Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

01/07/2019 à 15:27 - Les messages envoyés dans cette discussion et les appels sont désormais protégés avec le chiffrement de bout en bout. Appuyez pour plus d'informations.
01/07/2019 à 15:27 - Cette discussion est entre vous et un compte professionnel. Appuyez pour plus d'informations.
21/07/2019 à 11:47 - Cette discussion est entre vous et un compte professionnel. Appuyez pour plus d'informations.
05/08/2019 à 12:54 - Cette discussion est entre vous et un compte professionnel. Appuyez pour plus d'informations.
06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

*NI DA YAYA AL'AMEEN*

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


*STORY AND WRITING*

BY

*RAHEENAT M ABBAKAR*
_(Heenat)_


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHEEM*


*DUKKAN GODIYA DA YABO SUN TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DA YA BANI IKON DAWOWA CIKIN WANI SABON LITTAFIN, TSIRA DA AMINCI SU K'ARA TABBATA GA ANNIBINMU FARKON K'AGA K'ARSHEN AIKA WATO ANNABI MUHAMMDU S.A.W*.


*WANNAN LABARIN K'IRK'IRARRAN LABARINE BANYISHI DAN WATA KO WANI BA, DAN HAKA A KIYAYE JUYA MIN LABARI TA KO WANI IRIN SIGA*


```WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA CE GAREKU MASOYAN K'WARAI, FAUZIYYA MUHAMMAD WAKILI, SHAFA'ATU BALA BABA, AISHA NICHOI, MAMAN LABYB MAMIENMU, ADAMA TANIMU A BIYE, HAK'IK'I KUNA NUNAWA RAHEENAT SOYAYYA, DAN HAKA LITTAFIN NAKU NE.```



*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 1




Tafe suke a mota sai rusan kuka takeyi kamar wanda aka ce mata mahaifiyarta ta mutu, yanda na lura da kukan nata harda na shagwab'a ma, shi ko duk da kasancewar yana jin kukan nata har k'asan ransa bai saka ya daina tuk'in nasa ba ko kuma yayi yunk'urin rarrashinta, dan abinda ya sakata kukan shi nashi b'angaren farin ciki ya saka shi.


Jin kukan nata bana k'are bane yasa ya taka wani mahaukacin birki wanda sai da *Meenat* wanda take kuka ta hantsila sannan ta dawo ta zauna a mazauninta, take kuma kukan da take ya tsaya cak ta zaro manyan idanunta waje saboda tsananin tsoro.

Ganin yanda ta firgita yasa *Al'ameen* fashewa da dariya yace "ya kika bar kukan kuma, ai da kin ci gaba da kukanki tinda Abbie ne ya mutu. "


Wani kukan ta fashe dashi tana kai masa bugu, shi ko me zaiyi in ba dariya ba, dariya yakeyi yana fad'in "dukeni *Meenat* indai zai saka kiji sanyi a ranki. "


Sai da taji hannunta ya fara zafi sannan tabar dukanshi tare da jingina kanta a kafad'arsa tana sakin ajiyar zuciya, a hankali ta bud'e baki tace "yah *Al'ameen* wai baka tausayi na ne.?"


Ajiyar zuciya ya sauke ya d'ago da kanta ya kalli cikin idanunta sannan yace " *Meenat* me yasa zanji tausayinki bayan kina kuka ne akan abinda ya kamata kiyi farin ciki. "

*Meenat* tace "farin ciki?!! Farin ciki fa kake cewa inyi yah *Al'ameen*, ta yaya zanyi farin ciki bayan wanda nake so ya bar ni, wanda nake so ne fa aka rabamu dashi, shine kake cewa nayi farin ciki, shine kake cewa kar nayi kuka.?"

Murmushi *Al'ameen* yayi yace "to gani nayi fa mahaifiyarshi ce tace bata sonshi dake, k'iri-k'iri ta nuna miki k'iyayya, to dan yanzu ya kiraki yace an saka masa ranar aure da y'ar uwarsa sai ya zama abin kuka ? Ni zatona kuka ba naki bane, saboda ko aurensa kikayi ba zakiyi farin ciki ba, ni wallahi murna ma nayi miki, gara yaje can ya auri 'yar uwarsan, uwarsa kuwa taje ta bak'in halinta badai k'anwata ba. "


Shagwab'e fuska *Meenat* tayi tace "to amma ai shi yana sona ni ma ina sonsa."

Cike da jin haushi *Al'ameen* ya tayar da motan yana fad'in "to ai sai kije ki auresa, kuma wallahi kika k'ara cika min kunni da kukanki sai na tsayar da motar a ajiyeki sai dai ki nemi taxi ya k'araso dake gida. "


Turo baki tayi gaba cike da shagab'a tace "yah *Al'ameen* kai baka san soyayya bane shi yasa. "


*Al'ameen* bai san sanda ya k'ara taka wani Burkina ba ya kalleta yace "bansan soyayya ba kika ce *Meenat*,? To kallo ni nan. "

Kamar yanda yace aiko ta d'ago ta zuba masa ido shima d'in kuma ita yake kallo, cikin wata irin murya yace "me kika gani cikin idanuna.?"

Kau da kanta gefe tayi saboda irin tasirin da idanunsa yakeyi mata ajiki a duk lokacin da ta kallesa tace "ni ban ga komai ba. "

Murmushi yayi ya tayar da motar yana fad'in "k'arya kike wallahi"

Tab'e baki tayi tace "to ai kai idanun naka ko yaushe a haka suke, mutum ba zai iya kallonsu na mintuna biyu ba ma saboda tsaban kwarjininsu. "


"Ashe dai ki ce gwarjinin sukayi miki kika kasa ka gano abinda suke cikinsu. "


*Meenat* tace "ni dan Allah k'aleni naji da abinda yake damuna. "


Murmushi *Al'ameen* yayi ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya ci gaba da tuk'insa.

Kaitsaye unguwar nasara g.r.a suka nufa, daidai k'ofar wani tamfatsetsen gida naga yayi horn, me gadi ne ya lek'o ganin motar *Al'ameen* ne yasa ya koma ya bud'e masa da sauri shi kuma ya danna hancin motar nasa cikin gidan.



Suna shiga ko parking bai gama yi ba *Meenat* ta bud'e ta fice da gudu tayi cikin gidan ko tsaya ta d'auki kayan siyayyar da suka siyo ba tayi ba, girgiza kai *Al'ameen* yayi ya bita da kallo sannan ya k'arasa gyara parking ya d'auki ledan kayan shima ya fito ya nufi cikin gida.


Da sallama ya shiga falon gidan, *Ummi* da take zaune a falon ne ta amsa masa sallamar tana fad'in "d'ana har kun dawo. ?"

Zama yayi saman kujera yana fad'in "eh mun dawo *Ummi*. "


"To sannunku da dawowa, amma me ya sami mutuniyar taka ne naga ta zo ta wuce ranta a b'ace ina mata magana amma ko ta kulani. ?"

Murmushi *Al'ameen* yayi yace "hmmm *Ummi* kinsan halin rigimar *Meenat* sarai dai, kawai muna kan hanyar dawowa ne *Salis* ya kirata yake fad'a mata an saka ranar aurensa da 'yar uwarsa nan da sati biyu shine fa ta d'aga hankalinta take tayi min kuka. "

Tsaki *Ummi* tayi tace "au akan hakan ne take wannan kumburin, ni ai gara hakan ma, dama ni ba sonta dashi nakeyi ba, dan ko ta auresa mahaifiyarsa ba zata barsu suyi farin ciki ba tunda bata sonta. "

*Al'ameen* yace "nima haka na fad'a mata, amma ita so ya rufe mata ido."

"Allah ya kyauta" cewar *Ummi*

Ameen *Al'ameen* yace yana mik'ewa, sannan yace " *Ummi* ga kayan nan ki bata ni zan shiga gida, sai zuwa anjuma zan dawo na k'ara rarrashinta domin nasan yanzu ba zata saurareni ba. "

Murmushi *Ummi* tayi tace "da kanta ma zata biyoka na sani, domin shak'uwarku da juna ya wuce misali, ka gaida min da Ummar taka in ka shiga gidan. "

Murmushi shima yayi ya nufi hanyar fita yana fad'in "zata ji *Ummi*. "


*************


*Al'ameen* yana fitowa gidan dake manne dana su *Meenat* na ga ya shiga, gidan bashi da banbanci dana su *Meenat* hatta da fenti kuwa, tagwayen gida kenan wanda mamallakanta suma suka kasance tagwaye.


Da sallama ya shiga k'ayatatcen falon wanda bashi da banbanci dana gidansu *Meenat*, komai na falon irin d'aya ne da wancen, in ka shiga wancen gidan ka dawo ka shiga wannan ba zaka banbaceau ba, cewa zakayi gida d'aya ka shiga.

*Umma* ce da take fitowa daga kitchen ta amsa masa sallamar tana fad'in "ina ka bar min d'iyar tawa ne. ?"

Fad'awa *Al'ameen* yayi saman kujera yana fad'in "d'iyarki ko y'ar rigima, tana can tana kukan an sakawa *Salis* ranar aure. "
Ajiye abincin hannunta Umma tayi a saman dining sannan tace "ni bansan maitan me *Meenat* takeyi ba akan wannan yaron, inda aka ce ba'a sonka to meye na tusa kai.?"

Tab'e baki *Al'ameen* yayi yace "ohon mata."

Cikie da jimami Umma tace "amma saboda Allah tana kuka shine ka tawo ka barta ba ka tsaya ka rarrasheta ba. ?"

Mik'ewa yayi tsaye yace "Umma kin sani sarai bana son damuwar *Meenat* bare har naga hawayenta, amma a wannan gab'ar ba zan iya rarrashinta ba, saboda ni banga abin da zai sa ta d'aga hankalinta ba, in ta hak'ura da kanta zata tawo nemana, bari naje nayi wanka na d'an kwanta na huta *Umma*. "
Yana gama fad'in hakan ya nufi hanyar d'akinsa.



Da kallo Umma ta bishi tana fad'i afili "ni har yanzu na kasa gane wani irin so yaran nan sukeyiwa junansu, in kayi zargin soyayya tsakaninsu sai su zo su kifar da kai ka kasa gane komai kuma. "

Ta dad'e a tsaye tana sak'e-sak'e kafin tace "Allah ya kyauta."
Ta nufi kitchen tana me ci gaba da aikinta.


**********


*Al'ameen* yana shiga d'aki toilet ya fad'a ya shek'o wanka abinsa, yana fitowa gaban dressing mirror ya nufa yayi shafe-shafensa sannan ya nufi closet d'insa ya bud'a ya d'auko wani wando three quarter da wata riga singlet ya sanya, yana kammala ya koma gaban mirror ya fashe jikinsa da turaruka sannan ya d'auki computer d'insa da take saman wani d'an k'aramin tebur ya haye gado.

Yana bud'e computer d'in hoton *Meenat* ce ya bayyana saman screen d'in computern tana dariya, shima bai san lokacin daya saki murmushi ba ya kai hannu ya shafi fuskarta yace "I love you so much my *Meenat*" tayi kyau sosai cikin hoton, sanye take da k'ananun kaya riga da wando kanta babu d'ankwali k'ananun kitson kanta sun zubo saman kafad'unta, daga ganin hoton an d'aukesa ne cikin yanayin farin ciki.

Ya jima yana kallon hoton kafin ya shiga ya fara abinda zaiyi...






Muje zuwa🥰





More comment more typing





*Heenat ce💋*
06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

*NI DA YAYA AL'AMEEN*

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


*STORY AND WRITING*

BY

*RAHEENAT M ABBAKAR*
_(Heenat)_


_WAYYO DAD'I KARKA KASHENI😄 BARNI DA RAINA NA CI GABA DA GANIN COMMENT D'IN MASOYANA😂, HAK'IK'A NI RAHEENAT YAU NA GA RUWAN COMMENT TARE DA ADDU'OINKU READER'S, KUMA HAKAN BA K'ARAMIN DAD'I YAYI MIN BA WALLAHI, INA SONKU MASOYANA, KU CI GABA DA SAMBAD'O COMMENT NI KUMA NAYI ALK'AWARIN SAMB'A MUKU TYPING AKAI AKAI🥰😁_


SADAUKARWA GA

*MAMAN LABYB* *(MAMIEN MU)*
*FAUZIYYA MUHAMMAD WAKILI*
*SHAFA'ATU BALA BABA*
*ADAMA TANIMU A BIYE*
*AISHA NICHOI*


MARUBUCIYAR

*1 KOMAI YAYI FARKO....*
*2 HALIN RAYUWA*
*3 RAYUWAR SAUDA*
*4 RAYUWAR HANEEFA*
*5 MAHAK'URCI....*
*6 RUK'AYYATU*
*7 RAINA FANSA NE GARETA*
Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN*


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 2





Yana cikin aikinsa a computer yaji a turo k'ofar d'akin an shiga da sallama, d'ago kai yayi ya zuba mata ido yana kallo, sanye take cikin wasu riga da wando yar kanti, rigar har gwiwa take yayin da wandon ya kasance fencil ne, wandon fari ne k'ar yayin da rigar kuma pink colour ne mai adon fari, wani siririn gyale ne ta rataya akanta fari, tayi kyau sosai cikin katan yayin da fuskarta tayi fayau kasancewar babu komai cikinta, ma'ana ba tayi makeup ba.

Takowa ta farayi a hankali gurin gadon tana turo baki gaba alamar shagwab'a, shiko *Al'ameen* har lokacin idanunsa na kanta, zama taje tayi gefensa ba tare da tace dashi komai ba.

Ajiyar zuciya ya sauke yace "my *Meena* fushi kikeyi da yayan naki.?"

D'ago manyan idonta tayi ta watsa masa su ba tare da tayi magana ba, rufe computern yayi ya juyo sosai ya fuskanceta cikin taushin murya yace " *Meenat* shirunki na iya tarwatsa zuciyar *Al'ameen*, dan Allah kice wani abu. "

Hawaye ne suka fara zuba mata, cikin wani irin rud'ewa wanda ni raheenat yayi matuk'ar bani mamaki naga *Al'ameen* ya kai hannu yana share mata hawayen yana fad'in "dan Allah kibar zubar min da wad'annan tsadaddun hawayen, kin kuwa san zubar hawayenki kamar zubar ruwan dalma ne a zuciyata, daina kuka my meenat fad'a min damuwarki. "

Cikin muryar kuka tace "kar ka rink'ayi kamar baka san komai ba mana yah *Al'ameen*, me yasa ne kuka kasa fahimtar irin rad'ad'in da na keji a zuciyata ce ? Yah *Al'ameen* ina son *Salis* amma an rabamu da k'arfi da yaji, ku kuma kun kasa fahimtar halin da zuciyata take ciki, dan dama ba sona kukeyi dashi ba, ya kuke so nayi yah *Al'ameen*, me yasa aka kasa samun wanda zai taushi zuciyata cikinku ? Har dakai ma yayah wanda nake ganin in kowa ba zai fahimceni ba kai zaka fahimceni."


Hannunta *Al'ameen* ya kamo ya rik'e yana kallon cikin idanta yace "yanzu na fahimceki *Meenat*, ina so ki sakawa zuciyarki hak'uri dan Allah, ki sani komai da kika ga ya faru da sanin Allah, in *Salis* mijinki ne wallahi komai rintsi sai kin aureshi, ko kin manta babu mai auren matar wani ne ?, to da wannan nake son ki ajiye komai gefe ki rungumi k'addara, in Allah yayi da aure tsakaninki da *Salis* kina zaman zamanki zaki ga ya dawo gareki, in kuma babu aure tsakaninki dashi sai kiga ya fito miki da wani zarkad'ed'an saurayin kamar yayanki, ko bakya son miji irina.?"
Ya k'arasa maganar da sigar zolaya.

Murmushi ta saki tare da kai masa bugun wasa tace "kai!!! Yayah ai kai mijin manyan mata ne ba irina y'an sakayau ba. "
Ta k'arasa maganar da dariya.

Had'e fuska *Al'ameen* yayi yana hararanta, saurin gintse dariyarta tayi tana fad'in "sorry yayah."

Murd'a kunninta yayi yace "nak'i sorryn."

"Wayyo kunnina, yayah da zafi fa. "

Murmushi yayi yace "ai nasan da zafin nayi miki, ke in kika samu miji kamata ma ai kin more, amma saboda kin rainani sai ki rink'a fad'a min duk abinda yazo bakinki. "

Turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "wallahi da gaske nakeyi yayah kayi min girma, kalleni fa. "
Ta mik'e tana juya jikinta a gabansa cikin sangarta da tab'ara, dan bana ce yarinta ba, wai ita a dole ya kalleta ya gani.

Shi ko *Al'ameen* gaba d'aya ya shagalta gurin kallonta, zuciyarsa na k'ara narkuwa cikin soyayyarta wanda ita ta kasa gane hakan.

Rintse idonsa yayi yana ya mutsa gashin kansa cikin wani irin yanayi, har *Meenat* tazo ta zauna kusa dashi bai sani ba, muryarta yaji kawai tana cewa "yah *Al'ameen* lafiya.?"

Bud'e idonsa yayi ya kalleta yace "ina sonki my meenat. "

Murmushi tayi tace "nima ina sonka yayana. "

Wani irin murmushi yayi tare da lumshe idanunsa, ita kuwa *Meenat* ko ajikinta saboda ba yau ne suka saba irin wannan ba, tun tana yarinya take jin kalmar so daga bakin *Al'ameen*, kuma a kullum in ya fad'a mata ba ta d'aukarsa da wani abu face soyayyar jini d'aya.


_Niko nace kinyi kuskuren fahimta Ameenatu😄_



*Meenat* ce tace "yah *Al'ameen* bani wayarka na buga game d'in nan..."

Murmushi yayi yana yi mata nuni da wayar nashi dake kan seat-drower da hannunsa.

Mik'ewa tayi ta d'auko ta dawo ta zauna ta fara buga game d'in cike da nishad'i.

Shiko Al'ameen kallonta yayi a ransa yace "Meenat kenan, yanzu har ta manta da damuwarta. "
Girgiza kai yayi yana murmushi ya janyo computer d'insa ya ci gaba da aikinsa yanayi yana kallon Meenat lokaci zuwa lokaci wacce ta mayar da hankalinta kacokan kan game d'in da take bugawa.



Kiran sallar magriba ne yasa *Meenat* ajiye wayar ta mik'e ta kalli *Al'ameen* tace "yayah ga wayarka nan ni zanje nayi sallah. "

Shima mik'ewan yayi ya nufi hanyar toilet yana fad'in "ajiyeshi inda kika d'auka nima alola zanyi na wuce masallaci. "

Ajiyewa tayi kamar yanda yace sannan ta fice daga d'akin.


Tana fitowa suka ci karo da *Abba* wanda ya fito zaije masallaci, gaisheshi *Meenat* tayi tare dayi masa sannu da zuwa dan tasan bai jima da dawowa ba, amsa mata yayi cikin sakin fuska yana fad'in "maza kije kiyi sallah *Meenat* ni na tafi masallaci gashi can za'a tayar. "

To tace ta nufi d'akin *Umma* shi kuma *Abba* ya fice da d'an saurinsa.

Kan sallaya ta taras da *Umma* ta tayar da sallah, dan haka itama sai ta nufi toilet ta d'auro alolan tazo ta saka hijjabin *Umma* ta kabbara nata sallar.


Sunanan zaune suna lazimi aka kira isha'i, nan suka mik'e suka kawo nasu, sai da sukayi shafa'i da wutiri tare da addu'oi sannan suka mik'e suka fito zuwa dining.

Zaune suka samu *Al'ameen* a dining d'in yana danne-dannan wayarsa, ganinsu ne yasa ya ajiye wayar yace "sannu da fitowa *Umma* "


Jan kujera tayi ta zauna sannan tace "yauwa sannu *Al'ameen,* ina ka baro Abban naka da sauran 'yan uwanka.?"

Ya bud'e baki zaiyi magana kenan sai suka jiyo sallamar Abban da Usman da Aliyu k'anninsa.

Amsa musu sallamar sukayi sannan suka k'araso suka zazzauna suma.

Meenat ce ta fara saving d'insu d'aya bayan d'aya tana turawa kowa gabanshi, sai da ta kammala sannan ta zuba nata ta zauna ta fara ci itama.


*******


Suna kammala cin abincin *Meenat* ta mik'e tace "Abba Umma ni na tafi saida safenku. "

Kallonta sukayi da murmushi a fuskarsu Umma ce tace "mu kwana lafiya Meenat. "

Abba ma dai cewa yayi "sai da safe yar gidan Abbinta. "


Murmushi tayi ta kalli su Usman tace "yah Usman yah Aliyu mu kwana lafiyanku. "
Tana gama fad'in hakan ta nufi hanyar k'ofa.

Had'a baki sukayi gurin cewa "Allah ya tashe mu lafiya Meenat."

Al'ameen ne ya mik'e yabi bayanta yana cewa "wato ni ba za kiyi min sai da safen ba kenan.?"

D'an d'aga murya tayi tace "to ai nasan kai d'an rakiya nane. "

Da sauri ya taka ya bita yana cewa "tsaya ki fad'a min waye d'an rakiyar naki. "

Tana jinsa a bayanta ta kwasa a guje ya rufa mata baya, su kuwa su Abba da kallo suka bisu sunayi musu dariya...





Muje zuwa🥰




Ga mai k'orafi ko wani gyara yayi min magana ta wanann layin👇

07033643262

A shirye nake da amsar gyaranku ko k'orafinku readers🥰😘






*Heenat ce💋*
06/08/2019 à 10:53 - HASBUNALLAH: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

*NI DA YAYA AL'AMEEN*

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


*STORY AND WRITING*

BY

*RAHEENAT M ABBAKAR*
_(Heenat)_


MARUBUCIYAR

*1 KOMAI YAYI FARKO....*
*2 HALIN RAYUWA*
*3 RAYUWAR SAUDA*
*4 RAYUWAR HANEEFA*
*5 MAHAK'URCI....*
*6 RUK'AYYATU*
*7 RAINA FANSA NE GARETA*
Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN*


SADAUKARWA GA

*MAMAN LABYB (MAMIEN MU)*
*FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI*
*SHAFA'ATU BALA BABA*
*ADAMA TANIMU A BIYE*
*AISHA NICHOI*


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```



Page 3






Da gudun tare da sallama a bakinsu suka shiga falon su Meenat, Abby da Ummi da sauran y'an uwan Meenat da suke zaune suna hira ne suka bisu da kallo, domin hakan ba bak'on abu bane a gurin su, Abba ne ya fara magana yace "Al'ameen sai yaushe zaka girma kabar wasan yara da k'anwar naka ne wai.?"


Murmushi Ummi tayi tace "hmmm ai banga wannan ranar ba kuwa, dan kullum k'ara girma yakeyi amma yana biyewa Meenat suna shirme. "

Murmushi *Al'ameen* yayi yana sosa kansa cikin jin nauyi ya nemi guri ya zauna yace "Ummi ita ce fa ta kirani da d'an rakiya. "

Girgiza kai Ummi tayi tace "shine kai kuma ka biyota a guje ko. ?"

Dariya yayi yace "a'a Ummi ita ce dai ta fara gudu."

Abba ya amshe da cewa "kai kuma sai ka biye mata ko.?"


Dariya k'annin Meenat suka kwashe dashi, shi kuma Al'ameen ya had'e gira irin ba wasa d'in nan yace "ina wasa daku ne.?"

Aiko nan take suka gintse dariyarsu suna zare idanu, domin sun san yah Al'ameen babu wasa yanzu zai masge yaro, dan shi iya wasansa da shiriritarsa akan Meenat ce kad'ai, sauran k'anninsa kuwa tsoronsa su keji sosai.


Abba da Ummi ne suka mik'e suka shige ciki, nan suma su Isma'il suka mik'e suka nufi d'akunansu aka bar Meenat da Al'ameen zaune su kad'ai, kusa dashi Meenat ta koma ta zauna suka ci gaba da hirarsu har zuwa k'arfe 10:00pm, Al'ameen ne ya mik'e yana hamma yace "ni zan shiga gida na kwanta. "

Itama Meenat mik'ewar tayi tace "ok, muje na rakaka dan nima baccin nake ji. "

Baice komai ba sai nufar k'ofa da yayi ta mara masa baya, daidai get taja ta tsaya tace "to sai da safenmu yayah. "

Kallonta yayi yace "mu kwana lafiya k'anwata, gobe ki shirya da wuri karki saka nayi latti gurin aiki. "

Meenat tace "to yayah. "

Hannunta ya kamo ya sumbata yace "kiyi mafarkina bye. "

Murmushi tayi ta juya ta fara tafiya, har ta d'anyi nisa taji Al'ameen yace "Meenat!!"

Juyowa tayi tana kallonsa ba tare da tayi magana ba, shima kallontan yakeyi yace "dama cewa zanyi karki manta da addu'a. "

Wani murmushi ta sakin masa tace "insha Allah ba zan manta ba yayah. "
Tana gama fad'in hakan ta juya ta ci gaba da tafiya, sai da Al'ameen ya ga shigarta cikin gidan sannan ya fice daga gidan ya nufi nasu gidan.



*************


Washe gari misalin k'arfe bakwai da mintuna arba'in na safe Al'ameen ne ya fito cikin shirinshi na tafiya aiki, sallama yayi wa Umma wacce ke zaune a falo tana kallon sunna tv tayi masa addu'ar tsarewa dana dawowa lafiya sannan ya fice daga gidan.

Yana fitowa gidansu Meenat ya shige, da sallama ya shiga falon, Meenat ce ta amsa masa wacce take zaune saman dining tana break, k'arasawa yayi dining d'in yana fad'in "ke sai yanzu ne kike naki break d'in. ?"

Mik'ewa tayi tare da d'aukar jakarta dake saman dining d'in tace "ai nama gama muje kawai. "

"Ok, ina Ummi take.?"


"Ummi ba ta dad'e da hawa uptsar ba."


Be k'ara magana ba sai hanyar fita da ya nufa tabi bayansa.


Gurin motarsa da ya ajiye jiya ya nufa ya bud'e ya shiga, itama Meenat bud'ewa tayi ta shiga ta zauna, sai da ya tayar da motar nasa yayi ribas ya nufi get sannan Meeenat tace "good morning yah Al'ameen."

Kallonta yayi yace "morning how are you. ?"

"Am verry fine yayana. "


Murmushi yayi daidai lokacin da mai gadi ya bud'e mana get yace "k'arfe nawa zaku shiga lecture.?"

Meenat tace "k'arfe 9:00 ne. "


Agogon hannunsa ya kalla yace "da sauran time ashe. "



Babu wanda ya k'ara magana cikinsu har motarsu ta daidaita saman kwalta.




*************


Suna tafe Meenat nayi masa hira har suka isa B.U.K, parking Al'ameen yayi gurin ajiye motocin makarantar yana kallon agogon hannunsa, "k'arfe takwas da talatin da biyar. " Al'ameen ya fad'a a fili, sannan ya kalleta yace "to ni zan wuce asibiti k'arfe nawa zaku tashi na zo na d'aukeki.?"

Fari tayi da idanunta sannan tace "sai k'arfe biyu zan bar makaranta, yanzu zamu shiga 9 to 11, sannan 12 to 2. "

"Ok, zuwa k'arfen biyun zan zo. "

D'aukar jakarta tayi ta fice tana fad'in "sai ka zo, Allah ya kiyaye hanya. "


Ameen yace yana tayar da motarsa ya nufi inda suka fito, wato ya koma zoo road Inda asibitinsa yake.


**********


Duk da tarin aikin da yake dashi a asibitin amma yana ganin k'arfe biyu tayi ya ajiye komai ya rufo office d'in nasa ya shiga motarsa ya fice daga asibitin, kai tsaye b.u.k ya nufa, da zuwansa ya iske Meenat ita da wata k'awarta mai suna Suhailat tsaye bakin get tana jiransa, tana ganinsa tayiwa Suhailat sallama ta shiga suka kama hanya.


Suna tafe Meenat ta kalli Al'ameen tace "yah Al'ameen banyi tsammanin zaka dawo ba fa, dan nasan kana da aiki sosai a asibiti. "

Murmushi yayi yana ci gaba da tuk'insa yace "ai duk aikin da nake dashi ba zai hanani zuwa na kaiki gida ba, kinsan fa bana son direba yana kaiki ko da unguwa ne. "

Murmushi tayi cike da jin dad'in kulawar da yake bata tace "shi yasa kake da babban matsayi a zuciyata yah Al'ameen. "

Kallonta yayi ta gefen ido sannan yace "har yau Meenat baki bani matsayin da nake son kaiwa ba a zuciyarki. "

Da mamaki ta kallesa tace "wani irin matsayi kake son na baka bayan wanda na baka yayah.?"


Waigowa yayi ya kalleta sosai sannan yace "bar maganar

Please Login or Register in order to submit comment