Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

****
BANANA ISLAND, LAGOS
P
rincess Fatima, ta shigo da dan saurinta tana cewa da mahaifiyarsu Hajiya Sappa.
“Ni me ya faru da kunnen Nenne na ne? Anata kiran ki a waya tun dazu kina kallonta ido hudu amma dagawa ta gagara, halan baki ji kiraye-kirayen bama Nenne?
Tun daga falo nake jiyo ringing din wayarki ba kakkautawa. Nenne meke damunki haka yau? Tun safe nake ganinki haka sukuku (moody) cikin tagumi da damuwarnan, duk kin birkice”.
Princess Fatima, ta karasa shigowa dakin na mahaifiyar su cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan manyan sarakuna, ta fadawa mahaifiyarta Nenne Sappa kalaman cikin taushin murya, Nenne dake gyangyadi akan dardumar data yi sallahr walha ta dago tana duban Fatima fuskarta fal damuwa.
A hankali ta bude ido sosai daga lumshewar data yi musu ta dubi doguwar diyarta Gimbiya Fatima, kyakkyawa ta karshe, wadda ke tsaye a kanta da wayar Nenne din a hannunta data sunkuya ta dauka a gabanta, har zuwa lokacin anata kira ba'a daina ba.
Da sauri Nenne tace “Miko min wayar, Allah yasa shine, bana cikin nutsuwa Fatima, saboda yau kwana biyu bai kira ni ba, gyangyadinnan da kika ga nake yi mafarkinsa nakeyi a cikinsa, wai bashi da lafiya, dadin dadawa tun shekaranjiya rabon da ya kira ni, abinda bai taba yi ba, jinkirta kira na a duk yanayin da yake ciki (koda kuwa ace yana kan Doki ne)”.
Fatima ta mika mata wayar, sannan ta zauna a gefe tana bata labarai. “Nenne jiya ne ‘Championship Tournament’ din su Hammah fa, a can Argentina, bashi da lokacin kansa kin sani. Na so inje kallo physically Dade (Baba) ya hanani, tun dazu kuma na kunna ‘PoloLine.TV’ ba’a nuno gasar ba.
“I am worried too”. Ta karasa fada da harshen yarbanci. Wato itama cikin damuwar take kwatankwacin ta mahaifiyarsu.
Ba tareda ta amsawa Fatima maganarta ba Nenne ta amsa wayar da ake tayi mata ba kakkautawa da sallama cikakkiya irin tata ta nutsuwa, ta hanyar nemawa wanda ya kirata amincin Ubangiji ba tare da ta san cewa katon Bayahude bane ke kiranta ba musulmi bane ba kuma Dan nata ba, duk kuwa da cewa da lambarsa aka kira ta.
A wayar aka shiga yiwa Nenne bayani da harshen da ba ganewa take yi ba, wato yaren “Araucano” na Argentina.
“Sunana Pareto Danny, ina magana daga wayar ubangidana, ya samu tsautsayi ne… muna asibiti, inason magana da Mother dinsa…”.
Don haka sai kawai ta mikawa Princess Fatima wayar cikin yamutsa fuska tace “ungo nan Fatima, kiji me wannan yake fadi haka?”.
Ba don ma taga lambar ta Ajantina bace da bazata amsa kiran ba, a ka’idarta Nenne Sappa bata amsa bakuwar lamba, amma kasancewar ta san cewa AbdulRasheed yana can, kuma yau kwanaki biyu kenan tana alhinin rashin kiran wayarsa da bata samu ba kamar kullum, domin duk halin da yake ciki baya kasa kiranta kona minti uku ne, shine yasa ta amsa wannan kiran da gaggawa don jikinta ya bata ya shafe shi.
Maganar mintuna kusan uku Princess Fatima tayi da Pareto a wayar, ta fahimci me yake kokarin sanar dasu, wato Prince ya fado daga Doki, ya jikkata fiyeda koyaushe, yana asibiti a kwance da karaya a hannunsa, don haka Fatima sarkin raki sai kawai ta saki wayar a kasa ta dora hannuwa aka ta sakawa Nenne kuka.
Kasancewar Fatima mai tsananin so ga Yayan nata kuma mai saurin kuka. Suna son junansu suna kula da juna shigowar bare cikinsu ne dai karbarsa sai a hankali. Nenne nata tambayarta ta gaya mata me aka ce mata?
Da kyar, kafin Fatima tace cikin hawaye “Nenne Hammanmu wai, ya fado daga Doki yaji raunuka a jikinsa, yana asibiti can a kwance, an kira Dade a gaya masa ba’a sameshi ba shine aka kira ki”.
“Subhanallah!”
Inji Nenne, cikin kidimewa da mikewa tsaye, tana cewa “wannan DOKI!” Nan dai ta nemi fulatancin da take gwadawa akan AbdulRasheed sau tari yau ta rasa, Nenne bata jure rashin lafiyarsa ko kadan, duk da yana jimawa bai fadi a doki ba amma ko ya fadi baya jin wani ciwo na azo a gani, yaushe rabon ace yana kwance a asibiti ma ta manta koda ya fado daga Doki bai taba kwanciya asibiti ba sai dai ya sha maganin ciwon jiki yakwanat zuwa wayewar gari ya shiga harkokinsa, bait aba samun mummunan wani rauni ba.
Cikin damuwa ta ce da Fatima tayi mata ‘booking flight’ mafi kusa, tace da kanta zata tafi har can ta yi jinyarsa, tunda dama duk suna da Visa na shiga Argentina sun saba zuwar masa koyaushe suke so.
Kasancewar a kasar Argentina Prince AlbdulRasheed ya mallaki gidan kansa (Ranch House) mai ‘field’ na ‘Polo’ a cikinsa.
Iyayensa, Taiwo da danta na fari Hakeem (kafin a haifi Kiki) da kannensa mata ‘yan biyu Firdausi da Fatima, na yawan kai masa ziyara gidan, kafin ya samu aiki a Qatar refinery y araba rayuwarsa gida biyu tsakanin Qatar da Argentina. A Qatar Penthouse gareshi wanda bai kai girman gidansa na Argentina ba kuma babu Dawakansa acan.
Sai Princess Fatima tace itama don Allah zata bi Nenne gun Hamma suyi jinyar tasa tare, tace bazata iya zama a gida ba, alhalin bata san halin da Hamma ke ciki ba, damuwa zata isheta, don haka suka fara shirin tafiya itada Nenne.
Princess Firdausi kadai da masu aikinsu aka bari a gidan, don ta jira dawowar Dade ta kuma kula da gida wato ta jira mahaifinsu da zai dawo a satin, kada ya dawo gidan babu kowa kuma agidansa kawai yake cin abinci, wanda shima ya tafi nasa ‘medical check up’ din ne na lalurar sugar dinsa a Egypt.
Wani abun burgewa da wannan gidan nasu Prince Abdulrasheed shine tringualism dinsu; Babu irin yaren da bazaka ji anayi a gidan su AbdulRasheed ba cikin manyan yarukan nan uku su da iyayensu biyu da kannensa mata, tsakanin Hausa, Fulatanci da ‘native language’ na Babansu wato Yoruba, duk babu wanda basa ji, kuma babu wanda basa yi, wato babu wanda basa yarawa a junansu.
**** **** ****
THE PRINCE
N
enne Sappa da Princess Fatima sun sauka lafiya a kasar Argentina a wani marece na tsakiyar winter season, ana tsaka da tsuga yayyafin kankara. Nenne Sappa sanye da Hijab dinta ruwan kasa-kasa daga samanta har kasa, yayinda Princess Fatima ke sanye cikin wasu ‘Blue Royal Outfits’ masu kauri.
Kamar yadda aka riga aka tsara hakan ce ta kasance; yaronsa Pareto shi yazo ya daukesu da wata kankanuwar motar Abdulrasheed din (Alfa Romeo), daga filin jirgi zuwa asibitin da yake, Pareto yayi musu jagora har dakin da Prince yake a kwance yana jinya a asibitin kashi.
Sanda suka shiga dakin barci yake yi sadidan, don zugin hadewar kashi ya ishe shi, hakan yasa aka yi masa allurar barci don ya samu sa’ida ya kuma huta azabar.
Nenne da Princess Fatima, suka taka suka isa gareshi suka tsaya a kansa suka kura masa ido, suna kallon kyakkyawar fuskarsa (with great affection) da alhini cikin idanunsu, daga bisani duk suka aje mayafansu akan kujera don yin alwallah su sauke sallolin da suka riskesu a hanya.
Har suka yi sallah suka idar duk AbdulRasheed yana barci na karfin allura baima san da zuwan nasu ba.
Pareto wanda shi yake kula dashi a asibitin kafin isowar ‘yan gidansu, shi ya kawo musu abinci na alfarma daga ‘restaurant’ din asibitin, daga cikin provisions din da aka yiwa Engnr. AbdulRasheed, duk irin abincin da yake so shi asibitin zai bashi, haka wadanda ke tare dashi don kula dashi.
Sai magriba ya farka, yana bude ido a hankali, ya yi tozali da Nenne a gefensa tana sallah, Nennensa, daidai lokacin data sallame sallahr, wani kyakkyawan murmushi Prince ya saki yana fadin,
“welcome my Nenne, saukar yaushe haka babu zato? What a surprise!”
Sannan ya yunkura ya tashi zaune da kyar, ta mike daga kan dardumar ta gyara masa filo a bayansa yadda zaiji dadin jingina sannan taja kujera daidai kansa ta zauna, shikuma ya gaisheta cikin harshen Yoruba. Ita kuma sai ta mayar masa cikin fulatanci, haka sukeyi daman, in sun yi mata tana ji amma bata mayarwa, don har gobe Nenne jefi-jefi take yin yaren mijinta da ‘ya’yanta, tafi rike nata da kyau. Bata son yadda yaranta suka fi yin na Babansu suke kin yin nata, ba kuma don basu iya ba saidon sun fi girmama nasu.
Nenne ta koma kujerar daidai kanshi ta zauna, ta dubi yadda ya sha daurin bandeji waje-waje, hannu da kafa duk karaya, tayi kwafa cikin damuwa da takaici ta ce.
“Isn’t this enough Hammansu? Ni na tabbata yadda ka dauki hawa Dokinnan da muhimmanci bana jin ko aikinka kana maida hankali haka a kansa.
Balle kuma sallah da ibadar Allah, na tabbatar suna wuceka, alhalin kana bisa sabgar Dawakai, wadanda su kadai zasu tserar da dan adam ranar lahira ba wasan tseren Doki ba”.
Sai kuma Nenne ta dakata kadan sannan ta sassauta murya ta koma yin magana wannan karon cikin lallashi da lumana, ganin yadda Prince ke wani irin yamutsa fuska akan zantukanta, baya so take cewa baya ibadah sai hawa Doki.
A ganinsa yana baiwa kowanne lokacinsa yana kokari kwarai wajen kiyaye sallah a duk inda ya samu kansa. In akayi la’akari da irin schedules dinsa. Yana irin nasa kokarin a ganinsa.
“Magana ta domin Allah, Hammansu, ka maida kan ka kamar wani tsuntsu mai tashi sama kan fiffike, yau baka nan gobe baka can duk don hawa Doki?? Ni menene a cikin hawa doki ne? Ka ki tsugunnawa a wuri guda ka fuskanci rayuwa ta reality. Saboda Allah yaushe rabon ka da zuwa aikin Hajj don sauke farali balle umarah da take sunnah?
A tunanina duk wata daukaka, ko suna da kake nema cikin wannan sana’ar ina ganin zuwa yanzu daka mallaki kofunan Zinare sau ba adadi a sanadinta, in ban yi kuskure ba kofunanka sun kai biyar, ko shidda, ina ganin ai ka gama samun daukakar Polo kuma Hammansu.
Ko tunanin aure da aje iyali baka yi wanda shine wajibinka a rayuwa ta hakika kuma mai ma’ana ga dan adam, ba don komai ba sai don saboda hawa doki ne kadai a ranka, ka manta cewa harka fita shekarun kuruciya da jimawa ka shiga na girma, don ma dai bakayi kama da shekarun ka ba; you are still looking fit and healthy”.
Nenne ta kara kwantar da murya yadda dole dan nata ya tausaya mata, tace “Abdulrasheed ko tausayina baka ji, duk faccalolina sun ajiye jikokin ‘ya’yansu maza ni ko daya babu, ba don Taiwo ta bani ba, jikoki ba da saidai kowa ya riga ni tarawa, har wadanda sukazo a bayana, ga maganganun nan marassa dadi da duniya ke yi akan ka suna dawowa kunnenmu, haka ‘yan uwan ubanka suma suke yimin irin tasu tijarar a kanka, suna ganin ni na hana Ubanka kara aure har tsufansa, haka zai mutu da mace daya kamar rai sai kace auren zobe, kai kuma dana haifa mun daure maka gindi kana yawon tambada da lalata a duniya ka ki cika Sunnah, kana gudun aure wanda yake sunnar Annabi SAW.
Ka ki ko tsayawa kayi tunanin ya kamata ace a wannan matakin na rayuwarka kana da yara lafiyayyu har guda uku ko hudu.
Yau dai tunda Doki ya kusa hallaka ka kana ji kana gani, ina ganin ya kamata ka hakura dashi haka Kehinde! Babu sauran alfanu kuma a cikin hawansa”.
Prince AbdulRasheed ya muskuta ya gyara kwanciyar sa cikin jin azabar zafin ciwo irin na hadewar kashi, yace.
“Nenne bana so ko kadan kike sakawa kanki damuwa akan abinda at least kin riga kin san bazan iya bari da sauki ba.
Polo ya zama wani bangare na jikina Nenne, ina yi ne kawai don jin dadina da biyan bukatar sha’awata ga wasan Polo, amma ba don tara kofuna ba, yana debe min kewa yana hanani tunani yana kuma hana ni damuwa da komai, ba don neman wani abu kuma nake Polo ba ko da can balle yanzu da nake da aikin yi kwakkwara, don haka banaso kina damuwa da ance-ance din mutane wadanda basu da gadonka. Su mutane ai al’adarsu ne damuwa da abinda bai shafesu ba.
Abinda ka kwashe rabin shekarun rayuwarka kana yi yana da wuyar bari a dare daya kuma farat daya Nenne. Kimin addu’a, idan inada rabon barin hawa Doki in bari a hankali.
Nenne nifa zan iya ajiye aikina na refinery dungurungum! In rungumi wasan Polo shikadai.
Idan Doki shine ajalina haka Allah ya kaddara min Nenne”.
Yayi dan shiru yana dan haki, na zafi da zogin ciwon karaya, kafin yace “Nenne tun shigowarki bakiyi duba da halin ciwo da nake ciki ba, sannan ko jajen raunin da SAHEEB yaji baki yimin ba kin hau ni da fadan rashin aure anya Nenne?
Ki godewa Allah da ban zarce ba, na barki da ciwon rashina bana rashin aurena ba.
Kimin addu’ar samun sauki da gaggawa kinji Nenne na, ki daina damun kanki akan abinda banida rabo a cikinsa, ki roka min tsahon rai da lafiya mai amfani mu rayu tare, yafi min rayuwa da wata mace, tunda ba wani abun kunya na ke yi a yawon hawa Dokin nawa ba, sha’awa ce kawai, hobby na ne kawai yin wasan Polo.
Amma ba haka kawai rana daya kice lallai in bar abinda nafi so a rayuwata ba, wai don tsautsayi ya gitta min wand aba yau farau ba, kuma mutane suna maganar banza a kaina da ke, ina ruwana da maganar mutane?
Ko an gaya musu inada business da mutane su yabe ni ko su zage ni?
Aure ra’ayi ne, kuma banida ra’ayin yinsa a yanzu, tunda dai auren nan Sunnah ne ba farillah ba”.
Nanne sai ta zama speechless, ta rasa me zata ce masa kuma, duk ta inda tabi don Kehinde ya gane damuwarta da ciwon ranta akan rashin aurensa bazai gane ba, ta yarda kuma babu abinda zai sa AbdulRasheed barin Polo, idan wannan karairayewar da ta sameshi yanzu, basu saka ya barta hakannan ba.
Ta kuma yarda bashi da niyyar yin aure nan kusa, aure baya ransa kwata-kwata, baya cikin burikansa da fatansa na gaba, burinta na samun jikoki daga jikinsa, bata san ranar da Allah zai dubeta ya cika mata shi ba.
Wayar Murjanatu ce ta katse tunanin Nenne, ta boye dan guntun hawayen da ya tsatstsafo mata. Hankalin sa kacokam ya koma kan waya da Aunty Taiwo dake ta koka jin abinda ya sameshi ta waya tana zata taho itama yana ta zauna ai ya ji sauki, yana lallashinta da taushin murya, yana gaya mata ta san dai ba yau ya fara faduwa a Doki ba, shi nasa ciwon bai daga hankalinsa ba kamar lafiyar SAHEEB dinsa.
**** **** ****
Zaman jinyar Nenne da Fatima tare da AbdulRasheed a asibiti, ya taimaka matuka gaya wajen samun lafiyarsa da wuri, sakamakon addu’o’I na (Ayatushshifa) da Nenne takeyi kullum a ruwa tana bashi yana sha dare da rana, da kuma dorewar lafiya da take roka masa a duk bayan kowacce sallahr farillarta.
Ya fara jin sauki sosai cikin ‘yan kwanaki kalilan, har yana tashi ya zauna yayi sallah daga zaune, bakin Nenne baya hutawa da yi masa nasiha akan bin Allah da tunasar dashi soyayyar Manzonsa, saidai in basu kadaice a dakin jinyar ba.
Har ila yau Nenne bata gushe ba da nasiha sannan bata fasa ba. A kullum bata gajiya wajen nuna masa muhimmancin aure da ajiye iyali ga faein ciki da cigaban rayuwarshi, cikin nasiha da lumana, ta kan ce masa ‘ya’ya sune gatan bawa duk arzikinsa, tunda su zasu dinga yi masa addu’a a bayan ransa. Kuma su tsaya masa a sanda yake bukatar su.
Auren kuma da yakewa kallo na daban Nenne tana kokari wajen nuna masa cewa ibadah ne ba son rai bane.
Koma meye dalilinsa na gudun yinsa bai isa dalili a wurin Ubangiji ba, tunda dai ya bashi lafiya da abinda lafiya zata amfana.
Tace ana yinsa ko ba’a so domin katange kai daga sabon Allah da tsarkake kai daga daudar zinah da katange zuciya daga sha’awar aikata sabo kowanne iri ne.
Wadannan sune ire-iren kalaman Nenne Sappa ga danta Prince Abdulrasheed lokacin jinyarshi. Princess Fatima kuma ita ke bashi abinci a baki da cokali.
Yau daya gama cin abincin rana, Princess Fatima tana gyara masa filon da zai kishingida ta bayansa, a cikin tarin sumar kansa sai ta hango tsillin ‘furfura’ a cikin gashin kansa. Ta kai waje guda 20 a cikin lallausar sumar kansa, ta kuwa ce me zata yi ba sakin shakiyyar dariya ba.
Princess Fatima tasa hannu ta tsigo furfura guda daya daga saman kansa, tana dariya tana kanne ido ta nunawa Nenne, tana fadi cikin yanayi na (banter) harda neman sikewa don dariya,
“someone has finished, ooh my Dear! Getting white hair before even getting a first wife…
Nenne furfura ce fal! A kan Hamma!”. (Ta kara gishiri).
To ma yanzu sabida Allah Nenne, wacece zata yarda ta auri mutum over 40 kansa duk yaci furfura?
Ai saidai kwantan ‘yammata kamarsa dan (mid forties), irin bazawara mai ‘ya’ya biyu haka, ko widow (wadda miji ya mutu ya barta) haka dai, amma ba dai (sweet 16) ba!”.
Nenne an sosa mata inda yake mata kaikai, sai ta gyada kai tace “in ya samu sweet 16 din sai ki hana ruwa gudu! Furfura baiwa ce ‘yar nan, ba itace tsufan namiji ba, wani ma sai ya fara ta yake fara jin mazantaka da karfin samartaka, rashin aure haka kawai babu dalili shine mishkilarsa, domin tamkar izgili ne ga rahamomin da Ubangiji yayi maka Abdulrasheed.
Saidai kuma bansani ba ko abinda mutane suke fadi marar dadi a kanka din, ko gaskiyane Abdulrasheed?”
Yanayin fitar sautin muryar Nenne, a halin yanzu ya nuna helplessness din da take ciki akan situation din, wanda hakan yayi matukar karya zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi matuka, amma dai bai yi magana ba.
Princess Fatima, ganin yanayin da suka shiga na damuwa su duka, sai ta dauki ipad dinta ta bar musu dakin, ta koma can reception na asibitin ta samu kujera ta zauna tayi tagumi itama, don taga zancen na Uwa da Danta ne, kuma yau raunin Nenne da bakin cikin ta na shekara da shekaru akan rashin aurensa yafi na kowacce rana bayyana a tare da ita da nauyin shekarunta da suka bayyana kan kyakkyawar fuskarta yau saboda damuwa.
Wai AbdulRasheed ya fara furfura ba aure!!!
Wannan al’amari ya tsorata Hajiya Sappa matukar tsoratawa.
Fitar Princess Fatima keda wuya, sai ga hawaye mai kauri ya tsinke a fuskar Nenne Sappa. Kamar jira take Fatima ta gusa.
Hankalin AbdulRasheed yayi tashin da bai taba yi ba yau, ba yau Nenne ta soma korafi da kuka akan rashin aurensa ba, amma na yau yafi na kullum daga hankalinsa ko mai yasa? Don ya ga bakin cikinta muraran a idanunta.
Abdulrasheed ya shiga rokon Nenne cikin kaskantar da kai, akan ta gaya masa menene exactly damuwarta har haka akan rashin aurensa, take irin wannan zafafan hawayen dalilinsa, masu barazanar tarwatsa rayuwarsa?
“Zubar hawayenki a kaina Nenne masifa ne a gareni kin sani”.
Nenne Sappa saida ta yi sharbe son ranta, tana gogewa da habar hijab dinta. Kafin ta soma Magana cikin rauni da karaya.
“Na soma zama cikin zargi mai girma a kanka nima!
Na soma yarda da zargin da duniya ke maka, na cewa neman maza ‘yan uwanka kake yi (you are gay) shine abinda yasa ka juyawa auren Sunnahr Ma’aiki SAW baya. Haka ne ko ba haka bane Kehinde?”
Nenne ta tsatstsareshi da jikakkun manyan idannunta da suka rine kamar garwashi suke jike shatab da hawaye mai yawa.
Ko kadan babu firgita kan kalamanta a tare da shi, ko don ba yau ya fara jin ana zarginsa da hakan ba? Jin maganar yau daga bakin mahaifiyarsa shine babban abinda yafi tada hankalinsa.
Amma ko kadan babu tashin hankalin maganar akan fuskarsa sai tsantsar damuwa da yanayin da mahaifiyarsa ke ciki.
Abdulrasheed yace (cikin despair).
“Nenne in kowa zai min wannan mummunan zargin ke UWATA (mahaifiya) ya kamata ki kyautata min zato.
Ban taba zaton Nenne ranki zai yi bacin da zakiyi duba da wannan banzan zargin na mutane marar tushe da hujja ba, tunda kin san irin tarbiyyar da kika yi mun da hannunki, ba wani ya tarbiyyantar miki ni ba, kuma kinada tabbaci a kan ingancinta, na cewa ko bayan ranki bazan zubar da ita ba, balle da ranki da lafiyarki in yi wannan mummunan aiki.
Anyway, bazan musa ko daya ba, cikin abubuwan da ake zargina dasu din.
Allah ne kadai ya san zahiri da badinin zuciyar bayinSa, da abinda suke aikatawa na fili dana boye, kuma shaidarsa nake nema bata mutane ba Nenne, tunda ke kanki da kika haifeni kin kasa shaidata….…”.
Yayi shiru, ya koma ya kwanta yana maida numfarfashi da sauri da sauri kamar mai ciwon asthma. A hankali AbdulRasheed ya rufe idanunsa…. Mummunan ‘scene’ din na Hasinah da dan uwansa kuma wanda ya rika a matsayin “amini” duk cikin family dinsu Adetokumbo akan gadonsa na gilma masa. Abinda ya faru kusan shekaru goma sha hudu a baya, amma har yau yake ‘haunting’ dinsa… ‘trauma’ din abun ya kasa barin ransa ya huta, zuciyarsa ta sake da mata.
Cousin dinsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni da fiancée dinsa Hasinah Ambursa turmi da tabarya, kuma a kan gadonsa sannan a dakinsa mallakinsa a gidansa dake kasar Japan.
Wani ‘incidence’ ne da kullum yake komawa ‘GREEN’ a idanunsa… ya kasa barin duhun idanunsa su huta ko hasken wata mace ya ratsa ta cikinsu.
Shikuwa me zaiyi da mata yanzu? Ai ya dade da rufe babinsu daga kan Hasinah Bello Ambursa.
A cewarsa dukkansu are nothing but ‘Gold-Diggers’, wadanda in dai namiji zai basu kudi to ya gama samun mutuncinsu, kowanne kare da kowanne doki ma yazo ya fanshi

Please Login or Register in order to submit comment