Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan ya ji shigowar sako.ya ce,sako ne dear.ki duba ko momy din ce ko?cikin sauri ta amshi wayar.usaina ta gani.har ta ajiye wayar sai kuma ta bude.ga abin da usaina ta ce:
[01/10 10:34 pm] Abdul: (24)SIS MIMI DON ALLAH KI DAWO DAD BA LAFIYA YA FADI SABODA JIN CEWA KIN GUDU NE,BA SACE KI AKA YI BA.ANJIMA ZA A DAURA AUREN NA'IMA DA ABBAS. Ihun da MIMI ta yi ne yasa khalil mikewa. tambayar ta yake yi,me ya faru?cikin kuka take fadin, dad ba shi da lafiya.ni zan koma gida ne kawai.khalil hankalinsa ya tashi.ya shiga lallashin ta.ki yi hakuri mana dear.za mu koma ai.amma bari su neme mu.ta ce,ba ni wayata.bari in kira dad din.ya ce,aa kar ki kira shi tsaya ki ji.MIMI ta tsaya tana kallon sa ya ce,ki kira su usaina din kiji komai daga bakinsu.nan suka kira layin.hasana ce ta daga wayar:MIMI cikin kuka ta ce, usaina!hasana ta ce,ni ce ba usaina ba ce,ta ce,yanzu wane hali dad yake ciki?hasana ta ce ya ji sauki,babu laifi,amma ya kwana a asibiti ne.ya ji zafin sakon da kika turo masa cewa kin tafi saboda wani.usaina ta amshi wayar tana cewa,sis MIMI ki dawo kawai zai fi miki. dad ya ce,ba zai damu daki dawo ko kar ki dawo ba, don na'ima ta gama fitar da shi kunya,ta amince anjima za a daura aurenta da abbas.MIMI ta kasa magana kuka kurum take yi.suka nufi hajiya da wayar usaina ta ce.ga sis MIMI tana jin lokacin da hajiya take fadi me za a yi mata don ga ta a waya?abin da ya kamata ta yi ta kasa.don haka bani da lokacin sauraron ta.ubanta ma da ya nuna mata so,ta yi masa butulci, bare wani.da allah kashe wayarki!hasana ta katse wayar.kuka sosai MIMI dinga yi tun khalil yana bata hakuri,har yayi shiru ya tsaya yana kallon ta.sai da ta gaji don kanta,ta kalli khalil ni zan koma gida.ta sauka ta soma duba jakarta.zan koma gida khalil in yi wa dad dina biyayya. amma har abada ka sani ina son ka a cikin zuciyata. ya ce,ki tsaya ki ji sauki mana.ba a sallame mu ba.ta ce,ba na bukatar sai na samu sauki zan tafi.ka zo ka kai ni gurin da zan hau mota.tana daukar jakarta,ya nufi ofishin likitan,ya sanar da shi cewa wai tana son ta tafi.lokacin da likitan ya fito,ta kai harabar asibitin.suka sha gabanta,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (25)Khalil ya ce,MIMI ki saurari likitan mana.ta ce, likita ka yi min afuwa, awanni suka rage a daura min aure.ka san cewa guduwa nayi?babana ya fadi sbd na gudu.likita ya ce,na ji zaki koma,amma ki bari ki gama karbar allura. MIMI ta ce,bari in tafi.na yi nadama sosai da na bijire wa mahaifina.zan koma in ba da hakuri,in nemi ya yafe min.ya aurar da ni ga ko waye yake so. Dole likitan ya ce,ka bar ta ta tafi kawai.ba shi da zabi,dole ya koma ya dauko tasa jakar suka je titin bypas don samun motar zuwa abuja.suna cikin motar ne ta sake kiran usaina,karfe nawa za a daura auren?ta ce,bayan azahar ne a babban masallaci.mu ma hajiya ta ce,da an gama daure aure za mu koma gida.ta ce,shi ke nan sai na iso.ta kalli khalil,ina za ka tsaya?ya ce zan je har gaba mahaifinki, yayi yadda ya ga dama da ni.amma na gama hango mutuwata,in har na rasa ki. ta kalli agogo,yanzu sha biyu da wani abu,kana ganin har za mu je abuja ba a daura da na'ima ba?ya ce zan fi kowa so in hakan ta kasance.ki yi adduar allah ya sa ni ne mijinki.daya saura alhaji ya shigo gidan don shirin zuwa masallaci ko kuma in ce gurin daurin aure.daidai lokacin ne kuma hajiya binta ta shigo,ita da yaranta. mamakinta da tunaninta alhaji ya rasu ne?ko an ga amaryar ana ci gaba da biki,shi yana asibiti?ta ga harabar gida an zuba kujeri da rumfuna,ga mutane da yara.suka shiga falo.nan ma duk jamaa.dakin nafisa hajiya bintar ta nufa.cike da manyan kawayenta,tana zaune a gaban madubi,ta yo wanka ana yi mata kwalliya.hajiya binta ta ce,nafisa wai biki ake yi ne?ta mike da sauri,sannun ku da zuwa kun iso?eh,kin san tafiyar mota,tun bakwai muka fito.ban gane ba,wai bikin ake yi ne?eh bikin na'ima.cikin mamaki, hajiya binta ta ce,na'ima kuma?momy nafisa ta karaso gurin ta cikin murmushi,eh,kin san MIMI ta gudu.shi ne na'ima ta zabi ta fitar da mahaifinta kunya. hajiya binta ta ce,to shi alhajin wane asibiti yake?ta ce,ya shigo yana gefensa,zai yi wanka.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (26)Tun jiya aka sallamo shi.yana jin na'ima ta yi wannan furucin,sai ya gyare.wata daga cikin matan da ke zaune a kan gadon ta ce,yarinya ai ta share wa ubanta hawaye. wata ta ce,ai ko ta yi saa jiya maigidana ke ba ni labarin irin gudummawar da abokan kasuwancin alhaji suka yi ta ba amarya. babban dan kasuwan nan wanda yafi kowa shahara a afrika an ce zunzurutun kudi miliyan ashiri ya ba da, banda motoci.hajiya binta dai ta ce,bari in duba alhaji. momy nafisa ta ce,to ki duba shi.yawwa hajiya sauda ma suna saman MIMI to kawai hajiya binta ta ce, ta nufi sasan alhajin,cikin al'ajabi.gani take yi momy nafisa murna take yi da aure ya juye a kan 'yarta. Ta kalli yaranta ku hau saman sis MIMI,hajiya sauda tana nan.da farko har za su noke,don suna tsoron MIMI,tunda bata kula su.amma jin cewa sauda tana nan,sai suka nufi saman cikin murna.suna son hajiya don in sun zo hutu ba sa son tafiya.ta iya tafiyar da yara sosai. Ta samu alhaji ya fito wanka,ya ce,aa ku ma kun iso?ta ce,eh,alhamdulillah sam ban zaci zan samu jikinka haka ba.na ji an ce sugar,mene ne mene ne.ya ce,da sauki.da ma karin damuwar kunyar da MIMI ta so ta ba ni ce,sai kuma na'ima ta zo ta tare matsalar.yanzu dai burina a daura auren nan.zan koma asibiti,likita ya duba ni yadda ya kamata.ta ce allah ya sawwake.to,yanzu mene ne labarin MIMI? ya kalle ta.bayan ya gama saka wando,yana tura singiletinsa,ba ni da labarinta, kuma bana bukatar in sani.hajiya sauda sun zo da su abba.lna zaton suna saman.hajiya binta ta ce,to bari in ji gurinsu.ta samu su abba za su fito.nan suka tsaya suka gaisa.suka ce bari su fita su yi salla.ln an daura aure za su wuce.hajiya binta ta ce,wai ni hajiya yaya lamarin ya zama haka?ba kya tunanin cewa nafisa ta san komai a kan gudun MIMI ko bijirewarta?ba na tunani,in ji hajiya sauda.ba na zargi a kan abin da ban ji ban gani ba.abin da na sani kawai alhaji shi ne silar komai.haka nan kullum ina cikin adduar allah ya shirya MIMI.ya bata miji na gari.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (27)Ban yi fushi ba ko da aurenta bai kasance da dan gidan minista ba.kila ba alherinta.hajiya binta ta ce, haka ne allah zai amshi adduarki,domin bakin mahaifiya yana da karfi a kan yara.hajiya sauda ta kalli usaina wadda ke dube-dube a kan kwamfutar MIMI,ta ce,ku sa wa yaran nan abinci ga shi nan.hasana ta sa wa hajiya binta.hajiya binta ta ce,ni duk damuwata ta a ba na jin yunwa.sauda ta ce,damuwar me,bayan ga jikin mijinmu da sauki? hajiya binta ta ce,batan MIMI ai abin tunani ne.ko kusa,in ji hajiya sauda,guduwa ta yi,ba bata ta yi ba.kin ga kwanukan da su abba da abdulkarim suka ci?cewa suka yi tunda jikin dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci.ni ce ma ban riga na ci ba.na fi son abu mai ruwa da safe,mai kuma dumi kamar shayi.hajiya binta ta ce,ya fi dadi ai hasana sa min wainar allah ya rufa asiri.suka ce amin. Duk da gudun da motar da su MIMI suka shiga take yi,gani take yi kamar ba gudu ba.ba ta taba shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau.bugu da kari bata taba shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta.shiru da ta yi daga zaune abubuwan da take lissafawa ke nan.duk da tsananin son da take yi wa khalil ba ta jin za ta sake barin gida,ba tare da yardar mahaifinta ba.abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba.cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati,wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi lmani da shi.ta zaro idanu,lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya, sosai ta firgita,ta soma fadin wayyo allah!daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak.wai ashe taya ce ta fashe,tana duniyar tunani,bata ji kara ba.babu wanda ya zaci motar nan za ta tsaya.motoci suka tsaya ana ta yi musu allah ya kyauta.hankalin MIMI ya sake tashi.har aka canza taya jikinta bai daina bari ba.haka nan duk lallashin da khalil ke yi mata bata daina kuka ba.shi kansa yayi dana sani sosai na tahowa da ita.da kyar ma ta yarda ta sake shiga motar suka nufi hanya.karfe biyu daidai aka daura auren.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (28)Karfe biyu daidai,aka daura auren na'ima da abbas.daurin auren mai dimbin tarihi irin manyan mutanen da suka halarci gurin.babbar matsalar angon yaki halartar daurin auren,yana gida kwance,lta kuwa na'ima suna can gidan yayar mommy nafisa suna cashewa da makadan da suka dauko.sun koma can ne wai kar a ce suna murna da auren ya koma kan na'ima.wani karin abin aushin ma na'ima ita da abbas din ba su taba yin magana ko da ta waya ba. kuma daga momy har na'ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala mai zaman kanta ba ce.uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar layinsu.kasancewar layin baya fita,sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin,ga mutane ta ce,me ke faruwa?ba dai dady ya mutu ba?dan tasi din ya ce,gaskiya ina zaton ba mutuwa ba ce,sai dai biki.ta ga nisan su karasa har kofar gidan,don haka ta ce,tsaya ina zuwa.yana tsayawa ta dauki jakarta,ta zura da gudu.kofar gidansu duk jamaa.gate dinsu a bude.tana shiga da malam lsma'il ta soma yin ido hudu. mutane ba su gane ta sosai ba,saboda ita ba maabociyar saka hijabi ba ce.lsma'il ya ce,daga ina kike?ta ce,me ake yi a nan gidan?ya ce,auren na'ima ta zaro ido,an daura da na'ima?ya ce,tabbas!sai ta juya,yana cewa ke!za ta fita ke nan su abba da abdulkarim za su shigo don yin sallama da hajiya sauda don basu so su kai wannan lokacin ba a abuja.dad ne ya tsare su,wai sai an gama daurin aure.yana ta nuna su ga abokansa, wadanda a da MIMI suka sani,basu san ma yana da wasu yaran ba.sai abokansa na tun farko irin su alhaji lsa.abdulkarim ne ya gane ta,don abba ne a gaba,amma bai kalli fuskarta ba,kuma hijabin da ta sa ya kara boye ta.da karfi abdulkarim ya rike hijabinta,har ta dan gota shi.ya jawo ta ya falla mata mari.sai da ta ga wani haske,ya ce,gidan uban wa za ki koma?ta tsala ihu,wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan.lsmail ya iso gurin yana cewa a yi mata hakuri.abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. suka iza keyarta tana kuka, suna rankwashin ta,gami da zagi.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (29)Momy nafisa ta fito da gudu,domin wata kawarta ce zata tafi gida,sun yi sallama.amma tana fitowa ta ga MIMI a hannun su abba.sai ta koma da gudu ta sanarwa momy nafisa cewa ga fa MIMI.da farko momy nafisa idanu ta zaro,tana cewa,na shiga uku!me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?sai yarta ta ce,kar ki damu tayi ta dawowa.an riga an daura aure.momy nafisa ta ce, kuma fa haka ne.bari in fita in ga yadda wannan fim din zai kare.suka sa dariya gami da shewa,ita da kawayenta.ta kalli wata hajiya nana,ba ni wayata!ga ta nan kusa da ke in sanar da ubanta.ln ya zo fim din zai fi dadi kallo. shine nan ta fito da gudu.a daf da hawa sama ne ta iso ta rungume MIMI ta fashe da kukan karya.lna kika shiga ne yata?me ya sa kika yi haka?abdulkarim ya ce,momy sake ta mu je sama.sake komawa za ta yi.abba cikin fushi ya ce,ki wuce mu je mana!don shi yana jin haushin momy nafisa ta taimaka gurin lalacewar MIMI.momy nafisa ta sake ta suka iza keyarta zuwa sama. abdulkarim yana rike da jakarta.momy nafisa cikin kukan ta kira alhajin ya ce? tana sheshekar karya ta ce,ka zo gida,ga MIMI nan ta dawo su abba suna ta dukan ta ya ce,haka shi ne daidai.na gode musu.ya kashe wayarsa. hajiya sauda tana inda take zaune ba ta tashi ba tunda ta yi sallar azahar sai ko ga MIMI ta shigo da gudu.a gaban hajiya sauda suka yi mata duka.dama kowannensu yana da haushinta.hajiya binta ce ta kwace ta.ko kallo bata ishi hajiya sauda ba,bare ta yi magana.hasana da usaina sun yi jungum-jungum cikin tausaya mata ta rakube gefen kujera tana ta kuka. abba ya ce,wawiya mara hankali kin bata sunanki a duniya.kin zubar da mutuncin kaki.abdulkarim ya ce,sosai kuwa,duk yarinyar da ta gudu ta bar gidan iyayenta,ai sunanta yar lska.hajiya binta ta ce, gaskiya baki kyauta ma kanki ba MIMI.ba ki yi wa mahaifinki adalci ba lrin son da alhaji ya nuna miki,ln kina da hankali,ko wuta ya hura ya ce MIMI shiga,ba za ki yi tsalle ki shiga ba,bare aure?
[01/10 10:34 pm] Abdul: (30)Sai lokacin hajiya sauda ta yi magana,ta ce. ai shi yasa haihuwa ma da yawa take da dadi.ln wani ya saka kuka wani sai ya share maka hawaye.na'ima ta kai yar albarka.allah ya bata zama lafiya a gidana,ke kuma sai ki zauna mu gani,wanda kika bijire mawa din kika watsa masa kasa a ido,kika so ki kunyata shi zai ci gaba da jiyar dake dadi,gami da nuna miki kauna kamar da. Daidai lokacin alhaji ya shigo yana cewa,ba ta da mazauni a gidana.ta zo ta fita ta ko inda ta fito.na sallamawa duniya ita!hajiya binta ta ce,haba alhaji wannan ma ai ba mai yiwuwa ba ne.ka yi mata afuwa,ta yi kuskure.alhaji ya isa gabanta,ke khadija!na ce ki zo ki bar gidana!sunan uwata kika ci,ni uwata ta dade da mutuwa.don haka yadda kika yi min abin da ba zan manta ba.haka nan ke ma zan yi miki abin da ba za ki manta ba.MIMI ta mike ta zo gabansa tana kuka a tsugune,dad don allah ka yafe min.wallahi dad na yarda na dawo,zan auri duk wanda kake so.dad ya ce,me abbas zai yi da ke a halin yanzun?kin je kin kwana da wani ki zo ki ce kin yarda!cikin tashin hankali MIMI ta ce,wallahi ban kwana da wani ba.na rantse maka dad! hajiya sauda duk dauriyarta ba ta san lokacin da ta soma zubar da hawaye ba.su usaina suka je jikinta suna bata hakuri. abba ya ce,daddy to kawai ka daura mata aure da shi wanda ta bi din mana.dad ya sake daga murya,har abada wallahi!ba zata aure shi ba.yadda bata yi min abin da nake so ba,ita ma har abada ba zan taba yi mata wanda take so ba. momy nafisa ta shigo tana kuka,tana ba alhaji hakuri. ya ce,na yi rantsuwa,yau dole yarinyar nan ta bar gidana,ko da ita kadai na haifa.yarana ashiri da biyu. don na rasa ita kadai bana jin cewa nayi asara. Hajiya binta ta ce shi ke nan za mu wuce da ita gidana can malumfashi.ya ce,gidanki ko gidana?can ma gidana ne,don haka ba ta ba shi.ta gama cin arzikina,don ko gidan mahaifiyarta na yi mata tsakani da shi.abba ya lumshe ido,yana tunanin dad ya tsaurara da yawa.don haka ya ce,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (31)Dad shi ke nan bari mu wuce da ita,in tafi da ita gidana.alhaji bishir ya girgiza kai,ban lamunta ba.ln kuma ka yi hakan ba zan yafe maka ba.ka sa min idanu kaga irin hukucin da zan yi mata.hajiya binta ta ce,don allah alhaji ni dai kar ka ce zaka kore ta a gidanka,ka ji?momy nafisa ta shigo cikin kuka tana cewa,don allah alhaji kayi hakuri,ka yafe mata,tunda na'ima ta riga ta auri abbas din sai a bar zancen.MIMI ta zo tayi shirin komawa makaranta.cikin zafin rai,ya waiwayo,wace makarantar?nafisa za ki sa in tafka miki ashariya!ya nuna MIMI,wannan yarinya don ubanta ta gama boko a gidana,ta je tayi zaman aure.yau din nan zan aurar da ita ko ma ga uban wane ne.bana son kowa ya ce,min uffan.a kalle ni da hukuncin da zan yanke duk inda na bada ta da sunan aure.na gindaya allah ya isa ga duk wani ahalina da ya je,ko na sani ko ban sani ba.sai lokacin hajiya sauda ta daga ido ta kalle shi,duk da halin MIMI,amma da da mahaifi sai allah.ta ce,alhaji kana ganim wannan hukuncin bai yi tsauri ba?a fusace ya kalle ta,bana bukatar ki sa bakinki a cikin lamari,kamar yadda tun farko kika ce ba ruwanki ke yar shawara ce.to don allah ina son shawarar ma ki bar ta.kina da kima sosai a idona bana son mu fara abin da bamu yi a da ba.za ta yi magana.abdulkarim yayi mata alama da hannu wai ta yi shiru.don haka sai ta kulle bakinta.shi kuma alhajin ya fita yana fadin zata gane ba ta da wayo. Hajiya sauda ta kalli MIMI maganinki ke nan!hajiya binta ta ce,ni fa ina zargin cewa MIMI shigo-shigo ba zurfi aka yi mata. momy nafisa ta ce,me kike nufi?ke nan ni na sata bijirewa mahaifinta?hajiya binta ta ce,komai zai iya faruwa.yaran da suka tashi a karkashin tarbiyyarki me zai sa na'ima ta lankwasu, amma MIMI ta kasa lankwasuwa?hajiya sauda ta ce,ku bar zance nan.laifi dai duk na MIMI ne.ban ji haushin alhaji ba,duk hukuncin da ya yanke mata.da ta tsaya a kan bata so,sai ya fi mata a kan gudun da tayi.wa ya san abin da ya faru a gudun da ta yi?MIMI ta ce,hajiya ku yarda da abin da zan ce
[01/10 10:34 pm] Abdul: (32)Na rantse muku babu wani abu da ya faru da ni.ni kadai na kwana a dakin da na sauka.abba ya ce,kin dai cuci kanki da kika sa kafa kika bar gidan mahaifinki,kika bi wani kato. kuma duk sunan da aka kira ki da shi dole ki amsa. abdulkarim ya ce.alhakinmu ne yasa ta yi wa alhajin haka.don haka ni duk mai zai mata ba zan ji haushi ba.usaina bata ce,yaya ni kuma a nawa ganin tunda wannan ne karo na farko da sis MIMI ta soma saba masa da ya yafe mata,sai in ta kara.momy nafisa ta ce,yawwa usaina,abin da ni ma nake so ke nan. shi kuwa alhaji ya fita ne da niyyar ba ta duk wanda ya ci karo da shi.babu abin da ta fi tsana a duniya kamar talaka,don haka za ta dandana rayuwar talauci.har zai fita gate,sai idanunsa suka hango lsmail yana alawala,tamkar an tsai da shi ne,ya tsaya cak, yana kallon lsmail.sai ya tuna ta taba furta masa cewa ta tsani lsmail. murmushin takaici ya yi,ya ce,malam lsmail yana kan wanke kafafu,ya dago da azama ya karasa,ya mike cikin girmamawa yake cewa,alhaji barka da arziki.na ga MIMI ta dawo.alhaji yayi yake,tare da cewa,barka ka dai.wato malam lsmail kamar kai ne kake fada min an aurawa budurwarka wani ko?lsmail sam baya ko son tuna lamarin don haka sai ya ce,ni ne alhaji,amma na dangana.haka allah ya hukunta.alhaji ya ce,wane ne wakilinka wanda zai amsar maka aure?gaban lsmail ya fadi,cikin in-ina ya ce,alhaji ban gane ba.ka ce mene ne?ya ce,kar ka damu,in mu i sallar laasar ka samu ko baba maigadi ne ka wakita shi ya amsar maka aure.kar ka ji mamaki hausawa suna cewa wani hani ga allah baiwa ne.sai kawai alhaji ya wuce ya bar lsmail tsaye,zuciyarsa cike da tambayoyi,amma bai san wa zai amsa su ba. Maigadi da hamisu suka nufo lsmail suna cewa, malam lokaci fa,baka yi kiran salla ba.maigadi ya ce,kodayake alhaji ne ya tsai da shi ko?lsmail ya ce,ku ji alhaji wai in samu wanda zan wakilta ya amsar min aure,wai ko kai. su ma suka cika da mamaki.hamisu ya ce,ko cikin yan aikin gidan ne tunda ya san kayi rashin budurwarka?
[01/10 10:34 pm] Abdul: (33)Isma'il ya ce,ni don na riga nayi fushi da soyayya, don ma kar in ce na daina yin ta ne,a ce na dauka da zafi.hamisu ya ce,tunda ya zabe ka zai yi maka alkhairi kar ka ce aa,ka yi shiru.lsmail ya ce,ba zan iya musu da shi ba,dana yi tun tuni.ku taya ni adduar allah yasa in ci jarabawar don ina cikin gwaji.suka ce,amin allah ya sa ka ci. bayan sun idar da salla,alhaji ma ba a nan yayi sallar ba.kamar minti goma,sai ga alhaji da abokansa hudu da kuma kaninsa kawu shafiu wanda daki lsmail yake kwana tunda suka zo bikin.nan alhaji ya ciro naira dubu talatin,ya mika wa maigadi.sadakin malam lsmail ne.ga wanda zai ba da auren nan,ya nuna kaninsa cikin masallaci suka koma,inda aka daura auren KHADIJA DA ISMA'iI duk ba su yi saurin dago wace ce khadija ba,saboda sunan MIMI ya boye.sun fito suna tambayar juna,alhaji kuma da kaninsa suka shiga gida. daki lsmail ya shiga yana kai-komo a fili ya ce,kaddara ta kawo ni abuja.ya dauko wayarsa yana ta zufa,ya kira mahmud ya sanar da shi komai.cikin murna ya ce, allah ya sanya alherh.lsmail ya ce,ba na son wulakanci jaje ya kamata ka yi min ba murna ba.mahmud ya ce bari in sanar da malam, in kuma je gida yaya amina in fada mata.lsmail ya ce,ni damuwata ko daki ban kama haya ba ban san ma yaya zan yi ba.amma komai ake ciki zamu yi waya.alhaji kam da ya shiga ciki,shi da dan uwansa kai tsaye suka wuce saman MIMI,inda su hajiya sauda suke.alhaji ya ce,mika wa binta sadakin, duk suka zura ido,hajiya sauda salla take yi,amma sai da ta ji kamar ta fadi.momy nafisa da ke biye da su alhajin don tana falon kasa da baki suka shigo,ta ce,wane ne mijin alhaji?ya ce,zai shigo ai lna take MIMI?hasana ta ce,ta shiga cikin tana wanka.ya ce,to in ta gama ku fada mata ta shirya maza-maza alhajin ya sake sauka ya bar su nan cirko-cirko shi ma dan uwan ya basu kudin,ya fice.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (34)MIMI tana fitowa wanka,hasana tana shiga dakin ta ce,in ji dad ya ce ki shirya.MIMI ta zaro idanu, zuwa ina?hasana dai ta ce,haka dai ya ce,amma ban sani ba.riga doguwa ta zura ta zauna bakin gado tare da yin tagumi.hajiya sauda ta idar da salla ta zabga tagumi,tana hawaye,lalle alhaji.jim kadan ya sake hawowa, wai ina su abba ne?usaina ce ta iya cewa,sun tafi tun dazun.sun ce za su je suyi salla su wuce.ya sake sauka ya fita.hamisu ya samu a bakin gate,ya ce, malam hamisu ga shi ka je ka cika tankin motarka.don allah ka zo ka kai amaryar katsina.lna shi lsmail din yake ne?hamisu ya ce,yana dakinsa.ya ce,to ka je ka ce masa na ce ya shirya kayansa,ya zo ina nemansa.yan kayansa da ma basu da yawa,ya tattara su,ya zuba a jaka,ya fito ya tsaya a wajen su maigadi,shi kuma hamisu ya tafi siyan mai. Alhaji ya sake fitowa ya yafito lsma'il da hannu. lsmail ya nufi alhaji cikin faduwar gaba yana cewa,kaddara da ta same ni,allah ka duba min.ya isa gurin alhajin.ya ce,biyo ni. suka ratsa falon.har yanzu da mutane,amma sun ragu ba kamar dazun ba. matakala alhaji ya

Please Login or Register in order to submit comment