Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[6/24, 10:49 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*


©️ XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*


PAGE-1


_Hi Mutanena,mutanen amana,gani na dawo fa ku shirya ku gyara Zama._
😻🤍


PLATEAU STATE,
JOS NORTH.
RingRoad.


Dauke take da tulin daurin kaya akanta hannunta kuma tana rike da rake tana gatsa tamkar mayunwacin zaki.
Tsohuwar dake gefenta suna tafiya ne ta ce, "Salame ai yau dai zan yi maganin Ilu duk iskancin da yake ji dashi da matar tashi sai na sauke masu shi kasa basu san cewa a zamanin ina daya daga cikin tantiran yan iskan kauye bane shiyasa suke mun wannan iskanci."
Sai da Salma ta gatsi rakenta kafin ta ce, "Aradun Allah kuwa Inna kar ki raga masu sam sam kar ki raga masu gwanda ayi maganinsu ai."
Ta karasa maganar suna tsaya daidai wani gida madaidaici baza ace da shi karami ba kuma ba za asa shi sahun manyan gidaje ba sai dai kam ba laifi ya tsaru wanda kallo guda za asama a tabbatar da cewa lallai mai gidan na da rufin asiri daidai gwargwado.


Buga gate din suke dukansu su biyu tamkar wa inda suke dakan sakwara.
Jiki na bari mai gadin ya bude yana, "Subhanallahi wasu gidahuman ne haka?"


Inna ta kalleshi ita da Salma kafin ta ce, "gidahumai? Ni kake cewa gidahuma? Na ce ka ci gidanku ka ci gidan ku to nan gidan Ɗana ne nice nan uwar illu mai gidan nan ka kiyaye tun kafin inyi tamola da kai da shegen kai kamar kwallon mangoro."


Mai gadi ya ce, "ehto ayi hakuri ranki yadade amman ni ba kan mangoro gareni ba."


Inna ta bude baki kafin ta ce, "Au da ance ma raina ba zai dade bane? To ahir dinka dadewa kan munyi kuma muna kan yi sannan kuma kace kanka bana mangoro bane?" Ta fada tana maka masa rankwashi aka.
Ita ko Salma me zata yi ban da dariya, "yawwa Inna wallahi ki kara masa har sai kan nasa ma ya koma irin na mangoron."


Hayaniya ce ta kaure tsakanin mai gadi da Inna har sai dai Alhaji Ismail da Matarsa Hajiya Maryam suka fito.
Kaka na ganinsu ta fashe da kuka tana faduwa kasa.
Hawaye da majina shaɓe-shaɓe a fuska ta ce, "Ilu wai har kaine zaka dauko wanda zai dunga tozartani a gidan nan? Har kaine zaka dauko wanda zai ci mini mutunci."
Durkusawa Salma ta yi tana share mata hawayen tare da fadin, "kiyi hakuri Inna mu koma kauye kawai tunda tun a kofa aka fara yi mana kora da hali kiyi hakuri ni ina sonki bana so ki mutu." Ta karasa maganar ita ma tana kakulo nata kukan.


Da sauri Hajiya Maryam ta karasa tana rike Inna.
Inna ta bangajeta tana , "Dalla cen guzumar munafuka ai gwamda kowa dake ni barni bana son munafurci."


Alhaji Ismail ya kalli mai gadi ya ce, "kai ko me yasa zaka yi haka? Baka san cewa wannan din mahaifiyata ba ce?"


Mai gadi zaiyi magana kenan Inna ta tunkure shi da kafarta sai da ya fadi a kasa ta ce, "munafiki ne ai kuma indai ina gidan nan sai na gyara masa zama."


Karasawa Alhaji Ismail ya yi da kanshi ya daga Inna yana, "kiyi hakuri Inna In sha Allah ba zai kara ba."
Tashi tayi tana tafiya dakyar kamar wacce aka ma duka.
Suna tafiya Salma ta juya tayiwa mai gadi Gwalo, can ma sai ga Inna ta juyo da tsukeken bakinta ta masa gwalon.
Sake baki ya yi yana mamaki
A zahiri ya ce, "Ikon Allah gaskiya akwai matsala babba a gidannan."
Suna shiga cikin gidan salma ta aje tulin kayanta ta fice.


★★
Ya fito daga wanka kenan daga shi sai towel dinsa a daure karasa ya yi daidai gun windown dakinsa yana budewa.
Budewan da zaiyi fitsari ne ya fara sauka masa a fuska.
A gigice ya daga kai suka yi ido biyu da Salma ce tsaye ta haye kan setin windown tana tsura fitsarinta hankali kwance a tsaye.
Kallonshi ta yi tana murguda baki, "ji wani kasurgumin dan iska ina fitsari yana leƙena."


Kasa hadiye yawu Abdul-Saheer ya yi kasancewar sa mutum mai zafin rai cikin sauri ya dauki belt ya fita ita kuwa Salma har lokacin tana zaune abunta tana, "gwanda ma da ka tafi don ni wallahi bana wasa da yara."
Saukar Belt taji a gadon bayanta ta tsalla wani irin ihu.
, "Ance miki nan gun fitsari ne da zaki zo kina yiwa mutane?"
Ya daga zai kara mata tayi wani irin tsalle ta shige ciki da gudu tana, "kwarto jama'a kwarto yana dukana dan iska ne."


Tsaki Saheer ya yi ya koma dakinsa kai tsaye toilet ya nufa zai kara yin wankan domin koda yace zai wanke iya gun ne yata tsarguwa.


Salma na shiga ta birkitasu duka suka fito basu ga kowa ba.
Inna ta ce, "daga zuwa birni har za a fyeɗe mun jika? Na ce har za a fyeɗe? To wallahi sai na dau mataki zan baku mamaki ga dukkan alamu dukanku yan gidannan sai na gyara zaman duwawunku domin a karkace suke duk."


Haka Inna ta zauna Salma na jikinta ance su je suyi wanka fur sunƙi.


Saheer ne ya fito cikin shirinsa zai fita dake weekend ne.
Ko sallamar da ya fara bata bari ya karasa ba ta katse shi.
ta fara nuna shi tana, "Inna wallahi wallahi shine kuma har lekani ya yi kuma ya dakeni."
Tashi tsaye Inna tayi tana rike kwankwaso, "Iya ah lallai wato gadon uwarka ka yi Sahaaru? Gadon iskanci da fitsara Kodayake ai kasha a wancen tamulallen nonon uwar taka wacce ko nawa ya fita fasali to baka isa ba yadda ka fara gane mun ita sai ka aureta domin ka riga ka gama da ita ba zan bar gidan nan ba sai ka aureta e na ce sai ka auri salame."
Daga Saheer har Iyayen nasa suman tsaye sukai sun gagara cewa komai.
Salma ta.....






08103080717
Urs Xayyeesherthou
[6/25, 11:07 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*


©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*


PAGE-2


Ta ce, "Aa fa Inna ni bana son auren dan iska yaje ya iskanta ni a banza a wofi."
Tsaki Inna ta yi kafin ta ce, "Ya iskanta ki ban da tambadar da ya fara miki tun yanzu? Aure ba fashi."
Ta ja kunnenta ta fada mata magana suka dago suna tafi da dariya kafin Inna ta gyara zama ta ce, "Yawwa ilu na san ka ji me na ce ai ko? Ko sai na maimaita ne? Ina so Sahaaru Ɗanka ya auri yar uwarsa salamatu."


Kallon kallo suka fara yiwa juna.
Momy,Daddy da Saheer.
Dady ya ce, "To Inna In sha Allah za ayi hakan."
Dauko garin goronta ta yi ta zuba a baki tana mamula domin tsabar tsufa gabadaya hakoran sun wawushe.
Ta ce, "Ah to ka ma Musa mana bawai naga kuna kifi kifi da ido ba kai da matar ta ka mai baki kamar tsohuwar jaɓa ga hanci kamar agwagwa na magana, eheem so nake a daura masu aure gobe da safen nan."


Wani irin mumman faduwa gaban Saheer ya yi take ya fice daga dakin cikin sauri, Momynsa ma ta fice.
Dady ya ce, "To Inna amman kinsan ba a gaggawa a aure ki bari a shirya komai a tsanake tukunna kamar zai fi."


Galla masa harara ta yi kafin ta ce, "ji mun wani salon rashin daraja da guntun iskanci, me za a shirya? Na ce me za a shirya? Ba abun da za a shirya kuma aure gobe nake so a daura, yoo Ɗan naka ma da rufa mai asiri za ayi ayi masa auren kafin ya gama tambaɗewa ,tunda ya fara leƙen duniya kuma ai gaba gaba sai yawo a ciki to ba dani ba na ce ma ba dani ba auren nan gobe gobe kafin ka dawo daga asuba ka tabbatar da cewa ka zo mun da albishir andaura auren sahaaru da Salamatu in ba haka ba kuwa kasani sarai zan iya zan iya daga maka nono ka bi duniya ka watangale ."


Jiki a sanyaye ya amsata ba don yaso ba kuma ba don yasan ta ina zai bullowa lamarinta ba.
Babban tashin hankalin ma bai san Dalilin zuwansu ba zato ba tsammani ita da bata son zaman birni.


Kwatsam kuwa sai jin mai gadi ya yi yana sheda cewa ana sallama da shi.
Bayan ya fita ya ga yaron fadar mai garin kauyesu ne.


Bayan sun gaisa yake sheda masa cewa Mai gari ne ya aiko shi domin sheda masa cewa Salma da Inna sun yi laifi babba da ake nemansu ruwa a jallo domin kuwa sun kama matar mai garin duka su biyu sun mata dukan tsiya wanda har sai da ya kai ga ta suma sanadin kawai Don Salma ta kwacewa yaronta mangoro ta yi magana suka hadu suka dunga jibgarta kamar sun samu kayan wanki har sai da suka ga ta daina motsawa suka kwashe kayansu suka bar garin.


Sallallami Alhaji Ismail ya fara ya bashi hakuri tare da sanar da shi cewa ya bawa mai gari ma hakuri kuma In sha Allah yana nan tafe zuwa kauyen shi ma.


Jiki a mace ya koma cikin gidan ya nufi dakin Momy.
Tagumi ya yi ya zauna ya yi shiru.
Ta zauna gefen shi tana fadin, "Alhaji ba zama kayi tagumi bane mafita fa tunani zaka yi yadda za a bullowa lamarin domin kasan halin Inna inta kafe akan abu."


Numfasawa Dady ya yi kafin ya ce, "Hmm abun ne na rasa da wanne zan ji, yanzu fa zuwa akai nemansu daga kauye na ce basa nan na bada hakuri ga wannan batun auren da ta taso da shi kuma sannan Saheer ma ko kadan ba zai iya rayuwa da Salma ba domin yarinyar an riga an gama sakaltata gyaruwarta da nutsuwarta zaiyi wahala sosai."


Momy ta ce, "to ya za ayi karshen zancen dai kawai ka yi mata biyayya shi ma Saheer din ya yi hakuri."
Dafe kai Dady ya yi ya ce, "abune mai wahala hakan ba zan so in cutar da Ɗana da hanuna ba dole zansan yadda zan bullowa lamarin."
Ya fada yana tashi.
"Bara in dan fita in dawo."


Saheer kuwa yana fita a gidan kai tsaye School ya nufa duk da cewa weekend ne domin ya ji bai son zaman gidan sam kuma daman gashi ba mai son hayaniya ba hakan yasa yaje ya bude office dinsa kawai ya zauna.


Saheer Namiji ne wanda ya amsa sunan namiji karfaffa domin kuwa wanda bai san shi ba zai iya alakanta da shi da jami'in tsaro kasancewar yanayinsa daya da nasu miskilanci,rashin son magana da rashin fara'a.
Baya cikin sahun farare kuma ba asa shi cikin sahun bakake ba,yana da kyawun gani daidai gwargwado wanda kowacce mace zatai burin mallaka,saboda miskilancinsa yasa ko mata bai kulawa abokinsa ma guda ɗaya ne kadai wanda ya aminta da shi.
Yana da tsafta da son gayu sosai daga nesa turaren jikinsa kan iya bayyanar da zuwansa waje sai dai yana da dabi'ar shan taba sigari wanda ta zame masa jiki musamman a lokutan da aka bata masa rai bai samun sukuni in bai zuƙa ba.


Yana zaune Inya tuna da abun da Salma ta mai da maganar Inna sai yaji ranshi ya baci Sosai ban da tsaki babu abun da yake.
Take ya kunna tabarsa yana sha.


Salma kuwa ko a jikinta dadi take ji har cikin ranta Inna ta ce mata inta aure shi zata zama hajiya babba tayi kudi su koma kauye su kori mai gari da matansa.


Salma irin yaran nan ne masu gaɓa-gaɓan jiki gata karamar yarinya da bata zarce sha uku ba amman girman jiki da kibarta ya kai na mai shekara Ashirin.
Baƙace sosai amman irin bakin nan mai kyau da sheƙi.


★★★Salma da Inna zaune suke a filin gidan sun shinfida taburma sunyi kane-kane su ci wannan su ci wancen.


Inna na ganin Saheer ya shigo da mota ta kalleta ta ce, "yawwa ga mijinki nan ya dawo maza tashi kije ki karbe shi ki mishi sannu da dawowa gwanda ki fara koya tun yanzu."
Aikuwa tashi Salma tayi tinki tinki ta je gefen motar ta tsaya.
Yana fitowa ta washe baki tana kokarin karban file hannunshi ta washe baki, "Barka da Zuwa Mijina."
Wani takaicine ya sarƙafi zuciyar Saheer ya bita da wani gigitaccen kallo yana bisge hannunshi sai da ta fadi.
Kafin Inna ta bude baki har salma ta tashi tana daga hannunta sai setin marar Saheer ta sauke masa.
Bai san lokacin da ya saki wata kara ba,ta zura a guje.
Ita kuwa Inna me zata yi ban da dariya.
"Maddallah yoo daman Salma in baki rama ba ai ke ba jinina bace tunda shi ya yi gadon figaggiyar rashin daraja ke lukuta na koya miki."


Mai gadi ne da sauri ya karaso ya rike Saheer.....




08103080717
Comments, Share and like Fisabilillah.
Urs Xayyeesherthou 🤍🌾
[6/26, 10:16 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*


©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*


PAGE-3


Ganin yadda Saheer ya fara muradadawa lokaci guda kuma yanayinsa ya canja,hakan Yasa Inna da Salma tashi a guje.
Suna tashi kuwa aka dauke wuta dake dare ya yi.
Karo suka ci da juna karaf goshin Salma ana Inna.


Wata irin kara ta yi jiki na rawa Inna ta ce, "Na shiga uku na lalace na shiga ukuna ni Shatou, Lawakiri ka yi mun rai aradun Allah bani na yi kisan ba Jikata ce, jikata Salame ce." Inna ta fada hannunta dauke a fuskarta ta rufe idanunta da daya,dayan kuma ta kankame goshinta da yaji bugu.


Har an kunna Gen bata sani ba tana kankame a tsugune tana ta sambatu lawakiri ya yi hakuri ya mata rai lokacin baiyi ba tukunna da saura.
Sautin dariyar Salma ta jiyo akanta tana, "Kai Inna Sarkin tsoro karo muka yi fa da goshi ba wani lawakiri."


A hankali Inna ta bude ido tana kif-kif da ido kamar karamar munafuka ta ja dogon numfashi, "Allah na gode maka, yoo ko salame wai haka goshinki ke da azaba kamar an turo roka? Wannan ai sai ki kashe mutum amman dai goshin nan naki kwai rashin daraja ba don ni da kaina na mulmula miki maɗiga ba lokacin da aka haifeki da na ce anguwar zomanki bata iya karban haihuwa ba."


Ita dai Salma dariya take harda shidewa.
Inna ta ce, "Muguwa yar masara ni rikeni in tashi don ina ji ma har fitsari na gama yi a jikina aradun Allah, jina nake fa rabi a duniya rabi a lahira."
Salma ta mika mata hannu ta tallafa mata ta tashi tana fadin , "Inna anji goshin manya ysn kin bani dariya yadda kika zauna dinnan nishadi kyauta."


Da haka suka shige cikin gidan suka baje a falo domin sunki shiga daki.


★Saheer kuwa mai gadi ne ya tallafa masa ya shiga daki domin mararsa ciwo take yi masa sosai ta rike.
Kwanciya ya yi na yan mintuna kafin ya tashi ya hada ruwan lipton ya sha.
Aransa ya kudarci cewa duk yadda za ayi sai ya kama Salma ya hukuntata.
A zahiri yake fadin, "wannan yarinyar sam bata da tarbiya babu shakka sai nayi maganinta na sa ta samu nutsuwa."
Ko cikin gidan bai shiga ba ya kulle kanshi a daki hatta sallah ma a ciki ya yi.


Salma da Inna na falo suna kuskus da tsoron cewa kar fa azo ace sun kashe Saheer.


Salma ta ce, "ni gwanda ma ya mutun ai yana nan kamar wani dan kasar waje."
Inna ta ce, "ke wawiyace matsalata dake salame gwanda ya rayun ai ki aure shi baza ki gane abun da nake nufi ba, ba don ba ba aure tsakaninki da uban shi ba ai da ubanshi zaki aura amman sai dai kash shi yasha Nono ya barwa Uwarki ta sha."
Suna cikin magana sai ga Alhaji Ismail ya shigo falon.


Durkusawa ya yi gaban Inna ya gaisheta sai ya yi shiru.
Fara wura hanci Inna tayi tana dagawa ganin ya shigo da leda ga kuma kamshi na tashi.
Ta ce, "Illu miye ne a ledar cen? Ji nake kamar kamshin gashasshiyar kaza miko min nan Salame."


Jiki na rawa Salma ta tashi taje ta dauko ta baje a gaban Inna suka bude.
Fara ci suka yi kamar sabin kamu musamman Inna da saidai ta mamula ba iya taunawan ma take ba.


Alhaji Ismail ya yi gyaran murya kafin ya ciro wani dumin kudi a aljihunsa ya ajewa Inna a gefetan tukunna ya ce, "Inna Daman ina neman alfarma ne ban sani ba ko zaki amince."
Inna na mamular nama ta ce, "ina jinka Illu illu dan albarka ina jinka ka yi gadon mahaifinta wajen sanin abun da nake so Illu nawa."


Dady ya ce, "daman kan auren Saheer da Salma ne,na ce me zai hana ki bari ta kara girma tukunna sai nake ga kamar ai tayi karama a yanzu za a cutar da it.....


Kafin ya karasa maganar ta fecar da kasar bakinta ta rike bango ta tashi tsaye ta kalli Salma ma ta ce, "ke salame tashi tsaye."
Salma ta tashi tana jan cinyar kaza.
Inna ta ce, "Yawwa juya gaba da baya."
Salma ta juya.
Ta ce, "to yi tafiya daga nan zuwa can."
Salma ta taka daga farkon falon har karshe.
Inna ta ce, "yawwa ince dai idanunka sun gani? Ko ta kara juyawa ne?"
Alhaji Ismail ya girgiza kai alamar aa.
Inna ta ce, "Yawwa batun aure ba fashi ka kalleta ka kara kallo." Ta nuna salma da hannu kafin ta ci gaba da fadin, "Diri iya diri gashi nan sassakar budurci iya sassaka gata nan,inma ƙirjin ne gashi nan a wadace dake gado tayi ba irin da shamulaliyar matarka ba,shi ma duwawun dai gashi nan kamar a dasa turmi ya zauna, mace iya mace son kowa kin wanda ya rasa salame ta kai,don haka ahir dunka da cewa tayi karama a aure ka cuceni ka kasheni da raina bayan danku ya fara leƙe mun ita,kai tsaya ma,wai kai bakasan diri ya gani ya furgice ba har yake kokarin fyedemun ita ? To ko yau na fadi na mutu indai Sahaaru bai auri salame ba ban yafe ma ba." Tana fada ta barke da kuka tana jan majina ta tattaro gefen zaninta tana gogewa.


Salma ma zama tayi tana kukan tana kwanciya jikin Inna.


Jiki na rawa Dady ya ce, "kiyi hakuri Don Allah Inna, kiyi shiru In sha Allah za ayi abin da kike so."


Inna na sheƙan majina ta ce, "Illu Indai ba so kake in hadiye zuciya in mutu ba ka hada Sahaaru da Salame ."
Murya na rawa ya ce, "e e In sha Allah Inna yanzu to kiyi shiru Don Allah."


Share hawayen ta yi ta dauki kudin da aje mata gefe tana, "wa innan kudin da su zan yiwa salame hadin amare, kai ma kuma kaje a hada danka ehee."
Salma ma ta share hawayen tana washe baki.


Dady ya ce, "amman za a bari zuwa jibi ko Inna? Kinga yanzu ban tanadi su goron daurin auren ba."


Inna ta ce, "e ba matsala Allah ya kaimu ai kamar yaune amman ka sani daga ranar ba dadi ba kari."


★★★Washegari.
Da sassafe Salma ta fice tana zaune gefen motar Saheer tana wasa da kasa dake wajen akwai kasa ita har ma ta manta da abun da ya hada su jiya.
Shi ko ya fito kenan ya shirya zai tafi school dake monday ne.
Aiko yana ganinta ya koma da sauri ya ciro belt.
Har ya fito sai kuma ya koma ya aje belt din tasa ya kara fitowa.
Ji tayi kawai an dauketa cak.
Ta fara wuntsili da kafa tana ihu hannunsa yasa ya rufe mata baki ya kaita dakin nasa yana shiga ya dauki tsimma ya rufe mata bakin ya daureta a jikin Window sannan ya dauko belt din ya......




08103080717
Urs Xayyeesherthou
[6/27, 9:54 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*


©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*


PAGE-4
Ya zabga mata a gadon baya, kara Salma take son yi amman babu hali saboda ya riga ya kulle bakin.
Tana ta wutsil wutsil da jiki tana kokarin kunce daurin da ya mata.
Cikin fushi Saheer ya kara sake mata Belt dinnan a jiki wanda don azaba sai da ta saki fitsari a gun ga wata irin zufar wahala da ta keto mata.
Jin karar abu na zuba ya kalli kasa, aiko idanunsa suka ci karo da fitsari na tsiyaya kan tais dinsa kamar famfo.
Wani takaicine ya kara sarƙafansa a zuciya.
Ya ce, "Wai ke wacce irin bagidajiyar kazamiyar yarinya ce? Fitsari? Fitsari zaki mun anan? Aiko sai kin goge shi tas da kayan jikin ki, kafin nan ma zaki kara zuwa ki hau mun mota inyi magana ki mun rashin kunya har ki kai mun duka mara?" Ya fada yana murɗa mata kunne.
A galabaice ta girgiza masa kai alamar e.
Ya kara sake mata belt din kafin ya ce, "zan kunce ki kuma ki cire wannan zanin naki mai dauda ki kwashe fitsarin nan tas."
Ya fada yana kunceta.
Salma ido ya yi fiki-fiki anji azaba.
Haka ya tasata a gaba ta cire zaninta tana kwashe fitsarin daga ita sai wani gajeran wando da dauda tasa ya canja launi domin yanayin fari garesa amman ya koma brown brown don azabar kazanta ga wani munafukin wari da ke tashi.


Kasa jure tsayuwarta agun Saheer ya yi,tun yana toshe hanci har ya gagara ya ce, "Just Go." Yana kara rufe hancinsa.
Ina Salma kam bata san me yake fada ba kara gogewa take.
A fusace ya ce, "Ya isa ki fita na ce."


Rungume Zaninta mai fitsarin ta yi ta fice da gudu sai da ta zaga daidai windown da yake tsaye ya yi tsuman tsaye ya tura kanta tana fadin, "Mugu azzalumi Dan Masara mai bakin Daddawa kan tafarnuwa aradun Allah sai na rama mai idon damusa kawai." Tana fada ta tattara yawo ta watsa masa daidai fuskarsa kafin ta arce a dari ta shige ciki.


Rikicewa Saheer ya yi take kansa ya fara wani gigitaccen ciwo,idanunsa suka kada suka yi ja.
Cikin sauri ya shiga toilet ya fara wanke fuskarsa yana wanken bakinsa.
Karshe sai da ya kara brush ya kara yin wanka yasa kaya.
Da sauri ya bar dakin domin gabadaya a tsarge yake da dakinma.


Ciki ya shiga domin gaida iyayen nasa, ya shiga dakin Momy ya gaidata har zai fita ta ce, "Saheer."
Ya juyo ya kalleta yana amsawa.
Ta ce, "sai dai ka yi hakuri kuma ka sa aranka cewa babu Ɗan da zaiyiwa iyayensa biyayya ya taɓe biyayya bata taba zama a banza ka da kasa komai aranka ka ji cewa kawai duk abun da Ubangiji ya tabbatar shine daidai a garemu duka."


Da mamaki ya kalli Momy domin sam bai gane inda ta nufa ba,don shi ya ma mance da wani batun auren shi da Salma.
Ya ce, "Momy ban gane ba,me ya ke faru wa?"


Momy ta ce, "magana nake akan aurenka da za a hada dana yar uwarka Salma."


Momy na fada Saheer ya kara ji kanshi ya yi wani irin sarawa.
Da sauri ya dafe kan.


"ka karbi hakan a matsayin kaddara da biyayya kuma In sha Allah nan gaba zaka alfanun hakan." Momy ta fada.


Kau da kanshi ya yi kawai bai ce komai ba ya fice.
Momy ta kara fadin, "Dadynka na falo kaje ku gaisa kafin ka fita."


Falon ya shiga kuwa ya tarar da shi zaune da Inna da Salma.
Salma na ganin shi ta fara murguda mishi baki tana harara.
"Inna kin ga wallahi duka na ya dunga yi da wani abu kamar wayar injin mugun ne."


Gaishe da ita Saheer ya fara,
"Inna an tashi lafiya?".


Da harara ta bishi kafin ta ce, "Gidanku na ce ka ci gidanku da ban tashi lafiya ba zaka ganni hakane? Kodayake ai daman kai da Uwartaka fatan mutuwa kuke mun to ahir dinku na fiku tijjara da tashanci ni fa na gama fahimtar take taken yaron nan wato saboda kazo fyeɗeta baka samu galaba ba shine ka daura mata karan tsana da duka? Na ce to karbi nan gidanku gobe goben nan za a daura maku aure sai kaje can ya karata da maitarka." Ta kalli Dady kafin ta ce, "Illu ka ga abun da nake gudu ko? Wannan Ɗan naku tuzurun tuzure indai ba a gaggauta anyi abun nan ba akwai lukutar matsala kana ganin idanun sa ma ai ka ga mai bidar aure , gabadaya ya ga yarinya yar dumurmur ya birkice to ahir ayi abun da ya dace amman ban da duka."


Dady ya ce, "In sha Allahu Inna."


Saheer ya gaida Dady ya fice cikin sauri a dakin domin ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment