Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka dawo gida.
Sai da Zarah ta yi 40, ita da Aliyunta, sai k'ara
murjewa suke, ita dai Zarah ta ki sakin jinkinta
dashi, gani take kamar shi ma mutuwar zai yi.
Sun dawo gida Najeriya yana da kwana 45, gaba
dayan su da Naseer.
Gagarumar walima ya shirya, bata wasa ba,
'yan uwa da abokan arziki suka taru, aka taya
juna murnar samun Aliyu tare da fatan Allah ya
raya shi cikin danginsa, rayuwar Islama. Sati 1
Naseer yayi ya dawo Potugal.
Tun Zaran na fidda rai da Aliyu, tana ganin yau
zai mutu ko gobe har ta zo ta saki jikinta,
zuciyar ta ta zauna waje daya ta daina ba Aliyu
mutuwa. Watansa 9 kenan yayi girman mamaki,
da kan shi yake mikewa tsaye, yana nema cira
k'afa yayi tafiya.
Yana kuwa shan ja wajen 'yan uwan sa suna son
yayi tafiya dole.
Rayuwar su mai dadi suke sha, tare da abokan
huldar shi, domin a halin yanzu Sageer yana
lakcarin a nan (State Poly) da yaransa 3. Kausar
na da 2. Zumunxin su kodayaushe k'ara k'arfi
yake tare da k'aruwar arziki. Ko Zarah ta gyara
gidan su dai-dai gwargwado tare da taimakon
Naseer. A cikin su da iyayen su babu wanda bai
keta hazo ba, ya sauke faralinsa. Komai maka
Allah shekaruna mikawa hada da tarindaukaka.
Naseer ke zaune shi kadai bisa kujeran alfarma
a farfajiyar bayan gidansa. Yayi shiru ya
zunduma taunan baya, har ya zo kan rayuwar
da yake cikin ta a halin yanzu.
Ya dubi tafkeken gidan sa a birnin Potugal,
mallakar sa wanda ya zuba makudan daloli ya
siya. Babu abinda ke ransa, sai dumbin godiya
ga Ubangiji da yayi masa baiwar da ba kowa ke
samun irin ta ba.
Sannan ya mallaka masa ingantattun mata na
nunuwa a fadin duniya.Zarah idan ya tuna irin
baiwar da Allah yayi mata na kaifin hankali da
sanin yakamata, ya tuna ita ta fara gaya masa
rayuwa shirin Allah ce, bai kamata Dan-adam
yana alkawari a hurumin da ba nasa ba, sai ya
ji son ta ya shafe ko'ina a jikin sa, yana neman
zautar da shi.
Nusaiba matar da yake wa yak'inin sa'a ce a
gare shi, Allah ne yayi masa arziki daga gare ta,
'ya'ya da dukiya tare da fice a duniya. In dai
ana maganar wasan Polo, duk masoya wasan
sun san da Naseer Jah-Jah.
Shi yasa idan ya dube ta, haka kawai ya kan ji
hawaye sun cika idanuwansa, sbd tsabar
tausayin kan sa, da ace ya rasa ta akan wautar
banza. Son ta ruwa ne, ya aje wa ransa, don ko
ya fadi, shi kansa yana ganin karya yake yi.
Yayi mika, take nan kewar su ta kama shi,
domin babu ko dayan su a tare da shi. Zarah
na jarabawar karshe ta kamala B-ed din ta.
Nusaiba kuwa ta na watan haihuwa ta 6.
Ita kadayaushe ta fi son haihuwa a gida. Gaba
daya hankalin sa ya koma gun sun, daren nan
ya kasa barci. Kamar wasa zuciyar sa ta rasa
sukuni, ba shiri ya nemi hutun shekara.
Bai hada sati ba, ya baro Potugal, sai ganin sa
suka yi kwatsam!
-----------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
'Ya'yan sa suka baibaye shi, tun isowar sa har
la'asar yana tare da su. Direba yayi kiran su
lkcn Islamiyya, kowanne ya fito cikin shiri, ya
shiga mota. Direba ya wuce da su. Zarah ta idar
da Sallah, ta fito babban falo ta iske Nusaiba
zaune tana kallo.
Kusa da ita ta zauna tana fadin,"Ki na nan ki na
kallon fadace-fadacen nan da ya ki ci ya
kicinyewa." Ta ce,"Ke dai bari, ai ni wannan
fadan na k'asashen larabawan nan tsoro yake
ba ni." Zarah ta ce, ke me kika fahimta daga
gare shi?
Ta ce,"Karshen duniya mana. Dama ance idan
zamani ya zo karshe, alamun har da 6arkewar
rikicin k'asashen gabas ta tsakiya. Yanzu dubi
k'asashe nawa ke rigima, ana kashe su, kamar
ana kashe kiyashi, tsakanin mu a musulmi
kenan."
Zarah ta tallafe kunci ta ce,"Wannan rayuwa
tana firgita ni, me mu2m ya kamata yayi, banda
ya kadaita Allah, yayi masa ibada, sannan idan
ya ci, ya bada sadaka, don neman karshe mai
kyau? Ta ce,"Wallahi kuwa Antina, musamman
na mu mata da aka ce mun fi yawa a gidan
wuta.
Biyayyar aure ce matsalar mu komai muka yi
gidan miji lada ne. Amma sai ki ga abin ya
gagara.
Kar ma ace miki akwai abokiyar zama, abin ya fi
kazanta.
Sai ki ga mace ta mance cewar akwai hikimomi
da yawa cikin auren mace fiya da daya shi yasa
Ubangiji ya halasta shi.
Haka kawai ta dauki bakin kishi ta dorawa
kanta, daga nan ne za ta fadawa hallaka.
Allah ya kiyashe mu.
Zarah ta kamo hannun ta, suka runtse,"Kin yi
gaskiya amarya, shi yasa na ke wa Allah godiya
da yasa ke ce abokiyar zama na." Ta yi
murmushi,"Ni din Antina? Na fi kowa farin cikin
samunki. Allah ya k'ara hada kan mu, ta yadda
yayanmu zai ci gaba da samun kwanciyar
hankali.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Tafi suka ji ana yi ta bayan su.
Duk suka waigo,yayan na su ne a tsaye yana jin
su. Ya zagayo suna dariya ya tsaya gaban su, ya
ce,"To a matsa min in zauna." Suka ware ya
zauna tsakiyar su." Allah ya kamaku, ashe zama
ku ke kuna gumalta ko? Zarah ta kama baki,
"Lah!
Allah mai halitta, jaba ta dubi bakin mijinta.
Gulmar me kuma a mu ka yi ta ka?
Ya kamo kunneta. Nusaiba na kwasar dariya, ya
ce,"Ita jabar 6ata dubin ta ba ne? Ta ce,"Oho."
Ya k'ara murdawa, ta yi k'ara. Nusaiba ta kamo
na shi ta ce,"Allah sakar min Antina, ko ni ma in
cire na ka. "Ya saki ya dube ta,"I see, kun hada
kai ko?
O.k, yayi kyau, ke ba zan ta6a ba, kin zama
yangwam!
Amma ke, za mu hadu."
Duk suka yi dariya.
Ya rungumo kafadansu ya sake fadin,"Allah ya
yi maku albarka, kun zama abin alfahari na, kun
zama jigon rayuwa ta.
Na kuma gane rayuwa shirin Ubangiji ce,
mutane da yawa suna samun dama, amma sai
su ki amafi da da damar har ta wuce su, daga
baya su zo suna cizon yatsa.
Allah ya ba mu ikon amafin da damar mu."
Suka nisa suka amsa da Amin.
Kowacce ta dora kanta bisa kafadar gefen sa.
Suka yi shiru na 'yan dakikai.
Cikin shirun ne suka ji kamar suatin T.V, a wani
sashi na gidan. Naseer ya ce ,"Wai ba duka
yaran nan sun taifi makaranta ba?.
Eh mana."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Ya mike yana fadin,"Ga sautin (Game) can ina j?
Duk suka mike suka bi shi sashin yara. Ameer
ne ya kuke yana buga Game na tseren Polo,
sautin T.V ya rage can k'asa, yi yake kamar zai
tashi sama, sbd kwaikwayon yadda dawakan ke
gudu. Naseer ya lalla6o ya cafke kunnansa, a
tsorace ya waigo manyan idanuwan nan na sa.
Suka kara yo waje tamkar Naseer a zamanin da
yake shagalinsa a filin sukuwa.
Bai tanka masa ba, yai ta jan kunnan sa har
falo, sai su Zarah ke ta faman salati suna
fadin,"Amma dai Ameer Allah ya shirye ka!
Ya tsaya ya k'are masa kallo, kafin ya ce,"Kai ne
babba, amma babban kwabo? Kullum da kai ake
complain! To zan kwashe Game din tunda shi ke
hana ka zuwa makaranta! Yayi sukuiti yana
kumbura.
Nusaiba ta zungure shi, "Maras kunya, sai anyi
magana, ya rink'a cika yana hura hanci, wa ka fi
zuciya? Come on wuce ka dau ko jaka Lado ya
kai ka! Zarah ta kamo shi,"Wuce mu je, ka
dauko jakar, kai ba ka ganin kannin ka sun tafi?
Ta raka shi ya dauko jaka. Nusaiba na ta fada,
ta fita ta kira Lado Direba, yasa shi a mota zai
wuce da shi."
Nusaiba ta zauna kusa da Naseer ta ce,"Ameer
sai addu, ace yaro baya maida hankali a karatu.
Sai game din tsiya? Shi yasa ban so ka kawo
masu wannan sabin Game din ba."
Ya ce,"Zai bari ne." Zarah ta dawo ta zauna inda
ta tashi,"Ameer kenan an dai tafi ana ta
kunci,"Nusaiba ta ce,"Ai kin ji Babansa ya ce zai
bari ne, amma complain din Ameer yayi yawa,
ko makarantar kuka suke da rashin maida
hankalinsa, ga masifa, ni na rasa irin sa."
Ya ce,"Ni kuwa in na kalle shi, dariya yake ba
ni." Kin ji ko Antina? Ta ce,"Ya dai kamata ka sa
baki, ka yi masa fada sosai, kafin ka bar garin
nan, kila ya fi jin na ka. Ameer yan aikin gidan
nan bai kyale ba, haka 'yan kanninsa. Aliyu
kadai bakin sa ke ceton sa da yake duk gautan
ja ne.
Baba na da Alhaji kuwa, sai dai su yi kuka su
share hawaye, balle kuma 'yan matan."
Ya kama kai, ya ce,"Wayyo Abba na, duk
wannan laifin shi kadai? Wai ba yarinta bace?
Nusaiba ta ce,Yarinta? Me yasa............
Ya katseta,"Ya isa! A yimin shut up nace! Rashin
jin nan fa kowa yayi shi, ke kin yi, ke ma kin yi.
Ni ma na yi."
Nusaiba ta ce,"Oho, ashe abin gado ne, ta
6angaranka, amma mu ba muyi rashin jin kin
zuwa makaranta ba."
Yayi 'yar dariya ya ce,"Yan rainin wayau, kun
cika ni da , kamar ban san sirrin kowacce ba."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
Zarah ta gyara zama ta ce,"Ai sai ka
fadi"Yalla6ai, mu na ji." Ya dube ta, ya ce,"Ke fa
kullum ki na like bayan taga, ki na zuba ihu,
hawaye sharaf-sharaf, majina har baki. Da an
tambaye ki menene? Sai ki ce kudin (Break) dina
ne suka 6ace."
Ya fadi yana kwaikwayon muryart har da
shashshekar kuka.
Ya juya kan Nusaiba,"Ke kuma ai Abba ya gaya
min da zarar Direba ya fito da mota, zai kai ki
makaranta, sai ki ce kashi ki ke ji."
Ni din?
Zarah ta ce,"Ke ma ki ka tsaya tambayar sa. Ta
figo filon kujera. Nusaiba ma ta dauko na ta,
suka rufe shi da duka.
Me zai yi ba dariya ba, yana fadin,"Mugaye,
k'arya na yi.........?
Na kwashe 'yan biro na da takarduna na bar
gidan, don ba zan iya ceton Naseer ba.
Tsokanar fada A JININ SA YAKE!!! ,
saboda haka ALHAMDU-LILLAH, na gaji da
shari"a.
Idan kuma akwai ma iyawa, to Bismillah!
Jah-Jah na can yana dakuwa a hannun zaratan
matan sa.."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
afuwan bakujini da wuriba sakamakon wayata
tadan samu matsala, daga bayakuma nadanyi
rashim lafiya, your prayer is needed pls












Zaharaddeen Shomar
Whatspp 08168575100 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment