Haba baka gani marance yayi ina zata samu abin hawa mu sauke ta mana sai mu tafi aiba dadewa zamuyi ba a can ko may kace yana bukatan jin ra ayin shi.
Da sauri nace a a zan hau napep a bakin titi zaku iya tafiya na gode yana kokari bude mota yace a a ai ba zamu bar yar mama a nan na shiga kawai mu sauke ki kada ki fada ma mama mun ganki muki rage maki hanya tayi muna fada.
Ya fito ya bude booth din motan yake magana ban da yadda na iya dole ina kallo yasa mun kayan a booth din su ya bude min bayan hangamaymay jeep din su na shiga sanyi da kamshi kawai ke tashi a cikin motar.
Ya shigo ya tayar da motar muka fara hanya shiko mijin buzuwa ko ta kan mu bai yi ba sai faman aiki yake a sytem din shi saman jukin shi.
A hankali yake tukin motar mun dan bar sahada din Yusuf yace mijin buzuwa sorry fa mun bata maka lokaci ko ?
Ban son iskanci yace a harzuke sai kuma ya juyo gare ni yana fuskanta yace and ke kuma duk na kara jin kin kirani da wanan sunan sai na bata maki rai wallahi.
Da sauri nace ni kada kaga laifi na haka naji kowa na kiran ka da mijin buzuwa bani na fara fada ba ina magana ina jujuya idanuwa na manya.
Dariya Yusuf keyi muna yace a a mijin buzuwa da haka kowa ya sanka a layin mu don ta fada yanzu shine zakaji haushin ta nace ai shi nagani nima.
Yace dakyau yar mama har lokacin wani kallon takaici yake min yaja tsuki ya mayar da kan shi ga abinda yake yi ya fita batun mu da Yusuf din.
Yace yar mama ke may sunan ki sai naji mijin buzuwa yaja wani uban tsuki yace kai malam kafa san aiki nake yi ka samu yarinya kana biye mata don wauta.
Kasa kasa nace wai yarinya yarinyar dai tafi buzuwan matarka yasin ban dauka maganan duk sun jini ba a motan sai gani nayi ya rufe laptop din ya dafe kan shi da hannu daya.
Shiko Yusuf cewa yayi a sosai ma yasani ai gashi yana gani a gaban shi yace kai Yusuf tsaya in fita motar nan don Allah kun isheni wallahi ban son damuwa kasani.
Maimakon ya tsaya kamar yadda yace sai ya kara ma motan wuta ya harba saman titi da sauri shi yana dariya ya sake cewa baki fada min sunan ki ba mana.
Khadija nake yace suna mai kyau a uni ke karatu ko ina nace eh anan nake yace dakyau aji nawa yanzu nace ban dade da farawa ba biyu muka shiga yanzu.
Kai amma kinyi kokari nake ganin ki yarinya ashe yarinyar da kwazon ta yace may kike karantawa anan ?
Ban kai ga bashi amsa ba yace yaushe ne kazama dan jarida haka Yusuf ban sani ba wanan tambaya ai yayi yawa haka yace ai ba zaka san na zama dan jarida ba sai na karasa tambaya na tukun.
Kawar da kai yayi gefen window motar yana kallon titi Yusuf din yace baki bani amsa ba nace bari in ogan ka ya fita bai san ni nafishi rashin son magana ba ma .
Yace aini naga alama shi ne dai kamar bai ga hakan ba ke nan zan bari sai next haduwa mu sai mu dora a ida muka tsaya tunda ku dukan baku son hayaniya jin nayi shiru yasa ya dan juyo yana satan kallo don jin banyi magana niko ina kokarin ciro wayana daga ciki jakkata da ake kirana.
Bayan na dauko naga baba nane ke kira da sauri na dauko ina fadin daddy i miss you ina mama yace gata kusa dani jiya anty ki tace kin dawo makaranta nace eh daddy amma ban zan zo minna yanzu ba sai dai hutu ina gani.
Mun gama watan da naji Yusuf yace ashe ke yar Niger state ne nace eh ni yar minna ce yace a cikin garin minna kuke da zama ?
Ohh god wanan wani irin abune haka for god sake in kana son jin kwab ne basai kuje gidan redio ba kuyi wannan abi damay yai kama don Allah.
Ku ajeni daga nan don Allah zann karasa da napep don ma mun kawo kusa da inda nake ai a haba ke ko baki son muga a inda kike ne don watarna idan za a bamu sako mu baki.
No I no wan wahala ne ji yadda yake ma fada ban son in ja maka matsala gun ogon ka ne don naga kamar bai so dauka na da kayi ba beside nima din ban son shiga mota dashi don takurawa.
Ke yace yana kallo na a zurke yace ka neman min rai ni a wurin wanan yarinyar Yusuf harta kalli idona tace ina takura mata.
Ya kara yana jan tsaki don Allah yaya Yusuf ka tsaya in sauka anan tun bai yi ball dani waje ba don ban daukan irin wanan na karasa fadi a hankali.
Ina zamu bi don mun kawo unguwar Yusuf ya ke tambayana nace wancan layin zaka bi anan gida jen namu suke ya dan gangara kadan sai nace wancan get din zaka tsaya nagode ina kokarin mikewa ya ja ya tsaya get din a wagale yake a lokacin.
Bai bode motar ba sai yace a nan kike da zama ke nan eh kawai na bashi amsa yana sake bin gidan da kallo sai can ya bude mota nima na bude gefen da nake na fito.
Ya fito ya fara fitar min da kayana daga cikin motar ina tsaye gefe har ya gama ya dago yana cewa kona shigar maki dashi ne ciki.
Abinda yasa ni murmushi ke nan har dimple dina ya dan lutsa kadan yace ko maza basu shi nace ko haka na gode Allah ya saka da alheri kai min godiya wurin mijin buzuwa.
Dariya ya kwashe dashi ya shige mota yana dariya ina tsaye a wurin suka ja motar suka wuce na sauke ajiyan zuciya a hankali

Please Login or Register in order to submit comment