Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kai bakinsa,samira kuwa zumbur tayi ta miqe dafe da qirji ido a waje,Fadila ce kadai ta kalleta da sakakkiyar fuska ta kuma sauko daga dining area din tana mata marabà



"Me kika zo yi gida na?"aliyyu ya fada cikin Daga murya take jikin Salima ya hau bari,don har kyau ba5a manta Waye aliyyu salim maitàma ba
"Ko kin biyo su ne a yañzun ma ki dauka ki kashe?,ina mai baki shawarar ki fice Tun muna shaida juna,don baki da alaqà da kowa a cikin gidannan"
"Wlh kuwa kada ta cuce mu ba,ta cutar mana da yara"inji samira da ta Kasa zama
Fadila ta dan bata fuska tana kallon su"gaba Abby pls mana"
Shima ya sake hade rai"cewa fa nayi ta tashi ta fice,tunda dai ai ba gidan su bane"



Cikin son kau da hañkalin yaran fadilar tace"kuzo Ku gaida mamarku"
Tsawa aliyyu ya daka musu,sum sum suka soma qoqarin fashewa Daga gurin




*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 5:32 PM] My Mom: *WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION 4⃣7⃣*


👬👫👭👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👦👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦👪


*_I DEDICATE THIS CONTINUATION TO MY SISTERS AND BROTHERS, SONS AND DAUGHTERS OF ALH ABDULLAHI MUSA HUGUMA*😍😘
*AS'ALUL LAHA TA'ALA AY YUWAH HID SUFUFANA*👏🏻






Ya dakatar da su ta hanyar basu umarnin duka su tafi sashensa su zauna a can,suka fice din kuwa ya rufa musu baya,fadilan tayi ta tsayar da shi yayi banza da ita yace da ita
"Parlor dai naki ne kuma mun bar miki abunki,amma Kiyi a hankali kada Ki manta dai wace ce wannan a gabanki"yasa kai ya fice



Ta dakatar da samira dake qoqarin rufa musu baya,ido dai a waje ta kalleta tana nuna kanta
"Ni?,ai Nima din ai ba tsayuwar zanyi ba wannan ai tauraruwa mai wutsiya ce,banda mana da saura shan ruwa a gaba ai da tuni muna kushewa,zan dai tsaya a waje idan naji kina buqatar taimako na kawomiki"tasa kai ta fice



salima ta rushe da kuka ganin yadda kuwa ya gujetà,Fadila ce ta dinga lallashinta da qyar ta ciyo kanta,tirysn tiryan ta zayyanewa fadilan halin da ta shiga bayan barinta gidan ba tare da ta boye mata wani Abu ba,ta rife da ce wa"abba na da Mimi Allah yayi musu rasuwa sakamakon hatsarin mota,da aka tashi taba gado Kuma Ashe abinda abba ya bari bai taka kara ya Karya ba duk kudin banki ne ashe,sai suka raba yasu yasu,din kowa ya manta da ni,sakamakon asirin da auwal yayi musu,da naje ma da kaina ce wa sukayi ba su sanni ba haka dole na haqura"



Tausayinta ne ya kama Fadila,lallai duniya zancan banza,tab as Wanda baji tsoron Allah ba ya shiga uku,abincin ta sabo mata Wanda yaran da babansu sukayi hijira suka bar mata,yadda take can abincin hannu Baka hannu qwarya kawai ya isheka abun tausayi,to abun ka da an dade ba'a hadu ba,kimanin awarta biyu sannan tace zata tafi,alheri sosai fadilan ta sake yi mata tace zata neme ta

⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜

Bata sake ce masa komai ba kan abinda ya danganci salimar ba sai ranar dabgirki ya sake zagayowa kanta,sai da suka zo kwanciya sannan ta Sanar masa qudirinta,tana so a kayan da akeyi a company dinta ake kawowa nijeria tana rabawa samira da farida ta saka Salima a ciki,sannan tana so ta Gyara mu'amala da alaqar dake tsakanin salimar da 'yarta iftihal,don mahaifiya ba wasa bace



Bai tanka mata ba sai da ya ware shigar da bayanan harkokin kasuwancinsa cikin computer laptop dinsa ,ya kasheta sannan ya rufe,ya zare farin gilashin nan nasa ya dora a samanta,ya soke yatsunshi cikin na juna yana kallonta
"Fadeelah"yayi kiranta cikin dakakkiyar muryarsa,ta amsa masa a nutse
"Dukiya taki ce,company ma naki ne Kiyi Duk abinda like so da su mallakinki ne ba mallaki na ba,but........akeai Abu daya da nake umartarki ki zare hannunki ciki........za can Gara alaqa tsakanin salima da iftihal,babu ruwanki,na riga nayi magana da yarinyar tace bata buqatarta,Ku kun isheta,so......don Allah kada ki dawo mana da Hannun agogo baya,I hope kin fahimta?"
Ya shige bargo yayi kwanciyarsa abinsa



Duk da maganan bata yi mata dadi ba amma ta shanye,tayi alqawarin sai ta qarshe jihadin nan
Container din kayanta da tazo a satin ta taba kayan harda saliman,kika ta dingabyi tana sake roqarta ta yafe mata,sannan ta rows mata iftihal da aliyyu gafara,tace tuni ita ta yafe mata,suka insha Allahu zata yi qoqari su yafe matan



Ganin Daga aliyyu har iftihal din sunqi su fahimceta,aliyyu ke fiya wa diyarshi bakya sai ta gwada dauka matakin fiya harkarsu gaba daya,ai kuwa ranar dabiftihal tazo gidan yin weekend dinta kamar yadda ta sabà,tana jirin"Mamee,Mamee na"fadila tace ni ba maminki bace,kike ki nemi maminki,tunda ni ban isa na gayamiki ki ji ba



baqaramin gigicewa iftihal din tayi ba,ta dinga kuka bana bawa Mamee haquri,tace indai tana so ta haqura to ta shirya maza yanzu driver ya kaita gun momin ta,ta Kuma gaya mata da bakinta ta yafe mata



Haka kuwa akayi,ranar ma salima sai da ta koka din,ta Gode ma fadilan ba iyaka,ba laid I iftihal din ta saki jiki da ita,don har zancan sure ta da Muhammad din fadilan sukayi,sosai Salima taji dadi



Saidai bayan dawowar Aliyyu Daga office ya tambayi ina iftihal tunda yasa anan take weekends,ya samu labari ta tafi ganin ummanta salima,fada ya dinga zabgawa,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,ya bata mata rai sosai,amma tunda Allah yaga niyyarta Kuma har muràdintà ya cika shikenan,samira ce ta dinga bashi haquri domin itama ta fuskanci fadilan Daga baya,lokacin sunavtare fadilan na biya mata *minhajil Muslim* da Samira ke koyarwa a makàantarta,bai ko kula su ba sai da ya gama zazzagarshi ya wuce sashensa



*Mrs Muhammad ce👑*


📘📘📘📚📚📚✍🏻✍🏻
[1/29, 5:33 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*PART 3*


4⃣8⃣


🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊

*WANNAN PAGE SADAUKARWA NE GA DUKKANIN WANI MASOYIN LITTAFIN WA YASAN GOBE*


*_AHABBAKUMUL LAZI AHBABTANI LAHU_*👏🏻👏🏻😘😘😍😍





Kwana daya biyu yaso dauke mata wata kamar yadda tayi masa dif,don irin salon horonta da ba iso kenan Kayi masa a dauke masa wutà
Sai dai inaaaa ya Kasa,ya yarda ya Kuma amince shi sadauki ne Kuma jarumi ta kowanne Fanni na rayuwa,saidai tuni ya dade da sanin cewa shi mugun rago ne indai bangaren abinda ya shafi Fadila ne



Bashi da jarumta kan fushinta,bashi da juriyar haqurin rashinta a kusa dashi,musamman kasancewarta tamkar uwa ga kowa dake cikin gidàn,jaruma ce mai juriya da kawaici yakanah da haquri,Duk wa su làlurorin da matsalolin cikin gidan Matuqar baya kusà zata sa kafàdarta ta dauke su,koda ma wani lokacin yana cikin gidan takan bashi damar hutawa,Bango ce ita a cikin gidàn kowa na samun kulawarta



Zakayi mamakin yadda yaran ke qaunarta,kuwa Mamee Kasa,Mamee maza,hatta da Fatima sai Kayi zaton Bataan samira ce mamàrta ba,to itama Samira idan ta sabo tarin matsalolinta da shawarwarinta gun Mamee fadilan take saukewa,Tun danginta na ganin tamkar ta shanyetà ne har daga baya suka fuskanta,ganin yadda 'yar uwa tasu ta sauya,Duke Kuma morarta ba kamar a baya ba,Daga qarshe har godiya suka miqa ga fadilà



Qawaye kuwa nata irin na da a yanzu babu burbushinsu ko daya,Tun tuni ta fatattakesu daya da daya,tayi wa tayi kyau ta sauya

🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉

Tana cikin kitchen yau ita daya ce,ita dai Tun safe take jiñ kaya kayar yaran suna ta shiri,abbun su na bada direction na inda za'a kai kowa,aslam da Muslim dama na Egypt su na shiru shiryen shiga *jami'atu al azhar* bayan sun kammala secondary dinsu kenan



Zuhra Islam da iftihal yasa aka kaisu gidan ummi,faruq da saddiq Kuma aka kaisu gidan uncle abba,afrah da amrah Kuma sukayi gidan farida,sai gidan yayi tsit,baba talatu na sashenta,samira kuwa tayi gidan su itàmà bikin qanwarta,can zata kwana



Ita kam batasan tafiyar tasu duka ta kwana bace don haka har da su take girkin,tanayi tana mita cikin zuciyarta an kwashe mata 'yan aikin,don idan su na gida bata yin komai banda Gyara bedroom dinta da part din abbunsu,nata bada umarni ne da yin gyara inda aka kuskure






*Mrs Muhammad ce*👑👑
🎊🎊🎉🎊🎉🎊🎉🎊🎉
📕📕📗📗📘📘✍🏻✍🏻✍🏻
[1/29, 5:39 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


*part 3*



4⃣9⃣



👬👫👭👫👬👫👭👭👫
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*wannan page din naku ne HUGUMA NOVELS READERS tare da iyalanku gaba daya*
*Allah ya bar qauna ina godiya*
👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻





Ta juya don dauka abarba cikin freezer zata niqa ta hada zobo,sai riga mutum tsaye a bakin qofa,sqnye yake da long sleeve t.shirt maroon colour wadda tayi masa dai dai jikinsa,sai trouser baqi,idanunshi tsaye da gilashinsa nan,hannayensa duka harde a qirjinsa,gaba daya ya zuba Mata mayatattun idanunshin nan masu shegen maganadisu,



Tayi masa kyau matuqa da gaske,ba zai iya tuna lokacin da yazo ya sameta ba cikin ado da kwalliya ba,haka itamq din a dan Kallon sakqnnin da tayi masa,aliyyu bai tsufa,ko yaushe kamar ana sabuntashi,idan ka ganshi tare da su aslam sai Kayi tsammanin yayansu ne ba wai mahaifi ba,Duk wani kyau kwarjini da farin jini nashi sunyo shi,ginshira gaji da shan qamshi tamkar shi da su din tagwayene,shine gamboñsu



Sai ta kawar da kanta tamkar ba yanzun suke qarewa juna kallo ba,ta duqa don ciro abinda tazo daukan,ya saki lafiyayyen murmushin nan nasa,wato har yanzu fadilan nan tashi ce dai,miskilar nan,mai shan qamshi jan aji da dauke kai,yana jin shima ya kamata ya tuna Mata aliyyun nan nata, *Aliyyu Salim maitàma* mai qarfin hàlin nan da yawan qaunarta



Kafin ta kai ga ciro abarbar taji caraf an riqo hannunta,da sauri ta dago gami da juyowa,sai dai tuni yayi mata masauki cikin qirjinsa,yasa hannayensa ya rufeta,kafin ta kai ga furta koma ya hade bakinsa cikin nata



Sai da ya zare mata laka baki daya,tuni tsaiwa ta gagaresu suka zube saman tiles din kitchen,ganin yana qoqarin wuce makàdi da rawa yasa tayi qarfin halin tureshi
"Abbu so kake muyi abun kunya?,yara fa zasu iya dawowa kowañne lokaci"
"Eh shi yasa ai na korasu don kada su hanamin cin amarci da matata,ke da ki gañsu sai after three days"



Harararsa take saidai da ka kalli tsabar qwayar idontà zaka gane cike hararar take da qauna da bege
"Wanne amarci kuma?,mutumin dake shirye shiryen aurar da first born dinshi"
"Haka kika ce,to zamu gani?"yace da ita gami da sungumeta da hannayenshi,bai sauketa a ko ina ba sai a fadarshi,Kallon juna suke suna murmushi cike da shauqi,sake rungume ta yayi cikin faffadan qirjinsa yana rada mata
"Fushinki kashni yakeyi *HASKEN IDÀNIYATA*,zuciyata ràguwa ce a kanki,zan iya jure koma amma banda lamuran da suka shàfeki,na tuba *RAYUWA TÀ*,kace *GATA NA*



itama cikin salon radar take ce masa"idan na dau ke ma wata tamkar ina hukunta kaina ne bisa ga Kasa bin ra'ayinka da nayi,mijina Kaine *DUNIYA TA*gaba daya,na gode wa Allah da ka zamo *uban 'ya'yana*"
Da sauri ya tari numfashinta "ni yafi cancanta na godiya ga Allah da ya rufamin asiri ya hana inyi asararki,da haka ta faru Fadeelah na,........da tuni na dade a kushewa ta"
Sai jin qauri suka cikin kitchen,da sauri suka rige rigen isa kitchen din






*Mrs Muhammad ce👑*
🎊🎉🎊🎉🎊🎉🎊🎉🎊
📗📗📕📕📘📘✍🏻✍🏻✍🏻
[1/29, 5:44 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*YASAN GOBE?........*
🎊🎉🎊🎉🎊🎉🎊🎉🎊



*PART 3*


5⃣0⃣

💘💝💘💝💘💝💘💝💘

*_I DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY HUSBAND,MAY ALLAH HELP AND GUIDE YOU,I LOVE YOU_*😍😍😘😘



Shi yayi nasarar kashe gas din,suka kalli tukunyar miyar da tuni ta qone sannan suka kalli juna,dariya sukayi a tare,ya kama hannunta yasa cikin nashi tafin hannun bayan ya dage girarsa
"Kwanaki ukun nan na amarci ne
Babu girki.......
Babu aiki.......
Babu hayaniya.......
Babu yara.........
Ba surutu........
*just Fadeelah and aliyyu* kawai zasu more duniyarsu"
Itama girar ta daga "wow....I like it, *duniyar Fadeelah da aliyyunta kenan ko?*"ya gyada kai
"Yes!,yes my own"



Riqo hannunta yayi suka jero Tun Daga kitchen din,tafiya Duke very slowly kamar ba zasu isa bedroom din ba,kowanne jikinsa da zuciyarsa ta mutu da qwayar son dan uwanshi

*"na miki alqawarin kasancewa dake har bada"*

*"na maka alqawarin zamowa kusa da kai duk rintsi duk wuya"*

*"na miki alqawarin bata wa zuciyarki da gangar jikinki*"

*"na maka alqawarin zamo wa wata babbar duniya a gareka"*

*"na miki alqawarin dawwamar dake cikin farinciki har qarshen numfashin mu*"

*na miki alqawarin........*
*na miki alqawarin*.........


Haka aliyyu ya dinga hero mata har ta Gaza fadin koma,kukan dadi ya kufce mata,ta samu aliyyu fiye da yadda take zato hasashe ko tsammani,tabbas
*BABU WANDA YASAN GOBE SAI ALLAH*



Tana tsaye tana Hawaye ya zube a gabanta kan gwiwoyinsa,ya lalubo qwayar idonta ya sanya nashi ciki,ya soma girgiza kai
"Um.....um baby, *No more tears* kin manta?, *na miki alqawarin ba zaki sake kuka ba fa har abada*"
Dai dai lokaçin da hawayen idonta suka silmiyo su na qoqàrin dinga a tiles,yayi maza yasa tafin hanñuñshi ya tareshi,tas ya lashe hawayen kan fuskàrta



" *NURY* kukan farinciki samun ka a matsayin miki nake,irin mijin da ke wa mata tsada da wuyar samu a wannan lokaçin"

"Kamar yadda mata irinki ke tsada a wannan lokaci ko
ladabi,biyayyatsafta,dadi ni,haquri juriya da kawaici
Kyau,Zubi diri,kullum kamàr ana dada miki yarinta da wani dadi na......."
Da Sauri ta rufe masa baki da tafin hannunta cikin kunya tana boye fuskarta cikin qirjinsa
"Kai dear don Allah"
"Yes,zancena haka yake wlh *qurratu ainy*"



Bakinsu ya subuce a tare suka fadi *ALHAMDULILLAHIL LAZI BINI'IMATIHI TA TIMMUS SALIHAAT*
Sai suka hada ido kowaññensu ya sakarwa dan uwansa amintaccen murmushi



*tammat alhamdulillah*
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻


*dukkanin wani yabo da godiya sun tabbàta ga Allah madaukakin sarki*

*tsira da aminci su sake tabbata ga dan gatan Allah shugaban dukkan wata halitta baki daya annabi Muhammad s.a.w*


*bakina bazai iya fasalta tarin godiyà ta ga dubban masoya na ba masoyà littafina,Wanda goyon bayànku haquri da juriyàrku ya kàini gà bigiren da nake kai yanzu,Allah yayi muku sakamako mafifici,mutane Daga qasashe da garuruwa daban daban*


*ina Neman afuwa da yafiya ga duk Wanda na bata wa ko littafina ya batawa rai,duk dan Adam ajizi ne,ba lallai Kuma mu sake saduwa bà*



*fatan alkhairi ga mahaifana*


*godiya mai qima ga HUGUMA novels readers*


*shin cikin littafina waye gwaninki?*

*wa kika fi so?*

*wa kika fi tsana?*

*me yafi burgeki?*

*me yafi bata miki rai?*

*wanne darasi kika gano cikin littafiñ?*

*mene yafi baki dariya?*

*mene ra'ayinki kan wa yasan gobe?*

*ina jirañ saqonninku ta watsapp dina*
08187255862

*Alhamdulillah* *Alhamdulillah*
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻


*Mrs Muhammad dinku ce*
👑👑👑👑😘😍


📕📕📗📗📘📘✍🏻✍🏻

Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment