Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nabihat har aka samu isa inda wannan ƙofa, take suka shige izuwa cikin wannan ƙofa tekun mai ɗauke da siririyar hanya ta cikin karkashin kasa.
Lokacin da aka fito izuwa inda aka bar sauran dakaru da dawakai, sai Mazabir ya yi umarni aka ɗora jama'ar su Nabihat akan dawakan dakaru aka sake nausawa izuwa cikin daji cikin matuƙar farin ciki maras musaltuwa.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya su jarumi Najwas suka kammala shiri tsaf
A wannan karon dakaru dubu huɗu aka ɗauka sannan aka ƙara samu waɗansu gwarazan 'yan mata mutum shida daga cikin jama'ar su Nabihat da aka ceto suma suka shiga sahun MAYAƘA
Wato jaruma AMATULLAH, KHADIJAH, SAFNA, jaruma FATIMAH, Basadaukiya TEEMERH, da KHADIJAH bintu Yahya, Jaruma Nabihat tayi matuƙar mamakin yadda akayi sunayen yan uwannata ya canja zuwa masu daɗi haka.
Amma sai ɗaya daga cikin su wacce ta kasance kyakyawa ta gaban kwatance mai suna AMATULLAH ta bayyana mata cewa
Sunayen nasu sun sauya ne sakamakon sun karɓi addinin Musulunci a hannun wani fursuna da ake yiwa laƙabi da sheik ABDULLAH IBN ZAID.
Bisa wannan dalili ne ya sanya sunayen na su suka canja.
Tun a daren jiya jaruma Nabihat da gaba ɗaya fursunonin jama'arta har Mazabir da dakarunshi suka ƙarbi addinin Musulunci suka bayar da gaskiya da Ubangijin talikai.
A wannan lokaci inda ace mutum zai ga irin shigar da jaruma Nabihat da sauran 'yan matan su kayi dole abin ya burge shi gwanin ban sha'awa.
Shigar fararen tufafi na sulken ƙarfe su kayi tun daga ƙasa har sama, sun rufe fusakunsu da koren rawani, idanuwansu kaɗai ake gani, hatta dawakan da suka hau ingarmu ne farare sol! Ita kam yarinya Lazimat shiga tayi cikin ayarin ta na rataye da kwari da bakanta.
Bayan an kammala yin kalaci sai aka ɗauki hanya aka durfafi zuwa birnin Darul-kashmal qka wanzu ana ratsa duhuwar bishiyu da kwazazzabai haɗe da sarƙaƙiya a bisa dawakai cikin matsanancin gudu na keta sa'a,
tafiyar sa'a ɗaya kacal aka yi aka iso ƙofar birnin.
Tamkar sarki Uhaisu jira yake su iso tuni ya gama shirin yaƙi tsaf.
Koda tsayuwar su jaruma Nabihat a wajen sai aka ga Ƙofar birnin ta buɗe sai ga dakaru na tuttuɗowa wasu a bisa dawakai, giwaye, raƙuma wasu a ƙafa.
Tsamanin yawan su ya huce misali, duk inda mutum ya kalla makaman yaƙinsu ne birjik.
Bayan dakarun sun yi sahu-sahu a filin daga.
Sai aka hango sarki Uhaisu ya saki linzamin dokinshi ya durfafo inda suke, yana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke mai matuƙar kwarjini da ban tsoro tamkar wani ifritu.
A gefen hannunshi na hagu kuwa shugaba Yesiran ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi, a dama kuwa yarima Shaiban ne cikin shigar yaƙi.
Lokacin da ya zamana cewa tazarar da ke tsakanin su bata huce taku goma sha biyu ba sai kowa ya ja linzamin dokinshi ya tsaya cak! Aka shiga yin kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu,
Sa'adda shugaba Yesiran ya yi arba da yarinya Lazimat sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone ya na mai duban dungulmi hannunshi ɗaya da ta sake mashi .
Shi kuwa yarima Shaiban ya shagaltu da kallon kyakkyawar surar jaruma Nabihat, tsakanin ƙaunar ta na ƙara ruruwa a zuciyarshi, har sai da Nabihat ta galla mashi harara sannan ya kawar da kanshi.
Sarki Uhaisu da shugaban 'yan fashi Mazabir da Najwas haɗe da kilimat kuwa, wani irin kallo su ke wa junan su mai cike da matuƙar ƙiyayyar da mugun tanadi.
Sarki Uhaisu ya ce a cikin zuciyarshi "ya aka yi sadauki Mazabir ya haɗa kai da abokan gaba ta? Shin dama har yanzu mazabir na raye bai mutu ba?
Lallai babu tantama shi ne ya jagoranci rundunar mayaƙa a daren jiya suka ce ci rayuwar jama'ar su Nabihat
Sa'adda Sarki Uhaisu ya zo nan a tunanin shi sai takaici gami da baƙin ciki suka turnuƙe zuciyarshi.
Daga can ne sai sarki Uhaisu ya zare takobinshi ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu sannan ya ruga izuwa kan su Najwas.
Koda ganin hakan sai Najwas da Mazabir suka sakarwa dawakansu linzami suka yunƙura kan shi. Shugaba Yesiran ya durfafi yarinya Lazimat, ana haɗuwa sai aka ruguntsume da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA.
Sa'adda dakarun ɓangarorin biyu suka ga cewa shuwagabannin su sun kacame da yaƙi, sai kowanne su ya yi kukan kura ya afkawa abokin gabar shi aka yamutse da masifaffan yaƙi.
Koda ganin hakan sai jaruma AMATULLAH, KHADIJAH bintu Muhammad, SAFNA, jaruma FATIMAH bintu Yahya da Basadaukiya TEEMERH suka ƙwala kabbara da ƙarfi suka zare takubbansu suka kutsa izuwa cikin dakarun kafirai aka cigaba da artabu.
Wohoho! Haƙiƙa wannan rana ƙasa ta jiƙu da jinin bil'adam, kaico! Tabbas yaƙi abin tashin hankali da ban tsoro wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi
Duk inda su jaruma SAFNA suka sa a gaba sai dai ka ga dakarun arna na zubewa ƙasa matattu.
Wani sadauki mai ƙarfi na Allah ya isa ya kaiwa jaruma AMATULLAH wani wawan sara da takobin shi, cikin baƙin zafin nama AMATULLAH ta sunkuiya takobin sadaukin ta sari iska,
Kafin ya sake dawo da martani AMATULLAH ta kafta mashi wani sara a wuya take ta tsinke jijiyar wuyanshi ya faɗi ƙasa yana shure-shuren mutuwa.
Jaruma FATIMAH kuwa ta zamto tamkar shaiɗaniya a tsakanin mayaƙan sarki Uhaisu, Khadijat kuwa da ƙarfin damtsen ta take ragargazar dakarun babu sassauci.
A ɓangaren yarinya Lazimat da shugaba Yesiran kuwa sun wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin JURIYA DA BAJINTA gami da baƙin zafin nama tamkar za su cinye junan su.
A ɓangaren manyan GWARAZAN SADAUKAI, sarki Uhaisu, Mafarauci Najwas da shugaban 'yan fashi Mazabir kuwa. Tuni labarin ya sha banbam, domin kuwa sai da suka lalata gaba ɗaya makaman yaƙinsu suka yi jifa da su suka dira ƙasa daga kan dawakansu bisa turba suka shiga kaiwa juna naushi da bugu cikin juriya da nacin tsiya.
Nan fa ya zamana cewa idan Najwas da Mazabir suka nushi Sarki Uhaisu sai su ji tamakar buhun hatsi suka daka domin ko gezau ba ya yi sai ƙura ce kawai ke tashi.
Idan kuwa Sarki Uhaisu ne ya naushi ɗaya daga cikin su sai kaga ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo kasa tim!
Nan fa yazamana cewa Uhaisu ya tara masu jini kuma ba sa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kai, sa'adda su Najwas suka fahimci halin da suke ciki sai kawai su shiga neman Ubangijin musulunci
a cikin zukatansu, ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai suka fara samun nasara akan Uhaisu ya zamana cewa suna haɗa ƙarfin su waje guda su gabza mashi naushi. Kafin cikar rabin sa'a sunyi mashi jina-jina ya zamana cewa ya faɗi ƙasa daƙyar yake numfashi yana kakarin mutuwa.
Kawai sai Mazabir ya yi wuf ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a jikin wani badakare ya datse wuyan Sarki Uhaisu.
Kaico! Inda a ce mutum ya na wannan waje lokacin da Sarki Uhaisu ya yi irin wannan mutuwar ta wulakanci dole ne ya yi farin ciki ya yiwa Allah godiya bisa ganin mutuwar AZZALUMI.
A dai-dai lokacin ne yarinya Lazimat ta samu nasarar hallaka shugaba Yesiran ta hanyar soka mashi kibiya a kan ƙahon zuciyarshi ya yi mutuwar banza.
Sa'adda dakarun marigayi Uhaisu suka yi arba da gawar jagoran su sai suka zubar da makamansu suka miƙa wuya.
A wannan rana aka shiga izuwa birnin Darul-kashmal aka musuluntar da gaba ɗaya jama'ar birnin, aka fito da dukkan fursunonin dake kurkukun, aka karya gumaka da ababan bauta.
Tsawon kwani uku aka shafe kowa ya yi jinyar raunin dake jikinshi. Sannan aka ɗora yarima Shaiban abisa karagar mulki, bayan an ɗaura auren shi da da Jaruma Nabihat da Jaruma Zulfirat.
Najwas kuwa ya zamo angon 'yan mata uku wato
Khadijah, Luwaisat da Shamirat, kuma yazamo waziri ga yarima Shaiban.
Mafarauci Najwas kuwa ya zamo shugaban majalisar dokokin birnin Darul-kashmal.
Sheikh ABDULLAH IBN zayyad yazamo jagoran harkar addinin musulunci da amsa fatawa na birnin.
Yarinya Lazimat kuwa ta zamo wacce zata gaji sarkin yaƙin birnin wato shugaba Yesiran.
Tun daga wannan rana aka kawo ƙarshen FATAUCIN BAYI a nahiyar baki ɗaya addinin Musulunci ya mamaye ko ina, sarakunan dake nahiyar da kansu suke zuwa su miƙa wuya su karɓi addinin Musulunci, saboda mulkin adalci da yarima Shaiban ke gudanarwa saboda HASKEN MUSULMI.


Ƙarshe


ALHAMDULLILAHI


A nan na kawo ƙarshen wannan ƙasaitaccen littafi nawa mai taken FATAUCIN BAYI.
Ubangiji ya haɗa mu cikin laɗan, ya yafe mana kusakuren da muka yi.
Zaku iya samun litattafan mu a yanar gizo (Google) idan kuka rubuta
SUFINOVELS.COM




Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.


MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment