Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki yana jiransu,aisha ta rungume MIMI sis sai naji ki,MIMI ta ce,yawwa sis aisha sai kin ji ni. Tunda suka koma gida, abbas ke kiran layin da na'ima ta sa mi shi na MIMI, wani ke dagawa,duk ya damu sai kai kawo yake yi a gefen nasa,ji yake yi tamkar ya nufi gidan su MIMI ya fada mata ya na sonta. a gidan alhaji bishir kuwa bayan sun yi bankwana da juna kowa ya shiga makwancinsa, dad da momi sun shiga nasu makwancin,sai take ce masa,alhaji na ga kamar na'ima da abbas sun aminta da juna,ya ajiye rigarsa da ya dauka da niyyar sawa ta bacci ya ce,haba!!ta ce,(cikin dariya) da gaske kuwa,har canjin number ta ce min sunyi.ya kamo hannunta nafisa ALLAH yasa haka ta tabbata da sai nafi kowa murna.da na'ima ta ga aure gata,ina son mu hada surukanta sosai,ta haka zan zama na gaba a cikin masu yin dillancin man fetur,buri na in zama na daya mommy nafisa ta ce,kar ka damu,zan kula maka da wannan alakar tasu,lnsha ALLAHU har a kai ga yin auran,ya rungume ta,ke kanki kyautar ki daban ce,suka sa dariya. Abbas ya samu aisha a cikin falon su,ya sami waje kusa da ita ya zauna ya ce.sis don ALLAH ba,ta ce ina jin ka,ya ce lamba za ki bani,ta kalle shi,ta wa?ya ce kawarki,ta sa dariya, wacce kenan?ya ce.ta gidan da muka kai ziyara mana,na ga kun kulle.aisha ta ce,ok,MIMI ko lallai ka samu 'yar gaye,ka ga gefenta kuwa?ta shiga ba shi labari.yana sauraronta zuciyarsa tana kara fari.ta bashi number ya koma sasan shi.sai dai abin takaici ya kira ta kusa so biyar amma ba ta daga ba. abinda bai sani ba.MIMI bata daga number din da bata sani ba,don haka tana kallon wayar tana yi tana katsewa.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (74)Sake komawa ya yi hankali tashe gurin aisha yana tuhumarta cewa bata bashi lamba daidai ba.ta ce,bari in kira ta da layi na,a ringin na hudu ta daga ta ce,hello sis aisha ya ya aka yi?lafiya lau in ji ta,bros ne yayi ta kira baki daga ba,shine ya zo ya tare ni wai na bashi number ba daidai ba.ta ce ok dama shine?ayya ban sani ba tsari na shine bana daga bakuwar number, amma zan yi saving dinta yanzun nan,ta ce to zai kira ki,MIMI ta ce babu damuwa ya kira kawai. Sasan shi ya sake komawa,sanna ya kira ta,sun gaisa bai tsaya bata lokaci ba ya ce,MIMI kin tafi da dukkan tunani na,tun da na ganki naji gaba daya na birkice,ke ce matar dasu dad su ka ce in nemo, lokacin da suke min maganar aure,ke kawai nike kallo a amaryar.MIMI ta yi shiru tana jinsa,sai da ya kai aya sannan ta ce kayi hakuri da abinda zan ce yaya abbas.gaskiya ina da wanda ni ke so sosai,ban san adadin son da muke yi wa juna ba.don ALLAH kayi hakuri saboda gudun faruwar haka na bar falon don na lura da yawa satar kallon da ka ke min,amma ina me yi maka adduar samun wadda tafi ni.sannan zan baka shawara ga kanwata na'ima,bata tare da kowa, kuma tana da hankali,ya katse ta,ki bani lokaci in zo muyi maganar daga zaune. ta ce kowane lokaci ina gida,ya ce,in zo yanzun?ta ce a!haba dai mu barshi gobe.sannan sharadi kar ka zo da batun so na kazo da batun kanwata,yayi 'yar dariya,sai dai in na zo din,ta ce shikenan. Misalin shadaya lsmail ya nufi gurin karatunsa kamar kullum,ya jira sannan ta fito,haka nan ya bude kur'ani yana karantawa kamar yadda ya tsara.ya gama ya kalle ta,gaskiya ya kamata yau ki karanto in ji,ko kina rikewa tunda kin ga mun kammala shafi biyu na suratul bakara,sai ji amma a ce kullum ni zanyi karatu,ke kina danna waya don ban sa ran cewa kina ji ba.ta ce,in fahimta,ko kar in fahimta ya shafi albashinka?don haka kayi kawai ina jin ka dama aya biyar yake yi kullum,don haka ya karanto mata ko daya gama ya dago ya kale ta daidai lokacin..
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (75)Wayarta ta yi ringing,ta daga tare da cewa,brother abbas,ya na'am gani nazo fa,ta ce,ok ka shiga mana,na'ima tana nan a falo ka ce ta kawo ka falon baki na ciki.ya ce, ok to,lsmail ya kalli agogo abin haushi yanzun shadaya da rabi saura minti talatin. Bako yayi sallama lsmail ne ya amsa da ya shigo,sai ya mika wa lsmail hannu.shi ma ya miko masa kenan za su gaisa MIMI ta ce,aa yaya abbas,kar ka hada hannu da shi,abbas ya dakata sannan ya kalle ta lafiya?ta nuna ma shi gurin zaman,zauna kawai,lsmail ya bude kur'anin shi ya ci gaba da karantawa a zuciya,sai dai kunnansa yana gurinsu.ta ce,dan aiki na ne,kana dan minista zaka hada hannu da talaka? ni da zai koya min karatu ma na ki ya ji karatu na don bai kai matsayin ba, sai kai ka hada hannu da shi,kodayake mu bar zancan shi,ka iso lafiya?ya ce,lafiya lau,da farko ai na zaci shine na musamman din naki,ta ce,shishshhh haba mana abbas ka cuce ni,daka hada khalil da wannan,don ALLAH ka bani hakuri don ka cuce ni.abbas ya ce,to shikenan yi hakuri,amma so ba shi da haka,kuma wannan din ban ga laifinsa ba,ta ce zan hau sama in kana irin wannan zancen,ka yi abinda ya kawo ka. Abbas ya ce,ok na san jan ajin ku ne na mata shi ya sa kika ce min kina da wani,kar ki damu da jan aji don kina da ajinkin MIMI.tun ranar da muka zo ban kara sukuni ba don ALLAH ki duba ni.ta ce,yaya abbas don ALLAH ka bar zancen nan,ni da khalil mun fi shekara daya muna tare, shi yasa tun jiya na ce kar ka zo da batun nan,ka zo in ba ka kanwata na'ima.ba laifi in ka ce mu zama abokai,mu dinga ba juna shawara,ya ce,MIMI ni dai ke ni ke so,ta sa yatsan ta a kan lebenta ta ce shhhh, don ALLAH bar zancan,ka amince da batuna, bari ka ga na'ima,tana da kyau kuma ga hankali. Kafin ya ce komai ta danna kiran layin na'ima,ba ri ka ganta da kyau,na'ima daidai lokacin tana dakin momi cikin damuwa tun zuwan abbas da ta nuna mashi falon baki kamar yadda MIMI ta umurce ta. dakin momy nafisa...
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (76)Momy ta ce dama na san zai zo,na'ima ta ce,ai gurin sis MIMI yazo. gaban momy ya fadi ta maimaita cewa,gurin MIMI? na'ima ta ce,suna ma falon baki,momy ta yi shiru tana tunani,can ta ce,ni wai yaya zanyi da wannan shegiyar MIMI?wayar MIMI ce ta katse su ta dubi momy,ga MIMI tana kira na,momy ta ce,daga muji,MIMI ta ce,sis na'ima ki kawo ma bros abbas abin sha ta ce,ok gani nan.ta kalli momy,wai in kai masa abin sha,ta ce maza je ki kai masa,har ta fita,ta kwalo mata kira,zo na'ima ta ciro wani turare a jerin turarukanta ta fesa mata sosai,ta ce,je ki ko babanku na fesa turaran nan yana sa shi nishadi.a falo ta ajiye dan kwalin kanta,a ranta tana fadin in gashi ne ni ma akwai. Da sallama ta shiga falon,nan ma lsmail ne ya amsa,wanda ke zaune yana jin komai,ta shiga ta aje,sannan ta sake gaida shi,MIMI ta ce,zuba masa a kofi na'ima ta zuba,sannan ta ba shi a hannu ya amsa yana ta kallonta,sai da ta tafi sannan ya ce,MIMI kuna da bambamci da yawa, kyau kuma ba irin daya bane,ina son ki don ALLAH. MIMI ta ce,in baka amince da na'ima ba to ka tafi ka nemi wata,na yi haka ne don na san iyayanmu za su yi murna.ya ce,ni da ke zasu yi murna,ta ce,to abinda ya yi ni,shi yayi na'ima,ya mike,ke da ita akwai bambamci,zan tafi amma fa ban hakura ba. Ismail dariya yayi ta yi a daki tare da tausaya ma abbas,don ya san menene so,in ya tuna zainabun shi, kila ma in ya ci wata daya sai ya je katsina ya ganta, ya sai mata waya don ya dinga jin muryarta kowane lokaci. MIMI tana cikin damuwa,sam ba za ta so zancan nan ya kai gurin dady ba,domin zai so hakan. tun bayan tafiyar abbas MIMI take sake-sake. momy ta hau sama ta sami MIMI tana ta tunani ta ce, na'ima ta ce min abbas ya zo gurinki,MIMI ta bata rai,ya zo ne ya dama min lissafi momy,wai sona yake yi.gaban momy ya fadi,ta dan zaro ido,sai kuma ta wayance,mene ne,to ki amince kawai.MIMI ta ce, gaskiya momy ina da wanda ni ke so,momy ta ce,haba da gaske?ta ce, ALLAH,sunan shi khalil..
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (77)Khalil,su 'yan kaduna ne,baban shine dan takarar da aka tsayar a jihar kaduna zai yi takarar gwamna.sunan mahaifisa usman kaura,haifaffan zariya ne.momy ta ce,to shawarar da zan ba ki ki yi saurin sanar da dadinku kafin shi ya sanar da na shi mahaifin. MIMI ta rike hannun momy,don ALLAH momy ki taimake ni ki fada min yanda zan fada masa. momy ta ce,kar ki damu in ya dawo ki same shi ki fada masa,inda hali ma ki ce da yaron ya zo ya gaida shi.MIMI ta ce,ai tsoro na kar dad ya ce masa ya turo iyayansa,to shi kuma karatu yake yi,gidansu ba za a yi masa aure yanzu ba,sai ya fara aiki.momy ta ce,ba damuwa don wannan kin san dadinku bai son damuwarki,ba zai takuraki ba.MIMI ta dan ji sanyi a ranta,ta kuma yarda duk abinda take so, shi mahaifin ta ke so. Abbas ya zauna kusa da mahaifinsa alhaji akilu bala ya ce,daddy na ga irin matar da ni ke so.ya tattaro hankalinsa ga dan nasa,'yar gidan waye? abbas ya sunkuyar da kai, gidan da muka je ziyara, gidan alhaji bishir masari. alhaji akilu ya dafa kafar danshi,yaro kayi abinda nake so,ka san buri na?mu zama surukai da shi,abbas ya ce,saboda me daddy? ya ce,saboda siyasa ta abbas,duk dan siyasa yana son hulda ya mutum mai jamaa.alhaji bishir babban dan kasuwa ne yana da mutane fiye da zato ka, lokacin da ya bukaci hulda da ni sai da na bincika,ka taimaka ka samo min soyayyar 'yarsa mu zama surukai.yana tare da mutanan da in suka goya min baya zai yi wuya ban dare kujerar shuganbancin kasar nan ba.abbas ya ce, na yi mata magana ta ce tana da wanda take so, amma ina zaton jan aji ne, don ALLAH kayi wa mahaifin ta magana. babbar na ke so,alhaji akilu ya ce,kar ka damu yanzu zan kira shi. Sun gaisa da alhaji bishir ya ce,ka samu hutu kenan mu kawo ziyaran,alhaji akilu ya ce,danka ne nan ya fiti ne ni wai tun da mun ce yayi aure,shi 'yar uwarsa yake so MIMI,tunda muka kawo ziyarar nan ya kasa sukuni.alhaji bishir cikin matukar murna ya ce,masha ALLAH.......
[01/10 12:47 pm] Abdul: (78)


ka fada masa kar ya damu, mimi ta zama ta shi don na bashi.
nan Alh akilu ya hau godiya cikin murna, Abbas cikin murna ya rungume mahaifin sa.
Alh bashir ya kosa ya iso gida don yayi Albishir ga mimi da momi nafisa, lallai burin shi zai cika.


Alh lawal ya kalle direban shi, yarin yar nan ba zata bamu hadin kai ba, dan haka kayi min sallama da maman ta.
haka kuwa ya rangada sallama, kaninta ya leko ya ce, yauwa ka ce Alh yana sallama da maman ku, yaron yace inannar mu...?
ya ce, eh, ka ce inji Alh lawal.
ba da jimawa ba, innar su zainabu ta fito, tamkar marokiya, haka take tayiwa Alh barka da zuwan ka ka iso lafiya, sannu sannu.
ya fito ta durkusa bari a yi shin fida a zaure, ta mike ta koma cikin gida da gudu.
daga gani Alh wanan yar raka yarima ce a sha kida, suka yi dariya tamkar ba direba da uban gida ba.
to direba za a kirashi ko kawali, tunda shi ne me kawo ma Alh mata.
suna zaune a kan tabarma a zaure, Alh ya ce, inna na zone akan maganar aure, zainabu taki bani hadinkai in turo manya ns, sai fada min take tana da wanda zata aura.
inna ta cefke zancen da cewa, karya ne bata da shi, ka turo kawai, ya ce, to na gode.
ya ajeye daurin yan dari biyar-biyar, inna ga wanan kyaci goro, kuma zan turo manya na gobe, bana son bikin ya wuce sati uku.
ta ce, ai kuma lokacin bamu shirya ba, Alh kasan sai min nemi na gado.
ya ce, ina da ko mai inna, mata na ce ina so, kuma ita za a bani ba tarkacen kaya ba.
ta ce, to shike nan, in gobe kake so a daura bare nan da sati uku.


tirkashi!!! ku biyuni a kashi na biyu don jin yadda zata kaya.
taku halima k/mashi.
ina sauraran ku,08081165107
dan shawara ko kuma korafi na gode...."" Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment