Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka shinfiɗa blanket a kasan gadon nan , ka kwanta..,
to zanyi haka..yanzu zan tafi nayi wanka ne na shirya sai na dawo..
Najlah tace '' nima zan yi wanka..sai nayi fitsari,
to ya faɗa yana daukar ta toilet ya kai ta ya nannaɗe mata riga ya saka ta akan masan zama riƙe shi tayi gam tana kuka tace '' yaki zubowa wallahi ciwo wayyo Allah na Hajiya ta wayyo aunty Hafsah wayyo Abba wayyo aunty rafi'at...,
yau jawad yayi dana sani yafi sau nawa , gaba ki ɗaya ya damu kan'sa ganin halin da take ciki daman, ga ciwon najlah raki, ya lafiyar kura ɓalle tayi zawo hakuri ya rage mai shi yanzu wannan yadda ake faɗar ciki idan ta samu besan ya zai ba..,
kwata kwata be dauki abin haka ba , jawaher tayi amma be kai na , najlah ba.
dakyar ta cije tayi fitsari. fita yayi tai tsari sannan ya dawo ya haɗa mata ruwa ya fita, cikin sauri yake hawa sama dakin sa ya shiga da sauri ya dauki wayar sa ganin ana kira number inna ce , ɗagawa yayi yana karawa a kunne yace '' Assalamu alaiki..,
haba Jawad ina ya ban ka sallah zaka , kasa alwala tun jiya da ka saka, kafa ka tafi yarinyar nan , na cikin mawuyacin hali ko a jikin ka shi ne baka dawo ba tun safe nake zuba ido ganin kai baka san zuru ba shi ne na kirawo wa ka barni tun kayan da na zo dasu jiya..
dafa kan'sa yayi yana cewa '' inna kiyi hakuri wallahi Allah aiki ne yayi min yawa , bawai ina sane naki zuwa ba insha'Allahu gobe zan kawo miki ya jikin nata..,
uhmm da sauki anma ce a siya wannan maganin aeropin paracetamol..
kudin su dubu biyar..
dan jim yayi yana mamakin son kudi irin nama matar nan komai a asibitin bayarwa suke sai dai kawai su cira a kudin ka shine take mai wannan lissafin amma saboda ita din uwa ce sai yace '' insha'Allahu idan nazo zan baki..,
yauwa sai anjima ko bari su gaisa ba suyi ba dariya yayi kai idan da ranka zaka sha kallo banda kudin data kwace shi ne yanzu take neman dubu goma..
shiga toilet yayi ya cire kayan sa , ta sakarwa kan'sa shower tana rufe idon sa , wani irin sanyi yake ji na ratsa shi da nutsuwa, albarka kuwa shi kansa besan iya adadin da ya sakawa najlah ba...
★★★.
buɗe maltina tayi tana cewa mutuwar wani tashin wani rabon naci nawa kason Ubangiji ya kawo ni nan , Allah ya hana jaburu zuwa domin ɗazu yace besan me take kullawa ba zai zo ayi komai dashi tasan son zuciyar sa , jaburu a yanayin satar sa ko mutum ya samu damar sacewa sacewa zai yi , idan yazo nan shikkenan tata ta kare wuf wuf zai yi ya dinga kwashe komai da sauri ta dauki waya tana kallon jawaher tace '' wallahi jawaher idan jaburu yazo tofa komai ya tsaya min gwara na saka yar ɗagwas ta hana shi zuwa..
da kallo jawaher ta bita domin tun ɗazu take mamakin INNA har karyar da tayi tana jin ta kash bata san wane ya faɗawa INNA wannan maganar ba.
ta kwaso jiki ta tawo gashi nan ko ɗazu sai da sukai fada da wata nurse ba'a isa a faɗa mata gaskiya ba sai tahau tijara yawa a gidan dambe aka raine ta.
juyar da kai tayi dakyar tana fatan Allah ya kawo jujal yayi gaba da ita ko nawa ne zata bashi ya tattara ta su koma BINYERI.
uhmmm kyayi kya gama sai wani kallo kike bina dashi wallahi jawa da ace ba'a gida na haife ki ba ta tabbas ce wa zanyi chanza min ke aka yi duk wani take taken ki ina lura tun jiya sai wani hade rai kike kina fici fici da ido, kamar kwallon a gwaluma ke daman ido ba ido ba..
karawa wayar tayi a kunne tace '' yauwa yar ɗagwas wani temakon za kiyi min kina jina naji kinyi shiru alooo aloo aloo (Hello )
ciro ta tayi a kunne dubawa tayi ashe ta , ta goce mita ta dinga yi tana ci gaba da shan maltinar ta,
wata gyatsa tayi ta miƙe kafafuwan ta , tana cewa malam yaso yi min tsakiyar da babu ruwa ya cuce ni , ina can a zaune ko ficika baki san ki turo mib ba gaskiya jawa ban san inda kika gado wannan bakin halin ba..
ta fadi haka gana ƙoƙarin zira batirin wayar ta , ta

★★★

fitowa yayi daure da towel a kugun sa da wani kuma a hannu yana tsane gashin kansa zama yayi akan dressing mirror chair yana dauko mai ya soma shafawa zuciyar sa na gurin najlah ko yanzu ta gama zai je dai ya gani..
shaf shaf ya gama ya zura wando three-quarter daukan blanket yayi ya dauki wayar sa ya fita samin ta yayi a ƙasa daga ita sai toilet tana jan ajiyar zuciya..
ajiye kayan hannun sa yayi yana durkusawa yace '' har kin gama baki jira nazo na dauke ki ba..?,
habawa najlah firgita tayi ganin sa ba kaya da sauri tayi baya towel din'ta ne ya kunce ba karamin gigita tayi ba da ganin sa da tayi ba kaya, jikin ta ya hau sama zikiri
JAWAD da sauri ya riƙe ta yace....


Alhamdulilah ayau na kawo karshen book 1

Wannan litattafin na kudi ne 1k

8141785374
Amina alhasan Muhammad opay

Turo da shedar biya ta wannan number 09061890481

Idan baki shirya ba , karki min magana dan Allah
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment